Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shafo cikin sa.


Cikin tausayawa tace "bari na kawo maka kaci" tace tana mi'kewa, yamu ya had'iye kut tare da kauda kai da sauri.


Bata 'bata lokaci ba ta dawo hannun ta d'auke da tire, dire wa tayi a gaban sa tare da zama.


Bud'e kwanon tayi, shinkafa ne da miya, gaskiya bazai iya cin wannan shinka fan ba.


Don haka sai yace "kici kawai bari naje masallaci" 'bata fuska tayi ba shiri ya fasa mi'kewa.


Tura masa kwanon tayi gaban sa, kallon ta yayi ta masa nuni da yaci.


"Bani to" yace yana bud'e baki, kallon tsabtataccen bakin sa tayi, yayi matu'kar burge ta.


Babu damuwan komai ta saka cokali ta d'ebo ta nufi bakin sa dashi.


Ta bashi kusan sau biyar aka kira salla, don haka ya dakatar da ita.


"Maza kiyi wanka kafin na dawo mu cigaba da fita" yace yana gab da fita.


"Oho har da abinci kici kinji?" d'aga kai nayi ina mai jefan sa murmushi, shima ya mayar mini.



Comment & share pls
[11/5, 9:50 PM] Safeeya Aliyu: 🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳

*'KAUYEN 'YAR KADDE*

🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳




*Story & written by: Safiyya Aliyu Wakili*





💫DA BAZAR MU WRITER'S ASS💫

*We are here to make you happy, smile, educate and realized that we are best among all........ DA BAZAR MU MUKE TUN'KAHO*




*Tell my mistake to me, not to others. Because my mistakes are to be corrected by me, not by others.*






*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*




🅿3⃣1⃣to3⃣2⃣


Bayan fitan sa na kwashe kayan da ya sayo min na kai d'aki na aje na fito, dawo wa nayi inda na tshi na zauna, wani irin farin ciki naji yana mamayeni, kasa tashi nayi daga wurin har na tsawon wani lokaci, ina nan zaune sai faman murmushi nake Aisha ta shigo, kallo na take tunda ta shigo, nayi nisa bansan ta shigo ba.



"Besty! Besty!! Besty!!!" sau uku duk banji taba, gashi sai faman murmushi nake ina karkad'a kai.



Jin kiran sunana da tai tayi shine ya farkar da mama, fito wa tayi tana cewa "kun dawo yaushe Aisha?" .



"Tun d'azu, mama anya 'kwa'kwalwar besty lafia yake kuwa?" dariya mama tayi kad'an tare da cewa "mai kika gani?".



" Matso kiga mama, wallahi tunda na shigo take a haka, kuma nakira sunan ta bata san inayi ba".




"Joy" mama ta kira ta da 'karfi, firgit na dawo daga duniya ta nida hubby na, kallon Aisha nayi dake gaba na.



Murmushi da tunda nake da ita bata ta'ba ganin nayi wa wani ba bare ita taga na mata.



"Besty wannan fara'an fah? da murmushi fah?" rungume ta nayi ina ta faman sakin murmushi.



"Shafa min mana besty mai muka samu bayan dawo war mu?".



" Am very happy today my 'kawa" nace ina kallon ta, itama ni take kallo fuska ta d'auke da murmushi.



"Really?" d'aga mata kai nayi tare da sake rungume ta, mama na tsaye tana ganin ikon Allah.



"Burina, farin ciki na, rauwata, anashuwa na, walwala na" sai nayi shiru.



"Uhum, ina sauraron ki fad'a min na tayaki murna sosai" cewar Aisha.



Lumshe ido nayi na bud'e su, basu sauka a ko ina ba sai a kan kyakkyawan fuskan sa da shigo wansa kenan, ya dawo daga masallaci ko gida bai shiga ba yazo yaga ko tayi wanka taci abinci.


'Kayataccen murmushi na masa, 'bata fuska yayi tare da harara na.



Fuuu naji gaba na ya fad'i, ido na zuba masa shiko ya d'auke kai.



"Shigo mana doctor" cewar mama, murmushi yayi mata tare da 'kari sowa ciki yana cewa "sannu da gida mama, nazo kina ta barci".



" Hmmm, kai dai bari wallahi jin jikina nayi duk a gajiye bayan na gama girki shiyasa na kwanta na huta har basan su Joy sun dawo ba " tace .



Kallon sa nake har yazo ya wuceni ko kallo na baiyi ba.



Shagwa'be fuska nayi tare da shashsha'ka, kamar zanyi kuka.


"Lafia ke kuma?" cewar mama, "ai ba lafia yau mama inaga sai yaya na ya duba ta dai, jifa yanzu take fara'a da farin ciki, amma lokaci d'aya ta canja" cewar Aisha.



Hararan ta nayi tare da turo baki ina waigo wa, had'a ido mukayi ya kauda kai.



Cikin shagwa'ba nace "bashi bane" nace ina le'ka fuskan sa da ya juya dashi gefe.



"Wake nan?" inji mama, jin haka yasa ya waigo mi'kewa nayi tare da cewa "ba gashi a gaban ki nan ba".


Zaro fararen idanuwan sa yayi yana kallo na, murmushi na sakin masa tare da 'kale ido nayi cikin d'aki.



" Ban son sharri daga shigo war sa, zaki wani 'bata rai kice shi" cewar mama "aiko dai, mai yaya na zai miki? muna zaune muna gani ya shigo ko kallon ki baiyi ba, dama besty kin iya sharri ban sani ba?".



Jin bai ce komai ba yasa na fito, tsayawa nayi akan sa, lokacin mama ta nufi kitchen, kallon sa nayi tare da cewa " ka rantse baka kalleni ba daka shigo, kuma ka rantse sharri nake maka baka min komai ba ".



Kamar ba dashi nake ba yayi banza dani, bubbuga 'kafa na farayi a 'kasa da fara shashsha'ka.



Kallo na yayi tare da mi'kewa yace a hankali yadda Aisha baza taji ba " wallahi nafi ki iya rashin kunya, a gaban mama kikewa saurayi shagwa'ba?, to Allah zan kunya taki".


Turo baki nayi tare da cewa "to bakai kaja ba to" "niko?" yace yana matsowa kusa dani.


"Uhum, lallai wannan shine a dake ka a hanaka kuka, mai nace miki fisabilillahi kafin na tafi masallaci?".



" Wanak da cin abinci" nace ina turo baki, kallon bakin yayi tare da runtse ido had'e da cije le'be.




Yace cikin wani yanayi "to mai yasa baki ba?" far nayi da ido, wanda saura kad'an ya fad'i yayi maza ya dafa bango tare da cewa a cikin zuciyar sa "yarinyan nan zata kashe ni idan banyi wasa ba".



Matsowa nayi gaban sa, dai-dai nan mama ta fito hannun ta ri'ke da abinci.



Ganin zan ta'ba sa yayi maza ya kauce, ban ha'kura ba na sake matsoshi ina mai cewa cikin damuwan da na shiga take ganin zai fad'i "maike damun ka?".



Kafin ya bani ansa mama tace " wani abu ya same shi ne?" tana mai aje abinci a kusa da kujeran da ya tashi.



Turo baki nayi cike da shagwa'ba zanyi magana yayi saurin cewa "ba komai mama".



Wani irin kallo na masa, yayi saurin d'auke kai a zuciyar sa yana cewa "bazan iya kasance wa kusa dake ba, musamman idan mu kad'ai ne, idan ba haka ba sai nayi sa'bon Allah, yanzu dama haka yarinyan nan take kana ganin ta shiru-shiru?".




" Ga abinci ka doctor " murmushi yayi tare da cewa "naci ai mama d'azu kina barci".



" Kai my.............." da sauri ya kallo ni, gar gad'i yayi min, Allah saura kad'an nayi dariya na gintse, ko meye tsoron sa oho.



Don haka na murmusa tare da cewa "mama ina sabulu wanka yake? na duba kwando bashi inda kike ajewa kuma ban gani ba".


Kafin ta bani ansa sai da tace da doctor " ka 'kara to" bai son mata gaddama yace "to" tare da bismillah ya fara ci.



"Wai wanka zakiyi ne?" cewar Aisha, "uhum" nace da ita ido na nakan doctor da yafara cin abinci.




"Kafin ki shiga bani littafin Husna da kika ara zan duba wani abu, to" nace da ita tare da shiga d'aki na d'ako na bata.



"Yauwa bari naje kiga, mama sai anjima, yaya sai anjima" tare suka ansa shida mama.



Ido na nakan doctor da ya d'ago yana kallo na yana min magana da ido, wai naje nai wanka nazo muci.



Tura baki nayi tare da cewa "mama sabulun" "sabulun nan sai dai kisiyo" tace tana shiga d'aki.


Kafin ta d'ako kud'in na zana kusa dashi har guwana na ta'ba nasa, da yake mama ta shinfid'a masa tabar ma.


Runtse ido yayi tare da cewa "meye haka?, mai nayi" nace ina dube dube.



"Ansa kisiyo" na kar'bi kud'in tare da mi'kewa, tara tafiya nayi bai ninyan magana ba yace "amm......." sai kuma yayi shiru, waigo wa nayi tare da cewa "kana magana ne? duba kayan nan akwai" daga haka ya gintse bakin sa.



Yana mamakin ta sosai, yace a zuciyar sa "yanzu ba don nace ba da haka zata fita duk mazan garin nan su gama gane min ita" tsaki yayi tare da cewa "musulunci yayi gaskiya".



Kallon mu mama tayi duka, tana mamakin sauyin da ta gani a tare damu duka, amma taje baki tayi shiru.



'Daki naje na bud'e kayan d'aya bayan d'aya ina mamaki da alajabi, har naga wanda sabulun wankan yake ciki.




Wani irin sonsa da 'kaunar sa naji ya 'kara nunkuwa a zuciya ta.



Gaskiya Auwal ya kashe kud'i, ya narke kud'i kamar bai so.





Cikin sanyin jiki na mai da kayan sannan na mi'ke.



Suna zaune da mama na fito, suna d'an ta'ba fira, ya bar macin abinci.


Kallon sa nayi koya waigo, wuce wa nayi na d'ebi ruwan zanyi bayin tsakar gidan.



"Mama yanzu ruwan sanyi zatayi wanka dashi?" daga ni har mama juyo wa mukayi muna kallon sa.


Ganin kallon da mama take masa yasa ya kauda kai yanajin kunya.


Murmushi mama tayi tana kallo na, nima kallon ta nayi tare da d'age mata gira ina murmushi.


Numfasa wa tayi da fara'a a fuskan ta tace "gata nan dai hanata yau 'kila ta bari, don naga tana ganin ka da gashi".



" Tafi shekaru uku tana wanka da ruwan sanyi" zaro ido yayi yana kallo na, "wuce ki dafa ruwa sai kiyi wanka" yace yana d'aure fuska.



"Inama da ruwan d'umi a kitchen d'in" cewar mama, ban musa ba na dawo nayi kitchen.







°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°*********************


Washe gari tun da asuba na tashi kai kace sallah zatai nace da ita, kallo na tayi tare da cewa "sorry Mrs ba addinin mu d'aya ba bare kiyi tunanin haka, saboda son ganin masoyi na yasa na tashi da wuri, don yau basai antasheni ba" Dariya nayi tare da cewa "a'a kinji 'kawan kwanta ruwan sanyi na jira" murgud'amin baki tayi tare da cewa "aniyanki ta biki, don yau na tabbata ko makaranta nace ba zani ba babu abinda zai min, ban cin karki ce nai rashin kunya da nagaya miki yadda zai tasheni ko ban tashi ba. Oh da gaske?" d'an kai tayi kawai tare da cigaba da sabgan gaban ta.


Don sai a wannan lokacin ne take bitan abinda aka koya musu a makaranta.



6:30am ta gama wanka tsaf ta shirya, wanda ganin ta shirya yasa mama koma wa barci bayan ta aje mata break fast.



Koda na gama shirya wa banko tashe taba na fito gidan a bina, tsaye nake a bakin zauren gidan mu ina kallon yanayin anguwan namu tsit kamar ba mutane.



Ko na abin mamaki bane, idan nai la'akari dako 'karfe nawa ne yanzu.



Murmushi na saki ina kallon gidan su besty da yake a rufe, alaman basu bud'e ba.



Kallon na sahibi nayi naga shima a rufe, ga motar sa a gefe.


Nufan 'kofar gidan nayi, tura wa nayi naga 'kofar ta bud'e, murmushi na saki tare da shiga ciki.



Komai tsaf kamar yadda yake haka komai na gidan yake a tsabtace a gyare.




Ga inji a kunne daga gefe kanajin karatun Qur'ani na tashi.




Zuwa nayi 'kofar palon, itama a bud'e take, nayi mamaki matu'ka .



"Bai tunani azo a sace masa?" nace a zuciya ta, shiga nayi babu kowa a palon, nufan bedroom d'in sa nayi, ina zuwa d'aga labule nayi, hango mutum nayi kwance a lullu'be akan gado.


Girgiza kai nayi tare da aje jaka ta akan sofa na nufi katifan ina dariyan abinda zan mai.


Ina zuwa nai tsalle na fad'a kansa, "innalillahi" yace tare da fara bud'e idonun sa, ai bai san sanda ya bud'e suba gaba d'aya yana kallon agogon bangon dake d'akin.



Mai da idonun sa yayi kai na tare da harara ta, niko na fashe da dariya, muskutawa yayi tare da cewa "d'aga ni, wai ma meye na zuwa tashi na da sassafen nan?".



Turo baki na nayi dake gaf da nasa ina kallon cikin 'kayan idanuna sa, nace " makaranta zaka kaini".


Kauda fuskan sa yayi don yaga kamar tana ninyan had'e bakin su yace "makaranta ne da uwar safen nan?, uhum, gari fa ko gama haske baiyi ba, ba ina ganin yadda kuke tafiya ba?".




" To naji, nazo na ganka ne" "hmmm, d'agani tom" 'kin d'aga san nayi, don haka sai ya fido hannun sa daga cikin abin rufan yace cikin lallashi "d'aga ni Queen d'ina kinji" ma'ke ka fad'a nayi.



Shiru yayi yana kallon yadda ta had'a fuska, "Allah barci bai isheni ba, jiya kin kanai nayeni kin hanani moruwa, ko asibiti fa banje ba".


"'Dagani kinji baby na" sauka nayi tare da kwanciya a gefen sa "oh Allah" yace yana runtse ido.


"Tashi kijirani a Palo yanzu zan fito, a'a muyi barci kawai" nace ina mai d'aura hannun na a jikin sa.



"Barcin ya tafi kuma ai, jeki yanzu zanzo" ma'ke kafad'a nayi tare da rufe ido kamar zanyi barci.



Rasa yadda zaiyi yayi, don haka sai shima ya rude ido, domin har ga Allah bai son kusancin nan nasu haka, don komai na iya faruwa, 'karin dad'i daga shi sai guntulallen wando.


Jin shiru yasa na d'ago tare da cewa "ka koma barcin ne?, a'a, ai na gaya miki ya tafi, kije palo kijiran nayi wanka mutafi, kin maci abinci kuwa?".



" A'a, mai yasa to?" yace yana mai bud'e ido, "tare nake son muci".




" To jeki kitchen kima kafin na fito wanka" mi'kewa nayi tare da fita a d'akin.




Ri'ke kai yayi tare da cewa "zan sha aiki" ya mi'ke bayan ya yaye bargon.................







Comments nake da bu'kata, idan ba haka ba sai bayan sati biyu🥰







Luv you all my fan's❤❤
[11/5, 9:53 PM] Safeeya Aliyu: 🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳

*'KAUYEN 'YAR KADDE*

🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳




*Story & written by: Safiyya Aliyu Wakili*




💫DA BAZAR MU WRITER'S ASS💫

*We are here to make you happy, smile, educate and realized that we are best among all........ DA BAZAR MU MUKE TUN'KAHO*





*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*




🅿3⃣3⃣➡3⃣4⃣


Jallabiya ya nema ya saka, ya saka kenan ta dawo cikin d'akin kallon ta yayi kamar yadda itama idon ta ke kan nasa, d'aga kai yayi alaman ya akayi ne, sai da ta 'kariso ciki gab dashi sannan tace "ina kitchen d'in yake?" kallon ta yayi tare da cewa "kai Habibaty, kitchen d'in ne baki gani ba?, uhm," nace ina kallon sa, don gaskiya bana gaji da kallon hasken idaniya ta.

"Muje na nuna miki tun kafin ki cinye ni da wad'an nan idanuwan naki" murmushi nayi ba tare da na bar kallon nasa ba.

"Muje nace, time na tafiya, gashi ko wanka banyi ba, kuma inason na le'ka asibiti da safen nan".

"To muje" nace ina dawo wa kusa dashi, girgiza kai yayi tare da d'aga 'kafan sa yafara tafiya, nima na fara.


Yana d'aga 'kafa d'aya nima haka, waiga gefen daman sa da nake yayi yace "wai ni kakan kine baby?".


" Kamar ya?" gaba yayi ba tare da ya bani ansa ba, ni kuma na bisa, kitchen d'in ya nuna min zai juya nace "mai za'a dafa maka?".


" Abinda zaki iya ci, don da ganin wannan shafaffen cikin babu komai a cikin sa".

"Hmmm, my heart kenan" kallo na yayi yana mai jin matsanancin farin cikin sunan da nakira sa dashi.


"Ina son ki" yace yana mai lumshe idanu wan sa, "nima haka" ba tare da na bud'e baki ba, lab'bana ne kawai suka motsa, kallon su yayi tare da jin wani irin yanayi.

Barin wurin yayi ni kuma nayi cikin kitchen d'in, tunani na fara "shin mai zan masa?" nai shiru ina nazari.


Ban iya kunna gas ba sai na kuna stove, d'aura ruwan zafi nayi, kafin yayi zafi na fere doya, yana tausa na juye, soya doya nayi da 'kwai.

Ina gama wa na fito, lokacin shima ya fito a lokacin ya fito 'kamshin shi ya cika ko ina na palon, ganin kallon da nake masa kamar wa wuya yasa ya saki wani had'ad'd'an murmushi.

Mayar masa nima nayi tare da nufo sa, cikin shagwa'ba nace lokacin da na iso gaban sa "gaskiya doctor kamin wayau" zaro ido da ya zama kamar al'adanshi yayi tare da min magana da ido, "name?".

Turo baki nayi tare da cewa "kasani ma break fast bayan nayi wanka, kana 'kamshi niko sai wari nake" nace ina shinshina jiki na.


Matsowa gab dani yayi yana murmushi tare da cewa "muji" yana kamo hannu na, tare da rankwafawa ya kai hancin sa a wuya na, yace "hunnnn, 'kamshi, kinji 'kamshin dakike kuwa baby?".

Fincike wa nayi don nasan tsokana ta kawai yake, murmushin gefen baki yayi tare da cewa " da gaske 'kamshi kike, zo na'kara ji".

Bibbiga 'kafa na farayi a 'kasa ina cewa "Allah ban wani 'kamshi ni na sani, kuma ni wanaka zan sakeyi yanzu na fesa turaren ka".

"Zo HAYATI, zo kinji" banza dashi nayi, shi kuma yana tsoron Allah yana tsoron abinda Joy za tayi.


Ko kallon sa banyi ba nayi hanyan d'akin sa "oh my god" yace tare da d'aura hannu aka, niko ina shiga nayi toilet d'in sa, wani irin 'kamshi bayin yake, tu'bewa nayi na d'aura towel d'in sa, na fito da uniform d'ina a hannu palon na fito.


Jin motsina yayi tunani ko na fasa ne ya d'ago da kai don kallo na.


Da sauri ya kauda kai, murmushi nayi tare da mamakin sa, sai kace yaga wani abun tsoro.


"Ga uniform d'ina ka ninke min kafin na fito, yadda ba zai ya mutse ba" nace tare da ajewa kusa dashi.


Bai ce komai ba har nabar wurin, kuma ko sake kallo na baiyi ba.


Wanka na nake cikin nishad'i, da ruwa mai 'kamshi, "nima yau zan zama 'yar gayu" nace ina sakin murmushi.


Bayan na fito na 'kwala masa kira don ba mirror bansan inda kayan 'kamshin sa suke ba.


Yanaji ya kasa magana, don yana nan inda ta bar sa, a daskare yake don ko uniform d'in da tace ya nunke mata baiyi ba.


Sake 'kwala masa kira nayi amma shiru babu ansa, don haka sai na fito tunani na ko ya fita ne, ina zuwa na gansa zaune inda na bar sa.



Cikin shagwa'ba na nufo sa, banyi wata wata ba na d'ane cinyan sa, d'ago da runannun idanuwan sa yayi tare da cewa cikin ma wuyacin hali.


Da sanyin murya "please kibar abinda kike, Allah addinin mu yahana haka, haramun ne abinda muke aika tawa, hakan zai kamu ga aika ta mummunan abu, ki bari kinji".


" Ki adana su zuwa bayan auren mu" yace yana kauda kai, kallon sa nayi da mamaki, nace "meye abinda nake mara kyau?" shiru yayi bai ce komai ba.


Hannaye na nasa tare da juyo da fuskan sa, ina kallon cikin idon sa nace "meye laifin abinda nayi?, kaban ansa".


Saka hannu sa yayi tare da zame hannu wana yace " addinin mu ya haramta ke'bance war mu haka".


'Dage gira nayi tare da girgiza kai "to d'an d'agani please, kije kuma kisa kaya mu karya zaku makara fah, kalli" yace yana mai nuna min agogo.


Takwasa saura minti goma na gani, mi'kewa nayi tare da cewa "ina ka aje kayan 'kamshin ka?" bai ce komai ba ya mi'ke, d'akin ya nufa nabi bayan sa.


Muna shiga ya mi'ka min wani jaka "gashi, please kiyi sauri muje" yace tare da fita bayan na ansa.


"My heart d'an kawo min uniform d'in" zuwa yayi bakin 'kofa ba tare da ya d'aga labulen d'akin ba .




Yace "gashi" turo hannu sa kawai yayi, murmushi nayi ina mamakin wani irin addinine haka mai shegen ta kura?.


Saka kaya na nayi na fashe jikina da turarukan sa masu shegen 'kamshi, amma abin takaici banji 'kamshin kamar na jikin sa ba.


Fito wa nayi, kallon sa nayi tare da kallon break fast d'in bai ko ta'ba ba.

"Ya bakaci ba?" kallon na yayi tare da cewa "ke nake jira" ya tsina fuska nayi tare da cewa "kaci kawai na 'koshi".

Mi'kewa yayi ba tare da yace dani komai ba ya nufi 'kofa, da mamaki na kira sunan sa.

Waigo wa yayi yana kallo na ba tare da ya ansa ba, " bakaci ba ".


" Na 'koshi ne nima" murmushi nayi tare da nufan inda yake tsaye, kamo hannu sa nayi .


Bai ce dani komai ba har na zaunar dashi, bud'e wa nayi tare da zuba wa a plat, na had'a masa tea duka nace "muci" tare da saka hannu.


Bai ce komai ba ya faraci, kad'an yaci yace ya 'koshi tare da mi'kewa.


Nima na mi'ke, kallo na yayi tare da cewa "ci inajiran ki waje" .

"Na 'koshi, kin tabbata? uhum".

" Shikenan muje 8:10am har yayi 'kila 'kawan ki ta tafi" fita yayi na bisa a baya, ina fita ya saka key ya rufe 'kofan.


Mukayo waje ya rufe gidan shima, rana ya fara fito wa mutane nata kai da dawo wa.

"Shiga kira ta" bace komai ba na nufi cikin gidan nasu.

Mama na tarar a tsakar gidan, gaishe ta nayi itako tana kallo na da mamaki a fuskan ta bata ansa min gaisuwan ba.

"Baku tafi ba?" tace, cewan ta haka ne ya ganar dani cewa Aisha ta tafi, don haka sai nai tsuru tsuru na kasa bata ansan tambayan ta.

"Joy dake nake fah" sosa 'keya na farayi sai na dake tare da cewa "mantuwa nayi shine na dawo, to na duba d'akin mu ban gani ba shine na tuna jiya tazo ta 'kar'ba, shine nazo duba wa".


Shiru tana kallo na kamar bata yadda da abinda nace ba, sai daga baya tace " me kenan?".

"Litafin wata 'yar class d'in mu, shiga ki duba, amma ai da kun dawo tare ta barki ke d'aya kin dawo".

" Amma a mashin kika dawo ko?" tace ina gab da shiga d'akin.

"Uhum" nace kawai tare da sa kai.

Kallon d'akin na tsayayi kawai har kusan minti biyar sannan na fito, ganin bata tsakar gidan na saki ajiyan zuciya tare da falfalawa da gudu.

Ina fita na bud'e mota na fad'a cikin tare da sauke numfashi.

"Lafia?, ina 'kawar taki?" yace yana kallo na.

Ban sa ansa ba nace "muje kawai" bai wani matsa ba ya tada mota muka bar wurin.


Mun fara nisa sannan nace "Aisha fa ta tafi, kuma nasan ta shiga gidan mu nema na".

"Yayi, kinga mai himma kenan" turo baki nayi tare da cewa "naji ni ban da himma".

" A'a ni bance ba" banza dashi nayi shima bai matsa ba ya cigaba da tafiyan sa.


Yana parking na bud'e 'kofa zan fita, "ansa" yace .


Waigo wa nayi tare da kallon hannu sa, "ki ansa nace" hannu a dun'kule.

"Me zan ansa?" nace ina le'ka sa'kon hannu 'kara dam'kewa yayi tare da sa d'aya hannu sa ya janyoni tare da kar'be jaka ta yasa min tare da saki na.

Zanyi magana yace "oyo wuce kin makara, maza aji kar a ta'ba min lafia jikin ki" murmushi nayi tare da fita daga motan.

'Daga min hannu yayi nima haka nayi cikin makaranta.



Sauri ya tada motan yabar wurin bayan yaga shiga ta aji.


Ina shiga Aisha ta tsare ni da ido, murmushi nayi tare da cewa "lafia kallon malama?".

"Ina kikaje ne besty? naje gida mama tace kin dad'e da fita".

" Gidan doctor " nace murya 'kasa 'kasa, don malam ya shigo lokacin.

Zaro ido tayi tare da bud'e baki, murmushi nayi tare da cewa gab da kunnin ta "rufe bakin, kinsan wannan malamin mai rainin wayau ne, ki bari sai ya fita sai ki sake wani tambayan".


Aiko kamar wa wuya ta kasa magana rufe bakin tayi muka natsu aka fara darasi.



Yana fita Aisha ba ta barni na koda matsa ba ta jefomin tambayan.

"Mekikai a gidan doctor fisabilillahi da girman ki da 'kiman ki?" .

"Tashin sa a barci nayi, bayan haka na masa break fast".

San'kare wa tayi a wurin.


Niko dariya nayi, in banda abinki Aisha ina ruwan arne........




**********


Rayuwa tama su Joy dad'i soyayya kawai suke kamar ba gobe, suna tsananin 'kaunar junan su da kulawa da junan su
Sosai.

Amma fa Auwal bai sake sakacin barin 'kofar gidan sa a bud'e ba, don yana tsoron Allah yana tsoron Joy.

Duk da haka bai tsira ba, a hakan tana yawan ta'ba sa, ko son shige masa jiki.

Wani abu da ta tsiro shine zuwa asibiti duk bayan ta dawo daga makaranta, sai tazo tawani kanai naye shi.


Haka suke ta tafiya har wa yau, yanzu haka saura jibi Auwal zai koma garin sa, ya gama sabis d'in sa, ya rasa yadda zai sanar mata.

Ganin cewa suna ta faman jarabwa, don bai son ya tada mata da hankali ko kad'an.

A haka har kwana uku tayi ba tare da yasan yadda zai ya gaya mata ba.


Can Abuja su mami sun kasa sun tsare suna jiran dawo wa Auwal shiru har washe gari bashi ba labarin sa.

Sun kira wayar sa a kashe, shiko yayi hakan ne saboda bai san mai zaice masu ba.

Sati d'aya da gama wan sa saura kwana biyu su Joy su gama jarabawa, yana zaune a 'kofar gidan sa

2 Comments On KAUYEN YAR KADDE
avatar
abdulrazak

1 year ago

Reply

Next pls

avatar
abdulrazak

1 year ago

Reply

Next pls

Please Login or Register in order to submit comment