Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a Fuska Ina kallonki,wannan wanne masifa ne Haka?.....Ni.....ya nuna Kansa da yatsa ni Zan zauna Ina tunanin mace,kamata Ni a'ahhhh....chaiiii......mikewa tsaye yayi ya kaiwa Iska Naushi yace Zan fasa Miki Baki fa......shi kadai yake ta abinsa a bedroom kamar sabon kamu,Zama ya sake Yi sai Kawai ya tafi tunanin Aamna...Tsaki Yaja yace again....Wai wannan wacce irin yarinya ce ki fitar min daga ido na daina ganinki....kasa ya sakko ya durkusa ya daga hannaye sama Yana Allah ka gani dai Yarinyar Nan sai Tunaninta nakeyi,Ina ta ganinta a Ido na,bazan Iya ba....nasan ni me laifi ne a gareka,nayiwa mutane da yawa laifi Allah karka Yi Fushi Dani ka jarabce Ni da yarinyar nan,Allah kasa na daina ganinta,Allah na tuba,ya Mike tsaye ya sake juyowa da karfi Yana tangadi yace Allah nayi Addua Kuma ban daina Tunaninta ba,kirjinsa ya dafe tare da furta wayyooo....my Heart woooo ....Ina ta ganinta fa ya Allah,Ya girgiza Kansa ya shiga zaga dakin Yana safa da marwa Yana Ohh....ohh.....Ni ta fita daga Ido na,ta fitaaaa.....a Haka ya yini Yana sambatu har dare yayi Bayan ya jero sallolinsa na yini Guda yace Bari na kwanta bacci da wuri ko Zan daina ganinta a idona,Yana kwanciya ya kasa bacci sai tunanin Aamna tana Masa gizo,Shi kadai yace kunga yau bazan iya bacci ba sai tunaninta yau an shiga Uku.....mikewa yayi zaune yace kaiii....yau bazan Iya bacci ba sai na ganta....naji idan ban ganta bazan samu nutsuwa ba,...Amma Bari naje na ganta nasan idan na ganta zan daina ganinta a idona...waiiii....ya akayi ne nake so sai na ganta,Kawai so nake Naga Yarinyar Nan yanzu yanzu,Kawai gidansu Zan tafi yafi sauki ai Zan Gane gidansu ko na Kira Mashkoor ya raka Ni gidan sabo da ai sunje daurin Aure zasu Gane gidan,a hankali yace Amma idan na Kira Mashkoor asiri na zai tonu Kuma na Gama kuri da cika Baki a gabansu abin kunya ne a ganni naje wajen mace,macen ma wannan yarinya,Amma fa gaskiya idan ban ganta ba bazan samu nutsuwa ba Dole na tafi,agogon Dake hannunsa ya duba yaga 9pm yace Bari naje ko ta katangar gidan ce na haura na ganta,gashi wani kunyarta nake ji da tsoronta bazan Bari ta ganni ba.

Cikin dare ya dauki pcap ya saka sannan yasa face Mark a Fuskarsa Wai Dan kar a ganshi yaji kunya an ganshi a wajen mace,Musa Wanda jiya ya dawo shi ya bawa key din machine yace Musa zuciyata yau wani Bugawa takeyi bazan Iya tuki ba kaini wata Unguwa,Musa ya karbi key ya hau shima Ahmad ya hau sanye cikin kayan baccinsa wando gajeren da Riga me gajeren Hannu ko a jikinsa Haka Suka tafi,Yana ta nunawa Musa Hanya da kyar ya samu ya gano gidan tunda an taba zuwa dashi sau daya,can nesa da gidan yace Musa ya ajiyeshi,ya sauka yace ka jirani a nan bance ka biyo Ni ba,Musa yace to Oga,Face mark dinsa ya gyara ya bi ta can bayan gidan,Kamar Biri Haka ya Dane saman katanga Dake Bata da tsayi Haka ya haura gidan su Aamna lokacin Baba ya fito zai rufe gida.

Ahmad ya labe Bai ganshi ba,Baba ya kulle ko Ina ta gidan,Bai San ya rufe kofa da barawo ba,Ahmad yace yanzu Ni ba abin na shigar musu gida ba,Kuma yanzu Taya zata fito na ganta? Ai wallahi idan Zan kwana bazan tafi ba sai na ganta,Yana tsaye har wurin minti goma sai yaga an Bude kofa an fito sai yaga Aamna ce sanye cikin kayan bacci ta fito da bucket,Ahmad ya Kara labewa ya gyara tsaiwa Yana kallonta Yana zuba murmushi yace kalli Hanci Dan Allah me kyau a Nan wajen.....Uhmmm .....Allah yayi baiwa, panties yaga ta Shanya Guda Uku da Bra Guda biyu,Aamna tafi so ta Shanya Rana ta dake su sabo da kashe kwayoyin cututtuka,Bata son Shanya su a inuwa tasan gobe Rana zata dake su.

Ta Gama shanyawa Yana ta kallonta Mama ta fito tace Aamna ki shigo da kujera ciki Tace to,Ahmad yace kaji sunan ma Aam....nah.....my Aamna...no sunan gayu Ahmnaa....Yes...Ahmnna vs Ahmad...A&A kenan a'a wannan Dadi Haka.....kumatunsa ya Mara kadan yace to yanzu Zan Iya tafiya nayi bacci,Zabura yayi yace Kai Nafa haukace,wannan fa hauka ce,Ahmad Ni king Haka Kawai na zauce akan Yar Yarinyar nan,Tsaki Yaja yace Nafa haukace gaskiya....lallabawa yayi ya sake haurawa ya bar gidan,Musa ya hango shi ya taho Yana ta murna Yana murmushi Bai San dalili ba,Machine ya hau Suka koma gida,ranar wani irin bacci yayi me dadin gaske.

Washe gari Yana farkawa da Aamna ya farka a ransa,Tsaki Yaja yace Wai na ganta ma bazan huta ba...Haba zuciyata me yasa Wai kike min Haka ne,jiya kinsa naje na ganta yanzu ma so kike ki Kara ganinta Baki koshi ba wannan wanne irin tsafi ne Yarinyar Nan tayi min ne,da safe sai na farka da ita Haba which kind juju be that? Ni ba sonta nake ba duk harkar love...love ba ruwana da shi Amma Kuma so nake na sake ganinta Haba nooooo.....ya Furta cikin karaji,Sannan cikin slow Yana yarfe Hannu yace idan na ganta anjima ai shike Nan Kuma sai na huta,ai abin kunya ne kamata Ina son ganin Yar yarinya,zuciyarsa ya dafe yace sai wani tsoronta nake ji zuciyata tana wani bugawa Haka Kawai idan na ganta to daga yau bazan sake zuwa ganinta ba aikin banza,tunani ya shiga Yi yace Naga kamar ma samari na zuwa wajen Baby dinsu da Kaya Decent,to Amma Ni ai ba Baby na bace,Kuma fa sai taji Dadi idan idan ta ganni da kayan hausawa? Murmushi yayi ya koma Gaban Mirror ya duka Yana karewa Kansa kallo ya shafa calabarsa yace gani kyakyawa ai dole ma na birge ta,hannayensa ya Buda a Gaban mirror ya saki murmushi yace chaii....see fine Boy.....oh..oh....baya Yaja sosai Yana kallonsa yace huuuu...Kalar birgewa kaga Kalar birgewa yesss.....Bari nayi wanka, Fuska ya Bata yace to Mene sai wani murna kakeyi zaka ganta aikin banza,Ni wallahi wani banza ne ma akan mace Subhannallahi ya Dan Mari kumatunsa kadan yace Bari na gwada Kalar murmushin da Zan Mata Nan fa ya shiga sakin murmushi kala kala Yana kallon kansa a karshe ya Dan yake kyawawan hakoransa yace ae tsaya dai dai Nan wannan yayi yawwa ae....sai ya wuce toilet.

Tunda ya shiga ciki Yace yau wankan na musamman ne so nake na Kara haske Nan fa ya shiga dirzar fatarsa ba ji ba gani,yace bana wanka da soso yau Zan koma Yi da soso sabo da na fita fes,dubawa yayi bashi da soso,towel ya daura Bayan ya dauraye jikinsa ya fito a Haka daure da towel har wajen me gadi,kudi ya mikawa Musa yace ungo maza ka siyo min soson wanka,karka sake ka dakko min na jarirai me laushi me karfi zaka siyo Wanda Ina wanka Ina Jin radadi,Musa yayi Dariya yace irin namu na talakawa kenan? Karka Bata min time sauri nakeyi Ina da abin yi akan wannan soson wallahi Zan iya sallamarka daga Aiki Matukar baka siyo Wanda zai wanke min fatata sosai ba,Musa ya karba da sauri ya fice,Minti biyar ya dawo da soso me shegen karfi ya bashi.

Wanka ya sake Shiga Yana dirje jikinsa Yana rumtse Ido sabo da zafin soson,Haka ya Gama tas ya fito Yana goge jikinsa yace yawwa Iska tafi shigata Ina Nan Ashe Ina ta cutar kaina da ace da irin wannan nake wanka tun farko ai da nafi Haka haske da Zama Fresh.
Lotion dinsa ya shafa me kamshi ya shiga gyara kitsonsa yace ya kamata nayi sabo wannan kwanansa biyar ya fara tsufa Amma Bari dai naje,sai da ya Gama feshe feshensa sannan ya Bude ma'ajiyar kayansa Yana binsu da kallo yace Suit Zan saka ko me?can ya hango shaddoji da yadika masu tsada da kyau Wanda Mummy ta kawo Masa lokacin da za a daura aurensa kala bakwai,Wata Shadda ya dakko sea Blue Tasha dinki me kyau Hannun dogo me links,Nan ya sa Boxers ya fara kici kicin saka wando Wai Bai iya ba,da kyar da wahala Yana uban Nishi ya saka cif cif shi dinki ya zanu,Singlet ya saka yanda Mummy ta koya Masa sannan ya saka Rigar Shaddar wacce ta Sha guga ga kamshi Shaddar nayi sabo da me tsada ce,calabarsa ya gyara ya shafe Kansa da man gashi me kamshi Nan take ya dauki sheki,Fuska ya kalla ya matsa baya Yana kallon kansa a mudubi ya hau taje Sajensa da gemusa,fuskar ya goge sosai ya gyara sai gashi ya fito fes da shi,Sarkar azufarsa wata sabuwa ya dakko ya saka,Yana cewa duk da hausawa basa so Amma tana min kyau sai na saka sabo da wannan shine wankan sugar sai da ya Gama ya fesa turaruka masu kamshi,Ya tsaya jikin mirror ya kame a wajen yayi mutuwar tsaye yace ya Ilahi Ashe Haka nake? Dan Allah kalli kyau a wajen Nan ai Dole ma na birge,ya sake kallon kansa yace ah.. ah kalli kyau Dan Allah,irin wannan saurayi ai sai an wanke Hannu daka taba,wani Dan lipgloss na maza ya dauka ya Dan goga a lips dinsa yace yawwa.....Kar Kuma na Zama Dan Daudu Mana ya Isa haka....tsayawa yayi yace to me zance Mata idan naje Kantin nasu? Tunani yayi yace na tuna ma Bari naje,Illar idan na ganta sai naji tsoronta Kuma Haka Zan daure,Fitowa yayi Yana Taku dai dai Yana wani Gadara,yace me kyau sai da takama Nan ya Shiga wata tafiya Yana takama Yana basarwa,Musa Baki ya Bude tunda yake a duniya Bai taba ganin me kyau irin Ogansa ba,Bai taba ganin wankan da yayi ya zuba Uban kyau Haka ba sai yau,Musa yace Oga gaskiya kayi kyau,Murmushi yayi yace Allah Musa?

Musa yace wallahi Oga Kar fa kasa Mata su haukace,Dariya Ahmad yayi ta Jin dadi yace Musa yanzu kana ganin duk wacce ta ganni zan birge ta? Bafa soyayya nake nufi ba Kai Musa Ni kasan ba ruwana da soyayya,Musa ya kalli sama ya nuna sama da yatsa yace Na rantse Oga duk wacce ta ganka sai ta kwana tana tunaninka yau ita da bacci haihata haihata,Machine Ahmad ya hau Wanda Musa ya wanke Masa Shar,a hankali yake tukin sai binsa ake da kallo da gani an San Yafi karfin yawo a Machine ko Ina ya gifta sai an koka.

Aamna kuwa yau wanka tayi ta shirya cikin doguwar rigarta peach color ta lefe ce tayi rolling da mayafi ta dauki hand bag da takalminta me Dan tudu Kalar adon rigar Golden tayi kyau ta dauki bokitin chin chin da takeyi da kanta tana siyarwa a shagon wannan da kundinta takeyi tana samu Yar riba,da kanta ta gyara kantin fes ta shirya komai sannan ta zauna tare da dakko Wayarta tana karanta novel,idan masu siyan Abu sunzo ta Basu ta koma karatunta.

Tana zaune ta dukufa taji machine yayi parking a bakin wajen,kanta ta dago da sauri Jin wani kamshi na daban me Dadi,Ahmad ta gani Wani tafiya yayi da Imaninta ita kanta sai taga kamar yau ta taba ganinsa,zuciyarta ta hau Bugawa da karfi,Kallonsa takeyi ba kyafta Ido tare da Mikewa tsaye,Babu alamun fara a Fuskarsa Yana wani Isa,a cikin ransa Kuma wani kwarjini ta Masa yaji wani tsoronta da shakkarta,duk kwarin gwiwarsa sai ya neme shi ya rasa,jikinsa yayi sanyi a hankali ya taka zuwa gabanta ya tsareta da idanunsa,Itama shi take kallo,can ganin Shirun yayi yawa sai Tace am...me kake so zaka siya Ahmad? Yayi Shuru ya kasa magana,ta kalle shi tayi murmushi Tace wow kayi kyau Wannan shigar tayi maka kyau,Wani sanyi yaji a ransa dama Dan ita yayi Kuma ta yaba,a hankali yana Ina Ina yace shi...shigar...ta...tayi Miki?da sauri ta daga kai Tace sosai wace zata ce ma baka Yi kyau ba,Yaji wani Dadi ya jinjina Kai kawai,sharewa tayi Tace me zaka siya? Kasa magana yayi sai da kyar yace Uhm....uhmm.....Yana ta kallon shagon Yana so yaga me zai iya siya....gumi ya hada Nan take tsabar abinda yake ji a ransa da kwarjinin da ta Masa gashi Bai Iya yiwa mace magana ba tunda ya taso a rayuwarsa wannan ne na farko,Tace Kayi magana Mana me zaka siya? Yace Uhmm....ahhh....ehmmm.....can ya hango chin chin yace Chin chin tare da nunawa da yatsansa,murmushi tayi Tace na nawa? Yace na....naira dari.....murmushi ta saki ta bude ta zuba Masa Guda uku dari cif a farar Leda ta Mika Masa,karba yayi Yana ta kallonta yace Zan....Zan...Iya Zama a Nan naci? Tace me zai Hana shigo ciki,kujera fara ta jawo Masa a ciki ya zauna Suka jere taci gaba da karatun Novel dinta.

Kallonta Kawai yake ta faman Yi idan yaga zata dago sai yayi sauri ya dauke Kansa,Daya gaji sai ya fara cin Chin Chin din,harga Allah baya son chin chin Amma Haka yake ta ci Yana kallonta,ita Kuma tana ji a jikinta Yana kallonta duk sai ta kasa sakewa da kunya,juyowa tayi karaf suka hada ido,Tace ya kake kallo na? Yace kallo? Kallo Kuma? Ni na kalle ki ai kece ma naga kina ta kallo na tun dazu ya fada Yana dauke Kai,Tace Ni nake kallonka din? Yayi Murmushi yace ae Mana,Kai ta girgiza taci gaba da karatunta,cikin Wayar ya leka yace me kike karantawa? Novel ta bashi amsa, ko kana karanta Novel? Yace No...me zanci da Harkar love ai Ni sai dai dambe, murmushi tayi Kawai.
Yace me yasa Mata kuke son Love ne? Wannan duk Bata lokaci ne,Dariya tayi Tace Kai baka so ta juyo tana murmushi wani kyau ta Masa ya gigice zuciyarsa taci gaba da bugawa,kasa magana yayi ya rike Hannunta wani mugun shock taji ko Ina a jikinta yace Ring din ya Miki kyau,Tace na gode Hannunta ya dauka ya maida Mata saman cinyarta yace kina boye Hannun Nan Kar wani yaga ya Masa kyau da yawa ya yanke Miki shi ya tafi dashi gida,Dariya ta dinga Yi shi kuwa ita Kawai yake kallo,komai nata Dariya a ransa ya furta,Yana sani ya dinga cin Chin Chin din kadan kadan sai da ya Dade lokacin Azahar tayi sannan ya Mike yace Zan tafi Tace ka Gaida gida yace to Zan fada Masa,Dariya ta sake Yi ta rako shi har bakin machine dinsa ya hau ya tafi da mugun gudu,Tun kafin ya karasa gidansa ya tsaya a Hanya ya cire rigar Shaddar tasa sabo da zafi yake ji ta dame shi Bai Saba ba,a kafada ya sakale ta har zuwa gidan.

Da murna ya shiga Yana sauka a machine ya zaro dubu biyu ya damkawa Musa yace je kaci pizza Musa yau Ranar murna ce,Musa yace Allah Oga? Allah kuwa cewar Ahmad ya sake zaro dubu biyu yace kudin lemo ne wannan,Musa ya daka tsalle Yana murna da Ihu har Ahmad ya tafi ya sake dawowa ya zaro dubu Daya yace ungo Musa ka sawa matarka Kati a waya ku kwana kula hirar ku ta Yan karya Kuma karka sake ka Bata duniyar mu Dan Bamu San Inda zamu shiga ba idan ka bata.,,Musa yace Allah Kai sai kayi,Ahmad ya daga hannaye sama yace nine nan yayi ciki Yana wata tafiya ta musamman.

Yana shiga ya cire duka kayan jikinsa ya watsa su a inda yake Tara wanki,saitin zuciyarsa ya dafe tare da furta shu'uma har ta dawo dai dai,Wato har wani bugu kike Yi a hankali da kika ga bana gabanta ai shike Nan kin kyauta,zuciya kin kyauta hakan ya Miki kyau kin Mai Dani wani Wawa Akan yarinya karama Ina ta zubar da aji na ai shike Nan Zaki sani ne.

Washe gari ma wani sabon wankan yayi tare da saka wani yadi Milk color sharara da shi ya Masa kyau matuka an kashe shi da dinki na haduwa,wani takalmin ya zabo me tsada,waje ya fito ya mikawa Musa takalman yace sauri ka kaiwa Shoe maker ya wanke min yanzu Ina jira,Dan Allah Musa kayi sauri ka kawo min su Suna kyalli,Musa ya fita da gudu ya tafi Bai Dade ba ya dawo,Ahmad ya shirya tsaf kyau ba a magana yace yau barkono da citta Zan tayata siyarwa,yau ma Aamna tana zaune ta Gama sallamar wani ya siyo Singlet sai gashi ya Parker machine,Aamna tayi murmushi Tace Sannu da zuwa,Irin Dan gayun Nan harda wani basarwa Direct ya shige ciki ya zubawa Kansa chin chin yace na Naira Dari biyu yau Zan siya Aamna Tace to,Zama yayi Nan ma Yana kallonta duk kunya ta isheta,Wani magidanci ne yazo yasan Ahmad da irin iya shegensu mamaki ya kamashi ganinsa a Haka da wannan shiga ta Kaya,Bai taba ganinsa da shigar hausawa ba,Kuma Yana Zaune a shago kamarsa me kudi,Shuru yayi yace a bani barkono da citta,Aamna ta Mike zata zuba da sauri Ahmad yace No zauna Bari na tayaki Mana Haba,Tace Kai din? Bai kulata ba yace na nawa? Yace na Hamsim,Aamna tace ga kullin Hamsim can ka saka,ya dauki bakar Leda ya saka Masa ,Citta Kuma Tace gongoni Daya zaka zuba,ya fito ya auna gwangwani Daya ya zuba,mutumin yace babu gyara? Ahmad yace a gindinku kuke so mu kare ne Ina laifi ma duk arahar Nan Baku gani ba,Tsaki Yaja ya dauki citta Daya ya jefa masa a Leda yace gashi Nan anyi gyara,Mutumin ya karba ya tafi shi Kuma ya dawo ya zauna a ciki,Aamna tana ta mamakinsa.

Wata Budurwa ce tazo Tace Aamna nazo siyayyar,Aamna Tace to shugo,Budurwar tayi layin bra da panties ai Ahmad Yana ganin Haka sai ya juya baya tare da rufe Idonsa ruf har sai da matar Nan ta Gama zaba ta biya kudin ta tafi sannan ya Bude Idonsa,Dariya ya bawa Aamna Yana jinta tana ta dariya,yau ya Dade sai Yamma lis ya koma gida,sai mamakin Kansa yakeyi Wai Kamar shi shine zai siyar da citta,Yana kwance a palonsa yace gaskiya na Gama fadowa nayi asara wallahi,Kansa ya dungure yace kayi asara kai Kam Ahmad.

Wasa Wasa kullum Ahmad sai yaje ya Taya Aamna siyar da Abu har wurin sati Daya,gaba Daya su Mashkoor sun daina ganinsa,idan sun Masa waya ma zasu zo gidansa sai yace Kar suzo baya gida ya tafi Unguwa,yafi so ya zauna shi kadai yayi ta tunanin Aamna Yana Jin dadi,Kwaya da giyar da yake Sha duk ya rage ba sosai ba sabo da tunanin Aamna.
Yau kin zuwa yayi gaba Daya Bata ganshi ba har duba Hanya takeyi ko zata hango shi Amma Shuru duk ta kasa sukuni ta shiga wani Hali,gashi Bata da number dinsa Kuma baza ta iya cewa ya Bata ba.
Sai washe gari yau cikin wata maroon suit ya fito kamar a jikinsa aka dinka yayi kyau matuka 3pm yazo wajen,Aamna ta taso da sauri tana murna a ranta a fili Tace me ya hanaka zuwa jiya? Ya rasa me zaice zuciyarsa tsoro yake ji....yace...ahmm...karya yayi yace kaina ke ciwo jiya,Tace Eyya Sannu ya jikin? Da sauki ya furta tare da tsayawa a gabanta Yana so ya fada Mata me yake ji a ransa Amma ya kasa....yace dama Ina so muyi wata magana ne,akwai abinda nake so na fada Miki,Aamna tace Ina jinka tana ta faman kallonsa,kasa fada yayi ta Masa kwarjini sai ya waske yace kina cin kifi tarwada? Dariya ta kamata Tace sosai ma ai Ina sonsa ya,girgiza Kai yayi Murmushi Wanda ya tafi da Imanin Aamna,yace to gobe Zan kawo Miki da yawa ko yau kike son ci? Aamna Tace goben ma yayi,Yana so ya fada Mata shifa zuciyarsa ta kasa sukuni Amma ya kasa sai yace Zaki Zama kawa ta?Aamna ta kalle shi tace me zai hana,murmushi yayi yace to daga yau mun Zama kawaye ko? Tana Dariya ta Mika Masa Hannu sukayi musabiha Tace na Zama kawarka kaima ka Zama aboki na,yace ae dama Ina so na dinga shawarwari Amma Banda kawa,Aamna Tace Ina abokanka fa?Tsaki Yaja kadan yace ai Bama wani haduwa yanzu sosai,taji Dadi a ranta Tace to shugo ka zauna,no tafiya zanyi Ina da wajen zuwa yau,Aamna Bata so hakan ba Amma Tace to shike Nan sai goben,ya hau machine yayi tafiyarsa gidan Mashkoor.

Yana zuwa ya samu Mashkoor shi kadai, Mashkoor yace Kai me Zan gani yau Kaine da wannan shigar lafiya king? Kafadarsa Ahmad ya buga yace ba lafiya ba yanzu ma taimakonka nazo Nema,ku kawo min agajin gaggawa, ka tashi mu tafi gidana akwai magana,Mashkoor yace to,Giyar da Mashkoor yake kurba ita Ahmad ya tiltila a cup ya Sha ya sake Sha yace muje,a machine suka tafi gidan Ahmad.
Aamna tana so ta fada Masa anjima da yamma zata tafi Sokoto ganin Dangin Babanta Amma Bai zauna ba bare ta fada Masa Amma sunyi waya da Mummy ta San da tafiyar.
Shi kuwa Mashkoor Yana palon Ahmad suna zaune Ahmad yace kasan Kai abokina na ne Zan fada maka ne Kawai sabo da yanda muke da Kai,Kai kadai Zan fadawa halin da nake ciki,Mashkoor da muryar Yan kwayarsa yace Ina jinka King,Ahmad ya kwashe kaf abinda yake ji a zuciyarsa game da Aamna ya fadawa Mashkoor,Mashkoor tsoro ya kamashi Yaja da baya Yana tangal tangal a zaune yace Sarkin namu Guda ah'ah,Ahmad cikin rada yace Ina fada maka idan na ganta zuciyata sai naji tana wani kida tana rawa tana wani foli..fafo..lifo...fil...fil....dardariya Mashkoor yake Kamar me,yace ah'ah duk Kai kadai?

Ahmad yace Ina fada maka Dan uwarka Yana dukan kafadar Mashkoor kana ganin Wasa ne bafa Wasa nake ba kana wani Yi min Dariya Dan Iska Kawai wallahi zaka bar gidan Nan, Mashkoor yace na daina Ina jinka,Ahmad yace Ina fada maka ba sai naji Ina tsoronta ba,Ah'ah Mashkoor ya furta da karfi yace wannan Yarinyar da ko Nonon kirki babu? Duka Ahmad dirka Masa a baya yace be careful matata ce ba Budurwa ba, Mashkoor yace dalla ba so bane sha'awarta kakeyi Kawai kaje ka dakko ta ka lallabata kaci abinka ka barta,Wani dukan Ahmad ya kaiwa Mashkoor yace Kai dalla Ni ba wannan nake so ba,baka ganewa Ni Kawai nafi so mu zauna tare da ita idan Dan wannan ne zamu iya shekara Nawa da ita sai Sanda take so zanyi wannan fa ba Maganar Wasa bane,Mashkoor yace cab abin Babba ne asiri tayi maka,Haushinka taji daka koreta ta maka asiri.

Ahmad yayi Shuru,Mashkoor yace Zan taimaka maka akwai wani malamin Baban mu zamuje da Kai Nan take zaiyi maka Rukiyya a cire maka tunaninta ka dawo normal asirin data maka ya karye,Ahmad sai ya tuno layoyin Daya taba gani a Kan Aamna,yace Mashkoor kaima kayi magana tashi mu tafi wajen malamin Nan Yarinyar Nan Yar bori ce muje a gwada, Mashkoor yace yawwa kasan yanzu duniya ta canja Wai Yan Mata Dan masifa da bin malamai suna shirka suna tsafi akan maza,Wai mace taje tayi shirka Dan wani ya aure ta ko taci kudin wani,wata ta mallake Miji etc,kawaye sai su cika Mota suyi Kauye Wai an tafi wajen Malam akan wani ya aure su ko taci kudi,ko ayiwa kishiya da yaranta,shi yasa aure yanzu baya Zama Ana ta Yi Ana Sako Mata barkatai,duk macen data auri Namiji da asiri ta sani wallahi idan ya karye sai saki,yanzu shirka Kawai akeyi an ma daina cewa malamai sai bokan Kan dutse,mutane suna ta maida kansu arna Basu Sani ba.

Tafiya sukayi me uban nisa zuwa wani Dan Kauye,Wani dattijo kazami Ahmad ya gani,Mashkoor bayan sun gaisa ya Gabatar da Ahmad da abinda ya samu Ahmad,tsohon yace ku bada dubu biyar kafin alkalami,Ahmad ya zaro ya bawa Malam,Malam yace saura kudin Aiki dubu goma,Ahmad yace Aiki baiyi ba za a baka kudi? Dattijon yace Kai ka cika son kudin tsiya ka bada kudi a rabaka da masifa,ciwon so ai masifa ne,Ahmad yace Nifa ba soyayya nakeyi ba,nace maka tunaninta Kawai nakeyi,Ni nayi love Allah kiyaye, gashi nan yarinyar ta Gama kashe maka zuciya cewar malam,Ahmad ya bada dubu goma shi Sam da gani yasan karya ne wannan cin

Please Login or Register in order to submit comment