Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya gansu tare suna soyayya ko da wacce mace ya ke tare idan baiyi tunanin kamar da Muwaddat yake ba to bai ta6a jin ya gamsu.

Bayan kammala karatunsa ya zama big boy sosai da yake kam Sadeeq kyakkyawa ne ajin farko akwai kyau kud'i ga wanka,haka ya had'o kwarmatsansa zuwa gida Nigeria tare da sakamakon karatunsa mai kyau.

A Nigeria kuwa zuwa wannan lokacin abubuwa da yawa sun faru,Kammaluwar karatun Ma'aruf duk da dai Diploma kawai yayi Zuwa lokacin Muwaddat ta girma tana SS2 a Secondry ta zama budurwa sosai haka Umma ta qara haihuwar yara biyu Zulfa'u da yanzu take jss1 sai Dawud da ya ke primary 4 dukansu makarantar gwamnati suke amma banda Muwaddat da take makaranta guda da Salma wato qanwar Sadeeq wacce suka qulle da qawance duk Hajiya Safiya ke komai na karatun Muwaddat wanda Daddy Abubakar ne ya mada umarni tare da turo komai da zata buqata,tun Alhaji muttaka baya son qawancen yaran har ya haqura domin ranar da ya fara ganin Muwaddat ya girgiza ganin kammanninta da qaninsa Abubakar kuma tana yanayi da Sadeeq da Salma sosai,tun yana kurarta amma hakan ba zaisa gobe ta dawo ba har ya hakura kunsan yara da naci,to ita Muwaddat nacin ta yana da yawa sosai,da haka ta saba da 'yan gidan duk da Alhajin ba magana ya ke mata ba.

Ma'aruf kuwa ciwonsa har yanzu yana nan,ganin basu da halin na asibitin sai suka dawo na gargajiya,ba laifi yana samun sauqi,ranar da Sadeeq ya dawo iyalan gidansu Salma sunyi farin ciki harda Muwaddat sune zuwa Airport tarosa ai abunda ya bawa Alhaji da Hajiya mamaki ko da yazo gurin da suke sai ya nufi gurin Muwaddat binsa sukayi da kallo baki bud'e yana zuwa sai gani sukayi ya rungume Muwaddat ya qamqameta sosai yana sakin ajiyar zuciya.....
*KARO ƊAYA...!*


©UMMU AFFAN


_GAWURTATTU UKU 2023🤟_


05

Alhaji Muttaka kasa magana yayi sai kallon Hajiya da yayi,itan ma shi take kallo a zuciyarsa yace"tabbas wannan abun nasu daga Allah ne domin duk raba sun da yayi na tsawon wani lokaci hkn baisa ya mance da yarinyar ba amma duk da haka yana nan kan bakan sa wallahi idan ma sonta yake ba zai ta6a yarda gudan jininsa ya auri SHEGIYA ba.

Ganin yaqi sakinta Hajiya ta qarasa gurin tare da kiran sunansa" _SADEEQ_" da sauri ya d'ago idanuwansa wad'anda suke lumshe shi sam ma ya manta da su a wajen da sauri ya cika Muwaddat yana sosa qeya wacce ita ma zuwa lokacin sosai ta ke kallonsa da mamakin abinda ya mata,rungumarta da yayi taji wani baqon yanayi da bata ta6a jin irinsa ba gashi qirjinta idan banda bugu babu abinda yake.

Gaishe da iyayen nasa yayi sannan suka runtsuma mota sai gida,tarba kala-da-kala an masa na daga kayan abinci da gyara masa part d'insa,bayan yayi wanka ya kimtsa sannan yazo yaci abincin wanda duk rabin hankalinsa nakan Muwaddat wacce da ita ake cin abincin ta riga ta zamowa AAlhaji muttaka qarfen qafa babu yarda ya iya da ita dole yayi hakuri ta shiga cikin iyalansa amma ba wai magana ya ke mata ba domin ya tsaneta.

Muwaddat ko da yaushe tana gidansu Salma domin irin yaran nan ce mai rawar kai domin ko a skul qaryar da take yi ai gidansu guda da Salma,duk wanda yasanta to d'aukarsa 'yar gidance domin komai a gidan take yinshi gashi duk abinda Alhaji Abubakar wato Daddy zai aiko mata dasu tare yake mata da Salma haka Hajiya duk abinda zatawa Salma to sai tayiwa Muwaddat hakan yasa ta taso yarinya 'yar k'walisa ga iyayi da rawar kai.

Su kuma Baba Malam da Umma sosai suke qaunar Muwaddat saboda maraicinta na rasa uwa da tayi,idan ta tambayesu iyayenta wato uwa da uba sai suce mata duka hatsarin mota sukayi suka rasu,wannan dalilin yasa ta san bata da iyaye su Baba Malam sune kawai ahlinta,idan sunce mata hakan bata ta6a tsaurarawa akan 'yan uwansu ba ita dai tasan tana rayuwarta a matsayin iyayenta sun rasu.

Sadeeq kuwa tunda ya dawo ko da yaushe yana liqe da Muwaddat suna hira dai harda Salma haka ya fara aikinsa a wani company duk idan ya dawo Muwaddat yake sawa ta masa komai.

Wata rana ciwon Yaya Ma'aruf ya tashi,to shi baya aiki kunsan yarda halin qasar tamu take 'ya'yan talakawa ba samun aiki suje ba sai an dace shi so yake ma ya koma karatunsa ko digiri ne yayi abinda kawai yake yanzu ita ce waqa Ma'aruf mawaqi ne kuma sosai abin ya amsheshi duk da dai alokacin shi d'in ba wani babba bane a harkar,rashin lafiyarsa ya tada hankalin iyayen nasa haka Muwaddat ta shiga cikin wani hali duk da basa shiri domon baya son shigarta gidan Alhaji muttaka baya son shigewa Sadeeq da take amma taqi bari,domin silar fara waqarsa akan so ne domin irin son da yakewa Muwaddat yasa shi zama ya rubuta mata waqa,ko da yaje studio domin yin waqa aka fad'a masa kud'un kid'a kasa biya yayi domin baida su baiba wani ajiya ba,hakan yasa sai da ya tara kud'in kid'an ta hanyar bin Baba Malam wajen aikinsa na gyaran mota bayan ya tara yaje yayi,saboda lalurarsa yasa Baban bai son yana aikin wahala kar ya tada masa chiwonsa,lokacin da yayi waqar sosai ta qayatar hatta makid'in ya yaba masa sosai da yake mawaqi ne yace idan yana so yaci gaba da harkar domin ya yaba da fasaharsa to koda waqar ta shiga duniya ma sai aka amsheta ta amsu matuqa duk da cewa muryarsa kad'ai ce wato baisa mace a waqar ba amma ta amsu yarda baiyi tunani ba,ta silar ubangidansa Haruna mai waqa wanda babban makid'i kuma mawaqi ne Ma'aruf ya fara koyan kid'a da farko bayan waqar Muwaddat da yayi ta farko wacce bai ambaci sunanta na Muwaddat ba amma yayi amfani da asalin sunanta wato Khadija,Ma'aruf ya kware a kid'a inda bayan nan ya ci gaba da waqarsa inda lokaci qanqani ya fara suna.

Ciwon na Ma'aruf ya tada hankalinsu NAn take aka kaisa asibiti likitan da ya ta6a amsar ciwonsa tun lokacin da Saratu na raye shine ya amshesa domin yasan kan lalurar ZUCIYA sosai,ko da ya fad'i abinda ake buqata sun girgiza domin basu dashi idan ba gidansu zasu sayar ba to basu da inda zasu same su,Muwaddat na kuka ta nufi gidan Alhaji Muttaka inda ta sanar da Hajiya abinda ke faruwa,Alhaji muttaka ya fara fad'a "to mu ina ruwanmu kinga tashi ki fitar min gida kin cika mana kunne da kuka" haka ta fita tana kuka Sadeeq ya bi bayanta Alhaji na kiransa bai sauraresa ba,cikin mota ya d'auki Muwaddat sai gidansa da ya saya inda yake kai 'yan matansa suna hulewarsu,rarrashinta ya fara saboda yarda take kuka"tace"Yaya Sadeeq wallahi Yaya Ma'aruf yana cikin wani hali don Allah ka temakamin a masa magani ya warke" yace"so nake ki natsu Muwaddat kin san ina sonki zan iya miki komai" bai ta6a cewa yana sonta ba sai yau d'ago idanuwanta tayi da sauri sai kuma ta kama murmushi domin tun dawowarsa take qaunarsa tana sonsa fiye da tunaninta sai kawai ta fad'a jikinsa tana kuka-kuka dariya-dariya wani sanyi yaji inda yayi ta shafa bayanta da niyyar rarrashi har takai yakai hannunsa saman nonuwanta,da sauri ta zabura tana kallonsa lumshe idanuwansa yayi yace"Muwaddat ina sonki ina son jinki a jikina ina son nonuwanki matuqa don Allah ki bani dama na nuna miki son da nake miki" girgiza kanta ta fara da cewa"a'a idan har da gaske sona kake to ka bari ka aure ni sannan sai kayi duk abinda kake so dani" girgiza kansa yayi cikin wata irin murya ya kamota inda ya hade bakinsu guri guda yana aika mata da wani zazzafan kissing hannunsa saman boobs nata yana burzar nipples nata,sosai take jin wani baqon yanayi da wani abu na ratsa mata daga kanta har zuwa tafin qafarta.

Da hanzari ta turesa ta ce"Please Yaya Sadeeq,Yaya Ma'aruf fa yana asibiti. Sake jawota cikinsa yayi yace"ki kwantar da hankalinki zan biya a masa aikinsa" hakan tasa tayi shuru amma hawaye bai bar zuba a fuskarta ba, sake jawota yayi jikinsa wannan karon bata masa gardama ba domin sosai ita ma take jin dad'in abinda yake mata.

Tun tana turesa har dai abinsa ya fara tasiri a jikinta,bai mata komai ba domin tana ta damunsa Yaya Ma'aruf yana cikin wani hali.

Tare sukaje dashi asibitin,sai-dai lokacin da Baba malam yaga Sadeeq gabansa ya fad'i ba abinda ya tuna sai lokacin da Saratu suka shugo da Abubakar,6angaren Umma ma haka abun ya kasance qirjinta banda bugu babu abinda yake.

Haka Sadeeq yayi magana da likitan ya biya komai sannan ya tafi,bayan tafiyarsa Umma ta kalli Muwaddat tace"Khadijatu me kika cewa yaron nan?ina fatan don Allah ya biya kudin nan bada wata manufa ba?" qirjinta ya buga da qarfi ta kalli Umma a tsora ce tace"Umma bada wata manufa ba ya biya temako ne kawai" Baba malam yace"to ki kiyayesa daga yau domin bana son wani abu ya biyo baya mutane basa tsoran Allah rayuwar yanzu kowa kansa ya sani" cikin sanyin jiki tace"to" sannan tayi shuru tana tunanin kodai su Umma sunga wani sauyin yanayi daga gareta na?tayi tsuru-tsuru kamar munafuka.

Bayan kwana2 Ma'aruf yana samin sauqi inda da yaji wanda ya biya masa kudin asibiti zubawa Muwaddat ido yayi cike da tuhuma sai yace a hankalin cikin sanyin muryarsa"Muwaddat akan me Sadeeq ya biya min kudin asibiti?" kallonsa tayi da sauri jikinta har rawa yake tace"kawai nace ya temaka mana ne domin gidansu na fara zuwa Babansa ya koreni shine shi ya biyoni mukazo tare" girgiza kai yayi yaci gaba da kallonta yanayin da jikinta yayi da tashin hankalin da ya gani cikin idanuwanta yasa shi cewa"Muwaddat ke macece ina son na fad'a miki wata magana guda d'aya ki riqe kimarki domin idan har kika rasata kinyi kuskure a rayuwarki da duk ta wani mai mafarkinki,Muwaddat kima abu ce mai matuqar alfanu da darajarki,akan ki rasa wannan darajar gara ki barni ni na mutu nasan lokacina ne yayi ke kuma ki raqe mutumcinki" sosai qirjinta ke bugu jin kalamansa ta d'ago a hankali ta zuba masa idanuwa shi kuwa kaida fuska yayi tare da lumtse idanuwansa masu matuqar kyau,zubawa kyakkyawar fuskarsa idanuwa tayi MA'ARUF kyakkyawa ne idanuwansa masu kyaune da annuri gasu manya amma idan yana cikin ciwo sukan dawo jajja-jajjja kore-kore duk da hakan kyawunsu na nan hancinsa yana da tsayi ba cenba gashi choculate colour yana da tsayi ba sosai ba domin Sadeeq ya fisa tsayi sannan yafi Sadeeq dirarran jiki donshi Sadeeq dogo ne a tsaye bashi da jiki,shi kuwa Ma'aruf baya sahun dogaye kuma ba gajere bane tsaka tsakiya sannan jikinsa mai kyau ne bai da qiba sannan ba siriri bane namiji ne mai matuqar burgewa ko da yaushe fuskarsa tana cikin annuri yana da jajircewa akan ra'ayinsa sannan akwai sanyin hali bai cika zafi ba,fuskarsa ta ustazai ce bashi da fara'a don gaskiya kafin kaga dariyar Ma'aruf sai an dauki lokaci,a hankali Muwaddat ta sauke sanyayyar ajiyar zuciya sannan ta juya ta fita d'akin daman Umma na waje.

Kwanansa biyar aka sallamesa maza da mata suna ta zuwa gaishesa 'yan mata masu aji da kyau,abin ya bawa Muwaddat mamaki ganin 'yan matan dake zuwa gaishesa domin ita bata san yana waqa ba,yawancinsu mawaqa ne da 'yan amshi suke zuwa gaishe sa da haka har aka sallame sa sun masa alkhairi mai yawa domin ogansa Haroon mai waqa dubu ashirin yabawa Baba yace ayi magani haka wasu daga mai dubu biyar dubu uku sai mai dubu biyu,kud'in mai makon ya aje karsu kashe sai yabawa likita dubu talatin yace zasu dunga zuwa amsar magani idan na hannunsu sun qare tabbas Baba yayi dubara.

Tun daga ranar da Sadeeq yaji dumin jikin Muwaddat hankalinsa ya tashi burinsa kawai yarda zaiyi ya mallaketa duk da yana sonta kuma yana jin zai iya auranta amma yana son su kasance a yanzu.

Ita kuwa Muwaddat tun akan maganar da Yaya Ma'aruf ya fad'a mata cikin azanci ko ince zauranci maganar ta shigrmeta tabbas kima wata abace mai matuqar alfanu,bata son rasa wannan kimar shiyasa ta fara baya-baya da gidansu Sadeeq sai-dai Salma ta shugo.

Dai-dai lokacin ne kuma akayi bikin saukarsu ta Qur'ani mai girma wanda duk Hajiya Safiya ce tayi kuma Daddy Abubakar ne ya aiko mata da komai,Muwaddat tayi farin ciki a saukarsu inda tazo d'aliba ta farko mai haxaqa da tsafta abinda ya faranta ran su Baba malam haka Ma'aruf, Sadeeq ya mata kyautar ban girma,bayan kalandu maimo siteka da bairo da ya musu ita da Salma yazo ya mata sarqa da 'yan kunne na gold kyautar da ta girgizata sai-dai a gurinsa wannan ba komai ba ne.

Ma'aruf kuwa duk wani drinks da cincin da sukayi amfani dashi shine yayi qoqari ya musu domin da kunun kid'a ma da yasamu yayi musu Muwaddat taji dad'i inda ta masa godiya,sannan ya saya mata wani zobe mai matuqar kyau a kwalinsa ya bata gift,zoben duk da baida kud'i sosai amma yana da kyau matuqa sai shinning yake idan ba sani kayi ba sai ka d'auka gold ne.

Nan take ta zura zoben a hannunta kallonta yayi yana murmushi yace"Muwaddat don Allah karki rabu da zoben nan" da sauri ta kallesa tace"yana tare dani Yaya Ma'aruf na gode" ta wuce binta yayi da kallo tare da lumshe idanuwansa yana jin qaunar qanwar tasa wanda yasan SON MASO WANI yake.

Sadeeq ne ya tsaya gabansa yana kallonsa tare da cewa" Malam Ma'aruf na lura da kana son Muwaddat ko?" Da sauri ya bud'e lumshashun idanuwansa yana kallonsa,d'aga gira Sadeeq yayi yace"yes na lura da hakan sai-.dai kayi kuskure guda domin ba'a had'a soyayya dani,ina son Muwaddat kuma tawa ce" Ma'aruf ido kawai ya zuba masa bai ce komai ba domin fagen miskilanci shi shegen gaske ne gashi daman shi magana fa idan ba dole ba bayinta yake ba sai ta kama.

Sadeeq cikin wata dariyar shaqiyanci yace"dani da kai duk mun san wacece Muwaddat domin da wayonmu komai ya faru don zamu gama primary ba dad'ewa lokacin kuma ina tunanin kamar yarda ban mance ba kaima baka mance ba" da sauri Ma'aruf ya kallesa baiyi tunanin Sadeeq na sane ba domin a lokacin yasan yafi Sadeeq wayau sosai domin kunsan yaran masu kudi da aka nunawa gata da sakarci baiyi tunanin yana sane ba.

Sadeeq yaci gaba dacewa"ni na dace da Muwaddat duk da bata da uba zan iya auranta sannan zanfi bata kulawa fiye da kai,Muwaddat bata dace da kaiba saboda idan har ta aureka zata qare cikin baqin ciki da talauci duba da yanayin da kake ciki da lalurarka don Allah kama cireta a zuciyarka da bata cika lafiya kabar min ita sam baku dace ba......


Tofa guys kuna ji fa,muje zuwa yanzu muka suma bama mu fara ba...
*KARO ƊAYA...!*


©UMMU AFFAN


_GAWURTATTU UKU 2023🤟_


06


Ma'aruf bin sa ya ke da kallo har zuwa lokacin bai ce komai ba,sai-dai sosai zuciyarsa ke harbawa kuma ya kasa d'auke idanuwansa akan Sadeeq wanda cike da shaqiyanci da gadara yaci gaba da cewa"Kai ba kowa ba ne,sannan ba komai bane face musaki mara galihu" da qarfi Ma'aruf ya runtse idanuwansa bai ta6ajin mummunar karmar da ta 6ata masa rai makamanci yar wannan ba,lokaci guda idanuwansa suka sauka launi cikin wani irin duba ya dubesa,domin Ma'aruf zai iya shenye komai amma banta wulaqanci baya wulaqanci kuma baya son a wulaqanta shi.

Yace"tabbas ina da tawaya a zuciya ai ban 6oye ba ko kaji wani nawa na 6oye lalurata da nake fama da ita?ai duk mai lalurar da zai 6oyeta domin wata manufa to a bincikesa,ni bana fahari ko fariya sai-dai ina me sanar da kai duk me abu baya fad'a wanda yake da abu yake d'agawa ko fariya to shid'in baqon abun ne,ka fad'i gaskiya da kace ina son Muwaddat na yarda ina SON MASO WANI amma ina me sanar da kai da sannu gaskiya zata nuna kanta,naji na amince kasan Muwaddat ko wacece kuskurenka na gaba sake kiranta mara uba ko shegiya alokacin ne zan nuna maka kuskurenka."

Yana gama fad'a ya juya yabar gurin cike da 6acin rai. Sadeeq kuwa binsa yayi da kallo ransa a mugun 6ace yaji haushi da takaicin maganar da Ma'aruf ya gaya masa idanuwansa sukayi ja sosai ransa idan yayi dubu ya 6aci,akan me wannan musakin zai gaya masa magana ai kuwa zai nuna masa kuskurensa, da haka aka gaba wannan walima ta sauka kowa ya watse Muwaddat da Salma suna cikin farin ciki.

Sadeeq ya qara qaimi a soyayyarsa da Muwaddat domin qara baqanta ran Ma'aruf,sosai Muwaddat ke qaunar Sadeeq wanda kowa ya shaida haka,idan ta shiga gidansu babu abinda yake sai ta6ata musamman zaice wai ita zata kaimasa abinci part d'insa,idan ta shugo kuwa ta6a ta yake son ransa musamman boobs d'inta da suke tsaye sun fi tsole masa ido.

Zaune suke suna hira amma hannunsa na jikinta yace"Muwaddat don Allah ki shirya zaki rakani wani waje" waro idanuwa tayi tace"wani waje kuma ina?" yace"don nace zaki rakani kike zaro ido haka,Muwaddat na lura ni ke haukana akanki" ya idasa da d'aure fuska,da sauri ta matso kusa dashi tace"kayi hakuri bata son ranka ya 6aci" yace kina so mana wai Muwaddat don nace zaki rakani kike zullumi" tace"bana zullumi akanka tunani na gida abinda zan fad'a" yace"ga qarya nan kala-kala na 'yan mata kice makaranta aka saku wani abu ko kiyi qarya da Salma" da sauri ta rungumesa tace"wannan gaskiya ne,yaushe zan raka kan?" yace"gobe misalin goma na safe" tace"ok badamuwa" har zata wuce ya jawo hannunta zubawa juna idanuwa sukayi na wani lokaci kafin tace"Yaya Sadeeq ina sonka ina qaunarka bana san wani abu ya gifto da zai iya rabamu wallahi zan iya rasa rayuwata saboda son da nake maka."

Murmushi d'auke a fuskarsa yace"Muwaddat babu wani abu da zaizo inaji a jikina samu mallaki junanmu karkiji komai ina tare da ke ina qaunarki Muwaddat sonki mai girma ne a cikin zuciyata" tace"nima haka" duka sukayi murmushi sannan ya rakota har gate ta wuce gida.

Washe gari kasancewar Asabar ce babu boko sai-dai islamiyya da yake sun koma hadda,tun qarfe takwas ta shiga gidansu Salma domin tasan takwas da rabi nayi idan Salma bata ganta ba zata biyo mata ne ita kuma bata san taje tana neman qaryar da zatawa Umma ne.

Bayan sun gaisa da Hajiya a parlour ta tambayi Salma tace"tana ciki" bedroom d'in Salmar ta shiga ilai kuwa shiri ta isketa tanayi.

Salma ta kalleta ganin ba cikin shiri take ba tace"ya na ganki haka?" marairaice murya tayi kalar ta tausayi tare da zama bakin gadon Salma da furta kalmar"washhh!tace"Salma yau na tashi bani da lafiya shine nace idan kinje ki sanar bana jin dadi sai gobe idan kuma naji dama zanzo da yamma shine nazo na fad'a miki" cike da tausayawa Salma tace"Ayya Allah ya qara sauki ba komai zan sanar" cike da farin ciki tace"nagode Salma bari na koma sai kin dawo" ta amsa da "to tana sake jajanta mata.

Tana komawa gida ta fara shirin fitarsu da Sadeeq Wajen qarfe tara da rabi taje gurin Umma dake zaune parlour tace...

Ta ce"Umma yau zan raka Salma gidan qanwar Hajiyarsu zata kai mata saqo,daman tun ranar Laraba mun fad'a a islamiiyya bazamu je ba" Umma ta d'ago idanuwa tace"amma me yasa baki fad'awa Malm ba tuntuni gashi yanzu ya fita wajen aiki" tace"Umma ba wani dad'ewa fa zamuyi ba don Allah ki barni naje" tace"ba hanaki zanyi ba Muwaddat na fi son Malam yasan da fitar taki ko ki fad'awa Yayanki" zaro ido nayi cike da tsoro araina nace da nasanar da Yaya Ma'aruf ai gara na hakura domin nasan ba zai barni ba da tashine ba inda zan dunga zuwa.

Gyara zama na nayi cikin kalmashe harshe da dad'in baki nace"Haba Ummana wai nan da rakon da zanwa Salma shine duk kika d'aga hankali haka akan sai na tambayi Baba malam ko Yaya Ma'aruf,idan fa mun dad'e to muyi awa biyu ba wani jumawa zamuyi ba" tace"idan Malam ya dawo yaga bakije islamiyya ba fa?ta tambaye ni tare da zuba min ido.

Kif-kifta ido na fara kamar munafuka nace"Umma ni nasan yarda zanyi dashi please ki barni naje" Umma tace"shi kenan ba komai" da sauri na rungume Umma tare da manna mata kiss a kumatu nace"na gode" shirina na ida goma sauran kwata na fito har zan fita umma dake aiki ta kira sunana"Muwaddat" juyowa nayi da sauri jin yarda ta kira sunan nawa,muryarta a sanyaye tace"a duk halin da zaki tsinci kanki ki kasance mai riqe kimarki ina mai umartarki da ki riqe mutuncinki na 'ya mace karkiyi yarda so ko dad'in bakin wani d'a namiji yayi tasiri agareki,domin idan har kikayi kuskuran rasa kimarki to kinyi babban kuskure sannan zafin zai miki girma da yawa ki d'aure ki zama natsattsiya mai kamun kai ko don nan gaba karkiji TAKAICIN HAKA." sosai ta zubawa Umma ido jikinta yayi la'asar yayi sanyi sosai idan banda bugu babu abinda qirjinta ke yi sai take ganin ko dai ummar tasan komai a kan fitarta sai tajo duk ta tsargu da kanta.

A sanyaye tace"to umma insha'Allah,sannan tasa kai ta fice asanyaye kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki.

Fitar ta ke da wuya ta shige gidansu Sadeeq lokacin shima shirin fitar tasu yake yana ganinta ya saki wani smiling yace"wellcome tawan" a sanyaye ta samu guri ta zauna,dubanta yayi bayan ya gaba zula belet d'in juens da yasaka baqi da farar t-shirt mai gajeran hannu ya gyara sumar kansa wacce idan banda tashin qamshi babu abinda take,kusa da ita ya zauna tare da riqe hannayenta yana murzawa d'ago kyawawan idanuwanta masu ruwa tayi da sauri yace"kuka?Muwaddat kukan me kike?" cikin raunanniyar murya tace"Sadeeq ina sonka,ina mugun sonka Sadeeq don Allah ko da wataran KAR KA GUJENI."

Chak ya d'agata daga zaunan da take kan kushin sai saman cinyarsa,harshensa yasa yana lashe hawayen idanuwanta,sai da ya gama lashewa sannan cikin wata mayen murya yace"Muwaddat ki dena mafarkin wai zan iya rabuwa dake koda a mafarki bana fatan kiyi mafarkin mun rabu balle a fili" sosai ta qamqamesa tace"na gode Sadeeq nima na rasa irin son da nake maka,ni dai nasan ina sonka zan iya mallaka maka koma menene" da sauri yace"kome fa kika ce" gyad'a kanta tayi cikin alamar tabbatarwa tace"eh" murmushi yayi tare da manna mata kiss a lips d'inta masu taushi kalarsu pink yace"ok zan gani idan da gaske kike" murmushi tayi bata ce komai ba.

Hannunta ya kama suka fita,suna zuwa ya bud'e mata murfin motar ta shiga tana murmushi shima ya shiga maigadi ya bud'e masa gate yayi waje da gudu,suna fita Ma'aruf ya fito da gida da sauri tayi qasa da kai qirjinta na bugu,Sadeeq ya kalli inda ta kalla,tsuka yaja mai qarfi mtsuuuuw da sauri ta kallesa,tace"yaya Sadeeq lafiya dai ko?" yace"lafiya ma kike tambayata bayan kinga wancen banza saunan Yayan naki kina wani sadda kai qasa,me yasa bazaki cire ZULLUMI a zuciyarki kiyi rayuwarki yarda ta dace ba wallahi na tsani MA'ARUF" da qarfi ta rumtse idanuwanta wasu marayun hawaye suka biyo kurmin idonta tace"KA TSANE SA fa kace?me ya maka?Yaya Ma'aruf bawan Allah duk da bamu jituwa dashi amma wallahi banta6a ganin ya aikata wani kuskure ba ko abinda bai daceba,shi ba ruwansa baya shiga abinda bai shafesa ba ga...

Tsawar da yadaka mata yasata yin shuru tace"eh wannan yabon nasa da kike yana d'aya daga ckn abinda yasa nake qara tsanarsa" hannu tasa ta share hawayenta bata sake cewa komai ba har suka isa wani Taraba Suyar inda ya saya musu kaza mai rai da lafiya wacce taji kayan had'i sannan ya saki drinks suka wuce gidansa.

Bayan sun isa da kansa ya d'auki Muwaddat kamar wata baby bai direta a ko ina ba sai bisa lafiyayyen gadonsa ajiye ledar gefe yayi ya jawota jikinsa tare da cire bata zumbulen hijabinta yana cewa"wannan irin abu haka kamar wata matar liman?" bata iya ce masa komai ba tayi qasa da kanta tana wasa da yatsun hannunta,kallabinta ya zame gashinta mai kyau da baqi ya bayyana zuba mata ido yayi ji yake kamar ya cinyeta saboda yarda yake jinta aransa.

Hannu yakai ya idasa fad'ar da kallabin gashin kanta ya shafa yace"Muwaddat kina da suma mai kyau sai kace ba'a 9j aka haifeki ba" jin yarda yake shafa gashin nata yasa tace"amma kace unguwa zan rakaka?" yace"eh to ba ga unguwar munzo ba" ya fad'a tare da jawota

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment