Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta tayi tare da cewa cikin tsawa" RAHAMA ba ita bace, kina haukane? a ina kika ta'ba ganin mutum ya mutu ya dawo? Kuma ma idan itace sai tazama yarinya? kin manta tana da d'an da ya isa aure da yayi da wuri idan Allah ya albarkaci auren da yaran sa biyar ko hud'u".

"Idan kina mafarki ne ki farka don ba ita bace" mami ta 'karisa idon ta na zubar da hawaye .

Tun da suka fara zancen su tsoro ya shigi Zarah, don haka mi'kewa tayi ba tare da ta kalli inda Husna take ba zata fita.

RAHAMA tace" mami kalli zata gudu anty don Allah ki dawo kada ki barmu muna tsananin bu'katar ki.. Munyi kewan ki sosai. Ga habibin ki zaiyi aure kinga ga matar da zai aura nan, Husna jeki, jeki ga mahaifiyar mijin ki can".

Kan Husna ya 'kulle shiru tayi tana binsu da kallon musamman ma RAHAMA da take tunanin ta haukace.

Mami ne ta tsinke RAHAMA da wani uban mari mai zafi tace" ki farka RAHAMA ba ita bace, wannan da kika gani tare da Husna suka zo. 'Kawar tace".

Marin ya shige ta sosai, natsuwa tayi tana sauraron mami da ta cigaba da cewa" kama ne RAHAMA, ba'a mutuwa a dawo".

Matso wa tayi kusa da mamin tare da rungume ta, ta fashe da matsanancin kuka.


Rarrashin ta mami ta kamayi ta dad'e tana rarrashi kafin ta fara a jiyan zuciya.

Mi'kewa Husna tayi tabi Zarah da tai gaba, koda ta fito bata kuma ga motar ta a ajiye.


Shiga motor tayi ta fad'a tare da barin gidan.......


Inason idan nayi kuskure fan's d'ina su gaya mini, nayi kuskure a page d'in baya, wata tamin magana ta PC kuma naji dad'in hakan sosai, don har ga Allah na sani kuskure ne aka samu.
Kuskure kuwa shine da nace bayan kakan Auwal namiji da matar sa ta mutu kakan sa na wurin uwan ya kar'bi jaririn da matar abokin sa ta haifa ya bama matar sa ta had'a ta shayar dash tare da jaririn ta da suka haihu tare, to kunga idan ta shayar dashi babu aure a tsakanin 'ya'yan su don addini ya haram ta hakan, sorry to sai ba haka naso rubutawa ba akasi aka samu. Madara ta basa ba nono ba.



Don gara, kuskure ko shawaraπŸ‘‰πŸ»08105039568 'kofa a bud'e take ngd, and mata kawai.


*COMMENTS*
*&*
*SHARE*
[11/5, 9:54 PM] Safeeya Aliyu: 🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳

*'KAUYEN 'YAR KADDE*

🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳




*Story & written by: Safiyya Aliyu Wakili*



*πŸ’«DA BAZAR MU WRITER'S ASSπŸ’«*


*we are here to make you happy, smile, educate and realized that we are best among all.........DA BAZAR MU MUKE TUN'KAHO*






*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*



πŸ…Ώ4⃣1βƒ£βž‘4⃣2⃣


°°°°°°°°°°°°°°°°°°°


Tafiya nake ba tare da sanin inda nake jefa 'kafata ba. jefa 'kafa kawai nake. Har na kusa barin layin sai ga Husna, parking tayi tare da fitowa daga cikin motan, bata ce dani komai ba illah jan hannun na da tayi. Bata saken hannun ba har sai da ta danganani da motar, zaunar dani tayi tare da rufe sead d'in ta zagayo mazau nin ta ta shiga tare dawa mota key muka bar wurin.


Tafiya muke babu maice da kowa komai, don kowa na fama da tulun tunanin a cikin ransa.


Har muka zo gida tai parking, sake jana tayi ta fito dani tare da shigewa dani cikin gida, niko binta kawai nake kamar ra'kumi da akala.


Babu kowa a falon, don haka d'aki na tayi dani, zaunar dani tayi a gefen gado tare da barin d'akin ba tare da tace dani komai ba.


Niko ina nan zaune inda ta barni har na tsahon wani lokaci, tunanin nake shin ma wai meye asalina?, waye ubana?, ina dangin mamana da na babana suke?


Anya ma 'yar halasace ni?


Tun da nake tunanin hakan bai ta'ba zomin ba sai yau, kuma mama bata ta'ba bani labarin wani nawa ba. Don haka yau ina da bu'katan son sanin meye asalina?


Farko ma dai waye ubana?, ban ta'ba tambaya ba tunda nake, don na taso na ganni tare da uwata ce kawai.


Ban ta'ba ganin wani yazo wajen ta da sunan d'an uwan ta kona babana ba.


Kai anya kuwa? da dai sake, da kawai alaman tambaya.



Dagani sai ita kawai, babu dangi ko guda d'aya.


Akwai sanda aka ta'ba min gorin asali amma ko kad'an banji wani abu akan haka ba.


Don da naji wani abu dana tunkari mama da maganan tun a lokacin, da yake lokacin bansan ciwon kaina ba.



Na d'au lokaci mai tsayi ina ta faman tunanin da zancen zucci, wanda har kaina ya fara min ciwo.


Tashi nayi na shiga toilet tare da sakin ma kaina ruwa, hakan yasa naji d'an sanyi kad'an.


Don haka sai na fito bayan na cire kayan jiki na tare da d'aura towel a jiki na.


Goge jikin nayi ba tare dana shafa komai ba na bud'e wardrop na d'au dogon riga mara nauyi nasa .


Kwanciyan nayi tare da cigaba da tunani na.


A haka barci ya d'auke ni, ranan na manta da zancen wani office.


Don duk ringing d'in da waya ta take tayi banji ba Sam.


Bani na tashi ba sai bayan la'asar, kuma ma Aisha ce ta shigo ta tasheni.


Mi'ka nayi da sallati, sa'annan nayi addu'an tashi daga barci tare da kallon Aisha itama ni take kallo.


Murmushi tayi min tare da cewa" yaushe kuka dawo?" ya mutsa fuska nayi tare da cewa" d'azu".


"Shine koki fad'an kin dawo? ina can inta faman tunanin har yanzu baku dawo ba. Tunanin zuwa d'akin nan nayi shine na shigo na cima kina barci, gashi la'asar ta wuce bakiyi salla ba. Sai ki hanzar ta".


Sauke 'kafafuna nayi a 'kasa ba tare da nace da ita komai ba.


Toilet na nufa, wanka nayi tare da d'aura alwallah na fito.


Tana nan zaune inda na barta a bakin gado, wuce wa nayi na d'akko wani dogon riga ba'ki na zirah tare da saka hijabi.


Shimfid'a dadduma nayi tare da fara sallah, cikin natsuwa take komai nata.


A haka ta gaba tar da sallan azahar da la'asar, duk Aisha na kallon ta har ta idah tayi addu'a.


Bayan ta gama sai ta jingina kanta a jikin gado tare da rintse ido, hawaye taji yana son zubo mata matsewa tayi batai ba.


Sakkowa daga gado Aisha tayi tare da zama kusa da Zarah dafa ta tayi tare da cewa" besty meke damun ki?"


Shiru tayi bata bata ansa ba, "besty ina magana kinmin shiru".


"Mai ya faru?" bud'e runannun idanun ta tayi. Kallon Aisha tayi tare da cewa" babu komai".


Ganin yadda idanuwan nata suka rine ya'kara tayar ma Aisha da hankali, don haka.



Cikin lallashi Aisha tace" yanzu bazaki sanar min da damuwan kiba ko? haba my Zarah, don Allah gaya min, ni kad'ai kike da duk fad'in garin nan, idan baki gayan ba waza ki fad'a mawa? idan kuma so kike nai kuka kuma shikenan ".


Ta'karisa tana majin damuwa a zuciyar ta.


" Aisha kin ta'ba ganin baba na? kin sanshi? ko kin ta'ba jin labarin sa? wai ma anya ina da uba?" tace hawaye na zubowa daga cikin idanun ta.

Sakin baki Aisha tayi da mamaki tana kallon ta har ta idah zancen ta.


Tace" wani shegen yace baki da uba? eyeh!" .


"Waye? nace waye?" Aisha tace cikin masifah.


Kamo hannun ta nayi tare da cewa" ba kowa, babu wanda yace bani da uba. Nine nace ma kaina, domin ban ta'ba ganin uban nawa ba, ban kuma san asalina ba shiyyasa nace haka".


"'Karya kike akwai dalilin da yasa kika ce haka ban yadda da abinda kikace ba, idan kince haka mai yasa tuntuni baki ta'ba zancen nan ba sai yau da rana tsaka?"


"Husna ce tamiki gorin uba ko kuma wani matsiyaci ne?"


Murmushi nayi tare da cewa" nace miki babu kowa, wallahi babu wanda ya tambayeni ubana".


Ganin ta'ki yadda da zancen tane yasa ta kwashe abinda ya faru a gidan su surukan Aisha ta fad'a mata, ta'kara da cewa" Allah jikina na bani inada ala'ka dasu".


Shiru Aisha tayi don bata san mai zatace ba.


Don gaskiya bata san mahaifina ba, don 'kawayen ta na 'kauye sunsha ai bantani a gaban ta bata ko kulasu sunsha cewa ta rabu dani donni shegiyace bani da uba.


Don iyayen su sunce da ciki uwan na tazo garin ita da wata 'kawanta kuma bata wani jima ba ta haifeni, ana tunanin tayi cikin shegene iyayen ta suka koro ta.


To me zata ce?


Ganin Aisha tayi shiru yasa tace" gobe zan tafi keffi insha Allah, don inason nayi magana da mama ina son sani ni wacece? meye asalina? tun kafin lokaci ya kuremin".


Numfashi Aisha ta sauke tare da cewa" Allah kaimu, idan Hubby ya dawo sai na mai magana idan yaso sai mu tafi tare".


Gyad'a mata kai tayi ba tare da tace komai ba.


Zama sukayi shiru-shiru babu mai magana a cikin su, kowa tunani ne fal a zuciyar sa.




**********

Husna bayan tabar gidan su Zarah gidan su ta shiga, zuwa tayi har d'akin momyn ta ta same ta.

Momyn nace da ita" har kun dawo?" ita kuma nace da momyn" momy dama ba Hajiya MARYAM bane ta haifi Auwal? "

Da mamaki uwan ke kallon ta, sai tayi murmushi tare da cewa" ba ita bace ko momy?"

"Injiwa ya fad'a miki haka dan ubanki?"


"Su da kansu".

" Da kansu kamar ya?" tace fuskan ta cike da mamaki.


Nan Husna ta kwashe abinda ya faru tasanar mata.


"Eh hakane ba itace ta haifesa ba".


" To momy waye mahaifiyar sa?"


"'Kanwan MARYAM d'in Balki itace ta haifesa, yayin da 'kanin mijin MARYAM d'in yanka sance shine uban Auwal d'in".


" To ina suke momy?"


"Bakiji mai RAHAMA take cewa ba? koke da'ki'kiya ce? to ta rasu tun Auwal na jariri".


" To mahaifin nasa fah?"


"Ke ubanki tashi ni duk kin isheni da tambaya, maza bar nan wurin".


Cikin sanyin jiki ta tashi tabar wurin.


'Dakin ta dake kusa dana momyn ta ta bud'e ta shiga, zubewa tayi a kan cushion tare da buga uban ta fumi.


Tace" meye al'kansu da Zarah? tabbas akwai dangan taka na jini a tsakanin su, domin ban ta'ba lura ba sai yau akwai kama a tsakanin Zarah da Auwal kama ma na'kin 'karawa. Sai dai tafi Auwal hasken fata, shi kuma ya fita kyau".


"Tabbas akwai cakwakiya".............




*************


Bayan natsuwa ya zoma RAHAMA ne sai tace da mami cikin sanyin murya" mami anya kamace kawai tsakanin anty da yarinyan nan babu wani abu ba bayan shi?"


"RAHAMA kibar maganan, domin bamu da wani al'ka da yarinyan nan, domin daga jihar nasarawa ta fito kuma bamu da kowa namu dake can. Ikon Allah ne kawai" daga haka tayi shiru.


RAHAMA dai bata wani gamsu ba tace" anya kuwa mami? a dai bincika, don wannan kaman ya wuce misali".

Shiru mami tayi ba tace komai ba.

Ganin haka yasa itama RAHAMA tayi shiru.





***********


Abdul bai dawo ba sai wurin 'karfe shida da rabi, don sai da yayi sallan magariba sa'annan ya shigo cikin gidan.


Zaune ya taddasu jigum jigum, da mamaki yabisu da kallo dukan su, da alamu ma basuji sallaman saba.


Ta'ba kafad'an Aisha yayi firgigif ta dawo duniyar mu, kallon sa tayi tare da mi'kewa had'e da murmushin ya'ke tace" hubby sannu da zuwa".


Bai ansa mata ba sai ma cigaba da kallon ta da yake famanyi.


Shagwa'be fuska tayi tare da cewa" hubby ina magana kamin banza".


Kamo hannun ta yayi suka nufi cikin d'aki, har lokacin Zarah bata dawo ba ita, ta tafi can duniyar tunani.


Koda suka shiga d'aki zaunar da ita yayi akan sofa shi kuma ya du'ka a gaban ta tare da kallon cikin idan uwan ta yace" maike damun matana da har zan shigo bata san na shigo ba?"


Hawaye ne ya zubo mata, zaro ido yayi tare da tara hannun sa hawaye na d'iga a ciki.


Yace" My Esha lafia kike min asaran hawayen ki?"


Kwantowa tayi kansa tare da cewa" don Allah hubby kada ka matsamin na san sani abinda ke damuna, domin sirrin besty nane. and gobe tace zata keffi don Allah kamin izini muje tare".


Numfashi ya sauke tare da cewa" shikenan amma don Allah abar kukan nan, a rage damuwa don za'a shiga ha'kina gaskiya ".


" sannan magana tafiya Ku bari sai jibi Saturday sai na kaiku".


Cikin murna takai masa sumbata a goshi daga nan ta taimaka masa yayi wanka suka fito cin abinci.




Kwana biyu nan Zarah tayi sane cikin za'kuwa da damuwa kai har da fargaba ma.


Ranan da zasu tafi ta riga kowa shiryawa.


Bayan sun kintsa suka d'auko hanya....................






*COMMENTS*
*&*
*SHARE*
[11/5, 9:54 PM] Safeeya Aliyu: 🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳

*'KAUYEN 'YAR KADDE*

🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳




*Story & written by: Safiyya Aliyu Wakili*



*πŸ’«DA BAZAR MU WRITER'S ASSπŸ’«*


*we are here to make you happy, smile, educate and realized that we are best among all.........DA BAZAR MU MUKE TUN'KAHO*





*Dedicated to my lovely fan's*



*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*



πŸ…Ώ4⃣3βƒ£βž‘4⃣4⃣



12:40pm yayi musu a 'kofar get d'in gidan su Aishan, horn yayi mai gadi ya le'ko. Da sauri ya koma ya bud'e suka shiga.


Parking yayi Zarah ta fita daga cikin motan tabar Aisha, part d'in su ta nufa.


Zaune ta tarar da maman ta a cikin palo tana kallo tashan su na arna.


Jin motsin mutum yasa madam Gloria wai gowa, ganin Joy cikin wani irin yanayi kuma a baza ta yasa ta mi'ke tare da nufo ta.


Rungume uwan tayi tare da fashewa da matsanancin kuka.


Shafa bayan ta tayi alaman rarrashi har na tsahon wani lokaci, sa'an nan ta d'ago ta tare da cewa" mai ya farune Joy? lafia kuwa?" a lokaci d'aya ta jefo mata wad'an nan tambayoyin.


Kallon uwan tayi face to face tace" mama waye ubana?"


Kallon ta tayi da mamaki kwance akan fuskan ta tace" wani abu ya farune?"


Bata nata ansan taba ta sake cewa" nace waye ubana? yana ina? don ina bu'katan mahaifina a halin yanzu. Inason sanin dangina".



Kauda kai madam Gloria tayi tare da cewa" ya rasu".



"Ya rasu fa kikace? to naji ina 'yan uwan sa? ko nace dangin sa?"



Tace" bansan inda suke ba".

"Wani irin magana ne wannan mama, anya kuwa taya ma hakan zai kasance?, hakan ba mai yuwuwa bane".


" Mama banson wani 'boye 'boye nazo nan ne saboda inason nasan wacecce ni?"


"Joy nace miki baban ki ya rasu, ya rasu naji bai da 'yan uwane?"


"Eh" tace tana hararan ta, kallon uwan tayi na tsahon wani lokaci tana nazarin ta.


Can ta jefo mata wani tambayan tace" mama ina iyayen ki suke? tunda baki san na mahaifina ba ".


" Bani da" tace cikin masifa tare da cewa" banson ki sake min wani magana anan haka kuma ya isa".


"Bai isa ba mama, ko dai cikin shege kikayi kika haifeni ya raboki da iyayen ki?".


Hawaye ne ya fara kwaranya akan fuskan mama.


Cikin ihu tace" mama ba kuka nake da bu'kata ba, sanin ko wacecce ni nada matu'kar mahimmamci, kodai daga sama na fad'o?"


Mari uwan ta wanke ta dashi tare da cewa" ya isah, ya isa, haka Joy ".


Tana ri'ke da kuma tunta tace cikin d'aga murya" bai isaba, ba kuma zai ta'ba isaba waye ni mama? ki fad'a min koni wacecce ke ko cikin shegene kikayi ki sanar dani".


"Joy ni kike ma magana na rashin kunya? am your mom fah?"


"Nasani ai, nasan koke wacecce amma bansan waye ubana ba, to a fad'a minin ko nakai 'kara".


" Joy nice fah? kalli kiga mom d'in kice fah" tace tana mai juyo da Joy d'in tana fuskan tan ta.


Zarah tace" na sani nasan kece uwata shiyasa nake tambayan ki ubana, don bai yuwuwa macce tayi ma kanta ciki ba tare da namiji ba".



"Da namiji ake had'u a samar da ciki, mama ina ubana, d'an uwan mu'amalan ki?"


"Kada ki damu sanar dani bazan miki komai ba, ko shi kan shi kawai dai inason sanin shine, idan bashi ai yana da 'yan uwa. To sanar dani ina suke?"



Kuka mama ta fashe dashi mai tsanani, niko idona ya rufe bai dameni ba, don babu abinda nakeso a halin yanzu ko ta halin 'ka'ka.


Cikin kuka ta fara zaiyano minin da asalin ta har zuwa auren ta da babana da kuma sa'kon rasuwan sa da ta samu da kuma yadda sukayi da iyayen ta har tabar garin ta (idan baku manta ba na baku labarin maman Joy tun a farkon labarin).



Kuka suke dukan su babu mai lallashin wani, sun dad'e suna kuka kafin Zarah ta tsaigai ta tare da cewa" mama yanzu tunda kike dashi bai ta'ba gaya miki garin suba? ko wani nasa guda d'aya baki sani ba?"


Shiru tayi tana tunani kafin ta nisa tace" bai ta'ba gaya min ba, don a wani masallaci a Abia aka d'aura mana aure" .


Bata hakurin abinda namata nayi bayan hankali ya natsu.


A nan ne nake sanar mata da cewa na musulunta, bata wani damu da hakan ba tunda ubana ma musulmi ne.




*****

Aisha bayan fitan Zarah ta bita da kallo tare da girgiza kai idanun ta cike da 'kallah.


Dawo da idanun ta tayi kan mijin ta taga ita yake kallo.

Ganin tana son yin kuka yasa ya girgiza mata kai, had'iye kukan tayi tare da cewa" muje ciki to?" fita sukayi daga cikin motan tare da nufan part d'in Umman Aisha.


Sallama sukayi a bakin 'kofan shiga falon, aka ansa musu, ba kowa bane illah Muhusin dake zaune yana home work, shigo wa sukayi yana arab da fuskan sister d'in shi ya taso da gudu yazo ya rungume ta.


Tare da cewa" oyoyo anty Aisha? " murmushi tayi tare da cewa" sannu yaron Umma ina umman?"


"Tana ciki" yace tare da kallon Abdul yace" sannu da zuwa yaya Abdul".


Hararan wasa ya jefa masa tare da cewa" ban ansawa, sai yanzu ka ganni?"


Murmushi yayi tare da sunkuyar da kai yace" yi ha'kuri yaya".


"Nayi to oyah zo" zuwa kusa dashi yayi ya rungume sa tare da masa yadda yaga Aisha tayi.


Dariya Aisha tayi tare da cewa" bari naje na kira Umman".


"Barta bari naje na d'an huta yanzu haka barci take kada a taso ta".


" Yauwa hubby ka amince mu kwanan ko?"


"To basai kisa na amincen ba, komin dare yau zamu koma tunda kuka taso tafiyan da ba'a shirya ba".


Yace yana hararan ta, murmushi tayi tare da cewa" Allah baka ha'kuri mijin Aisha to muje na rakaka".


"Barshi na hutar dake, maza kuyi abinda zakuyi saboda mu koma da wuri".


" To" tace dashi tana tsaye har yabar falon sannan taja hannun Muhusin sukayi ciki.


Sallama sukayi a bakin kofan Umma ta ansa musu, shiga sukayi.


"A'a wa nake gani kamar Aisha na?" turi baki tayi tare da cewa" waye to Umma idan bani d'in ba?"


Murmushi tayi tare da cewa" maraba da mutan Habuja, lale marhabun da amare".


Murmushi mai 'kayatarwa Aisha tayi tare da nufan inda Umma take tare da zama kusa da ita.


Tace" ina wuni Umma" "lafia lau, ya kuke?"


"Lafia qalau Umma" "to ya mai gidan naki?"

"Yana lafia, gashi can ma tare mukazo".

"Maraban ku, ina d'ayan amaryan?" cewar Umma cikin sigan tsokana.


'Kwala ya taru mata a idanu fuskan ta ya canza.

"Menene Aisha? ina take?"

"Tana part d'in su, lafia take?" tace kamar za tai kuka" eh".


"Anya kuwa Aisha? nafa sanki musamman akan Joy, yanzu haka wani abu ke damun ta".


" Lafia qalau take Umma, sai dai wani abu dake damun ta shine mukazo mama ta fad'a ma".


"Kuma ma ta musulunta yanzu Fatima take muna cema ta Zarah".


Washe baki Umma tayi tare da cewa" kai masha Allah, alhamdulillah. Amma nayi mata murna sosai, Allah kasa maman ta itama ta musulunta ".


" Ameen Umma".


"To meke damun ta kuma?" shiru tayi ba tace komai ba sai ma wasa da yatsun hannun ta da take.


Ganin haka Umma ta gane bata son sani don haka bata matsa mata ba sai ma cewa da tayi" Allah ya yaye mata damuwan to".


"Ameen Umma" tace cikin sanyin murya.


"Tashi kije ki kaima mijin ki ruwa da abinci".

Tace" yaje ya dawo" da mamaki Umma tace" yaje ya dawo kamar ya? daga zuwa kuma ko ruwa bai shaba, ki barsa ya fita amma dai babu hankali a lamarin ki".


"Sai ki kirasa a waya kice yazo yaci abinci".

" To Umma" tace tare da ciro waya a cikin jakan ta.


Koda ta kira sanar mata yayi bashi a kusa, don haka sai ta fad'a ma Umma, Umman tayi mata fad'an kada ta sake haka.



******

2:10pm Zarah ta shigo part d'in su Aisha ita da maman ta, Zarah ta gaida Umma. Aisha ta gaida maman Zarah.

Sai suka kama fira kuma, suna firan ne Abdul suka shigo tare da baban Aisha da yake Umma ta kirasa to ya dawo kenan shima Abdul ya dawo suka had'u a compound d'in gidan shine suka shigo tare.


Gaishe da su Umma yayi cikin girmama wa, su Zarah suka gaida baba.


Daga nan baba yayi musu nasiha na zama lafia da ha'kuri da juna.

Daga nan sai Abdul yace bayan baba ya sallame su" idan kun gama ina jiran ku saboda kada muyi dare" daga haka yayi musu sallama suka ya fita.


Yana fita yasa mai gadi shigo musu da kayan abinci ya kira Aisha ya'kara musu da kud'i, albarka suka sa masa sosai sa'anan suka mai godiya.


Basu suka bar gida ba sai da sukayi sallan la'asar sannan suka d'auki hanya.





********

Saura sati biyu bikin Husna aiki yama Zarah yawa ga shirye-shiryen biki ga aikin office, haka take ta fama, komai za'a sai Husna ta nemo ta. Tsare-tsaren biki itace kan gaba.

Anfara gudanar da biki tun biki ya rage saura sati d'aya, yau wannan bidi'an gobe wancan.


Kuma har yau Zarah bata ga ango yazo ba, daga 'kawayen amarya sai abokan ango aketa gudanar da abubuwa.


Da kyau dinner da za'ayi ana gobe biki bayan walima, sai Husna ta shiga damuwa na rashin halattan ango duk wurin shagulgulan biki, ta kuma gaji da tambayan da 'kawaye suke mata na rashin ganin angon, tun tana 'karya yanzu haka 'karyan ya 'kare kuma a rasa mai zata ce dasu.



Zaune take jugum a cikin d'akin Zarah ta buga uban ta gumi, har Zarah ta shigo bata san ta shigo ba.


Zuwa kusa da ita Zarahn tayi ta zauna tare da dafa ta.


Waigo wa tayi jin an ta'ba ta, ganin Zarah ne yasa ta rungume ta tare da fashewa da kuka.

Bubbuga mata baya Zarah tayi tare da cewa" lafia Husna? mai ya faru? mai akai miki?"

Cikin kuka tace" Zarah Auwal bai sona, da da yadda zanyi dana cireshi a cikin raina na huta. Zarah ina tsananin 'kaunar sa".


"Ni kad'ai nake haukata tunda aka fara shirin bikin nan, dai-dai da sau d'aya ya'ki halattan biki ko guda d'aya da aka gudanar. Gashi a halin yanzu 'karyana ya 'kare".


" Ya zanyi Zarah? ki gayamin, gashi anjima za'ai dinner ban san yadda zanyi yai attending ba".


Tace tana mai fashewa da matsanancin kuka.


Itama yanzu Zarah ta fara jin haushin abinda angon nan yake, mai yake ta'kama dashi?


Mai yasa baison Husna? Husna yarinya ce kyakkyawa, fara doguwa ga hanci ga zarara zaran yatsu, idanu.


Jiki ma masha Allah komai akwai, babu abinda tarasa na wanda d'ana miji yake so.


Uwa uba ilimi boko da na islama.


Ya fara bani haushi inason sanin abinda yake ta'kama dashi.


'Dago Husna daga jikin ta tayi tare da cewa tana mai kallon cikin idan uwan ta had'e da share mata hawaye.

"Husna tashi muje mu same shi" zaro ido tayi tare da cewa cikin tsoro" gaskiya bazan iya zuwa ba inajin tsoro gaskiya ".


Tsaki Zarah tayi tare da cewa" tsoro ya kasheki ya kuma kaiki ya baro".



"Tashi dallah muje" tace tana mai jan hannun ta.


Girgiza kai tayi idanun ta cike da hawaye tace" bazan iya ba, ya Auwal bai da mutunci nemo wani mafitan kawai amma ba wannan ba".



"Kirasa a waya to" tace" ko nakira sa ba zai d'auka ba".


"Bani number wayar sa" tace tana mai d'ako wayar ta.


Karanta mata Husna tayi ita kuma tana rubutawa.


Dialing number tayi, yayi ta ringing ba'a d'au call d'in ba.


Sake kira na biyu tayi sai da ya kusa tsinkewa sannan aka d'aga amma ba ai magana ba.


"Hello!" Zarah tace.


Zaune yake zumbur ya mi'ke tare da cewa" my baby, my Joyyyyyyyyyyyyyyyyyy"..................







*COMMENTS*
*&*
*SHARE*


Luv you all my fan'sπŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko

2 Comments On KAUYEN YAR KADDE
avatar
abdulrazak

1 year ago

Reply

Next pls

avatar
abdulrazak

1 year ago

Reply

Next pls

Please Login or Register in order to submit comment