Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fashe dashi da bata san na meye ba ta ƙarasa ta riƙe hannunta tana kuka mai tsuma zuciya tajima agun kafin Anty Nusaiba ta ɗagata itama tana share nata hawayen ganin yaddah Nanah takoma kaman tsinke tsabar ramar datayi ne yasa sanda cikinta ya nuna,nanfa zuciyan Ammih yakama ciwo sosai agun ta zube da gudu Anty Nusaiba tafita kiran Dr itama admitting dinta Dr yayi.



One week later,Anty Nusaiba da Salkhan suke lura da Ammih da Nanah,Ammih taji sauƙi sosai Alhamdulillah nan suka dakkufa lura da Nanah har roƙon Allah Ammih tasa akeyi mata dan Dr yace so yake tasamu like one month tana hutawa, kuma Dr yasanar ma da su Ammih cewa bbu abinda yasa mu cikin datake ɗauke dashi lfyn sa ƙlau bbu abinda ya same shi bbu wanda baiyi mmki ba,lalle bbu mai wannan iko sai Allah haƙiƙa idan kana jin wani abu sai kazata ƙaryane kuma yafarune a hakikanin gsky.......



Ɓagaren Maina kam yaci alwashi ko menene yau sai yaje ya duba Nanah siyayyah sosai yayi cikin booth ya kama hanyan asibitin,da tambaya aka raka sa har ɗakin da Nanah take Ammih na waje tana sallah Anty Nusaiba taje gida bbu kowa a ɗakin sai Nanah dake baccinta hankali kwance,sallama yayi bbu kowa ledojin hanunsa ya ƙarasa inda take hanunsa yasa ya riƙe nata yana ƙare mata kallo turo ƙofan da akayi ne nasa shi daga ido nan suka haɗa ido da Ammih da Salkhan dake biye da ita zaro ido yayi ya miƙe........




*Daga alƙhalamin* ✍🏽📝


*Nanah khadii* 💅🏽🛍️



*08069224458*
[8/28, 1:12 PM] Nana Khadiiii: 🕯️🕯️ *AUREN ƘIYAYYAH* 🔥🔥




*ELEGANT ONLINE WRITER'S* 📚

*A short story* 💋



*Na Nanahkhadii* 💅🏽🛍️




*Marubuciyar👇🏽*



*Cousins ne*

*Aruwan sama* *kaddara tasame*

*Almajiri ko attajiri*

*Hamdan paid book* *and now typing....* ✍🏽


*Auren kiyayya*




🅿️2️⃣2️⃣🔁2️⃣3️⃣





*This book is dedicated to my dearies my* *Dost and my behty can't heart you less you guys mean* *a lot to me* 💝💖





*Bismillahir rahmanin* *Raheem*



Baki buɗe Ammih kebin sa da kallo,cikin zafin nama Salkhan ya ƙarasa zuwa inda Maina ke tsaye,Maina duk ya razana jiran mezai faruwa kawai yakeyi.


Salkhan na ƙarasa wa gun ya kai masa mari,a tsawa ce yace "bayan ka kashe mata auren kasata cikin damuwa kuma still har kana right din daza ka shigo ka riƙe mata hannu, "oh! Sorry namanta kazo duba babyn ka ko?

Duk rashin kunyar Mainah,kasa mgna yayi kansa aƙasa,Ammih kasa fahimtar me Salkhan yake faɗa tayi,ƙara sowa tayi cikin tashin hankali tana faɗin "wai meyake faruwane? Idon Salkhan da sukayi ja kaman gaushi ya ɗago ya kalleta yana faɗin....


"Ammih wannan shine baban babyn da Nanah zata haifa, kafin yayi wani mgna Ammih ta sake salati tanafa faɗin, "Mainah ashe baka rabu da Nanah ba? "Kaga halin da ta shiga sbd kai ko kuma baka rabu da ita duk da hka kasake biyota sbd rashin mutunci harda riƙe hannunta,wannan abu dame yayi kama wuce kafita Allah ya isah tsakani na dakai ka ɓata mun rayuwar ƴa, tana kaiwa nan ta fashe da kuka mai ratsa zuciya.....


Kaman muna fiki ba tare da yace komai ba yabi ta gefen Salkhan ya fice a asibitin ransa a mugun ɓace to the extent da baisan tukun da yake ba,shi dai yabuɗe ido yagansa a asibiti ne kawai......



Ammih kuka takeyi sosai mai cin zuciya agun ta zube tana kukanta, Salkhan ganin ba iya rarrashin ta zaiyiba kawai yasa ƙafa ya fice a asibitin.......


Nanah nasamun kula sosai gun Ammih da Drs dan har roƙon Allah tasa ake tayata sosai,kuma cikin ikon Allah tana samun sauƙi sosai.



Wasa² yau kwannan Salkhan huɗu rabon sa da asibiti kuma Ammih nakiran wayan sam baya tafi a switch off yake abu duk yada mi Ammih sam bata cikin hayyacinta.




Yau watan su Ammih ɗaya a asibiti kuma yau Dr yayi sallama dan Nanah taji sauƙi garau bbu wani abu dake damunta.


Haɗa kayan su sukayi bayan Ammih ta clearing bill dinsu driver yazo zai kaisu gida har sun kama hanya, kaman daga sama Nanah taji Ammih na faɗin "gidan salkhan zaka kaimu zaro ido Nanah tayi tana faɗin "Ammih muyi me kuma? "Ubanki zamuyi acan uwar mgna da tambaya,jin haka yasa Nanah yin shiru ba tasake mgna ba har suka isa....




Saide gate din a rufe da key amma daga alama ƙofar ana shiga Ammih da kanta bbu mgna ta sauka, knocking tafarayi saide shiru kuma sake bugawa tayi still bbu mosti ganin haka tasa ta juya tafara barin gun sai kuma taji an buɗe ƙofan,juyowa tayi sukayi ido biyu da gateman din har ƙasa ya tsuguna ya gaida ta,ta ansa nan take tambayansa Salkhan,shiru yayi kaman mai nazari kafin yace, ya koma Abuja da aikin sa lst week yanzu weekend yake zuwa.



Zaro ido Ammih tayi cikin jimami da farga ba tace masa "tom idan ya dawo kace mishi dan Allah ina neman sa naci albarkacin iyayen sa yazo ingansa,tana faɗin hka ta wuce motan tana share hawaye.



Jikin ta asanyaye tashi ga motan suka kama hanya kallo ɗaya Nanah tayi mata ta juya kai zuwa window har suka isa gida bbu mai mgna a motan..




Haka rayuwa taci gaba Maina ya ɗanji sauƙi sbd yajijji ciwo sosai anata cinyan sa, Salkhan kuma ko waigo su baiyi ba tun ranar,Nanah kuma ciki sai girma yake abin du niya duk ya dameta kullun ta zauna kallon cikinta take tana hawaye tana tausa ya wa abunda zata haifa sbd ita kanta bata san cikin wa take ɗauke dashi ba yanzu, Salkhan ne ko Mainah duk ta lalace tayi wani iri sai cikin jikinta da yayi girma masha Allah kaman ma zai jata,duk faɗan da Ammih ke mata na daina kuka da tunanin nan abanza daga ta buya sai kuka.




8months later Nanah ce a labor room tanata fama dan tun dare take labor gashi yanzu kusan asuba duk ta gala baita ta fita a hayyacinta,"innalillahi wa'innah ilaihinji'un wayyo kute makeni zan mutu, "sorry dear insha Allah bazaki mutu ba Allah zai rabaku lfy,gyara ta Dr yayi ganin yanzu kam abun da gske ne wani nishi tayi tana faɗin "wayyo Allah Ammih zan mutu cikin ikon Allah kuwa saiga baby da ihu nan da nan aka shirya babyn,itama aka shirya ta duk da bata cikin hayyacinta sosai bai hanata cewa Dr she wants to see the baby ba, murmushi Dr yayi yace nurse din amiko mata babyn,nurse kam da saurin ta ta ƙarasa tana nuna mata babyn aiko jitayi zuciyarta ta wani buga ganin kaman babyn.........



Ɓangaren Ammih kam sai up and down take tana duk adduan daya zo bakinta tana faɗin Allah ya raba lfy,duk bata cikin hayyacinta damuwarta taga an fito dasu lfy........


*Daga alƙhalamin* ✍🏽📝


*Nanahkhadii* 💅🏽🛍️



*08069224458*
[8/28, 1:13 PM] Nana Khadiiii: 🕯️🕯️ *AUREN ƘIYAYYAH* 🔥🔥




*ELEGANT ONLINE WRITER'S* 📚

*A short story* 💋



*Na Nanahkhadii* 💅🏽🛍️




*Marubuciyar👇🏽*



*Cousins ne*

*Aruwan sama* *kaddara tasame*

*Almajiri ko attajiri*

*Hamdan paid book* *and now typing....* ✍🏽


*Auren kiyayya*




🅿️2️⃣4️⃣🔁2️⃣5️⃣





*This book is dedicated to my dearies my* *Dost and my behty can't heart you less you guys mean* *a lot to me* 💝💖





*Bismillahir rahmanin* *Raheem*




*_Idan kinsan bazaki_ _mun comments ba sticker zaki turo pls ki riƙe sticker dinki_ _nagode_*🥰🥰😘







"Congratulations it's a baby girl,cewar nurse din.

Murmushi kawai tayi ayayin da wasu hawaye masu zafi suka gangaro daga idonta,jikin nurse din ta ɗaura mata bayan,aiko rungumeta tayi bata san tym din da hawaye suka cigaba da zuba a idonta ba,ga wani jin son yar data keyi yana ratsa zuciyanta,kiss tamata agoshi tana faɗin,"Alhamdulillah welcome to the world swthrt,karban babyn nurse tayi aka fita dasu da sauri Ammih ta ƙaraso tana miƙa hannun ta karɓa babyn, bata san tym ɗin da idonta ya cicciko tana faɗin"Alhamdulillah Allah nagode nurse me muka Samu?? Murmushi nurse din tayi tana faɗin baby girl,"shikenan bbu wani garda ma ƴa kam ta Salkhan ce,kanta Ammih tabuɗe ko kwayar gashi bbu yanda ake haifan yaran turawa haka ƴar nan tafito,idan ba ance ba baza kace uwarta baƙa bace.


Ɗakin suka wuce Ammih na rungume da babyn suka shiga,nan suka gaggyara Nanah aka ɗaura mata drip suka fita,yayin da bacci yayi gaba da Nanah.


Ammih na riƙe da babyn ta miƙe zuwa office din Dr da sallama tashi ga yana rubutu ganin Ammih yasa shi ajiye file din da biro ya ɗago,kujera ya nuna mata ta zauna shirune ya ɗan biyo baya kafin tace "dama dan Allah huɗuba zaka temake ni kayi ma yarinyar nan,ɗagowa yayi ya kalleta baice komai ba ya miƙa hannu yakarbe ta,kallon Ammih yayi yace"da wani suna??shiru tayi kaman mai nazari kafin tace "Sofia sunan Maman baban ta knan dashi zaka matabbu ɓata lokaci yayi mata huɗu ba,Ammih ta ƙarbe ta suka koma ɗakin,Nanah kama baccin take sosai harda mun shari,haka yasa Ammih kiran ƙawarta kuma aminiyarta wato sa'ade takira akan tazo ta zauna da Nanah zata je gida ɗakko abun da suke bukata,batafi 30mins ba ko ta iso.

Daga Nanah har babyn bccin su suke tsakanin su da Allah,har Ammih taje ta dawo sai wajen magrib Ammih na sallah,babyn tafara kuka Nanah da takeji kaman a mafarki saide kukan gaba yakeyi, afirgice ta mike tana rarraba ido ƙokarin miƙewa tayi da kyar ta ƙarasa gun dan ancire mata drip din ta ciro babyn datake kuka sosai.

Rasa yazata yi da ita tayi kuma sai ta tsaya tana kallon yadda babyn ke kuka,Ammih na idar da sallah tafara mata faɗa "to kin tsaya kina kallonta baki iya rarrashi bane? Hannu tasa ta ƙarbe ta Nanah kuma takoma gadonta ta zauna dan yunwa takeji,Kaman yadda musulunci ya tanadar zam zam da dabino aka bata ta tasha ta koma bacci,nan Ammih ta kwantar da ita ta dama tea taba Nanah ko tass ta shanye ita ta koma baccin.....



Sai wajen ƙarfe 10 kukan babyn ya sake gau raye ɗakin dai² Ammih na zaune tana cin abincin da Anty Nusaiba ta kawo dan bata jima da tafiya ba,da sauri Ammih ta mike ta ɗauko ta tasata a jikinta saide kukanta take tsakani da Allah,hakan yasa Ammih tashin Nanah ta miƙa mata babyn,zaro ido waje tayi tana faɗin "Ammih mekuma zan mata? Kallonta Ammih tayi tace "mekika ga yadace ki mata koba nono zaki bata ba? Ji tayi zuciyarta ta buga ita fa tun rayuwar ta idan taga ana bada nono cewa take bazata iya ba,haka kawai ita sam shayarwa ma baya tsarin rayuwarta,ganin bata da niyan yin komai ne ga babyn sai kuka take yasa Ammih daka mata tsawa tana faɗin "wai kallonta nace kiyi ne?


"Ni Ammih da dai madara aka bata ni bada nonon nan sam wlh ban so, Ammih bata san tym ɗin data cire hannunta a abinci ba ta miƙe zuwa bakin gadon, "dan ubanki keda madarar na reneki kika girma? Bazaki bata ba amma zaki bawa wasu ƙartai daba muharra manki ba awaje suyi yadda suke so ko??

Jin mgnar Ammih yasata bata san tym ɗin da hawaye ya fara zuba a idonta ba,tuni ta ɗaga riga tama fara ɗaga rigar nan tweens dinta da suka cika suka tsattsaya suka bayyana,rasa ta inama zata sa ta tayi nan Ammih ta matso ta gyarata aiko tuni ta karɓa tafara sucking da ƙarfinta take ja Nanah har ranta takeji saide bbu yadda zatayi tunda ta fara sucking Nanah ke kuka harta gaji sa tasake tayi bacci,Ammih ta ƙarbe ta ta maidata gun baccin ta ta zubama Nanah tuwo shinkafa miyan ɗayar kubewa,da kyar Nanah ta iya cin loma uku sbd mgnar da Ammih ta faɗa mata yayi mata ciwo sosai...




Washe gari da safe aka discharging dinsu suka tafi gida,Ammih tasa aka ɗaura ruwan wanka tafara yima babyn kafin tayima Nanah da duk jikinta yake asanyaye,nan aka fara shirin suna sosai sai ana gobe suna Ammih tasanar mata sunan babyn,taji daɗi sosai nan tace ma Ammih dan Allah tana so akirata da (Noor) idan bbu damuwa "bbu komai Allah yakaimu.


Duk abun duniya ya dami Ammih duk yadda takeso tasamu taga Salkhan ko sakonta ya isar masa abu ya gagara gidan ma ya sallami mai gadin yanzu bako wani weekend ma yake zuwa ba sai ya bushi iska,haka ta hkra.


Ana gobe sunan Anty Nusaiba da yaranta suka iso gidan ranar Nanah taji daɗin ganinta sosai dan ta ɗauke mata kewa sosai,saide abu ɗaya ke damun ta tsotson Noor yayi yawa ko da tawa Anty Nusaiba complain hkri kawai ta bata tace kowani baby da yana yin cinsa.


Washe gari da asuba ka rada ma yarinya suna Sofia wace za'a dinga kira (Noor) tunda aka ce an raɗa suna babyn na hanunta tayi kyau sosai cikin set of lemon green tana bata nono kawai ta fashe da kuka,tana kallon babyn yadda take sucking hankalinta kwance idan ta tuna da abubuwan da suka faru sai tausayin babyn ya kamata,sosai take kukanta Anty Nusaiba ce tashigo tana ansa waya ganin kukan da takeyi yasata katse wayan ta ƙarasa inda take tana faɗin "subhanallahi meyafaru kuma me jego da kuka hanu tasa ta karɓa Noor dabata ƙoshi ba itama kukan tasa alamun bata ƙoshi ba,mayar da ita gun uwarta tayi tana faɗin "to acici mala'ikun tauna karɓan ta tayi saide kin mayar da ita tayi kawai ta rungumeta taciga ba da kukanta,guri Anty Nusaiba tana faɗin "Nanah Khadija me babban suna yada ɓacin rai kuma ranar farin ciki? Ɗago kanta tayi ta kalla Anty Nusaiba tace "Anty Nusaiba wlh inajin tausayin yarinyar nan inajin tausayin yadda zata taso tana kaiwa nan tafashe sosai da kuka mai ratsa zuciyan duk mai sauraro,jikin Anty Nusaiba sanyi yayi tasan akwai pains a abun saide daurewa tayi tace "mezai faruwa da ita Nanah gaki ga Ammih gamu muma insha Allah Noor bazata to zarta ba zata taso cikin gata da kulawa kaman ko wani ɗa, maganganun Anty Nusaiba sosai yasa taɗan ji sanyi tayi shiru.

Yan uwa da abokan arziƙi duk sun taru a sunan Ammih kwati biyar tayi uku na Noor biyu na Nanah kayan kam sai Masha Allah kowa na walwala banda Nanah data rasa meke damunta....


Life goes on haka rayuwa taci gaba Nanah bata ko fita kullun tana gida ko abu takeso saide Ammih da kanta tafita ko ta aika driver ya sayo mata Noor kam masha Allah tayi kiba kumatun nan na yaran turawa kaman zai zubo gashin kan sul sul yaso ma fita brown dashi ko makiyinta ya kalleta sai yasake kallonta,saide tana damun Nanah da tsotso kaman me har takai Nanah na bata rabo da abinci agefenta,dan ma tym to tym idan ba Ammih agun saita bata ruwa tayita rarrashin ta harta hkra takoma baccin......


Wasa² fa bbu ɗuriyar Salkhan bbu ɗuriyar Mainah akwana atashi yau watan Noor 8 harda yan hakorinta guda biyu tayi kyau sosai idan kashi go gidan ma kaganta zaka zaci mamanta da babanta turawa ne dan bbu wani abu data ɗakko na bakkin fata, gashinta akwance har gashi ga blue eyes datake da ga hanci yarinyar ta haɗu masha Allah abinda nima Nanahkhadii nace knan,Nanah ce zaune ta idar da sallah Noor ta rarrafo zuwa gunta tana ɗaga mata hijab ko kallonta batayi ba taci gaba da adduanta,ganin uwar bata da niyan kulata yasata kuka tana sake jan hijab din, hanunta ta ɗaga ta mareta ta tureta gefe tana faɗin "shikenan ni dan na haihu nono na bazai huta ba nima bazan huta,kuka sosai Noor ta fashe dashi ta rarrafa tana so yafita amma ƙofan arufe,kwanciya tayi kasan gun taci gaba da kukanta dan bata kuka sam bazakce da yarinya agidan ba,ganin yadda take kuka kaman zata shiɗe yasata miƙewa jikinta asanyaye ta ƙarasa gun tasa hannu ta ɗauke ta, koda taga itace kanta ta kwantar ajikin ta tana kuka bayan ta take shafawa harta ƙarasa bakin gado,taciro ta miƙa mata saide sam taƙi karɓa kuka takeyi sosai nan hankalin Nanah ya tashi tasan bata kyauta ba,tunda abincinta ne agunta da kyar ta rarrasheta ta karɓa duk saitaji wani iri kuma,koda tagama wasa tashi ga yi mata rana nafarko knan data tage tana wasa da ita,sosai take kyalkyala dariya wayanta taciro ta mata video ta musu hotuna ta mayar,dan yanzu wayan ma sam baya gabanta,haka tayi ta mata wasa har bacci ya ɗauke su agun.......




Yau shekaran Noor ɗaya da wata uku bbu inda bata zuwa da ƙafarta Nanah taso yayeta Ammih tace sai ta shekara ɗaya da wata 8 sosai Nanah taji haushin abun saide bbu yanda zata yi,zaune take a ɗakinta Noor tayi bacci ajikinta bata san meyasa ba yau tunda ta tashi take tunanin Maina num dinsa tayi searching saide takasa dialling ta kashe ta ajiye,still jikinta bai bata ba tasa sake dakkowa tayi dialling har ya kusa tsinkewa akayi picking,saide muryan mace taji jitayi zuciyarta ta buga ƙarfin hali tayi tace "assalamu alaikum "wa'alaiki sallam wake mgna dan Allah?cikin ƙarfin hali "tace dan Allah inaso nayi mgna da Maina ne,Ayyah ya fita school ya manta da wayan ne saide ki kirasa ta ɗayan number sa, "ok tom nagode saide idan bazaki damu ba dan Allah dawa nake mgna? Murmushi tayi tace matarsa ce,Nanah bata gama sauraron ta ba ta kashe wayanta ta ajiye Noor tashi toilet ta soma rera kukanta,ashe karya yake yi dama ba auren nawa zaiyi ba ashe yaudara ta yayi ashe macucine bayida Amana nikam nashiga uku wannan wace irin rayuwa nake ciki tajima tana kukanta agun kafin ta wanke face dinta ta fita ta kwanta agun bacci yayi gaba da ita da tunani kala².


A month later saide shiru bbu ko ɗuriyar Mainah bbu lbrinsa zaune take a parlor tana ba feeding Noor datake ta mata rikici tasha ta sake taciga ba da kukanta har tayi zuciya tace tinda bazata sha ba bari ta mayar da kayanta saide kuma ta dameta da kuka sosai,hakan yasa ta dakko ta ta dubgure mata kai tana faɗin idan zaki sha kisha idan bazaki shaba wlh lst tym da zan baki knan haba kibarni da damuwar da ke damun na,tasata aiko ta karɓa ta fara sha,kaman daga sama taji muryan dako a mafarki tasan me ita muryar da harta koma ga Allah bazata manta da ita ba da ƙamshin turaren da ko bacci taji saita farka,kasa ansawa tayi har ya shigo inda suke batako iya ansa sallaman sa ba haka bata ko ɗaga ido ta kallesa ba ji tayi zuciyarta ta wani bala'in bugawa miƙewa tayi ta cire Noor a nono ta ajiye ta agun ta yi hanyan sama da gudu tana share hawayen dake ƙokarin zubo mata,da ido yabita da kallo yana mamaki kukan da Noor keyine ya dawo dashi hayyacin sa koda ya ɗaga ido ya kalleta ji yayi zuciyan sa ta daina harbawa cak ta tsaya yana kallon Noor dake kuka tana bin Nanah tana blabbing.....


*Daga alƙhalamin* ✍🏽📝

*Nanahkhadii* 💅🏽🛍️


*08069224458*
[8/28, 1:13 PM] Nana Khadiiii: 🕯️🕯️ *AUREN ƘIYAYYAH* 🔥🔥




*ELEGANT ONLINE WRITER'S* 📚

*A short story* 💋



*Na Nanahkhadii* 💅🏽🛍️




*Marubuciyar👇🏽*



*Cousins ne*

*Aruwan sama* *kaddara tasame*

*Almajiri ko attajiri*

*Hamdan paid book* *and now typing....* ✍🏽


*Auren kiyayya*




🅿️2️⃣6️⃣🔁2️⃣7️⃣





*Bismillahir rahmanin* *Raheem*





"Kallon Noor yakeyi harta kai stairs ta fara hawa, kuma sai taja ta tsaya dan dama haka takayi idan a sama ne ko ƙasa zatayi ta yawonta,amma daga tafara hawa stairs sai taja ta tsaya har masu aikin gidan sun san halinta ne,saide a ƙarasa da ita.


"Cigabawa tayi da kukanta tsakanin da Allah,sai kuma tym ɗin ya dawo daga tunanin daya keyi,yabi bayanta yasa hannu ya ɗagata ganin bata san shiba yasata sake tsalla ihu,dai² da gangaro wan Ammih dan taji kukan yayi yawa kuma tana ta kiran Nanah shiru.

Baki buɗe Ammih kebin sa da kallo,Noor kam tunda taga Ammih take miƙa mata hannu,jikin Ammih a sanyaye ta karɓa Noor kafin tayi shiru,shikan sa kallon da Ammih ke masa sanda yaji wani iri,ba tare da tace masa komai ba ta juya ta haura sama,jikin sa a sanyaye yabi bayanta ɗakin Nanah tashi shiga,tana faɗin ina kika shiga?" kina ji yarinya sai kuka take kaman bbu kowa a gidan,Nanah kwance take a kan gado tana rusar kukanta mai ɗaci a zuciya,bata ko ɗago ba Ammih ta ƙarasa ta ɗaka mata duka tana faɗin,"idonki biyu nafaɗa miki ki dai na barinta tana wannan kuka mara anfani,miƙe wa Nanah tayi tana share hawayen idonta saide duk yadda taso ta boye ya gagara sbd jan da idonta suka yi,miƙa mata Noor Ammih tayi ta ƙarɓe ta saide koda ta ƙarbe ta,kallon mahaifinta kawai take mata tama kasa ko rarrashin ta kallonta kawai takeyi hawaye na zuba a idonta.


"Wai meye kike kukane?mutuwa akayi miki ne ko yaya? "Kibata Nono saiki kici gaba da kukun da ba zai anfane ki da komai ba,Ammih nakai wa nan ta juya zata fita Salkhan na tsaye ƙofar ɗakin saide ko nuna tasan yana gun bata yi ba zata wuce sa.


"Tsugunawa yayi dai² ƙafarta yana faɗin "ina wuni Ammih? Ko kallon sa batayi ba zata wuce sa,kaman daga sama taji yana faɗin"Ammih nasan nayi laifi kiyi hkri na dawo Ammih bazan sake tafiya nabar ku ba,cak ta tsaya ta juyo tana kallonsa, "Salkhan bbu abinda zan ce maka sai sai ka nuna min ni ba uwarka bace,mena maka Salkhan a rayuwa sako mun ƴa da cikinka a jikinta kace bana ka bane ka barni bani da lfy har gidan ka naje sai labari naji na kabar aiki a garinnan,haba Salkhan meyayi zafi haka gashi Nanah ta haihu ƴa tafito dangi mahaifiyar ka sak,to ko bamu ci arziƙin komai ba yanzu maci arziƙin yar ka kuma takwarar mahaifiyar ka ko?? Tana kaiwa nan tafashe da kuka mai ratsa zuciya guri tane ma ta zauna aƙasa tana faɗin,"ko dayake Salkhan baka da laifi kome kayi dai² ne duk halin da kuka shiga kai da Nanah nice sanadi, "naso kaina naso zuciya nasan bakwa son junan ku na saku Auren ƙiyayya gashi ya haifa mun ɗa mara ido,"dama inata roƙon Allah kafin na kwanta dama na nasaka a ido na nemi alfarman yafiya agunka,Nanah data zubo musu ido tanajin duk abinda Ammih ke faɗa tuni wani sabon kukan ya sake ƙwace mata,dan ko Noor dinma ajiyeta tayi gefe naciga ba da kukanta har tagaji tayi bacci agun, Salkhan dan Allah dan Annabi Muhammad S.A.W kaya femun abinda nayi maka a raywarka na roƙe ka,shikan sa hawayen yakeyi cikin kuka yace nayafe miki Ammih muna yima Allah ma laifi muroke sa kuma ya yafe mana bare mu ƴan Adam,cikin kuka Ammih ta kalli Nanah tace matso nan ta sowa tayi zuwa gun ta zauna a ƙasa kusa da Ammih,cema Salkhan ma ya zauna tayi shima zaman yayi kusa da ita,cikin kuka tace "na haɗa aurenku ne sbd wata manufa ta daban gara nasanar muku ko zaku yafeni ko da mgnar bazata yi muku daɗi ba nasan idan kunji zaku iya yafe mun karna tafi lahira baku yafe mun ba nakasa kwanciyar kabari dan nashiga hakkin ku yayi yawa,"abunda yasa na haɗa ku aure shine sai kuma tayi shiru kuka yaci ƙarfin ta,da sauri Salkhan yace "Ammih nasani ba sai kin faɗa ba wlh naya fe miki,cikin kuka ta ɗago idonta da sukayi jawur tana faɗin"me kasani Salkhan idan da kasani baza ka wai waye ni ba,karka ɗa kai yayi yace "eh nasa ni Ammih kuma nayafe miki,Nanah dai anbarta cikin ruɗani kallon su kawai take da ido,"aa Salkhan baka sani ba gara na faɗa dai kaji shiru yayi bai sake cewa komaiba ba,dan gsky har ransa yana so Nanah taji komai,"Na aura maka Nanah ne sbd mu mallaki dukiyar da mahaifin ka ya bar maka shiyasa duk abinda Nanah takeyi na dage sai ta aure ka duk da kuwa nasan ba kwa son juna,"Auren ƙiyayya bbu kyau haramun ne manzon Allah S.A.W yayi hani da auren dole duk na ture nasa son zuciya ta duk wanda baiji bari ba to zaiga hoho,Nanah kam tunda Ammih ke mgna ji takeyi zuciyarta nasa sake mata ƙuna kuka takeyi sosai har tana shiɗewa,cikin kukan Ammih tace "dan Allah ku yafe ni na ci amanar dana karɓa,cikin kuka Nanah tace "Ammih nayafe miki kuma nayi ma Allah godiya daya sa kika gane kuskuren ki nayafe miki Ammih na,nima ki yafe mun,"Nanah naya fe miki Duniya da Lahira Allah ya yafemu gaba ɗaya,saide ki nemi gafarar Salkhan yanzu da igiyar Auren sa kike bin wani, ko kallon sa batayi ba

Please Login or Register in order to submit comment