Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ke gefe ya hakimce kasancewar shi dama baifiyasan driving ba,shiru motar sai wa'azin _Sheikh Malam Aminu Ibrahim daurawa_ke tashi acikin motar yanata wa'azi akan Abubuwan dasuke kawo yawan zinace zinace yanxu da kuma irin hukunci da Azabar da Allah yatanadarwa masu Aikatata,Wa'azine da duk me sauraronshi sai ya ratsa xuciyarsa matuqar mutum mai imanine,A hankali Farouq ya kai hannu saitin volume ya rage,sannan ya kai dubansa ga Abdul dayayi resting ajikin kujerar ya lumshe ido kamar mai bacci,
"Abdoul" yakirawo sunansa,A hankali ya bud'e idonsa da sukayi jazur ga jijiyoyin goshinsa duk sunfito rud'u rud'u fuskarnan tayi jaaa, "What's happen?" Ya tambaya yana komawa,
Farouq yace "Do u knw wat?"gyara zama Abdoul yayi yace
" until u said"
Cikin Alhinin Abinda zaice farouq yace "wa'azinnan yasa na tuna banfad'a maka ba.." Sai kuma yayi shiru,
"Uhummn" Abdul yace yana kallon sa da rinannun idanunsa,
"Katuna yarinyar nan girlfriend d'in *K.B*?"
'Dan qaramin tsokiii Abdul yayi jin an ambaci sunan *K.B*don idan akwai abinda Abdul ya tsana to a ambaci sunan K.B,cikin yatsina yace
"Which one?,kasan suna da yawa"
'Dan murmushi Abdul yayi yace "qanwar Oga Sageer nake nufi"
Mood d'in Abdul ne ya canza nan take yace
"I didnt get u,so pls just keep that nonsense man issues"
Farouq yace
"That pregnant girl i meant"
Hannu yasa ya dafe kansa da yayi wani irin sarawa lokaci d'aya,sai da yayi 2minutes sannan ya kalli farouq da yaketa driving d'insa hankali kwance yace
"I remembered.."
Gyad'a kai farouq yayi yace "okay to jiya Hajiya ke fad'amin da daddare yarinyar tarasu due to delivery"
Ganin yadda Abdul yakasa motsi sai kafeshi da ido dayayi sai yazata ko bai fahimci abinda yaceba don haka yasake cewa
"I mean ta rasu wajen haihuwar Babyn.."
Bai qarasaba yaji Abdul yace _"Innalillahi wainnah ilaihir-raji'un,Alhamdulillahil-lazhi Afani mimbtalaka bihii wafad-dhalani ala kathirin mimman khalaqa tabtila,....farouq kana nufin tarasu?"_
Cikin tabbatarwa Farouq yace
"I'm sure cox thaz wat Hajiya told me,tace muje muyi musu gaisuwa"
Girgiza kai kawai Abdul yakeyi hawaye nabin kuncinsa wanda yasa Farouq neman guri abakin hanya yayi parking jin Abdul na kuka sosae don bai tab'a ganiba,cikin tsananin mamaki yake kallon Abdul yace
"Something wrong...?"
Hawayen fuskarsa yasa tissue ya goge cikin qucin zuciya yace
"Farouq!, Yanxu Wannan yarinya mezataje ta cewa ubangijinta?,me zuwanta duniya ya amfanar?me haihuwarta ta amfani Al'ummar musulmi da iyayenta?,ya ilahiii" yafad'a yana sake goge hawayen fuskarsa
Cikin jimami shima Farouq yace
"To yaza'ayi Abdul..qaddararta kenan, bayadda za'ayi"
Kallon out of ur sense yakeyiwa Farouq sannan yace
"Farouq K.B ya cuci yarinyar nan,K.B me zai cewa ubangijinsa,irin Wannan babban zunubi haka?, *SO*ya zamemasa musiba...."
Farouq ne yakatseshi yace
"Abdul Addu'a kawae zamuyi Allah ya yimata rahama,shikuma yasa yagane kuskurensa yarinyar kuma Allah yara yata..."
Zazzaro ido Abdul yayi yace
"U mean tama haihun?"
"Yes..female" inji Farouq
"Innalillahi...,Kuma Farouq kakecewa Allah yarayata"
Murmushin takaici Farouq yayi yace
"To Abdul me za'ace?.."
Numfashi ya ja yace
"Allah yasaka yata ta mutu"
Dariya Farouq yayi yace
"Haba friend wannan wace irin Addu'a kake?"
Harara ya makawa Farouq yace
"Me kake tunani idan ta rayu?,itama haka zatayifa"
Zazzaro ido Farouq yayi yace
"Injiwa?kasan gaibu ne Abdul?
Tsokiii yayi yace
" Farouq idan baka sani ba let me tell u,Wannan yarinyar idan tagirma sai tayi abinda uwarta tayi...cox itafa *ZINA* da kake ji to salsala takebi,jini takebi,kuma ita bashi ce"
Dakatar dashi Farouq yayi da sauri yace
"Ba'anan take ba,ita *YA'R ZINA*ba lalle ne tayiba,saboda ita bata da laifi,infact batasan ma me akayiba,idan da tasan ta hanyar da za'asametato itama dabazata yarda tazoba,kuma wallahi ina fad'a maka duk wata yarinya ko yaro da aka same shi ta hanyar ZINA to wallahi yafi kowa jin ciwon haka,don haka kama daina fad'ar haka Abdul sai kaga ita *YA'R ZINA*al'umma ta amfaneta amman yar halak ba a amfanetaba ko kuma kaga Itan bataiba saboda tasan qucin da ake shiga amman yar halak tayi,kai dai saidai fatan Allah ya datar damu"
Ko ajikin Abdul maganganun Farouq Dan shi kawae yariga ya musu kud'in goro shiyasa ya tsanesu a rayuwarshi sakamakon tsanar dayayiwa aikata ZINA, shiyasa baya qaunar a ambaci K.B abokinsu duk da Friend d'insu ne,amman saboda halinsu ya banbanta yasa sukayi separate,
Keb'e baki yayi ya d'aga shoulder alamar I don't care,
Murmushi Farouq yayi yace
"Ko kawae muwuce can muyi musu gaisuwa muga babyn..by then sai mu dawo gun Hajiya"?,
Harara Abdul yayi masa yana ja da baya yana nuna kansa yace
" who?..dawa? Wazaije?"
Had'e rai farouq yayi yace
"Kai Abdulkarim mana"
Murmushin takaici yayi sannan yadubi Farouq yace
"I will pray 4 her to hav perfect peace"
Tsokiii kawae Farouq yayi yace
"Wllh sai kaje,ae ko don umminsa kaje,infact kaima ba ka wuceba,"
Tab'e fuska yayi yana d'aura belt don ganin yadda Farouq ya fisgi motar yace
"God forbid ..me"
Shidae Farouq bai tanka masa ba saima qara speed yayi ya nufi anguwarsu K.Bn..
Ganin irin yadda yake gudu yasa Abdoul yace yana tab'ashi
"Hey!man I'm not ready 2 die,life began at 30"
Ko kallon sa baiba suka shiga street d'in gidansu K.B don yin ta'aziyyar...
_*pinky ce*_
[1/26, 3:01 PM] maryam Tahir Author Y4: *YA'R ZINA CE👄*
_......Adulterer's Daughter_
*A TRUE LIFE, TOUCHING HRT & LUV STORY*
_BY_
*MARYAM PINKY*
www.Maryampinky@facebook.com
*®REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S*
_{We don just entertain nd educate,we touch the heart of readers❤_}
#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
*IG PML WRITERS*
#https//www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com
*HIKIMA WRITER'S ASSOCIATION🎁,nd HAQURI DA JURIYA ONLINE WRT's🌐words enough can't express neither explain how u re in my❤,Tnxs once again🤝*
*PC chart plsss nd plsss I'm so sorry 4 not responding.....wllh u re tooo much to me......,pardon pls,👏🏻*
1⃣9⃣
Alhaji Abdulfattah ganin shiru Abdul bai ce komai ba yace
"Kai nake saurare.."
'Dagowa yayi fuskarsa tayi jaa ga wani irin gumi da yake fito wa daga goshin sa yace
"Toh Abba Allah ya biya Ku"
Cikin jin Dad'i Alhaji Abdulfattah yace
"Madallah...Eh..Madallah..Allah ya yi maka Albarka"
Ko Amsawa bai iya yi ba ya mik'e zai fita,Alhaji Abdulfattah yace
"To ya batun Auren ka da Mariya(K'ibd'iyya) fa??"
Ko waiwa yo wa bai ba ya 'Dan tsaya for some seconds sannan yace
"Abba duk yanda kuka ce"
Murmushi yayi yace
"To shikenan"
Ficewa yayi daga 'Dakin ko Gaban sa baya gani, rik'e da kan ya shiga 'Dakin sa ya zube a k'asa don tafiyar ma gagarar shi tayi,tinda ya fad'i bai san inda kansa yake ba sakamakon Duhu daya lullub'e masa ido.
Abdul na fita Alhaji Abdulfattah ya kira Alhaji Bello,mituna kad'an sai gashi ya iso shida wasu mutum biyu dattijai,bayan gaggai sawa da sukayi ne yake yi musu bayanin buk'atar shi duk da ya sanar musun,sunyi Na'am suma,daga nan suka tashi gaba d'aya suka fice don zuwa gidan su Husna zuciyar Alhaji Abdulfattah a cunkushe babu Dad'i Sam!, don ganin ba shi da kowa,ace 'Dansa gudan jinin sa za'a je kai kud'in sa amman ba wani 'Dan uwa nashi na jikinsa... Kansa ne ke neman tarwatsewa yasa ya runtse ido yana karanto Addu'a.. Haka take kasan ce masa duk lokacin daya nemi Tina wani 'Dan uwan sa sai ya kasa.
★★★★★★★★★★★★★★★
Babban falone sosae wanda kuma za'a iya kiran sa da sitting room, Alhaji Abdulfattah ne da mutanen sa gefensa,daga 'Dayan b'angaren ma Alhaji Muhammad Sani ne shi ma da mutanen sa,kowa ka gani cikin falon fuskarsa d'auke take da Annuri saka makon tsayar da Ranar Ya'yanna su da akayi a lokacin nan da sati uku masu zuwa,Addu'a aka rufe taron Da ita sannan suka sake yin gaisuwa sannan taron ya tashi zuciyoyin su cike da Farin ciki.
Kai tsaye Alhaji Abdulfattah gidan sa yasa Aka wuce da shi,yana motar Amman burin sa kawai ya ganshi a cikin gida don yaje ya sanar wa Mai 'Dakin sa wannan Dadda d'an labarin don har ya hango irin farin cikin daza tayi..shi kad'ai sai murmushi yake yi,duk ya k'agu su iso don gani yayi ma drivern baya sauri,sai da ya tsaya yayi sallar magariba sannan ya shiga cikin gidan,kai tsaye part d'in ta ya nufa,da sallama ya shiga ya tarar da su suna zaune da Alama sallah sukayi,cikin girma mawa Hajiya Amina ta tarbeshi,itama Hajiya Bilki tayi masa barka da zuwa,Amsawa yayi yana dariya lokacin da yake zama akan kujera,Dai-dai lokacin Hajiya Amina ta iso hannunta rik'e da lemo mai sanyi da glass cup,janyo centre table'Din tayi ta Ajiye masa bayan ta tsiyaya masa,'Dauka yayi ya sha kad'an sannan ya Ajiye,
Cikin Raha yace da Hajiya Bilki
"Yau dai kin wunar mana.."
Murmushi tayi tace
"Aikam..Kai ka tsayar ni Ai"
Dariya yayi yace
"Eh..kuma fa haka ne"
Hajiya Amina tayi caraf tace
"Alhaji da Alama da Akwai magana a bakin ka,tinda ka shigo naga kanata nisha d'i"
Wani Murmushin ya kuma yi sannan ya kallesu yace
"To Albishirin ku?"
Suma suka ce
"Goro.." Suna dariya
Yace
"To yau dai Allah ya nufa Munkai Ku d'in Auren Abdulkarim da Asma'u "
wata gud'a Hajiya Amina ta rangad'a zuciyar ta cike da Annashuwa tace
"Kai Alhaji dama zanga ranar nan?"
Murmushi yayi yace
"Gata kuwa"
Hannu ta 'Daga sama tana cewa
"Allah na gode maka fa ka nuna min Wannan rana mai matuk'ar mahimman ci,Allah ka yadda ka nuna min Wannan ranar Allah ka nuna min 'Daurin Auren"
Duk suka ce
"Amin"
Ita kuwa Hajiya Bilki Murmushi ne kawai ke ta fita kan fuskarta,wani irin farin ciki itama take ji,
Hajiya Amina ce tace
"Gaskiya Alhaji ina cikin farin ciki Mara misaltuwa"
Murmushi yayi yace
"Sai mu gode Allah.. Haka dama yake lamarin sa"
Hajiya Bilki tace
"Dama plan d'in da kuka yi kenan don Ku bamu mamaki?"
Dariya yayi yace
"To ko bakuji Dad'i ba..?
Da sauri Hajiya Amina tace
"A..aaaaa munji wallahi.."
Hajiya Bilki ta mik'e tace
"To ni zan wuce"
Kallon ta duk sukayi sannan Alhaji Abdulfattah yace
"Kuna ta murna baku tambayi Date d'in ba?"
Da sauri Hajiya Amina tace tana dafe kai
"Ahaf...Aikuwa dai ko da yake Ai ita Hajiya yanxu idan taje zata ji..koh?"
Dariya tayi tace
"Ba lallai bane tinda Aka fara da haka...Kawai a fad'a min Anan Nima na bada surprise"
Duk suka yi dariya,Alhaji Abdulfattah yace
"Sati uku masu zuwa"
Hajiya Amina tace
"Kaiiii Masha Allah tare dana Farouq kenan"
"Eh.."yace sannan ya dubi Hajiya Bilki da tayi shiruuu yace
" uhumm..Hajiya ko bai miki ba?"
Da sauri ta dawo daga 'Dan k'ara min tunanin da ta tafi cikin sauri tace
"A..ni na Isa?yayi Allah ya nuna mana da rai da Lafiya"
Duk suka Amsa da "Amin"
Daga nan tayi mata rakiya har main gate suka yi sallama sannan ta dawo falon ta,zama tayi gefen sa tana Murmushi tace
"Alhaji Ashe kana nan?"
Duban ta yayi cike da so yace
"Ina nan"
Kallon labaran da yake yi ta ciga ba da yi itama har Aka gama sannan tace
"Alhaji"
Kallon ta yayi bai Amsa ba,ta ciga ba
"Alhaji to SON kuwa ya sani?"
"Eh..na sanar mai"
Cikin sanyi tace
"To mai yace?"
Kallon ta yayi yace
"Addu'a yayi"
Ajiyar zuciya ta sauke tace "Masha Allah, Allah ya nuna mana,dole mufara shiri tin yanxu"
'Dan Murmushi yayi yace
"Uhmm..Abi naku kam"
Itama tace
"Maganin a Kwab'e mu"
Kirwo sunan ta yayi yace
"Ya kike ganin yadda zaiyi zaman dasu duka?"
Saukowa tayi k'asa ta zauna sannan tace
"Yawwaaa.. Ina ganin tinda dama gidan part uku ne kawai Akai su duka don kasan baza ta yarda ta zauna ba,..ko ya ka gani"?
Shiru yayi nad'an wani lokaci sannan yace
" Amman Hajiya kina ganin ba mu takura yaron nan ba?"
"Kamar ya?" Ta tambaye shi,
Ya nisa yace
"Ina nufin kinga dai Mariya munce za'a raba Auren nan bayan ya dawo,ga kuma Auren Husna da muka sa shi bayan duk babu zab'in sa a ciki amman yayi mana shiru baice komai ba,kina ganin munyi masa Adalci kuwa?? Bayan haka .."
Da sauri Hajiya wadda Ranta ya fara b'aci tace
"Haba Alhaji kadena Wannan zancen ma kar yaji yace zai yi disobey,K'ibd'iyya fa karka manta Yarinyar Ya'r uwa tace ciki 'Daya,kuma ko ba komai ka tuna fa irin so da kulawar da mahaifiyar ta taba shi,menene bata yi masa ba?ka tuna Ni da Mahaifiryar ta ta baro iyayen mu ta shigo musulunci don kar ta rabu dani,Ina ganin don nace Abar Auren nan ba matsala bane,ita kuma Asma'u na sa shi Auren ta ne don ganin K'ankantar Mariya baza ta iya bashi kulawa ba,Amman idan tana ganin Abinda Husnah takeyi shine zata koya,kuma nayi sha'awar Auren Husna ne saboda tarbiyyar ta da nutsuwar ta don bana fata ko burin ya Auro bare dama,ga kuma Amincin mu da mahaifiyar ta."
Alhaji Abdulfattah da yace
"Amman kinsan yana da hakki akan mu?"
Da sauri tace
"Eh..Amman yaza ma kuma dole yayi min biyayya tinda ni na haife shi"
Ajiyar zuciya Alhaji Abdulfattah yayi yace
"Allah ya kyauta" ya mik'e ya fice don jiyo kiran sallar ishaa cikin zuciyarsa yana mamakin irin Halin matar tasa na son tauyewa 'Dan na su Right d'insa da kuma Ak'idar ta na 'Dan ta bazai Auri bare ba,Kwafa yayi lokacin daya fice yace
"Zanyi maganinki"
★★★★★★★★★★★★★★★★★
Washe gari tinda suka tashi da Asuba basu huta ba saka makon shirye shiryen tarbar Yaran Hajiya mama da suke tayi wanda zasu sauka yau daga Abroad bayan kammala karatun su wato Aliyu 'Dan ta da k'anin ta Mustapha wanda ya dawo gunta da zama duk da ya girmewa Aliyun ta,Aiki kawai sukeyi basu suka sami Kansu ba sai gefin la'asar lokacin da aka tafi d'auko su,part d'in su suka koma don sun Riga sun gama komai,
Suna zuwa _Ameera_ta zube tana cewa "wash..Allah"
Hararta Khadija tayi tace
"Kefa Raguwa ce wllh"
Kwanciya ta gyara tana cewa
"Wallahi don baki san Aikin dana yi ba lokacin da naje gyaran d'aku nan su..harfa wankin toilet nayi duka fa,"
Cikin wasa Khadija tace
"Shi ne me kuma?"
Harara ta Ameeran tayi tace
"Bansani ba"ta fad'a tana juyawa Khadija baya,
Da sauri Khadija ta dawo kusa da ita ta dafata tace
" ke fa baki san wasa ba wllh,Banda Abinki ma Ai k'ara koyo ne"
Idon ta a rufe tace
"Naji,kyaleni" ta janye hannun Khadija,
Mayar da hannunta khadijan tayi tace
"Ae bana so nikuma na kyale ki don nasan tunani zaki,nikuma bana son kina damuwa...ko tunanin malam zakiyi?....
_I'm busy today kuyi haquri da Wannan_
_*pinky ce*_
[1/26, 3:01 PM] maryam Tahir Author Y4: *YA'R ZINA CE👄*
_......Adulterer's Daughter_
*A TRUE LIFE, TOUCHING HRT & LUV STORY*
_BY_
*MARYAM PINKY*
*®REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S*
_{We don just entertain nd educate,we touch the heart of readers❤_}
#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
*IG PML WRITERS*
#https//www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com
1⃣8⃣
Asma'u na fita kai tsaye gida tayi cike da murnar ganin K'awayenta kuma Aminanta,Tana shiga ta Ajiye Jakarta ta fad'a kitchen domin sama musu Abinda zasuci,cikin 30mins ta had'a jallop d'in taliya mai kayan lambu,duk falon ya cika da K'amshi,tana cikin kitchen d'in tana wanke abubuwan da ta b'ata tajiyo Muryoyinsu suna K'walla mata kira,da sauri ta Ajiye plate d'in hannunta tayo falon,Ae kuwa duk su ukun suka Rungume Juna cikin murna,breaking hug d'in sukayi suka zube a k'asa suna sake gaggai sawa,Rukky ce tacire Veil d'inta ta mik'e ta nufi fridge tana cewa "Ya'r Air baki iya tarbar mutum da Ruwa ba,sai washe baki" ta fad'a tana Ciro ruwan roba mai sanyi daga fridge d'in,Asma'u tayi ya'r dariya tace
"Oops..sorry wllh murnar ganinku ce"
Fadeela ce cikin wasa ta 'Dala mata duka A cinya tace
"Eh...dama kya ce haka mana..tinda yau kinje kinga sahibinki yasa kin manta da komai"
'Dan yatsina fuska Rukky tayi tana shan Ruwa tace
"Nakira wayar ki Aka kashe min...Ashe kina gunsa shiyasa bakiyi picking ba"
Mik'ewa Asma'u tayi tana cewa
"Mtsww kudai bari kawai,..ina zuwa nazo nagaya muku Abinda yamin don Advicess d'inku basu yi ba,"
Zaro ido Rukky tayi tace
"Kina nufin bawani canji?"
Murmushin takaici Husna tayi tace
"Hmmnn..ina Nasara sai ma cin kashi da jin kunya..Yaa Abdul ne fa"ta fad'a tana shigewa kitchen don K'arasa wankewa,
Sai da ta gama wanke komai tayi mopping d'in kitchen sannan tafito lokacin Anfara kiran sallar la'asar don haka da ta fito ce musu tayi suyi sallar tukun,
Ba musu Fadeela ta mik'e ta nufi toilet, Asma'u ta kalli Rukky daketa Danna wayar ta tace
"Madam kefa?"
'Dagowa tayi ta kalli Asma'u for some seconds sannan ta maida kanta kan chatting d'inta datake tace
"I'm off"
Murmushi Asma'u tayi ta shige bedroom d'in don yin sallar, Bayan sun idar ta kawo musu Abincin suka zauna kan rug d'in suka fara ci suna firar Assignment d'in daxasuyin,sunyi nisa cikin cin Fadeela takai loma sannan tace tana lumshe ido
"Hmmnnn Gaskiya Abdul zai more da delicious girkinki Hussy.."
Ta fad'a cikin sigar tsokana,
Rukky ce ta tintsire da dariya har tana neman kwarewa tace
"Wallahi kuwa..Ae idan Ya bari yara saki husna ko..wllh ta tafka Asara Babba"
Asma'u duk ta maka musu harara taci gaba da cin Abincin ta,Rukky ta sake cewa tana dariya K'asa-k'asa
"Hussy idan muka kaiki gidan Abdul to washegarin da kuka sha Amarci irin wannan girkin zaki mai...nasan sai kunnensa ya cire"
Duk suka fashe da dariya banda Asma'u data d'aure fuska amman cikin zuciyarta farin ciki ne fal don tana son Adinga fad'o mata wannan ranar,ganin ba zasu fasa tsokanar tata ba yasa tace
"Hmmnn...kunsan kuwa me yamin yau??"
"A'a" sai kin fad'a inji Rukky,
Gyara zama tayi ta basu labarin abinda yafaru duka....
Rukky ta tintsire da dariya har tana neman bige ta,tureta Asma'u tayi tana cewa
"U dey mad,I'm telling u serious tnz nd ur behaving like that" ta fad'a tana ture ta,Fadeela ce ta dena dariya cikin serious tune tace
"Amman fa guy d'innan wallahi sai ya gane kuransa duk randa yazo hannu"
Rukky ma ta goge hawayen dariyarta tace tana dafa cinyar Husna "Asmy?,"
Kallon ta tayi alamar menene,Murmushi ta sake yi tana girgiza kai tace
"Kuma shine zaki ce buk'ata bata biya ba?"
Kallon hmmn Asma'u tayi mata sannan tace
"To Rukky ina tabiya?"
Dafa kafad'ar ta tayi tace
"To wallahi tallahi buk'atar mu ta biya,Abdul mungano weaknesses d'in sa kuma...ta tintsire da dariya",
Da sauri Asma'u ta juya left hand d'inta jin Fadeela ma na dariya,sunfara bata haushi kuma don haka cikin hasalla tace
" look..bana son lack of manners, ya zaku sani a gaba kuna dariya like u re watching movie"
Fadeela ce ta kalli Rukky ta bata hannu suka tafa sannan tace
"Ohhkk sai yanxu fa nagane Rukky,kuma fa wallahi zancen ki gaskiya ne...Har Yafara bani tausayi wallahi" ta tintsire da dariya har da Kwallarta,Asma'u ganin rainin hankalin nasu yayi yawa yasa ta mik'e tace
"Mttsscc idan kun gama kwa yi min magana...me I hav lots to do..."
Da sauri Rukky ta jawo ta ta zaunar da ita cikin serious mood tace
"Banza kefa wata M.ce,ki tsaya kiji na fad'a miki abinda baki sani ba,kinga tashin nan da yayi daga falo da kika shiga? To wallahi structure d'inki ce tasa ya rasa nutsuwa ya fice,"
Fadeela ma ta d'ora da cewa
"Eh...wllh,rud'a shi kikai,nasan yau da kyar idan zai iya bacci yasin"ta fad'a tana kashe mata ido d'aya,
Asma'u da tinda suka fara take Murmushin jin dad'i tace "Allah friends?"
Rukky tace
"Allah kuwa...Don haka yanxu mun gano lagon sa ko kunyi aure idan yace zai kawo miki raini ko yace zai tsaya ja mana class wllh maganin sa za muyi cikin ruwan sanyi.." Sallamar Abbanta ne yasa sukayi shiru don ko kad'an basu ji shigowar motar sa ba,
Gaida shi suka yi ya Amsa cike da kulawa yana tambayar su Karatu,"Alhmdllh"duk suka amsa kan su a k'asa,kallon Asma'u yayi yace
"Kawun ki baizo ba?"
Cike da girma mawa tace
"Eh..Abba bai zo ba"
Hanyar d'akinsa yayi,
Suka ciga ba da firarsu inda tako ma kan Assignment d'in su na makaranta,..
Abba ne ya fito sanye cikin shadda galila sai K'amshi yake hannunsa Rik'e da keys sai K'amshi yake ya nufi dinning,yana zama Kawu Sani da bashir suka yi sallama suma cikin shiga mai kyau,gaishe su sukayi sannan suka nufi dining d'in suma gun Da Abba yake,
"Asma'u" Abba ya kira ta,
"Na'am Abba" ta Amsa tana nufar gun,
Yace
"Yauwa ki d'auko babbar Daddumar nan ki kaita sitting room Anjima Alhaji Abdulfattah zasu zo,
" to Abba "tace ta mik'e ta bar gun,haka kawai kuma taji gaban ta ya tsananta fad'uwa amman sai ta fara karanto Addu'a,bayan takai Daddumar ta koma ta sanar wa Abba sannan takoma gun su Rukky ta fad'a musu,suka ce
"Allah yasa Alkhairi ne" ta amsa da cewar "Amin"
★★★★★★★★★★★★★★
4:14pm firgigit ya tashi daga nannauyan baccin da ya d'ebeshi yana karanta Addu'a,jikin sa yayi sanyi sai gumi da yake ta tsatstsafo masa,tissue yasa yana tsanewa,Idon sa ne yakai kan wall clock d'in d'akin da sauri ya janye blanket d'in daya rufa ya fad'a toilet ya d'auro Alwala, bai dad'e ya fito ya tada sallar, ya dad'e cikin sujjuda yana kaiwa Allah kukan sa sannan ya idar ya d'ora da karatun All Qur'ani cikin sassanyar muryarsa, a hankali yaji zuciyarsa na sanyi har ya sami relief sannan ya rufe Qur'anin ya shafa Addu'a ya koma bakin gado ya zauna,laptop d'insa ya jawo ya bude don fara duba Aikinsa,sai dai me..? Babu Abinda yake gani sai surar Husna lokacin data shigo,dafe kanshi yayi ya furta
"Ya salam"
Rintse ido yasake yi jin yadda jikinsa ke neman sau yawa gaba d'aya yaji yafara loosing Appetite d'in sa..shikam Wannan yarinya ta cuce shi,shi dai yasan ba son ta a zuciyarsa ko kad'an,ya san shaitan ne ke neman jefa shi cikin...
Knocking ya jiyo Anayi daga falo yasa ya bud'e idonsa ya miqe bayan ya rufe system d'in,
Bud'e wa yayi yaga security ne...cikin girmamawa security yace masa
"Alhaji nasan ganin ka"
Ba tare da ya Amsa ba ya koma ciki ya zaro slifas d'in sa ya fito,
Kai tsaye part d'in Abbansa yayi,da sallama ya shiga ciki,can cikin falon ya hango Abbansa zaune cikin shiga ta Alfarma yana shan fruits, kan rug ya zauna ya tonk'o she K'afarsa yace
"Abba well-done"
Alhaji Abdulfattah ya dubi tilon d'an nasa yana Murmushi yace
"Yawwwa Kana hutawa an ta soka ko son?"ya fad'a cike da kulawa,
'Dan Murmushi yayi yace
" ba komai Abba "
Tare suka sha fruits d'in sannan ya d'auko wa Abban ruwa da bowl ya wanke hannunsa bayan shima ya wanke,
Cike da kulawa Abbansa yace
"May GOD bless you"
Cikin jin dad'i yace
"Amin Abba"
Shiru ya d'an gifta sannan Alhaji Abdulfattah ya gyara zama ya dubi Abdul da gaban sa keta fad'uwa yace
"Emm..ehmmn..Abdulkarim.."
Da sauri ya d'ago jin yadda Abba ya kira sunansa don idan bai manta ba rabon da ya kirashi da Abdulkarim 4yrs kenan..jin Abban nasa yayi ya sake kiran sunan nashi
"Na'am Abba.." Cikin karyewar zuciya
Alhaji Abdulfattah ya cigaba
"Abinda yasa na kirawo ka shine Akan maganar yarinyar nan Ya'r wajen Hajiya Bilki....Am..umm..Asma'u, kamar yadda kasan tuntuni maganar nan take,don idan ban manta ba da tuni Anyi Aurenku..to saka makon uzurin da ka kawo Abaya yasa Muka basu hak'uri bisa sharad'in idan kadawo Nigeria,to Alhmdllh Allah ya dawo da kai Lafiya cikin Nasara mun sake godewa Allah bisa irin ni'imomi da baiwar da yake mana,To bayan Haka kuma wata biyu da suka wuce mahaifin yarinyar ya nuna lalle shi Aure zai mata,da ni da Alhaji bello muka je muka taushe shi bisa yarjeje niyar da ga Allah ya yadawo da kai don shi ummaru tun Alikacin muka bada dukiyar Aurensa ga yarinyar nan fareeda kuma suka karb'a akasa biki don yanxu haka saura 3weeks ko da yake nasan ka sani,to..yanxu dai Abinda nake son sanar da kai shine Anjima Ni da Alhaji bello da Malam Mustapha zamu je domin kai kud'in kuma dama babu Abinda nake fata da buri rin naga Na had'a Aurenka da na ummaru(ya d'an share hawaye tuno da Amininsa)..inaso a had'a ayi rana d'aya kuma bayan haka ka cikawa mahaifiyar ka burinta...
_*pinky ce*_
[1/26, 3:01 PM] maryam Tahir Author Y4: *YA'R ZINA CE👄*
_......Adulterer's Daughter_
*A TRUE LIFE, TOUCHING HRT & LUV STORY*
_BY_
*MARYAM PINKY*
www.Maryampinky@Facebook.com.
*®REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S*
_{We don just entertain nd educate,we touch the heart of readers❤_}
#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
*IG PML WRITERS*
#https//www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com
2⃣0⃣
Hararar Khadija ta kuma yi batare da tace komai ba,haka Khadija tagaji da tsokanar ta ta kyaleta....daga baya ma bacci ya d'auke su duka kasancewar sun gaji.
Basu suka tashi ba sai bayan la'asar sosae shima hayaniyar su Hajiya Mamaa ce ta tashe sun,Khadija ta dubi Ameera da ta lumshe ido tace"tashi mu lek'a mu gansu.."
Harara ta maka mata tayi tsokiii tace
"Hmmnn Allah ya min suttura da ganin su"
Khadija ta marairaice murya tace
"Kaiii Dan Allah ko Dan Me sunan Daddyn ki AI kyazo mu lek'a...ni fa ganin yadda suka zama kawai zamuyi ba wani Abinba"
Twisting bakin ta tayi tace
"To menene sabo A ciki?.kawae ni ki kyaleni..baran jeba ke tashi kije"
Jin zasu wuce ta kusa da part d'in su yasa Khadija mik'ewa da sauri ta lek'a,ta kai kusan mins sannan ta zauna kusa da Ameera da har yanxu idonta ke rufe ta 'Dora hannun ta akan cinyar Ameeran cikin zolaya tace"Uhumm Ammee kinga yanda Mai sunan Daddy ya koma kuwa?"
Banza tayi da ita kamar bata ji ba,Duka ta kai mata tace"wllh baki ga yanda ya sauya ba,ya zama 'Dan gay.."bata k'arasa ba taga Ameera ta mik'e tana cewa "Na barki lfy" tana gama fad'a ta shige toilet don yin wanka ta bar Khadija da baki a sake.
Ta Dad'e a toilet d'in sannan ta fito d'aure da towel amman ta saka hijjabin gadon(inji Khadija),tana shigowa falon taga Baba larai a zaune da alama sallah tayi don ganin carbi a hannunta, hamdala tayi don tasan khadeeja bazata yi mata maganar banza ba tinda ga Baba larai, bakin katifa ta zauna ta shafa mai sannan ta sa kayanta Atampa ta sake sa hijjabin colorn Atampar,jiyo Baba larai tayi tana cewa "Masha Allahu 'Diyar nan tawa" Murmushi tayi kawae,Khadija tace
"Ba kyau dae kikai ba"
Shiru tayi bata ce komai ba,sun jima suna firarsu su uku,can Baba larai tace "idan an idar da sallar magariba Ku shiga Ku gaisa da bak'in karku yi laifi.."
Khadija ce kawae

1 Comments On YAR ZINA CE
avatar
abdulkadir-6

1 year ago

Reply

Is a very educated and interesting novel

Please Login or Register in order to submit comment