Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

karantata yayin baccinsa zai kasance yana da wani mai tsaro daga Allah, kuma shaidan ba zai kusance shi ba har gari ya waye. Akwai su da dama amma ki rik'e wannan."Na ce,"To." Na juya na soma karantowa, shimaya nufi gadonsa."Saboda dadin bacci ban san Asubahi tayi ba, sai da ya dawo Masallaci sannan ya tashe ni.Hakika ban ta6a bacci irin na yau ba a rayuwata, lallai dakin kai da dadi yake.Na yi mika yana tsaye kaina ya ce,"Ki ce(Alhamdulillahil lazyahyana ba'ada maa amatanaa wa'ilaihin nushur.) "Na fada ya ce,"To sakko in kullumin kin tashi bacci ki dinga karantawa, ita ce mai saukin fadi cikin addu'o'in bacci, na ce to.Har na kai bakin kofa ya ce,"Nasan dai kin iya ta shiga bandaki da fitowa ko?"Cikin murmushi na ce "(Bismillah) Allahumma inni a'u'zu bika mina khubusi wal khaba'isa, in na fito sai na ce"Gufranaka."Ya ce "Haka ne.""Ado ne ya koya min su."Na zo na yi Sallah yana zaunekan Sallayarshi cikin kayansa ya ciro ta, ya na krtn Kur'ani, dan karami ne irin mai zif din nan, na durkusa gwiwoyina 2 a gabanshi na ce"Ina kwana?"Ya amsa min da fara'arshi."Lafiya lau, mun kwana kalau?
[30/09 2:11 pm] Inna👬👫: 34."Lafiya lau."Na koma na kwanta bacci ya sake yin awon gaba da ni.Lokacin da na farka rana ta 6ullo, na yi mika game da salati, sanna na sakko. Ba yacikin dakin na leko tsakar gida shiru, na dawo na soma da linke kayanshi da ya cirejiya, na sauke jakarshi kasa na dora kayan a kai, sannan na shiga kici-kicn gyaran gadon, ya dan yi babu laifi na maida Jakar kai na gyara nawa gadon sannan na soma shara.Ina cikin sharar tsakar gidan na kusa soro(zaure) sai gashi ya shigo, na tsugunna na ce dashi."Sannu da shigowa."Ya rike kugunshi da hannuwa 2 ya ce,"Yauwa sannu da aiki Amarya, da kin bari nazo na share."Na dafa kirji tare daware idanuna."Haba dai, wace ni in sanya ka aiki."Yayi murmushi."Da gaske nake."Nagirgiza kai.""Wannan aikina ne."Ya nufi dakiyana cewa,"Allah ya baki lada."Na ajiye tsintsiyar na bishi dakin, kamar yanda dangin mahaifiyata suka fada mini, duk yanda zan dinga yi. Na shiga da sallama, yaamsa na ce "Za'a yi maka waniabu ne?" Ya dan murmusa tare da cewa dani"A'a je ki aikinki."Na gama na kwashe cikin wani danbuhu.Sallamar su Asma'u na ji kannan Binto, su 3 ne duk da kwanuka kansu.Cikin fara'a Asma'u ta ce min.""Amarsu kenan, ga sako in ji Haja.",Na dube ta da mamaki."Haja da kanta?"tayi 'yar dariya."To ita ce ta matsa min mu kawo."Na ce,"To."Sukai dakin.
35.Sun gaishe shi, sarkin kyautar har ya ba su kudi, ya ce "In dauko filat in zuba mishi abincin don ya duba yaga waina ne da kosai da kunun tsamiya, ya ce in zo da kofi.Na zo na aje ya ce zuba min to, na zuba mishi wai ya yi masa yawa in zo mu ci tare.Kunya ta cika nina ce a'a shi kuma ya ce ba zaya ci ba in har bn zo mun ci ba, na ce to bari in zo.Nima na zuba nawa kunun cikin kunya dai nake ci.Bako sallama sai muka ga an banko labule,Hinduwa ce tsaye a kanmu.Yakalle ta ya ce,"Lafiya?"Ta rike baki."Yau ni naga karuwanci, abincin ma tare kuke ci?"Na ce,"Hinduwa lafiya babu ko sallama?""Eh,ban yi sallamar ba don na zo gidanki shi neza ki dinga min jin kai?"Ai wallahi sai na fada wa Baba Gaje.Ya dube ta a fusace."Ke marar hankali, fitar min daga gida. Je kigayawa duk wanda za ki fadama wa, katuwa da ke ba ki iya sallamaba."Ta cije yatsa ta fita fuu...Ya dube ni."Wacece wannan din?"Kaina yana kasa na ce,"Yata ce Hinde, yanzun zata je ne gurin Baba Gaje ta kullanwani sharri.""Kada ki wani damu, ko ta fada me zata miki?"Ai yanzun babu wani umarni ko hani da take dashi a kanki."Na sauke ajiyarzuciya, muka ci gaba da karyawarmu.Ya ce,"Wanke min bandakin can zan yi wanka."
[30/09 2:12 pm] Inna👬👫: 36.Na ce,"To." Da na wanke sai da na kai masa ruwan wankan sannan na sanar dashi, na hada kayan da muka karya na wanke.Cikin sati 1n da dan birni ya yi na karu da abubuwa da dama, musamman ta 6angaren addini, krt kuwa daga Izifi dayan da na iya muka soma sai da na kai nasi, duk na manta ya tuna min tunda ran jiya ya sanar da ni in gari ya waye zai tafi birni, ya kwana 1 sannan ya koma can kasar da yake."Ban yi bacci sosaiba sbd tunaninshi, cikin satin 1n mun shakuduk da ko hannuna baita6a kwatanta rikewa ba, hakan nan mayuka cikin lefena ya zauna ya karantar da ni yanda duk zan yi amfani da su.Ashe turaren dakin ne muka yi ta fesawa nida kawayena a jiki, man shanfo kuma da shi aka min kitso, na kitson kuma shi muka yi ta shafawa a jiki, Allah wadaran rashin sani.Man wanke baki ma da har matar Yaya Auwalu ta ce min wai maganin kasbi ne da kurajan fuska, na ce tunda ban da shi bari na ajiye sai naga me kyasbin na ba shi.A daran duk ya fadan dokokinsa ya ce baya son yawan fita in ba da wani dalili mai karfi ba, shi ma din daga gidanmu sai gidan Haja, na ce,"To, insha Allahu zan kiyaye, amma ina so zan dinga zuwa gurin Binto tana min kitso.""To za ki iya zuwa, kuma mun gama magana da Haka akwai wata 'yar uwarta da ke can wani kauye, ta aika mata zata zota taya ki zama da kuma 'yan aikace-aikace.
37.,Na ce,"To." Ya kawo kudi masu dama ya bani ya ce,"In 6oye sbd cefane ko ciwo ko dai wata larurar, sannan ga abinci nan cikeda gurin aje abinci, duk irin na gwamnati.Hatta da garin tuwon ma na leda ne, ban iya amfanudashi ba ya dai ce min ba a mishi talge da ruwa ya tafasa takuwa kawai za'ayi.Cikin Satin dayan ma bn ta6a girki ba daga gidanMaigari ake kawo mana. Cikin akwatin ya nuna min guri yace in 6oye kudin don suna da yawa, sai dai na dan ragi wadanda zan rike a hannu.Tun Asubahi ya soma shiri, na kai masa ruwan wanka yaje yayo ni kasa karyawa ma nayi ganin duk na damu ya soma lallashina da cewa kada na damu, duk lkcn da ya zo zai tafi da ni birni ne gabadaya, ya sani a Mkrnt.Abin maganarsi ta soma tsiwa wadda ya cemin sunanta waya,yana dauka ya canza harshe na tsura mishiidanu una so in san me yake fada, sai dai na lura yana maganane da mutane daban-daban, don wasu yakin kira sunansu sannan kuma da Husna yake magana fa su.Sai dai na lura ya fi magana da wani wai*Mai Diya......Kuma yana yawan ce mishi lobiyu ko da misiyu ne.,Amma na lurako waye yana da mahimmanci a gurinshi, kamar in tambayeshi sai na share kada ya ce na cika tambayoyi....
[30/09 2:16 pm] Inna👬👫: 38. Ya gama magana sannan yace, "To dakko jakar kirakani kofar gidan su haja inda zan shiga mota,"Nace, " za'ayita maganata ace har nafara fita, ya dakko min hijabi ya mika mun sa muje" nasaka ya kulle dakin na daukr mishi jaka yayi yayiinbashi naki, inata jin kunya nuka jera sai dadda kai nakeyi a kofar mai gari duk jama'a sun taruna shige ciki, daki-daki nashiga ina gaida sumaman binto sannan na shiga dakin haja,lale take mun zan zauna kasa kan tabarma tace ina inzo bakin gado in zauna.muka gaisa sai kallonatakeyi cikin farin ciki,tace"Nagode Allah, Hauwa'u kulu keba jinina bace amma jinki nake kamar daya daga cikin jikokina, nasan muhammadu zai kula dake" nayi murmushinace gaskiyanki ne haja yanada kirki" Haja ta gyara zama akwai yar yata mai suna tasalla ta taba yin aiki a birni, itace natura tazo sai ku zauna tare zaki koyi girki gurintadon inda tayi aiki girki takeyi, tanada kirki sai dai tanada fada in antabota kenan, nasan ke zaku zauna lfy gata da aiki" Nace to Insha Allahu zan kula" yayi sallama yashigo na bishi da kalloduk sanda na ganshi nakan rasa dawata kalma zan gode ma Allah, wai dan birnine mijina? Kuma cikin kazanta ya ganni ya aureni, hakika nan duniya banida masoyin daya fishi, ya zauna suka gaisa da haja yana tsokanarta, uwargida zan daga yau mekikeso inmiki kafun intafi" babu komai muhammad aini kagama mun komai tundaka auri hauwa kulu yadubeni yayi murmushi, gatanan kikara kwantar mata da hankali naga duktadamu
39.haja tacd kada kiwani tada hankalinki kinji, aina mata bayanima yau tasalla na nan tafe nasan bakida raini kibata girmanta kinji ko? Nace to su Ado suka shigo, shima cikin shiri tare zasu tafi zai koma makaranta, yace angama wanke motar."nan ya sallamemu rakiya har waje haja ta mishi niko nakasa tashi dan damuwa, sai dai inna tuno yanzu koba komai yanzu na killatu awaje daya kuma matsugunin da babu irinta duk karkararmu.Basujima da tafiyaba binto ta shigo aa amarsu harkin fito"eh mai gidanne yatafi dazun" nan na yini saida azahar lokacin baba tasalla tajima dazuwa har taci abinci, sannan nuka nufi gidan tareda binto don tatayani gyarawa baba tasallagurin kwanciya, saida muka gama tashiga tana sallah sannan muma muka yi alwalanla'asar muka shiga dakina"har yanzu kamshin dan birni yananan adakin tamkar yana ciki sai da mukayi sallah sannan muka zauna hira da Binto tace ke yar gari baki bani labarin yadda kuka kwashe ba daangon nakiba" nadubeta da dan dariya kinsan har yatafi ko hanuna bai rikeba? Nafada miki shifa baruwan shi"Binto tace bawaninna ya dai tausaya mikine sai ya dawo"nimafa danaga ya ragesaura mu biyu a dakin har na soma fargaba, sai na kula sam ba wannan ne agaban shi ba baba tasalla ta katsemu Binto ke bazakiyi girki bane?"zanyi baba yanzu zan tafi, to maza taso kikama hanya kekuma fito muna muyi namu nan mukayi sallama da binto sai nazo kitso haka naci gaba da rayuwata cikin jin dadi harna cika sati biyu agidan, ranarce kuma baba ya kawo mun ziyara nayi murnan ganin shi shima haka ya dauko kudi a aljihun shi wai gashi ragowar sadakinki ne sauran anyi miki sayayya dashi nace nabar mishi yace aa zai saya mun tinkiya wai saina saki acikin gidana nace to. " watarana ina tsaka da cinabinci shinkafa ce da wake da miya dayakeduk ranar kasuwa baba tasallah ke mana cefane, girkinmu harda nama nakan saka akaiwa haja da babana, amma shi harfada yazo ya mun wai ba izinin mijina nakekai masa abinci in daina bayaso nace babafa yace abinci nane. Baba yace duk dahaka ba kullum ba.
[30/09 2:21 pm] Inna👬👫: 40. Baba gajece nagani tsaye akaina tashigo babu kosallama, gabana ya shiga faduwa ina fadin sannu da zuwa" itako sai kallon dakin take tana kada kai gamida tabe baki' Babu wai dama banda jere harda uwa ta rabe akayi miki? Lallai 'yar s0" tadubi kwanon abincin gabanta lallai dole kikori hinduwa kina cin shinkafa yar gwamnati da nama', bakorarta nayiba, maigidanne yace tadingasallama, Baba tasallatashigo tana cewa"kai kai surutun wanakeji harda zage zage, tadubi baba gaje lfy baiwar Allah? Ban saniba tadubi kuluwa wannanfa daga ina kamar kuncen hauka? Babata ce" nanfa baba gaje ta hau ruwan masifa wai ance mata mahaukaciyanan kuwa tasalla tasoma cewa ance miki mahaukaciya inba mahaukaciya ba mececeke kin shigo wa mutane gida babuko sallama, zoma dai kifita inajin zagin dakike mata ina jinki harda cemata mummuna ke kinga kanki? Nan dai nayi tsuru ina kallonsu,sukayikaca kaca da baba gaje ta shure kwanon abincindake gabana. Tasalla tace tafi dai kina bakin ciki ba kya cin irinshi" sai da ta tafi sannan tasalla take tambayata wacece? Nace mata kishiyar mahaifiyatace, nan dai tayitajinjina rashin hankalin baba gaje. Shi kuma daya kwana gidansa da safe yanufi gidan su dady don yamusu gasuwan ban gajiya da kuma sallama sannan ya daga." ya samu basma da husna lfy sai dai sunyi missin din juna sosai shida matarsa, don haka cikin kwanakin kamar suhadiye juna. Wani sabo tattali gami daji da ita yakeyi, wanda har yasa take jin kanta tamkar babuwata 'ya macen data kaita sa'a a doron duniya, yanzu tagama yadda Mb dinta zai iya zama mata uwa kuma ubanta,daginta kuma miji daya da daya.," Rayuwarsu abin sha'awa Basma tawaniyi kyau kamar balarabiya,MB yakan so ya zauna kawai yana kallonta, kullun kara jinta yake a ranshi bayaso ko daya ya bata mata rai.Aikin shi kuma yana tafiya yadda ya kamata, don haka shima ya goge fiye dada,daka ganshi kasan hutu ya zauna, kwanciyar hankali ya samu guri matsalar daya daya tuno da kasarshi zai tuna da jidda shi kuma baya son damuwar matan shi don hakama ya yanke shawarar kin sanar da ita, ko yaushe suna waya da daddy da kuma anty nana,tare da sauran 'yan uwa da abokan arziki, cikin haka yasamu wata hudu amma ko tuna jidda baya sonyi, duk da cewa yawa-yawan lokaci yana jin tausayinta don haka yakeso yazo yasata a makaranta.
[30/09 3:32 pm] Inna👬👫: 41. Wasa wasa har ana neman acinye wata shida lokacinne aka soma duban watan ramadan, wato watan azumi dady yace mishi suzo gida suyi azumi da sallah,yace dady kayi hakuri sai dai ni inzo inyi koda sati dayane don inada ayyuka sukuma karatu ya dau zafi yanzu" lokacin dayake wayan suna tare da basma ne dady yace sati daya amma kasan kabar matako? Da sauri yamike tsaye don kada lovely wife dinshi taji, yace nasani dady zanzo, suna gama wayan ta kalle shi." sweet heat me me dady yacene? Yazo ya runguneta tare dacewa dady yanaso ne muje muyi sallah agida "tace nima inason zuwa, yace kije kiyime? Tadubi fuskarshi haba dai nida kasata"Aa bayanzuba nidaai zanje saboda su haja inasoma tayi fasfot zan turasu Aikin hajji, Tabe baki tayi bata sake maganaba sai dai cikin ranta tace mayan kauye, shikuma sai yace da ita kinyishiru?' tace to mekake so ince?"Husna ma taso zuwa yahanata musamman ma don taga bilal dinta, suna haduwa ta internet kuma suna waya, ya tabbatar mata mahaifinsa yace sai wadda yakeso zaya aura don haka tarike masa amanar kanta yananan yana jiranta intazo zasuyi aurensu su shimfida rayuwarsu irin wacce suke wafarki. Nikam tun ina kirga kwanaki har nakoma watanni, inban mantaba wata shida kenan banida wata damuwa don inaci inasha, kowa yaganni sai yace nayi kyau, Binto kawai nakema korafin son ganinnshi.
42.Takan ce min kadana damu ga Ado in ya tafi yana fin haka dadewa amma Aina'u bata damuwa na kan ce to. Amma gara Ado ana samun lbrnshi, amma ni shiru babu lbr ko gurin Haja naje sai ta yi ta bani baki.Binto ta ce,"To in ki ka duba fa za ki ga kusan mazan garin nan fin rabi matasan sukan fita neman na kansu, ina nufin rani, saina ce kuma haka ne."A cikin wata 6 nan sau 2 naje gidanmu, bandamu da zuwa ba, don Baba ya kan zo lokaci-lokaci mu gaisa, zuwana na farko Baba ne ya ce nin dan wajan Hinde na fama da k'yanda shi naje dubo shi. Ina ta sallama babu wacce ta amsa duk da cewa suna tsakar gidan su, Jikina ya yi sanyi don na taho da dokin ganin su.Nawa zaton yanzun kowa ya saki na shiga dakin Baba Gaje, Hinde ce zaune kan katifa itama sai ta kauda kai, na ce Hinduwa ashe Zubairu bai ji dadi ba?"Budar bakinta sai cewa ta yi."Kin fi kowa sani tunda ke ce sila.""Za ki gane, garama ki sakar min da."Na mike tsaye tare da cewa."Kin san mi ki ke fada kuwa?"Na fito rai 6ace, na ce"Baba na wuce, Allahya sawwaka."Itama Baba Gajensai naji ta ce,"Lanti kun dai yarda da abindanake fada muku ko?" Gashi daga saka tsakin kukan ciki wuta har ta fice a gidan."Sai yanzun na gane nufin su. Ni ce na kamaZubairu shi ne ina shigowa aka zuba tsakin kuka cikin wuta. Hakan ya zo dai-dai fita saboda abinda Hinduwa ta min.Na yi shiru tsaye a kofar gida, ina cizonyatsa, zuciyata cike da dana sanin zuwa gidan.Na girgiza kai tare da cewa,"Ba komai."Gidan Binto na wuce daga nan zuwana na 2 kuwa rasuwar Zubairu ce najeranar 3 nan ma don Baba Tasalla ta matsa min ne sannan Baba ya zo ce in je i
43.Binto ma ta zo har gida ta ce in tura musu aniyarsu in je, don suna ta yada gare da cewa kin cinye shi shi yasa ki ka ki zuwa gaisuwa, har suna yada cewa mijinki kama shi ki ka yi kika rike mishi kurwa sai da ya aure ki, in ba haka ba me zai ci da ke?"Shi yasa ma tunda ya tafi satin bikin bai dawo ba.Na yi murmushikurum, bn san lkcn da zasu gane cewa Annabi, ya faku ba. Na ce, to zan je. Shi ne muka je tare da Baba Tasallah. Baba Gaje ce ma ta amsa mana gaisuwa amma Hindesabon kuka ta dasa tare da cewa zan ga karshena."Tasalla ta ce,"In ba taga nata karshen ba aiku kwaga naku." Sai da muka fita sannan Baba Gaje ke cewa nasan bani da gaskiya shi yasa na taso wannan masifaffiyar matar.Kun ji Baba Gaje shege yi da mai zina, sai ka ce itama ba masifaffiyar ba ce, tun dagasannan ban sake zuwa ba.Yau gidan Binto na tafi kitso, na same ta ta yi sanwar dambu, ta ce kin zo da son kananan kitsonku na fama gashi ina aiki, sai ki taya ni."Nan na canza zani muka shiga aiki, na ce mata."Kan sannan ma ya bushe, don na wanke.Ta yarfa min kitsona kanana masu ban sha'awa, na dawo gobe zamu tashi da Azimi cikin birni, su ance sun dauka tun jiya. Na rasa me yasa ba ma dauka Azimi gaba daya, abin yana damuna.Baba Tasalla ta ce,"Zaa siyo cefa ne?"Na ce to, na ciru sauran kudin daritara da hamsin, na cire hamsin din na ce je da su Baba su kenan.Abinda ya samu muyi amfani dashi, ita ce ko aje gurin Haja?Na ce a'a duk da tana tambayata ko ina bukutar wani abu?"Na ce a'a nasan dai tunda da danyan abinci ko ya ya zama sarrafa.
[30/09 3:33 pm] Inna👬👫: 44. Yau Juma'a mun dauki Azimi na 6, na fito daga wanka nayi sallah.Ina zaune ina shafa, na soma kwalliyata don ina son kwalliya.Tasalla ta leko ta dube ni.,"Ke wai ba na ce da ke in ana Azimi ba a wannan fente-fenten ba?""Tashi dai." Na tashi ina kallon fuskata cikinmadubi. Lokuta da yawa in na dubi kaina sai naga tamkar ba ni ba ce, fuskata ta washe ta goge ga laushi, ko yanayin manda nake shafaea ne? Haka nan cikin wata 6n dan nayi a killace jikina ya yi kyau, nayi 'yar kiba kuma kirjina ya ciko." Gashina ya koma kamar na fulani, na kan yi sha'awar kwayar idona farare tar gashin idanuna ya musu runfa.Dama hkrn kana ne da 'yar wushirya man bakin da nakw amfani da shiyasa sun zama farare tamkar kankara, kafufuna sunkoma bani da kaushi yanzun gwanin sha'awa Tiraren da nake shafawa da man da nake amfani da su sun kama jikina har dakina da kayan sawa na kamshin suke yi.Kan gado na hau na baje Akwatuna na ina duba kayan da zan sa, na dago wani jan yadi ina son saka kayan sai dai matsalar riga da siket ne kayan, naja tsaki kusan rabin kayana riga da siket ne.Na zuba musu idanu yanzu haka zan yi asarar kayan nan?Na ciro siket din na sauka nasa bai shiga ba, sai da na cire ciki in juya shi nan in juyashi nan na rasa ta ina ne dai-dai din, siket din sai da kyar.Na dorarigar a fiki na ce sai ku ce ta "yan yaye? Don Allah ga wannan 'yar riga, ga mamakina da saka 'yar shimin da nake sawa cire ta nayi sannan rigar ta zauna na daura dan kwali sannan na gyara kayan, nakuma gyare daki tare da karkade gadonmaigidan, duk da baya nan kullum sai na gyara gadon nasa sau 2, safe da yamma.Haka nan hankicin shi da ya mantada shi duk lkcn da zan yi wanki na kan wanke shi in linke in sa mashi kan gadon.Tasalla ta leko..
45."Ki zo ki kwashe naki abincin, yau dai mun cika kunun nan kiza ki kiran yaron nan ne ya kaiwa Baban naki?"Zan yi magana kenan muka ji sallamar danbirbi.Baba Tasalla ta shiga cewa,"A'a'a lallai yaumuna da manyan baki, da yamman nan kake tafe?"Ni kuma kasa motsi nayi ina kallon san6alelen mijin nawa, wanda ko cikin birni sai sa'a.Yana sanye da kananan kaya wando mai ruwan kasa riga mai ruwan madara.Ya yi 'yar k'iba har da dan tinbi.,Ya yi ado da saje da gashin baki, sam bn san ya zo kusa da ni basai da na ji Tasallahtana cewa so kuwa kai kin tsaya kina kallon shi ba sannu ba barka ya hanya? Kafin nayi magana sai na ji ya hura idanuna k'amshinsa ya gauraye gurin.Na sauke ajiyar zuciya tare da yi mushi sannu da zuwa, ya dubi Tasalla ya ce,"Amaryar ta wace kuwa?"Me ki ke bata ne Tasalla?"Cikin dariya Tasalla ta ce,"Kaji muke ci, ni kuwa sai na amshi Jakar tasa nanufi cikin daki.Ta ci gaba da cewa, sai ka ce tasan kana tafe yau gayan nata yafi na kullum. Ya shigo yana cewa ta ji a jikinta cewa ina tafeko Jidda?Na zauna bakin gadotare da rufe fuska. Yazauna kan kujera na tsugunna a gabnshi nace ina yini?"Ya amsa da lafiya.Sai kallona ya ke yi, ni kuma baki ya ki rufuwa, sam bai 6oye mamakinsa ba har lkcn shan ruwa, dama ya zo da tsaraba ciki har da su lemon zaki da kankana zuwa su Ayaba.Nan Tasalla ta hada su ta yanyanka wai irin yanda suke yi a inda ta yiaiki a birni har ina cewa "Allah yada dai ya ci kada yaga ko kazanta me an hada wannan da wannan sai ko ga mamakina yafi maida kai ga 'ya'yan itatuwan, sai kunu da kosai.,Har lkcn cewa yake ni ce kuwa?Na ganni kuwa?Nan fa dadi ya rufe ni, domin kowace mace na sani ta son mijinta ya yabe ta, ina nufin ta bir ge shi.
46.,Dama Binto koyaushe muke hira takan bani lbrn yanda zan ju da zaran mun soma rayuwa da mijina. Tun ina gwale ta har na soma kwadaita ma kaina hakan, don Binto irin matannan ne marasa rufi, na kan ce mata ke fa ki ke bani lbrn cewa Sama'ila yace miki ba kyau ki fadi sirrinku.Tunda ya fiya Sallar Asham bai shigo ba na sake yin wanka na kuma gyara jikina na canza wasuriga da siket din.Na dauki fitila ina dura kalazinr, na gama na gofe gurin. Ya shigo da sallama na amsagami da masa sannu da zuwa ya amshi fitilar hannuna yana haska ni.Yau dai kina son rikita ni da gayunki, ya ce zo ki ji na je ya zame dankwalin kaina."Kitsonki ya yi kyau."Na sunkuyar da kaina gabana yana faduwa.Ya shafa kitson da hannunshi, sai na ji waniyar........... a jikina, donni wani namiji bai ta6a rike ko yatsana ba. Ya ce,"Wacece ta miki kitso nan haka?"Kaina yana kasa nace,"Binto ce take mun.""Lallai zan yi mata biya na musamman ko?""To dama idan na bata kudi bata amsa, sai dai in Baba Tasalla zata je mana cefane Garko in bata ta siyo mato omo da sabulu na wanke hannu.""Ke ma kin kyauta amma zan yi mata biya."Na dauki dankwalina zan da
[30/09 9:01 pm] Inna👬👫: 47.Na ce,"To." Na koma na zauna a zuciyata kuwa cewa nakeshi kam baya raina abin kallo, ko menene na kallo a kitso?Can na tuna da krtna na ce duk fa krtna da ka koya min na haddace saigobe in ka huta ne zan karanto maka ka ji?"Ya ce,"Eh,amma yau ma da akwai wani sabon darasin da zan fara koya miki, kina so?"Na ce,"Eh,A raina na ce, kila na boko ne. Ya ce,"Yauwa yanzun fara da bani lbr da bana nan me ya faru?"Na ce"Ba komai."Ya ce,"To ina da ina ki ka je?"Na daga kai alamun ina so in tuno, na ce,"In gana dai fi zuwa gidan su Haja, sai kitso gidanBinto, in kaga na je wani gida sai dai barka ko gaisuwa."Ya ce,"To gidanku fa?"Shi sau 2na ta6a zuwa."Duk na fada mishi yanda muka yi da su Baba Gaje."Yar dariya ya yi tare da cewa dani."Allah ya sauwaka."Amin."Na amsa, sannan na tashi na hau gadona na kwanta

Please Login or Register in order to submit comment