Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ji yanda yaga Mala yana janmu a jiki,shiyasa yake jin haushi idan mukace Mala da matarshi sunyi mana wani abu ,bayan mun ida raka Baffah bakin mota mukace ya sawo mana ice cream sannan muka dawo part dinmu,muna sane da kallon banzan da Mala yake mana tun Baffah na nan har ya tafi,Amman mudai mun nemi tsari wajen ubangijinmu Allah.
Bayan mun dawo daga rakiyar Baffah muka shigo parlour muka iske Momy zaune tayi tagumi duk abun duniya ya isheta.
Dafata mukayi na fara cewa."Momy dan Allah kiyi hakuri insha Allah ba zamu sake ba munyi maki alkwari."
Cigaba da cewa Basma tayi."Momy munsan duk mune muka saki cikin wannan yanayin daga dawowarmu, amman insha Allah ba zamu sake ba."
Kallonmu tayi sannan ta mike tsaye ta shiga room dinta ta barmu tsaye a parlour muna kallon juna.
Cema Basma nayi."Basma please dan Allah kizo mu bita room dinta mu bata hakuri wallahi ko yau ban iya bacci idan har bata yafe mana ba."
Kallona tayi itama sai kawai naga hawaye yana zuba a idanun Basma, dan ita Basma kuka bai mata wahalar yin, cikin kuka tace. "Mun bani Salma mahaifiyarmu tana fushi damu, fushi mai tsanani, idan muka mutu yanzun mai zamu cema ubangijinmu."!?
Bance mata komai ba kawai hannunta naja muka nufi room din Momy dan maganar da Basma tayi ta tada man hankali sosai haka mukayi ta maza muka shiga room din....
Muna shiga muka iske Momy zaune bisa bed dinta tana tunani dan abun duniya duk ya bi ya isheta, abunda yafi tada mata hankali furuncin da Mala yayi kaimu sannan kuma ga Baffah ya daura mata laifi, bayan bata san abunda tayi ma su Mala ba har haka, da zasu gaya mata da ta basu hakuri.
Zaunawa mukayi muna kuka, dan mun tsorata a yanayin da muka ganta, dan ni irin kallon da naga tana yi mana sai da naji gabana yana faduwa, Basmace tayi karfin halin cewa."Momy please, wallahi.... Tas! "Momy ta wanke Basma da Mari tana nunata da yatsa gami da kulle ido tace."wallahi idan har baku banma room ba har na bude idona sai na tsine maku albarka."
Da sauri muka, Wago kanmu a tare muna kallon Momy da idonta yake a kulle, sake cewa tayi...." zaku fita ko sae na tsinemaku uban kowa ya huta." cikin kuka na girgirza kae nace...

NOTE

_A bisa a wani dalili litafin BANSAN INDA SUKE BA A HALIN YANZUN ya koma na kudi farashi maifi sauki, Yar'uwa shin kin shirya jin yanda labarin SALMA zai kasance da kuma sanin shin ina su BASMA da BAFFAH suke, ko kuwa wani abun Mala yai masu."!?_


_Kamar yanda nace maku da farko ba sae nace komae ba, da kanku zakuce komae a cikin novel din BANSAN INDA SUKE BA, dan yanzun aka fara wasan kuma naga kuna cewa komae din=ØÞ_


_anata biyoni ta private ana cewa yar'mutan kankia kin iya novel dan salonki daban yake, ni masoyiyarki ce ta asali dan kuwa ko wani novel kika saki baya wuce ni sae na karanta shi, to tanan zanga kaunar ta gaskiya wajen paid din novel din nan, dan nasan soyayyarce zata a saya har aji dadi>ØpÝ_


*Yanda zaki biya=ØGÜ*

NORMAL GROUP #400
VIPS KUMA #800
Via acc num 0777512438 access bank Jamila Abubakar Bello, idan kuma kati zaki turo kiyi man magana ta wannan numbers din 07034464517 /08160508316

Share pls=ØOÜ


*BANSAN INDA SUKE BA*
_A HALIN YANZUN_


*NA*

*Yar'mutan kankia c'þ*


*MANAZARTA WRITERS ASSOC*


*BISSIMILAHIR RAHMANIR RAHIM*

*Free page ya kusa karewa kiyi maza kije kiyi subscribe https://youtu.be/oP9HIZhDPaA kiyi screenshot ki turo ta wannan numbers 07034464517 /08160508316 sae nayi adding dinki a paid group, Vips kuma #500*


*Chapter 14&15<Ø9ß*


"Kuka muka fashe dashi lokaci guda, dan bamu yi tunanin jin haka daga gareta ba."
"Tashi nayi na rungumeta ina cewa."Momy laifin mai mukayi maki har haka."!?
"Na san ba ansa zata bani ba shiyasa na cigaba da ce mata."Momy dan girman Allah mun rokeki ki yafe mana, wallahi ba zamu sake ba har abada, munsan mu masu laifine, amman muna neman sausaucin ki Momy."
"Kallonmu take cikin tausayawa, dan itama ba dan ranta ya so ba take mana haka, amman dole zata nuna mana bacin ranta sosai, yanda ko mai sukayi yi mana, to baza mu biye masu ba, dan ta lura mudun muka cigaba da biye masu zamu rabata da gidan mijinta."
"Tashi tayi ta shiga toilet ta dauro alwallah ba tare da tace mana komai ba, ta fara sallah, tashi Basma tayi itama ta shiga tayo alwallahr ta cigaba da sallahrn, niko dai ban tashi ba, kuka kawai nike dan na tsorata sosai da naji Momy tace zata tsine mana albarka saboda su Baba Mala, ake niyar tsine mana."
"Sudai cigaba sukayi da sallar su niko ina zaune, tunani nike wani mataki zani dauka, dan idan bamu dauki mataki ba watarana sai Baba Mala ya rabamu da iyayenmu, abun farin cikinmu."

Shi ko Baba Mala tunda muka shiga cikin part dinmu ya shiga nashi nan ya fara yi ma matarshi magana yana cewa."wallahi! wallahi!! wallahi!! Zulai sai nayi ajalin Muhammad shida wannan tsinannun yaran, harda matarshi, dan ita take hanani yin abunda dace, dan naga tana saman ido cikin gidan nan."
Tashi matar tayi tana mashi wani kallo tana cewa."sai yanzun kasan Aisha tana sa maka ido a gidan nan."!? Ai ni ido kawai na zuba maka naga iyakar gudunka, yanzun Mala ace kana kallon dukiya amman ka kasa ansheta ta dawo hannunmu, jibafa ka gani yanda Aisha take daga man kai, dan takamar mijinta yana da kudi, mijina yana zama karkashin mijinta suna ciyarmu."numfashi ta sauke ta cigaba da cewa...."Mota wannan mota ace Muhammad ya rasa motar da zai saya maka sai Mercedes Benz , amman ai ya saya ma matarshi Prado Cruz ko."!?
Kallonta yake ranshin bace yace."kwantar da hankalinki Zulai, wallahi gidan nan sai ya zama namu, duk wata duniya ta Muhammad sai ta zama tawa, ke idan na kashe Muhammad ko dan uwanshi Muhmmud ba zai tambayeni dukiya ba."!?
Wata boss din dariya Matarshi tayi dariya irin ta basawa sannan tace."taya Mala? Nace taya Muhammud zai zuba maka ido yana kallon dukiyar dan uwanshi baice zai ansa ba? Karka manta Muhammad da Muhammud uwarsu daya ubansu daya kuma ranar daya aka haifesu wato Hassan da Husaini ne Mala."
Shima dariya yayi yace."karki manta da wanda kike magana Zulai,Mala ne fa, ko kin manta Mala mijinki? Kin san waye ni? Kuma kin san abunda zan iya da wanda ma ba zan iya ba, dan haka zuba man ido Zulai lokacin zan baki mamaki na karshe." Harararshi tayi sannan tace....."Shikenan ai na gani a kasa ba fadin ba."


Bayan sun gama sallahr Momy ta kalleni tace."Salma nasan ki, kuma nasan abunda zaki iya da ma wanda baki iyawa, duk da dai ba'a shedar dan yanzun, amman Salma ina mai rokanki dan Allah ki rufaman asiri, ki rabu da su Mala, idan kuma kina son aure ya mutu to ki cigaba da biye ma su Mala."
Kallonta kawai nike,dan jikina ya mutu ma sosai, da naji Momy tace auren ta zai mutu saboda dasu Mala, hangon fushin da Baffah yake shiga idan aka anbaci laifin da su Mala suka yi, take na sake jin wani weak ya lublubeni, dan bamu da gata sai Baffah to shi Baffah baya ganin laifin su Mala, aiko dole na ajiye makaman aikina dan ko bani da gata a wannan fannin.
Cewa nayi."Momy nayi maki alkwari komai zasu yi man bazan tanka su ba, zan barsu ga Allah kawai, kuma Insha Allah ba abunda zasuyi mana, dan Allah yana tare damu Momy."
Murmushi Basma tayi sannan tace."yauwa Sis, abunda nike so kice kenan, kuma mai hakuri yana tare da riba, abunda nayi tunani Salma shine bamu da gata sai Allah, Baffah shine mahaifinmu, amman ki sani baya goyan bayanmu a wannan harkar gani yake ma karya muke yi ma Mala, duk abunda zai yi mana, to maiye mafita? Mafita shine kawai mu ajiye makaman yakinmu tunda bamu da kayan Aiki ko ya kika gani."!?
Tashi nayi daga idan nike na rungume Basma ina kuka nace. "Tabbas Sis maganar ki dutse ce bamu da kayan aiki, dole mu ajiye makaman yaki, amman abun farincikin Allah yana tare damai gaskiya, Insha Allah mu zamu nasara akansu da addu'a."
Rumgume mu Momy tace tana samana albarka, tun daga ranar bamu sake biye ma su Mala ba acikin gida duk da ko suna mana abubuwa da yawa kuma muna gani ba bamu gani ba, amman mun sama sarautar Allah ido kuma muna kai kukanmu wajen Allah, tunda Baffah yaga bamu fada dasu Mala yake kulawa damu sosai sama da dama, soyayya mai karfi ta sake shiga a tsakaninshi da Momy, daman basu tab'a samun matsalar ba sai da Mala suka dawo gidan mu da zama.
Hutu yayi hutu, abubuwa da dama sun faru, amman muna sanyewa, idan abun yayi yawa naji zuciya tana shirin bugawa saboda bakin ciki, nakan shiga toilet na kulle kaina nayi kukana na koshi sannan na fito, nayi sallah ko naji dadi a cikin zuciyata.
Wata rana ina cikin kuka naji Basma ta dafa ni, juyowa nayi ina kallonta, itama alamu sun nuna kukan tayi ce man tayi."Salma haka zamu biyema Momy muna zuba ido abubuwa na faruwa cikin gidan nan Salma."!?
Hmmmm!."Basma kenan, nasa gabanki Momy tace zata tsine mana ko? Sannan kuma tace mu rufa mata asiri karda mu kashe mata aure ko."!?
"Eh hakane Salma, amman duk da haka ya kamata muyi wani abu."
Cikin faWa na taso ma Basma ina cewa...."Wani abu? Wani abu fa kikace Basma? Ni ba abunda zaniyi Basma ba Momy ta zaba soyayya ba akan rayuwarmu ba? Ta zabi ta faranta ma Baffah rai, tana kallo ana son kashemu daga mu harda su ma, Momy ta zabi son zuciyarta Basma,Momy tana son Baffah bazata iya tsayawa ba ta gaya mashi gaskiya duk mai zakinta, kuma bata zata iya tsayawa ta gaya mashi abunda ke faruwa ba a gidan shi, to mu ko mai zamu iya yi Basma."!?
Kuka ta fashe da shi tace."wallahi Salma na fara tsorata da lamarin Mala, rannan da kunnena naji yana cewa sai ya kashe mu harda ma Baffah duk zai kashe, Salma wallahi tsoro nike ji sosai, nidai idan gidan nan bazai gyaru ba Abuja zan koma da zama gidan su Yaya Basam kawai wallahi." girgirza kai nayi ina kallonta sannan nace...."Sai dai ki koma Abuja ke daya Basma, amman niko ina nan nida su Baffah duk wahala ba idan zani, kuma wallahi ki sani Mala bai isa ya kashe mu, mudun ko kikaga mun mutu to ki sani kwananmu ne ya kare."
Ji mukayi ance.....

*Yanda zaki biya=ØGÜ*


https://youtu.be/oP9HIZhDPaA

Idan kina bukata kuma kina son jin yanda labarin BANSAN IDAN SUKE BA A HALIN YANZUN to ga dama ta samu ki bude wannan video din ki kalla sannan ki dannan subscribe gami da bell tare da like kiyi screenshot ki turo man zan saki a paid group...

Nayi hakane sbd masoyana kije kiyi subscribe da danna bell da kuma like kiyi screenshot ki turo man zansaki a paid group ki turo ta wannan numbers 07034464517 /08160508316

*VIPS KUMA #500*
Via acc num 0777512438 access bank Jamila Abubakar Bello, idan kuma kati zaki turo kiyi man magana ta wannan numbers din 07034464517 /08160508316


*Share pls=ØOÜ*


*BANSAN INDA SUKE BA*
_A HALIN YANZUN_

*NA*

*Yar'mutan kankiac'þ*

*MANAZARTA WRITERS ASSOC*

*BISSIMILAHIR RAHMANIR RAHIM*

*na kudi ne, kije kiyi subscribe https://youtu.be/oP9HIZhDPaA Kiyi screenshot ki turo ta wannan numbers din 07034464517/ 08160508316 sae nayi adding dinki a group paid group Yan normal kenan, idan kuma baki da halin yin subscribe #300 ne kacal zaki turo nasaki a paid group, VIPS kuma #500*

*Chapter 16&17<Ø9ß*


"Salma mai kuke yi a cikin daki, baku fito mukaci Abinci ba."!?
Waigowa mukayi a tare muna kallon Baffah da yake mana magana, shima kallonmu yake ida shigowa yayi yace."subuhanalillah, Basma mai akayi maku kuke kuka? Mai ya samaiku? Maike yi maku ciwo."!?
Haka ya jero mana tambayar cikin tashin hankali, dan ya rude sosai da ya ganmu muna kuka, kyawkyalo murmushi mukayi sannan nace."wallahi Baffah kan Basma ne ke ciwo sosai tun dazun, kuma naga tana kuka shiyasa nima nike yi."
"Subuhanalillah, ku sanyo gyalenku kuzo mu tafi hospital, ai zama bai ganmu ba, maza ku taho mu tafi, bansan kuma naji kunyi wata magana, dan na lura baku san zuwa asibiti shiyasa kike zaune da cuta a jiki."...tafiya yayi dan ya dauko key dinshi, mu kuma muka shirya muka fito dan daman ina bukatar ganin doctor daman sosai.
Gaya ma Momy mukayi zamu hospital, kan Basma yana ciwo, cemana tayi a dawo lafiya, tayi mana fatan samun sauki, duk da tasan ba ciwon kaine ke damunta ba, amman ko hakuri ya zama dole.
*(>ØzÝniko nace anya Momy ta dauko hanyar gsky kuwa?)*

Haka muka tafi Doctor Dara, dan shine asibitin Baffah Doctor Dara friend din Baffah ne sosai, bayan munje mun gaidashi Baffah yace yayi mana duk abunda ya dace, dan mu duka bamu lafiya, amman ita Basma ciwon kai yafi damunta.
Haka aka fara zuba mu dan harda awon B. P akayi mana, bayan angama komai muka zauna muna jiran fitowar Doctor.
Kallonmu kawai Baffah yake yana mamakin abunda ke damunmu, amman tunda muka dawo hutu bamu sakin jikinmu sosai, kamar da amman shidai yasan ba abunda yake mana haka ma Momy, balle Baba Mala da yake tsananin kaunarmu, amman yasan abunda zai mana dan ya samu farinciki, muna cikin haka Doctor ya shigo office din ya tadda mu, sai da ya zauna yace."Umma Salam(Sunan Basma na gaskiya kenan Umma Salam) damuwa ce tayi mata yawa, sai ta rage tunani sosai dan yana gab da haifa mata matsala, sai kuma Umma Salma."
Shiru yayi da yace Umma Salma dan bai san ya ma zaice ba, daurewa yayi yace."Umma Salma maganar gaskiya jininta ya hau sosai, idan ta cigaba da sama ma ranta damuwa to zuciyarta yana gab da fashewa."
Tashi Baffah yayi tsaye gumi duk ya keto mashi.
Cewa yayi."inalillahi wa'inna'alaihirajiun, Salma gaya man matsarku dan Allah, ban shirya rasa ku ba, hawan jini? Mai ke damunku ku gaya man nifa mahaifinku ne, idan baku gaya man waya zaku gaya ma wa."!?
Kallon Baffah da Doctor nike na rasa abunda zance masu, tashi nayi, nayi hanyar fita, koda Basma taga zan fita itama biyo bayana tayi, Baffah mike ma Doctor hannu yayi sannan ya biyo bayan mu, bakin mota ya tadda mu, muka wuce gida, tunda muka shiga cikin motar ba wanda yayi magana, kowa da abunda ke cikin zuciyarshi, ba kamar Baffah da yake ji kamar ya kurma ihu, ace yarinya karama kamata tana da hawan jini was ma.
Yana yin parking na balle marfin motar nayo part dinmu.
Muna shiga ciki, room din mu na shiga, na fada kan gado na fara aikin kuka, dan maganar gaskiya a lokacin ina cikin tashin hankali wai ni Salma nice yau nike dauke da hawan jini, abunda da ban tsoro, ina cikin kuka naji an dafani, dago kaina nayi ina kallon Basma dake hawaye, mu duka kasa cema junanmu komai mukayi, Baffah ne ya shigo yace mu samai shi a parlour.
Toilet na fara shiga na wanke fuska ta, sannan muka tafi, kallo daya nayi ma Baffah jikina yayi sanyi, dan banga sauki a fuskarshi ba, shiru muka yi na wani lokaci sannan Baffah yace."Umma Salma, gaya man matsalarku a gidan nan, gaya man maike damunku har haka."!?
Shiru muka yi dan har ga Allah bamu san abunda zamu ce mata shi ba, tsawa mukaji yayi yana cewa."Salma ba tambayarki nayi ba, zaki yi shiru zaki saman ido."!?
Cewa nayi."Baffah ba abunda ke damun mu, am... "Karya kike Salma, nace Karya kike."Baffah ya katseman magana yana cewa karya nike, kallonshi nayi sai kawai na fara hawaye, dan nayi ma Momy alkwarin bamu sake yi ma Baffah maganar su Mala, dan ko bamu so ta rasa aurenta saboda damu."
Cigaba da cewa yayi."Salma tunda baku gaya man matsalarku, ban isa nasan maike damunku ba, ku tashi ku tafi ni nasan maganin abun."
Cewa nayi."Baffah ma yar... "Ya isa haka Salma, nace ku tashi ku tafi, Amman ku dunga shan maganinku."
Tashi muka yi jiki duk a sanyaye, muka shiga room, kallonmu Baffah yayi sannan ya girgiza kai yace ma Momy."Dear yaranan suna cikin matsala, kuma naga ba gaya man zasuyi ba, ko ke kinsan abunda ke damunsu."!?
Kallonshi Momy tayi, tashi tayi ya dawo kusa dashi ta zauna sannan tace."Nima bansan abunda ke damunsu ba, Amman Abu daya za'ayi shine muta addu'a."
Murmushi yayi sannan yace."hakane, Amman dole muringa yi masu abunda zai sasu farinciki, kisan su kadai Allah ya bani inasan farincikinsu."
"To Insha Allah."
Tunda muka shiga room ba Wanda tace ma kowa komai, dan ni wanka na shiga ma, Kafin na fito Basma ta fiddo mana da kayan da zata sanya, itama wanka ta shiga tana fitowa ta shirya kallona tayi tace."Salma karki damu, mu cigaba da hakuri kinji Sis."
Daga mata kai kawai nayi sannan na kwanta bacci nayi ban tashi ba sai 5pm, wanka kawai nayi sannan nayi sallah parlour natafi na tadda su Momy suna kallo, zaunawa nayi na fara kallo, muna cikin kallo Baffah ya dawo, cewa yayi." My twice girls, close ur's eyes."
Kulle idanuwanmu mukayi, ji mukayi ya sanya mana wani abu a hannu, sannan yace."open."muna dubewa muka ga makulin mota da ya ba ko wancan mu, kowa da tata kuma sabuwa dal."
Tashi mukayi lokaci guda, muka rumgumeshi muna cewa."Thank you Baffah."dan rasa abunda zamu ce mukayi, fitowa mukayi dan zuwa ganin motors din, muna fitowa muka hadu da Baba Mala dan da alama daga wajen motar yake, murmushi yayi sannan yace."Alhaji Allah yasa alkhari, ai shigowa ta Kenan naga kayi sabuwar mota kai da Hajiya."
Cikin farinciki Baffah yace."ai Alhaji Mala, ba motarmu bace,motar Yarankane Salma da Basma."
Take fuskarshi ta sauya, ™a™aro murmushi yayi yace."masha Allah, gaskiya natayasu murna, motar sunyi kyau sosai, Allah yasa akashe lafiya."
"Amin ya Allah, Alhaji Mala."
Nan muka wuce dan ida zuwa ganin mota, shi kuma ya shige part din shi, yana shiga yace ma matarshi."Zulai tabbas dole na tashi tsaye cikin kwanankin nan, naga na kashe Alhaji Muhammad shida iyalanshi."
Kallonshi tayi ta watsar, sannan tace."ai ni na haddace wannan maganar taka Mala, halan wani abu kaga yayi ma wannan tsinannun yaran nashi."!?
Kallonta yayi yace."Zulai Mota sabuwa fal ya saya masu, yau din nan, kuma yana sane da Dahira bai saya da ita ba."
Tashi tayi daga zaune tana dafe kirji tace."mota ya saya masu? Tabbas Mala kana da aiki gabanka, tsaya kallon ruwa kwaWo yayi maka ido."
Dariya ya fashe da ita yace zan baki mamaki ne, kin san waye Mala, wallahi yau din nan sae sun bakunci lahira.... Itama dariyar tayi tana cewa.....


*Wannan shine second to the last freee page=ØÞ*


*Yanda zaki biya=ØGÜ*
*NORMAL GROUP #https://youtu.be/oP9HIZhDPaA *
*VIPS KUMA #800*
via acc num 0777512438 access bank Jamila Abubakar Bello, idan kuma kati zaki turo kiyi man magana ta wannan numbers din 07034464517 /08160508316

Share pls=ØOÜ

*BANSAN INDA SUKE BA*
_A HALIN YANZUN_
*NA*

*Yar'mutan kankiac'þ*

*MANAZARTA WRITER'S ASSOC*

*BISSIMILAHIR RAHMANIR RAHIM*

*LAST FREE PAGE<Ø9ß*
*Na kudi ne, kije kiyi subscribe https://youtu.be/oP9HIZhDPaA kiyi screenshot ki turo ta wannan numbers din 07034464517 /08160508316 nayi adding dinki a group, idan kuma baki da halin yin subscribe #300 ne kacal zaki turo na saki a paid group, VIPS kuma #500*

*Chapter 18&19<Ø9ß*

Itama dariyar tayi tana cewa..."Mala kenan ba zan daena fadi ba na gani a kasa." Zagaye shi ta farayi sannan ta cigaba da cewa." Mala idan kai ka fasa aikata ™aramin aiki to ni Zulai zan aikata maka, amman kasani dukiya zata zama ta Zulai kai zaka zama kwalkwashin ikona, duka minti nawane kashe wannan tsinannun Mala? Kashe Muhammad da iyalinshi ban daukeshi komae ba, amman kai ka tsaya yin danmace tsaya kallon ruwa kwaWo yayi maka... "Ya isa haka Zulai."Mala ya tsada Zulai cikin fushi sai zara mata jaijayen idanuwanshi yake cigaba da ce mata yayi." niyi maki alkwarin yau din nan ba sae gobe ba dukiya zata zamo tamu dan yau ba sae gobe ba zan kashesu baki daya." murmushin farinciki Zulai tayk bata ce mashi komae ba ta cigaba da hidimar gabanta.

*Some week letr*

Tun da Mala yaga Baffah ya saya mana mota, ya sake taku, dan ko ba abunda baya yi mana,
Mudai tun daga ran da Baffah ya siya mana mota, bamu sake shiga harkar Mala ba, duk da muna ganin abunda Mala yake, amman mun sa ido muna kallon ikon Allah, dan bamu so wani abu ya samu Momy shiyasa muma muka kama kanmu duk muna kallon cin kashin da Mala da suke mana muda gidan ubanmu.
Watarana Momy taje gidan ™awarta, daman shi Baffah ba ma zaunin gida bane, kuma shi Baffah koda yana gida to baya shiga harka kowa.
Aiko kamar jira Šahira take Momy ta fita, ta shigo, apartment dinmu tana taunar chingum tana wani ya tsina, tun da ta shigo Basma ta kalleta ta watsar daman ita Basma ba son hayaniya take ba, niko tsaki nayi sannan nace."tsintaciyar mage bata mage, dan Allah Basma kalli yanda mutun yake cika yana batsiwa sai kace gidan ubanshi."!?
Kallonta Basma tayi sannan tayi tsaki gami da dariya tace."ai Salma ko da mutun gidan ubanshi ne, iyakar abunda zaiyi kenan, balle kai bawa gidan nan ba na ubanka bane, karaka akayi ana ciyardakai, har kake so ka nuna kafin ´a'´an masu gida."
Wani irin ashar Šahira tayi sannan tace."koda gidan bana ubanta bane, amman tafi masu gida yin iko, kuma nan da yan kwanaki gida zai zama na ubanta."
Cigaba da cewa tayi."wallahi wallahi wallahi, sai munga karshen ku, ku ba yan iska ba? To zamuyi maganin duk wani shege a gidan nan."
Tas na tashi na wanke ta mari, kafin ta Wago na sake wanka mata wani marin, sai da nayi mata mari kusan biyar, sannan nace."can kiga yan iska, amman ba anan apartment din ba, kuma shegu na can kin baro kika zo nan, kuma ki sani mufi karfinku da ayar Allah, kuna ta™ama da boka da malaman tsiSu, mu kuma muna ta™ama da Allah, dan haka take note."
Duk abunda muke Basma bata ce mana komai ba, ko ma kallonmu batayi ba, cigaba da chiting dinta tayi, dan tasan ni Waya ma na ishesu aiki ba sai ta sa baki ba.
Dafe kunci Šahira tayi sanann tace."kam bala'in nan, dan ubanki ni zakiyi ma wannan marinka, sai kace kin haifeni."!?
Dariya rainin wayau nayi mata sannan na fara zagaye ta,ina cikin zagaye ta, naji ™arar marika, gami da wani ihu da sauri na jiyo, aiko naga Basma ce take wanke Šahira da zafafan marika wanda ya sata yin wannan karar, da gudu Mala da matarshi suka suka shigo dan ganin abunda ya sa Wiyarsu kuka, aiko suna shigowa suka ga Basma tana tura Šahira waje tana cewa."wannan shine na karshe da har zaki shigo ki iskemu inda muke ki kiramu da yan iska gami da kiran iyayenmu da suna shegu, bayan ga shegunan sun biyo ki, dan haka idan kunne yaji." ta ida maganar ta nuna su Mala da yatsa ma'ana sune shegun, ko ni sumar tsaye nayi dan maganar tayi man girma ga mari ga kuma gaya bakar magana har haka, ita kuwa Basma ko a jikinta.
Wata irin tsawa Mala yayi ma Basma yana nuna ta da yatsa sannan yace."wallahi nayi imani da girman Allah sai kunyi da nasanin abunda kukayi ma Wiyata, ni Mala sai naga bayan ku, kuda iyayen naku."
Wani irin lalacencen kallo Basmaa tayi mashi sannan tace."kai Win banza kai Win wofi, kai waye? Nace kai dan gidan uban waye? To bari kaji Mala, ba tsoranka muke ba ka gane, karkaga kana mana abubuwa muna kyaleka ka dauka tsoranku muke, aa ko Waya kawai dai kana cin darajar Momy wallahi da sai mun yi maka zingir a gida nan, danma ka sani, kuma tunda haka kuka zaSa mu zuba muda ku cikin gidan shege ka fasa kuma dan halak sai yanke, Kai Mala kafin na buWe idona ku bar mana apartment ko nayi maku rashin mutunci ku dukan ku."
Tsoro ne ™arara a fuskar Mala, amman dakewa yayi yace."kuyi mai isarku mararsa kunya, lokacine." harara ta watsa mashi tace...."A banza a wofi, oya ku fitar mana daga waje ko wallahi

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment