Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

cewa,"Lafiya?"A'a wai na ce lafiya?"Kafin su yi magana Baba ya shigo da tabarma nan suka amsa suka shimfida suka zauna
19.Ya ce,"Gaje kawo ma baki ruwa."Da yake bata san dalilin zuwan su ba, nan ta nufi dakin Jama'a don aron kwanon sha, sbd Baba Gaje dai bata da abin kanta.Bayan ta kawo musu ne ta nufo inda ni ke ta zubamin rankwashi iya karfinta har sai da na gigice tare da cewa,"Tashi a nan uwar kallon tsiyakada ki sa su amai da wannan warin naki."Na mike na nufi cikin daki." Daga ciki ina jin lkcn da matan suka shaida ma su Baba Gaje cewa lefen Jidda suka kawo. Gaje ta fiddo da dukkan idanunta waje tareda cewa," Wacece me wannan sunan, kunanufin Kuluwa?"Suka ce,"Eh."Ta ce,"Kunyi 6atan kai, ina ga dai Kuluwar gidan Me jakai ce."Matan Maigari suka ce"Ta nan gidan ce ba 6atan kai muka yi ba.",Da saurita iso dakin ta janyo ni zuwa gabbansi."Kun ga fa irin tamu Kuluwar, wane mahaukaci ne zai ce yana sonta?Koko Birni suna matsalar Kuluwa ne ba su da masu sunan.
20.Baba ya yi tsaki sannan ya ce ma bakin "Toan gode muku."Matan Maigari tare da sauran bayin Allah da suka zo tare dai mamaki ya hana kowa magana.Suka mike suka ce,"To su daikan za su tafi."Baba ya kawo kudi ya ba su ya ce,"Ga tukuici."Suka ce ba za su kar6a ba, ya ce,"Su amsa ai haka ake yi, sannan suka amsa.Suna fita nan fa Baba Gaje Faifan bala'i wato ita muguwa ce har da za a dinga 6oyemata abu?"Lallai kuwa za a ja da ita.Yau kam sai ta ji dalilin da za a 6oye mata auran Kuluwa, ko ba ita ce ta haife ta ba ai ita ce taci kashinta ta kuma ci fitsarinta. Saiyau naga fushin Baba inda ya ce,"Karya ki ke Gaje!"Ya bugi kirjinshi "Ni nenan na ci kashin Jidda na ci fitsarinta, ke tauye ta ki ka yi tare da bautar da ita kin manta ne?"Ta ce,"Haka ka ce?""Eh,na fada."In ji Baba.Ta rasa me zata ce, sai ta zari mayafinta ta yi gidan Dija.Tana shiga tarushe da kuka tamkar waddaaka ce mata uwarta ta mutu.Dija ta taso tana sallallami, tana fadin."Kawalli me ya faru?"Cikin kuka riris take sanar da Dija cewa,"Ashe batun auran Kuluwa gaske ne?"Dija ta dafa kirje tare da cewa,"Kai haba?"Gaje ta ce,"Wallahi kuwa, ga lefe can an kawo Adaka ce kusan guda 6 ban ma ta6a ganin irin ta ba."Dija ta ce,"Wanene kuwa mijin?"
21.Gaje ta ce,"Ina zansani?Ni dai ba ruwana da harkar su kayan su ma ba dai dakina ba, kuma ko zan tafi tsirara ba dai su zauna lafiya da mijin ba."Dija tasa hannu ta dafe mata baki tare da cewa,"To sarkin shirme an ce miki ana fadane, batun ki ce ba ruwanki da biki bai ma taso ba, kin san halin kauyan nan ba su iya tsegumi ba.Yanzun a zaga gari da ke ace kina bakin ciki, yi kokari ki danne in yaso 'yan bori na sun ishe su.Za mu sa su turo musu Aljannu su hana su zaman lafiya,ko ya dinga ganinta a Dodo kin gani dole neya sako ta."Gaje ta ce,"Kin kawo shawara, sai dai Allahyasa na iya dannewa, in ga wannan Bakin cikin."Dija ta ce,"Za ki iya mana muje gidan yanun sai ki nuna cewa kin zo ne ki gaya min mu zo muga kaya daga nan sai ki aika duk Jama'a su zo su gani, ki nuna murnarki ki danne komai."Sai ga su sun dawo kafin su dawo ma gidanya soma cika nan kuma aka rasa yanda za a bude akwatuna.Sai da aka aika gidan Maigari sannan aka zo aka bude.Ba Baba Gaje ba, hatta Dija ta ji bakin ciki kayan, gashi matan Maigari sun dawo su ne ke daga kayan saboda sata, dankunne da sarkan ma ba su bari kowa ya ta6a ba, sun dai nuna suka ce daham ne dashi za sutafi.Cikin abin da bai fi sa'a biyar ba lbrn kayanaurena ya zaga har makotan kauyan sun soma samun lbr.Wasu da yawa da yawa in za su yi kwatancena kucakar gidan Wanzamai sukece min, shi yasa ba a sha wuya gurin gane ni ba.Dija da Baba Gaje cikin daki suka tara ni sai na gaya musu wanene mijin, na dinga rantsuwa kan cewani ban san shi ba............
[29/09 11:22 am] Inna👬👫: 21.Hinduwa kuwa kuka ta kwana yi wai Baba ya samo min miji a birni ita ya k'i samo mata.Hakan ya k'ara d'aga hankalin Baba Gaje dama akwatunan shagonsa suke kwana ta ce d'akinta ba guri. Sauran matan gida kuwa suna tsoranta.Matar Yaya Auwalu ma har da had'a ni da Allah wai in fad'a mata ko wanene mijin, wallahi ba zata sanar da kowa ba, na ce nima nan bn san shi ba, k'ila ma nakashsshe ne, ta ce haba?"Na ce Allah to in ba haka ba wa ki ka ga zaya aure ni?Nan kuwa matar Auwalu ta je ta sanar da su Baba Gaje cewa mijin nawa nakashasshe ne, wai ta lalla6a ni na gaya mata.Nan kuwa zance ya shiga yad'a gari, kai wasu ma har cewa suka yi K'ila dai irin 'yanshan jinin nan ne da yake ana cewa suna yin amfanin da Mahaukata, to wai ya ganniya zata Mahaukaciya ce.Babana ya tafi ya sanar da dangin mahaifiyata ya ce da wan mahaifiyata ya dace su zo don kula da kayan aurena da aka kawo, ya dawo kamar yau washe garinsuka zo."A lkcn Baba ya 6ulo da shagonsa ta cikin gida aka kulle k'ofar waje.Nan dangin mahaifiyata suka zauna, hakanya dad'a k'ona ran Baba Gaje don dai Dija tana tausarta."A na sauran kwana 3 daurin aure Baba Jummalata tsafe min kai, ni kaina na tsorata da irin kwarkwatar da ke zuba dagakaina, kalkashin suka sa suka wanke min kaina sai naji tamkar an cire min kayan nauyin nedaga kan nawa.Ana saura kwana 2 daurin aure Baba yaje suka sayo min kayan d'aki, ranar ce kuma aka saka ni a lalle.23.Gidan k'anwar su Babanmu muke zaman lallan, itama a tsorace ta amshe mu don duk 'yan gefen Baba Gaje ne. Kawaye kuwa har da wadanda ba su ta6a min magana ba, duk sun zo sun shiga bikina. Ban san abokan ango ba bare in dago ko wanene Angon nawa, komai da Angawaye za su baiwa Amare daga gidan Maigari akekawo shi.An saba kajin alibidi guda 2 ake kawowa, sai ga nawa guda 10. Kai komai nawa ya fita daban, ana gobe daurin aure mijin nawa yaaiko da buhunan shinkafa 'yar Gwamnati da Rago tikeke, tun lkcn aka yanka shi aka shiga suya, miya aka yi ranardaurin aure da safe kuma tyn Asubahi aka girka shinkafa.Wani abin alfahari ba a ta6a yin wani taro a k'auyanmu kamar na aurena ba, ko lkcn nadin Sauratar Maigari taron bai kai wannnan ba.Motoci daga birni 'yan daurin aure ga su nan.Bayan an daura ne kuma aka shiga cin abinci, suma angawayan sun zo da abincin cikin wani d'an abu ga kuma lemon kwali da na roba.Suka yi ta ba Jama'a kowa sai sambarka dahamdala, mata kuwa ba na kauyan namu ba hatta da na wasu mak'otada kauyan namu sun lodi abinci.Sai dafawaake ana ba Jama'a, ku ce min ina Baba Gaje lkcn???24.Tana nan daki ta kasa fitowa don damuwa,kawayan ta suna tausarta, in sun fito waje kuma suyita yi mata dariya tare da cin abincinsu gamida kaiwa gidajansu.Dangin uwa ba su da na 2, sune suka tsayatsayin daka a bikin matan gida ma in tana d'aki su fito suma susa hannu in kuma ta fito sai su koma daki.Mutanan k'auyen mu ba su girgiza ba sai da aka gama d'aurin aure suka ga wanene Ango.#MuhammaduBello­ Tahir,yana sanye da shadda danya ,mai ruwan k'asa 'yar ciki da malun-malun, ya murza hula Minsta itama mai kalar shaddar Haka nan takaliminshi duk in da ya ratsa k'amshine ke tashi.Na ya durkusa gaban su Baba wanda shima ya yi wankan farar shadda malun-malun aska tara itama daga Angon nawa ya kawo masa, ya gaishesu Baba ya gabatar da shi gurin abokansa da wan Mahaifiyata, da kuma sauran 'yan uwansa.Duk sun sha mamaki, da kyar suke iya furta Allah ya sanya alheri.Shi kuwa nanya cika su da kudi, shi da su Ado suka yi masa rakiya zuwa cikin gidanmu don gaida dangin mahaifiyata.Kafin su karaso tuni lbr ya iso cewa ga Angon nan shigowa, tuni mata suka shiga baza idanu don ganin wanene Angon.Tsohon ne ko nakashasshenne??"25.Lokacin nima ina zaune cikin d'akin da dangin mahaifiyata suke zaune, sanye nake cikin leshi ruwan d'orawa na rufa gyale fari, ni kaina samun kaina da faduwar gaba lkcn da Sayyada 'yar wan mahaifiyata ta shigo tana cewa wallahi ga Angon ya shigo, mutane suka bisu da kallo ga Marka har cikin gida.Baba Gaje ma tana d'aki hankalinta a tashe son take ta gani wanene Angon?"Suka yi sallama k'ofar dakin da muke, numfashina ya tsaya cak lkcn da na ji k'amshin turaran dan birni, ban san lkcn dana yaye gyalen daga fuskata ba ina kallon su.Su uku tsugunne shi da Ado da Sama'ila mijin Binto, idanuna suna tambayar shi cewa shi ne Angon?"Murmushi ya jefa min lkcn da suka soma gaida 'yan dakin.Ado ya ce,"Ga ma Amaryar tamu ai."Na sake rufe fuska da sauri wasu hawaye ne farin ciki suka shiga bin kumatuna.Ni Kuluwa ni ce matar dan birni, suma ya zube musu kudi sai godiya suke yi tare da shi masa albarka.Al'ajabi dai ya cika su. Baba Gaje kuwa kasa magana tayi don tsabar firgita, lkcn da Ado ya nuna mata Angon. Ba ta sanme suke cewa baita bata san ma ya aje kudu sun fita ba, sai da Dija ta girgiza ta sannan ta dawo cikin hayyacinta.Yana fitowa su Hinduwa dama sun ja tungasu da su Laminde suna ta musu kan cewa ko dai Ado ne mijin, don haka suna fitowa Talatu ta ce da Sama'ila."Sama'ila Ado ne Angon?"Tare da Ado suka hada baki gurin cewa,"Ga shi nan."Suka nuna dan birni.Shi kuwa ya dube su tare da cewa da su."Sannunku."Ado ya ce da shi."Yayan Amarya ne."Nan suma ya ciro kudi ya ba su.Cikin sanyin jiki suka amsa zukatansu nazogi,babu kamar Hinde wadda ta kura ma Angon idanu, so take dole sai ta gano makusa a tare dashi amma bata gani ba, don haka ta ja tsaki tare da cewa.""K'ila madan shan jini ne, ban da haka wanene zayakula wannan K'azamar..26.Bayan fitar su haka Jama'a suke ta fadin nayi sa'ar miji, gashi d'an ubansu ga kuma kudi. Ni dai ina aune cikin matsanancin farin ciki ina yi wa Allah godiya. An ce Amarya ko ta buzuzu ce ranar aurenta sai tayi kyau.Ni kaina na yarda da haka, ga kuma k'amshin na musamman sbd turakun da aka fesa min.Kusan k'arfe 2 aka soma jidar kayana zuwagidan dan birni mai Masallaci, nan fa Baba Gaje abin duniya ya bi ya dagule mata dama ko kan kaya sai da suka yi da Baba, ta ce na Hinduwa bai kai nawa kyau ba, gashi ni gadona mai rumfan lamba wanne.Baba ya ce mata lkcn auran Hinduwa bakya ma sako ni cikin lamuranki, sbd ban dasgi kada ki manta gona ta na saida nakawomiki rabi da kwatar kudin, ke ce ki ka sayo son ranki, don haka kamar ma ki dame ni."Anyi min jere tsaf kowa ya dawo yana yabawa.Da dare kuwa aka zaga da ni dku dakunan gisan mu wai kannan mahaifina da matansu su ti min fada, kowadai sai dai yace to ayi ta hkr Allah ya bada zaman lafiya.Dakin Baba Gaje nan ne karshe.,Kuka ta saka tana cewa, ta yafe min wai in yi biyayya.Na sani kuka bakin ciki ne ta dai wayance ne daga nan kuma sai muka nufi gidan mijina dama Baba shi ya riga ya yi min dukwata nasiha, abunda nake tunawa kowanelkc cikin nasiharsa ita ce kalmar da ya ce shi ba zaya ta6a yafe min ba in har nayi wani abu da ya 6atawa Bello rai, sai dai in bisa kuskure.Ana ta*wake-wake har muka isa gidan, ankunna fitilu gidan ya yi haske.Wasu manyan fitulu ne masu kwai, gidan Maigari ne kawai da irin su.Aka kai ni dakina inda zamu kwana da kawayena da kuma tsohuwa
27.Shayi da beridi aka dafo mana daga gidan Maigari, nasan bani kadai ba da yawan muyawan mu yau ce rana ta farko da muka soma shan shayi.Da rana suka dafo shinkafa da wake. Binto ta yi min kitso gaba daya aka yi budarkai sannan aka gyara min dakin gami da sharegidan, sannan Jama'a suka watse daga ni sai kawayena.Muna zaune sai ga Anguna sun shigo su uku, shi da Ado da kuma Sama'ila. Suka sayi baki da kudi masu dama, kawayena shi kuma ya raka suka tai jiki yana 6ari, sun samukudi shi kuma ya raka su Ado.Ina zaune ina kallon ko'ina na dakin ashe dai zan ga yau?Ashe zan yi aure?Sallamar shi ce ta dawo da ni daga tunanina.Na amsa ya shigo ya tsaya tsakiyar dakin yana kallon jeren.Murmushin yake yi da alama abin ya bashisha'awa."Jidda wannan shi ne me?"Yanuna jeran da hannu."Kwaba ce da jer.""To wannan gadajan guda 2 fa?""Ga naka, wannan kuma nawa."Ya nufi babban gadonmai runfa wanda ya hi katifa, ya kuma gyara ga labulaye.Ya daga labulan yana kallon gadon, ya kalle ni."Ina zan taka in hau?"Na ce,"Ba a taka komai, hawa zaka yi."
[29/09 11:26 am] Inna👬👫: 28.Ya jingina bayan shi sannan ya dafa hannunwanshi guda 2 ya dare kai.Ya jijjiga gadon sannan ya sauka tare da cewa,"Ashe ya zauna da kyau, a zotana zaya dinga lilo."Ya dawo kusa dani ya zauna, ya jawo leda baka."Nasan kina jin yunwa, kici nama kafin muyi krt ko?"Da sauri na ce,"Na k'oshi." Don na tuno Binto ta ce min wai in ya kawo kaza na ci zai ce in biya shi, ya yi min abinda Sama'ilake mata, koda dai ta ce min duk wasu mata da miji haka suke yi.Yayi-yai na k'i ci, shi kam ya ci tare da wanilemo na kwali ya gama ya ce na yi Isha'i?Na ce,"Eh,na yi."Ya ce,"To in sakko nazauna,shi kuma ya dakko wata ja mai dogon hannu ya dora kan gadon shi ya zuge ta ya ciro jallabiya fara kar da wandonta gajere, ya cire rigar jikinshi ta shadda.......
28.Ya jingina bayan shi sannan ya dafa hannunwanshi guda 2 ya dare kai.Ya jijjiga gadon sannan ya sauka tare da cewa,"Ashe ya zauna da kyau, a zotana zaya dinga lilo."Ya dawo kusa dani ya zauna, ya jawo leda baka."Nasan kina jin yunwa, kici nama kafin muyi krt ko?"Da sauri na ce,"Na k'oshi." Don na tuno Binto ta ce min wai in ya kawo kaza na ci zai ce in biya shi, ya yi min abinda Sama'ilake mata, koda dai ta ce min duk wasu mata da miji haka suke yi.Yayi-yai na k'i ci, shi kam ya ci tare da wanilemo na kwali ya gama ya ce na yi Isha'i?Na ce,"Eh,na yi."Ya ce,"To in sakko nazauna,shi kuma ya dakko wata ja mai dogon hannu ya dora kan gadon shi ya zuge ta ya ciro jallabiya fara kar da wandonta gajere, ya cire rigar jikinshi ta shadda.......
29.Singiletin jikinshi itama fara, na sun kuyar da kaina ban kuma kallonshi ba har ya gama.Ya ciro turare ya feshe dakin tare da ce min an fi so dakin Amarya ya dinga kamshi, cikin akwatunan ki ma akwai turarka kan daki na duba akwatunan akan gadona ta gefe, na ce sai dai da safe ka nuna min su don ni bn san su ba.Ya ce,"To."Ya ce,"Kin san daga yau ni mijinki ne ke kuma matata ce ko?"Na daga kai.""To ya wajaba in san iliminki iyaka inda ki ka tsaya in dora miki kafin nan gaba ki shiga Mkrnt."Na ce,"Ni kasan fa ba wai ina da wani ilimi ba ne.""Amma ki fada min tun farkon yanda baligi zaya yi tsarki har zuwa sallah."Kaina yana kasa ina wasa da yatsan hannuna.""Da farko mutum zaya kama ruwa."Ya ce,"In baya dauke da najasa kenan, kin san ni da tambaya."Na ce,"Meyewannan din?"Ya gyara zama."Kin ta6a yin al'ada?"Na maida kaina kasa na ce,"Eh,amma sau 2 ne kawai."Cikin tsananin kunya da fargaba na fada.""To sanar dani yanda ki ka gyara kanki."Nayi shiru,cikin zuciyata ina cewa,shi kuma dan birni ya soma shige gona da iri.Ya tausasa muryarshi.""Kada ki damu,Musulunci ya yarda da tambayoyin da nake miki, kuma bani da ishasshen lkcn da zan miki krt mai yawa, sati daya kawai zan yi na koma, sannan kuma zan dauki lkc ban dawo ba.
30.Na ce,"To ni dai lkcn da na ga abin sai na tsorata, kamar in sanar da Baba sai kuma sai kumana kasa sbd kunya,shine naje na fada ma Binto, ita ce ta bani wani yankin kyalle ta fada min yanda zan yi, kuma cikin kwana 3n da na dauka ina fama da abin gurin Binto nake zuwa ina gyara jikina da na gama kuma ita ce ta sanar dani kalar wankan da zan yi."Yagyada kai alamar gamsuwa.""Yauwa ko za ki sanar da ni yanda ki ka yi wankan?"Nasakaina cikin gwiwata.""Me yasa ya ka ke sonka sani?"Da sauri ya ce,"Saboda in ji in ba ki sani ba in sanar dake, domin tsarki bayan Imanin dukkan Musulmi to naga shine yasan abinda zaya gyara Ibadarsa."Nayi ajiyar zuciya, sannan na ce da shi."Ni dai haka ta ce min, in yi niyyar wankan da farko sannan sai na daura alwala bayanna kama ruwa, wai so dai-dai."Na kalle shi don jin ko nayi dai-dai."Ya ce,"Ina jin ki."Na ci gaba da cewa,"Wai sai na wanke 6arin damana sannan haguna, a takaice dai in wanke dukkan jikina ya kasance ko'ina ya samu ruwa har gashin kaina, to haka nayi har mata ce min wai Sama'ila ya ce in mutum ya yiwanka mai kyau zaya iya yin sallah ba tare da ya sake yin wata alwala ba?""Haka ne,ita Sallar ya ya ki ke yinta?"Na yi dan murmushi."Haba dai, tun tuni fa na iya Sallah tun ina 'yar kankunuwa Baba ya ke koya min.""Na sani,ina so ne kawai in ji."
Nafada mashi yadda akeyi,sai dai na gaya mishi cewa, lokacin da nake zuwa makaranta izifidaya na iya dana daina kuma sai duk sai na manta wasu. Yace badamuwa zaki shigamakaranta dolema, sallarki daidai ce sai dai bakya yin zakiri yayin sallarki, yana da kyau ki dinga yin zikirin Allah yanada falala,Allah da kanshi cikin (suratul Bakara) yace," ku anbaceni zan anbaceku, ku gode mini kada ku butulce mini." wata surar kuma yace " yakuwadanda suka yi imani, ku ambaci Allah anbato mai yawa. " Akwai surori da dama da sukayi bayani kan falalar zikiri, manzon Allah (S.A.W) ya bada misalin mai ambatonAllah da marar ambaton Allah kamar matacce ne da rayayye." Batun ya shigeni sosai, nasauke ajiyar zuciya nace dashi"zanso inyi, amma ban iya ba kozaka koya min?32. "kwarai kuwa, amma mastalar dai itacebaki iya karatu kona hausa ba, bare in koya miki a rubuce. Sai dai na sanar dake me saukin fadi a lokacin sallah," Nace "TO. Yace bari in fara miki daga Ruku'u don ta bayan kabbarar harama tanada tsawo, wannan sai a hankali kya rike " inkinyi Ruku'u sai kice ( subhanakalla humma rabbana wabi hamdika, Allahumma gafirlii)suna da dama, amma bari in barki nan inkin dago sai kice ( sami'allahu liman hamidahu, Rabbana walakal hamdu, handan kasiran dayyiban mubarakan fihi) shima mubar wannan donki rikeko?" Nace"Eh. Gamamakin shi sai yaji duk na fada, nace to sujjadafa? Yace "Subhana Rabbiyal a'ala sau uku. Sai zaman tsakanin sujjadar farko data biyu sai kice, "Rabbigifirli! Rabbigifirli!! Ko kice ( Allahummagfirli, warahamnii, wahdini wajburni wa'afini, warzukuni, warfa'ani), kirike wadannan sauran kafin na tafi zan koya mikisu Insha Allahu, koma zaki gyara." yakai karshen maganan yana hamma, nace "to. Nagode"yace, tashi ki saka kayan baccinki ki kwanta nayi shiru ina tunananin ai shima baccin harda kayansa? Yace kin jini? Namike ina ina made tabarma nace" Ai bani dasu" yanufo akwatin ya budesu, ya ciro wasu riguna guda biyu miko min, na amsa sai dai ina tunanin yadda zan sa agabansa, tankar ya fahimta ya dauki buta ya fita, kafin ya dawo tuni harna canza na hau gadona na kwanta. Ya tsaya gaban gadona sai da safe kenan? Nace eh, ya nufigadonsa yana cewa kinyi addu'a ko?' nace yaya zanyi." yasake matsowa daf dani
[30/09 2:08 pm] Inna👬👫: 30.Na ce,"To ni dai lkcn da na ga abin sai na tsorata, kamar in sanar da Baba sai kuma sai kumana kasa sbd kunya,shine naje na fada ma Binto, ita ce ta bani wani yankin kyalle ta fada min yanda zan yi, kuma cikin kwana 3n da na dauka ina fama da abin gurin Binto nake zuwa ina gyara jikina da na gama kuma ita ce ta sanar dani kalar wankan da zan yi."Yagyada kai alamar gamsuwa.""Yauwa ko za ki sanar da ni yanda ki ka yi wankan?"Nasakaina cikin gwiwata.""Me yasa ya ka ke sonka sani?"Da sauri ya ce,"Saboda in ji in ba ki sani ba in sanar dake, domin tsarki bayan Imanin dukkan Musulmi to naga shine yasan abinda zaya gyara Ibadarsa."Nayi ajiyar zuciya, sannan na ce da shi."Ni dai haka ta ce min, in yi niyyar wankan da farko sannan sai na daura alwala bayanna kama ruwa, wai so dai-dai."Na kalle shi don jin ko nayi dai-dai."Ya ce,"Ina jin ki."Na ci gaba da cewa,"Wai sai na wanke 6arin damana sannan haguna, a takaice dai in wanke dukkan jikina ya kasance ko'ina ya samu ruwa har gashin kaina, to haka nayi har mata ce min wai Sama'ila ya ce in mutum ya yiwanka mai kyau zaya iya yin sallah ba tare da ya sake yin wata alwala ba?""
31......Haka ne,ita Sallar ya ya ki ke yinta?"Na yi dan murmushi."Haba dai, tun tuni fa na iya Sallah tun ina 'yar kankunuwa Baba ya ke koya min.""Na sani,ina so ne kawai in ji."Nafada mashi yadda akeyi,sai dai na gaya mishi cewa, lokacin da nake zuwa makaranta izifidaya na iya dana daina kuma sai duk sai na manta wasu. Yace badamuwa zaki shigamakaranta dolema, sallarki daidai ce sai dai bakya yin zakiri yayin sallarki, yana da kyau ki dinga yin zikirin Allah yanada falala,Allah da kanshi cikin (suratul Bakara) yace," ku anbaceni zan anbaceku, ku gode mini kada ku butulce mini." wata surar kuma yace " yakuwadanda suka yi imani, ku ambaci Allah anbato mai yawa. " Akwai surori da dama da sukayi bayani kan falalar zikiri, manzon Allah (S.A.W) ya bada misalin mai ambatonAllah da marar ambaton Allah kamar matacce ne da rayayye." Batun ya shigeni sosai, nasauke ajiyar zuciya nace dashi"zanso inyi, amma ban iya ba kozaka koya min?
[30/09 2:09 pm] Inna👬👫: 32. "kwarai kuwa, amma mastalar dai itacebaki iya karatu kona hausa ba, bare in koya miki a rubuce. Sai dai na sanar dake me saukin fadi a lokacin sallah," Nace "TO. Yace bari in fara miki daga Ruku'u don ta bayan kabbarar harama tanada tsawo, wannan sai a hankali kya rike " inkinyi Ruku'u sai kice ( subhanakalla humma rabbana wabi hamdika, Allahumma gafirlii)suna da dama, amma bari in barki nan inkin dago sai kice ( sami'allahu liman hamidahu, Rabbana walakal hamdu, handan kasiran dayyiban mubarakan fihi) shima mubar wannan donki rikeko?" Nace"Eh. Gamamakin shi sai yaji duk na fada, nace to sujjadafa? Yace "Subhana Rabbiyal a'ala sau uku. Sai zaman tsakanin sujjadar farko data biyu sai kice, "Rabbigifirli! Rabbigifirli!! Ko kice ( Allahummagfirli, warahamnii, wahdini wajburni wa'afini, warzukuni, warfa'ani), kirike wadannan sauran kafin na tafi zan koya mikisu Insha Allahu, koma zaki gyara." yakai karshen maganan yana hamma, nace "to. Nagode"yace, tashi ki saka kayan baccinki ki kwanta nayi shiru ina tunananin ai shima baccin harda kayansa? Yace kin jini? Namike ina ina made tabarma nace" Ai bani dasu" yanufo akwatin ya budesu, ya ciro wasu riguna guda biyu miko min, na amsa sai dai ina tunanin yadda zan sa agabansa, tankar ya fahimta ya dauki buta ya fita, kafin ya dawo tuni harna canza na hau gadona na kwanta. Ya tsaya gaban gadona sai da safe kenan? Nace eh, ya nufigadonsa yana cewa kinyi addu'a ko?' nace yaya zanyi." yasake matsowa daf dani
33."Kin dai yi addu'a ko?" Na ce,"Ya ya zan yi?" Ya sake matsowadaf da ni."Ki karanta KULHUWALLU, da FALAKI da NASI, cikin tafukan hannunki ki shafe duk jikinki, kiyi haka har sau 3. Sannan ki karanta Ayatul Kursiyyu har zuwa karshenta. Duk wanda ya

Please Login or Register in order to submit comment