Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

rigar jikinsa dan sam baison kwanciya da kaya takura masa sukeyi.
Da ga shi sai boxer ya kwanta, bayan ya tura Mudanseer gefe da ƙyar saboda shima dai ƙatonne masha ALLAH.
Bargonsa yasa ya rufe jikinsa ruf har saman kai, dan komai zafi saiya lulluɓa yake iya kwanciya, sannan komai sanyi saiya cire kaya yake iya barci.


★★★★★★★★

Iya na zaune tsakar gida ta zabga uban tagumi tana jiran taga ta inane Samina zata ɓullo.
Inna mari kuwa babu ruwanta, tuni ta shige ɗaki tai kwanciyarta tana shaƙar barci.

Sai wajen sha biyu da kwata sabon saurayin Samina yay haramar tafiya, ya kalleta ido cikin ido yana wani narkesu a cikin nata.
Hakanne yasaka tsigar jikinta tashi, tai saurin janyewa ƙirjinta na wani irin bugawa, tabbas batajin magana, amma har yanzu rawar kanta bai taɓa sawa ta yarda wani namiji ya taɓa aikata mata wani abu mara ƙyauba koda runguma kuwa, duk da kuwa tana jin sha'awa sosai irin wadda kowacce mace mai lafiya kanji a lokacin da takai shekarunta.
“Babie zan tafi, amma babu abinda zan samu?. Yay maganar cikin raɗa kuma a saitin kunnenta.
Matse jikinta tayi kaɗan, muryarta naɗan rawa tace, “Yallaɓai kamar mi kenan??.
Wani mugun murmushi ya saki yana sake matso da kansa jikin wuyanta, sai da ya busa mata iska a wuyan kafin ya kai hanci yana shinshinar ƙamshin turarenta, cikin raɗa-raɗa ya sake faɗin, “Komai ma na samu inaso babie?.
Yanda gashin jikinta ke miƙewane yasata ɓalle murfin motar ta fice ba tare data shiryama hakanba, ya bita kallo da idanunsa da suka fara rinewa yana murmushi, “Babie akwai wayo, shikenan na gode ga wannan kiyi amfani dashi wajen kwalliyar gobe?.
Kamar bazata amsaba sai kuma ta ƙyalla ido taga yawan kuɗin, wani irin taji a ranta, tai azamar miƙa masa hannu tana faɗin, “Nagode sosai, amma kamar sunyi yawa ka rage?.
Wata siririyar dariya yayi mai sauti yana dukan sitiyari kaɗan, ya maido kallonsa gareta har sannan da sauran dariyar a fuskarsa, “Babie nawanema waɗanan kuɗin da har kike tunanin sunmiki yawa? Ai ƙyauta bata yawa, yanzunma dan babu kuɗine a jikina shiyyasa, kinga shiga gida sai da safe?.
Kanta kawai ta iya ɗaga masa, ta wuce sim-sim kamar wata munafuka.
Sai da yaga ta shige sannan ya tada motar yabar wajen yana dariya abinsa.

Da sauri Iya ta miƙe tana kallon Samina data shigo kamar a tsorace, tai kanta tana faɗin, “Samina kinada hankali kuwa? Tafiya biki shine har sulisin dare??.
Ƙaramar ajiyar zuciya Samina tayi, taɗan marairaice yanda iya zataji tausayinta,
“Iya wlhy mota muka rasa tun ɗazun, da ƙyarma muka samu wannan ta kawo mu?.
iya batace da ita komaiba, itama sai ta raɓa ta gefenta ta wuce zuwa ɗakin iyar ganin Inna Mari harta rufe ɗakinta ma ita.
Dan gidan nasu ɗaki biyune kacal sai runfar girki, ɗakin inna mari sai ɗakin iya Atine.
Iya dai bata yarda da maganar Samina ba, amma sanin bata da wani ƙarfin iko a gidan sai batace komaiba, ta ɗauki butarta ta zagaya ban ɗaki, koda ta fito ta shiga ɗakinta sai taga Samina na ƙoƙarin cusa abu cikin tsummo karanta na wanki data ƙule da safe zata aikama ƴarta dake aure ta wanke mata, saboda ita bata iyawa.
Nanma kallo ɗaya tai mata ta ɗauke kanta, ta haye gadon ƙarfenta rakuminka ɗaka tai kwanciyarta.
Samina kaɗai taita shigi da fici a tsakar gidan, sai da ta kammala shirin barcinta kafin ta kwanta kusa da iya a kan gado, babu abinda ke mata yawo arai sai haɗuwar sabon saurayinta.
Ya haɗu iyakar haɗuwar da zuciyarta ke tabbatar matama yafi mijin novels, da alama kuma sunada kuɗi kamar yanda kullum take mafarkinta akan mijin aurenta, ga ƙyaƙyƙyawar nasaba da itama take masa hasashe. Shin dama marubuta da gaske suke akwai mazan novels a zahiri kenan? A tunaninta koda akwaisu bazasu so ƴaƴan talakawa ba kamar yanda na littafi keyin soyayya da ƴanyan talakawa irinta, sai gashi a dare ɗaya tayi gamo da Ma'aruff. Ta lumshe ido a hankali, wani irin daɗi na kamata, yau gata zata mallaki mijin novel.....
“Yah Ahmad fa??
Wata zuciya ta ambata mata acan ƙasan ranta, da ƙarfi ta rintse ido tana sama da ƙasa da numfashinta, dan wani irin faduwar gaba taji a ranta, tabbas tanason Ahmad, tanada tabbacin kuma yafi dukkan maza matsayi a ranta, sai dai bashida kwalitis ɗin da take buƙata ga namiji, tabbas tanason namiji ƙyaƙyƙyawa, Ahmad ƙyaƙyƙyawa ne, tanason namiji mai suffa mazan gaske, Ahmad yanadashi, tanason namiji ɗan gayu, Ahmad ba ɗan gayu bane, tanason namiji mai dukiya, Ahmad baya da dukiya, tanason namiji mai nasabar sanannan gida, iyayen Ahmad talakawane babu wanda ya sansu sai danginsu da iya jama'ar layinsu, tana so!, Tana so, tana so da yawa, sai dai Ahmad baida su, bai dasu da yawa.
Yaya zatayi kenan tunda a yanzu tasamu mai dukkan nagartar da ita take buƙata? Zatabar Ahmad ɗinne ta samu *CIKAR BURINTA?* kokuwa zata bar cikar burinta ta anshi *BUƘATAR ZUCIYARTA?......*
“K Samina wai mike damunkine haka??
Firgigit ta dawo hankalinta, ta juya kwanciyarta tana faɗin, “Babu komaifa Iya, kawai ina lissafine na jarabawar dake tunkaromu kwanan nan, saboda Yah Ahmad yace na dage da karatu?.
“To ai bakiji maganar tashiba, tunda kinyi watsi da ita kin koma bin gidajen bikin da ba tsarankiba, Samina karki ruɗar da kanki, karki bari ƙarya ta lulluɓe ganinki, karki yarda da wasiwasin zuciya, kar dauɗar duniya ta toshe jinki da tunaninki, inba hakaba wlhy zakiyi *GUDU DA WAIWAYE...* ƙarshe kuma zai kawo miki *mugun zato ne* ga duk masu ƙoƙarin ɗora tunaninki akan *keken ɓera*?.
Shirun da Samina taji Iya tayine ya sakata gane ta gama, maganganun Iya sunyi tasiri sosai a ranta, sai dai sheɗaniyar zuciyarta na mata kutse cikin tunanin dake nuni da (A'a), baki ta ciza da ƙarfi kamar zata huda laɓɓanta, gaskiya tana buƙatar dogon tunani akan wannan al'amarin, idanma son samune harda shawara.
Da wannan tunanin ta ingije abun a ranta ta samu barci ya saceta mai cike da mafarkin Ma'aruff.😳🤫


*Washe gari*

Asubar fari Ahmad ya farka tamkar yanda ya saba, da addu'ar tashi barci ya buɗe idanu, ya miƙe zaune yana janye bargonsa tare da yin miƙa mai ɗauke da hamma, sai da yaɗanyi minti biyu a zaunen kafin ya miƙe da ƙyar, fitowa yay daga ɗakin nasu zuwa soro daga shi sai boxer ɗin, ɗan jujjuya jikinsa yay yanda ko ina zai motsa kusan na mintuna biyar, kafin ya koma ɗakin ya ɗauki jallabiyarsa ya saka ya ɗau buta zuwa cikin gida.
Babu wanda ya fito harya shiga bayi ya fito, ya zauna saman ɗan dutsin dake tsakar gidan kusa da kwatanniyar ruwan agwaginsa ya fara alwala.
Ayyah ce ta buɗe ɗakinta ta fito, ya kalleta yana kuskure baki, isowarta kusa dashi yay daidai da zubda ruwan bakinsa,
“Ayyah na kin fito??
Yay maganar cikin yanayin muryar wanda ya tashi a barci, yana kai ruwa a hancinsa zai shaƙa.
“Eh ɗan albarka, ka tashi lafiya dai ko??.
Sai da ya face ruwan daya shaƙa ya amsa da “Alhmdllh?.
Bayi ta shige ba tare data sake cewa komaiba, shima ya cigaba da alwalarsa.
Yana kammalawa zai miƙe Ayyah ta fito daga bayi, sai ga Gwaggo ma ta fito daga lungun ɗakin baba.
Itama barka da fitowa yay mata yana nufar hanyar soro.
Kamar yanda ta saba haka ta amsa cikin halin ko in kula.

Ahmad ya yarfama Mudanseer dake jan nashari ruwa a fuska, kamar kullum ya farka a fusace yana ƙun ƙunin faɗin,
“Kai yah Ahmad, kai yah Ahmad, ni ALLAH ka dainamin abunnan, sai kace wani ɗan riƙo kullum kaita tadani da ruwa??.
“Kai dai ka sani uban ƴan mita, dilla tashi kai alwala mu wuce masjid, saura ka tsaya shegen kashinka na ƙa'ida harmu makara kamar jiya?.
Cikin tuttura baki Mudanseer ya ɗauki buta ya fita yana layin barci kamar zai faɗi.
Ahmad ya girgiza kansa kawai, sallar raka'atainul fijir ya tada kafin Mudan yagama kalularsa su wuce...........✍?


_KADA KU MANTA MARUBUTAN DAI SUNE WANDA SU KA RUBUTO MUKU ZAFAFAN LITTATTAFAN NA BAYA, A YANZU MA SUN SAKE YUNKUROWA DA WASU SABBIN MASU SABON SALO_

_*KAUNARMU:* 💋❤️NA MAMUH GEE_

_*DAURIN GORO:* 💋❤️NA HAFSAT RANO_

_*ALKAWARIN ALLAH::* 💋❤️SAFIYYA HUGUMA_

_*GUDU DA WAIWAYE:* 💋❤️NA BILLYN ABDUL_

_*IGIYAR ZATO:* ❤️💋NA MISS XOXO_

_CANCADI DOMIN DUKKANIN LITTAFAN NAN ZAKA/KI IYA MALLAKAR SU A NAIRA DARI BIYAR_

_GUDA DAYA DARI BIYU_

_GUDA BIYU DARI UKU_

_GUDA UKU DARI HUDU_

_GUDA HUDU DARI HUDU DA HAMSIN_


_DOMIN MALLAKAR SU SAI A TUNTUBE MU TA HANYAR_

*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*


2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_

saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*

*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇

*09032345899*


_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_


Mucigaba da shakatawa da wannan dan yanzune aka fara kafta WASAN😁👉🏻📻




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻*ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*

07067124863

*Ko kuma*

09032345899


*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽

https://youtu.be/Zyl7_eSgXuo



*(5)*

............A ɓangaren Samina kuwa sai da Iya tayi da gaske ta tashi sallar asuba, rashin kwanciyar wuri da batayiba yaja mata nauyin jiki, tana gama sallah ta koma ta kwanta a gado.
Iya kam fita tayi kamar yanda ta saba, duk da tsufanta haka tai gohon haɗa wutar kokon saidawa da takeyi da safe, saida ta ɗora holoƙon tukunyar da takeyi ta zuba ruwa sannan ta ɗau tsintsiya ta fara share tsakar gidan, kafin gari ya gama haske ko ina yayi ƙal har soro, tasa ruwa ta wanke bayinsu, dukda kasancewarta tsohuwa ta tsani ƙazanta.
Sai da taga gidan ya mata yanda takeso sannan ta haɗa wanke-wanke ta fara, a haka tukunyar kokonta ya tafasa, ajiye wanke-wanken tayi taje ta sheƙa kokon a botikin fenti guda uku kamar yanda ta saba, ta kimtsa gindin murhun tana maida dumamen tuwonsu, saita koma wajen wanke-wanken ta ƙarasa da sauri.
Waken ƙosai data ajiye ta ɗakko a ɗaki, har lokacin Samina na baje a gado tana barci, hakama Inna Mari na ɗaki duk kiciniyar aikin da Iya keyi tana jiyo ta amma tai zamanta, Sa'idu autan inna mari, ƙanin mama gaje kuwa yana ɗakin soro kwance shima ko sallar asuba bana tunanin yamaje yayi.
Iya ta surfa wakenta ta gyarashi tsaf cikin hanzarin da ALLAH ya bata, ta ɗauka a kanta ta fita markaɗe makwaftansu.
Sammakonta ya saka itace farko kullum, yauma dai ita ta fara buga gidan Rabi mai markaɗe. Mijinta yazo ya buɗe, kafin ya koma ciki ya tado rabin.
Kamar jama'a jira suke, sai gasu sunata shigowa markaɗe, sai da aka fara markaɗa na iya ta dakko ta dawo gida abinta.

Koda ta shigo babu wanda ya fito, bata damuba ta sauke tukunyar tuwon ta sata gefe inda zafin wuta zai dinga kai mata ta aza kasko a murhun tare da zuba man gyada ta yanka albasa a ciki.
Zaman buga ƙullun tayi, wanda yay jajir saboda kayan miyar da yaji, gishiri kawai ta saka masa tai masa bugu mai ƙyau, zuwa lokacin manta yayi zafi yanda take buƙata.
Duk abinda zata buƙata ta kawoshi kusa da ita sannan ta zauna suya.
A hankali mutane suka fara sallamar sayen koko da ƙosai, dan Iya gwanace akan tsafta da iya sarrafa ƙosai harma da kokon, hakan yasa kullum customers basa yanke mata, hardaga layukan bayansu da gabansu duk zuwa ake sayen kayan sana'arta, shiyyasa kafin wani dogon lokaci zakiga komai ya ƙare.

Sai da hayaniyar ƴan sayen koko da ƙosai ta cika gidan sannan inna Mari ta fito daga ɗakinta, babu kunya taje ta ɗeba koko da ƙosan ta koma gefe tanaci tana kallon yanda masu saye suka yanyane iya har tana neman ruɗewa.
Maimakon taje ta taimaka mata saita kauda ido tana taɓe baki.

A haka Sa'idu ya shigo gidan, buta ya ɗauka ya shiga banɗaki, zuwa can sai gashi ya fito, shima dai koko yaje ya ɗiba da ƙosai ba tare da ya gaida kowa a cikinsu ba ya koma ɗakinsa.
Har dai akaci cinikin nan aka tsire Samina tana barcinta.
Bata fitoba kuma sai da iya na wanke kwanikan data ɓata.
Bata ko kalletaba ta fice cikin hijjab, kusan awa guda sai gata ta dawo ɗauke da leda baƙa.
Iya na zaune tanacin tuwo Samina ta zari kwano da kofi a wanke-wanken da Iya tayi ta shige ɗaki.
Ajiyar zuciya kawai Iya tayi tana janye idanunta ta maida kan tuwonta dake mata dadi fiye da kilishin dayay sati biyu a tsume😢😞😋.



________________________________


Sai da gari ya ɗanyi haske Ahmad da Mudan suka shigo cikin gidan, dan tuni baba shi ya dawo tare da sauran ƴan uwansa, tsoho baba Rabi'u kuwa baya iya fita saboda ƙafa.
Ɗakin baban suka shiga, suka gaidashi cikin girmamawa, kamar yanda ya saba ya jaddada musu nasihar jin tsoron ALLAH a duk halin da suka tsinci kansu, tare da riƙe gaskiya a zamantakewarsu da kowa a rayuwa, su nemi gumin halak komai wahalarsa da ƙankantarsa, su saka a ransu albarkarsa na wajen UBANGIJI ba wayonsu ba, duk sauƙin Haramun su gujeta dan ita halaka ce, karsu zama masu biyayya wa jagorancin miyagun abokai akan harkokin banza, ko bayan babu ransa su riƙe zumincin juna danshi tsanine mai kai bawa zuwa aljanna, idan mutuwa ta riskesa a wannan yinin karsuyi masa kuka, karkuma ai masa zaman makoki, ya yafema kowa, su roƙa masa gafara wajen kowa, baya bin kowa bashi ba'a binsa.
Wannan itace nasihar da yake musu akowacce safiya, wadda tun suna ƙanana sunma gama haddaceta a ƙwalwarsu saboda yawan bita da suke samu daga mahaifinsu abin alfaharinsu.
Jiki a sanyaye suka miƙe suka fito daga ɗakin, ɗakin Ayyah suka shiga, tana zaune saman abin salla tana jan cazbaha.
Ƙasa suka tsugunna itama suka gaidata cikin girmamawa, fuskarta ɗauke da murmushi ta amsa musu, kafin ta turo musu kwanon dabino tana faɗan, “Mudan gashi, nadai san Ɗan albarka yau azumi yakeyi?.
Murmushi Ahmad yay yana ɗaga mata kansa, Mudan yaja kwano ya ciri dabino bakwai yana ƙaramar dariya da tsokanar Ahmad, “To mudai bamayi Ayyah, kuma ci mukayi abunmu, amma tunda ɗaki ɗaya muke kwana da Yah Ahmad nasan za'a rinƙa dibamin ladan ganin ido a azuminsa?.
Dariya Ayyah takeyi, Ahmad kam dake miƙewa ya shureshi da ƙafa yana hararsa, akwatin ƙarfe na lefen auren Ayyah🤣 da kayansa ke ciki ya nufa, “Ayyah kibar biyema wannan shashashan wlhy, dan mudan bazai taɓa hankaliba inaga?.
“Tab lallaima Yah Ahmad ɗinnan, duk hankalinan da nake dashi baiyi makaba ashe? To zakasha mamaki kuwa, Ayyah samun albarka kinji naje na ɗebo ruwa yau inada wajen zuwa da safen nan?.
Ayyah dake haɗiye dariyar da take musu tace, “ALLAH yay muku albarka Mudanseer, ya shirya manaku ku zama jaruman musulinci da MANZON rahama zai alfahari da haihuwarku, ALLAH ya baku rufin asiri mai albarka da amfani ya tsareku da dukkan wani sharri da abun ƙi?.
“Amin Ayyahnmu, maman ɗan albarkanta?.
Mudan ya faɗa yana miƙewa, Ahmad dai da yasan neman magana mudan keyi sai bai ko kalleshi ba harya fice.

Ayyah ta juyo tana kallonsa da murmushi, “Ɗan albarka mi zakayi da safen nan??.
Kansa ya langaɓe cikin ƴar shagwaɓa yace, “Babu komai Ayyah na, akwai abinda zan mikine??.
“Eh to ba wani dai mai yawa bane, sonake kaje ka sanarma kawunku lurwanu matsalar da ake ciki game da ƴar uwarku, dan babanku yariga ya rantse babu ruwansa, ya kuma hana a sanarma ƴan uwansa, nima dai banason suma sani ɗin, saboda gutsiri tsomar iyayenku mata na gidannan. tun jiya Gwaggo keson fita tasamu ta sanarma Kawun naku Babanku ya hanata fita, saboda yasan ina zataje......?
Kayan hannunsa da yakeson ya ɗan goge ya ajiye saman akwatin bayan ya rufe, ya gyara zamansa sosai a ƙasa cikin sake tsuke fuska yace, “Ayyah, wannan karon banason kowa ya shiga wannan maganar, har kawunma ki barsa, ni da kaina zzan kawo ƙarshen matsalar Yaya Maryam, dan wanan mijin nata *KAREN BANA* ne, *ZOMON BANA* yake buƙatar yayi maganinsa, ku zuba mana idanu kawai......?
Shiru kawai tai tana kallonsa dajin ƙarin ƙaunarsa, muryarta naɗan rawa tace, “A'a ɗan albarka, karka jefa kanka cikin matsala, wannan maganar babbace, banason zuciya ta lulluɓe ganinka harka aikata abinda zaisa muyi nadama mu duka, kasan dai halin babanku?.
Murmushin takaici Ahmad ya ɗanyi, ya matso kusa da Ayyah sosai, “Karki damu Ayyah, insha ALLAHU ba mummunan abu zan aikataba, ta ƙyaƙyƙyawan hanya zan gyara komai da izinin UBANGIJI?.
“To shikenan ɗan albarka, ALLAH ya albarkaci rayuwarka, ya tsare gabanka da bayanka, ALLAH ya cika maka burukanka na alkairi ya kuma share hawayenka a duk lokacin da zasu kwaranyo koda babu ranmune?.
Cikin sukar zuciya ya amsa da amin.
Bai sake cewa Uffanba ya ɗauki kayansa a hannu ya fita.
Ɗakin Gwaggo ya shiga, ciki-ciki ta amsa masa sallamarsa, bai damuwa ya durƙusa har ƙasa ya gaidata.
Ta amsa masa tamkar yanda ta saba cikin nuna rashin kulawa.
Shiru yay zaune a wajen, shi bai tashiba bai kuma motsaba, gashi ba hira sukeyiba, tama maida hankalinta wajen bama zu Fa'iza umarnin ruwan kamu da zata ɗora.
A haka Abubakar ya shigo ya samesu, shima dai masha ALLAH ya fara zama saurayi, Gwaggo ya gaida kafin ya gaida Ahmad.
Amsawa Ahmad yay yana miƙa masa kayan hannunsa, “Abu amshi kayanan ka goge mani, zanje wani waje na dawo, ka tabbatar sun gogu daƙyau, karkamin iya shegen da kaima Mudan shekaran jiya a kaya kajini ko??.
“To Yah Ahmad, amma sai dai dutsin yana wajen Yaya Salisu, dan jiya daya amsa ina shago bai dawo dashiba, gashi babu gawayima ya ƙare?.
“Kaje ka amso dutsin, bara naga inada wata naira ɗari anan, saika sayo gawayi na hamsin, hamsin ɗin kayi kudin tara da shi?. Yana maganarne yana laluben aljihunsa.
Gwaggo da tun ɗazun tana saurarenau bata tankaba ta katseshi da faɗin, “Kabar kuɗinka, kai Abu kaje ga gawayi can lungun ɗakin Yaya na kashe jiya kayi masa gugar dashi, dama saboda ku aka fara tarashi kwa rage cacar kuɗin sayen tunda iccen yana bada rushi sosai?.
Murmushi Ahmad yayi har haƙoransa suka bayyana, a hankali yace, “Mun gode Gwaggonmu?.
Shiru tayi bata amsa masaba, shima sai ya miƙe sim-sim cike da kunya yay mata sallama ya fice.
Abu ya danne dariyarsa da ƙyar, danshi Gwaggon tasu da Yayansu dariya suke bashi a kullum, sai kace wasu surukai.
Gwaggo da tasan shakiyancinsa ne ya motsa ta ɗakko mafici tana kai masa duka, da gudu ya fito a ɗakin yana dariya.

Ahmad yana gaban kejin kajinsu tsugunne Sadiya tazo zata fice riƙe da kwanon langa babba, tai masa sannu tana ƙoƙarin wucesa.
Kiranta yayi, hakanne ya sakata tsayawa tana juyowa gareshi, “Na'am Yaya nazone??.
“A'a karki zo? yay maganar cikin gatse yana zaro ɗan tsakonsa sabon ƙyankyasa daya mutu daga kejin.
“Yi haƙuri Yaya?.
Baice mata komaiba sai da ya miƙe, “Mi zaki sayo muku??.
“Yaya ƙosai Baba yace, na ɗari da hamsin?.
Bai bata amsar maganartaba ya lalubo ɗarin aljihunsa ya miƙa mata, “Amshi wannan kije Mudan na fanfo ki amshi ɗari a hannunsa saiki sayo, shi kuma baban ki maida masa kuɗinsa?.
“To Yah Ahmad mun gode, ALLAH ya kara buɗi na alkairi mai albarka?.
“Amin? ya amsa akan laɓansa, ya ɗauke kansa daga sadiya yana ƙwalama Zainab autarsu kira.
Babu ɓata lokaci ta iso hannunta riƙe da tsintsiyar da take sharar tsakar sashensu.
“Idan kinzo shararnan ki sharo cikin kejin nan, wannan ɗan tsakon a wullasa masai karna dawo na iskesa anan wajen, sanan a wanke kwatanniyar agwagi a zuba musu sabon ruwa?.
“To yaya? ta amsa a ladabce.
Ficewarsa yay ba tare daya sake amsawa ba.

Majalissar abokansa yaje inda suketa bikin karya kumallo, wasu da koko wasu da shayi dai dai ƙarfinsu, sai indomie da ƙalilan ɗonsu sukeci da aka dafo daga wajen mai shayi.
Zama yay yana miƙama kowa hannu suka gaisa, duk sukai masa tayi, amma sai ya girgiza musu kai, nanfa suka hau masa ƙorafi akan hakan.
Murmushi kawai yayi, danshi babu wanda yasan yana azumin idan ka cire Ayyah, ko Gwaggo idan ba taga Ayyah nata ƙoƙarin haɗa masa abin shan ruwa ba bata cika sanin yana azuminba.
Text message ya shiga tafa ma Samina da ƴar ƙwaƙur din wayarsa, yanayi yana ɗan murmushi harya kammala ya tura mata sannan ya maida wayar aljihu yana fuskantar hirar da abokan nasa keyi mai kama da santin

Please Login or Register in order to submit comment