Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

daya shigo yaga gidan a cike.
Babu kuma wani ɓoye-ɓoye Ayyah ta sanar masa aurensa za'a sake ɗaurawa bayan sakkowa masallacin juma'a da Umm-Rumana.
“Ayyah da wuri haka? Nazata ai za a bari sai nan gaba ta kammala makarantarta?.
“Haba ɗan albarka, minene wani abin jinkiri anan, Rumana dai ai ta isa aure, kuma ba baƙuwarka bace balle kace kanason sanin halayenta, kaima ba baƙonta baneba, idan batun soyayya ne kuje can a gidanku zaku ƙullata, tamafi ta shirmen wajen nan daɗi da nagarta, makaranta kuma duka wata nawa ya rage, idan taje gidan naka saita karasa ai, muma munfison ayin kawai hankalinmu ya ƙwanta, dan nafison ka riga yarinyarnan yin auren, muyi addu'a kawai ALLAH yasa haka shi yafi alkairi, maza je kayi wankan ga waɗannan kayan saika saka?.
Jiki a sanyaye ya amshi farar shaddar dake a cikin leda viva yay mata godiya..........✍?







*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏🏻_**ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*

07067124863

*Ko kuma*

09032345899


*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽

https://youtu.be/Zyl7_eSgXuoeSgXuo


*(10)*

............Ƙarfe biyu da rabi na rana ɗunbin jama'a suka sake shaida ɗaurin Ahmad akaro na biyu tare da Umm-Rumana, akan sadaki naira dubu ashirin.
Kansa kawai ya duƙar ƙasa yana haɗiyar zuciya, wai shine aka ɗaurama aure a karo na biyu cikin kwana uku kacal, sannan kuma bada Saminar sa ba, wadda ya ɗauki dukkan buri ya ɗoramawa, dukkan rayuwar aurensa da kullum yake tsarawa a zuciyarsa da itane, amma yau gashi ta nuna masa data zauna dashi gara ta kashe kanta ko shi ta kasheshi.
Kenan yanzu da Rumana zaiyi rayuwar aure? Yarinyar da bai taɓa mata cikakken kallon minti biyarba duk da a gida ɗaya suka tashi, shi zaima iya rantsuwa bai taɓa maganar data kai kalma ɗari da itaba cikin lokaci ɗaya, tsakaninsa da ita a kullum gaisuwa ce, saiko aike, shima sai idan wani dalili yasa ta gitta ta gabansa ne........
Da ƙyar ya iya haɗiye abinda ta toshe makoshinsa, ya ɗago kansa saboda dafansa da akayi a kafaɗa.
Baba Iliyasu dake kansa tsaye yay masa nuni akan ya miƙe, babu musu ya tashi tsaye, kama hannunsa kawun nasa yayi har zuwa gaban jama'ar shema, nanfa Ahmad ya shiga gaishesu cike da girmamawa, saboda yasan dayawan cikinsu dukda bawani sosai ma yake zuwa Shema ɗinba.
Atare suka rankaya zuwa cikin gida, inda aka baje musu tabarmi a zaure suka zauna cin abinci, shi dai Ahmad baici komaiba, yana gefe abin duniya duk ya gallabesa, sai sauke ajiyar zuciya yake a jere a jere.
Bayan sun kammalane sukasa aka kawo musu Amarya Rumana, wadda tun a safiyar yau mahaifiyarta ta zaunar da ita cikin hikima da nasiha ta sanar mata abinda ake ciki.
Tasha kuka, amma tasan ko giyar wake tasha bazata bijirema iyayenta ba, dan ba wannan tarbiyyar mahaifiyarta tai mataba, fargabarta ɗaya tayaya Yah Ahmad zai sota? Mutumin da baya kallon kowacce mace da arziƙi inba Samina ba, ita kaɗai ke ganin fara'arsa, ita kaɗai ke iya jin doguwar maganarsa, ita kaɗai tasan sauƙinsa.
Sukam da ko wasa bayayi dasu, iyakarsu dashi su gaisheshi ya amsa, saiko idan hanya ta haɗaku ya aikeka idan da bukatar hakan, ko ɗinki zai musu baya tsayawa jin style ɗin da suke bukata ko wani ra'ayinsu.
Nasihar da mahaifiyarta da ƴan uwanta sukai mata ce ta sata sake ɗammarar sakama ranta haƙuri, koba komai zata zama sanadin dai-daita barakar dake neman shigo musu a family, sannan zasu hana fitar haƙoran maƙiya da sunan musu dariya, bakin ƴan bani na iya zai rufe ruf wajen maida yanda akayi.
Kanta a ƙasa ta rufe fuska sosai da gyalenta ruwan hanta da akaima kwalliyar ruwan madarar les a baki suka fito, tana sanyene da atanfa ruwan madara mai ƙyau, kayantane na salla da Ahmad yay musu ɗinkin ita da su Samina, kasancewar babansu ne yay musu kayan, dayake sawa biyu kawai tai musu sai kayan suke fes tamkar sabbi, sai ƙamshi take mai sanyi.
Inna marwa dake riƙe da ita tai mata izinin ta zauna, dan sun iso soro inda ƴan shema suke.
Tun shigowarsu kuma Ahmad yake binta da kallo ƙasan ido, wani iri yakeji a zuciyarsa game da wannan auren.....
Nasihar da ƴan uwan nasu ke musu ta sashi katse tunaninsa ya maida hankalinsa garesu.
An musu nasiha mai ratsa jiki, wadda duk ta kuma sanyaya jikin Ahmad, harma da ita Rumana ɗin, dan koba komai ta fahimci wannan auren nasu farin cikin mutane masu yawane, sannan kwaranyewar hawayen mutanene masu ɗunbin yawa da Samina taso sakawa kuka.
Bayan an gama musu nasiha kakanni da abokan wasa suka koma tsokanarsu, yayinda wasu acikin ƴan uwan ke karesu, dansu duka babu mai bakin ramawa, bare dama daga Ahmad ɗin har Rumana dama basu da yawan magana.

Bayan sallar la'asar ƴan shema suka juya zuwa gida, tunda bikine bana shiriba suma basuzo da shirin kwana ba, mutum huɗu kawai aka bari suma tsoffine.

Tafiyar ƴan shema tasa hayaniyar gidan raguwa, hakan yasa Ahmad shigewa ɗakinsu ya cire kaya ya ƙwanta saboda zazzaɓin da yakeji sosai, har ya fara rawar sanyi ma.

Daga cikin gida kuwa babu wanda yasan halin da ake ciki, dan sunata shirin kai amarya ɗakinta, kayan Samina da aka kaine za'a barma Rumana ɗin, tunda dama babu ko cokalin Mama gaje acan, duk dangin su Ahmad ɗinne suka tara suka kai.
Ƴan kayan da Ammin Rumana ta fara tarawa na auren Rumana ɗin aka fiddo ake ɗan wankewa, dukda bana kirki bane zasu taimaketa ko yaya dai.
Duk bikinnan da akeyi fa Samina na gidan, saboda ta nuna abinma bai dametaba komanta yinsa take kai tsaye a gadarance a gidan, hakama Mama gaje, har dariya takema Ammi akan haɗin auren Rumana da Ahmad, wai saji sa gani, nan za'a ringa ƙullar tuwo a kwano ana wucewa dashi gidan Rumana, dan sunsan dai Ahmad bashi da abinda zai riƙe Rumana.
Babu wanda ya kulata akan zancen, dan kowa kwllon wawuya yake matama yanzu, daga ita har ƴar tata.
Gefe kuma ga munafukan ɓoye irinsu Umma (Sailuba uwargidan baba Iliyasu, aminiyar Mama gaje a gidan idan baku mantaba) dan tana ɗaya daga cikin mai tunzura mama gaje da Samina akan auren Ahmad, bayan itama akwai sangamemiyar budurwa a gabanta Salima, dan sa'arsu Rumana ɗince, tarema suka tashi su uku tamkar tagwaye, Umm-Rumana, Fa'iza ƙanwar Ahmad, sai Salima ɗin.

Ayyah da bataga giccin Ahmad ba tunda aka dawo ɗaurin aurene abin ya dameta, dan haka ta aika a duba matashi ko yana ƙofar gida wajen abokansa.
Koda Abu yaje ya tambayi su Rabilu sai sukace aisu tunda aka dawo daga ɗaurin aurenma basu sake ganinsaba, sun zata yana cikin gida yana wani abun.
Babu shiri Ayyah ta fito zuwa ɗakinsu Ahmad, saita iskeshi yanata rawar ɗari a bargo, hankalinta ya tashi sosai, tasaka Abu ya kira mata Baba Hamza.
Tunda baba yaga halin da Ahmad yake ciki sai tausayinsa ya kamasa, sunata jera masa sannu shi da Ayyah, a ɓoye ba tare da kowa ya saniba Mudanseer ya kira wani mai aikin asibiti anan kusa dasu ya duba Ahmad ɗin.
Bai ɓoye musuba ya sanar musu damuwace tai masa yawa, shine harta haddasa masa zazzaɓi, dan baya samun isashshen barci ma, ga malleria kuma a gefe itama.
Magunguna ya basa, yace yaci abinci sannan yasha ya kwanta danya samu isashshen barci.
Har Ayyah ta kawo masa fura yasha da ƙyar, zata bashi maganin baba ya dakatar da ita akan ta barshi ba yanzuba, tunda likitan yace akwai na barci suɗan ɗaga ƙafa zuwa anjima, dan Malam yace yau za'a kai Rumana, to kenan bayasha magani yay barci a nanba kuma, bayan an kaita sai yasha yatafi can ya kwanta.
Dole Ayyah tabi wannan umarni na mijinta, suka bar Ahmad, sai dai ruwan ɗumi da aka kawo masa yay alwala yay sallar magriba da isha duk a ɗaki, lokacinne kuma Ayyah ta sawo Gwaggo gaba a ɓoye tazo ta duba Ahmad ɗin.
Sannu tai masa sau ɗaya ta ɗauke kanta sai kace bata damuba, nanko ranta sai suya yake da halin da yaronta ke ciki, amma kawaici ya hana agani koda a fuskartane.

Kusan ƙarfe tara aka mika Rumana da tasha kuka tamkar hawayenta zasu ƙare ɗakinta, tasha nasiha a wajen iyayenta da dangin mahaifiyarta, malam ya bata ƙyautar da ko ita batasan minene a cikiba, hakama Iya ta bata.
Duk wanda yaga yanda take kuka saita bashi tausayi.
Haka suka mikata, basu wani jimaba suka barota tana cigaba da sharɓar kukanta.

Tunda Ayyah taga ƴan kai amarya sun wuce tazo ta tada Ahmad, da ƙyar ya iya tashi ya watsa ruwan zafi da Ayyah ta ɗumama masa, Abu yakai masa bayi, bai wani jimaba ya fito, jallabiya kawai ya bukaci a basa ya saka, dan haka Mudan ya fesheta da turare sannan ya bashi.
Baice komaiba ya saka, Ayyah tai zaman lallaɓashi yasha magani, da ƙyar yasha kuwa yana tsuke fuska da yamutseta, harda yunƙurin amai saboda tsanar da yayma magani.
Suka dai samu ya haɗiye duka da kyar.
Nasiha Ayyah ta sake masa da baba, kafin Mudanseer ya rakoshi inda Sufyan ke jiransa da mashin.
Shine ya ɗaukesa ya kaisa gida, kafin suje sai rawar sanyi yake, yanata sake ƙudundune hannunsa a ƙirji, ga jiri na ɗibarsa sabida rashin ƙwarin jiki.
Dole Sufyan ya taimaka masa har cikin gida, yay sallama a ƙofar ɗakin Umm-Rumana da har lokacin take zaune tana kuka ta amsa.
Izinin shiga Sufyan ya nema, ta bashi sannan ya shiga riƙe da Ahmad cikin ɗakin.
Babu shiri ta mike tana kallonsu a firgice, dan sam batasan Yah Ahmad baida lafiya ba, da taimakon Sufyan Ahmad ya kwanta saman gadon, Sufyan ya mikama Rumana ledar maganin Ahmad da kazar da suka saya musu da lemon ɓawo sai kankana.
“Amarya kiyi hakuri, angonki ya shigo miki ba yanda kowanne ango ke shigoma amryaba, bashi da lafiyane, muna fatan zaki kula mana dashi nanda kwanaki kaɗan ya dawo mana Ahmad ɗinsa jarumi mai yawan juriya da kowa ya sani, ALLAH ya baku zaman lafiya da zuri'a ɗayyaba, ya kara muku hakuri da fahimtar juna, ya dasa muku soyayyar juna a zukatanku mai karfi daban mamaki da kwatance ga ma'abota soyayya?..
Itadai kanta a kasa tana hawaye bata iya bashi amsaba, ya juya ya fita yana faɗin ta rufe ƙofar shi ya wuce.


★★★★?

Sama-sama Ahmad ke jin Sufyan harya fice, daga bayama barci mai ƙarfi yay awon gaba dashi.
Har lokacin Rumana na tsaye tana hawaye, sai da taji tsayuwar ta gundireta ne ta ajiye ledojin hannunta ta nufi ƙofar ta rufe addu'a ɗauke da bakinta kamar yanda mahaifiyarta ta koyar da ita.
Zama tayi kawai ta zuba masa ido tsawon lokaci, tausayinsa na sake ratsa zuciyarta.
Itama kantane ke mata azabar ciwo, dan haka ta lallaɓa taja bargon dake saman gadon ta lullubama Ahmad data lura yana rawar ɗari, tana sakawa kuwa taga yajashi har saman kansa ya sake kudundunewa da ƙyau, ajiyar zuciya ta sauke tausayinsa na sake kamata.
Tsawon lokaci tana wajen har ta farajin saukar numfashinsa ya canja alamar barcinsa yay nisa sosai.
Tasan dolene a tausayama Yah Ahmad, dan halin da yake ciki abin dubawane, akwai tashin hankali abinda ka girma dashi a zuciyarka yazama shine sanadin rusa dukkan farin cikinka a dare guda.
Sabuwar tabarmar dake a ɗakin ta dauka ta shinfiɗa ƙasan ledar da aka saka a ɗakin ta kwanta ba tareda ta saka koda zaniba, sai filo data ɗauka kawai a gado saboda bata iya kwanciya babu shi.
Gyalen jikinta ta rufa dashi dukda bashi da wani kauri sosai.
A haka taci gaba da kukanta har itama barcin yay nasarar saceta, ga kanta yana sara mata sosai da ciwo.


_______________________________


A wannan darenma Samina da Ma'aruff sunsha hirarsu ta masoya, inda mafi yawan firar duk ta karkata wajen tsara yanda shagalin bikinsu zai kasance.
Daɗi tamkar zai narkar da ita, sai wani lumshe ido take tana dafe ƙirji da washe haƙora, har yanda take buƙatar lefenta ya kasance da kalar akwatunan da takeso da kayan gidan dazai zuba mata duk sai da ya tambayeta, sai events na garari na nunawa a gidajen tv da social media shima duksun tsara abinsu.
Cikin shagwaɓa take shaida masa yafayi ta turo manyansa, dan ita yanzu dukta tsani komai na gidansu, sotake ta kara gaba tabarsa kodan ƴan bani na iya.
Daga can Ma'aruff yay murmushi yana faɗin, “Karki damu gimbiyar mata, ni kaina na kagara na jiki a jikina lafe, ina baki gangariyar soyayya da babu sirkin ruwa a cikinta, burina kawai mallakarki tunda kinki bani damar hakan tun a yanzu, kince sai munyi aure, niko nayi biyayya na haƙura har a ɗaura a kawomin ke babie?.
“Oh ni kana bani kunya, gara dai kayi haƙuri harnazo, dan saboda na faranta makane ma nai duk abinda ya dace kar wancan shashashan ya sameni, dan kaɗan daga aikinsa ya kwata cikin ƙarfi, niko kai kaɗai nake burin cikama alƙawarin kawo maka budurcina har gida?.
“Nagode ta wajena, shiyyasa nake ƙara jin sonki na ƙaruwa a raina a kowacce daƙiƙa, dolene nazo na samu su baba ayi komai da wuri, insha ALLAHU nanda karshen wata kina nan kwance a ƙirjina?.
Yanda yay maganar da wani irin salone yasaka tsigar jikin Samina tashi, ta sauke nannauyan numfashi daya sake haukatar da Ma'aruff daga can, hakan yasashi kuma manne karuwarsa dake barci a jikinsa, dan saida ya gama holewarsa ne ma ya kira Samina ɗin.
“Sai da Safe?
Samina ta faɗa a sanyaye saboda kasalar da ya sakar mata da kalamansa.
Shima da “Uhmm? kawai ya iya amsa mata ya yanke wayar yana sake maida karuwarsa a network.

Haka Samina tai barci da ɗunbin begen abokin hakittarta, dolene ma tai yadda zatai ai aurensu da Ma'aruff a nan kusa, koba komai ta samu nauyin shekaru dake gallabarta ya fita. A shekarun da suka shuɗe Ahmad kawai take iya suffantawa da wannan yanayin, amma zuwa yanzu sam ba haka bane.
Wani gefe na zuciyarta yace yanama can yana hutawa da kanwarki amaryarsa kuma Rumana.
Baki ta taɓe tana jan tsaki, sai kuma ɗayan gefen zuciyarta ke shaida mata sam Ahmad bazaiyi hakanba, dan tafi kowa sanin halinsa idan ka ɗebe iyayensa, dan ko ƴan uwansa tafisu sanin wanene Ahmad akan abinda yake so, tasan kafin Rumana ta samu gane kan Ahmad za'a yara, dan soyayyarta ta riga ta masa ƙullin yaɗon wake a gona, kafin zuciyarsa ta fara kallon Rumana matsayin mace sai anyi babban dagama...............✍?








*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*a: *ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*

07067124863

*Ko kuma*

09032345899
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment