Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ko wani abun.
Ahmad ya aminta da hakan ɗari bisa ɗari, dan haka yashiga wani shagon koyan ɗinki anan bayan layinsu kusa da makarantar su samina.
kusancin da suka samune ya kara sake ƙullesu sosai, dan kullum daga gida Ahmad da Samina tare suke tahowa, saiya rakata makaranta zai dawo shago wajen aikinsa.
Sannan da an tasosu daga makaranta komi yake a shago sai ya ajiye ya rakata har gida, wataranma sake biyoshi shagon ta keyi, data shiga gida babu daɗewa zata fito wajensa su koma tare..
Ƴan shagon kan musu dariya, musamman da suke ganin sunyi ƙanana, badai za'ace za'ai musu aure a wannan shekarunba.
Lokacin da Baba ya fahimci wannan shashancin nasu sai yaytai ma Ahmad ɗin faɗa, yakuma ce karya sake ganin Samina ta bishi shago bayan ta dawo makaranta.
Yaji faɗan baba ya dakatar da Samina, amma dukda hakan wataran saita ɗan zagaya a ɓoye taje, musamman ranar weekend da babu karatu.
Shekararsa ɗaya a shagon aka yayesa, zuwa lokacin kuma ya kware a aikinsa sosai dan ya nuna ƙwazo matuƙa.
Ayyah ta fasa ɗan asusunta da takeyi da ribar kayan sana'arta ta siya masa keken ɗinki, yayi murna sosai, hakama yan uwansa sunyi farin ciki, wani ɗakin dake cikin gidan aka fasama kofa ta baya aka saka masa keken ɗinkin, sai yazama shike ɗinkama baba yadika ana kaiwa kasuwa a siyar ɗinkakku, sai kuma masu kawowa da yakemawa, harma na mata yana dan jagulawa dukda bai wani ƙwareba saboda dinkin maza ya koya.
A hankali hannunsa ya fara faɗawa akan dinkin matan ma, kafin kace mi komai ya zama Alhmdllh, harma yana taimakawa gidansu da abinda ALLAH ya hore masa, gefe kuma yanama Samina hidima sosai dasu ta karatu da buƙatun yau da kullum.
Ganin yasamu madogara kuma yana samu Alhmdllh sai yay aniyar komawa karatu.
Kowa ya bashi goyon baya, dan haka ya shiga kokarin neman gurbi a jami'ar b.u.k.
Ya samu shiga jami'ar B.U.K, dayake takardunsa sunyi ƙyau sosai, kuma a lokacin tsadar rayuwa batakai hakaba sosai.
Komawarsa makaranta yasakashi sake zama busy, ko ɗinkima sai yayi da gaske yake samu yaɗanyi, ga kuma aikin yana samu, ganin zai iya korar customers ta wannan hanyar sai ya fara koyama ƙaninsa Mudanseer shima, aiko Alhmdllh Mudanseer ma sai ya maida hankalinsa sosai, sai ya zam yana taimakawa Ahmad ɗin da wasu ayyukan.


Tunda Ahmad ya shiga rayuwar Samina ya fara canjata sai baba Yusha'u kejin daɗi sosai, dan abubuwa da yawa sai Samina tabar biyema mahaifiyarta, dan a hannunta ta tashi, lokacin da mama Gaje ta dawo gidansu Ahmad sai tarbiyyar Samina ya banbanta dana sauran yaran gidan.
Daɗin hakan da Baba Yusha'u ya jine ya sashi zaunar da ƴan uwansa duka a gaban iyayensu su iya ladi, aka kuma kira masa Ahmad da Samina, a gaban kowa ya kuma sake damƙa ma Ahmad amanar kula da Samina, tare da alƙawarin aura masa ita a duk lokacin da suka kai munzalin girma, ya kumace ko bayan babu ransa bai yarda wannan alƙawarin ya tashiba.
Murmushi kawai Ahmad yayi kansa a ƙasa saboda kunya.
Yayinda sauran ƴan uwa da tsoffi su malam Rabi'u wannan abu yay musu daɗi, dankuwa koba komai zumincin ƴaƴansu zai ƙara danƙo da ƙarfi.
Albarka kowa ya sakama abin, tare da addu'ar kaiwa lokacin da rai.

Tun daga wannan lokacinne kuma Samina bata kula kowanne namiji, kowa yasan an mata miji Ahmad, hatta da danginsu na Shema kowa yasan hakan.
Mama Gaje dai batace hakan bai mataba, bakuma taji a ranta zuwa nan gaba idan Samina ta sami wanda yafi Ahmad zata hanata barin Ahmad ɗinba, idan kuma Ahmad yayi arziƙi dama ta dawo hannunta, dan kuwa sai yanda tayi dasu Ayyah akansa.

Tunda Ahmad ya gama secondary ya koya ɗinki yana kama ƴan kuɗaɗe sai nauyin Samina ya kusan koma kansa, shine duk wani bukatunta na makaranta, shine dinkinta da bukatun yau da kullum na ɗiya mace, hatta dasu kayan ciki na mata bai gazaba wajen bata kudin saye.
Wannan hidima da yake da ita sai ta ƙara saka mata girmansa da ƙaunarsa a zuciyarta, bata da hira sai ta Ahmad, duk wani namiji a idonta mace ne, Ahmad ɗintane kawai take kallo da gashin arziƙi, shine kuma kawai nagartaccen namiji a idonta.
Bayan samina ta gama secondary lokacin Ahmad na shekararsa ta ƙarshe a jami'a sai yake bata shawarar komawa karatu.

Lokacin suna zaune a ƙofar gidansune a shagon ɗinkinsa suna hira, dama mafi yawan lokuta anan suke hirar tasu.
Kallonsa tayi da ɗan murmushi ta dukar da kanta ƙasa saboda kunyarsa, cikin muryarta mai cike da yanga tace, “Haba Hubby, kamar ka manta yanda al'amuran suke a gidannan namu, idan nace zan cigaba da karatu yanzu a ina baba zai samu kuɗin ɗaukar nauyina?, kullum ana haɗa na masara da ƙyar a ina za'a samo na karatu kuma?, sannan a ziri'ar mu kaf babu macen data taɓa gama secondary sai nifa, shima da taimakonka, saiko ƙannenmu uku mata da ayanzu suma zasu kammala, iyayenmu ma bazasu amince naje jami'a ba nima nasani?.
Murmushi Ahmad dake kallonta da tausayawa yayi, ya sauke ajiyar zuciya har lokacin idonsa a kanta, a hankali yace, “Samie na ai komai na ALLAH ne, indai kina da ra'ayin karatun baki da matsala, dan ba baba zamu dorama wannan nauyinba, nine zan ɗauki nauyin matata da kaina, kinga insha ALLAHU idan ubangiji ya shige mana gaba sanda zaki kammala ƙila koda karamin aikine na samu, sai maganar aurenmu ko, kodama baki gamaba inhar aka samu ɗan abin rufin asiri sai mu rufama kanmu asiri a wankemu a miƙamu daga ciki kowama ya huta?.
Maganarsa ta ƙarshe ce ta sakata jan hijjab ɗinta ta rufe fuskarta saboda kunya tana ƴar dariya.
Shima dariyar yayi mai sauti yana shafa kansa, yace, “Sorry bazan sake bama matata kunyaba, ammafa randa aka kaimin ita zan cire kunyarnan dukanta insha ALLAHU?.
Babu shiri Samina ta tashi ta gudu zuwa gida, duk kiran da Ahmad yake mata akan ta dawo su karasa magana kasawa tayi, dole ya haƙura ya ƙyaleta.
Daya shiga gidan suka haɗuma da sauri ta kauda fuska taƙi kallonsa, lokacin suna a tsakar gida itada su Rumana suna shafa kurkur a fuska.
Murmushi kawai yay yana ɗauke kansa, dan baya wasa da yaran gidan, idan ka cire Samina babu mai yawan ganin haƙoransa a cikinsu.
Duk sannu sukai masa, ya amsa kamar yanda ya saba, sai da yazo gab da shiga sashensu ne suka haɗa ido da Samina data saci kallonsa.
Ido ɗaya ya kashe mata yana murmushi, tai saurin ɗauke kai tana murguɗa masa baki.
Shigewa yay yana maijin nishaɗi da ƙarin kaunarta a ransa.

Da daddare Samina take sanarma mahaifiyarta yanda sukayi da Ahmad.
Mama Gaje da daɗi ya lulluɓe ta washe baki tana rungume Samina.
“Yo Samina wannan kuwa abin amincewane da guduma, damacefa tazo mana, ai wannan yaro bamusan abinda zamuce masaba a rayuwa, ALLAH dai ya saka masa da alkairi, yakuma kaimu lokacin aurenku, dan kuwa Suwaiba ta haifama Ruƙayya, niko Ruƙayya ta rainar mini?.
Duk da Samina bata fahimci zaurencen mahaifiyarta na ƙarshen maganarba Babu kunya ta amsa da amin, dan tana tsananin son Ahmad da har takai batajin kunyar yin duk wani abun daya shafesa a gaban kowa, iyayensu maza kawai take iya ɗagama ƙafa akan Ahmad.
Hatta kakanninsu Iya ladi da baba Rabi'u bata jin kunyarsu akan Ahmad.

Sai washe gari Ahmad ya samu saƙo a rubuce daga wajen Samina akan amsar cigaba da karatunta.
Yaji daɗin hakan sosai, a ranar kuma ya samu su baba da batun su duka harma da kakanninsu.
Da farko dai tsoho mai ran ƙarfe malam Rabi'u har yace a'a, danshi kam baiga dabara ba a wajen nan sam.
Amma sai Ahmad yayta lallashinsa da nuna masa ra'ayinsa akan matarsa tai karatu mai zurfi, tunda yanzu suna da dama saita fara kafin shi yaɗan samu madogarar da za'ai hidimar aurensu, in yaso ita saita ƙarasa karatun a gidansa.
Fatan alkairi yay musu, tunda ya fahimci Ahmad nason lamarin, bai kamata a katse masa hanzariba matsayinsa na babba namiji a gidan.

Kwana biyu dayin zancen Ahmad ya amshi takardunta ya tafi dasu makaranta.
Tun daga ranar Ahmad yashiga faɗi tashi wajen ganin ya samawa Samina gurbin karatu, kasancewarsa mai ƙokari a makarantar yasashi kusanci da mafi yawan malaman cikinta, ta hanyarsu ya samawa Samina gurbin karatu.
Lokacin da labarin hakan yazo mata tayi farin ciki harma ta rasa ina zata saka kanta dan daɗi.
Hakama iyayensu kowa yaji daɗi, babu kuma wanda ya nuna rashin dacewar hakan, dan a ganinsu Ahmad ɗin yanada ra'ayin matarsa tasamu karatu mai zurfi shiyyasa ya maida Saminar makaranta.
Sauran ƴan uwantama ƴammatan gidan sun tayata murna da wannan cigaba, koba komai suma zasu saka ran cigaban tunda aka fara daga kanta.

Nauyin karatun Samina daya dawo kan Ahmad sai ya sa abubuwa suka sake masa yawa, dan kuɗin shigarsa basu kai nauyin ɗukar hidimar da yakeyiba, gashi dai-dai da kuɗin mota wannan sai Samina tazo wajensa take amsa. Ga nauyin karatun Mudanseer ma shine yake bada mafi yawan ƙarfinsa, dukda mahaifansu na taimakawa tanan ɓan garen.
Kuma a gefen hidimar gidama baya zuba ido baneba, yanayin ƙoƙarinsa wajen taimakon mahaifinsu.
Wannan abubuwan da sukaimasa yawane ya sakashi fara tunanin faɗaɗa neman kuɗin nasa, akuyarsa da ya saya Ayyah na kula da ita yace zai saida ya zuba kayan ɗinki na saidawa, saboda akuyar ta haifi yara biyu sai Ayyah ta amince masa aka saida, da kuɗin akuyar yaɗan sayo kayan su zare da wasu ƙananun abubuwa irinsu allura, almakashi, zips da sauransu ya zuba a shagon, teloli dake cikin gida da masuma shagunan dake kusa sai sukanzo sukan saya anan, kamar wasa sai ALLAH ya sakama abin albarka ake ciniki, idan duk suna makaranta sukan ɗan ɗebo kayan sayarwar a ajiye cikin gida, duk wanda yazo saya sai yayi sallama a bashi.
Ahmad bai tsaya ananba kawai, har komawa yay idan ya taso makaranta ya sari lemuka ya ɗora a kansa yana zuwa bakin titi saboda motoci masu wucewa, wani lokacin kuma biredi, ko kayan fruits haka.

Da waɗannan sana'oi da wahalhalu Ahmad ya cigaba da kula da karatunsu shi da Mudanseer da samina, sauran ƙannensa ma yakan basu gudunmawa, hakama yayunsa dake gidan aure sukan taimaka masu da abinda ALLAH ya hore musu.
Ahmad ya kammala degree ɗinsa ya samu yay bautar ƙasa, daga nan kumane ya dawo zaman gida sosai, dan babu dai maganar aiki.
Yaci gaba da sana'oinsa na ɗinki da saida kayan ɗinki, zuwa yanzu kuma hannunsa ya faɗa sosai ya ƙware, ɗinkuna yake na zamani masu birgewa, duk wasu samari ƴan kwalisa da ƴammata zaka samu ɗinkinsu ya fitone daga shagon Ahmad, wanda aka fi sani da Ahmad sharukhan, idan ɗinki yaɗan kwanta saiya koma sana'arsa ta sai da lemo da ruwa, kokuma kayan fruits.
Yanzu dai haka takai Ahmad yana hayar keke napep ne, yay ɗinkinsa da yamma ko dare, da safe zuwa la'asar yana neman taro da kwabo da adaidaitarsa a gari.

Matsala ta farko data fara shigowa tsakanin Samina da Ahmad shine, bayan barinsa makaranta Samina tayi sabbin ƙawaye, sanda yana nan koda yaushe suna tare, sai dai lokacin karatune zaka samesu ba tareba, duk wanda ma yake mu'amula dasu yasan suɗin masoyan junane.
Samina tun tana secondary takanyi karatun novels ɗin hausa, rayuwar jin daɗi da dukiya da akeyi a novels na ƙayatar da ita, har wani lokacinma takanyi addu'ar ALLAH ya buɗama Ahmad ɗinta shima yay arziƙi ya gina musu ƙaton gida, ya narka musu kayan alatu da jin daɗi, su ringa hawa motoci na alfarma ita dashi.
A wancan lokacin burin nata bai taɓa kaita ta nemi canjin Ahmad da masu irin suffar jaruman littafiba, shiɗin dai takema addu'ar ya samu su mora.
Takai koda Samina ta karanta littafi sam bata wani damuwa da ɗaukar darussan rayuwa ko ilimin da littafin yazo dashi, ita kawai soyayya da kayan ƙawane ke ɗaukar hankalinta da ƙara faɗaɗa burinta, tama kai inhar buk bana masu ƙazamin arziƙi bane ƴan gayu batason karantawa, data fara karatun taji ana faɗin jarumin littafi nashan wahalar neman nakansa sai buk ya fitar mata akai ta ajiyeshi, tafi son taji ana suffanta ƙyawun jaruman littafi tare da dukiyar da tunani bazai iya musaltawa ba, to takanji kamar tai tsalle ta ganta a buk ɗin saboda shauƙi.
Haɗuwarta dasu Nafy ne ya fara nuna mata hanyar samun cikar wannan burin nata, tun tanajin haushin kushe mata Ahmad da sukeyi akan talaucinsa har zuciyarta ta fara rawa da aminta da maganarsu.
Dan kuwa dai sunyi nasarar fara tsundumata shafe-shafen mayukan bilicin, dukda kuwa tanada haskenta gwargwadon iko, sannan Samina ƙyaƙyƙyawace babu laifi.
Ƙananun burikan Samina sun fara faɗaɗa, dan yanzu kowane biki saita san yanda ta ƙwalkwali Ahmad kuɗin ankonsa. Ada bata kula kowane saurayi sai Ahmad, amma zuwa yanzu kam ai samari babu iyaka take kulawa, dataga kazo da ƴar kalar manyan mutane babu wani jan aji take miƙa kanta.
Tun Ahmad na zuba mata idanu akan ƙananun sabbin ɗabi'unta harya kasa haƙuri ya tuhumeta akan bilicin data fara, ya tabbatar masa shi bama ya ra'ayin farar mace, yafisonta da kalar fatarta choco color, alokaci haƙuri tabasa, ta shirya masa ƙaryar ba bilicin baneba, kayan gyaran jikine irin namu na gida take amfani dashi.
Cayay kosu ɗinne tabar amfani dasu sai sunyi aure ya yarda da ingancinsu.
Ta amsa masa da to, amma tana bama su Nafy labari sai suka zugata akan ai ba aurenta yakeba, taci gaba da abinta, gashinan harta fara zama big girl shine zata wani biye masa, inharfa bazata cire tsoron Ahmad a rantaba to bazata taɓa wayewaba ta zama cikakkiyar ƴar jami'a balle shima ta maidoshi kan hanya su shinfiɗa ƙyaƙyƙyawan rayuwa irinta jaruman littafi🤦🏻‍♀.............✍?








*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻*_Typing📲_*




*ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*

07067124863

*Ko kuma*

09032345899


*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽

https://youtu.be/Zyl7_eSgXuo



*(3)*

...........Da waɗannan shawarwarin dukkan ginin Ahmad ya fara rushewa ga tarbiyyar Samina, ta fara biyema ruɗin su Nafy, idonta ya fara buɗewa da rayuwa ta manyan yara masu aji, duk wani dandalin wayewa suna wajen matsayin manyan baƙi masu lokaci, wannan damar samarin jami'a ƴan ƙwalisa da lectures suka samu wajen shiga jikin su Samina, sai ga ƴaƴan manya masu abin magana a aljihu sun fara kutso kai cikin rayuwarsu.
Tunanin Samina ya fara bata cewar lallai Ahmad bazai zama dai-dai da burinta na rayuwar Jaruman novels ba, saboda har lokacin dai ana nan jiya iyau, buga-bugar sana'a ce dai kawai a samu na yau na gobe sai an fita nemansa, suturar kirki wannan ta shiga taro Ahmad bashi da ita, gaba ɗaya kayan nasa duk yadin (Tashi sama sallau) ne, idan ƙananun kaya ka gansa dasu ma dai na gwanjone ba sabbi ba, ƙyawune kawai Ahmad ɗin zai iya mata burga dashi.
A samarinta kuma na yanzuma akwai waɗanda zasu iya linkashi ƙyawun, ga kuɗi na gaske suna mata wasa dasu, wanda suka fara lulluɓe zuciyarta dana mahaifiyarta wajen mance alkairin Ahmad a garesu.
Duk tsiyar da Samina ke aikatawa mama gaje ta sani sarai, kwaɗayin abinda Samina ke kawo musu na ciye-ciye ne ya lulluɓe idanunta ruf.
Idan cikin samarin Samina wani yace zaizo bata kawoshi gidansu, sai dai ta kaisa can gidan kakanninta da suka haifi mama gaje.
Hakan yasa Ahmad baisan mi Samina ke aikatawa ba, dan bai taɓa kawoma ransa zata kula wani saurayi bayan shiba, musamman da yasan akwai alƙawarin aure a kansu da ƙaunar juna mai ƙarfin gaske.


_________________________

A yanzu haka Saminar na gidan kakarsu, taima Ahmad ƙarya Inna mari bata da lafiya dan kawai tasamu taje wani bikin ƙawarta da za'ayi.
Sai dai tsoron kar wani yakai masa gulma yasata kiransa a waya ta sanar masa cewar zataje wajen kamun bikin ƙawarta.
Bai musa mataba ya barta, amma yace ta jirasa yazo da mashin ɗin Sufyan zai kaita.
Hakan ba ƙaramin haushi ya bataba, amma yaya ta iya dashi.

Shiri take da sauri-sauri gudun kar Ahmad yazo ya sameta a gidan...... Dan tafison su tafi tare dasu Nafy, kiran da taji Iya kishiyar kakarta Inna mari na ƙwala mata daga waje yasa gabanta faɗuwa, tasan dai yanzu haka Ahmad ne yazo.

“Samina!, Samina!!, Wai Samina baƙya jinane kokuwa lalatar takice ta motsa ne??.
Ta sake jiyo muryar iya daga tsakar gida.
Cikin cuno baki ta fito daga ɗakin dake can cikin wani lungu tana gyara ɗaurin ɗankwalinta ture kaga tsiya tana kumbura fuska.
“Kai Iya, irin wannan kira haka saikace na mafarauta, ɗan kwalifa nake ɗaurawa saboda su Nafy zasuzo yanzu mu wuce, mi kuma zan miki??.
Baki iya dake tsaye bakin murhu tana ƙokarin hura wuta ta riƙe, “Samina anya wannan rayuwar ta dace dake kuwa? Baƙya ganin kinason wuce gona da iri? Yanzu nan kodan yaron nan Ahmad ai ƙyaɗan sassauta wani abun, wlhy kibar biyema lalatattun yarancan su Nafisa karsu kaiki su baro?.
Baki Samina ta ɗan taɓe tana gyara zaman gyalen kafaɗarta, “Iya nifa wlhy banajin daɗin irin maganganun nan naki, ni mi nakeyi mara ƙyau a rayuwata dan ALLAH??.
“Ba nace kina wani abu mara ƙyau bane ba Samina, Inason dai ki tsaya matsayinki kodan Yaronnan da ya gama wahalar duniya a kanki, karsuje su hure miki kunne akan ɗabi'u mara amfani?.
“A'a Atine, anface ka fadi alkairi ko kai shiru, dan Ahmadu yaymata wahala sai akace bazata mori ƙuruciyarta ba? Naga ba aure aka ɗaura musu ba alƙawarin auren ne kawai ko??.
Wata dattijuwar tsohuwa mace dake fitowa daga bandaki ta faɗa tana ƙokarin ajiye butar hannunta.
Su duka kallonta sukayi.
Iya tace, “Amma dai Mari ai kowa yasan dama ALLAH shine yake yanda yaso ga mutum, amma kinsan ta yaro ƙyau take bata ƙarko, tunda har da alƙawarin auren, wataranama ɗaurawa za'ayi kamar yanda muke fata
“Uhm Atine, mubar wannan batunma dan ALLAH, dan yanzu ba lokacin yinsa bane, ni dai abinda nasani kawai shine bazamuyima yarinya auren doleba, idan tace Ahmad takeso zamu bata, idanko ta kawo waninsa shima zamu bata?.
“Hakane Mari?.
Iya ta faɗa tana ɗauke kanta daga garesu ta koma ƙoƙarin hura wutar data fara.
Daga Samina har inna Mari kakarta harar Iya dake duke sukayi.
Samina ta maida kallonta ga kakar tata tana murmushi, “inna mari bara naje karsu Nafy suyita jirana, kinsan za'a fara kamun ƙarfe uku na yammane?.
“To Samina ALLAH ya tsare, a dai dunga kula saboda ƴan saka ido, kana rayuwarka baka damu da kowaba saikiga anata ƙokarin taɗo ƙafarka da harshe, bayan ko MANZON ALLAH ma yace mu kiyayi harsunanmu?.
“Humm Inna ai mutanen duniya ba'a iya musu, sunfi son kullum su ganka jiya iyau, kuma idan arziƙin kayi sune zasu fara zakalkalewar kai nasune?.
“Maganarki na kan hanya wlhy ƴar albarka, kedai jeki karki makara?.
“Okey my sweet kakus bye?.
“Duk da ban iya turancinba Samina, nima bye?.
Ficewa Samina tayi tana dariyar zancen kakar tata.
Itama inna mari ta shige ɗakinta tana ƙyalkyata dariyar sake ƙular da kishiyarta iya Atine.
Murmushi kawai Iya tayi, tasan duk ita akema habaicin, ta girgiza kanta tana nemawa abokiyar zaman nata da jikarta shiriyar ALLAH, tare da fatan ganewa kafin guri ya ƙure musu.

Kamar an saita Samina na fitowa daga ƙozajjen soron gidan kakanninta da Ahmad ta fara cin karo zaune bisa ɗan dandamalin dakalin dake ƙofar gidan maƙwafcinsu.
Ta tsaya tsam tana ƙarema kwalliyarsa kallo, tabbas Ahmad ƙyaƙykyawane, shiyyasa duk rashin tsadar kaya sukan zauna masa a ƙyaƙyƙyawar surarsa suyi ɗas.
Ba wani kayane mai tsada a jikinsaba, hularsa ƙube da ita kaɗai ta iya saninsa dashi ta ƙarshen gayunsa ya saka, ta zauna ɗas akansa, inda daga bayan ƙeyarsa kwantacciyar sumarsa ta jinin fulanin rumawan asalin katsinawa ta bayyana, sai yadi mai ƙarancin kuɗi mai kama dana ƴan makaranta kalar ruwan shanshan bale, takalmansa ƴan saƙe suma masu ƙarancin kuɗi, sai agogon fatar da itace ta saya masashi naira ɗari huɗu ɗaure a hannunsa da zoben azurfa a yatsansa, kayan sun ɗauki guga, dan haka suka kwanta luff tare da ɓoyewar tsufan da suka fara a idon mai kallonsa, ƙamshin turarensa yake mai ƙarancin kuɗi, amma akwai daɗi ga hancin mai shaƙa.
Ganinta ya sakashi miƙewa yana ƙawata nutsatstsiyar fuskarsa da murmushi na musamman.
“Barka da fitowa tauraruwar mata ma'abociyar haske da walwali?.
Samina ta kallesa a wani

Please Login or Register in order to submit comment