Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yarinyar,sanin halinsa kuma ya basa labarinsa da komai yasa ya amince ita ma Rabi ba asami matsala ta amince akasha biki.

Bayan bikinsu da watanni biyu Ibrahim ya je ya taho da Saratu bayan Rabi ta basa k'warin gwiwar hakan,yawa Malam Bawa alkhairi sosai da mak'otansu sannan suka taho Kano.

Saratu yarinya ce mai hankali da biyayya ga son aiki,hakan yasa sosai suje zamansu lafiya da Rabi wacce shekara biyu da auran ta haifi d'anta masha'Allah tubalakalla ranar suna yaro yaci MA'ARUF Kyakkyawan yaro mai matuqar kyau da annuri,Malam Sani mahaifin Rabi Kaka a gurin Ma'aruf yayi murna sosai da haihuwar yaron domin bayan tinkiya da Malam Ibrahim ya yankawa Ma'aruf haka shima ya sayi qatun ragonsa aka sake yankawa ga uban kaya da yasaya abokin nasa Ma'aruf Sarati kuwa ko yaushe yana goye a bayanta ita ce mai raino domin ko Rabi da ta haifi Ma'aruf bata kai kulawar da Saratu ke masa ba ko rabinta bata masa,ita ce wankansa goyansa sashi dariya tana masa wasa gashinsa fitsarinsa,shiyasa yaron ya taso da qaunarta matuqa.

Shekarun Ma'aruf biyar aka gane yana da lalurar ZUCIYA Abinda ya furgita iyayensa matuqa,duk da alokacin abin da sauqi,inda aka d'aura shi akan magani dai-dai da ƙarfinsu.....

*Silar samuwar Muwaddat....*
Page na gaba👯‍♀️👯‍♀️
*KARO ƊAYA...!*


©UMMU AFFAN


_GAWURTATTU UKU 2023🤟_


03


*SILAR SAMUWAR MUWADDAT!*
Alhaji Muttaka babban mai arzik'i ne,wanda ya tara dukiya mai tarin yawa,babban d'an kasuwa wanda yake da jiragen ruwa manya mallakinsa har guda biyar wanda ake shugo da kayayyaki yana da campany wanda suke qera kayan qarafa,bayan nan yana da company wanda ake shugo da motoci na alfarma,Allah ya hure masa dukiya mai tarin yawa wanda shi kansa ba zaice ga yawanta ba.

Alhaji Muttaka mutum ne mai ra'ayi ta tsattsauran ra'ayi bazamu kirasa mai k'yirki ba domin maganar gaskiya ko 'yan uwansa hakuri suke dashi bashi da sauqi ko kad'an,hatta talakawan unguwarsa baji dad'insa suke ba baida mutimci gashi da tarin dukiya sai dai baida temako kansa kawai ya sani.

Alhaji Muttaka matarsa guda Hajiya Safiya kamilar mace mai addini,sam halinsu ya ban-banta da mijinta inda ita ta kasance mace mai hakuri da tawakkali ga son mutane tana da tausayi matuqa. Duk tarin wannan dukiyar tasa a lokacin Allah bai basa haihuwa ba,gashi yana son haihuwar matuqa,shawara aka basa ya qara aure ko Safiya ce bata haihuwa,haka ya fara aure-aure ya auri mata kusan bakwai bayan nan amma fa da kin shekara guda yaga baki haihuba zai sake ki,Hajiya Safiya ce kawai,a gidan,akwai qaninsa *ABUBAKAR* wanda shi yake riqonsa qaninsa ne uwa daya uba daya iyayensu sun rasu hakan yasa rayuwar Abubakar duka ta dawo hannun Alhaji Muttaka,inda yasa shi makaranta yayi karatu mai zurfi,Alhaji Muttaka yana qaunar Abubakar tamkar d'an cikinsa sosai yake bashi dukkan gatan da ya dace qasar waje ya turasa karatunsa bayan kammala secondry nasa.

Yana qasar waje karatu Alhaji Muttaka ya kirasa cewa Hajiya Safiya ta sami ciki,sosai ya taya Yayan nasa farin ciki wanda yake ta murna. Bayan wata tara Safiya ta haifi d'anta kyakkyawa son kowa me matuqar kyau,saboda son da Alhaji muttaka kewa Abubakar yasa wa yaron sunansa *Abubakar* sai suke kiransa *Sadeeq* Abubakar da yaji labari yayi farin ciki inda ya qosa ya dawo yaga yaron amma Alhaji muttaka ya hanasa cewa sai ya kammala karatunsa zai dawo.

Shekarun Sadeeq biyu a duniya sannan Abubakar ya dawo,lokacin Sadeeq na tafiyarsa ko ina,Sadeeq d'an gata ne wanda iyayensa ke qauna matuqa bai nemi komai ya rasa ba haka Abubakar ke qaunarsa komai zai iya sayawa Sadeeq hakan yasa Sadeeq tasowa cikin farin ciki da shaqiyanci saboda bai nemi komai ya rasa ba,lokacin shekarun Sadeeq biyar kamar yarda Ma'aruf ma yake biyar,Abubakar ma'abocin zama qofar gida ne duk da Alhaji Muttaka baya so ya hanasa amma hakan baisa ba idan har ya dawo aiki to anan k'ofar gidan yake zama bisa dakali shi da Sadeeq wanda zai ta wasansa da Ball ko akan kekensa,shi kuma Abubakar yana aikin kallon BF ko pic na 'yan matansa dake turo masa tsira domin shi mutum ne haraji wato mai yawan sha'awa duk da yana amfani da tabilat amma idan har yana son sassauci to sai ya kalla,baya zina domin duk zamansa bai ta6a kusantar wata ba shi mutum ne mai qamqami amma hakan baisa yaqi kallon bf ko tsiraicin 'yan matan nasa ba,karatunsa ya hanasa aure yanzu kuma da yadawo Daddyn wato Alhaji muttaka yace sai ya sake zama mutum wai sai yasan ya tara wani abu ba haka kawai zaiyi aure ba,baija da shiba duk da yana byqatar auren domin bai iya musa masa akan komai.

Kasantuwarsu maqota da gidansu Ma'aruf hakan yasa duk sanda Saratu zata fito sai ya ganta saboda ita ce yarinya a gidan ita kad'aice hakan yasa duk wani aike ita ke zuwa lokacin shekarunta goma sha biyar tayi girma abinta domin tana da jikin girman ta zama budurwa,duk da hijabi take sawa gyale baya cikin tsarinta hakan baisa duk idan zata wuce ba Abubakar bai bita da kallon qurulla ba.

Tun farko ganinsa da ita yaji ta burgesa,bai ta6ajin zai iya kusantar wata mace ba tare da aure ba sai akanta,sai abin ma yadawo saboda ita kawai yake zama gurin,duk da magana bata ta6a shiga tsakaninsu ba,amma yana son ya mata maganar sai-dai tana da matuqar kwarjini Saratun hakan yasa ya kasa tarar ta.

Aka ce komai yana da mafari haka maganar take,wata rana da yamma jikin Ma'aruf yaqi dadi sosai zuciyarsa ke bugu da qarfi abinda ya tada hankalin duka mutanan gidan hakan yasa Malam yace Saratu taje ta kira mai napep sukaishi asibiti,ta fito cikin damuwa da alhini,tana fitowa shi kuma lokacin yana zaune qofar gidan ganin yanayinta yasan da damuwa tararta yayi da cewa"baiwar Allah lafiya?" a rikice ta d'ago hawaye na zubowa a fuskarta tace cike da damuwa"Yaron Yayana ne bashi da lafiya mai napep zan nema a kaisa asibiti" cikin damuwa shima yace"ayya Allah ya basa lafiya" har zata wuce sai ya sake shan gabanta yace"idan babu damuwa ko na d'auko mota na temaka muku?" cike da farin ciki tace"da kuwa mun gode sosai" yace"ba komai."

To a motar Abubakar aka kai *Ma'aruf* asibiti inda likitoci suka tabbatar zuciyarsa ta kumbura hankalinsu ya tashi jin irin maqudan kud'in da aka fad'a za'a masa aiki,Malam wato Baba kuka haka Umma da Saratu hankalinsu ya tashi,sosai Abubakar yaji tausayinsu yaje gurin likitan inda ya masa bayanin cewa idan har ba'ayu aikin cikin gaggawa ba yaron zai iya rasa ransa,Saratu kuka take sosai ta rasa ina zata soma ranta,Abubakar kuwa gani yayi wannan wata dama ce da zai sami cikar muradinsa da cika burinsa akan Saratun don haka ya kirata gefe yace"am menene ma sunanki?" muryarta na rawa tace"Saratu" yace"yawwa Saratu to naji na kuma amince zan biyawa yaron Yayanki kud'in maganin da za'a masa aiki" cike da farin ciki ta duqa qasa tace"mun gode sosai na rasa ma da bakin da zan maka godiya Allah ya biyaka" ta qarashe da zubar hawaye.

Ajiyar zuciya Abubakar yayi yace"amma akwai wani sharad'i fa guda d'aya" duk da gabanta ya fad'i tace"sharad'i kuma?sharad'i na me?" yana murmushi yace"ba wani abu mai wahala bane idan har kin amince zaki biyani da wannan abu to yanzu take zan biya kud'in harda na magungunansa na shekara biyar domin zan bar komai hannun likitan nan don naga kuna buqatan hakan" ai jin wannan alkhairi sai Saratu tace"na amince koma menene zan biyaka matuqar zaka mana wannan alkhairin" yace"idan yaron Yayanki yaji sauqi zan sanar miki komai" haka ya biya komai Malam Ibrahim da Umma Rabi sai godiya dasawa Abubakar albarka suke basu san abinda ya faru ba.

*Ma'aruf* ya sami sauqi sosai bayan sati guda da masa aikin sannan aka d'aurasa kan magani,inda suka gama magana da likitan wato Dr Musa cewa duk wata zasu dunga zuwa amsar magani har shekara biyar ta qare in Allah ya yarda.

Lokaci qanqani *Ma'aruf* ya dunga jin sauqi domin magunguna masu matuqar tsada ne,wad'anda suka dace da lalurarsa. Alhaji Muttaka ya gamawa Abubakar shirinsa na komawa qasar Ingila inda zai fara sabon aiki da qasar ta d'aukesa saboda qwarewarsa a fannin,babban company ne wanda duk suna hurd'ar cinikaiya a tsakaninsu.

Ana gobe zai tafi babban al'amarin ya faru,inda ya sanar da Saratu muradinsa na biyansa akan abinda ya musu ta hanyar mallaka masa budurcinta,inda maganar ta girgiza Saratu taqi amincewa shi kuma saboda ya k'wad'aitu da ita ya kasa hakuri,k'addara da rabon samuwar cikin *Muwaddat* yasa ya mata ta qarfin tsiya wato dai ya mata *Fyade* inda ya barta a sume,baiyi tunanin komai ba haka ya kinkimeta zuwa qofar gidandu ya yasar da ita a gurin,qarfe shidda na safiyar ranar jirginsu ya d'aga zuwa Ingila...

Lokacin da Malam Ibrahim ya tsinci Saratu cikin wannan yanayin sosai hankalinsa ya tashi,ya kira Umma Rabi ta fito ai kuka ta saka inda suka kamata zuwa cikin gida.

Ruwa ta fara d'aurawa a wuta sannan aka sama Saratu ruwan sanyi inda ta farfad'o tana kuka da ihu sosai tana cewa"kayi hakuri don Allah kayi hakuri karka keta min haddi komai zai iya baka amma banda wannan" Malam Ibrahim yana hawaye yace"Saratu me ya faru?waye ya aikata wannan mummunan zunubin akanki?" jin muryar Yayanta yasata bud'e ido a gigice ganin Malam Ibrahim Umma da kuma Ma'aruf yasata saurin rungume Umma tana kuka kamar ranta zai fita ta kasa magana idan banda rawa jikinta babu abinda yake,ita ma Umma kuka take haka Ma'aruf wanda yazo jikin Saratu yana kuka ta rungumesa da sauri.

Umma ta mata wanka ta gasa mata jiki sosai,Chemis Malam Ibrahim yaje ya amso mata maganin zazza6i dana rad'ad'i harda na barci domin yarda yaga qanwar tasa na kuka ya basa tausayi,haka Umma ta bata abinci qinci tayi da qyar tasha kunu kad'an sannan ta bata maganin tasha,ba a d'auki lokaci ba barci mai nauyi ya d'auketa,Malam Ibrahim da Umma haka sukayi ta jimamin abun da Allah wadai da wanda yama qanwarsa haka.

Ko da safe da Saratu ta farka da kuka ta tashi ta dunga yi ba sassautawa,Ma'aruf na tayata,Malam da Umma suka tambayeta abinda ya faru,bata 6oye musu ba ta sanar dasu abinda ya faru tana kuka sosai. Suma suna tayata Umma tace"yanzu mutane basa abu saboda Allah yanxu don Allah wannan ya dace kenan?saboda yana taqamar yana da kud'i da abinda zai iya komai sai ya aikata hakan" Malam yana sharar hawaye yace"Saratu me yasa tun farko baki sanar mini ba don Allah zaiwa Ma'aruf magani ba?idan da nasan abinda zai faru kenan wallahi da mun hak'ura komai ya sami bawa Allah na sane" haka su ka dunga kuka idan ka gansu a lokacin dole ka tausaya musu.

Umma tace"to yanzu kuma ya zamuyi kenan Malam?yace"ya kuwa zamuyi bayan hakuri kedai kinsan halin Alhaji Muttaka wallahi zai iya sawa a d'aure ni akan wannan maganar kawai mun barsu da Allah,Allah ya mana sakayya" ya idasa yana kuka da face majina.

Ma'aruf yana ta kallonsu domin sosai ya ke fahimtar baya nan su shekarunsa tara a lokacin kunsan yara da sauri fahimta ga riqe abu a k'wak'walwarsu.

Haka suka miqa lamuransu ga Allah inda Umma taci gaba da temakawa Saratu da 'yan hikimomi na mata da gashi domin ko asibiti basu kaita ba. Saratu ita ke kai Ma'aruf makaranta duk da lokacin yana primary 5 ne amma kasancewar makarantar tasu da nisa ta gwamnati kuma sai an tsallaka babban titi yasa dole ita ke kaisa.

Sau da yawa sukanga an wuce kai Sadeeq tasu makarantar da 'ya'yan manya da hutu a mota,kullum idan taga an bud'e gate d'in takan tura kanta ta hanga ko zata hango Abubakar amma bata ta6a ganinsa ba domin tana so ta gansa ko don ta amayar da abinda ke zuciyarta game dashi na tsanar da ta masa sai-dai bata ta6a sa'ar ganinsa ba.

Babban tashin hankalin da ya tun karo su shine,bayan wata uku ciki ya bayyana jikin Saratu wanda ke mugun bata wahala sosai take ciwo,hakan yasa dole Malam Ibrahim ya kaita asibiti bayan ya tara kud'in domin yanzu samunsa yana wuya,kasancewar rasuwa da surukin nasa yayi shekara biyu baya yasa komai ya jagule masa.

Allah ya amshi rayuwar Malam Sani mutumin k'warai sai-dai Addu'ar Allah yaji qansa amin,Gwajin farko likita yace tana d'auke da ciki na wata uku,fad'in tashin hankalin da suka tsinki kansu a wannan lokacin 6ata baki domin Umma kasa d'aurewa tayi saida ta dunga kuka. Malam kuwa kukan zuciya da yafi na fili ciwo,yayin da Saratu sumanta uku,shi kansa likitan ya tausaya musu ainun.

Bayan sun dawo gida Umma tace"Malam maganar 6oye-6oye fa dole a barta domin bazai yuwu ace ba a sanar da uban cikin nan cewa ta sami ciki ba" Yace"tsorona daya tsorona yarda zasu d'auki maganar nan Rabi banda kud'i ban ba wani ajiyar su ba,idan suka yi qarata fa?" cikin kuka tace"to Malam ya kake so muyi?ba mu da wata hanya fa bayan wannan."

Malam yace"to shi kenan mu gwada mu gani" haka suka tasa Saratu gaba zuwa gidan wacce duk ta wain kod'e ta zama wata iri,tana riqe da hannun Ma'aruf,to maigadi shima da qar ya yarda suka shiga ciki sai da suka dunga had'asa Allah da Annabi ya barsu.

Knocking suka fara bayan isarsu bakin qofar parlourn,wajen minti talatin sannan mai aikinsu Larai tazo ta bud'e qofar,ta basu hanya suka shugo.

Alhaji Muttaka da Hajiya Safiya sai d'ansu Sadeeq da ke wasa da Lapton games d'insa ta yara,sallama suka musu. Alhaji muttaka mai d'ago ba yana karanta jarida Hajiyar ce ta amsa musu da fara'a,zubewa qasa sukayi suna gaishe su ta amsa cikin fara'a,yayin da Alhaji muttaka ko d'ago fuska baiyi ba bare ya amsa musu.

Cikin kuka Malam ya fara bayani yace"mu ne maqotanku dake gida na hannun damanku,daman akan wannan qanwar tawa ne da d'an wajenku Abubakar ya ma Fyad'e shine ciki ya shiga muka ce bari muzo mu sanar da ku" "Fyad'e!Ciki!" Alhaji muttaka ya fad'a cikin qaraji da d'aga murya.

Malam zaiyi magana yayi saurin d'aga masa hannu"dakata!Malam Ibrahim kake ko Iro kai koma menene wallahi bazan k'yaleka ba tun da kawa qanina sharri" Da sauri Hajiya Safiya ta kallesa cikin 6acin rai da damuwa tace"amma yana da kyau kaji ta bakinsu ko?wani kallo ya mata tare da jan tsaki mtsuuwww!ya zawo wayarsa Number d'in Abubakar ya kira"Hello Alhajina barka da yamma" shine abinda Abubakar ya fad'a yana d'aga wayar,da yake a hansfree ya sakata dukansu suna jin maganarsa,cikin muryar damuwa yace"Abubakar wacce 'yace kawa fyad'e" daga ji zaka gane muryarsa a rikice take yace"fya...fyade kuma Alhaji ni da bana qasar kuma?,yace"to nima abinda na gani kenan,sunje 'yarsu ta kwaso ciki sunzo sunce min wai ka ma 'yarsu fyade har ciki ya shiga zasu liqa mana tsiya aini nasan halinka" cikin wata irin murya ya furta" _CIKI!CIKI KUMA ALHAJI?_ Yace"eh wai cikinka to wallahi tunda sharri suka maka sai nayi sharia dasu bazan barsu ba" qittt! ya yanke kiran,Malam da Umma Rabi tuni suka fara hawaye yayin da Hajiya Safiya jikinta yayi sanyi matuqa kuma daga jin yarda taji muryar Abubakar tasan dole akwai magana a bakinsa,cikin masifa ya miqe tsaye tare da nuna musu hanya yace"ku tashi ku bar min gida matsiyatan banza kuma ka saurari sammaci domin bazan barka ka 6ata min suna a banza ba gara nawa tubkar hanci idan ma biyanka akayi ka 6atani za kayi bayani."

"Get out!" ya fad'a yana nuna musu hanya,jiki ya sanyaye suka miqe Umma ta kama Saratu wacce kwata-kwata bata gane abinda ake ciki suka fita,Alhaji muttaka na biye dasu yana zagi har gate,sannan ya farawa maigadi masifa"kai na lura bakasan aikinka ba don haka zama da kai bai dace dani ba" maigadi duqa yayi yana basa hakuri dacewa ba san wani abun suka zo yi ba ya d'auka masu neman temako ne da suka saba zuwa......
*KARO ƊAYA...!*


©UMMU AFFAN


_GAWURTATTU UKU 2023🤟_


04


Da kyar Alhaji Muttaka yawa Maigadi hakuri bayan ya tabbatar masa ba ma suba duk wad'anda suka sake zuwa nemansa yace su kirasa a waya idan kuwa basu da number d'insa to kar ya sake ya barsu su shugo masa gida.

Hajiya Safiya wacce hankalinta ya tashi matuqa su Malam suka bata tausayi,suna fita ta wuce bedroom d'inta tare da kiran Abubakar,murya a sanyaye ya amsa mata sallama cikin sanyi murya tace"Abubakar kaji tsoran Allah kasan zaka komawa mahaliccinka cikinka ne?ko banaka bane?", hawaye yake ta maqewa amma sai da ya fashe da kuka yace"Hajiya wallahi nawa ne tunda Alhaji ya min maganar nakasa natsuwa,amma wallahi tsautsayi ne da qaddara ba halina bane don Allah Hajiya kisan abinda zakiyi amma ban son Alhaji yasan wannan maganar"

Ajiyar zuciya Hajiya tayu tace"tun tuni jikina ya bani hakan amma gaskiya Abubakar baka kyauta ba,idan kaga yarinyar da ahlinta halin da suke ciki abin zai baka tausayi" cikin kuka yace"wallahi qaddara ce da son zuciya tabbas na yarda harda son zuciya tawa amma ba halina bane,na amshi cikin domin nasan nawa ne,ni na fara sanin Saratu kuma nasan biye-biyen maza ba halinta bane,Hajiya zan turo miki da kud'i don Allah a kula da Saratu da cikin da ke jikinta ina son abuna" ya qarashe da kuka"Abubakar kayi shuru tabbas kukanka ya nuna min kana cikin damuwa da lamarin sannan ba sai ka turo kimai ba ni mai maka komai ce" tace da shi,godiya ya dunga mata sannan sukayi sallama bayan ya qara roqarta kar ta sanar da Yayansa tace"to ka masa magana kar yayi qararsu kasan dai talakawa ne basu da abinda zasu kare kansu" yace"Insha'Allahu" da haka sukayi sallama.

Acen gidan Malam kuwa suna cikin damuwa domin rasa sukunun Saratu da sukayi wacce ta kasa magana sai-dai bin mutane da ido ba uhmmm ba Ummm-ummmm abinda ya d'aga hankulansu matuqa.

Haka rayuwa taci gaba Saratu bata lafiya sosai,Hajiya Safiya ita ke kula da lalurar Saratu a bayan idanuwan Alhaji muttaka wanda Abubakar yasa ya janye daga qudirinsa na kaisu kotu,inda ya masa dad'in bakin cewa idan ya kaisu shine zaisa sunansa ya 6aci idan yayi qararsu tamkar ya tonawa kansa asiri ne,da hakan yasa ya hakura amma sosai yake jin zafin Malam Ibrahim d'in.

A haka har cikin Saratu ya kai wata tara wacce bata iya komai,damuwar da tasawa zuciyarta yasa mata ciwo mai tsanani,inda take kwance cikin ciwo Satinta biyu asibiti tana kwasar azaba inda haihuwa taqi zuwa,hankalinsu ya tashi Hajiya tayiwa Saratu kuka tamkar me,likita yace"sai-dai a mata aiki" nan take suka amince domin Saratun na cikin wani hali,Abubakar kuwa duk bayan minti biyar sai ya kira wayar Hajiya Safiya yaji ko ta haihu?.

Shi kansa hankalinsa a mugun tashe yake. Yana cikin yanayi na damuwa da danasani addu'arsa kar Saratu ta mutu a sanadiyyarsa.

Ammata aiki kuma an ciro kyakkyawar yarinya sak Abubakar mai kyawun gaske fara sol.Baby lafiyarta qalau yayin da uwar ke cikin halin mutuwa ko rayuwa. Umma kuka kawai take haka Ma'aruf baya cikin hankalinsa hatta makaranta ajiyeta yayi domin baya cikin hankalinsa gashi sun kusa zana jarabawar kammala primary amma halin da Auntynsa Saratu take ciki yasa ko makarantar mancewa da ita ya ke,to mai kaisa ba lafiya,sosai ahlin suke cikin damuwa da tashin hankali.

Hajiya Safiya ta turawa Abubakar photon Jarira wanda ya qurawa photon idanu yana kuka sosai yarinyar bata da maraba dashi hasken fata ne kawai na uwarta amma komai nasa ne,wata irin qaunar yarinyar ke shigarsa ta ko ina qamqame wayar yayi a qirjinsa yana kuka sosai,tare da rad'a mata suna da cewa *KHADIJATUL MUWADDAT!*

Inda ya sanar da Hajiya Safiya sunan da yasawa yarinyar.

Ta fad'awa su Malam,ganin hankalinsu ba kwance yake ba,yasa bata sanar musu ba,sai da Sadeeq ya dameta da tambaya wai sunan babyn kamar yarda shima Ma'aruf ya ishe Umma wai sunan Babyn,lokacin suna tare domin sosai suke fada akan d'aukar babyn,tace"musu to sunan Babynku *Khadeejatu* da sauri Ma'aruf yace" *Muwaddat!* murmushi Hajiya tayi tace"wannan gaskiya ne" Sadeeq ya farajin haushi akan me Ma'aruf zai ce Muwaddat sai shi yaqi kiranta haka yana ce mata *Khady* ita dai Hajiya murmushi kawai tayi tana mamakin yaran sosai.

Saratu kusan watanta guda a asibiti sannan ta sami lafiya duk da dai bawai kamar yarda take da ba amma da sauqi har zuwa lokacin bata cewa kowa komai sai dai kallo da ido.

Bayan wata guda da haihuwar Muwaddat ita ma Hajiya Safiya ta sake haihuwar 'yarta Salma.

Shekarar Muwaddat biyu a duniya Saratu ta kwanta wani ciwo inda ko magana bata iyawa daman kuma tun bayan haihuwar Muwaddat take cikin wannan hali tana dannewa ne kawai haka tayi ciwon dare d'aya cikin daren juma'a Allah ya amshi rayuwarta😭Allahu akbar rai yayi halinsa daman kowa kuma lokacinsa yake jira.

Baba Malam da Umma sunji mutuwar Saratu hakkun haka Hajiya Safiya lokacin da Abubakar yaji ai nan take ya suma Allah yasa ma a cikin office yake lokacin akwai wani abokinsa da suke tattaunawa aiko shine ya kaisa asibiti sai da ya kwana sannan ya dawo hayyacin sa idan banda kuka da kiran sunan Saratu babu abinda yake yana cewa "ki yafemin Saratu wallahi qaddara ce amma ban ta6a ba sai akanki."

Haka akayi zaman makokin Saratu inda har akayi bakwai Umma ta ci gaba da riqon Muwaddat wacce son da suke mata har yazarta na 'ya'yan cikinsu,haka ma Hajiya tana qaunar Muwaddat sosai.

Sadeeq kuwa in har baida Skul to yana gidansu Ma'aruf gurin Muwaddat,tun Alhaji muttaka bai sani har ya fara sani inda yace ya dena zuwa gidan talakawa" shi kuma yace"Daddy nima na tsane su wllh Muwaddat kawai nake so,don Allah ka dawo mana da ita gidanmu" yace"akan me?ai iyayenta bazasu bari ba" sosai ake rigima da Sadeeq akan Muwaddat tun abin bai damun iyayensa har ya fara damunsu musamman Alhaji muttaka a ganinsa akan me d'an nasa zai nacewa d'iyar matsiyata bayan shima ga qanwarsa nan. lokacin da yaje da niyyar ganin wacece Muwaddat anan ne ya gane yarinyar da aka liqawa d'an uwansa cikin ta ne wai ita ce D'ansa Sadeeq mafi so yuwa a zuciyarsa ke magun qauna irin haka wacce ko cikin dare da hirarta ya ke barci.

Anyi tsiya sosai inda ya nuna idan harma asiri sukawa d'ansa to suyi saurin warwaresa Malam yace"ai bamu ke kiransa ba,idan ya isa ya hana d'ansa zuwa gidansu suma basa gayyatarsa..

Wannan abu yasa Alhaji muttaka hana Sadeeq zuwa gidan amma yaro yaqi,da yadawo masa kulle kuwa sai kawai ya fara ciwo,abin tun bai damun Alhaji muttaka har ya fara Hajiya kuwa sosai ta damu da wannan halin mijin nata bata so amma bata da yarda xata yi,ko da ta sanarwa Abubakar ranar kuka ya wuni ganin yarda Yayan nasa ke gudun gudar jinin tasa da yake so fiye da kansa.

Sadeeq yana zana jarabawar Primary Alhaji Muttaka ya d'auke sai sai Ingila ya miqawa Abubakar shi,wanda ya auri wata baturiya suna zamansu acen,ai kuwa ta kama ma Sadeeq ta riqe qam.

Nan Abubakar ya mayar dashi makaranta inda yaci gaba da karatunsa acan,Abubakar da Messi wato matarsa basujin kunyar yin komai a gaban Sadeeq,sa6anin iyayensa da ko kusa da juna bai ta6a ganin su ba zadai su zauna kujera daya amma bai ta6a ganin ko ta6a mahaifiyarsa mahaifinsa nayi a gabansa ba,sa6anin Daddy Abubakar da matarsa Mummy Messi,haka zaiga sun rungumi juna yana kissing d'inta ko tana yi masa yaga yana ta6a nonuwanta da sauransu saduwa ne kawai basa a gabansa amma duk wani tsotse-tsotsensu a gabansa suke saidai yaga ya d'auketa chak yayi bedroom,a haka rayuwarsa ta taso kuma idan ya fita ma abinda yake gani kenan,hakan yasa ya taso da son ta6a mata ko a cikin class haka ya ke ta6a mata ko yace zai tsotsi bakinsu ko kuma ya dunga ta6a musu nonuwa tun bayayin hakan da wata manufa a tunaninsa hakan dai-dai ne ganin Daddynsa haka suke,daga baya ya fara jin dad'in abun tun yana qanqanin yaro d'an secondry yasan ya ta6a mace yaji dad'i,balle da ya had'u da abokan banza sai suka fara shaye-shaye,Daddy wato Abubakar bai san halin da Sadeeq ya ke ciki ba amma Mum tasan komai bata hanasa domin ai a ganinta duk wayewa ce balle ba musulma ba ce.

Haka rayuwar Sadeeq ta ci gaba har xuwa kammala secondry d'insa bai ta6a zuwa lokacin tuni yasan mata domin mugun manemin mata ne duk Dad baisan halin da yake ciki ba saboda yana futa aiki sai yamma.

Haka har Sadeeq ya kammala duka karatunsa a lokacin burinsa shine ya dawo gida Nigeria saboda Muwaddat duk da Mahaifinsa ya rabasu a zahiri amma tun wancen lokacin har zuwa yanzu da tunaninta yake kwana yasan zuwa yanzu Muwaddat d'insa tayi girma sosai,duk kan mafarkinsa akanta yake kullum mafarkinsa

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment