Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dire ta Dan baje daga kasa.
Har zai tashi sai ya koma ya sake daga Hannu sama yace Ya Hayyu ya Qayyum na kawo karar Daddy wajen ka Allah kasa ya daina min fada kasa ya dinga so na,Allah kana gani dai Tsoho Nan nawa ya tsane ni kamar ba a son ransa aka haifo Ni ba,to Allah Kaine ka halicce Ni ya zaiyi Dani Allah kasa ya daina tsanata Yana gamawa ya Mike tare da zare jallabiyar da ya saka domin yin Sallah,ya dakko gajeren wando wani me tsada iya gwiwa ya tsaya Masa me Dan Fadi Yana da Aljihuna kala kala a jiki gashi Kalar ruwan kasa yasa Riga Armless baka me rubuyu a jiki da zanen fari,Pcap ya saka Kalar wandonsa Takalminsa ma na Yan gayu Wanda suka San mene wanka ya saka Kalar wandon,wow ba karamin kyau yayi ba Kamar a sace shi a gudu,damatsan Nan gasu Nan na mazaje mul mul irin na Wanda ke Dan Gym,turare yabi jikinsa sannan ya dauki key din machine dinsa ya fita,time ya duba 12am wani 24hrs shawarma joint ya nufa,Ko da ya Shiga ga mutane Nan Kamar Rana,Ana ta shige da fice,wasu Kuma suna ta Shan Shisha shi baya Harkar Hayaki,Take Away yayi na Abubuwan ci sannan ya nufo Hospital wurin Mummy.

Bayan Tafiyar Ahmad daga Asibitin Mummy ce ta Dan yiwa Aamna magana da kyar Tace 'ya ta kin iya cire kudi a bank? Nan take tace ae,Tace duba handbag Dina ki dauki Atm card Dina ki ciro min dubu dari,Mamaki tayi lallai masu kudi ne,Haka ta dauka tana mamaki da Bata Santa ba Amma har ta yarda Da ita, Code dinta ta fada mata ta fita da sauri taje ta ciro,Handbag dinta ta sa ta zuba kudin da Atm card din,lokacin Likita yazo yace Hajiya anyi komao dakin da kike bukata ya Zama ready aje a biya kudi sai ku koma ciki.
Yana zuwa ya Iske an canja wa Mummy daki Already Kuma dakin na masu kudi ne Idan kana da kudi sai ka biya kudin daki Guda karami a baka Kai Daya,Gado ne daban na me jinya a dakin da Kuma me cutar nata daban,cikin abubuwan Daya siyo ya Bari masu yawa ciki ta Bude ledoji Aamna taga Naman kaza gasashiya ga tsire daban,ga wata Hanta me ruwa ruwa,sai pounded yam da Miyar Egusi shima a take away daban,Sai Lemuka kamar hauka da fruits ga kayan tea,ga plates da spoons,cups etc,komai an tanada,Ido Aamna ta zaro kenan,Mummy duk jikinta inda taji rauni yayi tsami ko Ina ciwo yake Mata Allah yasa Bata karye ba Sannan Bata Yi Mummunan rauni ba Wanda zai wahalar da ita,Dan Nishi tayi Tace Yar Nan zo ki taimaka min naje bayi,Aamna ta Mike da sauri tare da Rike Mummy ta taimaka Mata tana sannu...Sannu Baiwar Allah Sannu Hajiya me kudi Allah ya tashi kafada,Mummy sai da Aamna ta Bata Dariya yanda take Abu kamar tsohuwa,Mummy tace Yan Mata Kamar tsohuwa,Aamna Tace ai itace Hajiya shekarata ashirin da Hudu Babana yace na tsufa gashi naki aure,kin San Baba a Kauye ya taso shi yasa halinsa Bai canja ba,Mummy Tace Uhm,Bayan ta kaita har Toilet sai ta rufo Mata kofa ta fito,Mummy Tace Miko min brush da toothpaste Zaki gani Dana ya kawo,Aamna ta duba ta dakko ta kawo komai da Mummy ke bukata ta Kai Mata,duk Abinda Mummy zata Yi tayi ta fito,Aamna taje da sauri ta taimaka Mata ta kwanta saman bed,a Haka ta samu tayi sallolin da ake binta tayi Addua sosai,Aamna Tace Abinci fa Hajiya?Mummy Tace bani pounded yam din na Dan ci,Amma ta dakko ta zuba a plate tare da cokali ta Bude Hanta da kaza tare da tsire duk a Gaban Mummy,Fruits ma ta yanka sannan ta hada Mata tea me kauri ta zauna tare da sa Mummy a gaba kamar ta samu Yaron yaye,Tace yawwa mashaallah Bismillah ta yanko sakwara da Miya Tace to Hajiya ayi hankali gashi Naga gefen bakinki kin danji rauni tana ta Bata a Baki sunyi Shuru kamar ba kowa,Mummy tana ta ci Tace Baki magana ne? Me zance Mummy sai dai idan tatsuniya Zan miki,Mummy Tace sai kace wata yarinya bana so,Sai da Mummy taci da yawa sannan Tace na koshi,Aamna Tace to Naman fa? Ta Furta tare da ballo cinyar kaza ta mikawa Mummy.

Mummy Tace Alhmdllh na koshi,Aamna ta zaro Ido Tace Kazar Hajiya?kaza ce fa,Mummy ta girgiza Kai Alamar Bata ci,Aamna Tace inda ake arziki ba a tsiya Ni Bari na aikata,Nan Aamna taci Kazar Nan ta gaji ta ajiye sauran,taci tsiren taci duk sauran,Mummy kuwa kankana ta Sha taci Banana da Red Apple,Aamna Kam yau harka ta samu sai da taji zata yiwa kanta Illa sannan ta hakura,ta Mike kenan Tace Bari na wanke Hannu da kwanikan tana juyowa gabanta ya yanke yayi muguwar Faduwa ganin Ahmad a tsaye a jikin Kofa da Alama ya Dade a wajen,Fuskarsa ba kwayar Rahma a ciki,Idonta ta dauke a Kansa ta rabe ta gefensa zata wuce wani kamshi Wanda ba irin na dazu ba ya daki Hancinta sai da ta lumshe ido ba tare da ta shirya ba Haka ta wuce da sauri tayi waje,sai da ta wanke komai sannan ta dawo da su ciki ta Adana a tsaftace ta Iske Mummy da Ahmad suna magana da,Mummy tana ta Masa fada ya Bata Rai yayi Shuru,Aamna tana dawowa Mummy ta bar zancen,ita kuwa Aamna saman gadon da ba kowa ta kwanta tare da dakko Wayarta wacce take Ringing tana bukatar a kawo Mata dauki.

Ganin kanwarta Zuhra ta daga da sauri,Tace Amarya bakya laifi,Zuhra ta zuba murmushi tana kwance jikin Angonta Adam tace nayi missing naki sis yau naji ban Iya bacci sai naji muryarki,Wallahi Aunty Amy Aure Niima ne,sai yanzu nasan Ni mutum ce Ashe a baya gunki ce Kawai,da ace nasan Haka ne da bazan Dade Haka ba zanyi Aure,Aamna Tace to me yasa bakiyi ba Ana Haihuwar ki ba,ai sai kiyi tun kina jaririya,Ke Aunty Aamna ke fa adawa kike da Aure,ki daina min sharri wa zai ki Aure? Kawai Ni abinda nafi so a aure shine na ganni Ina fasa kwai a kitchen Zan soya Ina kwas kwas a kitchen,Dariya Zuhra take yiwa Yayarta Kamar me,Aamna Tace ban San Iskanci Dan na fada Miki Buri na a Aure shine kike wani dariya,To Ni ba abinda nake so a aure face in cakare da kwalliya Ina kitchen Ina fasa kwai,Mummy tana bacci Ahmad Yana jinsu Amma wayarsa Kawai yake dannawa,Zuhra Tace Aunty to babbar Harkar fa ta soyewa? Aamna Baki ta tabe tare da Furta Dan tani a yanke shege na kowa a duniya a jefar,Ahmad Yana jinsu wannan Maganar Bai Gane me suke nufi ba.

Zuhra Tace Aunty Amy Allah ya Baki kema Kalar da kike so Wanda zai biya sadakinki da shegen tsada,Aamna Tace ke na rage tsada na zaftare farashi na yanda su Baba suka damu Ina Ni Ina zaben Yawan Sadaki,Adam ne ya kwace wayar dake Hannun Zuhra tare da Furta sai da safe Aunty kitt ya kashe wayar Baki daya sannan ya ja Amaryarsa Suka kwanta ita kuwa Aamna kwanciya tayi itama tana latsa Wayarta gashi ta kasa bacci sabo da Ahmad Yana ciki Ta kasa kwanciya bare tayi bacci,Bacci ne ya dameta Haka ta kwanta tare da rufe jikinta da katon Hijab Nan take bacci yayi gaba da ita sai Ahmad shi Daya baiyi bacci ba,sai wurin 2am sannan ya bar Asibitin ba tare da kowa ya sani ba.

Washe gari da Asuba Mummy ta farka da karfi a jikinta sosai kamar ba ita ba,Kawai rauni ne da Bai warke ba Amma jikinta fes taji,Da kanta ta lallaba taje Bayi gaba Daya kyankyamin Asibitin take Yi shi yasa ta kasa wanka,Sallah tayi itama Aamna Haka Bayan sunyi Brush da komai suna Azhkar Sai da suka Gama sannan Mummy Tace Aamna kike ko? Aamna Tace ae Tace Yau Zan sa a sallame Ni naji sauki Zan iya karasawa a gida tunda Ina da masu Aiki masu kula da Ni,Aamna tana murmushi tace mashaallah Alhmdllh Haka ake so Allah Kara lfy,Ameen Mummy ta furta,Biro da takarda Mummy ta mikawa Aamna Tace rubuta min Address dinki full sai accnt number dinki,Aamna ta karba ta rubuta komai,Nan take Mummy ta kunna Wayarta tayiwa Aamna transfer na dubu Hamsim,Farin ciki ya lullube Amy Tace Hajiya naji kararrawa na gode Allah ya Kara budi,Ameen Mummy ta Furta tare da mikawa Aamna katinta gashi ko Watarana Zaki neme Ni,Aamna ta karbe jiki na rawa.

suna Haka sai ga Ahmad ya shigo cikin jallabiya fara Kar ta kirki,yayi mugun kyau,Nan take Aamna ta bishi da kallo a ranta Tace wannan Dangin Larabawa ne gaskiya,ko kallon Inda Aamna take baiyi ba ya koma wajen Mummy dinsa suka gaisa Yana ta murna taji sauki,Itama Aamna Bata kula shi ba ko gaisuwa,Kayan breakfast lafiyayye ya musu take Away Suka ci tare da godiya ga Allah,Wasa Wasa Mummy ba a sallame ta ba sai 4pm,Aamna tana gani Wata galleliyar mota tazo tare da tafiya da Mummy,Suka Yi Sallama Aamna ta shiga Napep sai gida,ta samu yan kudinta Bata da matsala abinta.

Bayan Aamna ta dawo gaba Daya kayan da taje asibiti da su har na jikinta ta cire ta wanke fes tayi wanka dama a koshe take,Zama tayi a gefen Mama,Lokacin Baba ya fito daga daki yace yanzu Zuhra tana can a dakin mijinta tana zamanta lfy Abinta,abin kunya Yaya Guda Bata da ko saurayi ko me Gadi babu Wanda ke zuwa zance,Mama Tace an Rubuta Hatimin Annabi Yusufa har an gaji Shuru kake ji sai Neman kudi,Iskanci ne Kawai da samun waje shi yasa Taki fitar da mijin,laifinta ne cewar Mama Kuma kudinki kwandala mun daina karba kije da abinki,Aamna tayi Shuru har Suka Gama ta Mike tayi waje zuwa Kofar gida a kasa ta samu ta zauna dirshan tare da kurma Ihu iya karfinta tana wayyooooo.....Allah.....na shiga Uku na lalace.....Ina samari suke ko Dattawa ku fito ku Aure Ni,Dan Allah gani sadaka ga me bukata,,Ko me tallan rake ko Shoe shiner ko me Gadi,me Mata uku ma yazo Zan Shiga a ta hudu.

Wasu ma tunaninsu tabin kwakwalwa ne ya kamata,sai Dariya akeyi Amma Aamna ko a jikinta,sai da taji Rana ta ishe ta sannan ta koma gida,tana Shiga Baba ya rike ta ram tare da zaro katuwar Sanda ya samu Aamna Kamar Allah ya Aiko shi ya shiga jibgarta kamar zai kashe ta,Mama tana Kara Mata Yar Iska mu Zaki kunyata a Unguwa,Ihu Aamna takeyi ga Yan hayar gidan ba kowa,Karshe ta tashi da kyar ba Mayafi jikinta duk kulun Sanda ne ko Ina da gudu tayi waje tana ihu,Baba baya gudun Abin kunya Kawai ya bita a million Suka zuba tsere layinsu rigarsa tana tashi Kamar mahaukaci Ana ta kallon ikon Allah,har saman Titi suna falfala gudu Baba Yana na koreki a gidana karki dawo daga Nan kiyi gaba,Aamna tana gudun masifa tana cewa wallahi sai na dawo me yasa aka haife ni,Ni Nace ku haife Ni Ina ruwana,Suna Haka zugar machininan su Ahmad Suka taho gaba Daya Suma sun kure wuta,Ganin Baba da Aamna suna falla gudu,Dariya ta kwacewa su Mashkoor, a wajen Suka ci birki,Ahmad ne ya bi Aamna da machine tare da sa hannunsa me laushi ya cafko Hannunta da karfi ya daga ta Kamar ya dauki tsinke ya cilla ta a bayan machine ta zauna daram,tana Jin dadi har da godiya Amma sai taga Ahmad yayi reverse ya juya da ita wajen Baba,Ta saki Ihu shi kuwa Baba zuciyarsa Dake tafarfasa yace Alhmdllh ya tsaya cak,a gabansa Ahmad ya Zana wani shegen kwabo da machine yaci birki sannan Aamna ta dire zata gudu Ahmad da shishigi ya samu ya yarfawa Aamna Mari ji kake gauuuu.....Nan take fuskarta ta kumbura ta zube a wajen kuwa,Baba yace na gode Dan Albarka,Ahmad ya kalli Baba da tsageranci yace Gata Nan Yi Mata dukan tsiya Ina Nan ba inda zata je,ko Kuma Ni yanzu nayi maka maganinta,Baba ya saki Baki yace Kai Malam Taya zaka marar min yata, Mace Budurwa ka mareta kalli yanda ka kumbura Mata Fuska,baka da hankali ne? Wata Mahaukaciyar Tsawa Ahmad ya yiwa Ba ba,Hey....tsoho,da sauri Baba ya rufe Baki jikinsa na mazari.

Da yatsa Ahmad ya nuna Baba yace Kai tsoho baka Sanni ba Zan sa yarana su babbalaka,Baba yayi Mukus,Su Mashkoor suka saki Ihu da sowa,Kallon Aamna Ahmad yayi tana kuka,Tsawa ya buga Mata Dan Uwarki Ina Mayafinki? Irinku ne kuke sawa Ana yiwa Yara fyade a kasar nan,Dan uban Babanki Ina Mayafinki eyeeee yayi kanta da hargowa,Aamna ta Mike tsaye tana kuka Tace baka Gane Ni bane nice fa wacce nayi jinyar mahaifiyarka,wani dariyar hauka yayi yace ke dalla Ware so what Dan kinyi jinya,kyauta kikayi? Bar Nan wajen ko yanzu na Tara Miki gajiya,Aamna Tace wallahi sai dai mu Tarawa juna gajiya,Kai Malam Nifa ba ruwana muyi kokawa ba komai bane,baka Isa kaci min mutunci da Mahaifi na ba,sai mu Buda Nima fa Yar Tasha ce,tashancin Nan na Iya shi ta Furta tana dukan kirjinta,Tace baka San har yankan Aljihu nayi ba a kasuwa,su Mashkoor suka hangame Baki,Suka ga Kuma Ahmad Bai sa sun Mata duka ba,Jibson da Maganar Yan kwaya yace King kana fa jinta kana kallonta ka bamu Dama mu sassarata.

Mutane tunda suka ga su Ahmad babu Wanda yayi gigin zuwa kallo Dan sun San halinsu,Baba ne ya cire Rigarsa daga shi sai wando dogo da Singlet ya mikawa Aamna yace lulluba mu tafi gida,Aamna Tace Ni a Haka Zan koma ba Kaine ka kwance min zani a kasuwa ba,ka biyo Ni Muna ta tsere Ana kallo duk da dama ai mun Saba,Baba zuciyarka bata da control Wai? Baba yace ai kece Aamna Yar Iska ce,kiyi aure kinki Ni fa duk na washe ki ma wallahi,shekara ashirin da Hudu zuwa da biyar ba ko saurayi,25yrs shine girma tsoho? Mashkoor ya tambaya,Baba yace ae ,to Jibson Yana tangadi yace to ke kiyi auren Mana,Aamna sai da tayi Dariya yanda ya fada da muryar maye,Baba yace ai Bata iya magana ba,Bata waye ba,kwana Nan Muka dawo birni,shekarar mu hudu kenan a birni,sai cin mutuncin samari takeyi na rasa yanda zanyi da ita tafi karfi na,Ahmad yayi Murmushi tare da da shafa gemunsa Yana wani rangaji ya furta Tsoho Bari na kaji idan tayi laifi Kawai ka kirani ka fada min har gida zanzo na kera maka ita,Baba yace na gode Dama ta ishe ni,ta gagareni,Aamna mamaki ya kamata,Tsawar data razana ta taji ance yafa rigar tsoho,jiki na Bari ta karba tare da yin Mayafi da ita,Tace wallahi sai na Rama Nima na iya tashancin,Baba yace kuce Mata ta taho mu tafi gida,da yatsa Ahmad ya nuna Mata Hanya ta juya salin alin tabi Baba suka tafi.

Su Aamna suna tafiya wata Budurwa ta taho da gudu wajen Ahmad Tace Dan Allah kaga wani can Haka Kawai ya dameni da naci sai Maganar Batsa yake min nace bana sonsa yaki hakura Wai sai na bashi kaina ko yayi min fyade Dan yaga Kawai Ina tallan gyada tunaninsa Yar Iska ce Ni ta karasa da kuka,Ahmad Fuska a Murtuke yace Yana Ina guy din? Da yatsa ta nuna musu,Ahmad yace Boys kuje ku min maganinsa,ai kuwa Suka tafi Kamar an Aiko su Suka hau jibgarsa,sai da suka Masa ligi ligi sannan Ahmad ya karasa wajen tare da yarinyar,yace Kai Dan uwarka wannan kake so?Kai Dan Iska ne?zaka lalata Yar wasu Tace Bata sonka dole ne? Matashi Yana Nishi jikinsa duk jini Ahmad yace daga yau idan kaga wannan yarinyar hanyar da take idan kabi wallahi sai na yankaka,Matashin yace bazan sake ba,Zan gyara halayena,ayi Hakuri Oga,Ahmad ya Shure shi da kafa yace bace a Nan,ya tashi ya fece da gudu,Yace wa Yarinyar ki dinga saka Hijab idan Zaki talla,Tace to na gode yanlabai,ki daina talla ki Shiga makaranta ko kiyi aure,Tace to ai an kusa biki na Kuma Ina Islamuyya yace Good Ware ke ban son surutu,da sauri ta tafi tana murna.

Tafiya sukayi sunyi nisa Suka samu wani yaro ya fisge Wayar wani a Hanya,Ashe Ahmad yaga abinda Yaron yayi ya arce,Sai da ya Bari Yaron yasha kwana sannan yabi bayansa,ya sauka a machine ya cafke Yaron a nutse ya dinga kashe Yaron da Mari yafi a irga tun Yana gani sai da Yaron ya sume,Wayar da Yaron ya fisge Ahmad ya karba tare da kwarawa Yaron ruwa ya farfado yace Kai barawo ko Nan take ya Kira police Suka Yi gaba da Yaron shi Kuma ya maidawa Babban mutumin da aka satar Masa,mutumin ya dinga godiya,yace yaro daga an kirani na dakko waya Kawai naji ya fisge,Ahmad Bai kulashi ba ya wuce gidansa Kawai su Mashkoor suka rufa Masa baya.

Tunda suke tafiya Aamna kuka takeyi jikinta duk rauni,Baba yace kece dai kika jawo Kuma kin San Halina wallahi Sai in Miki jina jina,Aamna taci gaba da kukanta tana tafiya,Baba yace Jeki ki Siyo kayan Miya da Salat ki Shiga da shi gida,Aamna Tace bani kudin tana kuka,yace a aljihunki Ni Ina da kudi ne an fada Miki,Nima yau bazan ciyar da kowa ba wallahi tunda aka Dake Ni ta furta tana shesheka,Zan tsine Miki wallahi Aamna Naga kin rainani,Aamna tayi banza da mahaifinta,kwafa Yaja ya juya ya tafiyarsa inda zai je yace yunwa ta kashe ku, Zaki sani Zan dawo gidan ne,Aamna tayi tafiyarta da rigarta a kanta har Gaban me kayan miyar kusa da gidansu tana goge Hawaye tana sheshekar kuka Tace Dan...tala....Dantala... ba....bani kayan Miya na dari hudu.....Salat na na ... Naira dariiiiiiiiiiiii......sai ta karasa da sakin Kuka me karfi a Gaban Dantala,Dantala ya saba da halin Aamna yasan Kuma yanda dama suke fada da Babanta,Yace kiyi Hakuri,ita rayuwa ko da wa zaka zauna sai kayi Hakuri Aamna,da girmanki da shekarunki haba Haba,Aamna ta sake fashewa da kuka Tace Wal....wallahi....wallahi tallahi yau bazan ci abinci ba da yunwa Zan kwana,Kuma na rantse bazan Taya Mama Aiki ba,Dantala Ina da zuciya,Kawai duk an bi an tsaneni akan ban samu Miji ba,a kauyen mu kowa sai ya fada min bakar magana bana Iya Shiga cikin dangi na sakata na Wala,Haka a gida ace Iyaye sun tsaneka,Dantala yayi Dariya yace sai hakuri Aamna,Tace wallahi Watarana za a ga na mutu a tsinci gawata Kawai,kiyi Hakuri cewar Dan tala ya zuba Mata kayan Miya ta bashi kudin ta tafi gida.

Tana yin Sallama Mama ko kallonta Bata Yi ba,kayan miyar ta Ajiye zata juya Mama ta rike Hannunta caraf,Tace wa kike wa raini Wai? Waye sa'anki a gidan Nan Dan Kan uwarki,Aamna tayi Mukus Mama ta shiga zuba Mata Rankwashi ba adadi sannan ta saketa Tace tashi ko na nayi ball da ke, Aamna ta Mike ta fada daki tare da sake fashewa da kuka,Ita kuwa Mama girkinta ta shirya shinkafa da Miya da salat.
Wato Islamiyyar Asabar da lahadin ma kin daina zuwa ko Aamna cewar Mama,Aamna Dake kwance a katifa ta fito Fuska a kumbure Tace na girmi Islamiyya Ni,Duk abinda ya kamata na sani na sani na addini sabo da Haka zanci gaba da saurarar wa'azi Kawai a gidan Radio ya isheni zaman duniya,a kyale Ni inji da matsalata,Ni yanzu ba karatu ne a gaba na ba,Alhadisissani,salisu duk na Iya ya ishe Ni,Sira da Ishmawi na haddace quarter,Zikiri na iya,Qurani saura Izu goma nayi sauka to me Kuma zanyi,gishirin zaman duniya na sani ya ishe Ni,Mama ta rike Baki Tace tab ke Baki ji kunya ba 25yrs Baki sauka ba,to ai da a sauke ba a Aiki da shi gwara ka samu Izu goma kayi Aiki da shi,Bulala Mama ta dakko Aamna ta jawo kujera ta zauna daram Tace a tafke Ni ai na Saba,kamata kullum a Duke Ni to a Dake Ni,Mama kuwa itama akwai zuciya Nan ta dinga tsulawa Aamna Bulala iya karfinta,har ta Gama Aamna ko motsi Bata Yi ba ta tashi a nutse ta shige dakinta,Haka Baba da dare bala'i yakeyi Kamar me,Ita kuwa Aamna washe gari sai da taje chemist aka Bata magunguna,tana dawowa ta Hado kayan sawarta a Akwati ta fito sanye da Hijab Tace Zan bar muku gidanku gwara na shiga duniya.

Baba ko a jikinsa yace a gaisar da Yan bariki maza Kar dare yayi a dawo lafiya,Mama ta tabe Baki Tace sakarai,Aamna tana ta jira a lallashe ta ko ace Kar ta tafi Amma taji Shuru,Tace Zan tafi fa bazan dawo ba,Baba yace to,Duniya fa Zan shiga Mama,Mama Tace madalla,Juyawa Aamna tayi ta fara tafiya ba Wanda ya kulata har taje bakin kofa,Tace baza ku kirani ba Wai? Tsaki Baba ya ja,Aamna tayi waje kenan taga wata dalleliyar mota me tsada,Wata Dattijuwa ce ta fito a motar,da wani Dattijo shima fari ya fito,Aamna taji an kirata,Matar ta kalla sai taga Mummyn Ahmad ce cikin shiga ta Alfarma,Aamna fara'arta ta karu har kasa ta zube tare da Gaida su,Mummy Tace ga Baban Ahmad,Aamna ta sake Gaida shi tare da rike Hannun Mummy Suka Shiga gidan.

Baba da Mama sunga masu kudi Nan Suka rude,Baba yace laaaaaa Alhaji Ja'afar Kaine a gidan Nawa? Wanda aka Kira da Alhaji Ja'afar yace ikon Allah Malam Hussaini Umar dama a Nan kake yanzu? Baba yace ae wallahi,me ya kawo ku?Aamna dai da Mummy suna mamaki aka shimfida musu Tabarma,Aamna ta kawo musu pure water da lemo,Nan ta ebo musu shinkafa da Miya da salat ta Ajiye,Tace Baba kasan su ne? Baba yace kwarai kuwa zauna kiji labari.

Labari














AsmaBaffa
10/26/21, 8:51 AM - A Maryam: 🌵🌵DUNIYA TA🌵🌵









16-20






FREE PAGE










DUNIYA TA IS DEDICATED TO GARBA BUTALAWA FAMILY.








NA KUDI NE

GA MASU BUKATAR SHIGA GROUP DARI BIYU 200 NE

ACCOUNT NUMBER TA
0175487861
ASMAU GARBA MUHAMMAD
GTBANK

MASU TURA KATIN MTN KO VTU GA NUMBER
08033933642

'YAN NIGER KU NEMI WANNAN NUMBER
+227 90 79 59 39









Official







By
AsmaBaffa









Page naku ne

MAMAN SAMHA
ZAINAB SABO
BK
UMMEEN SADEEQ
BASMAM GLAM
ALHUSNA(MRS IDRIS)











Ni Hussaini Umar kamar yanda kika sani mu Uku Mahaifiyar Hajiya Maryam ta haifa,Kuma mu kadai ne a wajen Mahaifinmu Malam Umaru,Ni Yan biyu aka haife mu Ni Hussaini da Hassan,Hassan tun Muna jarirai Allah ya Masa Rasuwa sai Ni,daga Ni aka Haifo Kawunki Isma'il sai Kanwar mu Kursum wacce kika Sani a kauyenmu Sokoto take aure,Munyi karatun Muhammadiyya har muka girma Noma da kiwo muka gado, tun baya dama mu Bamu taso a cikin kudi ba sai rufin asiri,sai da muka girma lokacin aka hadani aure da Aishatu Yar Uwa ce itama auren zumunci ne,daga Nan Bamu samu Haihuwa ba har Ismail yayi Aure shima a can kauye,sai da ya haifi Yara uku sannan aka yiwa Kursum Aure a kauyenmu itama ta Haihu Daya,duk Ni Allah Bai bani Haihuwa ba har Iyayenmu Suka rasu sai Yan Uwa da dangi,wannan da kike gani Shine Alhaji Ja'afar Wanda shima a Sokoto na sanshi Amma Asalinsu Yan Yemen ne kasashen Larabawa,kasuwanci ya kawo su Nigeria Sokoto suna da company Wanda a lokacin suna da Company na Yogourt da Kuma kamfanin Dake sarrafa Fulawa,sabo da Haka suna bi kauyuka suna siyen madarar shanu da Alkama Wanda a lokacin sana'ar mu kenan a wajen mu suke siya,mun Saba sosai muna mutunci da Alhaji Ja'afar lokacin ya Dade da Auren Mummy har da yaronsu Ahmad Yana shekara bakwai lokacin,su dama masu kudi ne da danginsu duk suna zuwa,ita Mum Yar Sokoto ce,bafulatana ce ya ganta ya aure ta sabo da sonta da yake Yi,Tun Bai Jin hausa har ya koya ya Zama Kamar bahaushe shima ga matarsa bahausa,Tunda yayi Aure ya dawo Nigeria gaba Daya da Zama Amma yanayin Lagos ya fiye Masa Dadi shi yasa yayi gida a can

Please Login or Register in order to submit comment