Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kowa ya ji."Na ce,"To Baba menene?""An kawo kudin Sadakin ki na gani ina so, da kuma dukiyar aure."Na zaroido, batun kmar cikin mafarki."Da gaske ne Baba?"Ya yi 'yar dariya tare da cewa."Na ta6a miki irin wannan wasan ne Jidda?"A"a Baba." Na yi shiru ina tunanin wanene wannan zai taimake ni?Ina jin nauyi da na tambayi Baba, sai dai ko wanene kuma ko ya ya yake ina nufin tsoho ko kuturu ne ko kuma Makaho ne kaiko Mahaukaci ne na gode Allah, kuma zan bishi......."Baba ya katse ni da cewa,"Ba ki tambayi ko waneneba."Kaima na kasa na ce,"Ko wanene ma Baba nasan ya yi ne don Allah, kuma ya yi miki albarka.Baba ya ce,"Haka ne, Allah ya yi miki albarka.Kudinnan kuma zan baiwa Maigari ajiyarsukafin isowar lkcn, sai a saya miki kayan daki dasu.
[29/09 8:48 am] Inna👬👫: IDAN RANA TA FITO 3

4.Murmushi kawai nayi ban ce komai ba. Duk da haka zan so in san ko wanene amma Baba bai fada ba, kamar yasan me nake sakawa sai ya ce,"Duk da ba zan sanar da ke wanene mijin ba, ina mai farin cikin sanar da ke cewa duk kauyan nan da mokatan kauyannan baa ta6a samun mace mafi darajan Sadaki bakamar ki, kai ko cikin birni sai an tona."Ya kama hannuna."Jidda kudin auranki wallahi-wallahini mahaifinki ban ta6a koda ganin kudi masu yawan su ba bare in rike su, naira dubu dari ne cif."Na zaro idanu tare da kankame hannushi."Dubu dari Baba?"Ya jijjina hannuna cikin muryarka kuka."Dubu dari Jidda, talatin Sadakinki, ashirin na gani ina so, hamsin dukiyar aure."Na dafa kirji tare da ajiyar zuciya, hawaye na sauka kan kumatuna."Amma kiyi shiru, wannan tsakanin ni da ke ne, ko 'yan uwana ba zan gaya wa ba.Zan dai je insanar da dangin mahaifiyarki suma kuma zan kwa6e su......."Baba Gaje ta hankado labalen tare da cewa."Ai Hinden tana jiranki ki kakka6e mata shimfida shi ne ki ka zo ban ki ka yi zamanki kuna zagina ko?"Zaraf na mike tare da godiya da Allah da yasa bata ji me muke cewa ba.Ganin takarda da 6awon rake ta zo ta budeledar ta sassana, sannan ta dubi Baba."Allah ya isa in anci da kasanmu."Ni kuma ta zuba mun dankwashi a tsakiyar kai tare da ce min......Like·[image­]3·Report·Oct 10, 2014Msmart BG Zee Town*Kuka*Kai antyna kin dai san nafi Haidar ko??tun da niwataran ina ta6a aiki.Ku nayi sututu......Ai Allah ya kara kinayi masu amma aka raina ai ka yanzu an ba parrot aiki da cikawakubari na kara don zata amshe wayartaLike·[image]2­·Report·Oct 10, 2014Khadijah AdamuAdd FriendtomLike·Report­·Oct 10, 2014MsmartBG Zee Town5."Tsinanniya, ke ce 'yar so saiya saka ki a daki ku ci kifi ku sha rake." Ta hankada ni na fadi sannan na tashi na yi cikin gida.Duk da haka yau sai na samu kaina da rashin jin zafin abinda ta yi min, domin yanzun ina da tabbacin lkc yana zuwa da zab fita daga wannan halin, dominduk abinda aka sa ma lkc mai sauki ne, zai zo ya wuce.Na kakka6e mata shimfidar ta kwanta tanata zagina."Shegiya, tuntuni ina jin bacci kin ki zo ki kakka6e min shimfidar.A haka da ki kare mummuna kawai mai kama da naman daji."A cikin zuciyata na ce,"WANNAN KUMA SAI KI GAYA MA UBANGIJIN DA YA HALICCE MU."Ranar dai ban runtsa ba don faran ciki,kwana nayi ina tunani."Gani nake yi kamarin nayi bacci zan farka in ga cewa mafarki ne.Kwana nayi ina nazarin waneneangon nawa?"Amsa daya zuciyata ke bani, ita ce koma wanene Attajiri ne.Ko tsoho ne haka yana nufin zan dan samuhutu.Kai anya kuwa akwai yarinyar da ta kai ni sa'a duk cikin kauyanan?, Ina alfahari da wadannan abubuwan.Na farko duk cewa nafi duk yaran kauyan baki da muni (kamaryadda su Baba Gaje suke fada) kuma ni ce kadai dan Maigari wato Ado ya ta6a buda baki ya ce yana so.Na biyu, ni ce kawai dukcikin kauyannan dan birni da bakon gidan Maigari suka ta6ayiwa magana, sannan duk munin nawa ni ce na fi duk 'yammatan kauyanmu tsadar Sadaki.Lallai mai hkr yana tare da nasara.Washegari ina ta aikina na kosa in fita talladon in je gidan Binto in fesa mata, ko zan 6oye wa kowa batun aurena dole in sanar da Binto, sannan Haja

6.Sai da na gama talla sannan na shiga gidansu Binto, tana zaune tsakar daki nayi sallama na shiga. Sama'ila yana shan kunuya ce,"A'a Kuluwa ce?"Cikin murmushi na ce, "Ni ce kuwa. Binto sannu wai cikin nan naki da girma yake haka ma na Hinde."Ta ca,"Don Allah ke kin cika shirme, zauna mana."Na zauna muka gaisa da Sama'ila, ya miketare da cewa,"Ya tafi Gona."Binto ta yunk'ura zata tashi, ko rakiya zata yi masa? Sai ya ce"Zauna abinki na hutarki.""Allah ya tsare ya bada sa'a."Ta ce mishi.Ya yi murmushi ya ce,"Amin Kuluwa sai anjima."Na ce,"To sai anjima."Binto ta dube ni."Kin san Yaya Ado zai zo hutu kwanan nan kuwa?""Kai! Da gaske?""Allah kuwa." Ta tabbatar min.Ta turo min wani kwano."Ga d'umame nan ki ci ga kuma kunu cikin wancan kwanon shan."Na ce,"To bari in ci, nasan kona koma gidad'an ruwan kokon ma da kyarzan samu tunda Hinde ta zo."Binto ta ce,"Har yau dai abin na Hinde ya k'i ne?"Nace,"To Binto yaushe kuwa lamura zausudai-daita, ko yaushe Baba Gaje tana shiryamata yanda zata ci mutuncin uwar miji da shi kansa miji. Binto ban ta6a rik'e su BabaGaje cikin raina ba ina ga shi ne Allah ya yi min wata sakayya."Ta dube ni da kyau."Wani abunne ya faru?"Na gyara zama na fara kora mata duk yanda muka yida Baba jiya. Murna gurin ta ba a magana.Sep 4Aisha Ummu Shureim Sa'eedMsmart BG Zee Town7."To ya ya ba ki tambayi Baba ba kin ji ko wanene?"Na ce,"Na kula baya so in sani ne, ana shi zaton ba zan yarda ba k'ila tsoho ne."Binto ta ce,"Insha Allahu ma ba tsoho ba ne.""Ni ko nakasashshe ne ma na gode Allah, tunda ya d'aga ni daga gaban Baba Gaje. Sai dai fa Amana na baki bana so ki fada ma wani, don su Baba Gaje ba su sani ba.""Ai ko babu mai ji, sai dai zan so ki fadawaHaja, nasan zata yi murna sosai.""Daga nan can zan nufa."Haka kuwa nayi.Ina shiga dakinta ta tare nida fara'a muka gaisa. Cikin zumudi na shiga karanto mata abubuwan da suka faru. Jin baba bai gaya min ko wanene mijin ba yasa Haja yin shirutare da nuna min bata san komai ba akan auren.San da na ce mata "Ina zaton tsoho ne ko yana da nakasa shi yasa baba ke 6oye minko zan ki.Sai naga Haja ta kwahe da dariya tare da cewa."In Allah ya yarda ma yaro ne."Na ce,"Ko wanene ma Haja in dai Musulmi ne ya yi min.¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤An­ samu kusan sati 2 da faruwar lmrn, rannan sai ga Dija Aminyar Baba gaje."Ina gibdin murhu ina jiyo su lkcn da take cewa da ita."Kawalli kin ji lbrn da na samo gidan Hassi?"Ta sake nisawa tare da rik'e bakinta.""In ko haka neGaje kin yi sake."Gaje ta ce "me aka yi kuma? Ko kina nufin batun Hinduwa?"Dija ta gyara zama.""Tabbbas ba ki
[29/09 9:19 am] Inna👬👫: Idan rana tafito

n8.Dariya Baba Gaje tasheke da ita har da kwarewa, sannan ta ce da Dija.""Don Allah ina ki ka samo wannan lbrn k'anzon kuragen?Ai ko cikin mafarki haka ba zata ta6a faruwa ba, bare gaske."Dija tayi 'yar dry tare da cewa."Ke dai bincika a hankali, domin kuwa za su iya 6oye miki."Cikin rashin yarda da zancen take dariya da cewa"To zan bincika, don ance ba a k'inta mu2m. Amma bisa gaskiya shirme ne wannan zancan." Ta nuno ni da yatsa."Dube ta fa sai ka ce dabbar daji, tayimiki kama da mu2m wadda za a duba ace ana so har ma a aura?"Dija ta shek'e da dry."Wa yaga Mujiya."Da suka fito zata tafi sai ta ce"Tambayar ta mu ji."Baba Gaje kuwa sai cewa ta yi."Kuluwa da gaske aure Babanki zai miki?"Na dube ta sannan na ce,"Yaushe?"Nan suka shek'e da dariya.Dija ta ce,"Har da saurin tambaya taji batun barin gidan nan, babu inda zaki."Baba Gaje ta ce, "Ina kuwa zata, aure sai dai ki ga wasu nayi. Yanzun ma ai kin yi bandaro tunda duk sa'o'inta sun yi aure.Da za su yi sallama ne Dija ta sake jadda matacewa ta tuhumi Babana. Bba gaje ta ce,"Ki daina damun kanki, "k'arya ce kawai,amma zan tuhumi 'yan uwansa tynda in ya6oye min ba zaya 6oye ma 'yan uwansa ba. ai sune za su bada ta."Suka yi ban kwana ta tafi. Cikin zuciya na ce,"Allah ya shirye ku in madu shiryuwa ne,in kuma ba masu shiryuwa ba ne Allah kai kasan yadda za ka yi dasu.Duk in da Baba Gaje tasan zata samu lbrn auren nawa ta bincika amma bata samu komai ba, daga k'arshe dai ta tattara ta watsar da batun
9.Cikin satinne sai ga Ado, na sha mamakin ganin yanda Ado ya yi kyau tamkar shima dan birni ne. Har gidanmu yazo yagaida Baba, kuma ya saka wani yaro ya kira ni na fito muka gaisa, na ce,"Ya birni ka gankakuwa Ado?"Ya yi dry tare da kallon jikinsa.""Kemaai kin kusa zama 'yar birni."Da sauri na ce, In ji wa?"ya sassauta murya."Kina nufin za ki 6oye min ne? Ai na samu lbrn auranki.""A can birnin mijin yake." Nayi saurin tambayar shi.Ya yi 'yar dariya tare da cewa,"Gaskiya kina da sa'a Jidda, duk kauyan nan ke ce ki ka fara samun miji daga birni."Cikin dariya na ce,"Ni fa dan san ko a ina ne mijin yake ba, ban san ma irin shi ba."Ado ya ce,"Za ki san shi, ke dai ki yi ta addu'a Allah zaya dai-daita miki lamuranki."Na ce,"To na gode, ai lamura ma sun somagyaruwa."Baba Gaje ta fito."Kai me ka ke yi gurinta?Ban raba ku ba?"Ya ce,"Na zo ne ai mu gaisa."Tasa bayan hannu ta mauje ni tare fa ce min"Karya kawai, wuce ciki."Ado ya dube ta cikin rashin jin dadin abinda ta yi min."Bana da kin daina nuna hassadar ki da k'iyayyar wannan yarinyar ba ki san irin baiwar da Allah ya yi mata ba, k'ila nan gaba inuwarta zaku sha ke da 'ya'yanki.Nan ko ta shiga jaraba tare da tsine-tsine. Ado ya ce,"Ki dai yi tunani Baba,in babu duniya dai akwai lahira." Ado dai ya manna mata hauka ya tafi.Sai zuma bala'i take duk makota sun taru wai kan me Ado zai ce mata ita da 'ya'yanta za su sha inuwar Kuluwa?"Wacece Kuluwa?"Ko uwarta ma wacece har ta mutu bate ita.Ta gaji ta wuce cikin gidan, nan ko ta shiga jibgata wai ko'ina naje sai in dinga zaginta, sai da ta barni kwance sannan ta ce in zo indebomata ruwa."¤¤¤¤¤¤¤¤Su M.B ana can soyayya ba dama ne, duk wani tattali suna yiwa juna.Tuni kuma sun soma zuwa Makaranta.Sep 4Aisha Ummu Shureim Sa'eedMsmart BG Zee Town10.Basma tana yin duk wani abu da ta san zata faranta masa rai, haka shima. Ta fannin abinci ne yake da matsala, in yana gida ya kanyi irin wanda ya iya suci, in kuwa ba shi da lkc dama suna da masu aiki.Rayuwarsu abin sha'awa, Husna ma ta kiraHjyrta ta shaida mata suna tare da Brotherdin su a America, kuma tuni ta soma zuwa Mkrnt. Nan take Hjyr ta shiga zaginta tare da cewabata da kishin uwa ta nuna maya cewa Bello yafi ta kenan, duk da tozarcin da ya yimata. To ta gaggauta baro shi ta dawo ta yafe ta itama kamar yanda suka yafe Basma.Husna bata katse mahaifiyarta ba sai da takai aya sannan ta ce,"Hjy magana ta gaskiya Brother ba shi da laifi, duk da abubuwan da ku ka mishi bai sa ya ta6a nuna min ba, haka nan bai ta6a min hirar abinda ya faru ba. Hsali ma shi ne ya somamin albishirin cewa yasan va za a tsare ki ba, kuma hakan e ta faru."Hjy ta ce,"Na gode kin dai nuna min cewa Bello ya fini."Ta ce, "Ba haka ba ne Hjy. Dady ba zaya yarda in dawo gurinki ba haka nan zama gidanmu babu dadi tunda ni kadai ce in Dady ya fita.,Sannan kuma Bilal Hjyr sa ta ce ba zaya aur ni ba, saboda abin da kika yi.Ni kuma gaskiya zaman gurin ya ishe ni, ina jin dadi a anan gani ga Anty Basma.,Tsaki Hjyr taja sannan ta ce, "TO shikenan ki zauna ke da makiyan nawa, tundasun fini mahaifiyarku." Ta kashe wayarta."Kuka Husna ta saka, nan Basma ta shiga lallashinta tare da cewa, "Wata rana zata gane, Kuma zata yarda cewa mijina mai gaskiya ne.
[29/09 9:28 am] Inna👬👫: Idan rana tafito

11.Mata da yawa suna bada lbrn halin maza na rashin kirki ko cin amana, ko kuma sakacin alkawari, niko zan bada lbrn rike alkawarinshi gami da yafiyarsa.Ki lura Husna, Bello Tahir bai ta6anuna min cewa mahaifina yasa a harbe shi ba, kuma an harbe shin ya yi jinya amma bai nuna min ba, sai da ya taho Sajan yake fada mana tare da ke."Sannan mahaifiyarki'yar uwarta ce dubi abinda ta mishi amma hakan bai sa shi juya baya daga gare mu ba ni da ke.Hasali ma sai tattalinmu gami da nuna kuluwarshi gare mu. Kalli irin kudin da yake kashe mana."Husna ta ce,"A gaskiya Anty Basma kin gama dace shi ne dalilin da yasa ki ka ga ina son Bilal, don wasu da'iun Bros rin nashi ne."Basma ta ce,"Na Allah in yaso sai ki ga ya shirya lmrnkun auri juna.""Allah yasa haka ne."Duk abinda Basma take fadi kan Bello Tahir haka ne, har cikin ranta ta ba shi dukkan gaskiyarta, duk abinda ya ce gare ta gaskiya ne.Ta yi matukar yarda dashi, shi kan shi in yatuna da batun Jidda gabanshi yana matukar faduwa, sai ya samu kanshi da da ya sanin auren da ya dedo ma kanshi, amma kuma in ya tuna da halin Jiddan ke ciki sai yaga cewa taimako ne, fatan shi daya Allah ya shige mishi gaba kan niyarsata alkhairi.Yana cikin mota kan hanyarsa ta dawowa gida Dady ya kira shi yana sanar da shi cewa.""Bello an bani mata, ina nufin shawarar da ka bani nayi kanta. Yanzun haka zuwa ranar Jumma'a zaa daura aure, kuma ta tare."M.B ya ce,"Kai amma fa nayi murna sosai,amma ka bincika sosai ko?"
12.Ya yi 'yar dariya."Na bincika mana Bello, Bazawara ce amma yarinya ce haihuwarta daya, mijintaya rasu ne."M.B ya sake cewa da mahaifin nasa."Ka bincika dalilin mutuwar mijin nata ko?"Saboda cutuka da suka yi yawa yanzun."Ya ce,"Eh hadarin mota ne."Yar limamn anguwar mu ce tana da hankali sosai, hakanan ga duk binciken da nayi bn ji wanda yafadi aibunya ba.""Alhamdulillahi,­a gaida mana Anty sai in mun zo."Yana isa gida ya taras da su Basma sun dawo daga Mkrnt, duk kansu suna zube kan kujera. Da sauri Basma ta taso ta rungume shi tare da mishi sannu dazuwa, Husna ta mishi sannu da zuwa. Ya zauna a gajiye ga yunwa.Basma ta zauna kan cinyarshi tana cewa da shi,"Darlingyunwa muke ji sai yanzun Helin ta dora abinci, kaje ka amshe ta don ka fi tasauri kuma naka yafi dadi."Yasa bakinshi ya dan tsotsi le6enta tare da cewa.""Na gajiMy Dear,nima in so samu ne in hau cin abinci yanzun."Dukkansu da Turanci suke magana tun zuwan su k'asar ba sosai suka cika yin Hausa ba."Ta ce,"To kaje ka taya tamana."Ya sake manneta a jikinshi."Basma ke da Husna ya dace ku koyi dafa abincu fa, musamman ke Hunsa in ni na jure baki sani ba ko wanda za ki aura ba zaya jure ba.""To kuwa Brother in ba zaya jure ba sai dai ya yi ta cin Indomie."Dukkan su suka sa dariya."Ya ce,"Na tuna Dady fa ya yi aure."Husna ta zaro idanu.""Aure kuma Bros?""Uhmhm!Ba a dai daura ba sai ranar Jumma'a."Ta ta6a baki, Basma kuma ta ce,"Budurwa?""Yariny­a ce amma ta ta6a aure."Husna ta ce, "Ni kam Bros ka ce mishi ya hkr ya dawo da Hjy.,Ganin yadda ta 6ata rai tamkar zata yi kuka sai ya ce,"Tozan shawarce shi amma kin san ba lallai bane ya yarda."Husna ta ce," In ma ba zaya dawo da ita baya hkr da auren ya auro karamar yarinya ta raina mu?"
[29/09 9:29 am] Inna👬👫: 13.Dariya Husna ta bashi, ya dai gano cewa kishi ne ke damun Husna. Waton tana kishin mahaifiyarta."Dady bai isa ya zauna haka ba tukunna batare da wadda zata dafa mishi abinci ba."Ta zum6oro baki."To baga kuku ba?""To in mun yi waya zan fada mishi, ko kuma ki kira shi ma."Ta ce,"A'a kai ne zaka fada masa don ya fu jin maganarka.""To zan fada, ki ka ce in ce mishi kina gaidaAntynmu ko?"Husna ta sake turo baki.Basma tana dry tana kalon fuskar M.B, ta sumbaci wu yanshi tare da cewa.""Honey kana k'ara kunna Husna ko?"Helin ce ta katse su da cewa"Ta shirya musu tebur."Shi kam M.B ya kanci abincin Helin ne kawai don yunwa, amma ba wai don dadi ba, su kuwa su Basma har da santi.¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤Ran­ar Juma'a kuwa bayan an tashi daga Sallar Jumma'a aka daura auran Alhj Tahir da Amaryarsa Fatima, wadda aka fi sani daNana, kuma a ranar ne ta tare a gidanta wanda yasha gyara tare da cana dukkan Ma'aikatan gidan.Rayuwa sosai su Dady suka shiga Shimfidawa shi da Nana, lallai namiji damaan ce namjin yana tsufa ta wani gefe ya kuma lkcn karfinshi ke kara zuwa ya dinga jin shi tamkar saurayi.Nana zata shaida hakan.14.Ni kam ina nan zaman jiran miji har an sa kimanin wata 6 ni da Baba ya ce nan da wata 3 har an kara 3 ga matsi da nake fuskanta daga gurin Baba Gaje fiye da da.Ga Hinde tunda ta haihu aiki ya karu gurina, wankin kashi, goyon yaron mai suna Zubairu, du in da zani dashia baya, ko talla har ma wani lkcn ya ki uwarsa sai ni.Binto ma ta haihu 'yarta budurwa sunanta Jamila, matar Ado ma tana nan da nata cikin.Shi kuwa M.B baya son zuwa Najeriya ne sbd batun auranshi da Jidda wanda kusan shi ne ya janyo ma kansa, amma in ya yi wani tunani sai yaga kamar bai yiwa iyayanshi da ita kanta yarinyar adalci ba, inya san ba zaya iya ba me ya kai shi cewa za ya yi?"Koda yaushe cikin saka wannan lmr yake, daga karshe ya tattara lamuranshi ya mikasu ga Mahaliccinshi, duk abinda ya faru da shi ya yarda daga Allah ne kuma zai amsheshi hannu bibbiyu
[29/09 9:32 am] Inna👬👫: 15.Cikin haka kwatsam sai gashi aiki ya taso mishi daga gurin aiki an tura shi Najeriya, alissafin shi aikin zai dauke shi tsawon sati 2amma an bashi sati 4, don haka sai ya yi tunanin yin amfani da damar ya cika alkawarin da ya dauka duk da dai Lagos aka tura shi aikinki.#NIGERIA!Ya sauka Najeriya a Abuja, watanshi 9 kenan rabonshi da kasar.Ya sake hawa wani jirgin don zuwa Lagos. Cikin taimakon Ubangijinshi a kwana gomaya kammala aikin shi, ya nufi Kano.Kafin ya bar Lagos din sai da ya hada lefenshi tsaf,a kwatuna ne guda biyar da dan karamin su cikon na shida.Ya bi jirgi ne zuwa Kano sannan ya yi shatar mota zuwa gidansu, kafin ya karaso ne ya kira mahaifinshi ya sanar dashi cewayana shigowa yanzun nan don ya iso Kano din.Dady ba ya gida amma ya kira Nana yashaida mata zuwan dan nasa.Lokacin da yashigo gidan bayan ya sallamimai tasi, 'yan aiki suka kwashi kayansa zuwa ciki.da salla,a ya shiga falon, babu kowa ya sake yin sallma tare da zaunawa kan kujera.Ta fito tana sanye da atamfa 'yar Ingila da bakin hijabi a kanta.Kyakkyawar mace mai cikar mutunci, da fara'a ta tare shi tare da cewa "Kai ne tafe?"Ya yi murmushi."Ni ne Anty."Bata samu matsala ba don bata baringidan babu abinci.
[29/09 11:21 am] Inna👬👫: 16.Nan ko ta shirya masa abinci kan tebur ta zo ta ce"To Bello ga abinci fa sai dai Allah yasa kana cin rin shi domin namu ne na gida."Ya ce,"Anty kenan, ai ni na fi son komai nawa inda zai yiwu in yi amfani da na gidan ba ma abincin ba."Ya ci gaba da cewa,"Ba mu gaisa ba sai batun abinci." Ta ce,"To ai zamu gaisa tunda gida kazo."Tuwo ne na shinkafa da miyar shuwaka, yaci tamkar kar ya koshi don dadi, ya jima baikoshi haka ba. Yana idar da sallah Dadynshi yanashigowa.Ya dubi mahaifin nashi da murmushi cikin tsokana."Dady kai ne kayi k'iba haka?"Dariya suka sa har Nana.Dady ya ce,"Aikin Antunka kenan, cika miniciki take yi da kalolin girkinta."M.B ya ce,"Na lura don nima na shaida haka.""Yaya ya zo babu su Husna?"M.B ya ce,"Ai ya zo Lagos kuma ya kammala aikin.""Allah ya taimaka,ina fata dai ka taho da shirin ka na zuwa kauye, don Babanka Maigari da kansa ya zo kwanaki don jin yanda ake ciki, na kumatabbatar masa da ka iso da sati guda za a soma biki."M.B ya share zufar da ta feso mishi, sannan ya dubi mahaifinsa.""Kayan can lefe da shi na taho."Dady ya ji dadi tareda cewa Allah ya yi masa albarka.Shi kuwa ya ce,"Anty Nana ki duba duk abinda babu sai a zuba, sannan a yi mata dunkunan kayan da za da zai samu duka." Ta ce,"To, sai dai a raba ma Teloli."Nan ta shiga dubu kayan.Rantsattsun lesuna ne da shaddodi da kuma atamfofi duk na karshen kudi, takalma da gyalulluka zuwa after dress ba a magana.
17.Anty Nana ta yabakaya, sannan ta ce, "Sai kayan shafa zuwa kayan ciki irin su siket." Ya ce,"To Anty sai ku shiga kasuwa, yarinyar dai k'arama ce ina tunanin ba ta wuce sha shida zuwa sha bakwai ba."Anty Nana ta ce, "To za'a siyo. Sai batun dunkunan a dinka duka?""A dinkesu kawai don can ba su da wasu Teloli."Dady ya ce,"Haka ne."Bayan sun gama wannan babin sai Dady ya ce,"Ka sanar da Basma kuwa?""A'a sai nan gaba saboda wasu 'yan dalilai."Haka da dare sundawo daga Sallar Isha'i su da Dadynshi suka samu abinci kusan kala 4, kowanne dai-dai cin mutum uku. Nan fa M.B ya shigaruwan ido ya ma rasa wanne zai ci, nan ya ci wannan ya ci wancan ga kunun aya da kwakwa da dabino, ga so6o.Ya dubi Nana ya ce,"Anty Nana ina ma a nan nake."Duk suka saka dariya.Abinda ya k'ara birge shi da matar mahaifin nasa shi ne, yanda take matukar girmama shi da yin tsantsam da duk wani abu da tasan zai sosa masa rai.Cikin dare yana kwance gefensa na da tunanin Basma yake yi wadda ba su dade da gama waya ba yanzun.Yana son ta bayason abinda zaya sosa ranta. Yana tunanin ranar da zata ji ya sake aure ba tare da ta sani ba.,Gashi ta yarda dashi duk wata gaskiya ta ba shi, tana makutar sonshi.Ya tuna sanda zaya taho, rungume shi tayi tana kuka, kuka sosai da kyar ya sha kanta dama kwana biyu kafin ya taho ya shiga kasuwa da su sun siyi duk wani abu da za su bukata kafin ya dawo., Ya basu mota ya kuma ce baya son suje ko'ina sai Mkrnt, ya tsorata su da cewa kada su ga ba ya nan sucanza dabi'u ya saka abinda duk inda suka je za ya mishi bayani.
18.Duk sun yarda musamman Basma wadda ta tuna abinda ya faru baya. Ya yi murmushi da ya tuna yanda suka tsorata tare da rantse mishi cewa ba za su canza ba.Ya janyo filo ya rungume yana me tuna lallausan jikin Basma tare da kamshinta, kanta ya soma sanin wacece mace, don haka baya wasa da ita. Ma'ana baya son abinsa zai sosa ranta, nashi ganin tafi dukkan wata mace a bayan kasa.Cikin kawana 2 duk wani abu da lefen ke bukata ya kammalu, hatta dinkunan.Ya jinjinawa Anty Nana, don ta tsaya tsayindaka don ganin komai ya hadu.Sajan Sani ne ya ja motar zuwa Garkosukadauki wasu daga dangin mahaifinsa, sannan suka nufi kauyan su Maigari.Gidan Maigari suka sauka, sun ci sun sha sannan suka kuma dunguma zuwa gidan Amarya.¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤­¤¤¤¤Ni ina zaunebutu- butu gidin murhu ina yiwa Hinduwa dimamen tuwo, ga danta a bayana yana ta kuka hancinsa dam da majina, sai muka ji tsayuwar motoci.Babana ya fito ya tare su tare da yi musu sannu da zuwa.Sajan ya shaida ma Baba cewa lefena sukakawo, tabarma Baba ya amso nan makotanmu shi da kanshi ya shigo ya same su tsattsayemutan gidan sai kallonsusuke yi.Baba Gaje ce ma ta zo tana baje jayayan hakoranta tana cewa,"Sannunku bayin Allah, daga ina?"Sai kuma ta hango matan Maigari nan taketa nufi gurin su tana

Please Login or Register in order to submit comment