Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

matar sa anrasa.

Don mursisi suka'ki, damuwa yasa duk yabi ya zaganye, ga jariri anrasa mai kar'ba ga kuma yayyayye babu mai kulwa dashi.

Ismail ne ya share masa hawaye ya kar'bi jaririn ya bawa matar Amina ta had'a ta shayar dashi tare da yaron ta Muta'ka don itama bata dad'e da haihuwa ba.

Tsakanin su kwana biyu, yayi farin ciki matu'ka sosai gaya, don haka zumuncin su ya'kara 'kaimi.

Malam Ismail bai tsaya nan ba har da KABIR ya kar'ba yaba wa matar sa ta cigaba da kulawa da nata da nasu bata ta'ba nuna banbanci ba sam.

Bayan shekaru shida yara su uku maza sun taso kusan kai d'aya cikin gata da soyayyar iyayen su uku.

Alhaji Bashir ya had'a su kaf ya sasu makaranta boko, na addini kuma ko dama malam Ismail na koyar dasu shida matar sa.

Yarane kyawawa, ana haka umma ta sake haihuwa kamar yadda suke kiran ta, macece aka samu zokaga farin ciki wurin iyayen da kuma yayyin yarinyan, ranan suna yarinya taci suna MARYAM.

MARYAM 'yar gata 'yar gaban goshin wannan ahali, kowa bai son kukan ta.

Shekaru uku da haihuwa MARYAM aka sake haihuwan 'ya mace ita kuma Bilkisu .

Yara sun taso cikin gata da soyayya ga tsantsan tarbiya.

Bayan wasu shekaru Bashir ya kwanta ciwo, hakalin Ismail da yara yayi mugun tashi.

Haka ya kaisa asibiti, haka aka d'au tsahon lokaci ana jinya maimakon sau'ki kullum abin 'karuwa yake.

Kawai sai shima yace ga garin ku nan, Ismail yayi kuka, yayi ba'kin cikin rashin d'an uwan sa.

Kafin ya rasu ya basa amanan yaran sa, kuma ya kar'ba.

Haka Ismail ya cigaba da kulawa da yaran nan bisa gaskiya da amana, kuma komai da zai musu da dukiyan sa yake, bai ta'ba ta'ba nasu ba.

Sai dai yana jujjuya musu, a haka yara har suka girma bayan gama karatun samarin nan uku sai suka fara aiki.

Baba Ismail na cigaba da kulawa musu da dukiyan su, yayi yayi suyi suwanci fir suka'ki waisu basu shi'awa.

Lokacin ne kuma KABIR ya fara soyayya da MARYAM, shima 'kanin ba'a barsa a baya ba ya fara shima yace yana son Bilki.

Mukutar dai bai sami budurwa ba shi.

Baban nasu yaso abin baiso ba saboda surutun mutane.

Amma yara sun kafe, ba don yaso ba aka saka ranan auren su.

Gidan 'kerarre suka tamfatsa a Abuja wuse. Da yake nan dukan su suka sami aiki.

Bayan biki suka tare da matan su.


Shi kuma Mukutar a Abia yake aiki.

MARYAM ta haihu auren su da shekaru biyu, bayan nan ta 'kara haihuwa kuma duka maza.

Rashin haihuwan Bilki na matu'kar damun zukatan su, haka yayi bala'in ta'ba zuciyar miji da matan nan saboda Allah ya jarabesu da masifan son 'ya'ya.

Duk da yaran yayin su babu shamaki a tsaknin su amma suna masifan son na kansu.


Shekaru goma baya MARYAM ta sake haihu wannan Karo mace ta haifa.

Hakan sai da zuciyar Balki ya buga, haka sukai fama da ita suna ta jinyan kusan shekaru biyu.

Koda MARYAM ta gano damuwa 'yar uwan ta sai tabata 'kautan 'yar RAHAMA.

Bilki tayi farin ciki sosai, a lokacin ne aka canzawa mijin ta wurin aiki zuwa Kaduna.

Haka suka d'unguma suka tafi da 'yar su.


RAHAMA ta taso cikin tsanani soyayya da gata, ba'a son damuwa ta haka ma fishin ta.

Bilki na matu'kar 'kaunar RAHAMA kamar ranta.

Allah bai basu haihuwa ba sai da RAHAMA takai shekara goma shara biyar.

Zoka ga farin ciki wurin su, RAHAMA ma ba'a barta a baya ba murna take sosai za'a mata 'kani.

Komai taci ta rage ko ta samo sai tace" momy gashi kibawa 'kanina".

RAHAMA har tafi su son cikin nan.

Bayan wata tara Bilki ta haihu, ta haifi santalelen d'anta Auwal.

Tunda ta haifi Auwal ta kama ciwo, Auwal bai shekara ba ta rasu.


Batun zaiyana muku irin ba'kin cikin da wad'an ahali subakyi 'bata bakine.

Mutum ya ta'ba zuka tansu sosai, bayan wata biyar aka 'kara musu jarabawa da mutuwan mijin Balki AL'kasim.

Sunyi shekaru da yawa kafin ciwon nan ya warke a zukatan su.

Amma na RAHAMA shine 'kila ajalin ta, don itama kawai za'ace akaima wa mutuwa.

Wannan dalilin ne Auwal ya zamo d'anga tan kowa.

Musamman mutane biyun nan RAHAMA, mami.


Saboda soyayyar da RAHAMA kema Auwal yasa da takai minzalin aure ta'kiyi saboda bata son a rabata da Auwal.

Sai da 'kar tayi sai da Wanda zata aura ya yadda da zaman gidan su tukuna.


Wannan shine ta'kaitaccen tarihin su.




Comments & share plsπŸ™πŸ»
[11/5, 9:54 PM] Safeeya Aliyu: 🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳

*'KAUYEN 'YAR KADDE*

🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳




*Story & written by: Safiyya Aliyu Wakili*



*πŸ’«DA BAZAR MU WRITER'S ASSπŸ’«*


*we are here to make you happy, smile, educate and realized that we are best among all.........DA BAZAR MU MUKE TUN'KAHO*



*Wallahi kuna matu'kar bani haushi, mutum baiji wahalan muku typing ba. Amma ku kuna jin 'kashin kuma mutum comments. Sai mutum bai ba a isheshi da tambaya, to billahillazi nagaji, idan baku so babu dole kusanar dani sai na aje kawai ba nai ta ti'kin banza ba🀨. Inga gyara daga wanna idan ba haka ba na aje, kuma wanna ma badon ku nayi ba, saboda masu mun comments nayi, idan baku gyara ba ina iya bari kuma ko kin tambaya idan kikaji shiru bazan ko kalle kiba bare kisa ran ansa😏 kuyi ha'kuri idan maganana ya 'bata muku rai gaskiya ta na fad'aπŸ™πŸ»πŸ™πŸ»πŸ™πŸ»πŸ™πŸ»*





*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*




πŸ…Ώ3⃣9βƒ£βž‘4⃣0⃣



*******


Joy kuwa rayuwa tama ta zafi, kullum cikin tunani take, duk tabi ta rame, ta zama kurman 'karfi da yaji. Dama abinka ga miskila, abin sai ya'karu fiye da da. Kuka ya zama shine abincin ta, shine kullum dare rana. Anyi lallashi har angaji an barta, domin kamar 'kara zuga ta suke. Magana daga eh sai a'a idan ta gada ma taso, idan bata soba to sai dai d'aga kai ko ta girgiza maka, ko tayi kamar ba da ita kake ba. Makaranta ma barin zuwa tayi maman tayi tayi ta'ki zuwa Aisha tayi amma a banza. Jarabawa haka suna kallo ta'ki zuwa ta'kari sa. babban takaicin ta na'kin kula kowa da'kin zuwa makaranta shine saboda har kwana biyu da barin sa bai kira taba har wayar ta mace saboda rashin charge. Da wanna dalilin yasa kowa haushi yake bata, wayar ma ajeshi gefe tayi don tace bai da anfani.


Rayuwa tayi mata wani iri bata jin dad'in shi sam, kullum addu'a take ubangiji dawo mata dashi lafia.



Haka aka d'au kusan sati, wata, shiru babu Auwal. Wanda a wanna lokacin ne sukayi hutu kuma har sun dawo, amma Joy ta'ki makaranta fir.


Koda yaushe bata da aiki sai tunanin da kuka, har tsawon wata hud'u.


Maman ta fara nema mata taimako daga wurin 'yan uwan ta arna, shine aka fara samun sau'ki, don alhamdulillah yanzu tabar kuka, tunani ma ta rage sosai.



Makarantan dai ta'ki, ganin sau'ki na samuwa yasa basu matsa mata ba.



Rashin 'kin makarantan Joy ba 'karamin ba'kin ciki Aisha tayi ba.


Don Aisha ita kad'ai ke tafiya makaranta haka ma dawo wa.

Lokaci na ta tafiya, yanzu haka Aisha na SS2.


Joy na gida har yanzu, ganin yanzu ta kwantar da hankalin ta, yasa Aisha tazo har gida taro'ke ta har da kuka akan ta koma makaranta shine fa ta amince zata koma.



Tako koma d'in amma JS3 ta koma, ta mai da hankali sosai tana karatun.



Lokacin jarabawa nayi ta zana, koda sakamako ya fito sunyi farin ciki sosai.


Daga nan ta fara cuku cukun neman cigaba, ta kuma samu ta fara SS1 d'in ta cikin kwanciyan hankali.

Lokacin Aisha na SS3.

Karatu suke ba wasa don sun mai da hankali sosai.



Kada kuyi tsammanin cewa wai joy ta shafe babin Auwal a zuciyan ta.



Ko d'aya yana nan daram, kuma kullum bata cire rai da cewa zai dawo gare taba watarana.



Kuma kusan kullum sai tashiga gidan nasa, watarana ma a can take wanka da dai sauran su. Mama bata ta'ba hanata ba, don tasan zafin so, don shine silan rabuwan ta da iyayen ta.



Gidan na matu'kar d'ebe mata kewan shi sosai, yana rage mata wani abu.



Haka take tafiyar da rauywan ta cikin tsananin begen doctor d'in ta.


Amma dai-dai da rana d'aya bata ta'ba nuna ko a fuska tana damuwa dashi ba.


Nunawa take tama manta dashi, hakan ya faranta ran bestyn ta da maman ta.




Anzo anfara registration na waec da neco, sai Aisha tace ma baban ta ya biya musu, ya ansa akan zai biya, saboda haka da murna tazo gidan su Joy ta sanar mata.



Tace" besty an fara registration fah" shiru ta mata kamar ba da ita take ba.



Ta sake cewa" haba besty ina magana kina banza dani kamar ba dake nake ba" tare da ta'ba ta.





'Dago dara daran idanun ta tayi ta kalle ta ba tare da tayi magana ba.

Aisha ba tai zuciya ba ta sake cewa" besty an fara registration na waec da neco, nama baba magana akan ya biya mana don banson na barki a baya".



Ta tsaya tana kallon ta tare da jiran abinda zata ce.



Murmushi gefen baki tayi tare da cewa" ban bu'katan haka gaskiya, na fison nayi karatuna a tsari, banso wuce ba".


Daga haka tai shiru tare da kauda kanta, juyo da fuskan nata Aisha tayi tare da cewa cikin 'bata fuska" meye nufin ki wai?" shiru ta mata, tace" nufin ki na samu baba nace masa me bayan yace yau zaije ya biya? da yake tun jiya nayi magana".



"Bazan yiba nace miki" kuka ta fashe dashi tare da cewa" shikenan tun da ke ba'a iya miki sai abinda kike so shikike so kikeyi " .


Daga haka ta mi'ke ta fara tafiya da ninyan barin gidan.



Sai da takai 'kofa sai taga bata kyau ta mata ba, don haka tace" kiyi ha'kuri na amince".


Waigo wa tayi cikin tsantsan farin ciki tana kallon ta amma kamar ba ita tai maganan ba.


Fuska d'aure kuma kullum haka yake.


Dawo wa tayi da murna ta rungume ta.


*****


Lokaci nayi suka zana jarabawan su cikin nasara da kwanciyan hankali.


Alhamdulillah sunyi nasara don certificate yayi kyau sosai.


Daga nan sai aka fara shirin jam.


Shima sunci don haka suka samu gurbin karatu a jami'an nasarawa.


Kowa fanni da ta za'ba aka bata, Aisha low, Joy fanin habibin ta ta za'ba.


Karatu suke cikin kwanciyan hankali, a lokacin duk kannin halitan cigakkun mata sun bayyana a tare dash, ko dama can Joy ba bata ba tana da komai.


Kyawawan 'yan matane ajin 'farko, Joy dai farace kamar yadda kuka sani siririya doguwa, mai yalwataccen gashin kai. Ga bakin ta madai daita, masu d'aukan hankali. Ga fararen idanu.


Akwai diri mai d'aukan hankali, komai nata ya 'kara cika da fitowa, ba shakka Joy had'ad'd'iyar budurwace mai kimanin shekaru 20.


Kyawun ta mai d'aukan hankali ne, don a halin yanzu samari sun fara zarya ba kuma 'kananun mutane ba, a'a irin 'ya'yan manyan mutanen nan.


Bata sauraron su ko kad'an. Aisha ma babu laifi tana da nata kyau d'in dai-dai ita. Itama tana da samarin amma ba irin na Joy ba.


Kuma itama bata kula su karatun su kawai suke .


Da taimakon baban su Aisha suke karatun su cikin rufun asiri, yana matu'kar 'ko'karin ganin basu rasa komai ba na bu'kata.

Dai-dai na talaka.



°°°°°°°°°°°°


Lokaci ba 'karya bane, don a yanzu haka Joy ta gama karatun ta, Aisha ta riga ta gama wa tunda course d'in su ba d'aya bane. Aisha tayi service har ta gama, saura Joy. kuma dai-dai da sarannan Aisha ita da wani d'an mai kud'i.


Bata so haka ba amma bata da yadda ta iya saboda nacin wanna d'in da kuma mahaifin ta, don yace tunda angama karatu sai aure kuma.


Wata d'aya kacal aka sa, taso Joy ta tsai da wani a cikin maneman ta idan yaso a had'a ayi tare amma fir ta'ki.


Don da ta matsama tunda takama kuka sai da takwana uku bata magana da kowa ko abinci ta'kici shiyyasa ta ha'kura.


Shirye-shirye suke ba kama hannun yaro, daga 'bangaren angon har amarya kowa shiri yake.


Biki ya rage saura sati biyu ango yazo musu da albishir d'in ya sai musu gida a cikin gari can G R A keffi, iyayen Aisha sunyi murna sosai.

Tare wa washe gari don a can za'ai biki.

Kuma gidan yace parts uku ne har da maman Joy, itama tai murna tayi godiya sosai.


Koda Joy ta samu labari fir tace babu inda zata, don bata son Auwal yazo bai same taba..

Don bata cire rai akan cewa zai dawo gare ta ba.


Sai da maman ta ta nuna 'bacin ranta sosai sannan ta yadda suka bar 'kauyen sai faman kuka take.


Gida yayi sosai ba laifi, wani babba bane amma ya burgeni sosai.


Bayan tare wansu da sati aka fara gudanar da biki, tun daga wanna lokacin Aisha ta fara kukan rabuwa da Joy .


Babban tashin hankali ta shine ba a gari zasu zauna ba, don angon d'an abuja ne, can ma yake aiki.


Ana shirin biki Aisha na ciwo, tun tana a tsaye har ta kaima kwanciyan a gadon asibiti.

Tashin hankali sosai wad'an nan a halin suka shiga, likita kuma yace a mata abinda take so, idan ba haka ba komai na iya faruwa.


Don haka iyayen ta suka tambaye ta damuwa ta a gaban angon da kowa nata.


Tana kuka take cewa" so nake Joy ta bini" koda aka tambaye ta ina baki shakku tace abuja.


Iyayen sun ga rashin yuwan haka da dace wan abin.

Amma angon yace babu damuwa da haka Aisha ta warke aka cigaba da shagali, Joy taso 'kin yadda amma ganin halin da 'yar uwan ta take ciki yasa ta amince.



β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’


Rana bata 'karya, wanna haka yake domin yaune aka shaida d'aurin auren Aisha da Abudurrahaman.



Ayi cikin kwanciyan hankali kuma a yau d'ine daga d'aurin aure suka wuce da amarya.



Sai dai muce Allah basu zaman lafia.



-------------------------------



Zaman Joy a Abuja....

Zama ne cikin jin dad'i da walwala, bata da matsalan komai da kowa.

Sai dai tunanin Auwal da take lokaci zuwa lokaci, maganan tafiya service d'in ta na tashi KD suka tura ta, sai ta nuna bata shi'awan can.


Saboda haka sai Abdurrahaman ya mata cuku cuku aka barta a Abuja, don haka bata da matsalan komai.


Don sosai Aisha da mijin take 'ko'karin faran ta mata da sata farin ciki.

Kullum cikin tarairayan ta suke, itama tana 'ko'karin kyauta ta musu, tana bama mijin Aisha girma sosai tamakar wanta ta d'auke shi.


Zaman ta a Abuja ne Aisha tayi mata sha'awan musulunci, nuna mata tayi bata da ra'ayi. Don haka babu wanda ya matsa mata akan hakan.


Joy ta samu kwanciyan hankali don haka ta'kara wani mugun kyau.

Samari ko sai dai bata fita ba, ko kallo basu ishe taba, sabgan gaban ta kawai take, a haka har ta kammala bautan 'kasan ta cikin kwanciyan hankali.


Don haka sai ta fara zancen aiki babu 'bata lokaci Abdurrahaman ya nema mata aiki a wani aisibiti babba ta fara tafiya.


Aisha taso itama ya samun mata, amma yace shi bai da shi'awan iyalen sa da aiki kome take so ta fad'a masa zai mata.

Don haka sai ta bu'kaci jari, bai ko jah ba ya bata ta fara kasuwanci.


Watarana Aisha da mijin ta na zaune ranan weekend ne har Joy na gida, Africa TV3 suke kallo su biyu sai ga Joy ta fito, shirin yara ake a lokacin.


Zama tayi cike da shi'awan yaro d'an 'karami dake karatun al'qur'ani mai girma.

Murmushi kawai take, bata tashi ba har sai da aka cire shirin.


Tun daga wanna ranan shirin nan bai wuce ta. Yawan kallon shirin yasa taji tana matu'kar son musulunci don tana shi'awan itama ta iya karatun al'qur'ani.


Rana tsaka ta samu Aisha har cikin d'akin ta lokacin Abdul bashi ya tafi wurin aiki ita kuma night duty take da.

"Besty har kin tashi?" tace da ita lokacin da take shigowa.

Bata bata ansa ba illah 'karisowa da tayi ta zauna kusa da ita fuskan ta d'auke da murmushi.


Ri'ko hannun ta tayi tare da cewa" Aisha inason na musulunta" daga haka ta tsuke bakin ta.


Waro ido Aisha tayi tare da cewa cikin tsantsan farin ciki" da gaske my besty?" d'aga mata kai tayi.


Don haka Aisha ta rugume ta cikin tsantsan farin ciki, har da hawayen ta.


Babu 'bata lokaci Aisha ta kira mijin ta ta sanar masa, babu 'bata lokaci yace suje wurin limamin anguwan su.


Koda sukaje ba'a wani 'bata lokaci ba ta'kar'bi musulunci.

Aisha ta za'ban mata Suna Fatima, wani irin natsuwa da kwanciyan hankali taji yana wanzuwa a gare ta.

Ga wani irin farin ciki da takeji.


Fatima wanda suke kira da (Zarah) tana d'aukan abuabuwan addinin musulunci da ake koya mata fiye da tunanin ku.



Babu abinda tafiso a ciki rin Qur'ani, don haka ta mai da hankali sosai tana koya, saboda 'kwa'kwa da kuma son abun.


Cikin wata hud'u tayi sauka, zo kaga murna da farin ciki wurin ta da uwan uba Aisha, don haka gaga rumin walima aka shirya mata.

Sai dai abinka da boko da kuma ansaba shigan 'kananun kaya nana sai ma wanda ya 'karu sai dai na d'an d'aura 'karamin mayafi.




***************


Fatima mai farin jinine tun tuni balle ta musulunta don haka abin sai ya 'karu.

Maza da mata kowa nason ta kulasa tayi mu'amala da ita.


A haka ne tayi wata 'kawa a ma'kotan su mai suna Husna, Husna yarinyan nacin masifa. Kad'aci ke damun ta, da yake basu dad'e da tare wa ba. Kuma su biyu ne kawai 'ya'yan gidan daga ita sai wanta, da wannan dalilin yasa take shige-shigen ma'kota. Shine Allah ya had'a ta da Fatima taji ta Shiva ranata, sai ta maida gidan su faty ma kamar nasu tai ta shige mata. tun Fatima na 'kalleta har sai da yazo suka fara 'kawance domin sam bata da zuciya.

Tana zuwa gidan su Zarah sosai, amma ita dai-dai da rana d'aya bata ta'ba shiga gidan nasu ba.



β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’


"Don Allah ki rakani yau mana" cewa Husna suna zaune kan gadon Zarah bayan sun gama cin abinci.

"Kiyi ha'kuri gaskiya babu inda zani" cewar Zarah.

"Haba Zarah kullum nazo miki da bu'katata sai ki 'kimin, bansan mai yasa kike min haka ba. Wallahi ba kyau wula'kanci, har yanzu kin'ki sakin jikin ki dani. Wallahi Faty ina matu'kar 'kaunar ki har cikin raina, keko kin'ki sani a zuciyar ki ko kad'an".


"Meyasa? wallahi hakan bai dace ba".


" Allah baki ha'kuri tunda baki sona baki aminta dani ba nayi nan nagaji haka, kullum ni kenan nan nai ta bibbiyan ki kamar wata sarki to nagaji ba dole 'kawance" tace cikin fushi tare da mi'kewa idon ta cike da hawaye don tana matu'kar 'kaunar Zarah.

Amma ga dukan alamu ita bata son mu'amalan su.


Kamo hannun ta tayi tare da cewa" idan ba zamu dad'eba muje don inason naje wurin aiki 2pm dai-dai".


Dawo wa tayi tare da rungume ta tana maijin farin ciki.

"Ki muje idan ba haka ba na fasa".


" A'a muje hajiya ta mai ajin tsiya sai har dani za'a rin'kama wa?, gidan su hayati zani Maman sa ke nemana kinsan biki ya taso sauran sati uku, zani na kur'bi tsumi, kai matan nan Allah ya samata son d'an nan kamar shikenan mata".


"Bata gajiya sam wurin gyrani yanzu haka sati mai zuwa zamu India a min gyara na musamman, wanna kuma yayar sace ta d'au nauyi".

Ta'ba baki nayi tare da cewa" muje ni kada 'batan lokaci na'ki zuwa kimin kuka".

"Don idan na biye miki takan mutumin da bai San kinayi ba zamu iya kaiwa dare".


" Wallahi ni har mamaki kike bani ace wai macce kamar ke ki mutum ma mutumn da Sam bai ra'ayin ki, wallahi ko shine autan maza sai haka" ta 'karisa tare da sakin tsaki.

"'Karin kayan takaicin bai zuwa sai dai ke kije gidan su ku zanta, anya wannan auren za'a sami kwanciyan hankali kuwa?"

Murmushi mai ciwo Husna tayi tare da cewa" baza ki gane ba yarinya gayen ya had'u, yadda kika san ba mutum ba saboda kyau, ni tunda uwata ta haifeni ban ta'ba ganin kyakkyawan mutum irin saba".


"Oh really?"

"Allah kuwa idan kika gansa zaki ce na gaya miki, don gayen 'karshe ne".


Ta'ba baki tayi tare da girgiza kai ina mama kin ta, sai tace" muje fah kada na 'bata lokaci kije ki fasa rakani".

Fito wa daga cikin d'akin Joy sukayi suka mufi na Aisha kwance take tana duba wani littafin.

Sallaman su yasa ta kauda fuska daga littafin tare da zuba musu ido tana mai ansa musu sallaman.

Tashi tayi daga kwancen tana mai cewa" sai ina kuma 'yan mata?"

Husna tace" anty Aisha zata rakani wuse ne gidan 'kawar momy".


"Hummmm kice dai gidan siri kan mu" murmushi kawai tayi tare da cewa" sai mun dawo".


"Besty baki sallameni ba" cewar Aisha ganin Husna ta jata zasu bar d'akin.

Murmushin ta mai burgewa ta jefe ta dashi tare da cewa" sai mun dawo to" daga haka suka bar d'akin, ita kuma ta bisu da addu'a dawo wa lafia.



A compound d'in gidan suka tsaya Zarah tace" jeki d'ako motar ki ina jiran ki a nan".


Shagwa'be fuskan ta tayi tare da cewa" don Allah my Zarah yau mu fita a sabon motar can ta'ki".



Hararan ta tayi tare da cewa" na'ki" marairai ce mata tayi, ba don taso ba haka tasa aka fito mata da motar suka Shiga.


Tare da barin gidan, bata son hawa motar ne saboda wani saurayin ta mai nacin tsiya ya sayo mata.


Motar babu 'karya ta had'u.



Husna ke driving d'in sai faman santin motar take.




Wani tamfareren gida suka shiga, parking Husna tayi Tare da kallon Zarah tace" Zarahty ya kikaga gidan surukan nawa?" don taga tun daga get d'in gidan take kallo har suka shigo gidan.


Yatsina fuska tayi tare da cewa" gidan yayi".


"Muje to" tace tare da 'ko'karin fita daga cikin motan.


Rufe motar Suka yi tare da shiga ciki, sallama sukayi a bakin 'kofan babban falon gidan, shiru babu ansa.


Don haka suka shiga daga ciki, part d'in mami suka nufa, a nan suka tadda mamin. sallama sukayi ta ansa fuskan ta d'auke da fara'a.


Shiga sukayi har gaban ta suka gaida ta, ta ansa idon ta nakan Zarah da tunda ta gan ta taji wani irin fad'uwan gaba.


Idon ta nakan Zarah tace " Husna 'kawar kice wannan?"


"Eh mami" tana murmushi tare da kallon Zarah taga kanta a 'kasa kamar wata muna fuka.


Mami tace" sannu ko" take ce da Zarah.

Ansawa tayi sai mamin tace" tashi ku zauna a cushion mana, nasha gaya miki Husna kibar irin haka bakiji".


Tashi sukayi Husna na murmushi tace" Allah huci zuciyar mamin mu baza mu'kara ba".


"Allah sa, ya momyn naki?"

"Tana nan lafia qlau, tace a gai daki".


" Masha Allah, bari a kawo muku abinci" .

"Mami mun 'koshi" mamin tace tana hararan ta" dama nace baki 'koshi bane? kullum dama ke a 'koshe kike zuwa gidan iyayen naki".


"To yau sai kinci" tace tana 'ko'karin mi'kewa. Cikin murya mai dad'in amo da sauraro cike da natsuwa Zarah tace" mun 'koshi mami, don abinci muka gamaci muka fito".


Gaban mami ne ya sake fad'i dajin wannan muryan, tsayawa tayi cak tare da waigo wa tana kallon gefen da Zarahn take.

Had'a ido sukayi still fad'uwan gaba ne, murmushin ya'ke mami ta sakin mata tare gyara zama.

"Husna amma 'kawar nan naki ba 'yar nan bace ko?"

Murmushi Husna tayi tare da cewa" 'yar nasarawa ce, amma tana zaune a ne a garin nan".

"Oh sannu" tace da Zarah.

Ansawa tayi dai-dai nan RAHAMA ta shigo Auwal a bayan ta da sallama d'auke a bakin su.

Amma na RAHAMA ne ya fito, na Auwal kuwa sai idan ka kalli bakin sane zaka gane yayi sallama.

'Karisowa inda su mamin ke zaune tayi, shiko dodon mutane tsayawa yayi daga bakin 'kofar shigowa yana mai cewa" mami mun dawo zan tafi office sai na dawo" daga haka ya juya.

RAHAMA ko zama tayi tare da cewa" wassh mami nagaji walla............" bata samu zarafin 'karisawa ba sakamakon fuskan Zarah da tagani.

Idon ta da 'kwallan da ya taru cikin sakonni tace" mami kina ganin abinda nake ganin kuwa?"

Mami tasan me take magana akai amma tayi mata shiru.

Taso wa tayi tazo ta dur'kusa kusa da mami tare da kamo hannun ta tana mata nuni da Zarah tace" mami anty ce fah nake ganin, sai dai kuma jikin ta ya nuna na yara ne, dama idan ka mutu ka dawo yaro kake koma wa?"

Shirun mami yasa tace lokacin hawaye ya fara zuba" mami anty ce ko?... Itace ta dawo gare muko? dama ina mafarkin ta mami bata mutum ba, kullum haka take gaya min a mafarki, tana cemin zata dawo. Zata dawo ta rayu da Auwal d'in ta ".


" Mami taso, taso" tace tana janta, fizge hannun

2 Comments On KAUYEN YAR KADDE
avatar
abdulrazak

1 year ago

Reply

Next pls

avatar
abdulrazak

1 year ago

Reply

Next pls

Please Login or Register in order to submit comment