Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya fito central falo,K'ibd'iyya ya hango kan dining tana breakfast, shima gun ya hau yaja kujera ya zauna bayan ta gaishe shi ya kalleta da kulawa yace
"Kin iya karatun?"
Eh tace masa daganan ya shiga karyawa shima,bayan sun gama ne suka fito bala ya d'auke su suka tafi.
★★★★★★★★★★★★★
Ameera ce zaune acikin d'akin su suna cin abincin rana ita da khadija kasancewar Baba larai tana gun sai da Abincin yanxu kasuwa Alhamdulillah Dan yanxu shago ta bud'e kamar restaurant har ya'n aiki ne da ita,hannun ta rik'e da littafin Arabiyya tana ci tana karantawa a zuciyar ta,Khadija ce ta warce littafin tace
"Haba! Ke Wannan karatun yayi yawa.."
Hararar ta tayi ta d'aure fuska tace
"Ban littafina"
Khadija tura littafin tayi bayan ta tace
"Ank'i abakin,ba kin iya karatun ba,naga ma ko baki iya ba ke badukan ki zai yi ba"
Tashi tayi ta ajiye cokalin tace
"Amman ko ba dukana zai yiba ae na iya ko Dan kar ya'n ajin suga laifinsa kuma shima ae zai fi jin dad'i"
Tana gama fad'a ta fice tsakar gidan ta wanke hannun ta,
*@5:00pm*
Ajin cike yake da d'alibai kowa yayi tsit amman fuskokin su kamar ance musu iyayensu sun mutu,duk gumi sukeyi duk da fankar dake ta juyawa,babu abinda ke tashi sai sassanyar muryarta mai cike da haiba,karatu take ta karantowa tajweedan tarteelan wanda yasa Malam Ismael lumshe ido yana sauraren ta tare da sauran d'aliban da zuciyoyin su kamar zasu fito,ji suke kamar su shak'e ta Dan bak'in ciki,
_"sadak'allahul azeem"_ ta furta,a hankali ya bud'e idon sa ya sauke su akanta itakuma tayi saurin sauke idon ta k'asa,juyowa yayi ya kalli taron d'aliban dake gaban Allon da zasukai 45 mata da maza sai muzurai suke,gyaran murya yayi ya kallesu yace
"Ku kalleku kusan Ku 45-50 amman ace shafi guda d'aya tsawon kwana biyu kunkasa haddacewa sai mutum d'aya tak! Don Allah ko kunya baku ji ba?"
Shiru duk sukayi sai na bayan da suke k'us-k'us,
Ya cigaba da cewa
"Don haka yanxu...."sai kuma yayi shiru yana shafa kwantaccen sajen sa yace
"Ameera!"
'Dagowa tayi tace "Na'am..."
Yace "zo nan"
Tasowa tayi cikin nutsuwa ta tsuguna agan sa tace "gani"
Mik'o mata sharb'eb'iyar bulalar hannunsa yayi cikin d'aure fuska Dan kar tayi masa musu yace
"Ungo nan!!!"
Hannunta na kyarma ta Amsa ganin fuskar sa ba wasa,
Cikin zazzare mata ido yace
"Kowa kiyi masa 10-10, maza fara"
Tuni idanunta suka fara zubo da kwallah,muryar sa taji yace
"Maza fara mana!"
Kallon d'aliban tayi bugun zuciyarta na k'aruwa taga sai banka mata harara suke kamar zasu cinye ta,
Jin ya daka mata tsawa yasa ta matsa tafara dukansu a hankali, ganin ba dukan shigar su yake yi ba yasa ya karb'a yayi musu,bayan sun zazzauna ya cigaba da yi musu fad'a sannan ya gargad'e su akan ko kallon banza bai Amince ayiwa Ameera ba...
_*PINKY CE*_
[1/26, 3:02 PM] maryam Tahir Author Y4: *'YAR ZINA CE👄*
_......Adulterer's Daughter_
*A TRUE LIFE, TOUCHING HRT & LUV STORY*
_BY_
*MARYAM PINKY*
www.Maryampinky@facebook.com
*®REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S*
_{We don just entertain nd educate,we touched the heart of readers❤_}
#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
*IG PML WRITERS*
#https//www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com
_Alhamdulillah ala kulli Halin gaskiya babu abinda zance daku masoya littafinnan sai godiya,Ni na tabbatar da qaunar da kuke min,nagode Allah yasaka da Alkhairi masuyi min Addu'oi.Allah yabar zumunci_
2⃣9⃣
*After 3days*
Abdul yayi resuming office Dan baya k'aunar zaman gidan,ya shirya kamar kullum cikin brown Armani suit da cover shoe yafito sai sassanyan K'amshi yake fitarwa,part d'in K'ibd'iyya ya shiga ya tarar tana saka socks ta shirya,Murmushi amman cikin zuciyar sa don yaga so many changes daga Warning d'in da yayi mata kan late da take,bai shiga ba ya cake a k'ofar yana kallon ta,sai da tagama ta mik'e sai ta ganshi tsaye k'ik'am fuskar nan babu Annuri,ja da baya tayi zata yi k'ara sai tatino kashedin da yayi mata shekaran jiya akan k'arar da tayi,rufe baki tayi da hannunta tace
"Mrng Yaa Abdul"
Kamar bazai amsa ba sai kuma yace
"Mrng"
Yana fad'a ya juya ya bar gun itama cikin sauri ta biyo shi suka sauko,Bala da yake jiran su dama ya taho da d'an gudun sa ya k'ame yace
"Boss barka da Asuba"
Harara Abdul ya watsa masa yace
"Sai yanxu ka tashi?"
Da sauri ya jijjiga kai yace
"Sorry boss kallo nayi jiya"
Tsokiii Abdul yayi ya fad'a motar Dan baya son shirmen bala,K'ibd'iyya ma ta shigo bala yaja suka tafi yana basu labari.
Sai da ya Ajiye K'ibd'iyya sannan Abdul yace mata
"Zai dawo d'au kanki bala"
To tace sannan ta fita,
Bayan sun hau kolta ne bala ya d'an jiyo yace
"Boss Uwargidan nan taka jiya da naje daukar ta a islamiyya bakaga yadda suka yiwa wata yarinya ba sai kuka take,
Tsokiii Abdul yaja yana kallon kolta yace
" And so?"
Bala yayi k'asa da murya yace
"Boss shine nace ko zaka tsawarta mata,don babe d'in da suka sa kukan bakaga yadda tabani tausayi ba..."
Katse shi yayi yace
"Shut up bala,to whom it may concern?"
Bala yace
"Sorry boss Amman da kaga babyn..."
Da k'arfi Abdul yace
"Will u shut up or not?"
Girgiza kai yayi yace
"Sorry boss" sannan ya maida hankali kan tuk'in,bayan ya sauke shi ne yace
"By 12:00 ka zo ka d'auke ni"
Da sauri ya risina yace
Angama boss afito lfy,ko na zauna anan na jiraka?,"
Waiwayo Abdul yayi yaga har ya d'ane saman motar ya hard'e k'afa da juyar da facingcap d'in sa yana wani kashe ido,
Yaso bawa Abdul dariya amman ya basar ya watsa masa wani bahagon kallo yace
"U dey mad"
Da sauri cikin Abinda baifi 5seconds ba bala ya diro yana
"Sorry boss" sannan ya shige motar ya fice,
Abdul jijjiga kai yayi cikin zuciyarsa yace
"Ko nauyin jikin sa baya ji"
Muryar mujidat sectarian sa yaji a gefen sa tace
"Savant din ka mai abin dariya"
Kallon ta yayi ba yabo ba fallasa taci kwalliya sai wani rangaji take,muryar ta ya sake ji tace
"Mrng "
'Daga mata kai yayi kawae ya wuce cikin zuciyarsa yana mamakin naci irin na Mujeedat bello,itakuwa Murmushi tayi ta bisa da ido tace
"Ka kusa shigowa hannu"
12:00 bala ya zo ya d'auke shi,gidan su ya kai shi yace ya tafi shi,
Da sallama ya shiga falon gidan,bakowa sai wasu ma'aikata,upstairs ya haura ya shiga d'akin mummy ba ta falo don haka direct bedroom ya shiga,A bakin gado ya ganta tana waya,zama yayi shima ya d'an jingina yana kallon wani programm,bayan ta kammala wayar ne yace
"Mummy barka da gida"
Babu walwala tace
"Yawwaaa"
Ya d'an yi mamaki jin ba yadda ta Saba amsa masa ba,
Shiru duka sukayi sannan yace
"Mummy Abba fa?"
Wani kallo ta watsa masa wanda yakasa fassara shi,
Sunkuyar da kansa yayi kawae
"Abdulkarim.."
Da sauri ya d'ago jin ta ambaci sunan sa yau,
Amman sai ya shanye mamakin yace
"Na'am"
Tace
"Kana so na tsine maka?"
Da sauri cikin kid'ima yace
"Me yafaru kuma mummy"
Harara ta watsa masa tace
"Wato ni kake so ka nuna ban Isa ba?,so kake ka kunya tani ka nunawa duniya ban Isa da kai ba koh?,"
Girgiza kai yayi idon sa jazur,
Ta cigaba kuwa
"To idan ba haka ba menene?,Akai maka yarinyar nan Asma'u yau tsawon kwana uku amman ko lafiyar ta baka tab'a leqawa ka gani ba saboda baka d'aukeni da mutunci da daraja ba koh?,"
Girgiza kai yayi cikin d'acin zuciya yace
"Mummy ba haka bane"
Ta katse shi cikin k'araji
"To menene?,Ai ko baka son yarinyar nan tinda na baka ita ko Dan mutuncin mahaifiyar ta da kuma ni dana kawo ka duniya ka saurara mata,idan kuma ni ce ban Isa ba to ka sani ko Ubanka idan na ajiye Abu nace kar ya tsallaka baya tsallakawa balle kai.."
A hankali jin anfara had'owa da Abbansa yace
"Mummy ba haka bane,kawae ni da na barta ta huta ne"
Tsokiii mummy tayi tace
"Hutarwar me?,ko wanne cikakken namiji lafiyayye idan aka kai masa Amarya ko ta buzuzu ce yana d'oki da marmarinta amman banda kai,idan baka da Lafiya ne kuma to ka fad'a min afara nemar maka magani kafin yarinyar mutane ta gaji Dan ba dutse bace ita!"
Sunkuyar da kai yayi don maganar Mummyn ta yi masa nauyi,amman sai yace
"A'A mummy Lafiya ta qlau.."
Ya fad'a yana shafa kai,
Shiru Mummyn ta d'an yi sannan ta gyara zama tace
"Tinda Lafiyar ka k'alau to lalle ka tabbatar yau ko kai kaje d'akin ta ko kuma ka kirata da kanka,ka tabbatar ka sauke wa yarinyar nan nauyin ta na Auratayya kaji na fad'a maka!!!"
Shiru yayi cikin matsananciyar kunya amman cikin zuciyarsa shi dae gaskiya ba ya sha'awar Raya sunna da macen da baya so bare Husna,don haka gwara ya fad'awa mummy kawae zuciyarsa ta bashi shawara,Numfashi yaja sannan yace
"Am...mummy wallahi yau ina da Ayyukan office sosae ki k'aramin lokaci ko..."
Katse shi tayi tace
"Ni dae ga Abinda na fad'a maka nan inka yarda Amma fa,don kasani Auren ka da Husna mutu ka raba na ratse da Allah"
Tana gama fad'a ta tashi ta fice ta bar Abdul cikin tashin hankali,
Rik'e kansa yayi da yaji yana neman darewa gida biyu,banda innalillahi babu abinda yake furtawa cikin zuciyarsa,ganin zaman ba yi masa zai ba yasa ya tashi ya fice gaba d'aya daga cikin gidan,masallaci ya shiga bayan yayi Alwala sannan ya yi sallar Azahar,zama yayi bayan ya idar da sallar Dan ya sami nutsuwa,wayar sa ya Ciro ya kira bala yace yazo ya d'auke shi bayan ya gaya masa inda yake,minti 25 bala ya sanar mai ya iso,Rufe k'ur'anin yayi ya tashi ya fita,bala ne ya bud'e mai motar ya shiga sannan shima ya zagaya ya shiga ya tada motar,sai da suka hau kolta sannan ya d'an juyo yace
"Boss ina muka nufa?"
Batare daya bud'e idone sa da ke lumshe ba yace
"Gidan Farouq"
15mins suka iso k'ofar gidan,bayan bala yayi parking ya bad'ewa Abdul d'in ya fito ya juyo fuskar nan ba walwala yace da bala ya tafi shi zai taho"
Bayan mai gadin ya bud'e masa ya shiga ne kaitsaye main falo d'in gidan ya shiga,bakowa a falon sai K'amshi da k'arar AC ke tashi a ciki,kan 3 seater ya haye kawae ya kwanta bacci agun ya kwashe shi,
*@4:30pm*
Farouq da Fareeda suka fito daga bedroom d'in su cikin farinciki da k'aunar juna irin ta ma'aura ta masu son junan su,turus sukayi ganin Abdul kwance yana ta bacci,Farouq ne ya k'ara sa gun ya d'an daddake shi,cikin lumsassun idanunsa ya bud'e ya sauke su kan Farouq, a hankali ya tashi yana Mik'e hannuwansa da sukayi taruwan jini,Farouq ne yace masa
"Lfy?"
'Dan Murmushi yayi dan 4 now ya samu peace of mind yace
"Normal na shigo ne inata sallama naji shiru sai kawae na d'an kwanta,
Fareeda ce ta tsuguna bayan ta ajiye masa ruwa da softdrink tace
"Ina wuni Yaa Abdul"
Sai da ya d'an saci kallon ta ta gefe sannan ya amsa da lfy kawae,
Farouq ne yace
"Tashi muje masallaci daga nan kuma muwuce"
Har Abdul zai yi magana sai Fareeda tace
"Amman Dan Allah Dear kar ka dad'e plssssss"
Cikin shagwab'a take maganar wanda tasa Abdul suman zaune,Farouq ya tashi ya matsa kusa da ita yace
"I will not sweey,just take care OK"
Ya manna mata kiss a goshi unexpected wanda yasa taji kunya ta shige d'aki harda d'an gudun ta tana cewa
"Safe trip...kasiyo min ice"
Murmushi Farouq yayi cike da k'aunar matar tasa don yaso ya manta da Abdul agun ma,
Jiyowa yayi ya maze kamar ba shi ba yacewa Abdul
"Taso koh?"
Cikin d'an jin kunya yace
"Ok"sannan ya tashi suka fita amman cikin zuciyarsa yana imaging inama shi ne amman fa matar ba k'arama ba like fareeda amman kuma mamaki yake ganin yadda take tarairayar Farouq d'in,da irin wadannan tunane tunanen suka tafi sukayi sallar sannan suka wuce gun wani appointment da dama sukayi booking,Amman Abdul zuciyarsa babu dad'i Sam! Don duk wani motsi dazai yi maganganun mummy ne ke masa yawo akai gefe d'aya kuma yana hango Abinda zai yiwa Husna yanda ko next time bazata sake gigin had'a shi da mummy ba,
Sai magariba suka tashi daga taron,gidan Farouq suka koma suka ci dinner sannan suka fara kallo sai wajen 10 yayi musu sallama ya tafi cike da sha'awar rayuwar Farouq da Fareeda don yadda yaga suna tarairayar juna abin sai ya dinga birge shi,
Trekking yayi daga gidan Farouq d'in har gidan sa,
Abdul bayan ya dawo daga gidan Farouq part d'in husna ya nufa zuciyar sa kamar zata fito Dan b'acin rai sakamakon fad'an da mummy ta balbaleshi da shi don tinda ya shigo gidan komai ya dawo masa kamar ma yanxu ake mai fad'an yakeji,Ashe d'azu su Rukky sata sukayi ta kira Mummyn Abdul, bayan sun gaisa ne Mummyn take tambayar ta ya Abdul da K'ibd'iyya don takira wayan sa a kashe, sai Husna ta kwantar da murya kamar zatayi kuka tace
"Ayyaa mummy Nima dama kirawo nayi nace ki tura driver yaje gidan mu gun mummy ta bani Fatima tadawo nan Dan wallahi ni tsoro nakeji jda kyar nake iya bacci tinda aka kawo ni,
Cikin rashin fahimta mummy tace
" Haba Husna, ina Abdul d'in zaki nemi wata Ya'r kwana?,infact ba ga K'ibd'iyya nan ba,?"
Husna ta sake sanyaya murya tace
"Mummy wallahi duk basanan,gashi ni ko d'akin bai shigo ba at all,sai d'azu na jiyo fitar sa don banzaci ma ya kwana ba,
Cikin b'acin rai mummy tace
"Shi Son d'in?"
Kamar tana gaban ta ta d'aga kai tace
"Shifa mummy"
Ajiyar zuciya ta sauke tace
"Okay...kiyi hak'uri zan kira shi"
Wani tsoro ne Yakama Husna jin mummy tace zata kitawoshi Dan tasan mummy baza tayi masa da wasa ba,amman da su Rukky suka d'aga mata gira sai tace
"To mummy"
Daga nan su kayi sallama da Mummyn,
Bayan ta Ajiye wayar ne duk suka tafa Dan dama su suka sata, duk da ita husna zuciyar ta bugun tara-tara take amman Dan ta faranta ransu sai tayi reacting da babu komai,Rukky ce ta katse mata tunanin tace
"Yawwaaa saura next plan,"
Fadeela tayi shewa tace
"Ai sai mun kama guy d'in nan a tafin hannun mu yadda ko ita uwar tasa sai abinda kika ce masa akanta"
Husna ta zazzaro ido ta rik'e baki tace
"Rufamin asiri banda dai Mummyn"
Harara suka b'alla mata sukace
"Tsaya wasa yarinya"
Husna ta gyara zama tace
"Ban fahimce Ku ba ae"
Rukky ta turo d'aurin d'an kwalin ta gaba ta rike kunnenta tace
"To bari kiji,ita Mummyn tasa dakike ganin kamar tana sonki to wallahi matuk'ar taga yafara sonki to tsanarki zatayi"
Husna tace
"Allah koh?"
Suka ce "hmmn tsaya nan"
Rukky tace
"Yanxu dai ki tashi ki shirya sannan ki yi masa girki ko bazai ci ba kuma kiyi Amfani da sauran kayannan gaba d'aya...duk dae kingane?"
Tace "eh.."
Fadeela tace
"Kuma sannan Wallahi duk sai kin cire Wannan tsoron da kike masa indai kinaso kiyi Nasara,"
Husna tayi Murmushi tace
"Hmmn Yaa Abdul nefa,bazaku gane ba"
Rukky ta katse ta tace
"Bazan mugane me ba?,Baki ga yadda wancan shegiyar take shishshige masa ba?,AI kema haka zakiyi"
Husna ta sauke Ajiyar zuciya tace
"Toh..zan gwada"
Fadeela tace
"Idan bamuyi Nasara ta nan ba,wallahi gun wani bokan Anty na zamu kai shi,sha yanxu magani yanxu duk taurin kansa wallahi"
Duk suka fashe da dariya amman husna cikin zuciyarta tace
"Ban da dai boka,hakan ma ina laifi,"
Daga nan suka cigaba da yi mata hud'uba irin tasu sannan suka tashi suka tafi,ita kuma ta shiga kitchen don tarbar oga Abdul,
Rayuwa zuji-juyi cikin ikon Allah gashi su Ameera sunyi sati biyu cif a sabon gida,canji kam sai dai Godiyar Allah,suna gudanar da rayuwar su cikin Kwanciyar hankali da tarin nasarori cikin kwanakin don sun koma makaranta Boko da islamiyya sai dai government ce kasancewar babu mai tallafawa,Baba larai ta kama guri A bakin titi tun bayan kwana biyun da suka tare tasaka jari sosae kasancewar dama gonar gadon su ta sai da da sauran kadarorin ta ta tattaro kud'in ta taho,Allah yasa mata nasibi aciki kasancewar gun idon mutane ne,sosae take ciniki kuma dasu take amfani wajen kulawa da duk wani Abu daya shafi rayuwar su su uku tare da tallafin Mal.Ismael don yanxu wata shak'uwa ce mai k'arfi ta sake shiga tsakanin sa da Ameera don yanxu tinda suka dawo gidannan kullum kafin baba larai ta fita sai yazo ya gaishe su yaga lafiyar su,shikenan kullum cikin hidimama su da kyautata musu yake duk da ba wani k'arfine dashi ba sosae Amman kullum cikin yiwa su Ameera siyayya yake musamman situru da kayan kwalliya,duk da kasancewar ta bamai shekaru ba Amman tasan tana k'aunar mal.Ismael, shi mutum ne mai zuciyar nema da rik'e mutuncin sa,baya daukar raini ko da ga gurin waye,Kullum A makaranta shikenan cikin kwatarwa Ameera ya'ncin ta,baya yarda ko waye ya taka ta,duk d'aliban makarantar shakkar sa suke,gashi da farin jini gun ya'n mata kasancewar sa _Sage man_ Dan ya tattara komai da duk wani matashi mai ji da kanshi yake dashi duk da kasancewar sa ba d'an kowa ba,amman bai yarda wani yaci mutuncin wani ba ko aci nasa,ya tsayawa Ameera sosae cikin makarantar shiyasa kullum k'ara bak'in jini take gun d'aliban makarantar ciki kuwa har da na Ajinsu,Yanxu Makarantar kasancewar ta fitacciyya kuma d'aliban ta masu hazak'a aka sami wani Attajiri ya yi musu register da gwamnati,Ameera karantun ta take haik'an ba ruwan ta da k'awaye ko sha-sha,Dan ko aji ta shigo ba ruwan ta da kowa sai Al'qur'anin ta shi yasa ya'n Ajin suke ce mata "Ya'r president" saboda ita ba kowa bace face YA'R ZINA amman sai girman kai kamar Ya'r shugaban k'asa acewar su,Mal.Ismael yayi namijin k'ok'ari sosae wajen yak'i da dena kiran Ameera YA'R ZINA acikin Wannan makarantar,Dan yanxu sai dai a fad'a abayan idon sa ko kuma a yimata habaici tinda sun san ba tankawa take yi ba sai dai takifa kai tayi kuka ko Khadija tayi ta tausarta,haka dai take gudanar da rayuwar ta cikin makarantar babu walwala idan ba mal Ismael ne a ajin ba....
_*PINKY CE*_
Copied By
YAYA HAYAT
(admin
Hayat hausa novels
Hausa novels and fashion
Cool novel, makeup and kitchen1⃣
Cool novel, makeup and kitchen2⃣
AND
Cool novel, makeup and kitchen3⃣)
WHATSAPP NO:+2349030159301
[2/22, 10:26 PM] +234 703 459 6468: *YA'R ZINA CE👄*
_......Adulterer's Daughter_
*A TRUE LIFE, TOUCHING HRT & LUV STORY*
_BY_
*MARYAM PINKY*
_Follow me @facebook..._
www.maryampinky.facebook .com.
*Godiya Mara misaltuwa agareku masoya littafinnan, wallahi inajin dad'in qaunarku gareni,Nima kuna❤nan d'ina,I wish zan iya lissafoku,especially ya'n group dina PINKY NOVEL FAN's 1&2,I'm proud of u guyz💋🤝*
1⃣3⃣
9:00am daidai yatashi daga baccin daya koma bakinsa dauke da salati,Hamma yayi yana dafe kansa da yayi masa nauyi kamar ba'ajikinsa yake ba,kallon gefen sa yayi yaga Kibdiyya batanan,shiru yayi yana tunanin mafarkin yau,babu abinda yake tunawa a mafarkin irin maganganun da taketa fada masa,
"Ka taimakeni Dan Allah.." Shine yaketa yimasa yawo akai,cikin xuciyarsa yake tambayar kansa
"Taimakon me take so"?
Bashi da amsa..don haka sai kawai yaja tsokiii yace a fili,
" Mtsswwcc ke kika sani,tinda kinki bayyana ko fuskarki nagani"
Ganin 27minutes past 9:00 tayi yasa ya miqe yana cewa
_"why should I disturb my self?"_
Towel ya jawo a closet yanufi toilet,ya kai 30minutes sannan yafito yanata qamshim bathsoap din wankan,gaban dressing mirror yaje yajawo stool kamar mace ya zauna,cikin yauqi yake goge ruwan kansa da jikinsa,lotion din _smart-man_ya dauko ya Mirza,sannan ya dauko roll-on ya shafe lungu da saqo na jikinsa sannan ya miqe ya nufi closet,shadda getzna Light maroon color yadauko yasaka da hula match color din zaren da akai aikin,gaban mirror yakoma yafeshe jikinsa da designers masu qamshi....Kibdiyya ce tafado dakin tana qala masa kira
"Yaa Abdul,yaa Abdul.."
Ko kallo bata isheshiba yacigaba da gyara kan madubin yana maida komai mazauninsa,itakuwa ganin yana jinta amman yayi shiru yasata fushi tayi hanyar fita,har takusa qofa sai maganar da ummah rabi take yawan gaya mata ta dawo kunnenta..
"Kibdiyya kar kice zakina fushi da Abdulkarim, komai yayi miki karkina fushi,idan ma shi kinga yayi kije kiyi masa kiss kibashi haquri zai daina indai da gaske kina sonshi.." Tinowa da Wannan yasa ta koma gun da yake zaune bakin gado yanata danna wayarsa peacefully, da gudu ta haye kan gadon ta fada jikinsa ta baya,ta zuro fuskarta ta kan kafadarshi zatayi magana taji yace yana kara wayar a kunnensa
"Hello farouq kana ina"?
Tana jiyo farouq din yace
" I'm on my way"
"Okay" yace kawae sannan ya sauke wayar yasa hannu ya dawo da ita kan cinyarsa ya kalleta da sexy eyes dinsa yace yana daure fuska amman idonsa kyar akanta
"U don't knw hw 2 greet elders right"?
Shiru tayi tana kallon sa itama,
Tamke fuska yayi yasake cewa
" I'm talking to idiot"?
Girgiza kai tayi alamar A'a,a hankali tasa hannu tayi holding tight dinshi tace
"I'm sorry yaa,gud morning"
Sassauta fuskar yayi yace yana kai fuskarsa zuwa tata yace
"Mrng,was ur night"?
Murmushi tayi ganin yasaki ran tace
" fine,shine na shigo ina maka magana Kayi ignoring d'ina"
'Dan b'ata fuska yayi yace
"Kinyi sallama dazaki shigo"?
Girgiza kai tayi
" And u re complaining. So..so..nd so,Neva try that..again,is that clear"?
Kwanciya tayi sannan ta ce tana shafa sumar gemunsa datayi kyau
"Yearr,"
Yace "gud gurl,that's my cwt sister"
Bata rai tayi tace
"No,wife"
'Bata fuska yayi yace
"Who told u that"?
Cikin fargaba Dan ganin ya hade fuska tace
" ummah Rabee "
Gyada kai yayi yace
"Gud,yau da daddare idan kinzo bacci zaki fada min abubuwan da take fada miki a kaina"
Dariya tayi tace
"Tace fa karna fad'awa kowa"
Hancinta yaja yace yana nuna kanshi da d'an yatsa
"Wow,including me"?
"No,ban da kai"
Wayar sa ce tafara ringing,kallo daya yayi ma screen din ya kauda kai,ringing din take tay,hannu yasa d'aya ya dako wayar ya kara a kunnensa bayan yayi accepting kiran,shiru yayi...daga dayan bangaren Asma'u tayi sallama,a daqile ya amsa yana yatsine fuska kamar yana gabanta,
Ajiyar zuciya tayi jin daddad'ar muryarsa tana dukan doden kunnanta,cikin fargaba tace
"Ashe ka dawo,welcome back"
Siririn tsokiii yaja sannan yace
"Tnxs"
"He will Neva change" ta furta a xuciyarta,amman a fili sai tace
"Dama mummy ce tace na fad'a maka zamuxo"
"Sai kunxo" kawae yace ya katse kiran,gefen gadon ya kalla inda Kibdiyya ke kwance tana hawaye sha'be shab'e,dariya ce taso kamashi,amman sai ya dake,kuma dama yasan za'ayi hakan don tin da yadauki wayar tagani ta sauka daga jikinsa,
Matsawa yayi yadan kwanto saitin fuskarta yace
"Something happen?"
Tasowa tayi daga kwanciyar cikin kuka tace
"I hate her!"
Zaro ido yayi cikin tsananin mamaki yace..
_kuyi haquri mu hadu next page,bani da chargy ne_
_*PINKY CE*_
[2/22, 10:46 PM] +234 703 459 6468: *YA'R ZINA CE👄*
_......Adulterer's Daughter_
*A True life, touching hrt & luv story*
_BY_
*MARYAM PINKY*
www.Maryampinky.Facebook.com.
1⃣4⃣
"who d u hate?,Asma'u?"ya tambayeta cike da tsananin mamaki, Dan shi yanxu mamaki take bashi sosae,Turo baki tayi gaba tace
"Eh..itan"
Kallon baki da hankali yake yi mata sannan ya girgiza kai yace
"Olright,me tayi miki kika tsanetan"?
Anzo wajen Dan gyara zama tayi ta kalleshi tace
"Ba ita ce wai zata aure kaba"
"Uhumm,sai akayi me?" Shima ya tambaya cikin tsinkewar zuciya,nok'e kafad'a tayi tace
"To ni banaso ne"
"Why"? Ya tambayeta
Shiru tayi Dan ba amsa,Numfashi yaja ya futar sannan ya miqe yace " tashi mutafi cikin"
Nok'e kafad'a tayi cikin muryar shagwab'a tace
"A'aa ni sai dai ka Goya ni a bayanka ka kaini"
Baki ya saki galala yana kallonta cikin zuciyarsa yake cewa "lallai yarinyar nan yazama dole ma su Abba suyi breaking auren nan,Dan naga nema take tafara kawomin raini,..wata xuciyar kuma tace ka kyaleta jinin _Anty Aisha_cefa"wayoyinsa ya d'auka daga bedside table batare daya kalli inda take ba yafice,direct falo ya wuce cox yasan su mummy suna can,da sallama yashiga falon,duk suna zaune suna kallo,daga gani breakfast suka gama,Duk suka amsa masa suna murmushi xuciyoyinsu cike da qaunar tilon 'Dan nasu,1seater ya nufa ya zauna yana cewa wash! Nagaji fa mummy,dariya Abba yayi yace "sannu son" itama mummy tayi masa,bayan ya gaishesu ne Mummy ta kalleshi tace "Son Husna kuwa ta sanar maka zasuzo"?
Batare daya dago ba yace
"uhmmn"
Murmushi Abba yayi yace
"Okay shiyasa yau kaci kwalliya haka daman?, kace zance za'azo maka"
Dariya mummy tayi tana kallon Abdul da yayi reacting kamar badashi ake ba,
Mummy tace"Aikuwa dai,kuma kasan akwai ma Uwargidan anan"
Duk suka saka dariya banda shi,don idan da sabo yasaba da tsokanar Abba da mummy,muryar Abba yajiyo yana cewa
"Ahh,na mantafa akwai madam Rigima"
Mummy zatayi magana kenan sai gata nan tashigo tana kuka,duk suka kalleta suna tambayarta "Lafiya"?,
Gun Abba taje ta zauna gefenshi setin kujerar da Abdul yake tace
"ba Yaa Abdul bane nace ya Goya ni ba ya taho" tafada tana nunashi da hannu,
Dariya mummy tayi tace
"Son meyasa baka Goya taba.." Sallamar su Asma'u da mummynta yasa duksukayi shiru,da sauri mummy ta tashi ta taro Aminiyarta tana yi mata barka da zuwa,zama sukayi kan 3seater suna murnar ganin juna,Asma'u ta qaraso falon kanta a qasa sanye take da doguwar Riga bak'a mai Stones pink,tayi rolling kanta da veil din,lips dinta sunsha 24hrs pink color,har qasa ta tsuguna cikin ladabi ta gaishe da Abba,yana murmushi yana Amsawa yana tambayar ta karatu,miqewa yayi bayan sun gaisa da Hajiya Bilki ya haura upstairs, Abdul kuwa da tun shigowarsu ya zubawa Husna ido Dan ba k'aramin kyau yaga tayiba,gashi tayi wata irin cika kamar ba YA'R 22yrs ba,kallon seconds yayi mata ya dauke kai Dan karta ganshi,amman cikin zuciyarshi soyake yasake kallon ta,Dan ba qaramin kasala ta saukar masaba gashi sai qamshi take,itanma agunta hakane don xuciyarta ce tadinga harbawa tinda ta shigo ta hangoshi,"he's olways cute"tafada a hankali,cikin xuciyarta kuwa wani son shine yake mata yawo,
Tsugunawa tayi tana gaishe da mummy "Ina wuni mummy" tace,
Da murmushi mummy ta shafa kanta tace "lfy low daughter,y studies?"
Cike da kunya take amsawa "Alhamdulillahi mummy"
Hajiya Bilki ce takai dubanta ga Abdul

1 Comments On YAR ZINA CE
avatar
abdulkadir-6

1 year ago

Reply

Is a very educated and interesting novel

Please Login or Register in order to submit comment