Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sai tace na wulakantata ta hakane yasa na sakar mata murmushi Ina "Hajiya daga Ina"?

"Unguwa naje fa ke na hadu da wani mai kudi yaseen amma bana Jin dai ya Kai Mijin ki kudi gaskiya amma ya zanyi haka zanyi maneji na aure shi kila ya Kara kudi a gaba ki tayani da Addu'a Allah yasa da gaske yake zai aureni ke gidan nan da Salis yake ginawa wlh Kamar wani hotel kawata kin chaba wlh"

Dariya nasa Ina "Allah ya baki fin gidana Luba wlh tunda nake ban taba sa rai zan tab'a tsintar kaina a cikin irin Wanan niimar ba insha Allahu kema Zaki samu"

"Kai kai kawata wanan shegen less din fa kinsan kudinsa kuwa"?

Ta dauki less din da na ajiye a gefena dana ga ta shigo wai Ina addua ma Allah yasa Kar ta gani.

Ai tuni ta jawo duka kayan ta hau dagawa tana ihun nasan tsadarsu kuwa duk ita ta hau fadamin kudin kayan ta mik'e tsaye ta fara Kara kayan a jikinta tana "Allah ya baki Aisha irin rayuwar da nake mafarki Allah ya baki Salis ne ya siyo miki ko dan nasan ba wani sanin kaya kikayi ba"?


"Eee shi ya dinko min na bikin gidansu Aunty Mami kinsan jibi zamu tafi"

"Gaskiya sunyi kyau kawar rufin asiri aikuwa dole ki bani aron daya dan gobe Alhajin nan zai zo kinsan gwara yasan tanadin da zaiyi idan yaga na saka irin wanan less din"

"Luba nace miki fa dinkunan bikin da zamuje ne taya zan baki aro ai sai dai Kuma idan na dawo sai na baki amma yanzu ko bikin ma banje na sa ba, sai na baki aro"


Sai ta saki less din hannunta take fuskarta ya sauya "ke yanzu aro ne bazaki iya bani ba Aisha aro dai ba kyauta ba wlh ban tab'a tunanin wai akwai abinda zan nema a wajenki ki hanani ba arzkin nan muma zamuyi Aisha bamu fidda rai ba dama nasan lokaci na zuwa da zaki wulakantani sabida kina ganin kin samu abin duniya"

"Kai Luba mai yasa kike hakane dan girman Allah kin tab'a tambaya ta abu na hanaki ko abu Kika gani ban taba sawa ba idan kikace na baki aro Ina baki ban taba hana ki ba wanan biki za muje Salis shi ya Kai min dinkin nan da kansa Kuma shima zaije bikin ai bai dace ace bai ga nasa ba ki fahimceni Mana idan Aron less kikeso ai zan iya dauko Miki wani akwai wayanda ma ko sawa ban tabayi ba ai sai ki zaba a ciki"

"Ki barshi kawai Aisha ba komai muma Allah ya Mana arzikin nan"

"Ta dauki purse dinta fuuu zata wuce na rukota da sauri (akwai abinda idan na tuna wlh kamar na rufe kaina da duka Sadnaf hmm)

"Kai Luba wai mai yasa kike haka ne mai na zuciya dan Allah dan annabi toh ki zabi Wanda Zaki ara din Shikenan ban miki rowa ba"

"Wlh ke din ce da haushi Aisha yanda na d'auke ki wlh ba haka kika d'aukeni ba wlh bana fatan Wai yau ace ke ki nemi abu a wajena na hanaki amma ke daga ki bani aro kin tsaya maganganu"

"Toh naji dauki Wanda kikeso din"

Nace Kamar nayi kuka sai addua nake Allah yasa Kar ta dau wanda yafi shiga raina sai kuwa gashi shi ta d'auka iya nan bai isheta ba sai da ta kara aron mayafin da zai Shiga da sarka da dankunne.

Har ta tafi zuciyata cike take da bakinciki wlh ba wai dan aron kayan ba sai dan less din ya Shiga raina Kuma nasan kila nayi bankwana dashi kenan wane kila ai less ya tafi sai dai nayi hakuri.

Koda salis ya dawo ya tambayeni an kawomin dinkunan ce masa kawai nayi eee nama saka a akwati,ya tambayeni sunyi kyau kuwa"?

Nace Masa kyau kai sai ya saki murmushi Yana "Wlh da tsada na siyesu sosai dan inaso duk Inda Kika Shiga asan matar Dr Salis ce ke Kinga wanan ruwan ganyen yafi dukansu tsada ranar da zaku fi taro Zaki saka"

Sai na saki baki Ina kallonsa dan shi Luba ta d'auka na wayance da aikuwa baka ga kyaun da yamin ba"

"Ai nasan dole ya miki kyau dan nasan kalar dake haska ki"

Nidai a ranar haka na kwana Kamar nayi kuka luba dai tamin fin k'arfi ba Wanda na tab'a fadawa addabata da take da aron Kaya sau daya nasan na fadawa Aunty Mami ita kuwa ta ringa min fada akan ya nake Abu kamar doluwa mara wayo na daina haka ai bai dace na ringa bada aron Kaya ba sai dai idan nayi niyya dai na bar mata.

Duk yanda naso d'aukar shawarar Aunty Mami kasawa nayi dan sai nake ganin kamar bai dace Ina da abu Luba ta tambayeni na hanata ba.

A haka muka je bauchi muka yi sati biyu bayan biki na dan huta a gidanmu da su Ashraf ga cikin dake jikina da ya tafi wata biyar.

Ba laifi Salis ba iya iyayena yake yiwa hidima ba har da yan uwana na Kuma ji dadi ba kadan ba.

Naso barin Su Ashraf ma a gidanmu tunda hutun makaranta ake suka k'i ahaka muka dawo a motar da Salis ya aika mana duk dasu Aunty mamy Mu ka dawo da yaranta sai da muka sauka a gidanmu muka huta suka tafi muhasim tace zata zauna har sai an koma hutu zata koma gidansu itace Yar yayana ta biyu a lokacin tana da shekara goma Sha biyar. Ta girmi Ashraf da wajen shekara bakwai.


Ina dawowa da kwana biyu sai ga Luba ta duro a ranar Salis bai fita ba sabida ranar lahadi ne.

Koda na ganta sai da gabana ya yanke ya Fadi.

Dan less dina data ara shine a jikinta.

Nasan Salis indai yaga less dinan a jikinta sai na Sha fada dan kwanaki da ta sako wani atamfata da ta ara data tafi sai da ya tambayeni nace masa tana da irinsa ba nawa bane yace "Aa toh dan da nakine wlh sai munyi fada kinsan wanan kawar taki bata da hankali Ina tausayawa Wanda tsautsayi zai saka ya aureta"

Murmushi kawai na Masa a lokacin dan har a raina bana Jin dadin yanda yake Mata.

Tana shigowa nayi sauri na mike na fara k'ok'arin janta dan mu Shiga d'akin Yara.

Ai ba muje bakin k'ofa ba naji Muryar Salis a bakin k'ofar d'akina Yana kirana gabana ya yanke ya Fadi na juya a hankali ita kuwa Luba ko a jikinta ta juya itama tana "aa likita bokan turai ashe kana nan?

Bai amsa ba naga ya fara Mata kallon sama da kasa take naga ya hade rai ya juyo ya kalleni Yana "Aisha wanan ba less dinan bane da na siya miki?Mai yake yi a jikin Luba"?

Runtsa idona nayi dan Sam banso Salis yamin haka ba

"Kai likita bokan turai mai dan kayanta ne Ni da ita fa dayane ko ka manta"?

"Na manta me ya zaayi na siyowa matata Kaya kizo ki ara kice min ke da ita daya ne ke na siyowa ko ita? A wane dalili zan siyo wa matata kaya mai tsada sai kizo ki ara ki saka"

"Dan Allah ka bari Abban Ashraf zan maka bayani"

"Bayanin me Zaki min Aisha dama idan na siyo miki Kaya dan kisa kawarki kike bawa sabida wulakanci kwanaki naganta da kayanki kikace min ba naki bane irinsa ne da ita?dama baki San ciwon kanki ba Aisha an gaya Miki kudin banza ne dani? Ko an gaya miki bansan zafin kudina ba na ciri kudi mai tsada na miki dinki ki bawa wata banzar kawarki"?

"Kaga dakata Mallam karka sake ka fadamin maganar banza kai har wani arziki kayi da zaka min rashin mutunci karka manta fa tare kaganmu da ita baka isa ka rabamu ba ko ni keda kayan da take dashi zan bata fin wanan har nawa kayan nan suke da zaka tsaya min rashin mutunci"

"Luba mai haka kikeyi"?


Nace hankalina a tashe dan naga salis idonsa ya kada yayi ja

"Cire min kayana tunda ba ubanki ne ya siya ba wlh sai kin cire ban damu ki tafi ko tsirara ba wlh zan nuna miki ni din banida mutunci maza ciremin kayan nan yanzu idan kawarki bata da hankali ni zan koya mata hankali idan taga kinyi tsirara maza ciremin kayana

Tunda nake da Salis ban taba ganin bacin ransa haka ba ganin ya nufomu yasa na tsaya a gaban Luba Ina "Dan Allah Abban Ashraf kayi hakuri dan Allah ka bari taje gida ta cire ta Aiko min dashi na hadaka da girman Allah"


"Ai wani iirn tureni yayi yana "ba bakida hankali ba yau zan gwada miki rashin hankali har na siyi kaya da tsada ki dauka ki bawa yarinya da bata San ciwon kanta ba ta kashe aurenta sabida babu kuma har tana da bakin ta ringa gaya min magana ciremin kayan nan yanzu ki bar gidanan"

Yace Yana fincike mayafin jikinta na saki ihu.


Present

Luba

"Asabe kinsan dai ban yarda da wani asiri asirin nan ba ko to yau Hindatu ta kaini bango inaso na kawo karshen zamanta a gidan Alhaji kinsan banda Ina da zuciya mai kyau da har Aisha na rabasu amma Hindatu dai inaso kije wajen mai miki aiki a raba ta da Alhaji inaso Yana dawowa ya danna mata saki uku mu cigaba da Zama nida Aisha da ta zama hoto sabida kishi"

"Luba kenan ai kece tun farko kika bar ta ta sake haka har ta raina ki ai idan haka kikeso tare zamuje wajen mallamin"

"Aa ba wani zuwa da zanyi nidai zan baki kudi ayimin aikin kawai Alhaji na dawowa ya saki Yar iska"

Ta zuge Jakarta ta d'auko kudi ta bawa Asabe ta mik'e tana "bari naje gida kafin ta kira Alhaji tace masa na fita"

Har bakin motarta ta rakata ta shige tana sai sunyi waya.


Alhaji Salis...


MG'S SKINCARE


Dame akafiki yar uwata?
Kyan fatar ko iya gyaran fatar?
Ina riba g macenda t Maida kanta sauran mata?
Shin haryenzu labarinmu kikeji ko kike bayarwa?
Hajiyata miye matsalar?
Fatar takice abun se lahaula?
Kingwada kingwada harkinsare?
Tsakanida Allah yaushe daren yayi balle wayewar garin?

Inbakida labarin MG'S wacce tasanki tasansu,
Gawurtaccen Kuma shahararren kamfanin gyaran fatane,duk lalacewar jiki,duk hautsinewar fata,duk yenda jikinki yazama abun kunya gareki, Ina tallata maki me gabadaya,

Muntarkato,munwarwaro,munqullo duk wani Abu daze maidaki wanke hannu kataba mun qara a cikin kayayyakinmu,muncire,muntsife,munfidda,mun tantance mun hadamaku wasu irin hadaddun lafiyayyun kaya masu masifar goge fata,wallahi duk fitinar fatarki inshallah,kinzo bustop,kisiya kiyikyanda ko mace,kan juyo ta waiwayo ta dubi halittar Allah,

Ga product din kamar hka,
Sabulu 4500

Mg's beauty kit
Karamin kit 12k
Body soap
Facial soap
Body cream
Face cream
Glow oil
Pink lip balm

Flawless skin beauty kit
Babban kit 20k
Body soap
Facial soap
Body cream
Face cream
Scrub
Glow oil
Pink lip balm

Note kowanne d kalanshi nd yanayin packaging dinma aren't the same,

Tsakanida Allah kigafa
Duk wannan garabasar Kuma kinazaune hba taso a dama dake a harkar yar uwata,

Ayi hakuri da sauyin farashi komi yatashine muma b hka mukasoba
Chat:08062991549,07046881166,07067210195,
Call,+2348064532391*NI DA KISHIYOYINA*

*NA SADNAF*

*E.W.F*


*PAID BOOK*




*Page 5*

Alhaji Salis

A lokacin daya je ya samu mahaifin Aneesa akan turo manyansa izini ya bashi akan ya turo dan Aneesa tace ita tana San shi Kuma mahaifin Aneesa ya dan yi bincike akan Alhaji Salis bai ga Yana da wani matsala ba.

Sati ukun da yayi niyyar yi ya fasa ya d'auko hanyar gida dan ya fadawa Iyayensa ko da wasa bai tab'a kawowa kansa sake aure ba, hasali ma addu'ar sa kullum bai wuce Allah ya raba sa da Luba da Hindatu cikin sauki ba, ya zauna da Aisha uwar yayansa Wanda tunda ya aureta sai dai Santa ya karu a zuciyarsa sai gashi kaddara yasa ta maida shi hoto shi yasan akan dole take zaune dashi sai gashi kaddara ta sake hadasa da Aneesa dayaji Santa a zuciyarsa kwatankwacin irin san da yake yiwa Aisha har a yau da yake da manyan Yara Allah ya hore masa lafiya Yana bukatar nutsuwa a rayuwarsa sabida k'in da Aisha take Masa yasa baya samun nutsuwar da yake so a wajenta tunda shi kadai yake kidansa yayi rawarsa Hindatu da Luba kuwa baya kaunarsu ballantana yaji a zuciyarsa Yana samun nutsuwa dasu, hasali har fargabar kwanansu ya zagayo yake,ko a yanzu da yake san auren Aneesa kasan zuciyarsa cike take da fargaba da tsoro dan Luba ba k'aramin daga masa hankali tayi a auren Hindatu ba ko tunawa baya so yayi kalar cin mutunci da ta masa, tayi dambe kuwa da Hindatu tun kafin ma ya aureta yafi a kirga Inda yake dan samun sauki shine Hindatu itama ba kanwar lasa bace sau tari Yana so ya samu ko wata daya ne a gida ya samu lokaci da yaransa ya samu ya cigaba da rarrashin Aisha sai dai bai isa ba dan tashin hankali Luba da Hindatu ke saka shi tafiyar da bai shirya ba.

Ko daya iso garin katsina sai da ya fara zuwa gidansu mahaifinsa shekara biyar kenan da rasuwarsa mahaifiyar sa ce kawai ta rage masa.

Sai da yaci ya koshi ya fada mata Auren da ya keso ya Kara.

Sai da ta jima bata yi magana ba kafin ta sauke ajiyar zuciya tace "Yanzu Aure zaka sake yi Salisu? Yanzu baka girma da Aure ba? na dauka zaka cemin Afrah ma aka sawa rana, mai zakayi da Aure yanzu tsakani da Allah Salisu? matan ka gasu nan har uku banda tashin hankali da kake so ka Kara karowa kanka tunda ga lokacin da ka tsiri aure aure kayi bankwana da farinciki Aisha dai itace matarka ta rufin asiri daka tashi mata sakayya sai ka auro kawarta Kai ma tunda kayi auren ka sake wani baka Kara samun kwanciyar hankali ba baka tsaya ma a gidanka ba yanzu kana zancen dauko aure anya Karin auren nan naka Mai yuwa ne kuwa?

"Hajiya ya zanyi banida bambancin da Wanda bashida aure shekara da shekaru Ina bawa Aisha hakuri ita kawai nake Jin dadin zama da ita kema wai a haka arzikinki naci Aisha take zaune dani har yanzu.

Luba da Hindatu kaddara tasa na aure su hajiya auren nan da zanyi wlh na dolene kawai da ace Aisha zata yafe min laifin da na mata wlh da ba wani aure da Zan sake to ya zanyi kimin addua kawai dan ko na auren ba gida daya zan ajiye su ba yarinya ce ma wacce zan aura bata fi Sa'ar Aliyu ba"

"Kai yanzu sa'ar Yar cikinka zaka auro cikin manya manyan matan nan naka Salisu kanka daya kuwa ai wahala kawai Yar mutane zata zo ta sha a gidanka ko ka manta suwaye matan naka? Ina laifi ma kace babba ka d'auko zaka aura?ai daga lokacin da ka aikata kuskuren auro kawar matarka ka tusa mata bakin cikin da nasan har ta mutu bazata tab'a mantawa ba Kai ma fa ba zaka tab'a samun farin cikin da kake so ka samu a rayuwar aure ba wlh ba baki nake ma ba hakki ba Wasa bane ba ni nasan Aisha cewa kawai take ya wuce amma ba yafe maka tayi ba"

"Hajiya Kun kasa ganewa kaddara yasani auren kawar Aisha Kuma rabon Yara uku ko inaso ko bana so tunda Allah ya kaddara da rabo a tsakanin mu sai na aureta bansan mai yasa Aisha ta kasa ganewa ba wlh bata kaini bakin cikin zama da Luba ba duk tsawon shekarun nan hajiya wlh ban tab'a kaunarta ba zaman hakuri kawai nake Hindatu Kuma kema kinsan kaddarar da ta saka na aureta mahaifinta ya kakab'a min aurenta nidai kawai ki cigaba da tayani da Addu'a ayiwa su kawu magana suje su kai kudin auren da sadaki tunda mahaifin yarinyar yace wata biyu za'a saka"

"Tom Allah ya bada sa'a Salisu bani wayata na kira kawun naka"

Alhaji Salis ya mik'e ya d'auko mata wayar a gaban mudubin d'akin ya Nemo lambar kawun yayi dailing tare da sakawa a handsfree.

Koda Hajiyar ta fadawa kawun tambayarta kawai yayi yaushe za'a je dan Alhaji Salisu Kam ba wanda baya san faranta masa sabida hannunsa a bud'e yake har dangi na kauye yana hidimanta musu.

Bai bar gidansu ba sai karfe shidda dan ji yayi ma Yana fargabar zuwa gidan bai san mai zai je kuma ya tarar ba idan a tsarine yau d'akin Aisha ya Kamata ya kwana tunda har yayi wa Luba kwana daya amma dan masifa sai ya karasa mata wanan kwana dayan idan ba haka ba kuwa bai Isa ya runtsa ba.

Koda ya isa gida da Bismillah ya doshi bangaren da yake na yaran dan part wajen uku ne a gidan masifar Luba yasa duk suka zaune part daya duk da katone na gaske sai daya part din daya hade da nasu sabida yara.
Ta k'ofar tsakar gidan ya shiga part din yaran a Palo ya tarar da su duk a zaune Afrah tana Kan doguwar kujera a zaune,Aliyu na gaban tv sai yaran Luba Faisal fawazz da bintu, sai na Hindatu da sune kusan Yara a gidan Mubarak Ummulkhairi sai Ummi.

Duk suna ganinsa Suka yi wajensa da gudu banda manyan.

Ya saki murmushi yana shafa kansu tare amsa gaisuwar da suke masa.

Sai da ya gama amsa gaisuwar su ya samu waje ya zauna dan bama yaso ya Shiga Bangaren iyayen duk da sun san daga tafiya yake hakan bazai Hana su daga Masa hankali ba.

Afrah dake k'ok'arin mik'ewa ya kalla Yana "Ina Nana banganta ba"?

"Tana wajen hajiya umma wai zata mata kitso Abba bari na d'auko ma ruwa"

"Ki barshi kawai daga gidan hajiya nake lokacin sallah yayi ku je kuyi alwala kuyi sallah ko nima bari nayi alwala naje massallaci"

Da sauri mazan duk suka kada kansu suka yi waje da Alhaji Salis.

Basu Kuma dawo gidan ba sai da aka iddar da Sallah Isha.

Alhaji Salis ji yake kamar Kar ya Shiga gidan.

A hankali ya doshi bangaren matan gidan hayaniyar da yake ji ya saka shi tsayawa cak ya fara jan sallati muryar Aisha da yaji yasa mamaki Kama shi dan bai tab'a Jin hayaniyarta dasu ba idan dai zasu kwana suna fada bata shiga harkarsu.

Da sauri yayi cikin gidan ya tsaya a bakin k'ofar Yana kallon Aisha dake sanye da hijabi har kasa hannunta rik'e da na Nana da bata fi shekara goma sha uku ba tana ta kuka "duk abinda zakiyi Luba kiyi luba ban hanaki ba amma idan har zaki tab'a Nana wlh bazan d'auka ba ki tab'a kowa daga Kan Ashraf zuwa Kan ummi amma karki sake ki yarda ki Kara tab'a Nana kinji na gaya Miki"

"Sai na tab'a ta Aisha sai dai kiyi duk abinda zakiyi tunda ba fin kowa tayi a gidanan ba wacce wata Nana da bazaa aiketa ba daurin gindin da ta samu a wajenki yasa take yiwa mutane rashin kunya kamar yarinya nan tace baza'a aiketa ba,tunda har yaran gida ma ake aikensu wacce wata agola da baza'a aiketa ba wa ta fi a gidanan aikuwa indan har na aiketa bata je ba wlh sai na doketa idan na daketa ki dau mataki ko a zuciya a maida ta inda ta fito"

"Luba ba fa wai tsoronki nake ji ba duk tsawon lokacin nan kike abinda kika ga dama Ina kyalleki idan shi Salisu asirice shi kikayi ni ba asirceni kikayi ba wuri na baki sabida kiyi duk abinda kikeso kiyi domin hankalina da naki ba daya bane daga lokacin da na fara biye miki mun zama daya dake amma wlh wlh kinji na rantse idan kika kuskura kika Kara tab'a Nana wlh zan baki mamaki"

"Ki bani yanzu idan ke Yar halak ce bari na daketa naga mai zakiyi"

Luba tace tayi wajen Nana da sauri

"Lubaaa ya isheki haka"

Alhaji Salis yace cikin wani irin tsawa daya sa suka juya dukansu suka kalli bakin k'ofa.

Alhaji Salis ya nufi wajensu cikin wani iirn b'acin rai kafin ya Isa wajensu Aisha ta masa wani irin kallo ta ja hannun Nana tayi dakinta da ita.

Luba kuwa ta hau girgiza tana jiran isowar Alhaji Salis

"Yana kuwa isa wajenta ya hau masifa "Luba ke wacce irin mata ce ke? A rayuwarki sam bakya san zaman lafiya kinfi san ayita tashin hankali da ke wanan wane irin balai da masifa ne Luba na gaji fa wlh wlh nagaji bazaki kasheni da raina ba har ace nafi samun kwanciyar hankali a waje akan a gidana Kuma duk gidanan ba mai daga min hankali sai ke a wane dalili"?

"Akan me toh za'a ce kar na aiki Nana wacce Nana da har za'a ringa gindaya min sharruda a kanta wa tafi a cikin yaran mu haka kawai dan San zuciya zaa ringa fifita ta sabida ta hada jini da Aisha toh wlh bazata tab'a sabuwa ba nima Zan dauko ilham ta dawo gidanan da zama ehe ai ba fina tayi a gidanan ba"

"Alhaji kawo jakarka na kai ma d'aki ai yaci ka Saba da halinta kake wani damuwa da abinda tayi ita idan bata San ciwon kanta ba ai Kai kasani haka kawai daga dawowarka zaa saka ma ciwon kai muje ka watsa ruwa kaci abinci na maka tausa"

Hindatu tace tana k'ok'arin karbar jakar hannun Alhaji Salis da idonsa ya Kada yayi ja kansa har wani sara Masa yake

Wani irin duka Luba ta kaiwa hannun Hindatu dake k'ok'arin karbe jaka tana "toh katuwar kwartuwa kafin kija shi d'aki dan jarraba yau kwana na ne ba ruwanki dashi kwana daya yayi a dakina yayi tafiya sai ya karashe min kwana dayan zai koma hannun uwar gida duk jarrabarki sai ki hakura sai kwananki ya zagayo"

"Kefa kwana ya dama da gado Luba tarbar da ya Kamata ki Masa ne bakiyi ba shiyasa nake San na masa,
tunda ke din ba abinda Kika sani sama da masifa da gado"

Wani irin Ashar Luba ta dura wa Hindatu Suka fara zage zage.

Alhaji Salis ya zube akan dogon kujera tare da dafe kansa Yana sallati.

Sosai yake ji kamar ya sa hannu aka yayi ta kurma ihu.

Magana yake musu amma Ina idonsu ya rufe Shirin dambe ma suke.

A hankali ya mik'e hannunsa dafe da kansa yayi d'akin Aisha

Yana tura k'ofar ya sameta a gefen gado a zaune tana ta share hawaye gefenta Kuma Nana ce a zaune a kasa.

Shigowarsa yasa ta dago da kanta ta zubawa Salis ido.

Salis kuwa yaji kirjinsa ya masa wani irin nauyi da ganin Aisha a cikin irin Wanan halin shekara nawa Aisha na zubar hawaye da duk shi ya jefata a cikin wanan halin.

"Aishaaaa"

Ka fita Salisu dan Allah ka fita a yanzu bana san magana ka fita dan girman Allah karka Kara min ciwo akan Wanda nakeji a zuciyata"

Salis a hankali ya juya ya fita daga d'akin Yana hadiyar yawu sabida ji yayi makoshinsa ya bushe har ya koma palon suna masifa akan kujera yayi kwanciyarsa ya runtse idonsa Yana Hindatu idan ban isa da Luba ba ke na isa dake dan Allah ki rabu da ita"

"Shikenan Alhaji ni bansan ma mai ya kaini biyeta ba kayi hakuri"


Tayi hanyar dakinta tana zabgawa Luba harara

"Alhaji tashi mu tafi daki na hada ma ruwan wanka"

"Bazan tashi ba"

"Bangane bazaka tashi ba kasan dai yau a dakina kake ko"?

"Anan zan kwana bazan Shiga d'aki ba"

"Idan kwanan Aisha ko Hindatu ne ai ba a Palo kake kwana ba"

"Idan kina da k'arfi Zaki iya daukana ki kaini d'akin"

"Banida karfin daukar ka amma kasani nima anan din zan kwana nima dan bazan shiga d'aki a ci amanata ba"

Alhaji Salis yaja tsaki dan kansa sosai yaji yana neman rabewa biyu ya gaji da Luba ya gaji ya rasa ya zaiyi da ita Aisha ce tsaye a ransa inama zata barshi da ya kwana a dakinta ya kwana Yana bata hakuri hawayen ta daya gani ba karamin daga masa hankali yayi ba.

A takaice a ranar a Palo ya kwana Luba itama ta d'auko bargo ta kwanta a kasa ta dora kafarta a kan kujerar wajen kafarsa wai kar ma bacci ya d'auketa ya tashi yaje d'akin Aisha tunda nan yafi zuwa idan bacci ya d'auketa.

Past

Aisha

"Dan Allah Abban Ashraf ka bari ka rabu da ita taje daki ta ciremin"

"Wlh sai ta cire kayan nan ba bata da hankali ba"

Ganin dagaske Salis yake yasa na zube agabansa tare da kankame kafarsa na saka kuka Ina magiya Luba kuwa wani irin hucci take da alama da tana da k'arfi sai ta kaiwa Salis duka.

Salis kuwa nasan wuyanta na fara kuka nasan na gama dashi bayasan kukana ko kad'an.

"Dalla sake min

Please Login or Register in order to submit comment