Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

malamin yace idan matashi baida aikinyi Kar ya sake yayi Aure sabo da rayuwar yanzu,Haka Rannan wani yace Mata Kar su sake su auri mara sana'a,yanzu Kai Kuma kace ayi sama da biyu,Ahmad yace da Allah ku dinga duba littatafai sosai kafin ku fadawa jama'a wani abu,Ya za a dinga zuwa Ana Raina Mana hankali mun rasa inda kuka dosa wannan yace kaza wannan yazo ya karyata.

Malam ya kalle su yayi Dariya yace Dana fara Wa'azin ai sai ku Bari na Kai Aya,da sai ku tsaya bayan na Gama fadar falala ai zanzo nayi bayani akan Kuma wannan matsalar da kuka ambata Amma sai kuka rigani,Dariya Tawaga yayi yace karka zo Mana da gyara Malam Kawai mun kureka ka zugo ta yawwa,Kai ku tashi mu tafi Sallah Kuma da Muka bika Allah ya baka ladan Jan Sallah Amma wa'azinka 0/0 baka ci ba,Suka Mike suka fice.

Liman sallamar mutane yayi yace gobe zai Dora daga inda ya tsaya ya fita da sauri,Liman hamshakin me kudi ne Dan kasuwa ne na gaske,Su Ahmad ya dakatar a wajen masallaci suna tafiya,Tsayawa sukayi Liman yace cikinku duk ba me aure?Ahmad yace Ni ina da shi Amarya ce Bata tare ba Amma ta kusa,Yace mashaallah ai Kai na sanka a garin Nan har mahaifinka na sani,Ahmad ya tabe Baki,Jibson ya kalla yace Kaine kace kayi Niyyar yin aure baka ga Budi ba ko? Jibson yace kwarai kuwa,Liman yace to kaje ka Nemo yarinya Ni Kuma na tsaya maka har gidan Zama kyauta Zan baka aikinyi me tsoka Kuma Zan maka komai na auren,Jibson yace Malam karfa ka min Alkawarin Yan siyasa baza kaji da kyau ba,Malam yayi Murmushi sabo da yasan Basu San shi waye ba,Karfa ka bashi gida irin na talakawa talak idan irinsa ne ka rike abinka Bamu shirya aure ba sabo mu mun tsara Dole matanmu suji dadin duniya shi yasa Muka hakura da Aure muna talauci jira mukeyi sai munyi kudi cewar Mashkoor,Bash yace yawwa kaji dai Malam,Malam yace cikinku ma idan akwai Wanda yayi Niyya ya fada,Tawaga yace Marayu kannena sun ishe Ni ma Ina Ni Ina aure banyi Niyya ba, Mashkoor yace Ni kuwa Muna da Hali ra'ayi ne banyi ba,Banga wacce ta min ba,Malam yace Ina da Yara kaje ka gani idan da wacce ta maka a ciki, Mashkoor yace rabani da Yar malamai tazo tayi ta zunduma min Hijab a gida,idan nayi magana ta jawo Aya gwara wacce ta rike izu biyu na Sallah Yar jahila jahila Haka,Dariya suka bawa Malam yace duk Sanda ka shirya kazo ka gani dai, Mashkoor yace bafa zanzo zance gurin yarka ba ta malamai Dan Hannu bazan rike Mata bare Yar runguma a fara min wa'azi ai sai anyi aure etc bazan zo ba,Bash yace Ni ka ganni Malam a ministry of Environment nake Aiki Ina samu,Kuma Iyayensa ma duk ma'aikata ne Kawai Ni sai fara doguwa,idan ba fara ba taje,Malam yace idan Allah yasa kuma ka fada son bakar fa? Yace sai tayi bleaching Dole na siyo Mata mayamayai ta koma fara,Dariya Malam yayi yace Kai Dole sai fara? Bash yace ko bamagujiya ko arniya Matukar fara ce an Gama,ko a gidan karuwai take ba ruwana,Ni dama Malam ban damu da wata mace Virgin ba,Nafi son wacce ta San komai yawwa,Ni mace taje da Virginity nata ba ruwana,Kuma Ni ban taba Zina ba Kawai Ni Ba ruwana da wani virginity.

Malam ya kallesu Kawai ya zaro check na kudi,ya rubuta dubu dari uku ya bawa Tawaga yace gashi kaje ka kula da marayu idan wani Abu ya taso na iliminsu ko auren wata ko wani Abu ka sanar Dani Zan tallafa,Tawaga ya karba da mamaki ya dafa Ahmad yace Malam sai kace wannan Abokin Nawa king shi yake mana irin wannan kyaututtuka,Malam ya kalli Ahmad da mamaki Ashe Yana da tausayi,Kudi ya zaro ya Basu dubu goma goma kyauta har Ahmad ya mikawa,Jibson ya kyaftawa Ahmad Ido Wai ya karba sai ya Basu su Kara,Ahmad ya karba,Tawaga Dake tura machine dinsa ai sai ya buga machine tare da zanawa Malam kwabo a gabansa,Jibson yace karya ne wani ya kawo ma raini a garin Nan,Maganar dazu daka fada a masallaci Muka karyata ka yanzu mun gano gaskiya ce,Wuhuhu Mashkoor ya daga hannaye sama Yana jinjinawa Malam,Bash yace sai kayi Malam mun baka Shugaban limamai na Nigeria wallahi,Malam dai Kai ya girgiza Kawai tare da komawa masallaci inda motocinsa suke na Alfarma.

Ahmad kuwa Jibson ya bawa nasa 10k din yace ungo ka siyawa su Aymana littafan makaranta naji sun maka waya ance a siyo musu Books yace wallahi ga naji sunce gobe ma za a koresu daga school sabo kudin makaranta Abba Mutum biyu ya biyawa saura su takwas kowanne dubu goma Sha biyu,ga Jamila zasu Zana waec, Kuma Dan Iskanci baka fada ba? cewar Mashkoor, suna komawa gida Ahmad ya turawa Jibson dubu dari da Hamsim, Mashkoor ya bada dubu talatin,Shima Bash ya bawa Jibson 20k ,Tawaga yace kudin sun Isa da za abiya ko da Kari sai a ciri wani Abu a Nawa,Jibson yace ai sunyi yawa ma ciki har sai na siya musu taliya da macaroni dama sun Kare,tausayin Abba nakeji duk ya rame.

Ahmad yace yayi rashin Ummati ba Dole ba,Jibson yace sai na ganshi a Dan dakinsa yayi malahooo....yayi tagumi bashi da kawar Hira sai dai idan mun shiga ko su Aymana suje su tayashi Hira,Amma lokacin da Ummati tana da Rai sai dai kaji dariyarsu kyalkyalkyal,Ahmad yace muje mu samo Masa Dattijuwa wacce ta daina Haihuwa mu aura Masa ita ya rage zafi.

Mashkoor yace mu samo Masa me kyau mu siya Mata kayan gyara ta dinga birge shi irin Ummati suka Kama Dariya tare da cewa Haka za ayi,ga case din Brown gobe za a fara Suka fara shirya plan abinsu,Jibson yaje aka canja Masa salon Aski me kyau na Dan Kamala Amma fa Sumar akwai yawa ta matasan yanzu,Sajensa da gemunsa yasha gyara dama gashi wani chocolate kyakyawan matashi,Kaya kuwa Shadda sababbi aka dinka Kala biyar za a hurewa Bazawarar Baffan Brown kunne,Shi kuwa Bash Searching yake na inda za a samowa Baban Jibson Bazawara me Dan kwari.

Tun safe Aamna ta fara amfani da Magungunan Infection dinta,ciwon yaji magani da Allura ya tabo shi sai ta fara Jin kaikayi a gabanta,dama Likita yace idan ta fara Sha zata ji sabo da an tabo ciwon,Sanye take cikin wata Riga karama me Hannun Vest fara da tight baki,Ahmad ya Mata waya zaizo da dare zai Bata labarin Wa'azin da Tace ya zauna ya ji,Bata Yi zaton cikin gidan zai shigo ba,sai Jin sallamarsa tayi a palonsu,Mama ya gaisar ta amsa sama sama Amma ganinsa dauke da ledojin take away sai ta washe Baki harda cewa shiga mutuniyar taka tana ciki, ai kuwa ya wuce bedroom din Aamna,Mama sai kallo sai Harara baza su iya komai ba dama,Aamna sai soshe soshe takeyi duk ta rasa sukuni.
Yana shigowa ta janye Hannunta da sauri Amma ya rigada ya gani,Dariya ce ta kwace masa yace ai sai ki fada min nazo na tayaki,Kuka ta saki masa yace yanzu zanzo na tayaki kwantar da hankalinki.

Ba kinyi zaton nine ba lafiyayye ba to gashi reshe ya juye da mujiya,Kuma yau Hira zamu Sha babu soshe soshe,Aamna ta goge Hawayenta tana Dariya Tace Allah baka Isa ba ka tafi gaskiya,Amma Kuma gaskiya yasha kyau cikin wani yadi brown me azabar kyau sai kamshi yake zubawa,Tana kwance Bata tashi ba,Saman bed din ya haura tare da kwanciya shima,Tace ka rufe Kofar da key kasan Mama Kar ta shigo,ai ba Wani Abu zanyi ba Dan Kawai na kwanta mene a ciki ya furta tare da gyara kwanciyarsa.



An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment