Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gefe kuma gasu Nafy sunayi ta waya da zahiri idan sunzo gidan da ƙaryar dubata.
Dan dukan da baba Iliyasu yay mata ciwo sosai ya sakata, ko magana mai ƙarfi ta kasa yi.
Kuma Ahmad ɗin dai da bakinta bai gajiya da munanawane ya samo likita ya dubata, ƴan kuɗin dake aljihunsa na ɗinki da aka biyasa ya cire ya biya kudin magani dama duk abinda aka buƙata.
Tun anama Samina mazurai har iyayenta maza da Amma suka koma lallashinta dukdan ta kwantar da hankalinta ta fahimci halin da ake ciki.
Sai dai sam taƙi fahimta ɗin.

★★★★?

Tsahon kwana huɗu abu yaƙi ci yaƙi cinyewa, saima neman ɗakin da zasu zauna haya akeyi.
Ahmad kuwa yaƙi cewa kowa komai, sai bushewa yake a tsaye saboda damuwa, harya fara duhun baƙi, gashi abun na neman taɓa masa aikinsa na ɗinki, dan yanzu ya daina yin komai sai tunani.
Wanka wannan sai Ayyah ta sakashi a gaba yakeyi, hakama abinci sam bayason ci sai an masa faɗa.
Yana ƙaunar Samina sosai, duk wannan haukar cin mutuncinsa da takeyi bama yajin haushinta, a ganinsa canja masa ita akai kawai, dan Saminar sa ba haka takeba da can.
Gashi duk yanda yaso su haɗu taƙi bada ƙofar hakan, duk sanda ya aika a kirata zagi ma take maido masa, idonta ya rufe gaba ɗaya, burinta kawai Ahmad yay zuciya ya saketa.

Yau data kasance duk yaran gidan na ma'auri sunzo gidan akan wannan maganar aure data bama kowa mamaki, masoya sun zama maƙiya, wanene a anguwar baisan soyayyar Samina da Ahmad ba, sai dai baƙon da bai wuce sati ɗaya ba.
Binta yayar Samina ta kalli Saminar dake kwance a saman gadon Mama Gaje tana sharɓar hawaye, ga zazzaɓi daya rufeta saboda ƙuntata kanta da takeyi a kwanakinnan.
“Humm anya Samina kina ganin kuwa kinma kanki adalci a wannan gaɓar? Anya kuwa kece Samina ƙanwata dana sani mai tsantsar ƙaunar Yah Ahmad. Mike ruɗaki hakane kike son tafka babban kuskuren da anan gaba baki da hanyar gyarashi? Miya shiga kankine? Samina kibar biyema mama wlhy, dan daga ita har Inna mari babu mai faɗa miki gaskiya akan batunnan, kwaɗayi ya rufe muku ido ku duka, kun manta UBANGIJI dake bayarwa bai manta da shi yah Ahmad ɗinba, sannan kuma aiba ALLAH ne ya sanar muku shima bazai taɓa yin arziƙinba ko? Duk gwamna da kika gani ko ɗan majalissa, ko minista, ko kwamishina, ko shugaban ƙasa, ko babban ɗan kasuwa, ko babban ma'aikacin gwamnati to shima a baya talakane, kije ki bibiyi tarihinsa kiji, talakannan da zaki aura wataran shine zaki buɗa ido ki ganshi a wancan matsayin da ayanzu ya maida ganinki duhu Samina, wlhy dana auri mai arziƙi gara na auri talaka musha wahala tare wajen tara arziƙin, koba komai zai mutuntani ya girmamani, sannan ko mata dubu yayi a bayana sai yafi nuna kulawarsa gareni fiye dasu, a wannan zamanin kuma Samina yanda maza suka lalace da wulaƙanta mace a gidan aure, wlhy kasamu mai maka soyayya irinta Yah Ahmad ka gama morewa, kwanciyar hankali a gidan aure ita mace ya kamata tayi fata a wannan zamanin ba dukiya ba, dan daga lokacin da mai dukiyar ya kaiki cikin gidansa to fa ina gaya miki komai zai canja, dan kinbar ganin farin cikinsa da lokacinsa kuma, ki zauna kiyi tunani, karki bari damarki ta wuceki, dan daga lokacin da kika kai haƙurin Yah Ahmad bango yaji ya dace ya sakeki tun a sannan zaki fara nadama har ƙarshen numfashinki wlhy.......?
“Aniyarki ta koma miki, kujimin Yaya Bintar nan da mugun baki, ai dawwama a auren Ahmad ne zaisa nayi nadama har ƙarshen numfashina, rashin auren Ma'aruff kuwa shine sakaci da damata, idanma tunani kike maganganunki zasuyi tasiri a kaina to basu shigaba, dan jinsu nake busar sarewa ma ta fisu daraja, idan kuma shine ya aikoki kije ki sanar masa ba'a daceba, nace bana sonsa a yanzu, ko dolene saina zauna dashi, ana so dolene? So kuke nima na ƙare cikin talauci da fatara a gidan miji kamar ku, a cikinku kaf babu wata mai abin nunawa a gidan miji inba talauci ba, jibeki, shekarunki gaba ɗaya basu wuce talatinba, amma saikace tsohuwar data ƙulla hamsin, a dalilinmi zan zauna na ƙare a talauci kamar ku, aini bama ƙaramin sona ubangiji yakeyi ba da ya kaini matsayin ƙara karatunnan, da haka nima za'a cutamin, a bankani ɗakinsa na ƙare rayuwata a wahale, wataranma har surfau ɗin masara da wankau sai an sameni inayi saboda fatara da rashin abincin arziƙi mai ɗan maiƙo-maiƙo?.
Binta da tai shatata da baki tana kallon ikon ALLAH daga Samina, taɓe baki, lallai ƴar uwar tata tayi nisan da sam bazataji kiraba.
“To ALLAH ya ƙyauta miki Samina, ai duk wanda yace zai iya haɗiye gatari sai a sakar masa ƙota, ALLAH yasa kar Yah Ahmad ɗin ya sakeki muga tsiya?.
Baƙin ciki sosai maganar Binta ta ƙarshe taima Samina, a masife tace, “Bakinki ya sari ɗanyen kashi, muguwa kawai azzaluma?.
Dariya Binta ta fita tanayi, inda tun fitowarta mama Gaje ke zuba mata harara tamkar idonta zai faɗo, ɗanwake take jefawa a tukunya, shiyyasa koda take jiyosu bata shiga ɗakinba.

A ɓangaren su Ahmad ma ƴan uwansa ne zagaye dashi, shawara suketa bashi akan yayi haƙuri yabar Samina tunda tace bata yinsa yanzu, da adawo ana dana sani nan gaba barin auren tun yanzu kamar shine yafi alkairi.
Murmushi mai cike da damuwa Ahmad yayi, murya a sarƙe yace, “Yaya Maryam ina sonta, nasan duk abinda take faɗa shirmene kawai, nan gaba kaɗan zata bari muyi zaman lafiya, ana kaitane zakuga wannan shirmen dukta bari, yanzunma zugata akeyi shiyyasa?.
Gaba ɗayansu zuba masa ido kawai sukayi da mamaki, sunsan ɗan uwan nasu akan Samina babu abinda zasu faɗa masa ya fahimcesu, sai kawai duk sukaja bakinsu sukai shiru.

Haka Samina taci gaba dayin bore tsawon lokacin satin nan uku da suka shuɗe, a kuma na huɗun da aka shigane tarewar nasu, dan an samu ɗakin da zasu zauna anan ƙasan layin nasu kaɗan, harma an masa fenti, yayinda iyayensu maza suka haɗa kuɗinsu kamar yanda sukeyi aduk ƴaƴansu da zasu aurar aka siyama samina kayan gadon gwargwadon ƙarfinsu.
Kasancewar bikin yazo babu shiri sai baba Rabi'u yace ƴan shema ba sai kowa yazoba, su zaɓi wasu a ciki su ɗanzo a raka Saminar ɗakinta shikenan, dan ta jama kanta baza'ai wani taron bikiba...........✍?


*_Bilyn Abdull ce_*




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻*ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*

07067124863

*Ko kuma*

09032345899


*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽

https://youtu.be/Zyl7_eSgXuo




*(9)*

............Ahmad dai duk abinda akace masa da to kawai yake amsawa, abokansa ma dake jin haushinsa akan dagiyar da yayi kan Samina haka suke taimakonsa da ɗan abinda ALLAH ya hore musu, haka suka ɗan gagganɗa sukai masa ɗinkuna kala biyar na angwanci, suka kuma haɗa kuɗin fentin ɗakin da za'a saka amarya tare da yin ƴan gyare-gyaren da suka dace ayi.

Mama gaje dai taƙi bada ko cokali da sunan kayan ɗakin Samina, haka su Binta sukaje suka jera katakan gado sai katifar da aka saka, amma ko zanin gado babu.
Sai da ƴan shema sukazo sai ga inna marwa da ƴar gudunmawarta, annan ne aka sami zanin gadon da aka saka a gadon, sai ƴan kwanika da dangi suka haɗa suma akaje aka ajiye mata.


________________________________

Ayyah harda kukanta lokacin da takema Ahmad nasiha akan haƙuri da wannan aure nasu da babu fasali a cikinsa, tasan matsaloli yanzunne zasu fara tunda zasu kasance a inuwa ɗaya, ga kuma Samina har yanzu tana akan bakanta na bazata zaunaba, harma da iƙirarin saita kashe Ahmad ɗin.
Shima baba ya masa nasiha, hakama Iya da malam, kowa dai muhimmancin haƙuri yake nuna masa, dan kuwa dai tsakaninsa da Samina haƙurinne kawai zai riƙe a zauna lafiya.

Ansha danben bala'i wajen fidda Samina a gidan, dan kuwa hayaniya ce sosai ta ɓarke tsakanin dangin mama gaje da nasu Ahmad, dan ɓoye Samina sukai suka hanata fitowa, sai da Baba Yusha'u ya shiga da kansa ya taso ƙeyarta yana cewa duk su tattara su bar masa gida.
Itama Saminar data nema tirjewa ya lakaɗa mata uban duka, ko wanka batayiba aka cimimiyeta zuwa gidan da zasu zauna matsayin Amarya.


*_10:30_*


Kowa ya kalli Ahmad a wannan lokacin yasan akwai damuwa, cikin danne fargabarsa yabi umarnin Ayyah yay wanka, cikin kayan da su Sufyan suka ɗinka masa ya saka ɗaya, yasa turare kaɗan ya fito.
Iyayensa sun bisa da addu'a, yayinda zukatansu duk suke a tsorace gameda ikirarin Samina na kashe Ahmad a randa suka tare.
A waje ya iske abokansa, ya basu hannu duk sukai musabaha, sannan suka take masa baya har gidan da aka kai masa amaryarsa.
A ƙofar gida su Salisu duk suka ja birki, Sufyan ya miƙa masa ledar da suka sayo kaza yana ɗan bugun kafaɗarsa cikin tsoka.
“Ayi amarci a hankali kar da safe mu nemo kafintan gyaran gado?.
Gaba ɗayansu dariya suka sanya, amma banda Ahmad da sam zuciyarsa ba'a wajensu tameba, sun masa sallama bayan addu'a da sukayi suka juya, rufe gidan yayi ya shiga da sallama.
Bawani babba bane gidan, irin dai gidajen talakawa ne da kowa ya sani, sai dai su biyune kawai a ciki suke haya, ɗayar matar ita kaɗaice sai mijinta da yaransu biyu, saisu Ahmad ɗin yanzu da suka tare.
Ɗakinsu shine farko, dan haka kai tsaye ƙofar ya dosa, gabansa sai faɗuwa yakeyi, hakanne ya sakashi dakatawa ya karanto addu'oi neman tsarin ALLAH daga sheɗan.
Labulen ya ɗaga ya shiga ɗakin da sallama, ɗakin sai ƙamshin sabon benti yake dana katako, Samina na zaune a bakin gado ta duƙar da kanta kamar mutuniyar ƙwarai, hijjab ne jikinta ruwan hanta, shiyyasa bai fahimci a wane yanayi take ba.
Jiki a sanyaye ya ajiye ledar hannunsa, murya can ƙasa yace “Samie na?.
Shiru bata tanka masaba, ba kuma tai motsiba, hakanne ya sakashi matsawa gareta ya kai hannu zai taɓata, wata muguwar zabura tayi tana miƙewa tsaye, ta fiddo hannunta dake riƙe da sabuwar wuƙa fil da keta ƙyalli.
Hawaye na kwarara a idonta tace, “Wlhy kana taɓani saina soka maka wuƙarnan, idan kanason kanka da arziƙinka ka sakeni kawai?.
Ahmad dake kallonta ya riƙe ƙugunsa da hannayensa duka biyu, murmushin da ya daɗe baiyiba ya saki, yace, “Haba Samina, Ahmad ɗinki nefa, ki kwantar da hankalinki dan ALLAH mu fahimci juna.....?
“Fahimtar juna? Yo ai kasani babu ita a tsakaninmu a yanzu, saki kawai nake buƙata daga gareka, inba hakaba ALLAH saina kasheka yau a ɗakinnan?.
Murmushin ya sake yi yana sauke numfashi, ya rungume hannunsa ɗaya akan ƙirji yana kai ɗayan a fuskarsa ya shafo ɗan gemunsa na gayu.
“Samina bazaki samu abinda kike bukatarba kuwa, sai dai idan ki kasheni, koba komai zanbar tarihin masoyiyata ta kasheni da hannunta, kuma koba komai zakimin takaba ai ko?.
Wata dariya da ta bama Ahmad mamaki da tsoro Samina ta kece da ita, ta ajiye wuƙar hannunta tana haɗe fuska, “Oh da wannan banzan ƙwarin gwiwar taka ka dogara shiyyasa ka kafe bazaka sakeni ba? To ai shikenan, nama fasa kashekan, kaina zan kashe, kaga saika zauna da gawa ai?.
Kallonta kawai Ahmad yake duk da furicinta ya tsoratashi, amma yasan faɗa kawai take danta tsoratashi.....
Katsesa tayi da faɗin, “Ka sakeni nace malam?.
Cikin halin ko in kula Ahmad ya zauna bakin gadon yana cewa, “Idanma zaki kwantar da hankalinki ki kwantar Samina, dan nikam dai ba sakin naki zanyib......?
Warin fiya-fiya da ya shaƙoma hancinsa ya sakashi saurin juyowa yana kallonta.
A wata irin zabura da ƙwala kiran sunanta yakai hannu ya cacumota, kwalbar fiya-fiya data kafa a baki har tasha kusan kwata ya kaɓe ta faɗi ƙasa, yayinda idanun Samina suka fara juyewa, saiga bakinta ya fara kumfa.
Sosai Ahmad ya fashe da kuka yana jijjigata tamkar mace....

Waɗanda suke gidan da duk suke jiyo mahawarar Samina da Ahmad daga ɗakinsu tun daga farko ne suka fito a guje, lokacin numfashin Samina harya fara fisga.
ALLAH ya taimaka mijin matar yanada motar da yake haya, nanfa Ahmad ya ɗauki Samina bisa umarnin mutumin suka kaita mota, babu ɓata lokaci suka doshi asibiti.

Da ƙyar su Ahmad suka samu aka karɓi Samina, sai da sukai ƙarya akan a mistake tasha fiya-fiya catake maganine sannan aka amsheta.
Komai ya kwancema Ahmad, babu abinda yakeyi sai hawaye, dan sam bai kawo shirmenta zai kai girman hakaba, duk ya ɗauka farfaganda ce kawai danya mata abinda takeso.
Har washe gari kuma basu sami labarin farfaɗowarta ba daga likitoci, duk wanda ya fito suka tambayesa baya basu amsar komai.
Tunda Safe matar wanda ya kawosu asibitin taje gidan su Ahmad ta sanar da duk abinda ya faru, hankalin kowa ya tashi a gidan, musamman ma iyayen Ahmad, mama gaje kuwa kuka take tana faɗin bazata yardaba, inhar Samina ta mutu sai sunje kotu wlhy, shima Ahmad sai an kasheshi, dan shine ya kashe mata yarinya.
Har suka iso asibitin babu wani bayani ƙwakwkwara daga likitoci, Ahmad ya faɗa jikin baba Hamza yana kuka, duk yayi wujiga-wujiga, kallo ɗaya zakai masa kasan shima yana buƙatar a bashi gadon.
Sai kusan sha biyun rana labarin farfaɗowar Samina yazo musu, amma dukda haka tana a cikin mawuyacin hali da addu'a kawai take buƙata.
Hankali yaɗan kwanta, amma banda na Ahmad, daga baya ma jirine ya kwasheshi ya faɗi, sai da aka saka masa ƙarin ruwan da ya sakashi dogon barci.

Har zuwa la'asar Ahmad bai farkaba, zuwa lokacin kuma ita Samina ta farka, idan ka ganta dolene ta baka tausayi, tayi wani zuru-zuru, idanun sun sake fitowa, amma dukda wannan mawuyacin halin da take faɗi take sai Ahmad ya saketa.
Zuwa dare Ahmad ma ya farka, babu laifi jikinsa ya ɗan masa ƙarfi, tunda har shiga yay ɗakin da aka kwantar da Samina ya dubata, lokacin ta sake komawa barci, sosai tausayinta ya kamashi, ya share hawayen da ke zuba masa saman fuska yana ɗauke idonsa daga gareta, son gaskiya yakema Samina, dan haka bazai barta ta ƙuntataba insha ALLAHU.


________________________________

Bayan kwana biyu abubuwa sun ɗan lafa, jikin Samina da sauƙi, haka shima Ahmad, sai dai damuwar da ta zame masa fitar numfashi.
Babu abinda ke ƙara sukar zuciyarsa irin zuwan Ma'aruff asibitin, a gabansa Samina ke nuna kulawarta ga Ma'aruff duk da igiyar aurensa har uku suna kanta, sannan komai na asibitin ma'aruff ne ya biya, har abinci da kayan ciye-ciye shiyake kawo musu, shi ko koya sayo ɗan abu dai-dai karfinsa koma kallonsa ba'ayi, agabansama za'a ɗauka a saka a bola.
Haushin hakanne ya saka Rahma yin magana, amma sai baba hamza ya ƙwaɓeta akan tayi shiru, komi zasu gani daga mama gaje karsu sake cewa komai.

Ranar da yamma aka sallamo Samina, ma'aruff ya ɗakkosu a motarsa ya kawosu gida, Ahmad sai mashin ya hawo ya biyo bayansu.
Babu wanda yace komai akan hakan, kowa ya shiga yay mata sannu, hakama maƙwafta sunata shigowa, ƴan son ganin zahiri a ɗauka ai gaba sunta gumtsar gulma.
Ahmad dai tunda suka dawo yana ɗakinsu kwance, sai bayan sallar isha'ine ya shiga gidan, Ayyah ta samu ta titsiyeshi yasha furar data saya masa tun da rana.
Bayan ya gama sha ne yaje ɗakin baba ya amsa kiran da yay masa, sun ɗan tattauna kafin su fito zuwa sashen malam Rabi'u.
Kamar yanda Ahmad ya bukata dukkan iyayensu mata da maza sun hallara.
Ahmad na share hawaye tamkar mace ya fara magana cikin nutsuwa.
*_“Da farko dai ina godiya ga ALLAH sannan a gareku iyayena, nasan kun nuna dukkan hallacinku gareni, tareda ƙoƙarin ɗaura igiyar da zata ƙulle zumincinmu fiye da da, ina neman afuwa a gareku badan, kubani dama na aiwatar da abinda zai kawoma kowa kwanciyar hankali, ba tare da abinda muke gani dai-dai ya koma kuskureba. Son gaskiya nake miki Samina, wanda babu ta yanda idan na musalta za'a fahimceni, a tawa fahimtar ka bama abinda kakeso kowacce irin damar da yake buƙata kuma zata kawo masa kwanciyar hankali da farinciki shine soyayya ta gaskiya, na fahimci a yanzu sam hankalinki baya gareni, to bazan tursasakiba, ni Ahmad Hamza Rabi'u ku shaida daga yau, na saki matata Samina saki daya, domin sadaukar da soyayyata ta gaskiya, taje ta auri wanda takeso, ALLAH ya basu zaman lafiya da zuri'a ɗayyaba?._*
Ahmad ya ƙare maganar yana share hawaye masu zafi dake gangaroma kumatunsa.
Tsit ɗakin yayi, hatta da Samina sai da taji wani iri a ranta, amma tai saurin ture tausayinsa tana sauke numfashi irin na na rabu da ƙaya ɗinnan.
Malam Rabi'u ya saki murmushi irin nasu na manya, cikin muryarsa ta tsufa yace, “Amadu ALLAH yay maka albarka, ALLAH ya tsare gabanka da bayanka, ya share hawayenka, ya sanya farinciki a rayuwarka har gaban abadan, lallai kacika namijin gaske mai soyayya dan ALLAH, inaji kuma a raina koda ba'a nan duniyaba zaka samu ƙyaƙyƙyawan sakamako?.
A tare baba Iliyasu da baba Yusha'u sukace, “Insha ALLAHU? daga nan suma suka ɗora da sanya masa albarka, baba Yusha'u yace, “Ahmad a karo na biyu inhar ka amince na baka auren Umm-Rumana, badan komai nake ƙwaɗayin wannan haɗinba sai ƙyawawan halayenka, duk uba daya mallakeka matsayin ɗa ya gama hayewa a rayuwarsa, hakama duk surukin da ya sameka matsayin suruki yaci riba, yanda naso wannan haɗin zumincin bana fatar bijirewar wadda bata ɗaukeni da muhimmanciba zaisa gwiwa ta sarewa?.
Murmushi nanma malam yayi, idonsa kafe akan Ahmad da ya kasa koda motsi, shida yake ƙudirawa a ransa safiyar gobe zai bar garin gaba ɗaya yay nesa dasu shine za'a masa wannan dabaibayin kuma?.......
Cikin katsema Ahmad tunani malam yace, “Amadu inhar wannan haɗin bai maka ba karka cutar da kanka, dan kuwa ba tilas bane a gareka, amma ni kaina nayi maka sha'awar hakan, dan Umm-Rumana yarinyar kirkice da kowane miji zaiyi fatan samu?.
Innalillahi...... Ahmad yaketa ambata a ransa, wannan magana ta masa girma, shidai a yanzu bai dace ya bijirema iyayensa ba kodan abinda Samina ta aikata, sannan koba komai itama zai maida mata murtani, kamar kuma yanda yay alƙawarin haƙura da ita auren Umm-Rumana ne kawai zai tabbatar masa da hakan tunda ubansu ɗaya...
Ayyah ce ta dafashi, hakan yasa yay saurin kallonta, da ido taimasa alamar ya amshi auren, dan haka ya maida kansa ƙasa ya duƙar yana faɗin, “Na amsa baba, ALLAH yasa haka shine mafi alkairi?.
Dandanan fuskar kowa ta washe da murmushi, banda Samina da mama gaje, dan mama gaje ma baki ta taɓe ta miƙe riƙe da hannun Samina da tai gajeren tsaƙi suka fice.
Babu wanda yabi takansu, balle a nuna an damu dasuma.


★★★★

A wannan daren kam inhar Ahmad yayi barci to sai dai ɓarawo kuwa, dan komai ya juye masa, har mamakin abun yake da tunanin koma dai mafarki yakeyine?.
Ya ayyana hakan a ransa yafi sau dubu, harma Mudanseer dake kwance gefensa ya kasa jurewa ya tashi ya fara masa nasiha da shawarwari duk da kasancewarsa yayansa, tare da haƙuri akan canjin da ALLAH yay masa akan Umm-Rumana, inhar yay haƙuri ya riƙe watarana zaiyi dariya insha ALLAHU, ya cire zancen Samina a ransa, ya fuskanci sabuwar rayuwar gida wata soyayyar, kamar yanda itama ta nuna ta manta da shi da komansa.
Yaji daɗin shawarar ƙanin nasa sosai, dan haka ya samu ƙwarin gwiwar tashi yayo alwala yazo ya fara nafilfili yana miƙama ubangiji kuka sa.
Ranar haka ya kwana kan sallaya, sai da suka dawo sallar asubahine ya samu ya kwanta ramuwar barci.


**********

Ɓangaren Samina jinta take sakayau, duk da wani gefe na zuciyarta yana suka akan maganar haɗa Umm-Rumana aure da Ahmad, sai dai kuma tana ƙokarin kauda abin a ranta baki ɗaya, musamman yanda jikinta har yanzu babu ƙarfi, ga Mama Gaje kuma nata zuga ƙoƙarinta akan abinda tayi har Ahmad ya saduda ya saketa.
Ranar dai da tsantsar farin ciki tai barci, kusan raba dare sukai tana hira ita da Ma'aruff a waya, kowa na ƙara jadadama ɗan uwansa irin ƙaunarsa da yakeyi cikin zuciya da ruhi.

Umm-Rumana kam batasan bikin da akeba a kanta, dan babu wanda ya sanar mata da komai, ko mahaifiyarta batace mata komai akan maganarba.
Amma batayi baƙin ciki akan aurar da ɗiyarta ga Ahmad ba, dan kowa yasan mutumin kirkine, bashi da wani mugun halin da za'ace abin gudu a rayuwarsa, to mizaisa tayi baƙin ciki da hakan, tunda har mahaifin Umm-Rumana da kansa yaga nagartar Ahmad yakuma ji a ransa zai masa halacci da ɗiyarta, fatan alkairine kawai nata da musu ƙyaƙyƙyawar addu'ar zaman lafiya.


___________________________

Babu wanda yay tsamanin a ranar za'a sake ɗaura auren, sai gashi kusan ƙarfe goma sha ɗaya na safe motocin ƴan shema har huɗu sun dira maza da mata, dandanan gidan ya kacame da hayaniyar ƴan bikin da sam babu shiri, hakama dangin Ammi mahaifiyar Umm-Rumana sun cika gidan, dangin gwaggo ma haka na kusa sai ɓullowa sukeyi ta ko ina, to abinka da maganar waya.
Duk wannan abu dake faruwa Ahmad bai saniba, sai da Mudanseer ya tadashi akan ya tashi lokacin salla yayi, mamaki ya kamashi lokacin

Please Login or Register in order to submit comment