Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

*Ayushailiasu.blogspot.com* Page
126 to 130 Tinda yaya kamal yai tozali d sarah yakasa
gane wane irin abu zuciyarsa ke saka masa gaba daya
tinaninsa ya koma kanta gashi baisan ita wace ba amma
zuciyarsa ta addabeshi d tinaninta ya kasa tantanceshi
kuma,yana zaune a dining amma abincin d yakecima
kawai ci yake yana hararo kyakkyawar surar sarar, ajiye
spoon din hannunsa yayi akan plate ya dau cup y zuba
juice,lokacin d yakai bakinsa y saki wani tattausan smillin
shi kadai sannan y kurbi juice din. Bayan y kammala cin
abincin y watsa ruwa ne yace d su mujahid su shirya
zasu fita su dan zaga gari, murna gurinsu mujahida
kamar me ,nan da nan suka shirya sukaiwa mama
sallama,sunkai dai dai kofa sumy tace yaya kamal ina
zuwa? Yace zamu dan zaga garine, cikin shagwaba tace
plxx yaya nima zanje,kallonta yai yana murmishi yace
srry sistr we will b back soon insha Allah yaja hannunsu
mujahid suka fice suka barta saroro tsaye a gurin. Da
yamma sakaliya bayan abbah y dawo dg kasuwa yana
zaune a palo suna hira da mama yake cewa kinga yaran
nan har yanxu basu dawo ba sun shiga gari,mama tace
aikuwa kaga shuru har yanxu, yace Allah y dawo dasu
lafiya dai tace amin sukaci gaba d hirarsu. Ana kiran
sallahr magriba yaya kamal dasu mujahid suka shigo
lokacin abba ya tafi masallaci suma alwala sukai suka
nufi masallacin. Suna zaune a palo ne byn anyi sallah
isha,abba cikin murna d farin cikin ganin yayan nasa
yake musu barka d dawowa d tanbayar ya karatu? cikin
farin cikin ganin mahaifin nasu sukace alhmdllh tare d
bashi labarin wahalar boarding, kallon tausayi abbah
yaimusu yace aidama karatu sai hakuri dan haka ku kara
hakuri d dagewa wajen karatu Allah yai muku albarka ya
bada ilimi mai amfani gaba daya suka amsa d Amin
harda kamal daya budo labule yashigo palon,karasowa
yai y zauna kusa d abba y gaidashi,y amsa masa tare d
tambayrsa ya karatu yace alhmdllh. Cigaba d hira sukai
amma kwatakwata hankalin kamal baya kan hirar, dan
gyara zama yayi yace inasu sumy ne bangansu b?
Mujahid ne yace wllh yaya kamal suna daki danaje m
koro ni aunty surayya tayi, abba ne yace je kiramin su d
sauri ya tashi yanufi dakinsu, shiko kamal azuciyarsa
murna yake yana cewa dama ina sane n tambayesu dan
so nake na kara ganin wannan kyakkyawar halittar d
………… bai karasa zancen zucin d yake b suka shigo
palon d sallama,sallamar d sukai ne t katseshi d sauri y
dago kansa tare d sauke idonsa akan sarah,bayan sun
xauna ne suka gaida abba d yaya kalam,abba yace kamal
kaga munyi bakuwa ko? Dasauri ya amsa da eh wllh
abba dg ina take? Nan abba ya fayyace masa matsayin
sarah a gurinsa take kamal yaji tausayinta y mamaye
masa zuciya. *BA DAI KAFI SON TA BA daga www.hausaebooks.com.ng* *Written by
Ayusha Iliasu.* *Story by Hawwa Saleh.* *Dedicated to
Abeeda n Baseera.* *_Ayushailiasu.blogspot.com_*
Abdullahi Aliyu Alkas Facebook.com/Abokinhira
WhatsApp Me 09038188199 Facebook.com/Abokinhira
Page No. 11 Page 136 to 140 Tinda yaya kamal y koma
dakinsa b abinda yake hararowa sai kyan surar sarah a
yanxu xuciyarsa ta gama tabbatar masa da lallaifa inba
kallon tausayi kake mataba to kallon so kake mata, tinani
yashiga yi to wane bangare n xuciyarsa xai bi? Furzar d
iska yai dg bakinsa ya mike yake ta zagaye tsakar dakin
hannunsa n makale a bayansa ya daga kansa sama sai
sintiri yake yana kaiwa d kawowa a dakin, haka y kwashe
tsawon mintina ashirin yana zazzagayawa bai samo
amsar b, fitowa yai dg dakin ya nufi farfajiyar gidan dan
hutawa. Sannu d fitowa abbah cewar sury d sarah da
suke tsaye a bakin kitchen sun gama wanke
wanke,kallonsu abba yai yace sannunku d aiki Allah yai
muku albrk suka amsa d amin abba, cigaba d magana
yai yace sarah ki shirya d yamma idan nadawo xamuje ki
nuna mana gidanku, wani zar taji a cikin jininta saida tai
jimmm kafin tayi magana sannan t nisa tace to abbah
Allah y dawo dakai lafiya yace amin,cikin marairaicewa
sury tace abba damu za'a yace a'a yasa kai yai waje.
Tinda sarah taji batun zuwa nuna gidansu gaba daya
kuzari yai kaura dg gareta zazzafan zazzabi taji yana
neman kawo mata farmaki sbd tsabar tsoron d takeji n
matar uba, ta ke taji tunanin kuncin rayuwar da tafada
abaya yana dawo mata, gado ta nema t kwanta, tinda t
kwanta b abinda take sai kwaranyar d zafaffun hawaye
tsoronta Allah tsoronta kar aje acewa ammi anganta taje
ta sake bunko mata asirin d zai rabata da wannan
gidan,haka tai ta tinane- tinane ba ita t tashiba saida akai
kiran sallahr azahar,toilet t shiga t dauro alwala ta
gabatar d sallahr axahar sannan t jero nafila raka'a biyu,
addua ta shiga jerowa tare d ambaton sunayen Allah
tsarkaka d siffofinsa madaukaka akan Allah y tseratar da
ita dg sharrin ammi ya makantar d ganinta dg kanta ya
toshe kunnunwanta dg jin labarinta y daure kafafunta dg
zuwa gurin boka. tadau lokaci tana jero addua gami d
kamun kafa d Annani muhammad SAW afadar Allah
sannan ta shafa,byn ta idar d sallahr saida t jima sannan
t tashi ta fito palo gurinsu sumy. Hirar makarantar
islamiyya su sumy suke amma sam sarah hankalinta
baya kansu dan tuni jikinta yai la'asar ta gama tsinkewa
d wannan tafiyar d abba ya bijiro mata d ita,abincin rana
kasa cinsa tai sbd tinani ya cushe mata cikin, haka dai tai
yinin wannan ranar b dadi,byn tayi sallahr laasar ne ta
sake wanka d shiri karfe 4:30 n yamma daidai abba y
dawo, shima shiga yai yasake shiri sannan ya ce tafito,
yaya kamal shine yai driving abba yana seat din gaba
mama d sarah d kuma auta mujahid suna seat din
baya,kafin yaya kamal y tada mota abba yace d sarah tai
directin din shi zuwa unguwar,tsaf tai masa saida abba y
tabbatar kamal y gane sannan suka dau hanya sai
shagari quarters,tinda suka fara tafiya b wanda yai
magana shiko yaya kamal sai satar kallon sarah yake ta
mirror,sarah kuwa batasan yanayi ba dan hankalinta
baya jikinta ta tafi duniyar tinani wanda ni kaina bazance
g irin tinanin d takeyiba ganin sun shiga lungunsu ne
yasata yin wani gwauron ninfashi d ajiyar juciya
k'wallace ta gangaro dg idonta kan kuncinta daidai
lokacin sukai ido hudu d umma, kallo daya za kaiwa
sarah ta baka tausayi, ninfasawa umma tai tace alhji
kaga kuka takeyi d sauri ya juyo yace haba sarah kukan
me kikeyi?cikin shasshshekar kuka tace wllh abba idan
ammi t ganni saita sake yimin asiri kun koreni,
tausayinta ne y mamaye zuciyar abba cikin tattausar
murya yace insha Allah baxata ganki ba kuma nace miki
ai b gidan zamu shiga ba kawai nuna mana zakiyi mu
juyo,handkchf din dake hannun yaya kamal abba ya
karba y mika wa sarah yace t share hawayen,kanshin
tiraren jikin sane y xiyarci hancinta take taji wani sanyi a
ranta, shiko yaya kamal xuciyarsa cike d tausayin sarah.
Haka sukaci gaba d tafiya har suka isa kofar gidan,saida
suka dan gota gidan kadan sannan sarah tace g gidan
can t nuna musu shi d hannunta, gidane matsakaici n
bulo yasha filasta d malale a kofar gidan anmasa milk
din fenti atakaice gidan masu rufin asirine baxa'a ce gdn
talakawa ba,sai da abba y tabbatar d nan ne gidan
sannan suka juyo d motarsu suka dau hanyar komawa
gida,ganin d sarah tai sun bar lungun ne yasa taji wani
nishad'i a zuciyarta rufe fuskarta tayi d handkerchief din
hannunta tana murmushi. Niko d nake biye dasu nace
ikon Allah ashe akwai masu gudun mahaifarsu. *BADAI
KAFI SONTA BA* *Written by Ayusha Iliasu.* *Story by
Hawwa Saleh.* *Dedicated to Abeeda n Baseera.*
*_Ayushailiasu.blogspot.com_* Page 141 to 145
Isowarsu gida yaya kamal yai parkin kowa y fito,bayan
sun shiga ciki ne,yaya kamal y kwallawa mujahid kira
yace yaje gurin sarah y karbo masa handkerchief dinsa
yace to, d sauri mujahida y nufi dakin su sarah yace
aunty sarah yaya kamal yace kibashi handkerchief dinsa
ido suka hada d sumy d mamaki sumy tace meyakawo
handkerchief din yaya kamal gunta a zuciyarta take
maganar,kauda kai sarah tai dg kallon sumy ta mikwa
mujahid badan tasoba dan baxata iyacewa y bar mataba
gashi tana son kamshin turaren jikinsa,karba yai d sauri
ya juya y kai masa. Tinda yaya kamal y karbi
handkerchief din y shige daki b abinda yake illa san
sanar sa yana kissin dinsa ynx y tabba xuciyarsa ta kamu
d son sarah ji yai baxai iya wanke hawayen b sbd lipstick
d tasanya a lebanta ya gogu a jikinsa yai alamun kiss
tamkar ita yakewa ,tinani y shigayi ya xaiyi y isarwa
zuciya sakonta zuwa wata zuciyar, zancen zuciya y
shigayi yana cewa gashi gobe zan koma schl gaskiya
baxan iya tafiya b tare d na bayyana wa sarah ina sonta
b,wata zuciyar tace haba malam kayi azarbabi kavari ka
dawo wani hutun mana lokacin ta kara wayewa d
girma,banyi aune ba naga yaya kamal y daki side drower
din gadon sa d karfi saida n dan tsorata afili yace what?
yama zaai n bari saina dawo kafin lokacin kuma wani ya
ganta sun kulla soyayya tinda bata san ina sonta b kuma
nasan abba aura mata shi zaiyi indai tace tana son sa,
kama habarsa yayi ya karasa maganar d tirkashi wannan
babban lamarine, ya zan kamo bakin zarensa gashi gobe
xan koma schl?. Ilailika dai,ka nemo kai kadai bada niba
dan nayi nan ni. Tinda sarah tai sallahr isha ta haye gado
taja blanket t rufa ba abinda takeyi sai tinano kamshin
tiraren yaya kamal, tambayar kanta tashigayi dalilin
meyasa nake son kamshinsa?xuciyarta tace t bata amsa
d cewa sonshi kikeyi shiyasa kike son kamshin sa kuma
duk lokacin d kuka hada ido dashi gabanki yake faduwa
bakya kara kallonsa,lallausan murmushi tasaki saboda t
amince d abinda xuciyarta tafada mata dan ta tabajin
friends dinta suna hirar alamomin soyayya a schl kuma
dg cikin abinda sike fade harda wadannan d ta tsinci
kanta a ciki,gyara kwanciyarta tayi tai rigingine idonta a
sama tana kallon fan din dake busa mata ni'imtacciyar
iska,limshe idonta tayi game d sakin murmishi taci gaba
d tunani karfa na fad'a tarkon son yaya kamal naje
nashiga tasku shi baya sona,daga can barin zuciyarta
tace mata dalla banza ke baki lura d abinda yake mikiba
ne kamar b mace ba musamman idan kuka hada ido
bakiga yanayin d yake miki d giraba gami d kashe ido to
ai suma alamun nuna soyayya ne,wata muguwar k'ara
naji sarah t saki ta juya ta rungume pillown d ta tada kai
tace Alhmdllh indai hakane kuwa na dace d masoyi,kara
rumgume pillown tayi gami d kissin dinsa tace I love u
yaya kamal,rufe bakinta ke dawuya tana murmushi sury
t shigo, dan dukan kafarta tayi tace mutuniyar smillin
din me kike ne? ko kodai kodai……………? sbd sury ta
gama karantar yaya kamal tsaf ya fada tarkon son sarah,
harara sarah t watsa mata tace kodai me? Dariya sury
tayi tace ba komai munacan muna jiranki a palo kinanan
kina smillin ke kadai har yaya kamal yashigo yana
tambayarki, dad'i ne y kama sarah d taji ta ambaci
sunan abin sonta saidai t basar d zancen t hanyar cewa
kyaji dashi dai suka topic n hirar. *BADAI KAFI SONTA
BA* Abdullahi Aliyu Alkas Facebook.com/Abokinhira
WhatsApp Me 09038188199 Facebook.com/Abokinhira
Page No. 12 *Written by Ayusha Iliasu.* *Story by
Hawwa Saleh.* *Dedicated to Abeeda n Baseera.*
*_Ayushailiasu.blogspot.com_* Page 146 to 150 Yaya
kamal ne kwance kan gadonsa yai d'ai-d'ai tinani yake
yadda ya zaiyi y tari sarah d wannan maganar? haka
yaita t sakawa d kuncewa baisamo mafitaba, gashi bai
kara sa sarah a idonsa b balle yai yunkurin bayyana mata
manufarsa ga km sammako zaiyi ya tafi,hk dai har bacci
ya daukeshi. Bangaren sarah kuwa abin sharrr yake
gwanin ban sha'awa dan baccinta tasha bil hakki ba tare
d tinane tunane ba dan ta gama ydd da abinda zuciyarta
ta shaida mata yaya kamal sonta yake. Yaya kamal ne
cikin shirin tafiya makaranta fuskarsa a daure ya karaso
cikin palon inda su abba suke xaune, rissinawa yai y
gaidas,yanayin d abba yaga dan nasa y shigane
yasanyashi tambayarsa meya faru naganka haka? ko
bakason komawane kaji dadin gida?sakin fuskarshi yai
yace bakomai abba bacci ne kawai a idon nawa shiyasa,d
mamaki abba y sake kallonsa gami d dafa kansa yace
haba son meya hanaka bacci? Kamal dai y kara bashi
amsa d bakomai,fatan alkairi abba d mama sukai masa
tare d adduar Allah y kaishi lafiya,amsawa yai d amin y
mike jiki sakaka b kwari ya nufi kofa,saida yakai bakin
kofar ya juyo yace mama inasu sumayya bamuyi
sallama b? Kaji su yaya kamal d wayo dan yaga sarah ne
y tambayesu fa mikewa mama tayi tace bari nakirasu
to,dad'ine y kamashi zaiga abar begensa d sauri y karasa
yin waje yana cewa a ransa sa biyoni yadda zanfi karewa
dear ta kallo. Yana tsaye jikin motar abba suka karaso
inda yake suka tsaya, face to face sukai d sarah wani dadi
ne yaji kamar me ya dinga aika mata sakonni iri-iri,
sundau lokaci suna hira idan yai yunkurin kiran sarah
gefe ya sanar d ita bukatarsa sai km ya kasa sbd kunyar d
yake d ita hakadai y hakura har sukai sallama sukai masa
Allah y tsare hanya ya tafi. Abba ne y kalli umma yace
hajiya anya yaron nan k'alau yake kuwa kinga yadda y
fito fuska a daure? Umma tace nagani ko bayason tafiyar
ne ko?oho dai abba yace ya kara da cewa koma dai
menene Allah y kyauta y kuma kaishi lafiya umma tace
amin (nan kuwa basusan soyayya ce take dawainiya
dashi b). Bangaren sarah kuwa bataso tafiyarsa ba dan
yanzu batason yai nisa d ita burinta kawai ya bayyana
mata soyayyarsa gareta tai alkawarin zata karb'eta
hannu bibbiyu dan ta tabbata tayi dacen masoyi dan
kamal yarone nitsattse mai hankali g biyayya, uwa uba g
ilimi addini d n boko, kyau kuwa kamar shi yayi
kansa,gashi dogo b gajere b km yana d dan jikin d
baxa'ace masa siririba ga kunya kamar wata mace dan
ita kanta sarah tayi mamakin yadda yake kallonta ido
cikin ido dan yadda sury t bata labarinsa ba haka bane,
niko nace soyayya ce t sanyashi canjawa , d ganinsa zai
iya soyayya tinda bai cika surutu any how b,sarah nima
n tayaki murna Allah y sa kamal y zamto abokin
rayuwarki dan nasan zaki samu kulawa d kwanciyar
hanka. Karfe 12:00 daidai mota t saukeshi a bakin gate
din schl karasawa cikin hostel yai ya ajiye kayansa
sannan ya nufi toilet y watsa ruwa,gado ya hau y kwanta
bayan y fito dg wankan ko yayi bacci ya rage gajiya, nan
bacci yace ina baiga mahalli a idon sa ba tinda soyayya
ta k'ek'asar dashi,wata duniya ya tafi a takaice dai akirata
d suna duniyar tunani, iya bakin k'ok'arina nayi na naga
n bishi dan jiyo irin tinanin d yake amma inaaaa tuni
jirginsa y daga y barni a kasa inata zare ido kamar
mazarin tsirehaka dole ina gani n hakura d rahotan gurin
amma f nasan b wani abu bane banda sak'onnin son
sarah d zasuyi tamai zarya suna miko gaisuwa d jinjina a
fadar zuciyarsa suna fadin angaida masoyin
sarah………… gaisheka mai kaunar sarah …………
takawarka lafiya masoyin sarah………taka asannu asannu
ka isar d sakon zuciyarka a zuciyar sarah………… haka dai
zasuyita kawo gaisuwa. *BA DAI KAFI SON TA BA daga www.hausaebooks.com.ng*
*Written by Ayusha Iliasu.* *Story by Hawwa Saleh.*
*Dedicated to Abeeda n Baseera.*
*_Ayushailiasu.blogspot.com_* Page 151 to 155 *AFTER
4 WEEKS* Yau juma'a yaya kamal yai niyyar zuwa gida
sabida y kasa samun nutsuwa, tinanin sarah ya
addabeshi dan haka ya kud'iri aniyar yau zaije y bayyana
mata sirrin zuciyarsa, bayan sallahr jumaa ya hau
kiciniyar shiri, misalin karfe hudu n yamma ya baro cikin
schl zuwa , titi yai saa yana zuwa y samu mota y hau sai
birnin dabo,ana kiran sallahr magriba ya sauka gida,
lokacin abba yatafi masallaci, mamakine y kama mama
sabida zuwan kamal ba zato b tsammani,abinda bata
tab'a ganin yai musu irin wannan zuwanba, gaisawa d
mama sukayi take tambayarsa lafiya dai kamal kake tafe
yanzu yace lafiyalau mama, tambayar abba yayi, tace y
tafi masallaci, alwala shima yayi ya nufi masallacin.
Dawowar abba dg masallaci ne mama ke sanar dashi
zuwan kamal,baki bude yace kamal tace kwarai,yace
inceko lafiya yake tafe yanzu? Mama tace na tambayeshi
yace lafiyalau, yace to madallah abba yana rufe baki
kamal ya shigo y nemi guri dan nesa d abba y zauna
sannan ya gaida abban, bayan sun gaisane abba yake
cewa kamal lafiya kake tafe yanxu ba notice, dan
murmushi ya saki gami d shafo keyarsa yace wllh lafiya
lau abba kawai dai naji inason nazo nai weekend a
gidane, shima abba mamakin abin yake yace to
madallah sannan y tambayeshi y karatu yace
alhmdllh,tashi yai yashiga dakinsa ya watsa ruwa sannan
y kara fitowa palo lokacin su sarah suma suna zaune
suna kallon wani film,dagowar d sumy tai suka hada ido
dashi tace laaaaaa yaya kamal yaushe ka dawo, guri y
nema y xauna yace dazu nazo wallahi, sannu d xuwa
sukai masa harda sarah d bakinta yaki rufuwa dan
murna, cikin shagwaba sumy tace amma yaya b notice
da banyima delicious ba,dariya tabashi yace ayi hakuri
aunty sumayya,gaba dayansu saida sukai dariya hardasu
abba dan jin yace aunty,turo baki tayi tace to yaushe
zaka tafi sainayi maka snack? yace sunday zan tafi tace
yawwa yayan Allah y kaimu sukace amin. Yau asabar
antaso dg islamiyya su sumy d kawarsu aisha suna tafiya
dan sarah bata jeba kanta na ciwo, sumy ce t kamo
hannun aisha suka koma gefe sukabar sury ita kadai,sury
tace gulma dai b kyau sukace eh din,sumy tace k'awata
wallahi nakamu d son yaya kamal fa ya zanyi ya gane?
Dariya aisha tayi tace haba qawas bakisan dabara xakiyi
ki janyo hanlalinsa b? Sumy tace kedai fadamin, nan
aisha ta zayyana mata yadda zatai sai d tagama sumy
tace wllh aisha duk b wanda banyib amma yaki ganewa,
(ashe dama duk abinda sumy keyiwa yaya kamal sonsa
takeyi)kaka tsara kaka,aisha tace tabb saidai ki fadamasa
to, wani mugun kallo sumy t watsawa aisha tace a
matsayina n mace zance inasonsa lallai aisha soma kike y
rainani, batare d taji me aisha zatace ba t janyo
hannunta tace zomu tafi dalla, itakam sury d ke tsaye a
gefe tana jiransu tace angama gulmar kenan sukace eh
sanna suka rankaya sukaci gaba d tafiya. Weekend haka
y kare yaya kamal bai samu y cimma burinsaba sbd
matsanancin ciwon kai dayake damun sarah ko palo
bata fitowa,haka ya shirya ya koma schl cike d tunanin
sarah, d daddare ne abba yaga ciwo na k'ara gaba yace d
mama tinda gobe monday d safe sai kuje asibiti tace to
Allah y kaimu. Gari n wayewa suka shirya sukaje
asibiti,gwaje gwaje akaiwa sarah an rasa abinda ke
damunta, haka likita yayi mata yan tambayoyin d yayi
mata prescribing magani suka dawo gida, bayan abba y
dawo gidane dg kasuwa mama ke shaidawa abba abinda
likita y fadamata cewar baiga wani ciwoba iya gwaje
gwajen d yai mata,abinne y daurewa abba kai ya shiga
tinani wannan to wace irin cuta ce. Abdullahi Aliyu Alkas
Facebook.com/Abokinhira WhatsApp Me 09038188199
Facebook.com/Abokinhira Page No. 13 *BADAI KAFI
SONTA BA* *Written by Ayusha Iliasu.* *Story by
Hawwa Saleh.* *Dedicated to Abeeda n Baseera.*
*_Ayushailiasu.blogspot.com_* Page 161 to 165 Kwana
biyu a tsakanin zuwansu asibiti ciwo y canja salo,duk
maganin d aka bata a asibiti kamar k'ara ciwon
sukeyi,ashe dai wasa farin girki ciwo y ta'azaxxara har
takai sarah tana sumbatu zantuttuka barkatai ba kan
gado bare n kujera hankalin abba d mama yai matukar
tashi,shawara suka yanke akan sukaita gurin mai
maganin hausa,aikuwa basuyi wata wataba suka dauketa
saigun mai maganin,yadda mai maganin yaga sarah nayi
ne ya sanyashi karanto wasu ayoyi dg cikin alkurani mai
girma, take wata murya tafara bayyana kamar muryar
yan yara tana cewa aikosu akai su salwanta hankalin
sarah, wata zabura d mama tayi d jin mugun nufinsu
neman tsari tashigayi d ambaton Allah,mai magamin ne
y tambayesu waya aikosu sukace masa bilki ce tasa aka
aikomu,take mai maganin yaita karanto musu ayoyin
alk'urani saida y tabbatar sunbar jikinta sannan y hado
musu magunguna d zata dinga amfani dasu yace kuma
azo a ringa karbar mata rubutun tsari duk sati, take abba
y biyashi kudin maganin d alkawarin shine zai dainga
zuwa yana karbar rubutun. Alhamdullih sati biyu d fara
amfani d maganin sarh t warke kamar ba itaba amma
duk d haka abba yace baxata daina amfani d maganin ba
saboda kariya d neman tsari dan haka duk sati saiyaje ya
karbo mata rubutun. Bangaren yaya kamal kuwa yaga b
sarki sai Allah y hak'ura d tunane tunanen sarah ya
mik'awa Allah yinsa indai rabansa ce Allah ya bashi idan
b rabonsa bace Allah yaimasa canji d mafi alkairi dan
haka yanzu y hada hankalinsa guri daya kan karatunsa
tinda shekarar karshe yake ,so yake ya kawowa abba
excellent grade, dan shi kadai zaiyi ya nunawa abba
godiya da dawainiyar d yai dashi tin yana tsimman goyo
dan hk y maida hankali kan karatunsa. Ita kuwa sumy d
son yaya kamal yai mata katutu a xuciya ta rasa yadda
zatai dashi kullin adduarta Allah ya karkato d hankalinsa
gareta tinda duk wata hanya tabi taga bamai b'illewa
bace ko daidai d rana d'aya bataga ya nuna mata wata
alamar so ba dan haka t fara bayyanar da son d take
matsa a tsakanin sarah da sury duk sanda suke hira zata
sako maganarsa tana dan nuna alamun sonsa azatonta
acikin sury d sarah wani zai tunkareshi y fadama sa,tinda
sarah t fuskanci sumy son yaya kamal take ta sawa
zuciyarta ruwan sanyi dan tasan b yadda zaai yar gida
tana sonsa abawa yar tsintuwa aurensa dan hk ta cireshi
a ranta. Haka rayuwa tacigaba d tafiya kwanci tashi b
wuya gurin mai duka yanzu sarah tashiga SS3 daf suke d
fara SSCE, sumy d sury kuma suna SS2 suma qualifying
exam zasuyi, yaya kamal kuma yafara final paper dinsa,
dan hk karatu ka'in d na'in sukasa agaba saboda su samu
abinda d ake nema kuma su faranta ran iyayensu dan
haka suka dukufa wajen karatu b dare b rana. *BADAI
KAFI SONTA BA* *Written by Ayusha Iliasu.* *Story by
Hawwa Saleh.* *Dedicated to Abeeda n Baseera.*
*_Ayushailiasu.blogspot.com_* Page 166 to 170 Sury d
sarah ne ke tafe sun dawo dg gidan aunty fateema
kasancewar gidanta d gidansu b nisa Sosai, yasanya sukai
strawling sukaje, sarah ce rik'e d Najma yar aunty
fateema da taketa shashsheqar kuka saita biyosu suna
tafe suna hira, sun kusa kaiwa gida ne wani matashi ya
kunno kai a mota saura kiris y bigesu yai saurin taka
birki ya tsaya cak, agigice ya fito y karaso gurinsu hakuri
y shiga basu sudai kallonsa kawai sukeyi basuce qalaba
saida y gama sarah tace bakomai malam amma dan
Allah a ringa kula Allah y kare gaba,tinda sarah t fara
magana ya saki baki y layar uban tafiya yana kallonta,ita
kuwa sury t tacika tai famm dogon tsaki taja
mtswwwwww wanda y dawo masa d hankalisa jikinshi,
hannunta Sarah taja fuuuuu afusace tace sarah zomu
tafi suka wuce sukabarshi tsaye, tinda suka tafi yake
kallonsu batare d ya motsa ba, ganin sun shiga wani gida
ya sanyashi juyawa y shiga motarsa ya tafi. Gobe
monday su sarah xasu farah SSCE exam tin dare take ta
bosho, she s ready for d exams, atakaice zamuce kawai
jiran question paper takeyi ta tsarge answer,cikin dare ta
tashi ta jero nafilfilu ,addua takeyi Allah yasa abinda t
karanta ya fito kuma Allah y basu nasarar jarrabawar.
*Bayan sati daya* Mahmoud ne xaune cikin d'akinsa b
abinda y keyi sai faman tinanin wannan kyakkyawar
surar d yai toxali d ita kuma yaji an kirata d suna sarah,
tinda yaji muryarta mai kama d busar sarewa yaji sonta
ya mamaye xuciyarsa kullin d ita yake kwana yake tashi
hatta cikin baccinsa gizo take masa,yanke shawarar zuwa
wannan gidan dayaga sunshiga yayi batare d bata
lokaciba dan sonta d yake addabar shi, baxai yi sanya b
kar wani ya rigashi,mik'ewa yai yadau key din mota da
niyyar tafiya yana adduar Allah yasa nanne gidansu.
Karfe 4:00 n yamma ya isa kofar gidan, maigadi ya
tambaya dan Allah nanne gidansu sarah yace masa
eh,ajiyar zuciya yai yace alhmdllh dan Allah zan samu
wanda zaimin sallama d ita? Baba mai gadi yace to
dakata dg waje n kirata tukunna yace to nagode,baba
megadi d sallamarsa y iske mama a palo y rissina sika
gaisa sannan y shaida mata ana sallama d sarah, cikin
Abdullahi Aliyu Alkas Facebook.com/Abokinhira
WhatsApp Me 09038188199 Facebook.com/Abokinhira
Page No. 14 mamaki tace waye yace shidai baisanshi b
tace to tana zuwa,sarah kuwa dake kitchen tana girki
wiki wiki tai dan taji abinda baba maigadi yace, maman
ce t kwallamata kira ta amsa saida t karaso inda take tace
maza kije ana sallama dake kiyi saurin ki dawo kuma
banda shashanci tace to,komawar baba maigadi y sanar
dashi tana zuwa b dadewa sarah tafito,ganin fuskar
mahmoud ne yasa t fara tinanin inda t taba ganin fuskar
amma har t karasa inda yake tsaye bata tinaba,bayan
sun gaisane taimai ixini d yashigo dg farfafajiyar
gidan,daya dg cikin kujerun d aka jera dan hutawa tamai
umarni y zauna, bayan y zauna suka k'ara gaisawa ne
yake cewa dftn kin ganeni,murmushi tayi tace gsky na
taba ganin face din amma namanta inda na santa, nan
mahmoud ya fada mata inda suka taba ganin juna gami
d wayancewa da cewa hak'uri ya kara zuwa y bayar,yar
dariya sarah tayi tace kaimadai wllh mun manta
abinma,nan suka taba hira kadan sukai sallama batare d
mahmoud ya fada mata abinda ke cikin ziciyarsa b.
*BA DAI KAFI SON TA BA daga www.hausaebooks.com.ng* *Written by Ayusha Iliasu.*
*Story by Hawwa Saleh.* *Dedicated to Abeeda n
Baseera.* *_Ayushailiasu.blogspot.com_* Page 171 to
175 Wasa-wasa soyayya tafara k'arfi tsakanin sarah d
mahmoud saidai duk wainar d suke soyawa su mama
basu saniba dan sarah bata nuna alamun tana sonsa a
gabansu. Hakika duk abinda akasawa rana zaizo yau ne
yaya kamal y zana final paper dinsa zai dawo gida, shirye
shiryen taryarsa sumy tafara tin jiya,meatpie,springrolls
cake shawarma, bugga, pizza n samosa taimasa sannan
tai white cuscus n vegetable soup n liver soup sai
pineapple juice,karfe 2:00 n rana tagama komai ta
jerasu a dining, wanka taje t sheqa tasha kwalliya tana
jiran karasowarsa dan tadauki kudirin yau zata bayyana
masa sirrin zuciyarta. Abin sha'awa y baiwa mama yadda
taga sumy n rawar jiki akan yaya kamal tasan d walakin
goro a miya, dan ruwa baya tsami banxa tini ta rafko
diyar tata son kamal takeyi addua tayi Allah y

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment