Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zai faɗa, a wahale cikin In-ina wacce yake son ya saba magana da ita ya mirgina kaɗan yana riƙe kansa da hannu bibbiyu ya ce "man ta ta manta kawai, ya ya yaushe za za kazo?" Murmushi Khalil ya yi cike da ƙaunar Sheikh Aliyu haydar ya ce "Zamu zo da mai martaba wajan Hakimi, I think I will spend my two weeks vacation with you in Kano" jinjina kai kawai Sheikh ya yi ba tare da ya ce komai ba. "You are just afraid of women because you see yourself as a Sheikh, women are the happiness of a man, try and see" Girgiza kai kawai Sheikh ya yi ba tare da ya ce komai ba ya kashe vedio call ɗin.
Umar-khan ne ke driving a hankali idanunsa akan titi amma hankalinsu na kan Sheikh dake manyan mota cikin wata dakakkiyar shadda fara tas ya ɗora golden ɗin Alkyabba sai rawanin daya ƙarawa fuskarsa kyau da haiba ya yi wani irin kyau kamar Balarabe ƙamshin Roja ya cika motar sosai. Yana ki shingiɗe a bayan motar tunani yadda zai sauya ya koma kamar yadda father yake buƙata, a haka suka ƙarasa Wani Restaurant mai kyau da tsari mara hayaniya, Umar-khan ya yi parking kasancewar fitar sirri ce yasa babu wasu masu take masa baya, cikin sauri ya buɗe Sheikh mota a nutse ya fito yana gyara zaman alkyabbar jikinsa tare da goya hannunsa a baya cikin kamala ya yi gaba Umar-khan na biye da shi zuwa cikin Restaurant ɗin. Zama Sheikh ya yi tare da kallon mutanan da zasu tattauna dasu, bayan sun gaida Sheikh ya ɗaga musu kai suka shiga nuna masa zanan bank ɗin daya buƙata na reshe uku, kaduna, Abuja, da Lagos. Baya cewa komai sai da Umar-khan suke tattaunawa gani ya yi zanan bai masa ba, domin babban bank yake so wanda ba a taɓa yin mai girman sa ba. Hakan ya sa ya amshi carbon paper da pen a nutse ya zana yadda yake so, zanan ya bawa ma'aikatan mamaki abin da basu sani ba, kaɗan kenan daga cikin baiwar Sheikh duk abin da ya sanya ransa yana gwadawa yake yi daidai. Sallama sukai bayan anyi musu transfer miliyoyin kuɗi domin fara aiki gadan-gadan. Ɓangaren Kamfanin sarrafa shinkafa ma tuni aiki ya yi nisa, ya yi ordern injina masu kyau daga Chaina. A gajiye ya dawo gida idanunsa na rufewa kansa ya sakarwa shower lokacin 1:30 ya saba barci tsakanin azahar zuwa sallar asr, fresh milk ya tsiyaya a cup tare da zuba honey ya sha kaɗan ya wanke baki, yana kwanciya barci ya ɗauke shi daman ya riga daya saba.
Washegari ya kama weekend Sheikh bai san meke faruwa ba, sai daya farka yaji labarin tun 7 su Uncle Haroon da Abba Hakimi tare da Baffansa suka nufi garin Yola nema masa aure. Ko ajikinsa bai ɗauki auren matsayin wani abu, shi dai ya san ko farcen mace bai taɓa sha'awa ba balle ya birgensa. Da yamma su Abba Hakimi suka dawo cikin jin daɗin an basu auren Zahrah nan da sati mai kamawa za a ɗaura aure. Kasancewar yau Friday ne ya sanya Sheikh ya shirya cikin wata bugaggiyar shadda fara tas da ita mai ɗinki jamper da babbar riga, bai sanya hula ba sai hirami daya saka a saman sumar kansa ya ɗauki zagayayyen abun nan na larabawa Black colour ya ɗora saman hiramin, shekarunsa suka bayyana a jikinsa, domin kowa ya kalli Sheikh Aliyu haydar ya san ba yaro bane, girma ya fara hawa jikinsa babu mamaki ya yi aure a same shi da yara biyar haka, shekaru 34 ba wasa bane ba. Kai tsaye babban masallacin juma'a ya nufa sai da ya yi huɗu ba sosai mai ratsa jiki akan tsaida sallah a lokacin ta, tunda duk In-inar Sheikh inda karatu zai yi yana farawa ake nemanta a rasa. Bayan idar da Sallah ya nufi zaga gidan marayu kamar yadda ya saɓa idan yana ƙasa, a hankali yake tafiya hannunsa goye a bayansa kansa a ƙasa fitowar su kenan daga gidan marayu zasu shiga mota yaje gida wajan Mother, kamar daga sama wata budurwa kyakkyawa ajin farko ta tsaya a gabansu da sauri Umar-khan da Saif-wazir suka sha gabanta tun kafin securities su ƙarasu bakinta na rawa ta ce "Don Allah ku barni nayi magana da shi, na jima ina son haɗuwa da shi" Umar-khan ya daka mata tsawa ya ce "Baya buƙatar ganin kowa, kuma a mu'amalar shi baya yi da mata ki nemi wani wajan" A nutse Sheikh ya dakata tare da juyawa idanunsa zuwa inda budurwar take, waro fararen idanunsa waje ya yi yana mamakin abin da ya haɗa shi da bayin Allan nan da suke bibiyar shi. Murmushi mai laushi ya yi ba tare daya bari kowa ya gansa ba, yana mai ƙarewar budurwar kallo musamman ƙafarta. "Ka taimaka mini daga yanzu ba zan sake zuwa inda yake ba" Umar-khan ya yi mata wani ban zan kallo ya ce "Ke ko mayya ce ke baki isa kije inda Sheikh yake ba, kunne masu ƙullawa mutane sharri ko?" Sosai taji zafin maganar Umar-khan sai kawai ta juya kamar zata kifa sbd sauri. Tana barin wajan Umar-khan ya dafe kansa Saif-wazir ya ce "Are you okay?" Ya ce "Kai na ke ciwo, zazzaɓi nake ji" Umar-khan ya faɗa bakinsa na rawa kafin kace wani abu wani zazzafan zazzaɓi ya rufe Umar-khan. Girgiza kai kawai Sheikh ya yi domin ya san za a rina waya aiki Khan musayar yawo da aljani?.

Da sauri Hamma Yabi ya shigo bukkarsu hannunsu ɗauke da kuɗi ya kalli Danejo wacce take sumar kanta ya ce "shai Alhmd kuɗi shun samu gobe zan kai Dada asibitin burni" murmushi Danejo tayi wanda ya ƙara fidda kyanta na fili ta ce "Kai Allah abin gdy Dadata zata samu lafiya yau ba zan barci ba sbd farin ciki aradu" Hamma Yabi ya kalli Dada dake kwance kamar haka cikin farin ciki ya ce "Insha Allah, da sassafe sai burni" fita ya yi farin ciki ya cika zuciyar Danejo Dada zata tashi su koma yadda suke rayuwa a baya. Hamma yabi bai dawo ba sai dare riƙe da ƙullin buduri da ƙosai mai zafi wanda ake a can wajan gari. Sai dai ko zama bai ba suka fara jiyo harbi ta ko wanne waje alamar ƴan fashi ne suka shigo cikin Rugar Rome. "Bone Hamma harbi harbi....," Bata ƙarasa faɗa ba suka ji an shigo bukkarsu wani mutum mai riƙe da bindiga ya kalli Hamma Yabi yana faɗin "Kuɗi,kawo kuɗi bamu da lokaci" jikin Hamma Yabi na rawa ya ce "Ba kuɗi bamu da shi" mutumin ya yi wata dry sosai ya ce "Babu? idan na bincika na samu duk hukuncin dana ɗauka akan kai ka sani" yana faɗin hakan ya fara bincike bukkar daga can waje harbi ake ta ko wanne sashe, cikin rashin sa a mutumin yaga kuɗin da Hamma Yabi zai kai Dada asibiti "Aradun Allah kuɗin asibiti ne, kayi mini ka taimaka Dada zamu bawa lafiya.....," Harbin da akaiwa Hamma Yabi a ciki ya sanya ya fasa ƙara tare da faɗuwa ƙasa ihu Danejo ta fasa ganin yadda jini ke zuba a jikin Hamma Yabi tana ƙoƙarin zuwa inda yake mutumin ya ƙara sakarwa Hamma harbi a tsakiyar kansa......


Wannan littafin na kuɗi zaka samu book 1, 2 akan ₦500 daga farkon labarin har ƙarshe ka tura ta wannan account ɗin 6850917335 Na'ima Shu'aibu Sulaiman fidelity bank shaidar biya 08119237616.
*🌈 IDAN BA KE 🌈*

*_Arewabooks@Nimcyluv_*

14......
Cikin ƙaramin lokaci ƴan Rugar Rome suka shiga cikin tashin hankali musamman wajan su Danejo. Ko kuka ta kasa ta kafe gawar Hamma Yabi da kallo sai Ajjiyar zuciya take, shatu na gefe ta ƙanƙame jikin Dada wacce ke sanƙame bata san meke faruwa ba sbd halin da take ciki. Bata taɓa ganin anyi kisan kai a gabanta ba, yaushe gashi an kashe mata yaya wanda ke kula dasu shi kaɗai ya rage musu. Halisa Danejo Rome ta shiga halin firgici ita kaɗai tai ta razana har lokacin idanunta bai motsa daka kan gawar Hamma Yabi ba a haka Asuba ta risketa. Sarkin ruga da Giɗaɗo ne suka shigo bukkarsu Danejo ba neman iso domin basu damu da cewa Dada matar da za a nemi aminci a wajen ta bace. "Allahu Akbar Allahu ya jiƙan Yabi shai abu bai kyau ba sam" Sarkin ruga ya girgiza kai ya ce "Allah sharki aradu harbi har biyu dole ya mutu" da sauri Danejo ta miƙe jikinta na rawa ta kama hannun Giɗaɗo ta ce "Da gaske Hamma Yabi mutuwa ya yi? Da gaske ba zan sake ganin Hamma ba?" Ta faɗa cikin rauwanin muryar kana ganinta kasan damuwa ta jima da kama zuciyarta ta samu waje ta zauna. "Ya mutu mana kamar yadda Baffanku ya mutu ba zai dawo ba" ƙurr ta kafe Giɗaɗo da idanu kafin taja numfashi mai tsayi sai kuma ta sulale a wajan ta faɗi babu numfashi.
A hankali take buɗe idanunta wanda sukai mata nauyi, hannunta ta kai tare da dafa kanta wanda yake mata ciwo sbd barcin data daɗe ta nayi. "Sannu kin farka Danejo?" Shatu ta furta cikin murnar ganin Danejon na motsi bayan suman da tayi. Danejo ta juya tana kallon Shatu kafin a hankali ta buɗe baki ta ce "Ina Hamma Yabi? Ya tafi da Dada asibitin burni?" Shatu tayi saurin faɗin "Hamma Yabi ya mutu ai kuma har an rufe shi a ƙasa" zuciyar Danejo ta buga da ƙarfi tana runtse idanunta sosai tsoro da fargabar makamar rayuwarsu ta dirar mata a zuciya, yaya za tayi da Dada? Ina zata samu kuɗin asibiti ko shanu zata siyar? Mai Hamma Yabi ya yiwa wannan mutunan da shi kaɗai kawai suka kashe cikin Rugar Rome?.
Juyawa tayi ta sake kallon Dada wacce kawo yanzu ko motsi ba tayi ruwa ma idan aka bata ta gefen baki yake zubewa, hawayen da take maƙalewa suka sakko daga cikin idanunta Shatu wacce ke shirin yin kuka ta ce "Kuka ki ke Danejo? Me akai miki ba ga Dada ba muna tare da ita?" Danejo ta goge idanunta da kyau ta ce "Ba kuka nake ba, ki zauna wajan Dada bari naje wajan sarkin ruga na dawo" miƙewa tayi jikinta sanye da fararen kaya na Fulani sumar kanta ta naɗeta da wani zare mai ɗauke da kuran duwatsu masu kyau. Kanta a ƙasa take tafiya cikin sanyin jiki kamar ko yaushe a haka ta ƙarasa bukkar su Sarkin ruga ta tsaya daga waje tana neman iso. Matar Sarkin ruga ta ce "A'a Danejo ne bismillah shigo" kamar ba zata shiga ba sai kuma ta shiga ta samu Sarkin ruga zaune yana shan kindirmo a diririce ta ce. "Jamɓanduna. _Ina kwana_" Ya ce "Jamni.. _lafiya_" zata sake yi masa wata gaisuwar ya dakatar da ita da faɗin "mene ya kawo ki?" Kanta a ƙasa tana wasa da yatsunta ta ce. "daman cewa nayi ko zaka sayi nagge guda biyar daga cikin garkenmu?" Kallon tsaf ya yi mata yana sakin murmushi kafin ya ce.
"Yabi bai faɗa miki ɗan cewa gaba ɗaya ba naggenku bane? Kiwo kawai aka baku?" Cikin rashin fahimtar maganar Sarkin ruga Danejo ta ɗaga kanta da sauri ta kalle shi tana faɗin "Dada ta sanar mini gaba ɗaya garken na Baffanmu ne, shanuwan sa ne, kuma kowa ya sani Hamma Yabi ma yasan da haka" Ya ce "E, to buɗe kunne kiji kaf cikin garken naggen nan guda biyu ne naku, sauran duk mallakina ne kuma yanzu zan ɗauka aje kasuwar burni a siyar dasu, idan kina buƙata sai a haɗa da guda biyun naku a siyar daga nan sai ku biyawa Baffan naku bashin da ake binsa ma" kasa cewa komai tayi ganin ƙarfen ƙafa da ake shirin yi musu, wanne irin son zuciya ne Wannan? A nagge sama da hamsin ace guda biyu ne nasu? Me ya sa Hamma Yabi bai taɓa cewa naggen Sarkin ruga bane? Da gaske nasa ɗin ne ko ba haka bane?. Jiki a saɓule ta dawo gida zazzaɓi na rufeta sbd fargaba. Kenan tana ji tana gani Dada zata sake mutuwa ta barsu basu da kowa a duniya?.

Sheikh Aliyu haydar Aliyu na zaune yana duba yadda ginin bankunan guda biyu suka ɗauki harami cikin ƙaramin lokaci tare da kamfanin sarrafa shinkafa. A nutse cikin kulawa da haibarsa kamar kullum ya miƙawa Umar-khan Album ɗin. "Ina fatan komai ya yi yadda kake so?" Kallo ɗaya Sheikh ya yi wa Umar-khan a hankali ya juya kansa yana mai jinjina shi a nutse alamar "Ya yi" Umar-khan yai murmushi kaɗan yana jinjina halin Sheikh da yawan lokaci ba tare da ya ce komai ba ya juya ya fita. Ɓoyayyiyar Ajjiyar zuciya ya sauke yana mai miƙe ƙafafuwan shi saman table a hankali ya fara tunanin yadda zai gina rayuwar shi wanda zai sanya father farin ciki duk ƙoƙarin shi na gano abin da ke sanya father yaji zafin shi har haka ya rasa, da yawan lokaci abubuwan na damun shi nunawa ne kawai ba ya yi. Zuciyar shi na shiga tunani na tsayin lokaci. Miƙewa ya yi cikin kulawa ya shiga takawa a parlourn na shi, ƙarar wayar shi ta dakatar da shi daga tunanin da yake jin ringtone ɗin is different ya sanya ya fahimci mai kiran na shi. Farar Alkyabbar shi mai fidda ƙamshin Roja ya ɗauka tare da ɗorawa saman jallabiyar jikinsa banda dole ko hannun shi bai son a gani sbd tsarin halittar jikin na shi. Kansa a ƙasa ya nufi Main parlour babu kowa sai Hajjir bai ko kalle ta ba ya nufi sashin Abba Hakimi. A zaune ya same shi saman ladduma gabansa ɗauke da kayan marmari sai ƙwaryar zuba da kuma ta fura da nono. Zama ya yi yana fuskantar Abban na shi cikin mutunci bakin na motsa wa alamar gaisuwa Abba Hakimi ya yi murmushi ya ce. "Ba sai kace ba, Allhamdulillah" Sheikh Aliyu a lumshe idanunsa yana mamakin yadda Abba Hakimi ke fahimtar zuciyarshi da yawan lokuta.
"Naga baka shirin auren naka, kamar dai you're not ready if i not mistaken?" Sheikh ya buɗe idanu da kyau akan Abba Hakimi cikin mantuwa domin gaba ɗaya ya manta da batun komai cikin In-ina yana riƙe Alkyabbar dake jikinsa da kyau tare da karkatar da kansa yana rufe idanu ya ce. "A...a...au au aure kuma A a Abba?" "E, Aure mana Sheikh haka za ka yi ta zama babu aure ni ma da kaina ban goyi bayan hakan ba, kayi aure kamar yadda Engineer ya buƙata ko dan samun kusanci da shi" Sheikh zai magana Abba Hakimi ya ƙara ɗaga masa hannu ya ce.
"Kada kai musu, ka amince Allah ya sanya albarka, Engineer ya buƙata ka tura kuɗin lefin ita yarinyar tun da ba auren kake so ba, yi maka za ayi na fanshe ka na bada kuɗin lefen kamar yadda suka ce 2.5m zai isa komai na lefen" Sheikh ya ware idanu jin wai 2.5m kuɗin lefen yarinyar da ko sanin kamarta bai ba,baya buƙatar kuma ya sani ɗin.
Cikin kyakkyawan lafazi Sheikh ya sake furta "2.. 2.. 2.5m A aaaa Abba yai yai yawa fa?" Abba Hakimi ya girgiza kansa yana mmkin yadda Sheikh babu abin da ya sani dan gane da rayuwar mace.

"Meke sani Sheikh Aliyu? Kasan kayan mata da tsada, ko kai Alkyabbar nawa kake siya? Duk Alkyabbar ka tafi nawa kuɗi sosai, kuma a arziƙin da Ubangiji ya yi maka dan an taɓa 2.5m har wani abu ne?" Shafa gemunsa zuwa sajansa kawai Sheikh ya yi bai damu da auren ba, amma yaji daɗin yadda Abba Hakimi ke nuna kulawarsa ga duk abin da ya shafe shi.
Abba Hakimi bai nunawa Sheikh ya san komai ga Bankunan da yake shirin buɗewa ba, dan haka sai ya ce "Ka tashi kaje can gidan, kuɗi kuma daman hakƙina ne na aurar da kai daga nan har sadaki" jin Sheikh yaƙi cewa komai ya sanya Abba Hakimi ɗago kansa ganin Sheikh ɗin ya yi zaune jingine jikin kujera ya dafe kansa da hannu bibbiyu zufa na yanko masa tsakanin gashinsa jikinsa na rawa kaɗan kaɗan.
Girgiza kai kawai Abba Hakimi ya yi tare da jawo rubutun da ya yi da safe ya tsiyaya a cup ya zuba zuma a ciki ya juya kaɗan tare da ajjiyeta gefe guda zuwa lokacin da Sheikh ɗin zai daidai a hankali shi kuma yaci gaba da duba wani littafin Tafsir.

Mother na zaune tana girgiza ƙafa cikin damuwa take kallon tilin kayan lefen dake parlourn, da sunan kayan lefen yarinyar da Sheikh zai aura. Yaya Halima ta ce.
"Na daɗe banga kayan lefe mai yawan haka ba, shi Sheikh ɗin har nawa ya bada?" Motar ba ta ce komai ba sai Dr A'isha data kalli kayan da kyau ta ce. "Kalli fa Yaya iya gold guda biyar ne, Wallahi sai na ɗaukar wa su Maimoon kowa ɗaya abar shegiya da ɗaya kawai" Mother ta kalli Dr A'isha ta ce. "Tsinke na kayan nan babu mai ajjiye mini cikin gidan nan, balle su Maimoon su saka ba su rasa komai ba, a barwa wacce aka siyawa". Dr A'isha ta ce "Amma Barrister kalli kayan fa? Ni dai sai na ɗauka dukiya ai ba hauka bane" cikin faɗa Mother ta ce "Wai meke damunki haka A'isha akwai abin da kika rasa ne balle kayan nan su dameki idan su kike let me know I'll buy it for you" a sanyaye Dr A'isha ta cewa yayat tata "Am sorry Yaya"... "Sai haƙuri Barrister" cewar Yaya Halima wacce take babba a cikinsu. Miƙewa kawai Mother tai tana faɗin "Idan ban yi haƙuri ba kashe kai na zan? Ina nan dai wlh sai na aurawa Sheikh wata macan ya haɗa mata biyu" Dr A'isha ta ce "Wai ya kaga Sheikh da mata biyu" Dr A'isha ta kalli Yaya Halima ta ce "Nifa ina da shawara Yaya Halima, mai zai hana mu kai kayan lefen nan da kanmu zamu ƙara ganin ita Zahran da ake faɗa sai mu ganu tarbiyyar ta" Yaya Halima ta ce "Gulma zamu kenan? Maza ke kaiwa a bari su kai kawai?" Dr A'isha ta ce "Please mana Yaya Please" da ƙyar Yaya Halima ta amince ta ce zata nemi Engineer domin tasan yadda Mother ta ɗauki Al'amarin ba lallai tai magana ba.
Da daddare duk suna zaune a parlour Mother, Yaya Halima, Dr A'isha dasu Maimoon da auta Fattoumah. Motar Sheikh tai parking a gidan da gudu Fattoumah ta miƙe yana faɗin "Yaa Lee Mother ta Yaa Lee nan" murmushin jin daɗi Mother ta yi ba tare da ta ce komai ba. A hankali ya fito da ƙafafuwansa waje kasancewar shi kaɗai ne da kansa ya yi driving hakan ya sanya gajiya ta saukar masa, yana fitowa Fattoumah na zuwa wajansa da gudu ta ce "Wlcm Yaa Lee" lumshe idanunsa ya yi tare da buɗewa, ganinta ƙarama kuma autarsu ya sanya ya sassauta fuskarsa tare da sunkuyawa ya ɗauke ta da hannu ɗaya, ɗaya hannun kuma ya rufe motar. Gemunsa taja ta ce "Yaa Lee ina kake zuwa muna ta missing naka" ya ware idanu bai ce komai ba sai hancinta da yaja kaɗan.
Da idanu suka bisa yana sanye da shadda ruwan madara babbar riga da jamper bai saka hula ba sai hirami daya rufe kansa da shi fuskar shi mai ɗauke sanje zuwa gemu ta bayyana ta cikin hiramin daya gewaye fuskar. Ƙamshin Roja tuni ya mamaye parlourn da ƙamshi, Maimoon da Zeefa duk suka miƙe tsaye suna sakin murmushi a tare suka ce "Sannu da zuwa Yaa Lee" bai kalle su ba ya tattara hankalinsa gaba ɗaya ga Fattoumah dake masa surutu, bayan ya zauna saman kujera ya daidaita nutsuwarsa da kyau cikin ƙasa da murya ya ce. "Barka" ya faɗa kai tsaye ba tare da In-ina ba, Dr A'isha da Yaya Halima suka kalli juna. "Dani ka ke ko Yaya Halima?" Bai kula Dr A'isha ba ko kallonta bai ba domin yasan nemen magana ce. Tai dry ta ce "Ka gama kame fuska duk girmata da kayi dole ace da mijin iya baba, ko yanzu goma ta faɗi tafi biyar albarka dole na amsa sunan uwa a gare ka" miƙewa yai da Fattoumah ganin Dr A'isha na neman fasa masa kai da surutu. Kai tsaye Upstairs ya nufa ɓangaren father domin amsa kira. Yaya Halima tabi bayan shi da kallo ta ce "Sannu Dr da tsaurin ido, lallai karanki ya kai tsako Sheikh kike faɗawa haka? Sai da Barrister Maryam ta yi aure ta haifi Sheikh da shekaru huɗu ba aka haifeki?" Dr A'isha tai dry ta ce "Wallahi yaya ƙarfin hali ne kawai, amma ba ƙaramin kwarjini ya yi mini ba, gashi ko inuwata bata samu albarkar kallo balle Ni" dry gaba ɗaya sukai. a zaune Sheikh ya samu Father hannunsa riƙe da jarida idan kaga Sheikh da Father ba zaka taɓa cewa Sheikh ne ɗa ba, domin yafi cika idanu da jiki tsayi faɗi uwa uba fuskar Sheikh data samu sumar ƙwarai ta ƙara fidda asalin shi. A kan carpet ya zauna yana sauke numfashi kansa a ƙasa bakinsa na rawar gaida Father ya yi saurin ɗaga masa hannu ya ce. "Bani da lokacin jin faa kakkkkka yayyyya, na kiraka domin ka shirya zuwa Yola wajan Zahrah kafin akai lefe jibi, umarni na baka Aliyu ba shawararka nake nema ba" Jinjina kai kawai Sheikh ya yi bai ce komai ba. "Tashi kaje idan ka zauna ba zaka amfane ni da komai ba, zan bawa Saif-wazir address ɗin" miƙewa tsaye Sheikh ya yi sai da yaje bakin ƙofa Father ya ce "Ka kwana a nan, ban amince ka koma gidan Hakimi ba daga nan har ɗaurin aure" Sheikh ya juya da sauri ya kalli Father wato ya fahimci duk abin da yake masa baya damunsa shi yasa ya sanya Abbansa cikin al'amarin. Juyawa ya yi kamar yadda ya ce ya nufi Part ɗin nasa yana tattare babbar rigarsa.

Washegari tunda ya yi sallar asuba bai koma ba, sbd wani irin mafarki da ya yi, abin ya tsaya masa yana son neman fassarar mafarkin wajan Abba Hakimi amma ya kasa, baya son mafarkin ya dangancin wani jinsi wanda ba nashi ba. Ƙarfe 7 daidai ya shirya cikin Milk ɗin shadda gezner bai saka babbar riga ba, sai golden ɗin Alkyabba daya sanya ya ɗora golden ɗin hirami, da ƙyar ya yi breakfast ɗin da Mother ta kawo masa shi ma sai da ta zauna ya gama jan ajinsa yaci kana ta fita ganin ko ƙala bai ce mata ba. Yana gamawa shirya wa Saif-wazir ya jashi zuwa garin Yola da taimakon Map. Sai da sukai nisa sosai sun ma bar Commission Quarter's ɗin sun nufi wani waje kamar daga Sama Saif-wazir yaji Sheikh yai gyaran murya kaɗan alamar ya tsaya. Waje ya nema ya yi parking gurin kamar jeji kamar ƙauye kuma. Cikin nutsuwa ya fito yana gyara zaman alkyabbar jikinsa, a hankali ya fara bin wata hanya hannunsa goye a bayansa. Sai da ya yi nisa sosai kana yaja ya tsaya. Kwance ya ganta kanta kife a ƙasa jini na zuba kaɗan a goshinta sai ƙwaryar kindirmon dake gefe guda hannunta guda riƙe da cikinta, da sauri ya zame idanunsa daga gare ta sbd kansa da yaji ya sara yana ƙoƙarin barin wajan wasu ƴan Fulani riƙe da Sanduna suka gewaye shi ɗaya ya ce "Aradu mun kama masu fyaɗen yara" Sheikh ya ware idanu amma bai nuna komai ba, wani ya ce "Wannan kamar kidnama waye kai?" nan ma shiru ya yi bai ce komai ba, Labo da yafi su iskanci ya kalli inda take kwance ganin jini a kanta ya ce "Aradu fyaɗe ya yi mata, kuma tunda kayi mata fyaɗe dole doka ta hau kanka" Sheikh trying to explain amma harshe ya sarƙe. "Kai ku saurara" Saif-wazir wanda hankalinsa bai kwanta da yadda Sheikh yabar motar ba, ya faɗa yana nufu wajan. Ƴan Fulanin suka tsaya ya kalle su sosai ya ce "Kuna hauka wanne irin fyaɗe mai yasa baku da tunani ne, yayi muku kama da wanda zai aikata haka?" Labo ya ce "Alkur'an sai na raɗeka da wannan sandan, ga jini nan muna gani ya kwantar da ita, dole kawai ya amshi hukunci" Saif-wazir ya

2 Comments On IDAN BA KE
avatar
al-kausar

4 months ago

Reply

Dan Allah ci gaba daga page 11 naga a page 10 ya tsaya Kuma kince akwai complete anan arewa books

avatar
taskar

4 months ago

Reply

Replying to al-kausar

sai dai ki saya littafin a wurin marubuciyar ga nambarta 08119237616

Please Login or Register in order to submit comment