Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

muka fara fada, sai ga Allah ya kawo Hafsat..
"Mai ya hadaku kuma."? Cewar Yaya Hafsat, aiko nace mata"Wai ni zata cema jarabatu." Cikin mamaki Yaya Hafsat tace."shine dan kawai tace maki jarabatu shine zaki batama kanki lokaci."? Turo baki nayi ina magana ciki, cigaba da cewa tayi...."Ku taso mu tafi bani san wanann sakarci, daga yau." Cewa nayi."to amman yaya Hafsat kice mata tabar jana fada."kallon Basma Yaya Hafsat tayi sannan tace...."ke Basma karki sake ce mata jara ba tu." Ciki Basma tace....."To na daina yi hakuri Salma." Dafata nayi sannan nace...."nayi hakuri, kema yi hakuri Basma."
Haka muka tafi fell, ita Basma ta shiga team din yan gudu, ni kuma na shiga team din boli...
Munyi wasa yanda ya kamata, da man ni ba daga nan ba wajen boli ina bala'in san boli, dan Hafsat tayi mamakin yanda nike ta buga ball din boli kamar ba ita ba..
Bayan mun taso daga fell aka yi ringing din dinning muka je muka ansa sannan ko wace yarinya ta tafi massalaci, bayan mun dawo daga massalaci muka tafi kwanar wata sabuwar friend da mukayi Sabira can muka tadda Asm'au akaita labarin gida, daga nan muka wuce night...
Bayan mun dawo daga night muka zauna muna labarin yan class din mu..
"Ni Basma Ina mamakin yan class dinmu wallahi, sudai sun cika tsoro kamar farar kura." Dariya Basma tayi sannan tace...."Kisan Allah Salma zasu warene har basu ida sabawa da juna ba, kowa dai sitmate dinshi yasani da ita yake labari." Dan shiru nayi sannan nace...."To mai zai hana inmunje class gobe kowa ya tashi yayi introduction din kanshi, kinga ta wannan hanyar zamu sannan juna."
"Hakane Salma kin kawo shawara mai kyau Allah ya kaimu goben lafiya..
"Amin, ke ni sai da safe bacci nike ji, kuma nan school din tashi asuba suke yi, "aiko sai da safe..
Washe gari Bayan mun gama potion da duk wani school athorities sannan muka tafi class..Bayan kowa ya gama zuwa class na ta tashi na fara magana..
"Yan class din nan, yau zanyi roster gashi ba kowa na sani class ba dan Allah kowa ya tashi yayi introduction din kanshi..
Nan fa yan class sukayi Naam kowa ya tashi yayi introduction din kanshi, ni kuma ina rubuta sunan kowace a roster har suka gama..
"Basma tashi muje admin block mu dauko check." Tashi Basma tayi tana cewa...."to mu tafi Mau sai mundawo..... Nan muka wuce muka dauko alli harda doster sabuwa muka taho da ita.. Bayan mun dawo daga Admin, nan muka zauna muna ta labari duka ajin ashe da man yan ajin likimo sukayi kowa da kunshin rashin jin maganarshi kunshe a wando=.
Haka muka cika makaranta da surutu sai da wani malami ya shigo yayi masu warning akan surutun mu yayi yawa, sannan ya sa ni naje na kira malamin Math dayake shi muke dashi.
Bayan yazo yayi mana lesson ya Kama gabanshi..
Bayan antashi daga class muka wuce hostel..
Yau dai da kanmu muka yi wanki, bayan mungama muka shiga wanka muka shirya muka anso dining sannan muka wuce evening...
Yau general muka tsaya bayan antashi daga evening..
"Yaran makarantar! "Naam!"yaran makarantar nan! "Naam! "Dan ubanku bakuji? "Muna ji! "Bakuji! "Munaji! "Uban mai yasa kwana biyu baku yi mana potion har sai an koroku."?
Wata prefer ce take wannan bayanin a filin general cleaning..
"To daga Yau kar yar'iskar yarinyar da ta bari muka sake korota yin potion kuna ji?
"Eh munaji, haka aka gama bugunmu a ringing sanann suka sallami ko wace ta wuce wajen potion dinta..
"Wai Basma baki daina wannan kukan."? Cikin kuka Basma tace."Salma baki ga yanda akayi mamu bane Wai."? Cikin takaici nace"To ya zamuyi." Tsaki Basma tayi sannan tace man."Ai dole kice ya zamuyi sai da nace maki karda muzo boarding kike ce boarding dadi ai ga dadin nan muna gani.. "Uhmm." nidai na cigaba da potion din na, muma nan gaba zamuyi ma wasu irin abunda aka yi mana Yau Basma. "



```Toh fa jama'a kunji wani dogan guri wajen Salma wai suma zasu yima wasu abunda akayi masu, yarinyar da take JS1 take hangen anbasu prefer =```


*Muje zuwa.... =ؤ*


*Yar'mutan kankia cec'*


Share
Comment
Please

*BANSAN INDA SUKE BA*
_A HALIN YANZUN_

*NA*
*Jameelah Jameey*

*Yar'mutan kankia cec'*


*MANAZARTA WRITERS ASSOC*

*Marubuciyar=G*
*Nana Jawaheer*
*Gimbiya Hakima*
*Izzah ko mulki*
*Sanadin link*
*A gidan haya*
*arawo ne*
*Sadaukin burhaan*
*Sanadin soyayyar shan minti*
*Bayi ma a'ane book 1&2*
_AND KNOW_
*BANSAN INDA SUKE BA*
_A HALIN YANZUN_



*BISSIMILAHIR RAHMANIR RAHIM*

*Chapter four nd five<9*


"Bayan mun gama potion din, muka koma hostel, ba wani abu mukayi ba tsintsiyar mu kawai muka ajiye sannan muka tafi muka anso kitchent, bayan mun anso kitchent muka tafi massalaci sallahr mangarid, bayan mun dawo mukaje kwanar Asma'u mukayi firar dare, daga nan muka wuce night."
"Da mukaje night ne, duk da ina class captain hakan bai sa mun daina yin surutu ba, Asma'u ce tace man, "dan Allah Salma kin kalli film din gwaska."?
Ce mata nayi, "eh na kalla kuma yayi man kyau gsky."
Ceman tayi niko ban kalli shi duka ba, dan Allah ko zaki bani labarinshi."?
Duk da ina class captain hakan bai hana ni na ma taba, daman mu yan class dinmu duk kusan ince maka halin mu Waya, dan haka na cigaba da bata labari, hankali na kwance, idan na manta wani waje Basma take yi man tuni, muna cikin haka Yaya Zainab tazo, wata prefer ce itama, nan tasa muka rage tsawonmu ta fara bugunmu, tana cikin bugunmu na mie na ci mata kwalar riga kafin ta farga na wanka mata mari dan gaskiya bugun da tayi man ya shige ni sosai, shiyasa na rama dan ban ma san na rama ba sae da na aikata sannna da lura da kuskuren da na aikata."
"Aiko ranar nasha wuya, dan cikin daren nan su duka prefer din suka taro kaina, duk da Yaya Hafsat taso basu hakuri amman suka ce ai idan har ba su bugeni ba to basu bane, bayan mun koma dakin Yaya Hafsat tayi man fada sosai."
"Haka muka kama rayuwarmu a boarding nida Basma watarana muyi kuka watarana kuma muyi dariya."
"Baiwar Allah Basma, duk kusan kullun nike ja mata bugu a makaranta, dan ban manta watarana lokacin muna Js2,a lokacin Yaya Hafsat tayi guaranteed bamu da kowa sai Allah, muke yi ma kanmu wanki da dibar ruwa, komai da kasani dan boarding yana yi ma kanshi to muke yi ma kaimu, duk da Baffah yaso ya ciremu nice nace sai dai ya cire Basma, amman nidai ba inda zani sai na gama, dan nayi ma kaima alkwarin sai na rama duk abunda akayi mana a g.g sandamu, da Basma ta yarda a fidda ta dan har anfara shirin maidata F.G.C Bakori, Amman kwana na, Waya da komawa itama Baffah ya maidota dan bata iya rabuwa dani, nima daman hakuri nayi dan tunda na dawo ni daya na zama wata kalla nidai kamar ba ni ba, aiko ranar da Baffah ya maido ta muyi murnar ganin juna sosai dan harda kuka mukayi, haka yan class dinmu suma sunyi Murnar dawowar Basma haka muka cigaba da rayuwarmu."
"Watarana na fito ni Waya banda Basma, dan Basma cewa tayi ita a ranar bata san fita niko naga ban iya zama waje Waya nan na barta a corner nikuma na fito zan zo wajen wata friend din ta Amina Darma, lokacin da naje nan na tadda Asma'u Darma ita da Sabira nan muka zauna muka cigaba da labarin gida, bayan mun gama nayi sallah nace ni zan koma corner na bar Basma ita Waya a corner , ashe tsotsayi ne ya fiddo ni a ranar, ina cikin tafiya naji anyi jeking dina, waiga wa nayi naga wata Senior Winmu ce mai suna Fatima Usman, amman ana kiranta da suna F.U, haka ta rie ta cigaba da jan yan'uwana junior haka ta gama haWa mu waje Waya sannan ta tusa mu gaba ta tafi damu domin mu Wauko mata ruwa, tunda mukaje wajen Waukar ruwan nike noewa dan banyi niyar dauka ba tun asali, aiko ina samun dama na rugawata, sai corner nayi zamana, tunda F.u taga bani nan ta hau zagi tana cewa wallahi idan ta kamani sai ta kusa kashe ni."
"Niko tunda na gudo ko Basma ban gaya ma abunda ya faru ba, nidai nace mata na dawo, nan muka zauna mukai ta labarin Momy da Baffah, da yake ranar ta kasance ranar Friday, da yake duk ranar Friday ba'a zuwa evening balle night, shiyasa ranar Friday ta kasance ranar walwala ta student a G.G Sandamu, da yake ansoke yi mana black Friday shiyasa muke watayawa yanda muke bukata, kwantawa nayi inasan nayi bacci, ita kuma Basma tace man zata corner din wata friend dinmu Hadiza Abdu, niko nace mata ta dawo lafiya nima bani fita, har ko taji haushina dan nace bani fita."
"Bayan tafiyar ta na cigaba da bacci na, itako Basma tana fita taci karo F. U, bata ji ba bata gani ba taji saukar mari, dafe kunci tayi tana kallon ikon Allah, bugunta sosai F. U tayi sannan tace mata, "dan ubanki daga yau idan na kiraki ki sake guduwa wallahi karya ki ne kawai bazanyi ba shasha kawai, daman ance baki da kunya to nice zanyi maganinki."
"Kallonta kawai Basma take, dan idan da sabo ta saba da abunda nike yi mata, dan nasha nayi laifi ta kwana a ciki, murmushi tayi sannan tace mata, "dan Allah kiyi hakuri insha Allah ba zan sake ba."
Cemata tayi, "dallah can tashi ki bani waje kona ci ubanki, jibaiki kamar wata ta Allah, wai inyi hakuri baki sakewa, to kima sake mana, ai ni aikina naci ubanki."
Haka Basma ta tashi ta wuto corner, zuwan da batayi ba kenan, wajen Hadiza ta dawo, ina cikin bacci naji ta faska man bugu a baya, tashi nayi nace mata, "ubanmai nayi maki ina bacci zaki yi man kallar wannan mugun bugu."?
Itama cikin fushi tace, "naje na bugeki sai kiyi abunda zakiyi."
Nima tasowa nayi nace mata, "haka kika ce ko."?
Wani kallar kallon banza tayi man sannan tace, "haka kikaji nac... Kafin ta kulle baki na faska mata bugu nima, nan ko muka kware da dambe dan naji haushin bugun da Basma tayi man sosai, itama da yake tazo bakin wuya aiko ta biye man mukai tayi sai da kazo aka rabamu, ana rabumu ta tashe da kuka, da yake duk fushi na bankai da kamo afar Basma ba, nidai kawai da anyi man nike ramawa amman ita zakayi mata sau dubu bata kalleka ba, amman kuma duk sanda ta ce zata rama, ko ka tabbata abun ya kai ta karshe, tashi nayi na fara lailashenta ina bata hakuri, itama rikoni tayi sannan tace, "dan Allah Salma kiyi hakuri, raina ne ya Saci har na biye maki mukayi haka, nagaji ne da bugun da kike ja man, kawai daga fitowa ta F. U ta rufe ni da bugu wai ta dauke ni haya na gudu."
ara rungumota nayi nima sannna nace, "nice zan baki hakuri, yar'uwata, insha Allah zanyi kokari na bar ja maki fada."
Haka tace Allah yasa."... Ni kuma nace, "Amin."
"Washe gari ya kama ranar saturday, haka muka tashi muka fara aikin inspection, aiki mukayi ba kama hannun yaro sai da muka gama aiki, aka kiramu wai muda Basma mu zamuyi ma house dinmu queen, haka ko akayi bayan angama inspection, mukaje muka anshi kitchen.
Haka mukaita rayuwa, dan har mun fara shirin yin exams din second term Js2, kuma da mun dawo zamu shiga thirdterm kuma a term dine za'a bada shadows prefer."
Haka muka gama exams muka tafi gida, nice nazo ta Waya sannan Basma tazo ta biyu haka muka koma gida cikin farin ciki."
"Tunda muka koma gida na lura da chanji wajen Baba Mala, Baba Mala ba dan'uwan Baffah bane basu hada komai ba, dan Baffahnmu shima su uku ne mahaifansu suka haifa, shi da Husaininshi sai kuma anwarshi Mama Khadija, shi Baba Mala unguwarsu Waya da Baffahnmu lokacin da suna kauyensu mai suna Safana a jahar katsina, tare suka taso tun suna ananu dasu Baffahnmu,duk da Baba Mala yayi karatu shima, amman baiyi karatu mai zurfi ba irin nasu Baffahnmu ba, dan su Baffahnmu sai da sukayi har phd, amman banda Mama Khadija ita Mama Khadija tana yin j.s.c.e tace ita aure take so, kuma wani ma'aikacin government tace tana so wanda aiki ya kawo shi dan nan asalin garin yobe ne, ba yanda Kakanmu baiyi da ita ba akan karta aure shi, amman ta dake tace ita shi take so, ranshi ya baci sosai sai ya bata zaSi yace ta zaSa ko shi ko kuma soyayya, da yake tayi nisa tace ita soyayya, take Abbie cikin fushi ya daura mata aure da wannna wanda ta aura kuma yace tashi ba ita ya yafe ta daga cikin zuri'arshi, haka akayi kuwa, wani ikon Allah yanda akace mana bayan bikinsu da wata daya akayi ma wannan mijin nata transfer ya koma da aiki Yobe har yanzun basu sake jin labarinta ba, muma lokacin da akayi abun Baffah ko aure baiyi ba, labari aka bamu.
Shi kuma Baba Husaini, bayan sun gama karatu, da yake engineer ya karanta, Abuja yake zaune shi da iyalanshi, mu kuma Baffahnmu Doctor ne a cikin birnin katsina muke zaune a unguwar goruba road, nan Baffahnmu ya gina mana gida, zuwan da yayi Safana dan gaida Abbie yace ma Baba Mala ya dawo gidan mu da zama, shi da iyalanshi, haka ko akayi dan ko tunda ya dawo Baffah yake ciyardashi harda saya mashi sabuwar mota."
Daman tunda suka dawo da zama gidanmu, Momynmu bata san laifin da tayi mashi ba shi da matarshi, Amman tuni Momy tasan Baba Mala ba sonmu yake ba shida matarshi, da farko ta fara gaya ma Baffah sai yace mata, ya lura bata san zaman Baba Mala cikin gidanmu shiyasa ta fara laaimashi sheri, dan haka daga ranar karya sake jin haka, inba haka ba to zai dauki mataki babba, tunda Momy taji yace haka ta kama bakinta tayi shiru ta sama sarautar Allah ido."
"Tunda ko muka koma, muke ganin chanjin hali sosai daga wajen Baba Mala, koda muka gaya ma Momy sai ce mana tayi mudai mu kula da kanmu, kuma kar mu kuskura wani Abu ya hadamu da yaransu, kuma Allah yana tare da Mai gaskiya."
"Duk hakurin da mukeyi dasu muda gidan ubanmu, sai da watarana ya hadamu da yarinyarshi mai suna Dahira, fada mukayi sosai da ita, Wanda har Baffah ya buge ni shine bugun farko a duniya da Baffah yayi man a rayuwa."
"Tunda haka ta kasance tsakaninmu dasu, bamu sake ko yin magana dasu ba, laifin ma sai ya tashi daga kanmu ya koma wajen Momy."
"Haka muke hakurin zama da su har muka koma school, Amman mun koma school hankalinmu yana gida, dan zuciyarmu bata yarda da yanda muka barsu da Momy ba, tunda komai zamu gaya ma Baffah ba yarda yake ba."






*Muje zuwa..... =ؤ*





*Yar'mutan Kankia cec'*


Share pls=O


*BASAN INDA SUKE BA*
_A HALIN YANZUN_

*NA*
*Jameelah Jameey*

*Yar'mutan kankia cec'*

*<
MANAZARTA*
*WRITERS ASSOC*


*BISSIMILAHIR RAHMANIR RAHIM*

*Chapter six and saven<9*

Numfasawa nayi sannan na kalli Salim nace."Salim dare yayi ya kamata, mu tsaya nan sai kuma sanda kake da lokaci, sai na ida baka labarin."
Iska ya furzar a bakinshi yana cewa."to Salma amman gaskiya naso naji ina Basma da Baffah suke, a yanzun dai idan na fahimta wannan baiwar Allah ba kowa bace face Momy." Wasu hawaye masu zafi da Wumi na goge, na maida kallona ga Momy da take kwance kamar gawa, dan ni har yanzun banga wani sauki taitare da Momy ba, hakanan Doctor yake ce mana da sauki, amman kuwa sauki babu shi sae dai addu'a, dan yanda take haka take bata motsi ko idonta bata buWewa balle naji koda sanyi,su kuwa su Baffah ai *BANSAN INDA SUKE BA A HALIN YANZUN* maida kallona nayi wajen Salim sannan nace."Tabbas wannan Mahaifiyata ce take cikin wannan halin, Salim kai dae ba labarina kake son ji ba? to zan baka labarina amman kasani *LABARINA AKWAI RIKITARWA A CIKIN SHI* nasan kana mamakin yanda akai nike baka harda labarin rayuwarmu da mukayi a boarding school, shima yana cikin labarina."shafa gefen fuskarta yayi cikin natsuwa irin tashi yace."Shikenan Salma, Allah ya kaimu goben lafiya, nima zan tafi dare ya fara yi, nasan Mamina nacan hankalinta a tashe dan har yanzun bata san ina taimakon ku ba keda Momy, amman insha Allah kika gama bani labarinki zan gaya mata, nasan koda tayi man tambaya ina da answer da zan bata akanki duk tambayar da tayi man akanki." duk da ina cikin yanayin damuwa da kuma tunoman baya da Salim yayi, haka bai hanani yi mashi murmushi ba nace...."Shikenan Salim, nidai bani da bakin da zani yi maka godiya, sai dai nace Allah ya saka da alkhari." Wagaman hannu yayi yana cewa."Bakomai Salma, ni zan wuce gud night, but please Salma take care about your self and Momy."....."Insha Allah Bye."


Haka Salim ya tafi gida yana juyayan labari irin na Salma, dan tunda yake bai tabajin rikitarcin labari irin Salma ba, duk ta kulle mashi tunani, ya kasa gane ya labarin yake, haka yayi driving din dai jikinshi a sake yake.

compound ne babba, wanda ya ansa sunanshi compound, dan gida ne babba daga gefe wani fool ne babba sai kuma parking space,wanda akyal mota kusan goma zasuyi parking a wajen, dare ne yayi amman sai kace rana ce, sojoji ne suke tsoran gidan, gate goma ne kafin kashiga main gate din wanda zai sadaka da cikin gidan.
Tunda ya kunno hancin motarshi a gate one sojoji suke kwashar gaisuwa, wasu kuma suna biyo matar aguje, haka ma gate two sojojin wajen suka sara mashi sannan suka biyo shi a baya, haka akayi har zuwa gate ten koda ya kashe motar sai da yayi twenty minutes sannan wani solder ya taso ya bude mashi kofar motar sara mashi yayi yana cewa."welcome Sir."
Kallon shi kawai yayi, ya daga mashi hannu ansar briefcase din hannunshi wani solder yayi, sannan suka bishi a baya, suna take mashi baya, lifter ya hau ta kaishi a parlour nan masu aikin parlourn suka fara mika gaisuwa, wata lifter din ya sake hawa sai da ya hau lifter shidda sannan yaje main parlour.
Yana shiga wata kofa naga yabi ya tsaya ya danna wani fingerprint lock sannan kuma wan abune kamar mirror shi ya kalla sannna door din ta bude, nidai Yar'mutan Kankia da nike biye da Barrister nake kwaso maku rahoto sai da abun ya so bani tsoro, Ina ta mamaki dan da gani ankashe ma gidan nan kudi, kofa har da fingerprint da kuma facelock>.
Bayan ya shiga wani glass ne naga ya dannna shima ga dukan alamu fingerprint ne ya dannan ji nayi door din na cewa "welcome back Barrister Salim.".... Sannan ta bude ya shiga, wooow!!! Masha Allah lakuwata ila billa, wani kallar parlour ne ya shiga dan komai na parlour da glass akayi shi harta kujerun dake jere a parlourn na glass ne, wal'wal suna nuna mix color's kala su blue, red, purple, ash suke ta haskawa, ga decoration anyi masu da ratsin ruwa da kifaye daga gefe, idan bako yazo yana Iya kasa zama yayi tunanin ruwane a jikinsu da kifaye a kujerun.
Wata dattujuwar matace zauna tana kallon N.T.A. News, kuma tana karanta dailytrust a hannunta ga kuma waya ta hau twitter tana jin abunda duniya take ciki, hankalinta baki daya yana kan abubuwan da take, inda taga Abu mai mahinmanci sai ta dauko wata joter da take gefenta tayi wani short note, Wanda ni dai bansan mai take rubutawa ba a jikin wannan joter din, samun waje yayi ya zauna baice komai ba, sai ma maida hankalinshi shima da yayi a wajen kallon da take, sai da aka gama labarai duka a n.t.a.news sannan ta ida karanta dailytrust din tayi note a wannan joter din sannan kuma ta sake shiga wasu page a twitter taga abunda ta gani ta sauka ta ajiye jaridar tare da wayar sannan ta dauki remote ta mai da Manaratv, sannan ta waigo tace a natse"Barrister daga Ina kake cikin daren nan? I said from whare are you? Kasan yanda ka tadaman hankali kuwa."
Dukar da kanshi yayi sannan yace...."sorry Mami, Ina wuni."?
Harararshi tayi sannan tace.."ba wannan na tambaye ka ba, ce maka nayi daga Ina kake."? Raurau yayi da ido, dan shi baisan gaya Mami tana mashi fada ko ya yake, ji yake har cikin kwakwalwar kanshi, dan baya son hayaniya ko ya take kuma Mami tasan da haka, amman gashi ta kulle ido sae ihu take mashi a kunne, tashi yayi ya koma inda take zaune hannuwanta ya kama yana murzawa a shagwaSe yace....."Mami wallahi yanayin aiki ne shiyasa nayi dare ban dawo ba believe me Mami."
Murmushi tayi tana girgiza kai sannan tace...."matsalarka daya Barrister baka Iya karya ba, ko kayi ta, bata yi maka kyau, tabbas ba zan hanaka fita ba Salim tunda kai ba Yaro bane, Amman kasani kaji tsoran Allah a duk inda ka tsinta kanka, ka sani komai kake yana nan yana ganinka idan ni da Abbanka bamu ganinka, dan haka ka tashi kaje kaci abinci, Abbanka ya dawo ya tafi jana'ida cikin unguwar nan." sosa eyarshi yayi, yana murmushi dan ya lura koya yayi ma Mami karya sae ta ganoshi ya rasa dalilin haka, cewa yayi.."Insha Allah Mami, zaku samaini mai jin tsoran Allah, amman ina akayi rasuwa kuma wa ya rasu."? Cewa Mami tayi...."Allah sarki, cikin masu aikin gidan nan, Allah yayi ma yarinyarshi rasuwa dazun nan, shine yace tunda baka dawo ba shi ya tafi dan yace ace anje mashi ta'aziya." cikin yanayin damuwa Salim yace."Allahu akabar, Allah ya jikanta, Mami yau kuma mai akace goverment tayi? Dan nasan yan kasar nan tamu ba'a iya masu." murmushin manya Mami tayi sannan tace.....Hmmmm!! "Barrister kenan, har yanzun kai Yaro ne, baka san siyasa ba, ranar da na haifeka aka ba Abbanka chairman, ba tare ba an tambayeshi shawara ba, lokacin da kake S.S one aka ba Abbanka senator, shima bai sani ba, haka akazo aka bashi dan majalisa lokacin ka gama degree dinka shima bai nama ba, asali ba shi da gurin yin siyasa, dan bata burgeshi, yana nan yana nan, yanzun kuma duniya ta daga hannunshi har ya zama prisedent baki daya, kasan mai yasa hakan ta kasance."? Komawa yayi ya zauna, girgiza mata kai yayi sannan yace..."Aa Mami."
Kallonshi Hajiya Khadija tayi, tana murmushi sannan tace saboda rike gaskiya da amana, ba yabon kai ba, mahaifinka shi mutun ne mai tausayi da kuma son yaga ya taimaka ma na kasa dashi, shiyasa kullun muna hanyar karanta news kuma muna zuwa gidan tv muna kallo, gami da hawa social media muna jin koken bayin Allah, shiyasa nike rubutawa domin share masu hawayensu, idan bamuyi ma tallakawa ba wa zamuyi mawa? Wannan dukiyar tasu ce idan munci wallahi ranar gobe kiyama sai Allah ya anso masu hakinsu, kaga solution shine karkaci, Kadai kayi tsakaninka ga Allah sannan ka barma Allah sauran, dan haka wannan matsalolin yau ne na dauka wanda
Allah ya kaddara zamuji, kuma insha Allah zamu share masu hawayensu, idan Allah ya bamu iko." tabbas yasan yayi dacen iyaye na gari, dan shi har mantawa yake shi daddynshi president ne, dan Dad dinshi baya mashi wasa, kullum nuna mashi yake ya tashi ya nemi halak din shi, cewa yayi...."Allah yasa Mami, shima Abba Allah ya taya shi riko, yasa ya sauka wannan mulkin lafiya, naji yace zamu koma da zama Abuja ko."? aga mashi kae Hajiya Hadiza tayi tana cewa...."Eh da haka yace, amman yanzun yace muyi zaman mu anan yobe."
Murmushi yayi sannan ya tashi baice komai ba, abinci yaci sannan yace shi ya tafi zai kwanta idan Abban shi ya dawo Mami ta gaida mashi shi....




*Muje zuwa...... =ؤ*



*Yar'mutan Kankia cec'*


*BANSAN INDA SUKE BA*
_HALIN YANZUN_

*NA*
*Jameelah Jameey*

*Yar'mutan kankia cec'*

*MANAZARTA*
*WRITERS ASSOC*



*BISSIMILAHIR RAHMANIR RAHIM*

*Chapter eight and nine <9*

Washe gari tunda safe Salim ya tashi, ya shirya fitowa

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment