Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

babu ƙari👌🏾. Muje zuwa

#Sarautar marubuta
#True life story
*🌈 IDAN BA KE 🌈*

Nimcyluv sarauta
_*Arewabooks@Nimcyluv*_

4.
A kusan tare macizan guda biyu suka ƙara fasa kai tare da kaiwa juna sara, ko wanne maciji ƙoƙarin jiwa ɗan uwansa ciwo yake da ganin ya kashesa har lahira. Gaba ɗaya macizan suka sarƙafe juna tare da nan na ɗewa waje guda ko wane huci yake yana fitar da hayaƙi ta baki nisan yadda Prince wanda ya a rikiɗe zuwa maciji ya matse macijin da Za'ai wasa dashi, gaba ɗaya ya ji masa rauni a hankali kuma Prince ya buɗe bakinsa ya fara haɗiye Macijin zuwa cikinsa sai daya haɗiyesa tsaf kafin ya sulale gefe guda ya kwanta yana mai da numfashi Wahala, sai fasa kai yake kamar zaici babu zuciyarsa tayo sama baki ɗaya zai iya sarar ko waye a wannan lokacin.

Sarkin ruga ya kalli tarin jama'ar da suke wajan hadda Shatu da Hamma Yabi, da sauran mutanan rugar kafin ya numfasa ya ce "Lokaci ya yi ake a kawo mana Halisa Dajeno Rome cikin fili, domin su fafata da maziji yau ranar tace" Wani mai suna Giɗaɗo ya rusuna tare da faɗin "Yanzu za'a kawota" yana faɗin hakan ya kalli Hamma Yabi tare da faɗin "Maza jeka kawo ɗiyar taku, tana ɓata mana lokaci" Hamma Yabi ya ce "Yanzu za'a kawota" yana faɗin hakan ya juya da sauri ya nufi bukkarsu tun daga nesa ya hangeta kwance a bakin bukkar inda Prince ya kwantar da ita tana barci.
Cikin sassarfa ya ƙara yana faɗin "Assha Subuhanallahi barci a ƙasa Danejo" ya faɗa yana ɗagota tare da jijjigata sosai, da sauri ya buɗe idanunta tana zabura "Hamma Yabi yaushe na dawo nan?" Kallonta yai ya ce "Kina nufin baki san lokacin da kika kwanta a nan ba?" Girgiza kai tai ta ce "Aradun Allah ban shina ba, kawai naji iska mai daɗi ta lulluɓeni wani barci yazo mini daga nan ban san komai ba" Girgiza kai yai yana kama Hannunta ya ce "Danejo ƙurushiya, maza muje sarkin ruga na jiranmu" dafe ƙirji tai cike da tsoro ta ce "Na shiga uku na lalashe, Kur'ani na manta yanzu hamma yabi shikenan mutuwa zan, zan mutu na bar Dada? Zan mutu banyi karatu na zama babbar mace ba? Don Allah kada na mutu yanzu bana son wasan nan" rirriƙeta Hamma Yabi yai sosai ya ce "Ma zaki mutu ba Danejo, sai na kai ki burni Kinyi karatu kin zama babbar mace abar ƙwatance, sai kin zama mace ta farko wacce zata kawo sauyi cikin Rugar Rome, ki daina kuka kinji" kai ta ɗaga masa kafin da sauri ta ce "Kuma zan zama wannan mutumin na jikin bango?" Zare idanu Yabi yai kafin ya ce "Wannan gwamna ne fa" murɗa baki tai cikin shagwaɓa ta ce "Ni dai irinsa nake son zama" Yabi ya dungure mata kai ya ce "Aradu ƙarya kike, ina zaki iya yin siyasa tayaya zaki zama gwamna daman mata na zama gwamna ne?" Banza tai masa bai ƙara ce mata komai ba ya jata zuwa filin da za'a gabatar da wasan.

Giɗaɗo dake tsaye shi da Sarkin ruga suna jiran zuwan Hamma Yabi da Danejo ya ce "Me ya sa ka zaɓi Danejo kasan ba zata iya wasan ba" murmushi Sarkin ruga yai kafin ya ce "Ina son ganin bayanta ne, kuma a hankali zan ƙarar da zuri'ar Manga a cikin Rugar nan, wannan macijin na tsafi ne hatta mutuwar Manga ni na shiryarta"... "Amma me Manga yai maka haka?" Cewar Giɗaɗo. Sarkin ruga ya ce "Sirri ne.." kaifin su ƙara magana Hamma Yabi ya ƙaraso hannunsa riƙe da Danejo wacce ta ƙanƙamesa sosai jikinta na rawa da ɓari.

Alƙalin wasan ya ce "Yawwa yanzu zamu fara, Danejo ta shigo cikin fili jama'a ku buɗe idanunku da kyau yau za kuga wasa wanda baku taɓa ganin irinsa ba" Halisa Dajeno Rome na tsakiyar fili ko kuka ta kasa a wannan lokacin ta tsaya ne kawai tana jiran taga ta inda mutuwa zata zo mata, domin abune mai wahalar gaske ace yau ta rayu ko ta tsira da ranta. Sarkin ruga ya bada umarnin a fito da Macijin, da sauri Alƙalin wasan ya nufi bukkar da macijin yake. Yana kwance sharkaf yau lamo a ƙasa tare da yin gammo da jikinsa, wani irin zabura yai tare da fasa kansa a lokacin da alƙalin wasa ya shigo cikin bukkar, ƙuri yai masa da idanu yana ƙare masa kallo. Ko me ya tuna Ohhu a hankali ya fara sauka daga dokin zuciyar ya koma ya kwanta, shi kansa Alƙalin wasan ya tsorata jikinsa na rawa yasa hannu ya ɗauki Macijin da ƙyar sbd nauyin da yake da shi.

Tun da Halisa Danejo Rome ta saka idanunta akan macijin taji gabanta ya faɗi, jikinta ya ɗauki rawa hawaye suka fara sintiri a saman Fuskarta, bata taɓa ganin maciji mai girman wannan ba, tama rasa wacce kalar addu'a zatai duk da ba wani abu ta iya sosai ba. Alƙalin wasan ya ajjiye macijin nesa da Halisa, aka fara kallon kallo tsakanin Danejo da Macijin, an shafe tsayin wasu daƙiƙo aka rasa waye zai fara kaiwa wani hari tsakanin Danejo da Maciji Prince?. Zaro idanu tai waje ganin ya fara warware tare da yin tsayi sululuuuu kuma ya nufo inda take, tana ja baya yana biyota har ya ƙaraso dab da ƙafarta tare da tsorawa zoben hannunta idanu. Juya tai tana neman inda zata gudu can idanunta ya sauka akan wani ƙaton dutse. Da sauri ta ɗauka tare da riƙewa a hannunta, ganin haka yasa Macijin bin ƙafafuwanta suuu haka ya dinga sufa a jikinta, har ya naɗeta ciff kansa daidai Fuskarta yana tsora mata idanu tare da kallon cikin idanunta.

Jirkinta na ɓari ta ɗaga dutsen tare da kwaɗa masa a tsakiyar kansa, wani kalar ihun azaba macijin yai yana fasa kai kamar zai sarata, sai kuma ya saki kansa tare da ɗorasa saman ƙirjinsa gaba ɗaya naman Macijin rawar azaba yake, kansa tuni ya fashe ya fara zubar da jini. Ganin nasarar da Halisa Danejo Rome ta fara samu yasa Hamma Yabi da Shatu tare da sauran jama'ar Rugar Rome suka fasa ihun murna, Sarkin ruga da Alƙalin wasan hankali tashe suka kalli juna tare da faɗin "Me ya samu macijin nan? Ki dai asiri akaiwa Yarinyar nan?".

Halisa a tsorace Macijin a tsorace amma a haka cikin dakiyar zuciya ta ƙara ɗaga dutsen a karo na biyu ta ƙara bugawa Maciji, Innalillahi a wannan lokaci kururuwar da Macijin yai sai da kowa na wajan yaji, jini ya sake ɓalle masa a hankali ya sulale ƙasa baya ko motsi alamar ya mutu... ajjiyar zuciya ta sauke haka kurum taji kuka ya ƙwace mata, durƙushewa tai a wajan ta shiga rera kuka tausayin macijin ya kamata musamman yadda taga jini na zuba a jikinsa, Hamma Yabi ya ƙaraso wajan Halisa Dajeno Rome tare da ɗagata yana dariya ya ce "Danejon Dada kin kashe macijin, kin kashe sa bana faɗa miki cewa ba zaki mutu ba? Zamu samu ƙwayar nono da Nagge masu yawa" ƙanƙame Hamma Yabi tai cikin kuka ta ce "Bana so Hamma Yabi, mu bar nan wajan kaina juyawa yake, bana son ganin jinin nan kaji" hannunta ya kama sukai gefe guda. Cike da taƙaici Sarkin ruga yake bin Macijin da kallo bai taɓa tunanin haka ce zata kasance ba, cike da baƙin ciki ya amshi wani sanda ya shiga kwarɗawa macijin aka tun macijin na motsi har ya daina jikinsa yai face face da jini tare da raunuka. "Ka ɗauke sa ku cillar a gefen gaɓar ruwa wani abin yai kalace dashi" Giɗaɗo da Alƙalin wasan suka ɗauki Macijin tare da nufar cikin jeji da shi. Suna zuwa suka cillar gefe guda da sauri suka juya cikin Rugar Rome.

Sanyin gaɓar ruwan daya ratsa cikinsa ya sanya ya fara Girgiza yana juyi tare da murmurɗe jinsa gefe guda, wani kalar ihu yake mai nuni da azabar da yake ciki, ya daɗe cikin wannan halin kafin yai Girgiza tare da rikiɗewa ya dawo siffarsa yadda yake fitowa a mutum ba Aljani ba, yana kwance sambal gefen ruwan Farar Alkyabbar jikinsa duk ta ɓaci da jini. A hankali ya ɗaga hannunsa tare da dafe kansa inda yake zubar da jini, runste idanun yai sosai cikin ƙasa da murya ya ce "Ya Allah" yana nan ƙwance yaji iska ta mamayesa baki ɗaya kafin kace wani abu iskar ta ɗaukesa zuwa sama.

Duk farin cikin dasu Shatu suke ciki banda Danejo rasa abin da yake mata daɗi tai, gashi jinin Dada ya matsa ga tunanin dake wanzuwa a cikin zuciyarta. Dada ta kalli Shatu ta ce "Farin ciki za kiyi Halisa ba damuwa ba, da tuni an rabani dake Allah bai ba, akwai ƙaddarorin da suke biye dake, amma duk wahala duk tsanani waya rana zaki zama abar ƙwatance tabbas zaki samu miji wanda zai kula da maraicinki" Danejo ta ce "Dadana nifa ba marainiyya bace, ina dake ga Hamma Yabi ga kuma Shatu" jinjina kai Dada tai idanunta akan zoben hannunsa Halisa ta ce "Ina kika samu wannan Halisa?" Girgiza kai tai cikin damuwa ta ce "Ban sani ba Dada, kawai na gansa a hannuna"... "Bana son ƙarya fa" da sauri Halisa ta ce "Da gaske nake miki, kalli kiga" ta faɗa tana nuna mata tambarin zoben, Dada ji tayi kansa ya sara idanunta akan Zoben da sauri ta riƙe kanta tare da rufe idanunta, kamar mai son tuna wani abu babu abin da take gani a cikin idanunta sai tambarin masarauta dake manne cikin zoben. Ganin yadda Dada ta rirriƙeta kanta ya sa Hamma Yabi fita da gudu ta tatso mata kindirmo mai zafi, da taimakon Halisa Dajeno Rome suka bawa Dada kindirmon nan da nan zufa ga shiga saukar mata bacci ya ɗauke ta.

Juyawa Halisa tai ta kalli Shatu dake barci a nutse ta kalli Hamma Yabi ta ce "Hamma yaushe Dada zata samu lafiya ne? Kullum a ƙwance take ina tsoran na rasa ta aradu" Hamma Yabi ya kama hannun Danejo ya ce "Ba zaki rasa Dada ba, gobe zan koma asiti bamu da kuɗin kai ta asibitin burni" Da sauri Danejon ta ce "A siyar da Nagge to" zare ido Hamma Yabi yai ya ce "Aradu ƙarya ne, Uban waye zai taɓa Nagge ai mu dasu mutu karaba" ba tace masa komai ta miƙe tsaye tare da yin waje lokacin rana ta faɗi, can gefe ta nema ta zauna ita ɗaya sai tunani take a haka har akai magariba tana zaune, ganin duhu ya fara yasa ta miƙe tare da zagayawa bayan bukka ta kwaɓe kayan jikinta, halittar jikinta ta tsorawa idanu, musamman ƙirjinta tana mamakin abun mene amfaninsu a jikinta? Ita a gareta basu da wani abu kullum sai dai su ƙara girma. Ruwa ta sheƙa babu ko sabulu tana gamawa tai alwala, wasu kayan fulanin ta ɗauka farare ta saka tare da Ajjiye waɗan can, da sauri tai sallah tana gamawa taci tsiran da Hamma Yabi ya kawo musu, tana ci ta kwanta barci domin da wuri take son zuwa kiwo ta dawo ta tafi tallan kindirmo.

Ciki zafin nama Prince ya saka hannu tare da ɗauke Safwan da mari ya ce "Ka fita a sabgata, kaje ka faɗawa Sarki halin da nake ciki ya ɗaukeni, kuma kasan yana gab da rabani da matata wanda ba zan iya jure hakan ba sam" Safwan ya kalli Prince cike da mamaki ya ce "Ban taɓa ganin mai taurin kai a duniyar Aljanu irinka ba Prince, cutar da yarinyar nan kake fa, babu haɗi tsakanin mutum da Aljani na faɗa maka, abin kunyane ka rasa wacce zaka so sai Bil adam? Allah zai saka mata fa" banza Prince yai da Safwan a wannan lokacin rabinsa na mutum rabi kuma na siffar Aljani da sauri ya juya zai tashi sama Safwan ya ce "Ina zaka? Ba dai wajanta ba?" Prince ya ce "Ba zan iya yin wasu daƙiƙo ba, ba tare da naga matata ba, da matata nake son kwana a yau ɗin nan" yana faɗin haka ya ɓace ɓat kai tsaye Rugar Rome ya nufa. Halisa juya cikin barci taji wani sanyi na ratsa mata jiki, ga wani mafarki da ke ƙafafuwanta sai motsawa suke amma ta kasa koda motsi bada ji take kamar ana danneta. Can dai ta farka a firgice Innalillahi a ruɗe ta fara kallon inda take, tana kwance tsakiyar dokar daji ba gida gaba ba gida baya...



Waye ya kawo Halisa Dajeno Rome cikin dokar daji?...

#Sarautar marubuta
#true life story
*🌈 IDAN BA KE 🌈*

*_Arewabooks@Nimcyluv_*
https://wa.me/+2348119237616

5..
A zabure ta miƙe tsaye tana ƙarewa cikin dokar dajin kallo, babu abin da ya bata mamaki irin yadda taga an sauya mata kayan jikinta, daga na Fulani zuwa na wasu saƙi farare masu kyan gaske. Jikinta na rawa sbd tsoro da tarin fargabar dake ratsa dukkan wasu lunguna na ƙofofin zuciyarta ta shiga ƙarewa jikinta kallo. Idan hankalinta yai dubu to ya tashi ta ƙara razana da halin da take ciki a yanzu, domin ba iya kayan jikinta da aka sauya mata ne kaɗai ya bata mamaki ba, zanan jan lallen data gani kwance a hannunta shi ne ya ƙara ta hanyar mata da hankali, ga sumar kanta da akai mata wasu irin kalba manyan gwanin sha'awa ita bata taɓa ganin kanta yai irin wannan kyan ba sai yau. Waye ya kawota nan Meke shirin faruwa da rayuwarta ne, ina Dadarta?.

Ƙare wa cikin dajin tai babu ko hanyar da zata bi ta nufi Rugarsu, daɗin daɗawa ita kanta bata san a inda take ba, wacce kalar rayuwa ce haka? Daga yin barci kuma sai mutum ya farka ya gansa a tsakiyar daji? Bayan tasan a bukkar Dada tai barci. Tafiya ta shagayi idan ta kalli gabas da Arewa, guda da yamma sai ta saki kuka tare da faɗin "Na lalashe jama'a ina nake ina rugar rume tayi, ina Dadata, ina Shatu, ina Hamma Yabi duk kuna ina wayyooo Hande en boni, Yettore jaumirawo" ta faɗa ɗora hannunta aka tare da sakin kuka, ta fiya kawai cikin dokar dajin tun tana kuka har tai shiru sai idanunta da take rarraba wa a ciki dajin.
Kukan da tayi da kuma gudun data jima tana yi sune suka taru suka haifar mata da wata gajiya wacce ta sanya ko idanunta bata iya buɗewa sosai sbd yadda kanta ke juyawa da kuma yunwar data keji, lokaci zuwa lokaci tana buɗe idanunta tare da zubawa zanan lallen hannunta idanu, tana cikin wannan hali ta ƙaraso wani waje wanda yake da rana sosai hakan yasa Danejo ta wahala fiye da zaton mutum, ga ƙishin da take ji. Daurewa tai taci gaba da tafiya sai dai duk yadda takai da daurewa ta kasa bata san lokacin da jiri ya kwashe ta ba, tai baya luuu zata kifa da sauri aka tareta ana faɗin "Subuhanallahi" mutumin ya faɗa a taushashe yana mai riƙe Danejo wacce ta faɗo jikinsa babu numfashi alamar ta soma kenan.

Kyakkyawan idanunta mai ɗauke da kuriyar ƙwayar ido su ya ware akan Danejo yana mai ƙara jin nutsuwa na saukar masa a jikinsa, a hankali a kuma dukkan wata ƙaunarta ta shiga nunkuwa a zuciyar Prince Bilal. Yanzu ne zai samu cikakken lokacin kasancewa da ita, irin kasancewar nan ta har abada domin baya jin akwai mutumin daya isa ya raba shi da Matar Danejo a cikin wannan Dajin, zai zauna da ita zai rayuwa da ita, tai ta haifa masa yara, ya kuma yi alƙawarin ba zata taɓa sanin shi aljani bane, zaici gaba da zuwar mata a suffar Balarabe kamar dai suffar wani Sheikh ɗin Malami. Ɗaukarta ya yi a hannunsa zuwa gaɓar wani ruwa, jallabiyar jikinsa ta sauka har ƙasa tare da rufe masa ƙofatonsa, a haka ya Ƙarasa tare da kwantar da ita a gefen ruwan wajan da yake da ɗan danshi danshi musamman daya lura da jigatar da tai duk da cewa duk wani abu da take akan idanunsa ne. Yana kwantar da ita ya zauna gefenta idanunsa na juyawa tare da sauya launi zuwa wata kalar, hankalinsa ya karkata gaba ɗaya zuwa cikinta idan yake hango ɗansa dake maƙale a mararta hakan sai cike da farin ciki Prince ya saki Murmushi bakin na rawa ya ce. "Ubangiji ya saka mini sonkiwa zuciyata, tun kina cikin mahaifiyarki, zanci gaba da sonki ba zanyi saken da za a rabani dake ba, kamar yadda aka rabani da mahaifiyarki tun tana asalin inda take rayuwa" shafa cikin nata yai idanunsa na tsiyyayar da wani ruwa ya ce "Babu alaƙa tsakanin mutane da Aljanu, amma naji a wannan karan dama Ubangiji a suffar mutane ya halittoni, mene yasa bakwa iya ganinmu a suffarmu ta zahiri sai dai mu muganku? Ina son ki matata Danejo,ina gab da ɗaukeki zuwa duniyarmu" dariya ya saka gaba ɗaya wajan ya ɗauki rawa da Girgiza can kuma ya ɓace da wajan.

Acan Rugar Rome kowa gari na wayewa suka saba Danejo na tashi zuwa garken Nagge ƙara tatsar nono, hakan yasa Dada bata damu ba sbd ganin Danejon bata cikin bukkar sai Shatu dake kwance a gefe tana barci, Hamma Yabi ya fita tun sassafe zuwa asibitin dake gefen Rugar Rome domin samawa Dada layi. Yana tsaye a a ɗan wajan da mutane suke tsayawa gaba ɗaya mutanan ba sufi mutum goma ba, suna zuwa kamar mutum biyar zai koma ya ɗakko Dada. Wani Likita ne hannunsu riƙe da waya yana dubawa ya raɓa ta gefen Hamma Yabi ya shiga office, Fuskarsa ɗauke da fara'a ya kalli mutumin dake cikin office ɗin ya ce "Dr Hamza na ganka a zaune ina patients ɗin?" Dr Hamza ya dubi Dr Iliya yana ƙara ware idanunsa ya ce "Patients suna can waje, bani da time na duba su serious,idan zaka shekara kana duban jama'ar Rugar nan ba zaka taɓa samunsu da cikakkiyar lafiya ba, ƙazanta ita take ƙara lalata musu lafiyar jikinsu na gaji wallahi, sai Shegen son shanunsu amma basu san yadda zasu kula da lafiyar jikinsu ba" Dr Iliya yaja kujera tare da zama sosai yana faɗin "Ai Dr Hamza sai haƙuri, kasan cikin karkara musamman ruga haka ba komai suka sani ba, kai dai barsu da arziƙinsu wato Nagge su kawai suka sani" Dr Hamza ya ce "Let's leave this matter, it is not in front of me" ya faɗa yana duba wani file, "I got the message you want to see me up, lafiya dai kake mini kiran gaggawa haka?" Dr Iliya ya tambayi Dr Hamza cike da jin don abin dake faruwa. Gyara zama Dr Hamza ya yi kafin ya ce "The government has given free medicine to the people of Ruga, maganin da gwamnati ta bayar suna da yawa, akwai maganin Suger, Hawan jini, Maleriya, da sauran maganin cuccutikan, yawwa sai maganin sikila irin folic acid, Paludrine, Peniciillin V,Hydroxyurea. Anfi kawo maganin Sickler sbd yawaitar samunta da ake cikin karkara, shiyasa nace a kiraka" cikin jin Daɗi Dr Iliya ya ce "Masha Allah yanzu yaya za'ai kenan?" Wani kallo Dr ya Hamza yaiwa Dr Iliya kafin ya ce "Ya kowa za'ai? Kasan Rugar nan ko an basu magani a banza, basu san important ɗinsa ba, so that zamu kwashi 88% a cikin 100 mu siyar mu raba kuɗin, kai ba kana da chamist ba? Sai ka zuba kawai acikin chamist ɗin naka" cike da gamsuwa Dr Iliya ya ce "that's good, amma gwamnati ƙoƙari sosai fa, banda haka wannan maganin sunfi ƙarfin miliyan 3 da wani abu fa,ana kula yanzu da ɓangaren lafiya sosai da masu juna biyu, anywhere zuwa dare zan zo da mota na ɗauki rabona" Sallama sukai tare da fitowa a tare ganin hakan yasa Hamma Yabi saurin kallon Dr Hamza ya ce "Aradun Allah na shafe awanni a nan gashi muna ta jira" a faɗace Dr Hamza ya ce "Wai kai fillon nan wani irin banza ne bagidaje ne kai? You doesn't know anything akan asibiti ka addabi mutane da wautarku ta Fulani, mu bamu da wasu kayan aiki cikin Asibitin nan kana kallo da idanunka ai, dan haka kada ka sake zuwa idan an kawo kayan aiki zamu sanar get out" jiki babu ƙwari Hamma Yabi ya koma cikin Rugar Rome, yana zuwa ya sake tarar da wani tashin hankalin babu Danejo gaba ɗaya acikin Rugar, sanadin hakan yasa jikin Dada ƙara rikicewa abu kamar wasa duk inda suke tunanin ganin Danejo babu ita sam har kusan kwana biyu.

Tunda ya kwantar da ita a gaɓar ruwan har gari ya waye ta kwana a wajan, wani daren ya yi ta sake kwana, kwana biyu kenan amma bata motsa ba. Bata kuma da ranar tashi sai lokacin da Ubangiji ya nufa ko kuma ya tsara. A can cikin barci ta fara mafarki gata da namiji suna kasancewa waje guda, wani abu mai kama dana auratayya na gilmawa a tsakaninsu. Numfashi ta sauke tana motsa ƙafafuwanta zuwa cinyoyinta da suke mata zafi, tana jin kamar an daddaneta a firgice ta farka tana kurma ihu tare da kiran sunan Dada, ba addu'a babu komai. Cikin tsoro ta fara bin jikinta da kallo babu komai lafiyarta ƙalau domin ba wani sauyi da taji. Ajjiyar zuciya ta sauke a bayyane tare da kifa kanta a tsakanin cinyoyinta ta shiga rera kuka, kenan haka rayuwarta zata ƙare cikin dokar dajin ko yaya ne? ya akai ta tsinci kanta a dajin gaba ɗaya ta rasa amsar tambayoyin zuciyarta. A hankali ta fara jin dariya na karaɗe wajan, tare da surutu ƙasa ƙasa. Miƙewa ta yi da sauri ta shiga duba inda take jiyo sautin dryar a haka ta ƙaraso jikin wata ƙatuwar bishiya, cike da tsoro da kuma tarin zullumi ta ɗaga kansa zuwa saman bishiyar idanunta ya sauka akan wani ganyen bishiya dake lilo shi ɗaya, sai ka ɗauka iska ke kaɗa shi amma abin mamaki shi kaɗai ne yake lilo daga cikin sauran ganyen bishiyar. Prince Bill wanda a yanzu ya rikiɗe zuwa suffarsa ta asalin aljani yana kwance saman ganyen yana karkaɗa ƙafarsa wacce ita ce take sanya ganyen bishiyar motsawa, Danejo dai kallon ganyen take cike da mamaki tana tsaye taci mangoro ya faɗo kanta abinka da mai jin yunwa da sauri ta ɗauki mangoron babu Bisimillah ta shiga sha idanunta na lumshewa sbd daɗi. Daga bayanta taci ance. "Kisha a hankali da wasu da yawa idan kina buƙata" juyawa tai da sauri baki buɗe take kallon mai maganar, iya tsoro da razani ta shiga domin bata taɓa ganin halitta irin wannan ba, mangoron ta saka tare fasa wani Ihu ta ɗaga ƙafa zata gudu yai saurin riƙe hannunta.

Share🥰🥰🥰
*🌈IDAN BA KE 🌈*

6....
*_Arewabooks@Nimcyluv_*

"Na shiga uku Aljani Balarabe" Danejo ta faɗa a ruɗe tana ƙoƙarin kwace Hannunta daya riƙe cikin nasa. A nutse Prince ya ware idanunsa sosai a kanta yana Mmkin Yadda duk ta ruɗe kamar taga mugun abu. "Me ya baki tsoro" murguɗa masa baki tai tana suɗe hannunta dake ɗauke da ruwan mangoron ba tare data ce komai ba. Prince ya saki tattausan murmushi mai kyau da tsari yana binta da kallo musamman idan ya tuna abubuwa da suke faruwa a tsakaninsu, sai yaji nutsuwa ta kamasa. Hannunsu ta make ta ce "Sakeni haka kurum kai mini ciki, bayan Dada ta ce ba kyau namiji ya taɓa mace" ta ƙare Maganar tana binsa da kallo, sai a lokacin da a shiga ƙarewa tsarin hallitar jikinsa da kallo, fari ne tas kamar ka taɓa shi jine ya fito, yana da faɗin ƙirji fuskarsa mai cike da ilhama, ga wani gudun saje wanda ya kewaye fuskarsa zuwa ƙasa wajan gemunsa, fuskarsa mai faɗi ce babu wani abu da zai bamban tasa da jinsin larabawa. Prince ya saketa yana mai faɗin "Ciki na nawa kuma?" Zuciyarta na bugawa sosai ta ce "Me kace?" Ya girgiza mata kai yana ware hannun shi ya ce "Babu komai Danejo" zare ido tai tana dafe ƙirji sosai a tsorace ta ce "Kasan sunana? don Allah kasan rugarmu wallahi ɓata nayi ka taimaka kaji ɗan Balarabe" idanunsa ya ɗaga sama tare da daidaita juyawar launin idanunsa ganin yana neman rikiɗe masa, jikinta duk rawa yake tai saurin cakumarsa tare da rirriƙesa wanda yai sanadiyar fitowar wata jela a bayansa, sbd ko yaya ya samu kusanci da ita, baya iya zama a zallar mutum, dole sai wani sashi na

2 Comments On IDAN BA KE
avatar
al-kausar

4 months ago

Reply

Dan Allah ci gaba daga page 11 naga a page 10 ya tsaya Kuma kince akwai complete anan arewa books

avatar
taskar

4 months ago

Reply

Replying to al-kausar

sai dai ki saya littafin a wurin marubuciyar ga nambarta 08119237616

Please Login or Register in order to submit comment