Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kafa wlh sai ta ciremin kayan nan idan bakyaso ni Ina da wayanda zan bawa masu mutunci Kuma wlh daga yau Kar na sake na sake ganin ta a gidanan tunda tace ban isa na rabaku ba sai nagani ta tsaya a matsayinta na bazawara ta nemo zawara Yan uwanta ta cigaba da hulda dasu tana aron kayansu"

"Salisu yau ni kake wa cin mutunci sabida nazo gidanka"?

"Anyi miki cin mutunci idan kin zuciya ki rabu da Aisha Kar na sake ganin kafarki a gidanan dan tunda har ta fara d'aukar kayanta masu tsada tana baki nasan zata iya Jin maganarki ki mata hudubar tsiya"

"Salis dan Allah ka bari haka da kakeyi bai dace ba daga aron kayana bai dace ka mata irin wanan cin mutuncin ba haba salis ka manta wacce Luba ne"?


"Wacce ita wato dan Kinga ban tuje kayan daga jikinta ba ko wlh kafin na fita waje na dawo ta tabbata ta cire kayan nan ta Kuma bar gidanan idan Kuma kin zabe ta a kaina sai ki bita ku tafi amma matsawar a karkashina kike wlh sai kin rabu da ita"

Ya juya fuuu yayi waje.

Luba ta bishi da ido hawaye na gudu a fuskarta na Mik'e tsaye Ina k'ok'arin Magana ta daga min hannu ta Shiga d'akin yarana na bita Ina bata hakuri.

Ta fashe da kuka tare da zuge zip din rigar ta cire rigar ta cire sarka da dan kunnen duk abinda take kuka take sosai nima na fara kukan Ina cigaba da bata hakuri wlh a rayuwata bana san wulakanci Salis ya wulakanta Luba bai kyauta ba tana gama cirewa ta d'auko zanin wanka dake rataye a kan k'ofar bandaki ta daura duk abinan bata cemin komai ba ta d'auko hijabin dake kan gado tayi hanyar waje tana cigaba da shesheka "Dan Allah Luba kiyi hakuri dan girman Allah wlh ban taba tunanin Salis zai iya min haka ba wlh ko da Wasa ban tab'a fada masa kina aron kayana ba"

Ta juyo da jajjayen idonta ta fara nuna kanta "har ni Salis zai yiwa irin wanan cin mutuncin dan na ari kayanki duk a tunanina yanda na d'auke ki haka Kika d'aukeni wlh ban daukeki kawa ba tamkar Yar uwata nake jinki a raina yau akan abun duniya salis ya murza idonsa yamin cin mutuncin nan ba komai Aisha insha Allahu bazai Kara ganin kafata a gidansa ba wlh ba'ayi namijin daya Isa ya rabani dake ba amma tunda shi ya rabamu shikenan idan naje gida Zan aiko miki sauran kayanki da wanan hijabin nagode"

Tayi waje da sauri tana toshe bakinta.

Na zube a kasa ma fashe da kuka a lokacin wlh har wani daci nake ji a bakina sabida b'acin rai bansan mai ya hau Kan salis yayi mata irin wanan cin mutunci ba Ina laifi ma ya bari ta tafi inyaso duk sai yamin gargadin da zaimin amma irin Wanan cin mutunci Kamar Mai jiran kiris.

A haka ya shigo d'akin ya Sameni Ina kuka

"Kinsan wlh kina bani mamaki Aisha yanzu ke kinyimin adalci kenan na siya miki Kaya Mai tsada ki dauka ki bawa yarinyar da bata San mutuncin kanta ba ta kashe aurenta dan kawai mijinta bashida kudi dan na koreta kike wanan kukan Kamar tare aka haifoki da ita ko idan kun rabu rayuwarki ta tsaya"?

"Haba salis wlh baka kyauta ba dan Adam ba'a abin wulakantawa bane har akan abin duniya ka wulakanta Luba haka Haba Salis ka manta irin hidimar da Luba tayi dani a bikina da yan uwanta tsakani da Allah dan ta nemi aron abu a wajena na bata shine zaka mata haka Salis bansan ka da rowa ba wlh baka kyauta ba arzikin nan naga Allah ne ya baka abaya baka dashi sai yanzu dan Allah ya ma niima baka San wasu su mora wlh baka kyauta min ba"

Tunda na fara magana kallona kawai yake Koda na gama sai cewa yayi "toh yanzu so kike naje gidansu na bata hakuri na maida mata kayan?

"Ni ba haka nace ba wulakanci da ka mata ne banji dadi ba"

"Allah ya kyauta"

Yace tare da mik'ewa ya bar d'akin.

A ranar ban Kara walwala ba dan wlh abinda Salis ya yiwa Luba ya dameni.

Gashi ba waya a lokacin ballantana na kirata na sake bata hakuri kwana uku a tsakani da yamma sai ga wani karamin kanin luba ya shigo da niki nikin leda wai inji Luba tace a kawomin.

Salis na zaune a palo yace masa ya kawo ya gani bakinsa sake cikin mamaki.

Nidai ban motsa ba Salis ya fara fito da duka kayana da Luba ta tab'a ara a wajena Yana ikon Allah "Ai bansan ku biyu nake siyawa Kaya ba Aisha dama kayan duk da nake siya miki Luba kike bawa ni Ina iya k'ok'arina dan naga na faranta miki amma kina bawa kawarki dan baki san zafin kudi ba toh yayi kyau"

"Kai mayar mata da kayan kace ba'aso"

Yacewa kanin Luba ya kuwa dauka ya juya ya fita nikuwa hawaye ya hau wanke min fuska.

A takaice sai da muka tafi sati biyu Salis ya kasa gane kaina daga baya san damuwata nasani tuni ya damu ya hau Kuma rarrashina Yana cemin abinda nayi bai dace ba nace Masa ni a rayuwa bazan iya wulakanci ba bazaa iya tambayata abu nace babu ba wlh ban iya Kuma banaso ya rabani da luba dan banaso taga dan dagasken da na samu niima nida mijina muka wulakanta ta.

Ya saki murmushi Yana toh shikenan bazai kara shiga tsakanina da Luba ba amma shi dai Luba alakata da ita bai ga alheri ba.

Baa san ransa ba ya kawo ido ya zuba min yamin Allah ya isa idan na sake bata kayan daya siya da kudinsa sai dai na siya da kudina na Bata.

Nidai ban damu ba tunda na samu bai datse kawancen mu ba,da kaina na shirya naje gidansu ban sameta ba haka na zauna na jirata ko da ta dawo ta gani sai ta hade rai "ke da mijinki yace ki rabu dani mai Kika zo nema"?

"Dan Allah komai ya wuce Luba kiyi hakuri da abunda ya faru shima yace kiyi hakuri"

Hmm kawai tace bata Kara cemin komai ba nidai nayita janta da hira tana bani amsa sama sama da nazo tafiya ta rakani na bata kyautar kudi.

A yanda na sake dawo da Luba rayuwata kenan.

Amma ta daina aron kayana sai dai ta tambayeni kudi na bata a haka cikina ya isa haihuwa na haifi da namiji aka sa Masa Aliyu arziki Kamar karawa Salis ake yi dan dagaske bansani ba ko lokacin banida wasu burika ne Rabin kudina Luba nake bawa burina ta sake samun miji tayi aure, dan Hamza yayi aurensa Salis ya bashi jari ya bud'e shago a lokacin kafin yayi Aure ma Salis ya sakoni gaba akan na tsara Luba ta koma dakinta wlh zai bata jari da kuwa nayiwa luba maganar kamar ta dakeni akan ko a lahira taga Hamza guduwa zatayi.

A haka muka fara shirye shiryen komawa sabon gidan da aka kwashi shekara uku ana ginawa wlh a lokacin babu Kamar gidan a unguwarmu gida ne Salis ya narka masa mugun kudi,daidai da kayan cikin gidan duk na waje ne.

Duk tsofafin kayana da Suma da kyaunsu haka yace na bada su na kuwa loda a mota aka kaiwa mahaifiyata ba abinda muka dauka a gidan komai sabone.

Har Kaya duk sababi ya mana Salis ne ma ya dan hada Walimar tariya nima na danyi gaya Luba kuwa itace Kan gaba tace har mafarkin gidana take sabida haduwarsa kullum maganarta a Ina zata samo miji Mai kudi irin Salis ai ita tama Raina kudin wanan Alhaji da yake santa.

A ranar da muka tare da yawa Yan uwa sun zo sun Kuma kwana dan duk Wanda yazo sai yaji kamar bazai tafi ba a ranar itama Luba ta kwana a gidan dayake gidan sama da kasa ne sama ne bangaren Salis kasan kuwa duk nawane ba wanda ya hau sama duk muka baje kolinmu a kasa dan wlh Ina balain san mutane yaran yayana suma duk a gidan suka kwana sai saintyn gidan suke Ina dariya Khadija da muhasim suma Suka ce ba abinda zai Mai dasu gidansu sun samu gida.

Wlh banki ma duk Yaya ya barmin su ba amma nasan bazai tab'a barinsu ba yace idan sunyi hutu zasu ringa zuwar min hutu wanan kenan.

Shekara daya a tsakani wani mugun iftilai ya fada mana da bazamu taba mantawa ba muhasim aka Kai gida bakinta a karkace wuyanta baya tsayawa Koda aka zo aka gayamin hankalina a balain tashe nayi gidan yayana Ina zuwa naga gidan a cike taf.

Koda na ratsa mutane na shiga ciki a kwance na tarar da muhasim a tsakiyar kafet aunty Mami idonta yayi luhu luhu Yaya mustapha kuwa jikinsa rawa kawai yake.

Na zube agaban muhasim da bakinta ke dalalan yawu tana binmu da Ido wuyanta shima a karkace.

Cikin tashin hankali nace "Yaya Mai ya sameta haka"?

"Wlh bamu sani ba daga makarantarsu aka kawo Mana ita akan an ganta a yashe a bakin gate.

"Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun"

"Mu kaita asibiti mana mai ya sameta haka"

Duk hankalinsu bai Kai su kaita asibiti ba sai da na nemo mota muka dunguzuma muka tafi asibiti.


Present.

Alhaji Salis

Tunda ya tafi massallaci bai dawo gidan ba sai da safe har wani zazzabi yaji yana neman rufeshi.

Yana shigowa suka hada Ido da luba dake karkada kafa ya d'auke kansa tare da nufar d'akin Aisha


Yana Jin Luba tana maganganu kasa kasa ko ta kanta bai bi ba ya tura k'ofar Aisha a hankali sallamar da yayi ta amsa ko dagowa batayi ta kalleshi ba ta maida idonta ta rufe.

Ya zauna a gefen gadon ya zuba mata Ido tsawon minti biyar kafin yace "Aisha dan Allah dan annabi ki tashi muyi magana wlh nagaji da irin zaman da muke yi dake Allah fa muna masa laifi ya yafe Mana haba Mana"

Sai a lokacin ta bud'e idonta ta tashi zaune tana "Wani abu ne ya faru"?


MG'S SKINCARE


Dame akafiki yar uwata?
Kyan fatar ko iya gyaran fatar?
Ina riba g macenda t Maida kanta sauran mata?
Shin haryenzu labarinmu kikeji ko kike bayarwa?
Hajiyata miye matsalar?
Fatar takice abun se lahaula?
Kingwada kingwada harkinsare?
Tsakanida Allah yaushe daren yayi balle wayewar garin?

Inbakida labarin MG'S wacce tasanki tasansu,
Gawurtaccen Kuma shahararren kamfanin gyaran fatane,duk lalacewar jiki,duk hautsinewar fata,duk yenda jikinki yazama abun kunya gareki, Ina tallata maki me gabadaya,

Muntarkato,munwarwaro,munqullo duk wani Abu daze maidaki wanke hannu kataba mun qara a cikin kayayyakinmu,muncire,muntsife,munfidda,mun tantance mun hadamaku wasu irin hadaddun lafiyayyun kaya masu masifar goge fata,wallahi duk fitinar fatarki inshallah,kinzo bustop,kisiya kiyikyanda ko mace,kan juyo ta waiwayo ta dubi halittar Allah,

Ga product din kamar hka,
Sabulu 4500

Mg's beauty kit
Karamin kit 12k
Body soap
Facial soap
Body cream
Face cream
Glow oil
Pink lip balm

Flawless skin beauty kit
Babban kit 20k
Body soap
Facial soap
Body cream
Face cream
Scrub
Glow oil
Pink lip balm

Note kowanne d kalanshi nd yanayin packaging dinma aren't the same,

Tsakanida Allah kigafa
Duk wannan garabasar Kuma kinazaune hba taso a dama dake a harkar yar uwata,

Ayi hakuri da sauyin farashi komi yatashine muma b hka mukasoba
Chat:08062991549,07046881166,07067210195,
Call,+2348064532391*NI DA KISHIYOYINA*

*NA SADNAF*

*E.W.F*


*PAID BOOK*




*Page 6*

Alhaji Salis


"Aisha kin hanani samun nutsuwar zuciya na rokeki nayi miki kuka na sa mahaifiyata ta rokeki duk wayanda kike Jin kunyarsu na hadaki dasu Abba da Umma ma sun baki hakuri akan laifin da na miki Aisha kin k'i ki hakura tsawon shekarun nan Aisha karki manta fa bawa bai isa ya tsallaka kaddararsa ba rabo ne tsakanin nida Luba shiyasa Allah ya hukunta na aureta"

"Toh kaji na ce ma wani abune yanzu"?

"Haba Aisha kafin na auri Luba ai ba haka mu ke zaune da ke ba yanzu kiri kiri nake ganin kiyayya ta a idonki"

"Hmmm daga lokacin da ka auro Luba da ka san kawata ce yaci kasan ka tarwatsa duk wata soyaya dake tsakanin mu da yarda har gobe Zan fada da babban murya wlh tallahi zaman yarana nake da hakuri babu digon kaunarka a raina Koda duk mutanen duniya ne zasu hadu su ringa bani hakuri batun Kuma baka da nutswar zuciya ai ba ni na hanaka nutsuwar zuciya ba tunda kana da luba,da kafi so da kauna ai Ina ganin baka da wani matsala abu daya nakeso.na fada ma shine ka ja mata kunne duk da nasan ba iyawa zakayi ba amma dai zan fada ma kace Kar ta kuskura ta Kara tab'a min Nana da na karbi amanarta wlh duk ranar da ta kuskura ta Kara tab'ata a ranar ba ita ba har kai sai na baka mamaki kaga duk abinda kuka min ban tab'a ce muku komai ba wlh ko Ashraf naga tana duka bazan kalli Inda take ba amma idan har ta tab'a min Nana wlh zan baku mamaki Banda kaddara data gifta mana da ba abinda Nana zatayi a gidanan ballantana har a kirata da agola"

Alhaji Salis kasa magana yayi ya zubawa Aisha Ido duk Yana jin kwarin gwiwar daya zo dashi ya sace.

"Aisha auren nida Luba da Hindatu wlh kaddara ce zan sake rantse miki ba wacce nake kauna a cikinsu".

"Hakane kam tsabar kiyaya ma gashi har da yaransu uku uku nifa daka so su da Kar ka so su Salis ba abinda ya shafeni bane bansan dalilin daya sa kake gayamin ba"

"Aisha rashin samun hadin kanki da rashin bani dama yasa zan sake Aure"

Sai ta saki murmushi har hakoranta suka bayyana tana "Allah ya sanya alheri kace su Luba za'a sake samun sabuwar kanwa"

"Abinda Zaki ce kenan Aisha yanzu banida wani mutunci a idonki da zakiyi kishina"?

"Ina mutuncin yake Salis mutunci ai ya dade da zubewa sai zaman ibada kawai kishi kuma ba sai kana san mutum zaka ji kana kishinsa ba ai ni yau banki Allah ya gwada min ranar da zaka shigo min da takardar saki ba"

Zuwa lokacin ran Alhaji Salis ya Kai kololuwa wajen b'aci

Ya mik'e yana " shikenan Aisha idan saki kikeso insha Allahu mutuwa ce zata rabamu ba abinda zai saka na tab'a sakin ki insha Allahu watarana zaki yafemin"

Daga haka ya fice daga d'akin Aisha taja tsaki.

Koda ya fito a bakin k'ofa yaci karo da Luba ba yau ya fara Kama ta tana labe ba ko a d'akin Hindatu yake haka take zuba laben ya zuba mata wani mugun harara Yana "Baki ji dadi ba wlh duk da kin manyanta kin kasa girma Allah ya kyauta"

"Ikon Allah ni na aikeka wajenta ta ma rashin mutunci da zaka zo ka hucce a kaina"

Bai kulata ba yayi waje ko zaman gidan bayaso yayi.

Sai da ya fara Shiga Bangaren yaran duk ya dubasu dan asabar ta Kama ba makaranta ya shafa kan Nana da murmushi Yana tambayarta mai zai taho mata dashi ta hau lissafa masa ya gyada mata kai tare da yin waje.

Yana Jin maganar luba a bayansa akan ga abincinsa can ko kallonta baiyi ba ya shige motarsa ya nufi gidansu.

Bashida inda zai je sama da can gwara ya wuni a wajen hajiyarsa da dai ya zauna a gidan.

Koda ya isa gidan Hajiyar sa bacci take bata tashi ba hakane yasa yayi kwanciyar sa a 3 seater ya nemo lambar Aneesa bugu biyu ta d'auka muryarta kawai data doki kunnensa ya saka shi sakin Ajiyar zuciya har a zuciyarsa yana kaunarta hira suka farayi ya maida kansa kamar Saurayi kalmomin soyayya kuwa ko saurayi albarka har yanzu Yana mamakin yanda akayi Aneesa ke Sansa duk da tazarar dake tsakaninsu.

Sunfi awa suna waya da ita har hajiyar ta farka ta fito ya hadasu suka gaisa hajiya ta musu fatan alheri ta maida Masa wayar tana jinjina auren a ranta da Jin muryar ta ma yarinya ce zata ga yanda Salisu zai yi da su Luba.

A takaice a cikin satin kawun Salis Suka Kai Dubu dari biyar dari uku kudin aure dari biyu sadaki.

Lefe dama Yayar Aneesa zai bawa ta hada dan haka Aneesa tace sunyi magana.

Duk da shiryen shiryen da yake zuciyarsa cike take da mugun fargaba sam baiji zai iya fadawa Luba da Hindatu ba,yasan kuma Aisha bazata tab'a fada musu ba.

Yana ta nazarin yanda zaiyi kafin auren.

Gidansa kullum cikin tashin hankali ake na yau daban na gobe daban.

Ya rasa yanda zaiyi iya wanan kawai inya gani sai ya ringa hararo Ina ga ya auri Aneesa duk da baiji a ransa zai hadasu gida daya ba warewa Aneesa gidanta zaiyi daban.


Past

Aisha

Duk binciken da likitoci sukayi basu gano abinda yasa muhasim bakinta ya karkace wuyanta yak'i tsayawa waje daya ba sun dai gane tana d'auke da ciki wai har na tsawon wata uku"

Aunty Mami har da sumewarta.

Yayana Kuma ya Yanke jiki ya Fadi dan kafafunsa rawa kawai suke.

Tunda nake bamu tab'a ganin tashin hankali irin na ranar ba kuka kuwa har sai da hawayen idona ya kafe ni ba cikin da aka fada yafi daga min hankali ba yanda bakinta ke zubar yawu,kasan raina Kuma inata mamakin garin yaya Muhasim ta samu ciki dan nidai nasan Yaya Yana da balain tsauri.

A asibitin Salis yazo ya same mu shima cikin tashin hankali kasancewarsa likita yasa ya nemi likitan da file din muhasim ke hannunsa akan Karin bayani.

Bazan manta k'ok'arin da Salis yamin ba a lokacin dan babban asibiti aka Kai mu ba karamin kudi ya kashe ba Muhasim ta sha.gwaje gwaje baa san abinda ya sameta ba, yayana har kwantar dashi akayi shi da Aunty mamy dan suna balain ji da muhasim gashi yarinya ba ruwanta duk a cikin yaran tafi su hankali nima kaina nafi kaunarta.

Haka na tsaya akan yayana da matarsa tamkar nima a bani gadon dangi duk da suka ringa zuwa duba mu ba Wanda yasan muhasim nada ciki dan Ina ganin sirrin mu ne banda ma Salis nasan dole yasani ta wajen likitan da sam bazan so ya Sani ba duk da duk zargin da akeyi Kamar fyade dai akayi Mata dama ana rade raden Yan makarantar su mazan baji suke ba sun tab'a raping din wata Yar ajinsu da yake babbar makaranta ce aka rufe case din.

A yanzu haka an saki kudi dan anyi binciike Wanda yayi wa muhasim wanan aika aikan.


Duk uban kudin da ake narkawa dan Muhasim ta samu sauki bamu ga alamar sauki ba sai a wajen Allah a haka dai ake ta siya mata.maganguna masu tsada.

Luba itama ba laifi kullum sai tazo asibitin duba mu tamin mutunci kwarai tunda ta nuna damuwata damuwarta ce.

Da nasiha da waazi yayana da Aunty Mami suka runguma kaddarar da ta same su Allah yasan damuwarsu nima ya haifa min tsananin damuwa babban tashin hankalinsu yanzu bai wuce cikin jikinta da baa san ko na waye ba dan har Yan ajin su da aka san suna magana da ita sai da aka kama su duk yanda aka so a gane ko su suka yiwa muhasim fyaden ba'a gane ba.

Yayana ma yaso a zubar mata da cikin likitoci suka bada shawarar hatsari zaa Kara jefata idan akace zaa zubar mata da ciki abar mata cikin idan lokacin haihuwarta yayi sai a yi Mata operation.

Abinan daya same mu yasa duk na rage walwala salis ma ba wani samun kulawata yake ba.

Zirga zirga kawai nake daga gidana zuwa gidan yayana.

Daga dogon tunani da shawara muka yanke kai Muhasim Bauchi wajen iyayenmu daga su ba wani bare daya san muhasim nada ciki sai Salis.

Dan ko Luba ban fada mata ba ita cemin ma take Aljannu ne suka shafi muhasim din.

Anan bauchin aka cigaba da bawa muhasim magani ana kula da ita Aunty Mami mace ce mai kib'a daga wanan tashin hankalin daya samu muhasim tayi wani irin zabgewa kamar mai cutar Aids.

Yayana kuwa Rabin kudinsa a nemawa muhasim magani ne dan shima ya fara yarda.shafar Aljannu ne.

A takaice a haka muhasim lokacin haihuwarta yayi aka mata operation aka ciro mata katuwar jaririya mai Kama da ita nima lokacin Ina d'auke da cikin Ummi haihuwa yau ko gobe.

Rashin zaman katsina sosai da zirga zirga yasa bamu fiye samun zama da Luba ba.

Ganin jaririyar Muhasim da aka sawa sunar Aisha da bansan dalilin daya sa yayana ya zabi sunan ba yasa naji kaunar yarinyar har a raina ni da kaina na zabi a ringa kiranta da Nana.

Na lura Kamar daga yayana har Aunty mamy basa san Rainon Nana dan har yayana cewa yayi ko gidan marayu zai kai Nana ni kuwa nace masa ba sai an kai ta ba su bani ita zan riketa.

Yayana cemin yayi ba lailai Salis ya yarda ba nace masa indai Salis ne nasan bashida matsala.

Koda na koma katsina na tari Salis da zancen shiru yayi yana kallona har na fara Jin ba dadi a raina yace min anya zan iya kuwa da wane zanji da rainon cikin jikina ko da rainon Nana sai yake ganin kamar bazan iya ba bayaso na dorawa kaina wahala ko dai maganar yayana zanji a kai ta gidan marayun.

Na girgiza masa kai akan zan iya nidai kawai ya bani izinin karbota.

Kamar dai na masa dole.yace min to Shikenan.

A yanda Nana ta dawo hannuna kenan kaunarta a zuciyata ta daban ce Inda nasan haka ya hada da san da nake yiwa muhasim da tausayin mahaifiyarta da ke fama da larura.

A lokacin da Luba tazo gidana sakin baki nayi Ina kallonta dan wani irin kyau naga tayi Kamar wata amarya,kayan jikinta ma masu balain tsada ta Sha lullubi har saman kanta Kamar dai matar aure.

Ni Ina Kare Mata kallo ita Kuma ta zubawa Nana Ido dake kwance a doguwar kujera tana "A Ina kika Samo 'ya nidai nasan ba haihuwa kikayi ba tunda ga ciki nan a jikinki"

"Wlh yarinyar wata Yar uwarmu ce na karbota dan maman ta tana haihuwa ta rasu.

Ta saki sallati tare da nufo wajen da na kwantar da ita ta d'auketa tana "Allah sarki baiwar Allah kice bata san mahaifiyar ta ba

Kwalla ya zubomin na kashe muhasim da nayi da ranta da tausayin ta hanyar da aka samu Nana Ina "wlh kuwa"

Na share hawayen fuskata Ina cigaba da kallon luba da nidai ta canja min sosai har sai da na kasa hakuri nace "Luba Kinga yanda Kika canja kike kyalli Kamar wata amarya kuwa"?

Ta saki murmushi tana "Ai amaryar ce tunda na kusa shiga daga ciki"

"Dan Allah fa"?

Nace cikin tsananin murna Ina "wa kika samo dan da alama kin samu irin wanda kike so"?

"Wlh na samu Aisha alhamdulillah tunda na kwallafa a raina sai na samo Mai kudi na samu dai"

"Kai Alhamdulillah na miki murna sosai wlh kawata a Ina yake aiki"?

"Gidan mai ne dashi fa sai dan aikin asibiti da yakeyi"

"Kai madalla naji dadi wlh ya turo manyansa?mai mata ne"?

"Ke fa dan baki fiye zama bane amma da duk kin san halin da ake ciki,ya turo manyansa mana a ranar da aka kai kudin kawai aka daura Auren,Yana Kuma da Mata"

"Na saki baki Ina kallon ta cikin tsananin mamaki"

"Wai kina nufin yanzu haka da aurenki"?

Ta saki dariya "kwarai kuwa tarewa ne dai banyi ba sai wani satin"

"Kai wai dagaske kike ko da Wasa"?

"Wlh dagaske nake toh mai abin mamaki nifa ba budurwa bace bazawara ce ni, shima ba saurayi ba wane shiri za'ayi ai kawai Aure aka daura zan tare sati mai zuwa"

Na saki ihu dan har ga Allah wlh kamar na taka rawa haka na ringa ji "Na miki murna kawata wlh bakiji dadin da naji ba Kai Kai Kai ke kinji dadin da nake ji a zuciyata a Ina Kuma zaki zauna"?

"Abuja zan zauna"

"Aikuwa duk da uban cikin jikin nan nawa dani zaa kai ki insha Allahu haba shiyasa wlh da kika shigo naga kina ta walwali Kai Aure ma rahama ne wlh zanso kuwa ganinsa ko baki bashi labarina ba"

"Kai ai yasan da zamanki dan baya garine da dashi zamu zo ku gaisa"

"Ba damuwa idan munje Kai amarya sai naganshi ai"

"Kijiki da wata magana Wai Kai amarya sai kace budurwa ai dagani sai mijina zamu wuce ba mai rakani"

Na saki dariya Ina "Ikon Allah kawata yanzu dai kin Shiga daga ciki kema kin zama matar Aure wlh naji Dadi takaicina daya ba gari daya zamu zauna ba"

"Ke dai bari dadin abin yanzu ai akwai waya kicewa mijinki ya siya miki nima yace zai siyamin sai mu ringa waya"

"Aikuwa wancan sati Salis ke cemin zai siyamin wayar ni kinsan ban wani damu da kyale kyale ba amma ko dan ke dole nasa ya siyamin ko ya zaiji

Please Login or Register in order to submit comment