Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kawai sai hango motocin gidan su yayi guda biyu suna taho wa.

Farin cikin ganin 'yan gida da fargaba suka taru suka diran masa a lokaci d'aya.

Mi'kewa yayi daga farin kujeran da yake zaune, dai-dai nan sukai parking, nufar motan sister d'in sa yayi.

Da farin ciki ya bud'e 'kofar motan, ita ce hakin CE a bayan motan sai Akaram.

Ko bari ta fito baiyi ba yace "oyoyo sis, oyoyo my son".

Harara ta maka masa, tare da cewa " shiga mota muje" d'aure fuska yayi tare da cewa "kai Anty wani irin in shiga mota daga zuwan ki?".

" Auwal ban wasa da kai nace ka shiga mota mu tafi" bud'e d'ayan motan da akayi ne yasa shi waiga wa.

Ba kowa bane illah Dady da kan sa, sai yaya wato Wanda ya kawo sa.


Ga farin ciki ga far gaba, amma hakan ya matse yayi musu barka da zuwa.

"Son mai kake a garin nan bayan ka gama abinda ya kawo ka?" cewan Dady ba tare da ya ansa sanu da zuwan da yake masa ba.

Shiru shima Auwal yayi, ganin zai 'bata lokaci yasa Dady yace "shiga muje" rasa yadda zaiyi yayi tunda Dady da Kansa yace haka.

Kamar zai kuka yace "Dady kuje kawai gobe zan.........." bai 'Kari saba sakamakon wani matsiya cin harara da Dady yayi masa.

Bai dan dara ba yace "Dady bari na had'a kaya sai muje".


" Bama wani ka wuce muje" "akwai takadduna fa a cikin gidan".


" Jeka maza rakasa" yace da yayan nasa, bai so hakan ba amma haka yayi gaba yayan yabi bayan sa zuwa cikin gidan.

Tarka ta takkdun yayi kaf tare da abubuwan sa masu mahimmanci suka fito, amma kafin su fito ya faki idon yayan ya rubuta leta ya aje a kan kujera d'aki .



Suna fito wa saka kayan a bot d'in motan yayi tare da kallon gidan yana mai jin wani iri a cikin ransa, gashi Joy suna makaranta yau bai san yadda 'yar rigiman sa zatai ba.

"Dady bari na bawa gidan nan key d'in nazo".


" Ga wani can bashi ya kai musu kana 'bata min lokaci " waiga inda dadyn yai nunin yayi.


Aiko ganin Muhusin ne yasamu kwanciya hankali.


Matsawa kusa dashi yayi tare da cewa cikin 'kasa da murya yana mai tura masa abu a aljihu "'kani na, don Allah ga wannan wayan da kye d'in nan Joy na dawo wa kaba ta, kace nace don Allah tayi ha'kuri zan zo bayan kwana biyu".

" To yaya insha Allah zan gaya mata, yauwa 'kanina nagode" yace tare da juyawa wurin motan .




Shigan sa keda wuya suka bar wurin....................
.





To fah, wata sabuwa inji 'yan caca🤨😅






Comment & share pls
[11/5, 9:53 PM] Safeeya Aliyu: 🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳

*'KAUYEN 'YAR KADDE*

🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳




*Story & written by: Safiyya Aliyu Wakili*


*💫DA BAZAR MU WRITER'S ASS💫*


*We are here to make you happy, smile, educate and realized that we are best among all........ DA BAZAR MU MUKE TUN'KAHO*



*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*



🅿3⃣5⃣➡3⃣6⃣

Tun shad'aya suka gama jarabawan su, tafe suke suna d'an fira har suka zo inda Auwal ya saba zama don jiran su, don basu ta'ba jiran saba kullum shike jiran su.

"Abin mamaki Aisha yau my heart bai zo da wuri ba" cewan Joy tana mai kafe wurin da ya saba parking da ido.

Aisha tace" Allah sa dai lafia, amin" nace ina maijin fad'uwan gaba na ya'karu fiye da yadda nakeji tun da na tashi a yau.

"Mu zauna daga nan mu jira shi besty" ba tare da nace komai ba na bita muka zauna a wata gindin bishiya.

Shiru muke zaune amma idanuna na hanya, muna zaune har na tsahon wasu lokaci babu doctor babu labarin sa.

Mune har 2:00pm babu shi, a lokacin kuwa zo kuga idanuwa na, idanuwa na fal da 'kwalla, gabana sai faman bugawa yake.

Nayi zurfi cikin tunani mai ya hanasa zuwa d'aukan mu, fatana dai ace yana cikin 'koshin lafia idan ba haka ba akwai matsala babba ma.

"Tashi mu tafi besty kinga rana tayi da uban yunwan da nakeji" cewar Aisha tare da mi'kewa tana kamo hannu na.

Dojewa nayi na'ki tashi, kallo na tayi tare da cewa cikin marai rai cewa "please ki tashi nasan wani babban uzuri ne ya tsayar dashi, don haka mu tafi kawai".

Gamsuwa da zancen ta nayi don haka sai na mi'ke, tare goyin mukayi muka nufo hanyan 'kauyen mu.

Tafiya muke amma gaba na na cigaba da fad'uwa, 'karuwan fad'uwan gaba na shine sanda muka zo muka cimma babu motan Auwal a inda ya saba ajeta, don sam bai zuwa da ita ko'ina da ya wuce kaimu makaranta.

Sai wasu lokutan da idan bai da wani abun anfani sai yaje cikin gari ya siyo. Kuma bai tafiya sam ba tare da ya sanar dani ba.

Barin Aisha nayi da sallaman mai mashin ni kuma na nufi 'kofar gidan sa, duk da na gansa a rufe.

Bubbuga gidan na farayi kamar mara kai, zuwa Aisha tayi tajani ina turjewa don jiki na ya bani ba lafia ba.

Da 'kar ta jani cikin gidan mu, mama ce zaune a tsakar gidan da alamu dai shan iska take, don zaune take da 'yar single a jiki ta sai faman fifita take.

Ko inda take ban kalla ba nayi hanyan d'aki, Aisha ce ta gaida ita tare da fita a gidan.

Ina shiga d'aki nayi wurgi da jakan makarantan, za gaye d'aki na farayi.

A haka mama ta shigo ta cimmini, kallo na tayi tare da cewa" lafia kuwa Joy? " kallon ta nayi tare da kauda kaina.

Gajiya da zaga d'akin nayi don haka na fad'a kan katifa tare da cewa" wayyo" da 'karfin gaske hawaye kuma suka fara ambaliya akan kyakkyawan fuska ta.

Da sauri mama tazo inda bake tare da d'ago ni tace" what happened Joy ".

" Mama ina doctor yaje yau bai gaya min ba?" Nace ba tare da naba ta ansan tambayan ta ba.

Wani irin kallo na tayi tare da cewa" lallai doctor nada aiki tunda zai auri matar da bazai ta'ba fita ba sai da sanin ta da kuma izinin ta" ta had'a da tsaki tare da tashi tabar d'akin.

Eyhu na sake saki ina cewa " wayyo doctor na ina kashiga ne zuciya ta zata fashe?" tare da rushewa da kuka.

Ranan babu zancen abinci, to yaya zakaci abinci ma bakaji yunwa ba? Toni ranan nama manta da wani abinci sam.


6:15pm Muhusin ya shigo gidan mu da uniform d'in islamiya a jikin sa.


Gai da mama yayi tare da cewa bayan ta ansa "Anty Joy na nan?"

"Eh tana nan shiga ciki" tace dashi, hanya d'akin yayi.


Ina kwance da uniform d'ina kuma har lokacin kuka nake ya shigo, naji motsi ban damu da sanin ko waye ba shiyasa ban waigo ba.


Ji nayi ance "Anty gashi inji yaya farin nan na kusa da gidan mu" ai da sauri na waigo hard murmushi na.

Nace ina kallon hannu sa "yana ina?" mi'ka min kye yayi tare da cewa" ya tafi gashi harda wayan nan yace na baki" yace yana bud'e jakan islamiyan tasa.

Gaba na ya fad'i na kalle sa tare da cewa" ina ya tafi?" Ina jujjuya kye d'in hannu na hawaye naji ya fara zubowa a fuska ta.

"Ban sani ba, wasu ne dai 'yan birni suka zo a motoci da yawa ya shiga suka tafi" .

Yace tare da mi'kamin wayar doctor, kar'ba nayi shi kuma ya fita.

Bin wayar nayi da ido ina jujjuya shi har na tsahon wasu lokuta.

Dana wayar nayi ta kawo haske, photo nane ya bai yana a fuskan wayan, ban san sanda akai photo ba amma yayi matu'kar kyau.

Tashi nayi da kye a hannu na nayi fito daga d'aki, nufan hanya fita nayi mama na kallo na batace dani komai ba.

Gidan nashi naje na bud'e, shiga nayi har ciki.

Tun daga yanyin yadda falon yake naji wani iri tsoro da fargaba.

Shiga bedroom d'in sa nayi, kaya ne na gansa a hargitse, kuka na saki tare da d'aura hannu aka.

"Wayyo doctor na, wayyo! Wayyo mai yasa zaka min haka?, mai yasa zaka tafi ka barni?"

"Baka min adalci ba" nace tare da fad'a wa katifan sa ina mai cigaba da kuka na.


Haka na kasance a gidan nan har dare kuma baci basha sai kuka kawai. Bani na bar gidan nan ba sai 9:00pm.

Koda na shiga gida banyi takan mama ba na kwanta kawai ina mai cigaba da kuka na.

Da fitana mama ta biyo bayana, ganin inda na shiga yasa tai zargin wani abu.

Gidan su Aisha ta shiga bayan na shige gidan doctor, bayan sun gaisa da maman Aisha sai ta nemi Muhusin, tambayan sa tayi yayi mata bayani ita kuma tabar gidan.

Shiyasa bata ko nemeni ba, ganin kukan ya'kici ya'ki 'karewa yasa ta matso cikin tausayawa ta kamoni tare da lallashi na.

Ta d'au lokaci mai tsayi tana lallashina, da'kar na dai na kuka.

Baccin ranan ban samu yin saba sam.




°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°


Auwal lafia suka kai gida, baiyi magana da kowa ba har da mami. Fushi sosai yake da kowa na gidan.

Duk wani gata da tarairaya da mami da uwar gayan suke sam bai burgesa, bai sa ya saki jiki ba.

Abinci sai anyi da gaske yake ci, kullum yana cikin d'aki, bashi da abinso dake saka shi nishad'i da jin dad'i wanda in har yana cikin yanayin zaka ga yana dariya ko murmushi, shine tunani masoyiyan sa.

Hakan da ya mai da kansa yasa damuwa mai tsanani a zukatan iyayen sa da 'yan uwan sa, musamman mami da Anty RAHAMA.

A haka har akai sati biyu, a sati biyun nan ko yayi muguwan rama kai kace wanda yayi ciwon shekara.

Kuma a yaune yasha alwashin koma wa 'KAUYEN 'YAR KADDE tun da nanne farin ciki sa yake.

Shirya wansa yayi ba tare da ya sanarwa kowa na gidan ba.

Bayan ya gama shirya kansa cikin 'kananun kaya wando na'ki da jan riga mai rane jah da fari sai wani zane na 'baki kad'an wanda yayi matu'kar 'karawa rigan kyau.


Kayan sun matu'kar kar'ba sa.


Fita yayi daga d'akin sa yayo main palon gidan. Da yake yau Saturday ne kowa na gida, zaune ya gansu duka, mami, RAHAMA, Dady har da yayyun sa maza.

Gai dasu duka yayi a cikin ciki ba tare da ya kallesu ba, ansawa duka sukayi idon su na kansa.

Sunji dad'in adon da yayi a tunani su ya kwantar da hankalin sane basu san ko kad'an ba hakan bane, domin kwanciya hankali sa shine yayi arab da za'bin ransa.

Gani sukayi ya nufi hanya barin palon, duk cikin su sun kasa masa magana.

RAHAMA ne kamar mai tsoro ta kira sunan sa, tsayawa yayi ba tare da ya juyo ba.

Tashi tayi tare da zuwa inda yake.

Dafa kafad'an sa tayi tare da cewa" ina zakaje habibi?" Banza da ita yayi tare da zare hannu ta daga kafad'an sa ya bar wurin.

Wurin ajiye motocin gidan ya nufa, 'barayin da motocin sa suke ya nufa.


Rufe suke ruf d'aga wa yayi d'aya bayan d'aya, gani yayi duka sunyi kura.

Cike da masifa yake 'kwala ma mai wankin motocin kira.

Da gudu ya nufo sa, ma'kaitan kaf sunji kiran nan har 'kwa'kwalwan su.

Hatta su mami sai da suka fito suga dalilin uban wannan kiran.

Abinda bai ta'bayi ba fuska babu walwala yana zuwa ya dur'kusa tare da cewa" gani yalla'bai" .


Ya bashi wani irin mari tare da cewa cikin masifa "wani irin iskanci ne zaka barmin motoci da 'kira eyeh?"

Yace yana 'kara masa wani, cike da girmamawa yace" yalla'bai go kwana hud'u baya sai da na wanke".

"Sai akace maka kuma jiya ko yau karka wanke ko?"

"Maza wanke min wancan jan yanzu na baka minti biyar kuma ya fita, idan ba haka ba yau sai kabar gidan nan" yace tare da tsaki ya juya.

Kamar d'azu suna kallon sa ya wuce ta gefen su baikoyiwa wani daga cikin su magana ba.

Da mamaki RAHAMA tace idanun ta cike da ruwan hawaye "Dady don Allah muje mu bashi ha'kuri muji meye damuwar sa, idan ma zaman 'KAUYEN yake so sai mu barshi ya koma idan yaso muyi masa ginin zamani a can. Sai ya rin'ka zuwa duk sati gida yana dubamu komu murin'ka zuwa".

Tunda ta fara maganan yake hararan ta har ta idda maganan ta.

Yau da badon 'yar gaban goshi bace tai maganan nan ai da tasha mari.

" Baki da hankali ko RAHAMA? ni kike so naje na bawa d'ana ha'kuri to bai zai ta'ba yuwu wa ba, don bashine ya haifeni ba, don ko uban sa.........."

Sai kuma yayi shiru "to bari kiji babu wata 'KAUYEN da zai koma, nd kwanan nan zai fara zuwa asibitin sa, don an gama komai bikin bud'e wa za'a sai ya fara aiki kinji ko?" Daga nan yayi tsaki tare da barin wurin.

"Kema dai inajin mahaukaciya ce ke, wai da bakin ki kike cewa Auwal ya koma 'KAUYEN da zama. Hmmm to bari kiji ko zuwansa sabis saboda ya rage wasu abubuwa da basu dace ba shiyasa muka dage kai da 'kafa ya tafi".

" Don sam bamu soba ke har Dady kan sa, saboda yayi hankali ne kawai muka kai sa" cewan babban wansu.

Kuka ta fashe dashi tare kallon mami da tai shiru .

Matsawa inda take tayi ta rungume ta tare da cewa" mami yanzu ya zanyi ya zanyi my brother ya dawo kamar da?" shiru tayi domin ita kanta abin na damun ta sosai.


Suna tsaye su biyu domin sauran sun bar wurin sai gashi ya fito.

Wuce su yake sonyi mami tace cikin matsawa da d'aure fuska.

"Ina zaka?" tsayawa yayi shiru ba tare da yace komai ba.

Tsawa da bata ta'ba masa ba shine tayi masa "dakai fa nake kayi shiru".

Fukan nan a had'e yace" nasarawa zani " daga haka yayi shiru.


"'KAUYEN nan zaka ko?" Shiru yayi ba tare da ya bata ansa ba.


"Wai shin Auwal meye kakeso? Meye kake nema a 'KAUYEN nan?" Still bai bata ansa ba.




"To tunda baka da ansan tambaya ta koma ciki" wani iri juyo wa yayi cikin tashin hankali yake kallon mamin.


Zaiyi magana tace" daga yau na sake jin sunan 'KAUYEN nan a bakin ka bare kace zaka sai na.............................










Comment nd share


Luv you all my fan's💋💋💋
[11/5, 9:54 PM] Safeeya Aliyu: 🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳

*'KAUYEN 'YAR KADDE*

🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳




*Story & written by: Safiyya Aliyu Wakili*





*💫DA BAZAR MU WRITER'S ASS💫*


*We are here to make you happy, smile, educate and realized that we are best among all........ DA BAZAR MU MUKE TUN'KAHO*


*My ❤, my kaka, my Hafsatuwa😉, my Hafnan is back.💃💃💃💃💃💃💃💃💃ina masoya ku fito, ga shahararriyan Marubuciyan nan da ta saba nishad'an tar daku, wato Marubuciyan, SHI SO 'DAYA NE, FATALWAN MIJIN NA da kuma HIBBATULLAHI. ta dawo muku da wani shahararran littafin ta mai suna KAICON SO! Masoya ku hanzar to kar kubari a baku labari Hafsat Mustafah (Hafnan) ta shirya tsaf domin nishad'an tar daku, wa'azantarwa da ilimantarwa. Da abaka labari gumma ka bayar, saboda haka masoya ku fito 'kwai da 'kwar'kwata domin wanke idanuwan Ku, karrrrrrr kubari.....................*



*you will never brave, if you don't get hurt. You will never learn, if you don't make mistakes. You will never be successful, if you don't encounter failure..................Good morning😉🙏🏻



*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*



🅿3⃣7⃣➡3⃣8⃣

"Wayyo Allah na, wayyo mami na. Wallahi mutuwa zanyi, mami in............" Sai kuma yayi shiru, kallon sa tayi tare da cewa "indai na isa zan gani" daga haka taja hannun RAHAMA suka wuce ciki, Kamar zaiyi kuka ya tsaya kallon hanyan da suka bi. Yana tsaye ba'kin ciki fal a cikin ransa, amma ya ya iya, haka ya gama tsayuwan sa yayi ciki, ko kallon inda suke baiyi ba san da ya shiga.


Sati na zagayo wa akai gagarumin bikin bud'e asibitin, Dady yayi 'ko'kari matu'ka ya cika uba na gari wanda kowani d'a zai alfaharin kasancewan sa uba a gare sa.

Ya zuba masa duk abinda ya kamata, had'a dasu manyan doctors, kayan aiki na zamani tun daga 'kasanr waje da dai sauran su.


Amma abin mamaki koda na waiga inda mutumin ku yake sam babu alaman farin ciki a tare dashi, fuskan nan a murtuke.


Angama taro lafia sai dai fatan Allah sa albarka.

Ya fara aikin sa cikin nasara, yana samun girmamawa ga duk ma aikatan, suna matu'kar girma mashi, aiki sosai suke a asibitin ciki tsantsan 'kwarewa.

Lokaci 'kan'kani asibitin yayi suna, sun sami lambobin yabo daga wurare daban, don gaskiya doctor Auwal 'kwararrene.

Kimanin wata hud'u da bud'e asibitin sa, amma Auwal bai ma kowa magana sai ta kama dole, walan gida ko asibiti.

Haka zalika fuska a d'aure, mata na son sa kamar zasu mutu amma babu fuska balle su san'kafa mai tayin soyayyar su.

Duk wata mace maiji da kanta da isa, burin ta Auwal ya kula ta.

Amma hakan bai samuwa sam, Auwal ya zama wani irin mutum.

Auwal ya zama fitinan nane 'karfi da yaji, abi kad'an kayi kuskure zaka sha masifa ko kuma ya kore ka, gida ko asibiti. shiyasa duk wani mai son kansa da arzi'ki yana gujewa 'bacin ran Auwal.

Ba gida ba ba asibiti ba kullum kwanan duniya ka sake kayi kuskure kad'an yanzu zai 'kore ka, haka zalika ko sakon baka 'karawa a wurin.



***********

Zaune yake a bakin bed d'in sa sai faman kiran wayar sa da ya bawa Joy yake da ya zame masa kullum kamar ibada amma bata shiga.

Kamar zaiyi kuka yace" why my happiness? Kullum sai na kira layin nan yafi abinda yafi, ko ba'a baki bane? Kai inah nasan yaron nan sosai bazai 'ki baki ba".


"To amma meye na kashe waya?".

" Oh Allah na help me" yace tare da sake gwada layin, still dai abu d'aya baturiyan nan take ta nana tawa.

Cikin fushi yayi wurgi da wayar, kwanciya yayi a gadon tare da runtse idanu.

Bai ankara ba kawai sai ga hawaye masu d'umi suna zubo mishi, bai hansu su zuba ba har sai da suka bar zuba don kan su.

Dai-dai nan yaji ana knocking, tsaki yayi tare da tashi ya nufan 'kofan, bud'e wa yayi.

Ganin wacce ke tsaye yasa ya mai da 'kofa ya rufe, abin mamaki fanz RAHAMA ce fa akai wa haka, lallai abin babbane.


Kuka ta fashe dashi, yana jin kukan har cikin ransa amma yayi biris da ita, da yaji kukan na damun sa ma sai ya tashi ya shige toilet abinsa.

Kuka tayi sosai kafin tabar wurin, daga nan ta zarce part d'in mami.

Da gudu ta nufe ta, tace cikin kuka "mami don Allah kuyiwa my brother abin da yake so, don Allah ku barsa ya tafi can d'in don samun kwanciya hankalin mu. Mami bai magana da kowa, baicin abincin gidan nan sai da matsi".


" Mami jifa, ni na raine sa da hannu na, na kula dashi kamar uwan da ta haifesa, shine abokin shawarata, abokin firata, shine kesani nishad'i. Shike sani farin ciki fiye da kowa, baya son ya ganni cikin damuwa ko d'an 'kan'kani ne, ya tsani ganin 'bacin raina. 'Kanina na sona, kullum......." Sai ta fashe da wani irin kuka mai ban tausayi.


Rarrashin ta mami take, tace cikin lallashi "ki fita harkan Auwal idan ba haka ba ciwon ki na gab da dawo wa".

"Mami ina fita harkan Auwal fa kika ce?" Tace cikin zaro idanu "amma mami bakiyi tunani ba sam, Mami Auwal fah d'anki ne na duniya da lahira, maraya ne kin sani sarai, mami kina tunanin share sa da kuke hakan ya dace? har yau kun'ki zama dashi kuji meye damuwar sa meye yake so?".

" Shin haka ya dace kuyi ma maraya? kunyiwa maraya adalci kuwa? mami kamar bake ba, mami kiyi tunani da kyau shin abinda kukayi dai daine? Auwal d'ane d'an gata, saboda iyayen sa ma 'yan gatan kune. Mami kiyi tunani ".


" Mami kamar bake ba, mami Auwal d'inki ne fah, yaron Anty ne fah. Anty baza ta ta'bajin dad'in ace yau ga yayan ta tabar mata d'a cikin wannan yanayi ba, kin bar mata yaro cikin damuwa".

"Mami kin manta wannan shine jinin Anty 'kwalllin 'kwal? Shine ita fah tunda bata, mami ina son da kike mata ya tafi? wai yau da bakin ki kike cewa na rabu da jinin Anty na? Bayan Anty na itace uwata.".


" Anty da Abbey mutanen kirki ne sosai ke kanki sheda ce, uwa d'aya uba d'aya kuke mami ko kin mata Abbey 'kanin mijin ki ne uwa d'aya uba d'aya? ".

" Auwal jinin mune gaba da baya, da mamaci na magana da tabbas Anty ta sanar miki bata jin dad'in yadda kika bar mata yaro kamar mara gata ba, Anty ta mutu tana murna da murmushi na tabar farin cikin ta a hannun ki, saboda tasan bazaki ta'ba wofin tar mata dashi ba".

RAHAMA ke zancen nan cikin kuka mai tsanani.

"Mami kije kiji mai d'anki yake so, mai yake bu'kata. Ki nemo yadda zakiyi Auwal yayi farin ciki, Anty ta baki amanan d'anta tana tunani kece kad'ai wanda take da ya'kini tilon d'an ta zai samu farin ciki daga gare ta".

Daga haka ta tashi tabar d'akin mamin, jikin mami yayi sanyi sosai, don gaskiya maganan RAHAMA ya shige ta sosai.

Su uku ne, amma kuma itace abokiyan shawara firan ta duka, tace tana maiji kewan 'yar uwan ta ta.

Tashi tayi cikin sanyin jiki ta fito daga d'akin nata, bata zame ko inaba sai 'kofar d'akin Auwal.

Knocking tayi tayi amma Auwal ya'ki bud'e wa don a tunani sa RAHAMA ce ta dawo, don duk abinsa yana ganin girman mami fiye da kowa a gidan, shiyasa ita kad'ai yake d'aga wa 'kafa.

Haka ta d'au tsahon lokaci tana bugawa amma ya'ki bud'e wa.

Kiran sunan sa ta farayi amma shiru kakeji tamakar bashi a d'akin.

Haka ta gaji ta ha'kura akan sai da safe.



°°°°°°°°°°°


Washe gari kuwa tsiro da wani abu yayi, suna idar da sallan asuba Dady na kallon sa yabar gidan a guje kamar zai tashi sama.


Dama yayi wanka sannan yayi alwallah, da mamaki baki sake Dady ke kallon hanyan da yabi.

Girgiza kai kawai yayi tare da shigo wa ciki.

Wurin break fast ne mami taje neman sa ta tadda bashi shine Dady ke samar mata da akan idon shi ya fita.

Jikin tane yayi sanyi, RAHAMA ma tashi tayi gaba d'aya tabar dining d'in mijin ta yabi bayan ta .

Mamin kanta kasa karyawan tayi, kiran layin sa tayi bai shiga, don haka ta buga uban tagumi hawaye na kwaranya akan fuskan ta.

Dady ya matso kusa da ita tare da bata baki sannan tabar kukan.


Auwal ko daga gida asibiti yayi, koda ya bud'e office d'in sa kwanciya yayi kawai tare da runtse idanun sa.



Wanene Auwal??????

Asalin sa, ko nace tushen sa.


Alhaji Bashir da malam Isma'il ma'kotan junane, kuma aminan juna. Idan ba wanda yasan su tuntuni ba zai tsammanin 'yan uwan junane, don yadda suke mu'amala ya wuce ka kira su da aminai, domin sun zama 'yan uwan juna.

Yadda mazajen suke haka ma matan su.


Alhaji Bashir mutumin kirkine, yana da arzi'ki dai-dai gwargwado, arzi'kin sa bai rufe masa ido ba sam, yana matu'kar taimakon talakawa, yana daraja ma'koci, matar sa d'aya itace HAJIYA Umma, macece mai kirki da zumun ta.

Sun d'au tsahon lokaci Allah bai basu haihuwa ba, tun suna damuwa har ya zamana sun fawalawa Allah.

Watarana suna zaune abokan junan nan suna fira, sai Bashir ya dubi Ismail cikin damuwa yake cewa" na rasa wani laifi nayi wa ubangiji na" sai kuma yayi shiru.

Sai Ismail yace" d'an uwa mai yasa kace haka?" numfasawa yayi sa'an nan yace" wallahi rashin haihuwan nan na matu'kar damuna, ka duba tsahon shekaru goma sha da auren mu amma har yanzu shiru bamu ta'ba ko 'bari ba, ga fitinan dangi".

Murmushi Ismail yayi tare da cewa" bai kamata kasa damuwa a ranka ba, duk bawa bai wuce jarabawan ubangiji ba, wannan shine jarabawan mu nida kai, saboda haka kar mu gaji, mu cigaba da addu'a Allah na sane damu, Allah ya bamu ikon cin jarawan nan".

Magagganu mai dad'i Ismail yayi masa, maganan ta shige sa, don yayi aiki da ita.

**********

Bayan wata biyar da maganan su sai gashi Allah ya bawa matan Bashir ciki, zoka ga murna wurin iyalan nan

Bayan wani lokaci ta haifi d'anta mai tsanani kyau aka samasa suna KABIR.

KABIR nada shekaru biyu ta sake samun ciki, wannan karon itama matan Ismail ta samu ciki. Sai dai wannan cikin yazo ma matan Bashir wani iri domin yana bata wuya sosai.

Kullum cikin ciwo, ranar da ta haihu na biyu tace ga garin ku nan.

Wannan karon ma namiji ta haifa, Bashir yayi kukan ba'kin ciki sosai malam Ismail ne yaba shi baki yazo har yasama zuciyar sa salama.

Bayan rasuwan ta da kwana uku yaro ya fara neman abinci, hankalin Bashir ya tashi sosai.

Fara zaga dangi yayi don neman mai shayar masa da yaro ya biya amma daga nasa har na

2 Comments On KAUYEN YAR KADDE
avatar
abdulrazak

1 year ago

Reply

Next pls

avatar
abdulrazak

1 year ago

Reply

Next pls

Please Login or Register in order to submit comment