Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kamar ba hausa girl ba saboda yadda accent d'in ya kama harshen ta duk da ba cikin walwala take ba amman muryar mai dad'in sauraro)_,
Tana gama fad'a ta kamo hannun Khadija kamar marasa gaskiya suka fara sand'a har suka fice suka bar layin gaba d'aya,
Sai da sukayi mik'ak'k'iyar tafiya sosae takusan 40mins ba wanda yacewa kowa komai,can Khadija ta nisa tace
"Wai yanxu Ameera ina muka nufa toh"
Shiru tayi sai hawayen da har yanxu sukan zubo lokaci-lokaci babu abinda ke yawo A xuciyarta sai maganganun Ya Haidar, sai da Khadija ta sake maimai ta tambayar da tayi mata sannan tace
"K'auyen Ku"
Da sauri Khadija ta dube ta kallon rashin fahimta tace
"Wane k'auyen namu?"
Cak! Tajanyo Khadija gefe ta fuskan ce ta tace
"Khadija inda Mama(Baba larai) take nake nufi!,nasan kin sani don haka kiyimin tai mako ki shige gaba muje mu nemota,zamana a garinnan akwai had'ari Babba!, k'auyen shine kwanciyar hankali na!,gwara nakoma can nak'arasa rayuwata!"
Ta k'arashe maganar cikin k'unar zuciya,
Khadija da tayi mutuwar tsaye da jin kalaman Ameera tace
"Haba Ameera wani irin k'auye kuma?,na cikin k'auyen ma suna baro shi su taho nan Amman shine zaki ce haka,Su Mama basu Isa suyi miki Abinda Allah bai hukunta miki ba,Ko kin manta na tuna miki? wace irin wuya da Azaba ce basu baki ba?kuma ba gashi Allah ya rayaki ba? Infact ma ki kalle ki mana Ai zaman k'auye bai kama ceki ba Sam!,Ni shawarata kawae ki taso mubi ta can layin mukoma makaranta gun Malam Ismael ya kaimu gun mahaifiyarsa mu zauna kafin Baba ta dawo musan Abin yi"
Ameera da ta kafe ta da sexy eyes d'in ta masu hautsinawa mai kallon su tunani tace
"Khadija duk ki ajiye Wannan maganganun a gefe,kawai indai kina k'auna ta da gaske ki tashi mutafi gun hawa mota just,kuma maganar Malam da kike Ai Sam bai dace ba infact Ai sirri nane"
Khadija tace
"To yanxu A Daren nan zamu tafi jigawa Ameera kinyi mana Adalci kuwa?, kuma inama muka ga kud'in transport ma safe?"
Mik'ewa Ameera tayi tace
"Duk ba matsala,Adalci kuma kiyi hak'uri hakan shine mafita!"
Girgiza kai Khadija tayi kawae itama ta mik'e ta d'au jakar suka tafi.
★★★★★★★★★★★★★
Duka b'angare biyu-biyun shirye shiryen biki Ake babu kama hannun yaro,Ta fannin gidan su Abdul mummy tayi rawar gani domin Ankaiwa Husna lefe na kece raini,Ankai Lafiya cikin girma da karramawa duk da har yau Abdul bai sake taka k'afarsa ko idon sa ga Husna ba don haka kawae xafin ta yake ji,
Ta fannin gidan su Husna ma Mummyn ta shirye shiryen suke gadan-gadan ta fannin komai duk da Mummyn Abdul tace musu kawae Husna za'akai basu buk'atar furniture's amman saida tayi mata komai dai sai Sam barka,
Ga su Husna da friends d'in ta kuwa shiri suma sukeyi sosae tare da bin duk wasu hanyoyi da zasu mallakowa Husna Abdul tun daga gyaran jiki,kissa da dai sauran su,
'Bangaren Farouq ma da Amaryarsa Farida haka Abin yake komai dai Alhmdllh,
Biki yau saura kwana 3 Afara Amare tin yanxu sun sha kyau sai muce Allah ya kaimu.
Ta fannin zaman K'ibd'iyya a gidan Abdul shima dae sae godiya domin baya mata wasa ko kad'an yanxu duk ta rage rawan kannan domin sau biyu yana Zane ta,Ya sanya ta A islamiyya tana ta zuwa,
Shikam Abdul komai yana tafiya dai-dai sai takurar da mujeedat bello sectarian sa kemasa a office don haka yanxu yasa Andawo masa da securities d'in sa da _BALA_body guard d'in sa,tinda dama Akwaisu dama,daga baya ya nunawa Abbansa baya buk'atar su Amman yanxu kasancewar yadda ya zama da yanayin unguwar da Aikinsa yasa Aka dawo masa da su,
Babu Abinda ya dameshi da harkar Bikin daya ke kusanto masa don komai mummy tace masa sai dai yace mata duk yadda tayi dai-dai ne,shikuwa Abbansa dama d'an kallo ne ganin abin duk nasu ne kuma dama mummy bata fiya sashi ba aciki Duk da hakan yayi masa dad'i don dama 2days baya jin shi okay ga tafiyan sa data taso,
'Bangaren Abokan su ma Abdul ya sakarwa su Farouq da KB ragamar komai a hannun su da duk wasu Kud'i da za'a nema don baya san tension, sukuwa Tsare tsaren su kawai sukeyi wanda hakan yayi masa dad'i.
_*PINKY CE*_
[1/26, 3:02 PM] maryam Tahir Author Y4: *'YAR ZINA CE👄*
_......Adulterer's Daughter_
*A TRUE LIFE, TOUCHING HRT & LUV STORY*
_BY_
*MARYAM PINKY*
www.Maryampinky@facebook.com.
*®REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S*
_{We don just entertain nd educate,we touch the heart of readers❤_}
#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
*IG PML WRITERS*
#https//www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com
*Congratulations SADNAF💅 Na taya ki murnar kammala littafin ki S🅰B🅰N S🅰LON Y🅰UD🅰R🅰,Hak'ik'a kin baje basira da zallar hazak'a,Allah yasaka miki da Alkhairi (lucky may not leave u dear),up.up.up.up..Allah yaraya Affan da Ikram tamu👏*
*DEDICATED THIS PAGE TO YOU*
2⃣7⃣
Kwanciya yayi akan gadon rubda ciki bayan ya janyo pillows guda biyu sannan ya runtse idon sa tunanin dream girl d'insa ya fara yi babu Abinda ke masa yawo a zuciyar sa da cikin kunnuwan sa sai kukan da ta dinga yi masa cikin mafarkin da yayi d'azu da Asuba daya koma bacci, _Ya ilahi_ ya furta yana toshe kunnuwan sa da duka hannu bibiyun,ganin ba wata mafita yasa ya tashi ya shiga ya d'auro Alwala a toilet ya fito,sallaya ya shimfid'a ya fara jero nafilfilu akan Allah ya shiga lamuran sa,bashi ya kwanta ba sai Around 2:30pm.
K'ibd'iyya kuwa tana fita daga part d'in Abdul part d'in ta ta wuce sai da ta zab'a sannan ta fito ta shiga part d'in Husnayi kallon falon ta shiga yi d'aya bayan d'aya tana tab'e baki kamar taga kashi,bedroom d'in ta nufa tayi knocking sau biyu ta kara kunnen ta,daga can ciki taji Husna tace
"Shigo..." Cikin wata irin murya,dariya K'ibd'iyya ta d'an yi don tasan Husna ta zata Abdul ne,cikin zuciyarta tace
"Hmmnn Yaa Abdul ne ma zaizo miki d'aki,u re lost"
Sannan ta tura k'ofar ta shiga,A zaune ta hangota kan tsakiyar gadon amman ta d'an rufa,
Husna da gaba d'aya ranta ya b'aci ganin ba Abdul bane ta bi K'ibd'iyya da wani banzan kallo sannan cikin k'ufula tace
"Ke kuma meya kawo ki d'akina?"
'Dan tab'e baki K'ibd'iyya tayi tace
"Anshi inji Yaa Abdul"
Tana Ajiye akan bedside ta fice tana dariya k'asa-k'asa,
Husna hawayen takaici ne suka zubo mata,takifa kanta kan filo tace
"Na shiga uku ni Asma'u, na d'au kowa kaina,Ace kusan 1:00pm ankawo wa mutum Amarya amman ko lek'owa saima Aike..." Wasu hawaye masu d'umi ne suka gangaro mata,tabbas tasan Abdul ba son ta yake ba but atleast ko Dan son da take mai Ai ya zo ko duba ta ne yayi,ledar da K'ibd'iyya ta Ajiye mata ta d'auko ta bud'e, Aikuwa ranta ya sake b'aci ganin kaza da yought aciki,wato bazai zoba...
Shawara ce ta fad'o mata don haka ta ta shi ta d'auko Phone d'in ta daga chargyn da ta jona,
Bakin gadon ta dawo ta zauna zuciyar ta na mata zafi,number Rukky ta yi dialing, sai da takusa tsinkewa sannan ta d'aga,Husna kamar zatayi kuka tace
"Hello Rukky.."
Rukky cikin alamun mai bacci tace
"Hello wacece?"
Husna tace
"Rukky na shiga uku Yaa Abdul fa bai shigo ba"
Rukky najin muryar Husna ta d'an ware tace
"Ki ce Allah?"
Husna tace
"Wallahi.. Da ya zo nama kirawo ki ne"
Rukky ajiyar zuciya ta sauke tace
"Okay...kinga karki damu,Gobe zamuzo but make sure da safe kinje d'akin a hakan da kike before goben musan what's next"
Cikin Gamsuwa tace
"Toh"
Daga nan sukayi sallama ta ja blanket ta kwanta zuciyar ta na suya.
5:00pm ya tashi ya shiga toilet ya d'auro Alwala cikin sauri ganin yaso ya makara,A d'akin yayi sallah sannan ya zauna agun yana Addu'oin sa,sai 6:40am ya tashi daga gun ya koma falo ya kunna TV yafara kallon labarai,lokaci-lokaci yana Jan tsoki don shi ya fiso yaje office da zaman gidan nan don babu abinda zaman yake Amfana masa,amman ya zaiyi hutun 1week Abba yasa aka bashi,mik'ewa yayi ganin 7:32am ya zira flat shoe ya fice daga d'akin cikin zuciyar sa yana mita
_mtsswcc Mutum yana zaune Yana rayuwar sa peacefully an had'a masa tensions_
Part d'in K'ibd'iyya ya shiga kamar me ciwon baki yayi sallamar, bata falo don haka bedroom d'in ya shiga nan ma bata nan Amman ga kayayyakin ta nan akan gadon,jiyo motsin ruwa yayi a toilet don haka ya zauna bakin gadon ya d'an kishingid'a yana danna wayar sa,can sai ga ta tafito d'aure da towel cikin gudu-gudu taje gaban mirrorn ta d'auko lotion ta tsuguna agun ta fara shafata tana zance ita kad'ai
"Yaa baizo ya tashe ni ba yau,I'm late nasan sai uncle Thomas ya zaneni..."
Shi kuwa Abdul yana jin ta yayi shiru Dan tinda tafito kallo d'aya yayi mata ya cigaba da browsing d'in sa,tasowa tayi da nufin d'auko uniform d'in ta hawo kan gadon Aikuwa tasa wata irin k'ara data sa Abdul Ajiye wayar sa ya toshe kunnensa, ganin tak'i ma bud'e bud'e idon ta sai k'arar da take cigaba dayi yasa ya gane tsora ta tayi,mik'ewa yayi ya rik'o kafad'ar ta,Aikuwa tayi wani irin zillo ta mik'e zata gudu wanda yayi sanadiyar fad'uwar towel d'in ta,zaro ido Abdul yayi ganin ta samb'al sai kuma ya mik'e ya rik'o ta duka jikin sa yana k'are mata kallo,ita kuwa da ta dawo hanyacin ta ta lura da yanda take,Aikuwa ta wawuri towel d'in da gudu tayi band'aki jikake bam! Ta banko k'ofar har da Mirza key,
Abdul kuwa da ya fara hawa network ya dafe kansa tare da rufe idon sa,wani irin bak'on yanayi ne yake ji,sai da yayi kusan 5mins ganin ba fitowa zatayi ba yasa ya mik'e jiki ba kwari ya fice,Bedroom d'in sa ya wuce ya zube kan gadon yana maida numfashi,gaba d'aya yayi loosing Appetite d'in sa,A zuciyar kuwa cewa yake
"Babyn!,baby!!.. Just imagine"
Wata zuciyar tace
"To yaushe ta girma baka tab'a kula ba?"
Mtsswwww yaja tsoki ganin zata burkita masa brain,shi dai yasan ba SO bane,sha'awa ce kawae da take damun sa,mtssww ya sake Jan tsokiii ya mirgina gefe ya rintse ido amman babu Abinda yake gani sai structuren K'ibd'iyya,sake runtse ido yayi ganin K'irjin ta namasa gizo, Abu kamar wasa sai ga k'aramin Abu na neman zama Babba,don marar sa wani irin rik'ewa tayi kamar zata fashe,ganin yana neman fita hayyacin sa yasa ya mik'e hannun sa dafe da marar sa ya jawo drawer ya d'auko pills d'in sa ya sha,Agun ya zube wani wahalallan bacci ya d'aukesa Agun.
K'ibd'iyya kuwa tafi 1 hour a toilet takasa fitowa dan gani take kamar yana nan bai tafi ba,jin cikin ta na kukan yunwa yasa ta lek'o ta Ya'r k'ofar toilet d'in, bata hango komai ba,don haka cikin sand'a ta fito taje tasawa keys A part d'in nata,dawowa tayi ta zauna kan gadon tana kallon kanta A mudubi sannan tana sauke Ajiyar zuciya kamar wadda tayiwa sarki k'arya,mik'ewa tayi ta dawo gaban mudubin ta tsaya tana zacen ita kad'ai tana bud'a towel d'in
"Yanxu A haka Yaa Abdul ya ganni?"
Rufe fuskarta tayi kamar da mutum agun tace
"Aikuwa bazan sake bari mu had'u ba"
Haka tayi ta zantukanta ita kad'ai kamar Mara sense,sai da tagaji sannan ta tashi ta d'auko Atamfa tasa don Makaranta ta sha ruwa don lokacin 10:00 tayi, zama tayi a falon ta ta d'auko kazar jiya da tafara ci tana kallo,idan kuma tatuna abinda ya faru d'azu sai tayi Murmushi daga haka itama bacci ya d'auke ta a gun.
Abdul hayaniyar motoci yafara jiyowa yasa ya farka around 11:30pm,A hankali ya bud'e idon sa da yayi jazur,A hankali ya tashi yaje ya rufe windows d'in da baya san jiyo hayaniyar nan,toilet ya shiga ya tsarkake jikin sa don kaca-kaca yaga jikin sa,zuciyar sa a cunkushe ya yi wanka ya fito d'aure da towel a k'ugunsa,gaba d'aya jikin sa A sanyaye yake don tafiyar ma neman gagarar sa take don haka zama yayi bakin gadon ya rufe idon sa,Wannan wace irin K'addara ce haka,wai ma wacece yarinyar nan ne me zuwa masa a mafarki?sake runtse idon sa yayi da dafe kansa da hannu d'aya tinowa da yadda Ya kusance ta a mafarkin da yayi yanxu,Kukan da ta dinga yi ne yake ta masa Amsa kuwa a kunnensa da zuciyar sa,Addu'a ya shiga karantowa Allah ya tsare shi daga Aikata ZINA.
Wayar sa ce yaji tana ringing, hannu ya mik'a ya janyo ta da nufin yin rejecting,ganin Farouq ne yasa yayi Accepting kiran tare da Karawa a kunnensa,
Farouq daga d'aya b'angaren yace
"Man ina gidan ka yanxu"
Mik'ewa Abdul yayi yace
"Enter mana,ina part d'ina"
Okay Farouq yace sannan sukayi hanging up,
Da sauri-sauri duk da ba kwari jikin sa ya shirya cikin wata Milk color shadda getzner,sai maik'o da kyalli take,tayi matuk'ar amsar sa,gashin kan nan yasha gyara,hula ya d'auko ya Koma falo ya zauna bai saba,Lipton ya d'auko da ruwan zafi a cup ya fara sha yana kallo...Amman kana kallon sa kasan Yana da damuwa,
Farouq ne yayi sallama ya shigo,Amsa masa yayi ya cigaba da kallon da yake yi,guri yasamu kan 1seater ya zauna yana kallon TVn shima,
Muryar Abdul yaji yace
"Ashe kana kusa ma"
Kallon Abdul d'in yayi yace
"Eh..har mafa na wuce naga kiran mummy tace wayar ka switch off da tayi dialing"
Ajiye cup d'in yayi ya d'an yamutsa fuska yace
"Uhmm,kai d'in ina kaje ?"
Murmushi Farouq yayi yace
"Sweety na kai makaranta yau tana da paper by 12:00"
Tab'e baki Abdul yayi yace
"Huummmnn..."
Dariya Farouq yayi ya d'aga masa gira yace
"Bani Lipton d'in mana"
Ignoring d'in sa yayi,
Tasowa Farouq yayi ya dawo kusa da Abdul d'in ya mik'a hannu kan d'an k'aramin centre table d'in ya d'auki Lipton d'in yafara sha,
Abdul ya d'an kalle shi ta gefen ido yace
"Ita sweetyn bata tsaya ta dafa maka ba.."
Ajiye cup d'in Farouq yayi yana Murmushi yace
"Jealousy.
Zama Abdul yayi a k'asa kan rug sannan yace
"Allah ya sauwak'e"
Kecewa Farouq yayi da dariya ganin yadda ya bada Amsar,
Abdul ya kalle shi yace
"What's funny?"
Yana dariyar yace
"Nothing.."
Farouq bayan yatsagai ta da dariyar yace
"Wai ina wifey's d'in naka ne?"
Banza yayi da shi don yaga Farouq d'in yau ya'n tsokanar ne akusa,
Sake maimai tama sa tambayar yayi namma yayi masa banza,sai ma janyo filon kujera da yayi ya jingina a bayan sa ya d'an zame ya kwanta,
Farouq ya sake cewa
"Da wacce Kayi Amarcin ne a ciki?"
Ya fad'a yana k'unshe dariya,
Tsokiii Abdul ya ja ya juya masa baya ma,
Cikin dariyar yace
"Bari naje na kirawo su duka nan muyi fira"
Jiyowa yayi ya tashi zaune ya kalli Farouq yace
"Stop that childishness plsss..something bothering me u re disturbing me,what's this plss,"
Saukowa Farouq yayi shima cikin serious tune yace
"Me ke damun naka friend?"
Shiru yayi for some seconds sannan ya kalli Farouq yace
"Jokes apart...wllh ina cikin damuwa tin ba yau ba,buh today abin yazama worst.."
Ya fad'a a sanyaye,
Shima Farouq tini jikin sa yayi sanyi Dan tinda har Abdul ya bud'e baki da kansa yace yana da damuwa to tabbas yasan abin Babba ne,don haka ya sake shiga serious yace
"Me ke nan friend?"
Sunkuyar da kai yayi k'asa sannan ya d'ago yana jijjiga kai idon sa sun sauya colour zuwa red,tunani yake cikin zuciyar sa shin ya sanarwa Farouq or not?,zuciyar sa ce tace
_A'a Abdul this is ur secret,_
Muryar Farouq yaji yace
"Kasanar dani Abdul matsalarka,ni ba wanda ya kamata ka b'oyewa bane,I will help u atleast ko da with a piece of Advice ne"
Abdul ya jijjiga kai yace
"I knw..buh wllh friend ina cikin matsanan ciyar Heart desire!..yau har takai a mafarki ina Auratayya da wata yarinya,Abin is too worst,bana iya controlling kai na idan na fara feeling d'in, I don knw what to do cox yanxu pills ma basa rik'e ni ko na sha!!!"
Ya fad'a kamar zai yi kuka,
Farouq da yayi sunan zaune tinda Abdul yafara bayani ya kalleshi yace
"Abdul wannen inaga Ai anyi akan gab'a,ina tunanin matsalar nan tazo k'arshe"
Abdul cikin rashin fahimta yace
"Like how?"
Murmushi Farouq yayi yace
"Menene Amfanin Husna tinda kace K'ibd'iyya tayi maka k'ank'an ta?"
Tsoki Abdul ya ja yace
"Farouq ya ina gaba kana mai dani baya?"
Farouq yace
"To fad'i bayan dana maida kai"
Dafa kafad'ar Farouq d'in yayi yace
"Farouq ka fahimce ni mana.."
Katse shi Farouq yayi ta hanyar d'aga mai hannu yace
"Abdul baka da wani sauran bayani,Babu wata hujja da za'a karb'a daga gare ka at this time,your problem ix lyf partner kuma yanzu ankawo maka har biyu,to kuma what next?"
Shiru Abdul yayi sannan yace
"Farouq wallahi har yanxu ban sami wata yarinya da zan iya so ba ko tayi dai-dai da ra'ayina,As for me gaskiya bazan iya rayuwar Aure da wadda bana so ba.."
Farouq da maganganun Abdul suka fusa ta shi yace
"To yanxu su kuma wad'annan na gidan fa?"
Abdul yace
"Nifa su ba damuwa na bane,mummy ce ta Ajiye su not me,don ba wadda nace ina so"
Farouq ya masa wani kallo yace
"To Aikuwa ya kamata ka sanar da Mummyn ta sani tin wuri"
Cikin rashin ko inkula Abdul yace
"It doesn't concerns me"
Farouq cikin kulawa yace
"Okay.... But why not kaje ga Asma'u first idan yaso nangaba idan ka samo dai-dai kai d'in sai ka sake Aura"
Batare da ya kalle shi ba yace
"Nagama magana fa"
Cikin fushi Farouq yace
"Okay...to tinda haka kace kar ka sake fad'a min wani problem Associated with this..kaje can ka k'arata da girman kanka"
Murmushi Abdul yayi ganin yadda Farouq ya fusata,matsowa yayi ya dafa Farouq d'in yana killersmile d'in sa yace
"Farouq nine mai girman kan?"
Farouq yace
"Eh..kai mana"
Girgiza kai yayi yace
"Friend girman kan menayi Yanzu nan?"
Ture shi Farouq yayi yace
"Ni matsa Dan Allah... An fad'a maka best solution kaje ka sauke girman kanka ka rarrashi Husna ka samarwa kanka lfy ka tsaya,"
Tab'e baki Abdul yayi yace
"Godforbbid, ko macen da nakeso bazan iya wani lallashi ba Akan wannan bare wadda bani da wani feeling akan ta After that ma taimakon ta zanyi"
Farouq Murmushi yayi wanda shi kad'ai yasan manufar sa yace
"Okay...Allah ya baka sa'a,Ai Alhmdllh naji dad'i ma da pills d'in suka fara dena yi maka Amfani that means kana kan gab'a"
Yayi wani Murmushin sannan ya cigaba
"Kuma idan tura takai bango kaga dole rak'umi ya sha ruwan ya'n tsaki, At the end of the day kuma girma ya fad'i."
Mik'ewa Abdul yayi without any concern ya nufi bedroom don anfara kiran sallah yabar Farouq yana b'ab'atu shi kad'ai.
Ganin Abdul ya fito d'aure da Alwala yasa shima ya shiga toilet d'in falon shima ya d'auro,bayan sun idar da sallar ne Abdul ya kwanta Agun yana fuskantar Farouq da yake ta cika yana batsewa,Abinma yaso bashi dariya don haka yana d'an Murmushi yace
"Amman dai dama sweetyn taka ta b'ata maka rai jiya shiyasa kazo kake sauke min shi Anan"
Farouq yace
"All those matters A side, I'm tasty ka tashi ka karb'o mana Abinci don naji ya'n uwan nata sun tafi,"
Murmushi Abdul yayi yace
"My one nd only friend over d world,Sweetyn taka bazata dafa mana ba?"
Remote ya d'auka yana neman channel yace
"Ai Dan bata nan ne,buh don't bother by 2:00pm zan d'auko ta,sai ta dafa mana tinda kai na gidan ka bashi da Amfani"
Abdul Murmushi yake tayi tinda Farouq yafara magana yana danna wayar sa,kara wayar yayi a kunnensa sannan yace
"Bala u re very stupid, for almost 3times I've called u.."
Ya d'an tsagaita sannan yaja tsokiii yace
"Mind it...just 2 mins inajiranka @sitting room downstairs"
Ya kashe wayar yana cewa
"Useless guy"
Sai kuma ya mik'e yana saka hula ya dubi farouq yace
"Tashi mukoma downstairs"
Ba musu ya tashi bayan sun kashe kayan kallon,ta gefen part d'in sa sukabi suka sauka cikin sitting room d'in na Alfarma,zama sukayi suka sake kunna TV suna kallo sometimes suna fira akan film din da ake haskawa ta tauraron d'an Adam(setellite)
Sai da sukayi 5 mins sannan Bala ya shigo cikin babbar muryarsa ko sallama babu yana cewa
"Gaskiya BOSS ka cab'a Aradu Kayi dace indai Wannan ce matar da ka Auro mana.."
Abdul cikin takaici yace
"Ina Abinda na Aikeka?"
'Dan durk'usawa Bala yayi yana gyara facingcap d'in kansa cikin d'an diriricewa ya wage baki yana cewa
"Ehh..boss Ai yanzu Amarya zata kawo.."
Cikin tsawa Abdul yace
"Wacece haka kake magana?"
Sake washe baki yayi UA d'an ja da baya yace
"Amaryar ka boss mana,Ai na taho zan kawo na gamu da ita tace nakawo zata had'o muku ta kawo Yanxu.. Gaskiya boss Madam tayi akwai kirki har..."
Dariyar da Farouq yake tayi ce yasa bala yayi shiru yana kallon Farouq Dan tinda ya shigo bai kula da shiba,d'an matsowa yayi kusa da Farouq yana Murmushin sa yace
"Oga ko ba haka bane?"
Cikin rad'a yayi maganar da d'an tsoro,
Farouq yana dariya yace
"Sosaima"
Bala yace
"Ahan nasan dama boss sai... "
Jifan da Abdul yayo masa da filo ne yasa ya fice da gudu yana cewa
"I'm sorry boss"
Dariya Farouq ya cigaba dayi sai da yayi mai isarsa sannan ya tsagaita ya kalli Abdul daya dafe kai da hannu d'aya yace
"Gaskiya Aikin Bala yana kyau.."
Tsokiii Abdul yaja ya firzar da iska yace
"He will regret it,zamu had'u"
Murmushi Farouq yayi yace
"Sai hak'uri, dama idan bakai ba wazai iya da bala,kullum shirmen sa gaba yake,Allah ya gyara dae"
Girgiza kai yayi kawai ya ciza d'an yatsan sa yace
"Friend wllh bala kad'ai zai iya samin minor hypertension"
Dariya Farouq yayi yace
"Allah ma ya kiyaye,naturen sa ne haka"
_Bala bodyguard din Abdul ne na cikin gida,Aikin sa gogewa Abdul mota,ko driving d'in sa ko rakashi gu,karb'o jakar sa da dai sauran su,bak'ine mai jiki,gajere amman mai son gayu ne musamman na k'ananan kaya,yana da ban dariya da shirme_
_*PINKY CE*_
[1/26, 3:02 PM] maryam Tahir Author Y4: *'YAR ZINA CE👄*
_......Adulterer's Daughter_
*A TRUE LIFE, TOUCHING HRT & LUV STORY*
_BY_
*MARYAM PINKY*
*®REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S*
_{We don just entertain nd educate,we touch the heart of readers❤_}
#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
*IG PML WRITERS*
#https//www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com
2⃣6⃣
Su Ameera kai tsaye tasha suka tafi babu wanda yake wa d'an uwansa magana,sai da suka je tasha suka yi sallar ishaa sannan suka sami motar zuwa jigawa direct,babu b'ata lokaci suka hau sauran passengers ma suka hau kasancewar golf3 ce nan da nan suka d'auki hanyar jihar jigawa,
Tinda suka fara tafiya Ameera ta kifa kanta cikin tsakanin cinyoyin ta tafara kuka Mara sauti,ko sau d'aya bata d'ago ba don kud'in ma kawae Khadija ta bawa,ita kad'ai tasan abin da take ji cikin xuciyarta, Haka ta kasan ce har Around 11:00pm suka sauka A bakin garin,kasancewar lokacin sanyi ne yasa babu mutane sosae sai d'ai d'aiku,Anan bakin shiga cikin k'auyen suka tsaya cirko-cirko,can saiga wani mai mashin zai shiga ciki,Khadija ce har ya gifta su ta tsaida shi,cikin sa'a kuwa ya tsaya,bayani tayi masa nason shigar dasu ciki da yake so yayi,ba musu ya fad'a musu kud'in sukayi goyo suka tafi,
Kwantace Khadija ta dinga yi masa har suka iso bakin wani gidan jar k'asa,bayan sun sauka sun sallame shi ne sannan Ameera cikin rawar sanyi tace
"Inane?"
Taso bawa Khadija dariya amman sai ta gimtse ta nuna mata,tare suka shiga ciki,gida ne k'aton gaske kamar gari guda,babu kowa a tsakar gidan duk mutanen gidan da Alama suna cikin d'akunan su,sai dabbobin su da ya'n tarkacen su,sallama Ameera tayi cikin muryar ta mai Daddan Amo,shiru har sau kusan biyar,Khadija ce tace mata
"Inaga fa sunyi bacci yanxu fa kusan 12:00,zo mu wuce kawai,"
Ba musu tabi Khadija a baya inda ta nufa wani siririn lungu,suna fita daga ciki sai gasu a wani sashin Amman ya d'an fi wanda suka baro kyau,kaitsaye wani d'aki daga gefe taga Khadija ta nufa,A bakin k'ofar suka tsaya sukayi sallama, shiru nanma,duk suka dubi juna,sake wata sallamar sukayi,daga ciki sukaji Anyi gyaran murya,yaye labulen Khadija tayi Suka shiga ciki,Aikuwa dai saiga Baba larai tana sallah, kan wani k'aramin gado Khadija ta haye ta tukuikuye cikin zunbulelen hijjabin ta don ba k'aramin sanyi take jiba,itakuwa Ameera gefe ta d'an takure itama ta shige cikin hijjabin saboda yadda wani irin zazzab'i ke neman shigarta.
Baba larai tana idarwa ta juyo ko Addu'a batayi ba don cike take da tsoro ta dube su tana mik'ewa tsaye
"Ku!..Lafiya kuwa?"
Ta zauna bakin gadon tana kallon Ameera dake k'asa,
"Kunyi shiru,daga ina kuke a Daren nan?"
Tasake tambayar su,
Khadija ce tayi juyi ta sauko daga kan gadon tace
"Kingan tanan ita ta dage sai mun taho wai su Mama da Ya Haidar ne suke neman ta zasu kashe ta.."
Mama da tinda Khadija tafara magana ta zazzaro ido da rik'e baki tace
"Kisa!..?to me yayi zafi haka?"
Ta fad'a tana sake kallon su,
Khadijan ce dae ta sake magana dan Ameera har yanxu ko motsi ba tayi ba tace
"Gata nan dai,Nima daga hanyar makaranta muka had'u dan ko gidan banje ba muka taho nan d'in"
Gyad'a kai Baba larai tayi alamar gamsuwa sannan ta kalli Ameera tace
"Me kikayi musu toh?"
Numfasawa tayi ta goge Kwallarta batace komai ba,baba larai tafara fusata tace
"Kinga ke matsalar ki ,Ace ayi ta yiwa mutum magana amma bazai ce komai ba eyeee?,wannan shirun da kike ina fad'a miki idan kika yiwa mai zuciya a kusa wallahi idan bai dake ki ba sai ya mangare ki,"
Tad'an ja saki zata tashi,
Da sauri Ameera ta rik'e ta tana hawaye da girgiza kai don tama kasa magana,Baba larai ta sake cewa
"To..idan bazaki fad'a ba matsa ki bani guri"
Sai da ta sai-sai ta kanta sannan tayi

1 Comments On YAR ZINA CE
avatar
abdulkadir-6

1 year ago

Reply

Is a very educated and interesting novel

Please Login or Register in order to submit comment