Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yasa Zahrah sakin tsaki a file ta ce "Is an assignment, ba zan wasting time ɗina wajan yi muku explanation ba, i have so much work to do bye" wani daga cikin students ɗin ne ya miƙe yana dariya tare da ƙwaiƙwayar yadda Zahrah ke tafiya ya tsaya gaban ɗaliban ya ce "I have so much work to do bye... Big Maaaa The arrogant one I hate this woman. But i like her style" gaba ɗaya Students ɗin suka saka dry ba kuma kowa ke ƙaunar Zahrah ba, wulaƙanci da disga mutane ya mata yawa, kuma idan ta shiga hall babu wanda ya isa ya shiga ga bada Assignment da shegen text da Attendance. Zahrah na fita ta nufi Office a nutse take tafiya cikin takun isa da gadara tana sanye cikin wata atamfa Amarya collection mai tsada ɗinkin riga da skert ya kama jikinta sosai, idanunta sanye cikin farin cat eyes wanda ya ɗan haska ɓakar fatar jikinta she's classes and educated ƴar wanka ce ga tsafta da tarin ilimi. Ƙafarta dake sanye cikin Derby shoes ta tura cikin office ɗin tana ya tsona fuska ta ajjiye handbag ɗin L.v akan kujera idanunta akan Surayyerh ta ce "Lafiya dai?" Surayyerh taja tsaki ta ce "ina lafiya? Can you imagine yau Mom ce ta mareni sbd wancan banzan?" Buɗe idanu Zahrah tai kamar ba zatai Mgn ba sai kuma tace "mene abin damuwa?" "Zahrah mari fa? Wallahi ba zan ƙara ɗauka ba idan aka sake marina, Look at me am 29 going to 30 ace Mom bata bar marina ba?" Girgiza kai kawai Zahrah tai ba tare da ta ce komai ba. "Ina magana Kinyi shiru, wannan miskilancin naki na tsana fa" "uban me kike son nace maki Surayyerh? Your mother has been slapped you sbd kinyi kuskure sai nace bata kyauta ba? Babu abin da zaki iya sbd Uwa ce dole ki hqr" Zahrah ta faɗa cikin ɓacin rai. "i can't bazan iya jurewa ba" cewar Surayyerh "ok zaki rama kenan? Are you going to beat your mother?" Surayyerh ta girgiza kai cikin damuwa ta ce "A'a kawai zan faɗa mata kada ta kuskura ta sake marina, Nasan Uwa tace kuma sai tai ta dokana akan wanne dalili, ɓacin rana nake gudu" Kallon Surayyerh kawai Zahrah keyi kafin taja numfashi ta ce "Ina cikin damuwa Surayyerh na fara tsorata fa" Surayyerh ta ce "Damuwa akan me?" Hannu Zahrah ta ɗora akan cikinta ta ce "Am pregnant Surayyerh ina da ciki wata uku, kuma na gaji da zubar da ciki wallahi" zare idanu Surayyerh tai tana faɗin "Pregnant? ciki na huɗu kenan fa Zahrah? Kina da hankali kuwa? Wannan karan dole ki yafe cikin kin manta mai Dr yace miki ko?" Ajjiyar zuciya Zahrah ta sauke kafin ta kalli Surayyerh da kyau ta ce "I'm not ready for this, kin san ba aure gareni ba, idan na bar cikin na haihu me zance a gida? Me zan faɗawa Mimi? daman Kullum cikin faɗan naƙi aure take wai na girma da yawa, karatun boko ya buɗe min idanu yanzu kusan shekaruna 31 ne Surayyerh" Surayyerh ta numfasa ta ce "Me kike jira? Ki kira Deen mana kuyi magana ya turo iyaye kuyi aure, Mimi nada gaskiya Kinyi primary, secondary, N.c.e, degree, kinyi masters to what are you waiting for wanda ya shige kiyi aure, haba ai ta boko ai ta boko nifa idan yanzu ne wlh ba zan wata boko ba, shekara 31 ana abu ɗaya sai zallar iskanci kawai da kike kina zubar da ciki a banza, sai kin gama zubar da ƙwayayen da Ubangiji ya baki matsayin zuri'a a banza wlh" Tsaki Zahrah tai "wani lokacin wlh ke Mahaukaciya ce, ni kike tunanin zan iya auren Deen yanzu? Inda a yanzu nasan rayuwa nai boko naje ƙasashe kala-kala da ace ko secondary schl ban rufa ba shi ne zan iya auren Deen amma yanzu kam i can't, zanje hospital a cire cikin, da kike maganar haihuwa waye ya faɗa miki daman ina son raya da haihuwa da yawa ne? Abeg ta shi muje Madam am not in the mood" Surayyerh ita dai mamakin Zahrah take bata, ta rasa ita da Zahrah waye yafi laifi, ita tana ganin mahaifiyarta na takura mata domin har kusan zaginta take a zuciya, ta hanata jin daɗin rayuwa komai sai ta ce wai taji tsoran Allah, ita kuma Zahrah iyayenta sun sake mata duk abin da zatai babu me cewa dan me gidansu gidan boko ne a waye suke gaba ɗaya, hakan yasa Zahrah keta aikata alfasha hankali kwance. "Kinzo da mota ne?" Surayyerh na miƙewa tsaye ta ce "E, kefa?" Zahrah ta ce "A'a, ba zan iya driving ba wannan cikin duk ya sauyani muje kiyi dropping nawa gida" "ok let's go" Fita sukai Zahrah da Surayyerh aminai ne duk faɗan da za suyi har abada babu mai ji, su gama fushi su shirya. Mota suka shiga Surayyerh na driving Zahrah na gefe a haka suka bar cikin Abti America.

Da idanu Dada take bin kuɗin da Danejo take bata, a sanyaye ta ce "Duk wannan?" "E, Dadana ɗan Almajirin mai yagaggun kaya ne yace mini aradu duk kindirmo ake siya dasu, kuɗin da yawa" Dada ta jinjina kai ba tare da tace komai domin magana bai dameta ba, tun bayan rasuwar Baffansu Danejo ta zama shiru-shiru sanadin hakan ciwonta ya sake yin tsamari. "Dadana nawa ce wannan?" Danejo ta tambaya tana nunawa Dada gudar dubu ɗaya, girgiza kai Dada tai bayan ta tsurawa dubu ɗayar idanu ta ce "Ban san sunanta ba, ki bari Hamma Yabi ya zo sai ki tambayeshi ko?" Miƙewa Danejo tai ta ce "Bari naje wajan Shatu na tayata irga Naggenmu" fita tai a hanya taci karo da Hamma Yabi, da sauri Hamma Yabi ya kama hannun Danejo ya shiga duba Funa, Fobbina, Wayla, Hirna. Ma'ana Gabas, Kudu, Arewa, da Yamma, ganin ba kowa yasa Hamma Yabi faɗin "Mun shigesu Danejo, gobe ake bikin gasar wasa da maciji, wanda Sarkin ruga yake sawa, kuma yau za'a zaɓi wanda za'ai wasan dashi" fararen idanunta ta juya sosai cikin rashin damuwa ta ce "Hamma mene abin damuwa, ni Dadana kawai nakeso ta samu lafiya ina ta mafarki wani kala" girgiza kai Hamma Yabi yai kaifn ya kama Danejo sosai ya ce "Baka iya wasa da Mashiji ba Danejo, kuma Sarkin ruga zai iya zaɓarki matsayin wacce zatai wasan, idan baki iya ba Mashijin zai iya saranki ki mutu murus, ko baki mutu ba idan baki iya ba Sarkin ruga zai iya korar mutum daga cikin Rugar Rome" cike da tsoro Danejo ta zaro idanu waje ta ce "Mi boni Hamma Yabi yaya zanyi?" "Yanzu shai mu jira muga wa za'a zaɓa, kije ki ɗauki kindirmo mai man shanu ki bawa Dada gobe zamu koma ashibiti" kai ta ɗaga alamar to Hamma Yabi ya nufi cikin jejin nemo wani sassaƙen magani ita kuma ta nufi wajan garke a nan ta samu Shatu ta kama bakinta a nonon Nagge tana ta sha hankali ƙwance. Zama tai kan wani Leggal (Icce amma kututture) samun kanta tayi da tunani wanne kalar Mashiji za'ai wasan dashi? Meyasa idan taje Birni take ganin wasu mutanan ba irinsu ba komai nasu daban ne, meyesa birni ta banbanta da Rugar Rome?. Ajjiyar zuciya ta sauke tana murza yatsun hannunta da sauri takai dubanta zuwa ga ƙadamin yatsarta idanunta ya sauka akan zoben dake maƙale da yatsar da tsananin mamaki take kallon hannu yaushe wannan abun ya zo hannunta? Mene sunansa ita bata taɓa ganin abu mai kama da zobe ba sai yanzu, ga wani zane a tsakiyar zoben kamar tambarin abu amma bata san ko mene ba, ƙoƙarin zare zoben take amma ta kasa hakan yasa dole ta hqr. Suna zaune a garken suka ji ana shelar Sarkin ruga yana neman jama'ar Rugar Rome baki ɗaya. Da Shatu da Halisa suka kalli juna zuciyarsu cike da zullumi amma Danejo tai ta maza ta kama hannun Shatu suka nufi wajan. A tsaye suka samu mutane wasu na sanye da fararen kaya na Fulani wasu kuma Kuraye yawancin su gaba ɗaya farare ne, amma sam babu cikakken addini ga rashin tsafta. Sarkin ruga ya gyara tsaiwa yana faɗin "Kamar yadda kowa ya sani, a gobe ne zamu gabatar da gasar wasan Mashiji, za'a zaɓi mutum ɗaya ya buga wasa da ƙaton Mashiji kamar yadda muka saba, idan mutum ya kashe Mashiji akwai kyautar Nagge da kuma ƙwayar nono guda hamsin, idan Mashiji ya kashe mutum Shi kenan wasa ya zo ƙarhe, idan mutum bai mutu kuma za'a kuresa daga Rugar Rome baki ɗaya, don haka yanzu zamu fito da alƙalin wasa ya zo ya zamu wanda za'ai wasan da shi" Shatu ta ƙankame hannun Danejo ita ko kalmar Mashijin bata so taji an faɗa balle ta gansa a gabanta. Dajeno kam shiru tai kanta a ƙasa tunani fal ranta domin gaba ɗaya ma hankalinta baya wajan. Alƙalin wasa ya fara zagaye mutane har ya shige kan Danejo gama dubawa yai sannan ya gyara murya ya ce "Mun zaɓi Halisa Dajeno Rome a matsayin wacce zata fafata da ƙaton Mashijin mu a gobe....

#Sarautar marubuta
#True life story
*🌈 IDAN BA KE 🌈*

Nimcyluv sarauta
*_Arewabooks@Nimcyluv_*

3.
"Na shiga uku ta ya ya zan iya wasa da maciji? Wallahi kashe ni zai yi" Danejo ta faɗa a fili cike da tsora wanda ya sanya har ta kusan sakin fitsari gaba ɗaya ta firgita. Shatu ta ce "Ki faɗa masa ba zaki iya ba a zaɓi wata, idan Mashijin ya kashe ki na shiga uku na lalashe aradu" da sauri Danejo ta fito tsakiyar fili idanunta akan Alƙalin wasan muryarta na rawa ta ce "A yi mini afuwa Alƙalin wasan ba zan iya wasa da maciji ba aradu sarata zai yi" Alƙalin wasan ya kalli Danejo sosai, shi ya ɗan jima bai ganta ba, ta ƙara girma da wayo sosai ta zama ƴar budurwa irin girman ƙauyen nan dai. Sai rashin tsafta da addini dake ɗawainiyya da ita duk da ana ƙoƙarin ganin an magance hakan a cikin Rugar Rome. Murmushi alƙalin wasan ya sake yi cikin kulawa ya ce "Zaki iya mana? Ai Baffanki ya ƙware wajan iya sarrafa maciji, a wasan ƙarshe kuma macijin ya zama silar mutuwarsa, ki yi wasan ko dan ƙarasa cikawa Baffanki burinsa na zama gwarzo a Rugar Rome. Tabbas zaki iya Halisa Dajeno Rome" girgiza kai tai da sauri idanunta cike da hawaye ta ce "Ba zan iya wasa da maciji ba, mene ya sa sai ni? Baffana daban ni daban kalleni ƙarama ga maza nan da yawa a zaɓi wani daga ci" Sarkin rugar yai saurin faɗin "Ke aka zaɓa, kuma dole kiyi domin ba zamu taɓa sauya ra'ayinmu ba, ya zame miki wajibi muddin kina cikin Rugar Rome" a tsorace Shatu ta ce "Hande en boni, yau mun shiga uku" kasa cewa komai Danejo tai domin gani take kamar ma ta mutu ne lokaci kawai take jira.
Da sauri ta juya idanunta cike da hawaye ta nufi cikin bukkarsu zuciyarta cike da zullumi da kuma fargabar abin da zai je ya dawo. A haka ta shiga cikin bukkar Idanunta akan Dada wacce take kwance cikin halin ciwo, domin a kullum ciwon nata ƙara tsanani yake. "Dada Alƙalin wasan ya zaɓi Danejo matsayin wacce zatai wasa da maciji a gobe" da sauri Dada tana jan numfashi ta kalli Danejo cikin damuwa ta ce "Mene ya sa baki cewa masa ba zaki iya ba?" Shatu tai saurin faɗin "Sarkin ruga ya ce wai dole tayi domin cika muradin Baffanmu" Dada ta miƙawa Danejo hannunta cikin kulawa ta ce "Waye yace muku Baffanku wasan maciji shi ne burinsa?" Danejo ta kasa magana sai ajjiyar zuciya take saukewa Shatu ce tai ƙarfin halin cewa "Sarkin ruga ne ya faɗa" Murmushin taƙaici Dada tai bata taɓa ganin zalunci irin haka ba, ta rasa me suka tsarewa Sarkin ruga da yake shirin ƙarar dasu ta hanyar kashesu da maciji wanda wasu suka tabbatar macijin tsafi ne. Cikin ƙonar zuci ta ce "Baffannku bai taɓa sha'awar yin wasa maciji ba, halima babu wannan al'adar ta wasa da maciji a Rugar Rome, daga baya Sarkin ruga ya samar da ita, bayan ya samar da ita ya zaɓi Baffanku matsayin wanda za'ai wasan dashi" shiru tai sbd tarin daya sarƙe mata numfashi, da sauri Shatu ta ɗauki ruwa ta bata, numfashi ta sauke kafin ta ce "Bisa dole Baffanku ya amince, yasha wahala kafin ya kashe macijn bayan ya samu raunuka wanda ya sa ya kwanta jinya, da shekara ta zagayo aka ƙara zaɓar Baffanku abin mamaki shi ne babu bambanci tsakanin macijin shekarar data shige da kuma wanda aka fito da shi, Baffanku ya tsorata, gashi idan ya ce ba zai ba to za'a kuresa daga Rugar Rome, tun daga wannan shekarar Baffanku ke gabatar da wasan Maciji, har zuwa shekarar da maciji ya kashe shi wanda kuma anyi hakan ne domin aga bayansa. a ruɗe Danejo ta ce "Kenan kashe Baffa akai Dada?" Dada ta girgiza kai ta ce "Ba zance ba, bani da hujja akan haka koma mene hukuncin na wajan Allah".

Danejo taja numfashi cike da raunin murya na rashin sanin mafita zuciyarta cike da tarin zullumi ta kalli Dada ta Shatu ta ce "Dada ba zan iya ba, ina jin tsoro" "Halisa idan ba kiyi korarki za su yi daga cikin Rugar Rome, ni kuma ba zan jure hakan ba, Ubangiji na tare dake. Dole kiyi wasan imma ki mutu ko kiyi rai Kinji ko?" Kafin Danejo tai magana Hamma Yabi ya shigo da sauri idanunsa akan Danejo yana faɗin "Tashi mu tafi Danejo daman nasan bayanki suke son gani kamar yadda suka kashe Baffa" kallo Hamma Yabi Danejo tai idanunta ya kumbura sbd kuka ta ce "Hamma ina zamu?" Muryarsa na rawa ya ɗaga ta tsaye ya ce "Zanje na ɓoyeki sai an gama wasan zaki dawo, zan nuna ban san idan kike ba" Dada tai saurin cewa "A'a Yabi, kada ai haka kamar Halisa tare damu, idan ta tafi to Shatu ce zata maye gurbinta kasan haka ai" zama yai sosai ya ce "Yanzu haka zamu zauna? Ke baki da lafiya ita kuma muna kallo maciji ya kashe ta?" "Akwai Allah" Dada ta bashi amsa tana rufe idanunta. Halisa kasa bacci tai ga yunwa ga tsoro can cikin dare ta tuna ai ha tayi sallar issha ba, da sauri ta fito daga bukkar gaba ɗaya rugar shiru babu kowa sai wutar da aka kunnawa ko wanne garke dake ci hankali. Can bayan bukkarsu ta nufa tai tsari a wajan tai alwala babu ko shafar kai ta kwararan ruwan ta dawo. Sallar ma dungure tai Fatiha kawai ta iya cikakkiyar babu gyara. Yadda taga rana haka dare, dab da Asuba ta nufi garke tare da tatsar nono, tana gamawa ta Ajjiye. Gari na fara haske bayan tai sallah ta kaɗa shannun zuwa cikin jeji. Har zuwa lokacin bata da nutsuwa ita a yanzu ba wasan majin ya dameta ba, illar rashin lafiyar Dada idan har macijin ya kasheta waye zaici gaba da kula da Dada? Zama tai a gefen wani dutse ta shiga rusa kuka da iya ƙarfinta.

Commissioners Quarter's
Haɗaɗɗiyyar unguwa ce wacce take cikin Jimeta, iya haɗuwa da tsari unguwar tayi, wanda bai saba fita kasashen waje ba idan ya shiga Commissioners Quarter's zaka ɗauka a ƙasar turawa kake. Gidajene duguwa zaka gansu kamar tangaran sbd yadda suka haɗu aka zuba dukiya. Unguwa ce ya masu kuɗi wanda talaka sam bai isa ya shige ta ba. Unguwannin masu ci da gindin biro kenan.
A hankali take sakkowa daga kan strains ɗin benan hannunta riƙe da waya tana latsawa, jikinta sanye da wani Short pencil jeans sai Balenciaga top a saman t.shirt ɗin jikinta. Ƙafarta cikin wani Hermes slippers. "Binta! Binta!!" Ta shiga kiran maid ɗin dake yi musu abinci tana zama saman Kujera, jinin Binta na rawa ta ƙaraso tana zubewa a gaban Zahrah ta ce "Hajiya gani" harara ta watsa mata cikin rashin ko ina kula ta ce "Kin san ban son buɗe murya sbd kawai zan kiraki?" Binta wacce a ƙalla zata iya yin shekaru 55 zasu iya kusan sa a da mahaifiyar Zahrah ta sunkuyar da kanta ƙasa cike da girmamawa ta ce "Afuwa Hajiya, ina can ina duba time table na list ɗin abincinki na me za a dafa miki zuwa dare" shiru Zahrah tai ba tare data ƙara cewa Binta komai ba, hankalinta yana kan wani abu da take searching akai, ita dai da karatun boko na yin magana a jikin mutum da tuni ya jima dayi a jikin Zahrah domin kaf gidan tafi kowa zurfi karatun boko shi ya sa take taka kowa hankali kwance. "Hajiya me kike buƙata?" Binta ta tambaya. Idanunta ta ɗaga ta kalli Binta a hankali taja tsaki ta ce "Nikam Binta na tambayeki?" "Ina jinki Hajiya" Zahrah ta gyara zama sosai tana ajjiye wayar hannunta a gefe kafin ta ce "Wai yaushe za kiyi hankali ki fahimci abin da nake buƙata, matsalar rashin ilimi kenan fa, gaba Binta ƙwaƙwalwarki bata riƙe abu ba lallai ko primary kin cika ba, wallahi na tsani harka da midille class,uneducated, villagers" da tsananin mamaki Binta ke kallon Zahrah ƴar cikinta ke faɗa mata wannan maganganun? "Kiyi haƙuri Hajiya" a fusace Zahrah ta ce "Sorry for yourself Binta, kije ki haɗa mini salad ki saka lemon sosai ciki" Binta ta jinjina kai tana Miƙewa tsaye tare da barin wajan idanunta cike da hawayen baƙin ciki. Wata mata wacce ta fito cikin parlourn ta kalli Zahrah ta ce "Why are you shouting?" Murmushi Zahrah tai ta ce "No Mimi ina game ne, akai mini game over" Zama Mimi tai ta ce "Ok, kwana biyu na jin labarin Deen a bakinki? Lafiya dai?" Zahrah ta ce "Baya nan ne Mimi" Mimi ta ce "Ai fa, naga idan yazo sai ku kai awa uku zuwa huɗu a part ɗinki kwana biyu shiru" Murmushi kawai Zahrah a haka Binta ta kawo mata haɗin salad ɗin. Mimi tabi Zahrah da kallo kafin ta ce "Wai lafiyarki ƙalou kuwa? Kullum cikin cin haɗin Salad kike?" "Lafiya Mimi, kawai zuwa makarantar nan ke sani gajiya da kwaɗayi naji bana son cin komai" Mimi ta jinjina kai ta ce "Lallai, ni banga me zaki da kuɗi ba da kuka zaɓi lecturing Zahrah" ba tare da data amsa ta ba ta ce "Mimi ina Daddy ne?" Mimi ta ɗauki waya ta ce "Jiya ya dawo, but yaje kano wajan wani babban abokinsa" "Ok" cewar Zahrah a nutse Mimi ta kalli Zahrah cikin damuwa sosai ta ce "Fatima-Zahrah yaushe kike tunanin yin aure ne, boko kin gama ta, completely sai abin da yai saura, familyna sun fara mini surutu akan wai na zuba miki idanu, wasu har cewa suke maybe yawonki kawai ki ke, ni dai nasan ba haka bane i trust you babyna" marairaicewa Zahrah tai kamar ƴar 20 nan kuwa shekaru 31 take da shi. "Mimi kin san familyn nan naki basu san darajar karatun boko ba, ta ya ya zan haɗa karatu da aure? Kana yin auren kuma ace ka haihu, kuma ba zan iya haɗa aikina da aure ba gsky Mimi a barni zuwa 35 na gama komai sai na fara tunanin auren, su kansu mazan ai mai ilimin boko suke buƙata ba kuwa ya damu da ilimin addinin nan ba, suna buƙatar mace wayayyiya a very educated women" murmushi Mimi tai cike da gamsuwa da maganar ƴarta kafin ta ce "Na fahimta, ko Dadynki sai dana kammala University mukai aure muna dai soyayyya a waje, dake kuma na wuri na shiga shcl shi ya sa na gama before we getting married" jinjina kai kawai Zahrah tai hankalinta akan salad ɗin da take ci sbd yadda cikin jikinta ya sanya mata kwaɗayi kala-kala. Da sauri Mimi ta ce "Subuhanallahi, maza kunna mini Plasma ɗin nan ki jonata da DS.TV tafsirin Sheikh sai shigeni" kwaɓe fuska tai kafin ta ce "Mimi wai kin damu da wani Sheikh, ni wallahi ban son tafsirin ɗin ko kaɗan, ga wata ƙinƙina da yake, da ƙyar fa yake iya karatun sbd ƙinƙina wani time ɗin har hawaye yake to me za'a gane?..." Da idanu Mimi tabi Zahrah tana mamakin jikar ƙirjinta a kullum "To ai kuwa da yadda, ƙinƙina kuma ai larura ce kuma a hakan Ubangiji ya ba shi bawai Zahrah".

Gudu take sosai hankali a tashe sai haki take ita kam sam ba zata iya irin wannan wasan na sai da rai ba, wacce ƙaddara ce take shirin bibiyarta ne? Tsayawa tai tana mai da numfashi, sai a lokacin idanunta ya sauka akan wasu fararen Kurciyo masu kyau da tsari ita a rayuwa tana son ko wacce kalar dabba ta daɗe tsaye tana kallonsu, ɗaya daga cikin kurciyoyin ya tsora mata idanu. Tunawa da tai ana gab da fara wasan macijn ya sanya ta ƙara saurayi domin samun wajan ɓoya. Girgiza kurciyoyin sukai wata iska da guguwa ta mamaye ilahirin wajan iskar data kasance mai daɗi sosai wacce ta haddasawa Halisa Dajeno rufe idanunta wani barci na fisgarta a hankali ta sulale a wajan babu jimawa barci mai nauyi ya ɗauketa. Kurciyoyin suka rikiɗe zuwa wasu samari masu zubin halitta ɗaya daga ciki wanda yake sanye da farar Alkyabba mai taushi wacce ta sauka har ƙasa ta rufe masa ƙafafuwansa yaja numfashi a hankali cikin ƙasa da murya ya ce "Danejona ba zata iya wasan nan ba" ɗayan dage gefensa ya ce "Haba Prince me ya sa kake da taurin kai ne? Sarki yace ka yanke duk wata alaƙa tsakaninka da bil-adam musamman wannan yarinyar Danejo amma kaƙi" murmushi mai taushi Wanda aka kira da Prince yai yana sake kallon Halisa Dajeno ya ce "A wannan karan ba zan iya yiwa Sarki biyayya ba, babu haɗi tsakanin mutum da aljani, amma kasan ba zan iya zutar da wani rai ba, muddin idan ba Danejo zai cutar ba? Na jima a jikin mahaifiyar Danejo tun tana da cikinta, amma rana ɗaya akai mata magani suka rabani da ita, wanda ya sanya na kwanta jinya, wannan dalilin yasa na koma kan ɗiyarta Danejo na shirya duk wani abu da sarki zai faɗa, ƙarshe dai ya ce zai koreni daga duniyar Aljanu ba?" Ɗayan zai magana Prince ya daka mishi tsawa ya ce "Ka saurara mini Safwan" ya faɗa idanunsa na juyewa zuwa kalar na aljanu a tsorace Safwan ya ce "Afuwa nake Yariman Aljanu, yanzu me ka shirya akan raba Danejo da wasan macijin nan?" Gyara Tsaiwa Prince yai tare da durƙosawa daidai inda Danejo take kwance tana barci ya ɗauke ta cikin nutsuwa ya ce "Ubangiji nake nema ya bani Sa'a, ina son Matata bana jin zan jure ganinta da duk wani wanda zai cuceta, balle kuma ya taɓa mini ɗana dake cikinta" buɗe baki Safwan yai da Mmki yace "Prince yaushe ta zama matarka? Har kuka samu ɗa?" Murmushi Prince yai yana shafa cikin halinsa wanda yake jin farin ciki na ratsa masa zuciyarsa kafin ya ce "Matata ce ita ɗin, duk wanda ya shirya rabani da ita to ya shirya zuwansa lahira, bani da lokacin magana Safwan, maza ku ɓace daga wajan nan" kamar gilmawar walƙiya haka suka ɓace, nan da nan Prince ya rikiɗe zuwa Almajiri mai yagaggun kaya. A nutse ya fara tafiya da ita zuwa cikin Rugar Rome dai da yaje daidai bakin bukkar su Danejo ya ajjiyeta da sauri ya bar wajan, sbd gaba ɗaya jama'ar Rugar suna filin da za'a gabatar da wasan Maciji. Prince ya ce "Ubangiji ka bani Sa'a da nasara" yana faɗin hakan yai Girgiza nan take ya zama ƙaton wani baƙin maciji mai narkeken kai a hankali ya sulale ya fara tafiya tsakanin bukkokin Rugar Rome har ya Ƙarasa wata bukka kai tsaye ya kutsa kansa ciki, kwance ya samu wani maciji shima baƙine sosai, da alama shi ne macijin da Matarsa Danejo zatai wasa dashi. Kallon kallo aka fara tsakanin Maciji Prince da kuma Macijin da Danejo zatai wasa dashi. Kamar haɗin baki haka suka fasa kai a tare lokaci guda kuma suka nufi kan juna.


🫣Bala'i🚶🏽‍♀️kada a manta labarin ya faru a gaske babu ragi

2 Comments On IDAN BA KE
avatar
al-kausar

4 months ago

Reply

Dan Allah ci gaba daga page 11 naga a page 10 ya tsaya Kuma kince akwai complete anan arewa books

avatar
taskar

4 months ago

Reply

Replying to al-kausar

sai dai ki saya littafin a wurin marubuciyar ga nambarta 08119237616

Please Login or Register in order to submit comment