Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yayi ya tadda Mami da Abban shi suna breakfast , shima zama yayi yace."Good morning my parent."
"Good morning too, how are you."!?
"Am fine Abba, Abba imiss you tooo."
Murmushi Alhaji Mubarak yayi sannan yace."miss you tooo Son, but fatan lafiya naga kwana biyu bamu haduwa sosai."!? Murmushi yayi yace...."Lafiya lau Alhmdulh Abba, wallahi aiki ne yayi man yawa shiyasa bamu cika haduwa ba, yanzun ma sauri nike bansan nayi late."
"Ok Allah ya bada sa'a."
"Amin ya Allah Abba."
Nan suka zauna suka cigaba da yin breakfast, bayan sun gama ci ya tashi, ya tafi wajen aiki, tunda ya tafi wajen aiki, kasa yin aikin yayi so yake ya koma ya ida jin labarin rayuwar Salma, dan ya matsu yaji karshen labarin nata, dan ya lura *Labarina Salma akwai rikitarwa* dan tunda ta fara bashi labarin ya kasa samun idan labarin ya kunsa, amman ai ance waka a bakin mai ita yafi dadi.
Haka ya kama tunanin yana aiki, bayan ya gama cika file, ya gama rubutun shi sannan ya tashi ya tafi gidan Salma.
Parking yayi a parking space din gidan sannan ya gaisa da masu gadi.
Sannan ya shiga cikin gida, wajen Momy ya fara zuwa, kwance take kamar kullun ba uhmm, ba uhm uhmm, kallonta yake ji yayi hawaye nabin kuncin shi, sa hannu yayi ya share, dan sosai take bashi tausayi, ita dai ba mai rai ba kuma ba marar rai ba, kuma kullun idan Doctor yazo cewa yake yi jiki yana samun sauki, shi dai dan karka yayi sabo da yace bai ga wani sauki a jikin Momy ba, yana tsigune gabanta yaji takun takalmin Salma, kallonta yake har ta iso kusa dashi, zaunawa tayi bisa kujera sannan tace."Barrister Sannu da zuwa, ina wuni."!?
Kallonta yayi sosai, dan tayi mashi kyau yau sosai, duk da ba wata kwaliya tayi ba, amman kayan jikinta sun anshe ta sosai, murmushi yayi yace."lafiya lau Salma, ya jikin Momy."!?
Numfasawa tayi gami ga maida kallonta wajen Momy a sanyaye tace."To jiki Alhmdulh, ga shi nan dai."
"Masha Allah,Allah ya karo sauki, Doctor yazo kenan."!?
"Eh yazo dazun, ya yi mata allurai, sannan kuma ya sake duba ta, ya kuma ce man jiki ana samun cigaba."
Shiru yayi na wani dan lokaci, sannan yace."niko ta fara yin wani moving ne."!? Cikin da kiya dan bata son tana yawan kuka gabanshi, cewa tayi...... "Nidai ban gani ba, dan har yanzun bata bude ido ba, balle ta daga hannu, yanda ka ganta haka, haka take, ni abun har tsoro ma yake bani Barrister."tashi yayi yana kama hannunta yana murzawa a natse yake mata maganar yanda hankalinta zai kwanta yace...."Karki damu, kedai ki cigaba da yi mata addu'a, insha Allah zata samu sauki, karki manta ko wace cuta da maganinta, insha Allah sai Momy ta samu lafiya."
"Allah Amin, bari na kawo maka abincinka, yanzun na sauke shi daman."
"Ok, amman kin san dai ba da yawa zanci ba dai ko."!?
"Yes of course, let me go.".... "Uhmmm."
Bayan ta kawo mashi abinci, itama ta samu black tea ta tasha, tashi tayi ta kama Momy taje tayi mata wanka ta shirya ta, tayi mata komai ba, sannan ta kwantar da ita, kiss tayi mata a goshi sannan tace."Allah ya baki lafiya Momy,Allah kuma ya baiya na mana Basma da Baffah."hawaye ne ta goge, duk abunda take yana tsaye yana kallonta, sai ji tayi yace."Amin ya Allah."
Waigowa tayi tayi mashi smile sannan ta tashi tace "mu koma parlour ko."!?
"Ok."
Tunda suka zauna ta tashi ta kunna masu kallo, Tauraruwa tv ta kunna masu, sannan tace."har ka gama cin abincin."!?
Daga mata kafaWa yayi, gami da gira daya, girgiza kai tayi, tana mamaki hali irin na Barrister Salim, yanzun ya bude baki ya bata ansa shine ya gagara sai dai yayi mata singing da kai gami da gira, watarana takan zauna tayi mamakin halin shi, dan yana iya zuwa wuni zungur basu yi magana ba, da ya gama tambayar ta jikin Momy shikenan, sai dai ya kama danna waya yana murmushi ka rasa mai yake yi da waya, tana cikin tunanin taji anyi mata waving da hannunshi sai yace."tunanin mai kike har haka."!?
Cute baby smile tayi sannan tace."bakomai, kawai dai ina tunanin rayuwa ne, ina tsoron randa zaka ce mu tafi mu barmaka gida, bansan inda zani ba, asalima ban taba fita dai dai da kofar gate din gidan nan ba, balle nasan ya garin yobe yake, ta sanadiyarka nazo yobe,amman ai da nisa sosai tsakanin Katsina da yobe."
Murtukewa yayi, sannan yace."daga yau karki kuma yi man irin wannan nonsense maganar understand."!?
"Yes."tace jiki a sanyaye dan ga alamu nan sun nuna yaji haushin maganar da tayi mashi, tashi tayi taje kitchen ta dauko masu ruwa mai sanyi gami da juices din da ta hada mai, yarda cake da dononut duk ta dauko ta zauna kusa dashi, ta marairaice fuska gami da karkatar da kai gefe, tace. "Barrister am so sorry, ba zan sake ba, ga wannan kasha please sai na cigaba da baka labarin nawa."
Yanda ta fara maganar da kuma gamata, sai ya nemi fushin nashi ya rasa, dan tayi mashi kyau sosai, cewa yayi."OK be careful karki kuma."
Hada hannunta tayi waje daya sannan tace."insha Allah."mike mashi juices din tayi itama ta zuba, shi dai ba wani sha yake ba, dan ya kosa ta cigaba da bashi labarin, fahimta da tayi da hakan ajiye cup din hannunta tayi bisa center table din dake gabansu sannan ta cigaba da cewa......
%%%%%%%%%
"Bayan mun dawo da sati d'aya zaune muke a corner nida Basma, shiru mukayi mu duka biyun ba abunda muke tunani sai Momy, dan munsan mun baro ta cikin wani yanayi, matar Baba Mala da shi kanshi Baba Mala din ba dadin zaman muke yi dasu ba, dan tun muna yara muka lura ba san Momy suke ba, balle yanzun da hankali ya fara zama jikinmu, kallon Basma nayi sannan nace."nifa Basma har yanzun hankali ya kasa kwanciya, ina ta tunanin halin da nabar Momy fa."
Kallona tayi sannan tace."wallahi Salma ji nike kamar nayi siliking naje gida naga halin da take ciki, tunda naga Baffah ba yarda yake da abunda muke gaya mashi ba akansu, dan ni gani nike yafi sonsu akan mu, kiji fa abunda yayi maki randa kukayi fada da Dahira, kuma kece keda gaskiya amman Baffah ya rufe ido yana ta yi mana fada at the end har bugunki yayi fa Salma."
Shiru nayi ina tunanin maganar Basma, kallonta nayi nace."Aa Basma kibar yin maganar zakiyi siliking, kinga za'a bada shadows sai ayi tunanin tsoro ne ya saki kikayi siliking, nidai abunda naga yafi shine gobe muje wajen Malam Aliyu mai kudi ya kira mana Momy muji lafiyarta, amman ya kika gani."!?
"Hakan ma yayi, dan ni ban taSa dawowa dai dai sai nayi waya da Momy naji lafiyarta."
Washe gari bayan munje class, anayin breakfast muka wuce wajen Malan Aliyu, muka taibaye shi waya aiko munci sa'a ko gardama bai yi mana ba, ya bamu, number din Momy mukasa, s mukayi darling tana dauka muka ce ta kira mune, bayan ta kira mukayi waya da ita, bayan mun gama gaisawa muka tambaye lafiya, ce mana tayi lafiya lau, komai na tafiya dai dai, ashe boye mana tayi dan kawai ta kwantar mana da hankali muyi karatu, amman ko babu dadi zaman da su Baba Mala, munji dadi da tace tana lafiya haka mukayi sallama da ita muka koma class cikin farinciki,bayan an gama yin lesson muka koma hostel, da yake gobe ake bada shadows ko wace yarinya a G.G. Sandamu jininta ya dawo bisa hakaifa, wanda bata da roba da kofi taje ta saya, idan kasan baka da abunda kasan za'a taSa lafiyar jikinka kaje ka sawo, muda bamu da yaya bamu san ya zamuyi ba, wajen zuwa Wabo ruwa da yi ma kanmu wanki, haka muka shiga cikin damuwa sosai, dan ranar Basma wuni tayi kuka, nice mai bata hakuri, da dare yayi mukaje mono muka ciko da botikanmu dukansu harda su jarkar oki mu sandamu muna cema mata oki, wasu makarantun kuma suna ce nata tasko da 25, har da bokitin fanti babba muke dashi guda uku, muna kiranshi da diram haka muka ciko su muka boye, mukayi hadi da komai abunda mukasan ya dace.
Washe gari munaka tashi da shirin cin ubanmu dan yau ake bada shadows......


*Muje zuw.....=ؤ*


*Yar'mutan kankia ce c'*

Share pls=O


*BANSAN INDA SUKE BA*

_A HALIN YANZUN_

*NA*
*Jameelah Jameey*

*Yar'mutan kankia cec'*

*MANAZARTA*
*WRITERS ASSOC*



*BISSIMILAHIR RAHMANIR RAHIM*


*SURPRISE PAGE, dan naji dadin comment dinku yasa na baku two page yau=d'*

*Chapter ten and elevent<9*


Tunda asuba, muka tashi muka shiga wanka, bayan mun fito daga wanka muka shirya komai da ake bukata muka tafi massalaci, bayan mun dawo daga massalaci muka dawo hostel, abinci muka ci sannan muka wuto class.
Duk zaune muke a class din munyi jigun dan, mu yau munsan rana ce ta cin ubanmu, kallon Basma nayi nace mata."Basma yanzun idan muka samu muka koma hostel, kafin ayi ringing din siester, mu samu muyi wankinmu ko."!?
Kallona tayi kawai ta cigaba da yin note dinta, har na fidda rai da zata yi man magana naji tace."to Salma ya zamuyi? Dole musan yanda zamuyi muyi wanki, dan idan muka biye kazamai zamu zama tunda ba yaiyai ne damu ba."
Yanda ta ban ansar yasa nagane yau bata jin yin magana, shiyasa nima na kyaleta, na dako litafina na fara karatu, muna zaune aka yin ringing din assembly, nan duk muka tashi jiki a sake muka tafi hold, layi muka shiga, nan S.S.1 suka hau step suka fara wakokin habaici, S.S.3 na tayasu, sudai S.S.2 tunda suka shigo basu kula su ba, sun dai san yau ranarsu ce, tunda yau za'a basu shadows, sune cikin haka malamai suka shigo nan kowace yarinya ta kama kanta, bayan sungama prayers da su national anthem, nan principle ta fara bayani, bayan ta gama ta fara kiran our's news shadow prefer dinta, bayan tagama kuma aka rufe assembly da national plage sannna ko wace ta tafi class jiki duk sake.
Bayan angama yin lesson, aka buga breakfast, da gudu mu juniors muka dauki hanyar kitchen, da bulali kawai suke buganmu, su kuma bayin Allah S.S. one kusan rabin prefer din sun tare su, sun sasu crooning haka suke je kitchen, rage tsawon mu muka yi nan, suka fara round suna duba masu cups wanda basu da cups kuwa ranar sun sha bugu abun tausayi su, sai da suka gama bugunmu sannan aka bamu fanke da tea da yake ranar Wednesday ake bada shadow mu a sandamu, kuma ranar fanke da tea ake yi mana, idan kika anshi breakfast dinki, da gudu zaki koma class bayan mun gama ci, muna zaune nan new prefer din sukai ta round suna sa ayi masu Noise, cikin dan lokaci kadan makaranta tayi shiru, baka jin motsin komai balle kuma kaji shiru, malamai ne kawai suke yawo a area classes,haka har lokacin tashi yayi alwallah mukayi muka shiga mosque bayan mun fito muka wuto hostel, Allah ya somu har muka shigo ba atare mu haya ba, kafin a buga siexter munyi wankin mu mun sa check dinmu, nan muka kwanta bisa gado robobinmu rike a hannun, Basma tsoro ya sata ta kasa daukar hadi, niko na sauko da kaina nayi mana hadi, ina gama yin hadin nan aka buga kitchen nan muka fito da gudu, dan ba mai so a tare shi, bayan mun shiga line, suka sake maidamu hostel, haka dai mukaita zuwa da dawowa har suka hakura suka kyalemu, bayan an bamu abinci muka wuce hold, muka shiga layi, cikin dubara muka samu muka sa ma abincinmu hadi,da yake basu da lokacin mu, suna can suna bugun S.S1,shiyasa.
Haka rayuwa ta cigaba da tafiya, rayuwa tayi mana kunci, wahalar yau daban ta gobe daban, kullun haka muke fama bamu black Friday bamu general cleaning, wata rana muna zaune a corner, wata senior ta shigo ta tafi damu mono dan mu dauko mata ruwa, da yake Basma ta gaji sosai, muna cikin tafiya ta fadi ruwan ya zube kasa, nan wannan matar ta fara wanka mata mari, ni kuma ji nayi ban iya jurewa, da gudu na rike wannan senior tamu ina kuka ina ce mata."dan Allah Yaya ki yi hakuri kibar bugunta wallahi ba ta lafiya shiyasa."
Ji nayi nima ta wanke ni da mari, nan ta hadamu mu duka biyun taita bugu, tashi nayi na kama hannun Basma ina ce mata."Basma tashi muje mu gaya ma Vice."
Ban damu da bugun da take mana ba, haka mu katafi admin, nan muka gaya ma Vice, yasa aka kirata mu kuma yace mu tafi hostel duk wanda ta kira mu muce mata shi yace bamu zuwa, haka ko akayi, bayan mun koma corner na fara ba Basma hakuri dan Basma tasha bugu hannun wannan matar.
Yau ta kama ranar visiting, da wuri Momy tazo mana visiting tana san daga nan ta wuto safana, wajen wani biki a safana, bayan mun gama gaisawa kallonta kawai mukayi muka san tana cikin damuwa, kasa daurewa nayi sai da nace mata."Momynmu dan Allah mike damunki."!? A maraice na ida mata maganar ina kama hannunta,murmushi tayi sannan tace."Salma mai kika gani."!?
Ce mata nayi."wallahi Momy duk ki ramai sosai, dan Allah ki gaya mana, har yanzun baki jin dadin zama dasu Dahira ko."!?
Kallona tayi sannan tace."na gaya maki haka Salma? Sannan kuma muna zaman mu lafiya dasu, kawai dai kece kika ga na ramai, amman ba wata rama da nayi."
Duk maganar da muke yi Basma najinmu, sai yanzun tace."Momy ko baki fadi ba kina cikin damuwa, kuma munsan zaki gaya mana damuwar ki koda bamu tambayeki ba, kuma Momy idan har yanzun su Baba Mala suna maki wani abu, ki gaya mana Momy."
Kallon Basma Momy tayi sannan tace."ba nace maku ba abunda ke damuna ba? Ko sai na gaya maku abunda ba dai dai ba."!?
Girgiza mata kai mukayi a tare, ta lura dai ba yarda muka yi ba, ba abunda ke damunta murmushi tayi sannan tace."kunga yanzun a kwana a tashi ba wuya wajen Allah har kun shiga J.S3,j.s.c.e zakuyi yanzun, to ku fidda duk wata damuwa a zuciyarku, ku maida hankalinku wajen karatu, yanzun shine gabanku, kuma na sake gaya maku ni ba abunda ke damuna, sannan next week insha Allah Baffahnku zai zo ya kawo maku kayan J. S. C. E dinku, dan haka ina mai kara jaijada maku kuyi karatu sosai."
Ce mata mukayi."to Momy insha Allah."
Haka ta dunga janmu da labari har muka saki jikinmu, sai da ta tabbatar da mun yarda ba abunda ke damunta sannan ta tafi, bayan angama yin visiting din muka kwashi kayanmu muka tafi hostel muka jera su, sannan muka tafi massalaci.
"Bayan anyi visiting da sati daya Baffah yazo ya kawo mana kayan j.s.c.e dinmu, ya kuma kara bamu kudi, sannan ya tafi, nan muke gaya mashi sauran sati uku mu dawo gida munyi b.e. c.e. "
"Abubuwa sun faru da yawa masu dadi da mararsa dadi, dan gab da zamu fara yin exams Basma ta tashi da wata rashin lafiya, nike yi mana komai, ga wahalar shadow ga kuma jiyar da nike yi ta Basma, da yake Basma ta sama kanta damuwa sosai, dan tunda taga Momy da visiting take tunanin akwai matsala ta dai i gaya mana ne, nima ina tunanin haka, amman dakewa nafi Basma, idan kuma muka kirata waya ansa Waya ce take bamu lafiyar ta lau."
"Kuma takan ce mana, munyi karatu sosai, dan karatu shine gatan mu."
"Ciwo Basma take yi sosai, dan harta exams ba ita ke yi ma kanta ba, ni ke yi mata, inyi mata sannan kuma nayi tawa."
"Sai da ana saura kwana biyu mu tafi gida Basma ta fara sumun sauki."
"Yau mukeyin final exams, Alhmdulh, muna fitowa ana bude mana gate, nan mukaga Abdul drive yazo daukarmu, da muka tambayeshi ina Baffah, ce mana yayi yana da meeting ne shiyasa bai samu damar zuwa daukarmu ba."
"Duk da bamuji dadi ba, amman dole mukayi hakuri, dan tunda muke Baffah shi yake zuwa daukarmu, amman yau ya turo wani yazo daukarmu bayan ba haka ya saba mana ba."
"Bayan mun dawo gida, wanka mukayi sannan muka tafi part din Baba Mala, dan zuwa gaidasu, tunda muka shiga matarshi ta fara yi mana wani irin kallon, haka dai muka zauna muka fara gaisheta, amman bata ansa ba, sai cewa ma da tayi."to munafukai andawo kenan."!?
Da yake ni ba hakuri ne dani ba, kuma haka kawai mata tace mana munafukai, nima ce mata nayi."mu ba munafukai bane, kuma dai ai nan gidan ubanmu ne, wasu ko taimaka masu akayi ana zaune dasu."
Tashi Baba Mala yayi ya wanka man mari yana cewa."wallahi sai nayi maganinku cikin gidan nan, daga ku har iyayenku, ai sun turo ku dan kuyi man rashin kunya ko? To daga ku har iyayen naku sai nayi maganinku ku tashi ku bani wuri banzaye."
Tashi nayi sannan nace."Baba Mala ka sani baka mari banza ba, tunda bansan abunda nayi ma matarka ba tace mana munafukai, kuma kasani baka isa kayi mana abunda Allah bai kaddara mana shi ba, komai ya samaimu mu munsan daga Allah ne."
Ina gama fadin haka ya fisge hannun Basma muka fito daga part din su, muna komawa muka gaya ma Momy duk abunda ya hadamu da Baba Mala, amman abun mamaki sai Momy ce mana tayi."ba abunda zaiyi maku, ranshi ne ya Saci har ya fadi haka, kuma kema Salma baki da hakuri wallahi, daga yau karki kuskura ke sake yin makamancin haka, ku tashi ku ban wajen, ina zaman zamana zaku jaman."
Kallon Basma nayi itama ta kalle ni, sannan muka tashi muka shiga cikin room dinmu, muna mamakin yanda wannan lamari yake faruwa cikin gidan mu."
"Bayan Baffah ya dawo, ya sawo mana waya, lokacin farkon shigowar IPhone, munyi j.s.c.e ya bamu ita a matsayin gift."
"Da muka so mu gaya mashi abunda Baba Mala, amman sai Momy ta hanamu."
"Ni kuma na guduri sai na gaya mashi, bayan ta shin Momy nan na fara gaya ma Baffah duk abunda ya faru, rashin ya baci sosai yace."daga yau karku kuma kawo man irin wannan nonsense maganar, kuma kun fara hali irin na uwarku ko? Baku san kuga Mala yana zaune gidanan? To kwalelen kwalelenku, nida Mala mutuwa ce zata rabamu, duk gulmar da za'a kitsa maku kuzo ku gaya man akan Mala ba yarda zanyi ba, ku tashi ku bani waje."
"Duk komai ya kulle mana kai, mun kasa gane mai ke faruwa wai a cikin gidan mu, wae shi mai yake shirin faruwa ne? Duk abunda muka gaya ma Baffah bai yarda ba sae dae ma hawanmu da fada da yayi, aiko da matsala sosae.....




*Muje zuwa.... =ؤ*


*Yar'mutan kankia cec'*

Share pls=O

*BANSAN INDA SUKE BA*
_A HALIN YANZUN_

*NA*

*Yar'mutan kankiac'*

*MANAZARTA WRITERS ASSOC*

*BISSIMILAHIR RAHMANIR RAHIM*


*CHAPTER 12&13<9*

"Kallon Basma nayi sannan nace wai Basma mai yake shirin faruwa ne a gidan nan."!?
Ceman tayi."maifa ke shirin faruwa abunda idonki ya gane maki mana shi yake faruwa a cikin gidan nan,ni daman tuni ban yarda da abunda Momy take cewa ba da tazo visiting,tace lafiya lau take zaune da wannan mugayen mutunan Wanda basu san alheri ba ,ina dalili."!? ta ida maganar cikin fushi, dan kuwa Basma bata iya fushi ba.
Kallonta nike sosai,ina mamaki dan ni kwakwalwata ta toshe na Rasa ma mai zance dan na tsorata sosai,duba da yanda Baffah yayi mana abunda bai taba yi mana ba, tunda muke dashi,duk da ni ya bugeni saboda su hakan baisa na dauki abun da mahimmaci ba Kamar yau,ga furuncin da Baba Mala yayi kanmu,kuma mun gaya ma Baffah yace karya muke,kawai tashi nayi nayo alwallah sannan nace ma Basma."shikenan Allah ya shige mana gaba,insha Allah Basma sai dai a ganmu a kyale munfi Karfin duk wani mugu da ikon Allah,tunda muna tare da Allah."
Murmushi Basma tayi dan ga dukan alamu maganata ta sanyata farinciki sosai,ba tace komai ba bayan murmushin da tayi ta tashi itama ta shiga toilet ta dauro alwallah ta kab'bara sallah itama ,nan muka cigaba da yin sallolinmu muna rokan tsarin Allah daga dukan wani mugun mutun da aljan harda muguwar dabba da kuma kwaro,mune bamu gama sallah sai waje 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~n daya na dare sannan muka gama karatun qur'ani mai girma mukayi sannan muka tashi muka kwanta lokacin biyu tayi ,sannan muka rintsa.
Kwantawa mukayi ,Amman ni maganar gaskiya bacci ya kaurace ma idona,dan dana kulle ido ba abunda nike hango wa sai Baba Mala da yake ce mana sai yayi maganinmu daga mu har iyayanmu,tuna sanda suka dawo gidan mu nike yanda Momy tace mana shima Baffahnmu ne Kamar yanda Baffah Hussaini yake Baffahnmu shima Baba Mala Baffahnmu ne,Amman gashi da bakinshi yana cemana sai ya ga bayanmu harda ma Baffahn namu ina cikin tunani na ina juyi na naga Basma ta tashi ta shiga toilet ta fito,kallo na tayi sannan ta kwanta ,haka mukai ta juye juye daga ni har ita har aka kira sallahr asuba,lokaci daya muka tashi a tare kallonta nayi gami da yi mata murmushi,itama murmurshin tayi man,dan Musan ba Wanda yayi bacci kenan cikin mu ,tunda muka tashi sallah ba tare da Momy tazo ta tadamu ba.
Nashiga toilet dan yin alwallah Momy ta shigo kallon Basma tayi kawai ta juya dan tasan itama ba muyi bacci ba kenan,dan da munyi bacci sai tasha fama sosai wajen tadamu yin sallah.
Koda na fito sallah na tada na cigaba da yi,itama Basma tana fitowa ta cigaba da yin sallah muna gama mukayi azkar sannan muka yi wanka muka shiga kitchen dan samun abunda zamu garki a gidan.
Tunda muka shigo kitchen Momy take mana wani kallo nice nayi karfin halin cewa."Momy ina Kwana."!?....ko kallona batayi ba balle na samu arziki ansawa cigaba da yin aikin gabanta tayi, bayan ba haka mukeyi ba idan muka dawo hutu to bata sake yin aikin komai mu zamuyi,Amman yau tun kafin mu shigo Momy har ta kusa gama hada breakfast ,Basma ma cewa tayi."Momynmu ina Kwana"!?....tsaki kawai Momy tayi ta barmana kitchen din ta ficewarta,kallona Basma tayi tace."Salma kinga fa?wata Sabuwa kenan yau Momy bata ansa gaisuwarmu.".ta ida maganar cikin damuwa tsantsa a fuskantar,nima kallonta nayi cikin damuwa nace."Basma banga laifin Momy ba dan bata ansa gaisuwarmu ba,ko kin manta abunda Baffah yace mana jiya?duk da Momy bata parlour nasan taji mu,Kuma Nasan kafin su kwanta jiya sai yayi mata fada sosai,ke Basma ba zan mace fada ba warning kawai zance yayi mata, dan muma ba warning din yayi mana ba kan Mala ba,wanda basu hada komai da Mala ba sai zaman unguwa."!?
"Eh hakane Salma jiya Baffah warning yayi mana,Amman Baffah ya bani mamaki Salma kyau ace yayi bincike kafin ya yanke hukunci Allah sarki Momy,mun ja mata." Ta ida maganar tana hawaye, dan Basma kuka bai yi mata wahala, hawayen nike goge mata ina cewa....."To ya zamuyi Basma kawai idan mun gama aiki mu ba Momy hakuri kuma karmu sake gaya ma Baffah duk abunda ake mana a gidan nan."
"Hakane ko Salma kin kawo shawara mai kyau."
Haka muka kama yin aiki jiki duk a sanyaye,dan da na tuna yanda Momy tayi mana a kitchen sai naji duk banda lafiya dan bani san abunda zai bata rain Momy,bayan mun gama mopping da komai muka sake yin wanka sannan muka fito yin breakfast,haka kowa yayi breakfast fuska a jagule dan koda muka gaida Baffah a daure ya ansa shi ma fushin yake damu ,bayan mun gama breakfast kafin ya tafi muka bashi hakuri,da yake Baffah yana sonmu sosai bai iya fushi damu mai tsawo ,shiyasa ya fe mana sannan yayi mana tsakani da Mala yace karmu sake shiga harkarshi inba haka ba si yasan abunda zaiyi mana,koda zai fita ko kallon inda Momy take baiyi ba ,balle yace mata sai ya dawo har tayi mashi rakiya Kamar yanda muka taso mukaga suna yi,sai mu muka yi mashi rakiya a ranar ,nan muka hadu da Mala a compound yana motsa jiki,daman shi Mala bai zuwa ko ina tun daga cin shi da sha harda sutura ma Baffah yake yi mai,har makka sai da Baffah yakai Mala,sannan ya siya mashi mota,gaidashi mukayi abun mamaki ya ansa sosai harda tsokanarmu a gaban Baffah,shi kuma Baffah dadi yake

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment