Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

an kawo min yarinya gida danginta sun dameni da zuwa gidana,Siyama tayi Shuru tana ta kallon Ahmad Kamar zata cinye shi,gefen Bash ta zauna Tace lemo kuke Sha ne? Kallonta Suka Yi Suka sake kwashewa da dariya,Bata hakura ba Tace Kai dama na sanka ma Brown ake ce maka ko ta nuna Mubaraq Brown,Siyama a ranta Tace Kan uba Taya Zan samu ko number Daya daga cikinsu ne? Tana wannan tunanin sai kuwa Jibson Sarkin son Mata yace Yan Mata kin hadu fa,Siyama tayi murmushi hankalinta na Kan Ahmad,Jibson yace da Allah bani number dinki Mana,ai da sauri Siyama Tace to dama abinda take so kenan ta kulla alaka da wani a ciki ko zata samu hanyar Shiga jikin Ahmad ta Haka,ta Bawa Jibson number ya Kira ta Nan take tayi Saving tana cewa ya matar gidan Bata kawo muku girki bane?

Abdul Tawaga yace ta fita fa,Cab Miji yayi Baki Amma matar baza ta kawowa abokan Miji abinci ba wannan wacce irin mace ce,Ahmad ne ya kalli Siyama kadan ya dauke kai,Tace Bari ta dawo ai dole ma na tayata ta shirya muku better,Jibson yace da kin kyauta Uwar Kinibabba,Siyama ta kalleshi da sauri Wato itace Kinababba,yace dama yunwa muke ji,suna Haka sai ga Aamna ta dawo da fara'a tayi Sallama.

Siyama ce Kawai ta amsa itama da fara'a Tace kawata kin dawo kenan,Aamna ta mikawa Siyama Hannu Suka tafa tace kinsan Ni jinin Larabawa ce Zan koma na tuno da Dan larabcina na Islamiyya Marhababiki ya Siyama,Kyaifal Ummati? Siyama tana Dariya itama da kalkala Tace Alhamdulillah...Alhamdulillah,Shukran cewar Aamna,Kujera ta nunawa Siyama tare da Furta Ijlis kawata,Siyama ta koma ta zauna tana cewa jalasna ya kawata,duk sai da suka Bawa su Jibson Dariya,Ahmad Kam Kawai Dan Baki ya tabe sabo da shi Yana mugun Jin larabci Dan Basu Sani bane.

Zama Aamna tayi itama,Siyama Tace Hauwa'u kuwa tace tana Gaida ki,Hauwa'u Yar class dinmu,na Gane ai kice Ina Amsawa na gode,Siyama da larabci tace Ma Fi mishkla,ya kamata mu shiga kitchen ayiwa abokan mijinki girki Bai kamata su zauna da yunwa ba,ya kike Abu kamar Baki San darajar mijinki da abokansa ba,Aamna Bata kawo komai a ranta ba Tace Kuma fa Haka ne muje to ki tayani.

Kitchen Suka Shiga Siyama tana ta wani kwarkwasa Wanda take Yi Dan shi Bai gani ba su Jibson sune Suka bita da kallo suna Hadiyar yawu.
Fried rice suka Yi hadaddiya taji hadi da soyayyar kaji,ga zobo sun hada me Dan Karan dadi,salat ma an hada daban,a Dining suka shirya komai tare da gyara ko Ina sannan Siyama da Shishigi tazo Tace mun Gama guys gashi can a Dining,Ahmad Bai ko motsa ba sai su Jibson ne Suka zagaye abinci suka far Masa,kafin kace me sun cinye komai suna Santi sun shanye komai,Siyama tana zaune a cikinsu Suka ci tare sai taga Aamna ta fito da katon tire da wasu miyagu food flasks na musamman komai ta jera a Gaban Ahmad kasancewar tasan Bai zuwa Dining side.

Serving dinsa tayi komai ta zauna a gefen kafafunsa tace tashi kaci Abincin,Siyama ta Bata Rai tana daga can Dining ta tsura musu Ido ranta a bace tana Jin Ina ma itace a wajen Ahmad Haka ba Aamna ba,Abinda Aamna ta fuskanta Kamar Bai da lafiya kwana biyu tunda yayi zazzabin Nan,Bata San tsabar kwayace ba take sashi Yana slow.
Ka tashi please tun safe baka ci komai ba,Ahmad yaki tashi,Siyama ta saki murmushin Jin dadi,a hankali Kuma da ya gaji ya Mike tare da Zama ya saki jiki sharaf yayi wani Slow ya tsaya a Haka yaki Kuma magana.

Aamna tasa spoon ta ebo abincin Tace to Bismillah,kamar bazai karba ba sai Kuma Yaja Tsaki tare da bude bakin kadan Tace ka Bude Mana ya Dan Kara budewa ta zuba masa,Kamar Yana tauna madaci Haka yake ci,a hankali yace kice waccen Yar Uwar Taki ta bar min gida kallo na take Yi bana son kallo,Dan kar ya fasa cin abincin Aamna Tace to Bari ka Gama cin abincin tana ta bashi a Baki Yana ci sai uban Tsaki yake ja,ya ci da yawa yasha Zobon ya daure Fuska Kuma yace cikin tsawa ta bar gidan Nan,ba Aamna ba Siyama ita kanta sai da ta firgita ta Mike ba shiri,ya kalli su Jibson yace daAllah kuje Ina son Zama Ni Daya Yana magana ya girgiza kitsonsa,gaba Daya Suka ce an Gama sarki Suka kwashe kayan mayensu Suka Yi gaba,Siyama ta kalli Aamna tayi murmushin yaudara Tace kawata na wuce,Aamna ta Mike ta saka Hijab Tace muje na rakaki,har bakin Titi ta raka Siyama,ta Bawa Siyama dubu Uku tace gashi kawata kiyi kudin Napep.

Siyama ta karbe Tace na gode kawas,Aamna Tace kiyi Hakuri da korar da ya Miki wallahi banji Dadi ba Amma Kinga ba yanda zanyi da shi idan kin dawo next time sai na Bude Miki kayan lefen Nawa ki zabi abinda kike so ciki,Siyama ta washe Baki Tace na gode kawata ai na matsu na fara daukan wanka zanzo jibi sai na zaba,Aamna Tace ba damuwa Amma me kike ganin Zan bawa Zuhra itama?Siyama ta daure Fuska Tace zuhran data auri me rufin asiri uban me za a bata,irin mu ai mune muke bukatar taimako,Aamna Tace haba Siyama ya Zaki canja Hali Allah ya Hana mutum zaiyi Alheri ka Hana hakan,ko mutum Yana tayar da Kai da million ai Alheri Dadi gareshi Kuma ma ai kamar Yar Uwata ce tare Muka taso itama abinda take so zata zaba,me Napep ja muje dalla cewar Siyama cikin Fushi,Dariya Aamna tayi ta juya gida,tana zuwa ta tura Kofar palon taji Gam an rufe,tasan Ahmad ne ya rufe Wato Bai so ma ta shiga Kar a takura Masa,Murmushi tayi Kawai ta Danna door bell har ta gaji Bai bude ba,a bakin Kofar ta zauna ta zuba tagumi Tace kaddara kenan,Allah ya jarabce ni,Kwalla ce ta cika Idonta taf.

Wasa Wasa har Magriba tayi Bai Bude ba sai jikin tap taje Wanda ke Garden tayi Alwala tare da Gabatar da Sallah a Nan tayi har Sallar Isha sannan ta dawo tayi bugun duniya Ahmad Yana can Yana baccinsa yaki budewa Kawai Kuma Yana sani yayi haka..
A bakin Kofar Aamna ta zauna tare da jingina da jikin bango a Haka bacci ya kwashe ta,har 9am lokacin Kuma Mama da Baba sunzo kawo Mata Ziyara,a Nan Suka hango ta,Mama Tace cab ga Alama mun gani Aamna Bata cikin Jin dadi,Baba yace Yar jakar uba gwara duniya ta koya Mata hankali ko ta koyi darasi,gida har gida sai Takaici a ciki,Allah yasa ba Zuhra bace a wannan halin, Mama ce ta taba jikin Aamna da Kalar tausayi Tace tashi Aamna,firgit ta farka taga gari ya waye sai Rana ta gani kwall a kanta,Salati tayi ta Mike tsaye cike da kunya Bata so su Baba suka ganta a wannan halin ba sabo da tasan zasu shiga damuwa.

Baba yace Ashe yau za ayi yaki a gidan Nan,yata Dana rike da Hannu na muka Raine ta in dauka in bada ita Amana Amma a wulakanta min ita Haka karya ne wallahi,ba a haifi mutum ba,Baba Yana bala'i ya kaiwa Kofar Naushi zai daki kofa Mama ta kifta Masa Ido tare da yin wuf ta damko hannunsa tana Haba Baban Aamna da Zuhra Haba,gidan suruki ne Bai kamata ba,Abi komai a Sannu,Aamna tana Jin tsoro Ta durkusa a kasa tana rokon Baba tana Dan Allah Baba kayi Hakuri ka rufamin asiri,Kayi min Rai Baba wallahi idan kuka tafi Ni zai duka,dukan tsiya zai min,a hakan ma ya muke karewa kusan kullum sai ya dakeni,Dan Allah Baba ku tafi gida Ni zanzo,Kamar gaske Baba yace Ina ai wallahi yau sai na Kira Uwarsa da ubansa Akan Haka baza mu lamunci wannan ba,Mama tace ai batun tafiya gida Bai taso ba akwai abubuwan da mukazo tattaunawa da yawa sannan Kuma yau a Nan zamu yini muci mu koshi muna Nan har sai ya Bude Kofar,Aamna ta dafe Kai Tace wayyo Allah na Shiga Uku,Baba Kar ya wulakantaku a gabana bazan jure ba sai dai ya kashe Ni a kanku Dan sai na Rama,Ashe akwai hargitsi da balbalin bala'i kuwa yau a gidan Nan cewar Baba ya nemi waje ya zauna daram,Mama ta gyara Mayafinta ta zauna itama,Aamna kuwa Tap ta nufa tayi Alwala tayi Sallah sannan ta dawo wajen,Suna zaune sai Suka ji baram an Bude kofa da karfin tsiya,kamshi ne na daban ya daki hancinsu,Yasha wata jallabiya Brown Yar tsangalalliya Takalminsa flat Brown yayi kyau kace baya Shan komai,Fuska ya sake daurewa ganin Dangin Aamna,Tsaki Yaja da karfi ya furta sai kace Uban tsohonki ne ya Gina min gida,Kun da dameni da wannan tsofaffin Banzan,Aamna Tace wallahi ba sune tsofaffin banza ba sai dai in naka ne na banza na wofi.

A fusace ya juyo Yana huci yace Mummy na data auro min ke wacce ta nace tana sonki kika zageta yau? Jikin Aamna ne yayi sanyi Tace ai ba da ita nake ba Ni,ko kaji nace Mummy? Mummy ai na fika kaunarta Aamna ta wayance Kar yaci ubanta,Baba ne yayi karfin Hali yace ae da ita ake din sai me? Aamna Tace Ni bada ita nake ba Baba,Mama Tace Iyyee.....Juyawa Ahmad yayi yace Zan dawo gidan Nan zamu hadu ya Haye machine dinsa ya bashi wuta sannan ya dage kafa Daya sama yazo har Gaban su Baba ya kotse machine din tare da bashi wuta ya bulbulesu da hayaki ya fita a tsiyace.

Aamna ce ta daka tsalle tare da nuna Bayan Ahmad da yatsa Tace sai nayi maganinka zaka dawo ne sai ka sani,sai na cije ka wallahi a gadon baya,Iyayen Nawa zaka yiwa haka,zaka San ni Yar halak ce.

Mama Tace ke dalla rufe Mana Baki, banza matsoraciyar banza kin Gama cika Mana Baki gashi a gabanki ya ci Mana mutunci Baki ce komai ba sai da ya tafi,Baba Kuwa Takaicin Aamna yasa yace tir dake Aamna muje ciki mu kiyi Mana girki muci mu Sha.












AsmaBaffa
10/26/21, 8:52 AM - A Maryam: 🌵🌵DUNIYA TA🌵🌵







31-35







FREE PAGE














DUNIYA TA IS DEDICATED TO GARBA BUTALAWA FAMILY.









NA KUDI NE

GA MASU BUKATAR SHIGA GROUP DARI BIYU 200 NE.


ACCOUNT NUMBER
0175487861
ASMAU GARBA MUHAMMAD
GTBANK

MASU TURA KATIN MTN KO VTU GA NUMBER
08033933642

YAN NIGER KU NEMI WANNAN NUMBER
+227 90 79 59 39







Official







By
AsmaBaffa










Page naku ne

MAMAN MURTALA
HAFSATOU
'YAR BAIWA
INNARO
AISHA
SALIHU UBAIDAT HARUNA











Aamna da sauri ta fada kitchen sabo da so takeyi suyi sauri su tafi,babu Bata lokaci tayi musu farfesun kaji,ta musu jallof din taliya Tasha kifi da kayan lambu sai lemuka da ruwa ta kawo musu,Suka zauna Suka dinga kwasar girki, Baba Yana yin Loma Daya yace Allahu Akbar sai na tuna da Uwar dakina Dake Kano Hajiya Sahura lokacin da aka kaini almajiranta na Zama Yaron gidanta,Haka take dafa Taliya Malam Kamar daga Otel(Hotel),Mama Tace taji tarihu kaga inda tsiya tayi tafiyar dogon zango,ai a Nan gidan Tsiya Balaguro tayi ba tafiya ba cewar Baba,Aamna tana ta dariya Tace ai kudi yake bani da yawa,kwana na Daya na fara fita,ba ruwansa da wani Ni Amaryace inda Naga Dame nake zuwa,Baba ya tsurawa Aamna Ido yace indai akan irin wannan cefanen ne ki dinga ficiwarki daga Nan ki dinga biyowa ta gida kina yaga mana.

Sai da suka koshi,Baba yace zuba min wani farfesun a flask na tafi dashi idan munje gida zamu ci da breadi,Aamna cikin sauri ta samo flask karami ta kwashe ta bar kadan ta hada musu harda lemuka,cikin lefenta ta dakko wata atamfa da turaruka ta bawa Mama atamfar turaren Kuma ta bawa Baba,Sai Jin dadi sukeyi,Mama ta zuge Jakarta ta sake zaro wata laya da guru na damtse ta mikawa Aamna Tace ungo Bude Damtsanki ki daura wannan,Aamna ta Bata Fuska kamar zatayi kuka Tace Mama Kinga fa wani a hips Dina kince idan na cire Baku yafe min ba Haka kaina layu ne fa har biyu idan zanyi wanka nake cirewa Ina Yi nake maidawa Kamar yanda kika ce shima Kar na cire,Mama ta Bata Rai Tace saka wannan layar a gashinki itama ki soketa ga pin Nan a jiki Kuma wallahi kika cire Bamu yafe ba,Aamna ta karba ta soke Laya ta Uku cikin gashinta,ta dauki guru ta bude farin damtsenta ta daura,Dake tana da haske sai ya Mata kyau.

Mama Tace to Haka ake so,sai magana ta karshe zamu Kira surakanki a waya mu fada musu kina cikin wahala zamu dauke Yar mu idan suna so ki zauna sai sun turo Mana kudi sabo da Haka ko sun kiraki sun tambaya kice Haka magana take wallahi idan kika ce ba Haka ba kinji mun rantse sai kin bar gidan Nan ta karfi sannan sai Kinga matakin da zamu dauka a kanki.

Aamna tace Haba Baba Wai me yasa kuke Haka ne,Ni fa ba sonsa nakeyi ba,Kuma ma Ni Nan gaba barin gidan zanyi Akan me zaku karbar Musu kudi,a gidan Ubanwa Zaki bar gida? Sai mun Gama kwasar rabon mu tukun yarinya,Shuru Aamna tayi Tace shike Nan to kuje Allah ya kiyaye Hanya na gode,sauri takeyi su tafi Kar ya dawo gidan,Mikewa sukayi ta rakasu Suka tafi,Suna tafiya ta dawo ta hau gyaran gidan sai da ko Ina ya fito fes sannan taci abinci ta sheka wanka tayi Sallar Azahar,Kwalliya tayi cikin wata English gown silk maroon,me Hannun vest tayi mugun Mata kyau ta fito da shape dinta matuka,Fitowa tayi ta koma kitchen ta duba farfesun data ragewa Ahmad,Sai tayi cabbage soup ta Sha kifi tayi sakwara,me Gadi ta bawa sauran ta Ajiye ta zauna a Palo tana kallo,Bayan tayi Sallar la'asar tana karatun novel a Wayarta taji ya shigo Yana waya yace Daddy Kuma me ya same shi? Yana asibiti? Bazan zo ba Allah ya bashi lafiya ya furta tare da Zama a saman kujera ya rufe Ido tare da dafe Kansa.

Duk da baiyi Sallama ba sai tace me ya samu Daddy din? Wani kallon wulakanci ya Mata yace ina ruwanki ko son gulma,na fada Miki ki daina shiga safgata Zan Tara Miki gajiya wallahi tam,Shuru tayi Tace abincin fa? Baza'a ci ba ko dole ne sai naci girkinki? Wai me yasa kike son takura min ne? Sabo da Kai Mijina na ne shi yasa,Baki gaji da duka bane Naga Alama,Kai baka gajiya da fada da mace? Ko kunya baka ji fada da mace,idan kana Jin Kai Namiji ne kaje can waje kuyi da maza Mana kaga yanda zasu maka jina jina,ka zauna a Nan Ni sabo da mace ce sai dukana kake Yi wallahi sai Allah ya tambayeka,ranar lahira sai Allah ya Kamaka da hakki na,Murmushi yayi na rainin hankali yace sai na karasa wannan idon Daya shima a manne shi,Sai lokacin Aamna ta tuna ma Idonta a manne yake,Haka duk inda aka ganta sai dai taji Ana ta Mata Sannu da Allah ya sawwake,tana sani Tace zo na yanke maka farce gasu Nan sun fara taruwa,kwanciya yayi a kujerar tare da juya Mata Baya yace wannan karon wallahi kika kuskura ko da Wasa kika taba min farce saina ballaki a gidan Nan,ka godewa Allah ba sajenka da gemunka na yanke ba,Banza ya mata yana tunanin Daddy da akace Hawan jini ya kamashi saura kadan yayi paralyse.

Damuwa ya Shiga a ransa sosai gashi shi bazai iya Addua ba baida time,juyowa yayi Aamna ta kalleshi da sauri,Je kiyi Alwala,tsoro ya Kama Aamna a ranta tace ko hakkinsa zai karba yau na Shiga Uku maybe nafeelar sunna zamuyi daga Nan sai Sex,Idonta ne ya kawo kwalla Tace Alwalar me Kuma? Fuska ya Bata yace Zan fa zaneki wallahi kije nace kiyi Alwala ki zo,Aamna Tace wayyo Uwata na shiga Uku,shi ya manta ma Daren farko Ana Alwala da Nafeela,Aamna tace ka Bari sai dare Dan Allah kayi min Rai,Yace Bari na tashi kiga tsayi na,da sauri ta tafi tayi Alwala ta fito da Hijab a Hannunta tana kuka Hawaye shabe Shabe a fuskarta,Alwalar kikewa kuka duk tsoron Allah naki da kurin Sallah da waye waye,Aamna tayi Shuru tana Hawaye Tace Dan Allah kayi hakuri ance da zafi,zafin me? Alwalar ce da zafi? Ya tambaya Yana zaro Mata Ido,Sallayar Dake Hannunta ta shimfida yace to kalli gabas ki fara Nafeela,Aamna Tace bangane ba,ba tare zamu Yi ba? Yace Kiyi Nafeela nace ki yiwa Daddy Addua Allah ya bashi lafiya a madadi na,Ni bazan iya Yi bane.
Baki Aamna ta Bude sai lokacin taji kunyar kukanta na banza na tunanin banzan ta,Tace Bari ayi magrib,tana yin Sallar Magriba ta fara Nafeela.

Haka tayi ta Nafeela tana yiwa Daddy Addua Allah ya bashi lafiya,sai da ta idar Tace nayi to,ko magana baiyi ba,Wayarta ta jawo ta Kira Mummy, bugu Daya ta daga Bayan sun gaisa Aamna Tace Mummy ya jikin Daddy din? Mummy tana murmushi tace waye ya fada Miki? Aamna ta saci Kallonsa yace in kika ce Ni na fada Miki sai na karya ki yau,Aamna Tace lokacin da kuke waya Ina wajen,Mummy Tace okay da sauki sosai gobe ma muke sa ran Sallama mu koma gida,yaya fatan dai rigimar Bata Yi yawa ba? Aamna Tace ae Mummy,Baba ya kirani jiya,Gaban Aamna ya fadi,Mummy Tace banji Dadin abinda suka Iske Ahmad ya Miki ba,naga Baba yaji Haushi da yawa yace zai dauke ki daga gidan,Kunya ta Kama Aamna Tace Mummy ki kyale Baba rikicin tsufa yake Yi.

Dariya Mummy tayi tace Mama Kuma Ashe Business take so ta fara lokacin Muna cikin damuwa a asibiti abinda ta Nema Bai samu ba sai dubu dari hudu ta samu kacal Amma Inshaallah Zan Kara Mata wasu,Aamna tayi Shuru sabo da Matukar kunya da nauyi data ji, Tace kuyi Hakuri Mummy wallahi Ni ba sa Hannun na ciki,ban San zancen ba ma,Mummy ta fuskanci Aamna ta Kuma Gane su Baba Kawai kyalewa tayi,karki damu Aamna na fihimci lamarin,kici gaba da Hakuri Zama Dan Allah kinji,Aamna Tace Inshaallah ba matsala,kina bukatar kudi ko wani Abu? Aamna tayi murmushi Tace a'a Mummy ba abinda nake bukata komai Yana Yi min idan na tambaya,kin tabbatar? Aamna Tace ae Mummy kiyiwa Daddy Sannu da jiki a gaisar min da Humaira Kuma,Mummy ta dinga yiwa Aamna godiya sannan ta kashe wayar.

Ahmad ransa ya tunzura Jin irin godiyar da Mummy ke Mata to uban me tayi ake gode mata,Cikin masifa yace ni baza a gode min ba Dana dauki kaddara nake zama dake cikin kunci sai ke Za'a godewa Ana wani sa Miki Albarka ke ga fitsararriya ko? Harda wani Jin dadi kina to Mummy...ya makale Murya tare da gwada muryar Aamna yanda take magana,Aamna Tace Wai Kai me yasa baka da kirki ne? Yace ke dalla rufe min Baki ke Wato an Baki lasisi ko harda wani Kara siyo waya Vivo sabuwa,wannan ba gata bane, ke ga tsigalalliya ko kina wani girgiza da kafada ya gwada girgizar Aamna Idan tana masifa,Aamna ta kyalkyale da Dariya gashinsa ya girgiza tare da gyara sabon kitson calabarsa,Aamna Tace shike Nan Zan Kai karar ka wajen Mummy,Yace idan kina yiwa bushashen tsohonki kije ki Kai karar tawa ki gani idan akwai Wanda ya Isa ya tankwara Ni ko yasa naji magana,an fada Miki wani Jin Magana nakeyi.

Baki Aamna ta Bude Tace ai Ni tsoho na ka ganshi me kiba ne,Ashe Ahmad ba Baba yake nufi ba yasan Baban Aamna na asali Dan Sudan wani mugun bushashen tsoho ne,ramarsa ta baci tunda lokacin da wayonsa Bai manta shi ba,Sai yace kije ki binciki tarihinki yarinya kiji waye tsohonki Dan lukuti ne ko kuwa,Aamna ta Mike tsaye tace Allah ban yafe ba sai na cijeka ta fado Kansa Kamar wata Kura ta Bude Baki da gaske ta Kai Masa cizo a wuya,wuyanta ya cafka da hannunsa ya shaketa sosai ta fara kakari Idonta ya firfito kamar zata sheka lahira ya hankadata gefe ta Fadi a kasa dabar, mikewa yayi zai fita ta jawo rigarsa Iya karfinta,ya juyo ya dauketa gaba Daya ya jefata saman kujera Kamar Yana wrestling,Aamna ta cakumo kafafunsa ya Fado gefenta,Idonsa Wanda ya canja yayi ja sabo da kwaya ta motsa ya watsa Mata wani kallo ai sai ta Mike ta arce da gudu.

Key din machine dinsa ya dauka ya fice abinsa ya hau machine kenan yaji an jefo Masa Robar ruwa a Kansa kwas,Kansa ya daga sama yaga Aamna ce ta baya balcony dinta ta sama tana cewa aje a Kai karata wajen human Right idan an isa,ko kazo ka dokeni,Yatsunsa ya wara ya Mata dakuwa Wato ambola Aamna ta Masa gwalo,yace zamu hadu ne da karfi yanda zata ji,mu hadu Mana gani ta matso jikin karfen wajen Dan Allah taho mu hadu tayi girgizarta da kafada,saura kadan yayi Dariya ya matse yace Fuck you....Aamna Tace Dadi ne da shi come and fuck me,Dariyarsa ya guntse yace Yar Iska ce ke ai,nafi karfin Iska sai dai Guguwa,Machine dinsa ya kotse yayi waje abinsa ya barta tana ta dariya.

Tunda ya fita Bai dawo ba sai wurin 4am ya shigo a chake yasha da yawa,tunda ya Shiga Dakinsa Bai tashi ba har gari ya waye,12pm Aamna ta Gama komai tana ta duba shi Bai tashi ba,Haka taje ta wanke Masa toilet ta gyara dakin bed din ne Kawai bata gyara ba kasancewar Yana kwance,Fitowa tayi ta zauna sanye cikin doguwar rigar Shadda purple ta Sha kyau,sallamar Siyama ta ji,ta Mike Suka Rungume juna Siyama Tace ba Zama nazo Yi ba maza muje na zabi kayan,Bedroom Suka haura Aamna ta bude Mata akwatuna Tace zabi,da mamaki sai taga Siyama ba hankali duk kayan masu tsadar take zabewa har ta zabi kala biyar ta koma Kan Arabian dress,ta zabi English wear, ta zabi Inners,Aamna gashi ita Tace ta zabi abinda take so tana ji tana gani Siyama ta zuba a katuwar leda,Aamna Kamar ta kwace Amma ta danne zuciyarta Suka fito haka,suna Fitowa Ahmad Yana Fitowa ya Sha wanka cikin kana Nan kayansa kamar kullum 3qtr da t-shirt marasa nauyi ne da Alama ba fita zaiyi ba,Kallo Daya ya musu yace Mene a Nan? Ya dakawa Siyama Tsawa.

Da sauri Aamna ta firgita Tace ka...Kaya...kaya ne na lefe kasan Ana Dan bawa kawa wasu abin,Ya Mika Hannu yace bani cikin tsawa....Siyama jiki na rawa ta Mika Masa ledojin ya fisge kuwa tare da budewa yaga Kaya da uban yawa,ya kalli Aamna yace waye ya Siya Miki kayan Answer me,Aamna Tace Mummy ce,yace ke ta siyawa ko wannan jakar ya nuna Siyama da yatsa,Aamna Tace Ni,yace to ba don Mummy tana sonki ba ta siya Miki shine Zaki bayar sabo da ba kudinki bane,Mummy ta me yasa bakya respecting din Mummy ne Wai duk son da take miki,Siyama ya kalla yace last warning duk abinda Zaki ki tsaya a Downstairs main Palo Kar na sake ganinki a sama Nan,sabo da idan na sake ganinki baza kiso abinda Zan Miki ba,baza kiji dadin abinda Zan Miki daga ke har kawar taki,bi hanya....ya furta da karaji,Siyama tayi kasa da gudu,Aamna zata bita yace wait...tafin hannunsa ya Buda kamar zai mareta yace karaso ki Mari kanki da kanki.

Aamna da sauri tazo ta Kara kumatunta a hannunsa,yace Baki ji zafi ba da karfi Zaki taho ki taskawa kanki mari,Matsawa tayi baya ta taho da gudu tare da hannunsa da Hannunta ta Kara kumatunta a tafin hannunsa da karfi ta taskawa kanta Mari yace Good tare da murde Mata kunne yace daga yau idan kika sake ebar wa Mummy

Please Login or Register in order to submit comment