Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kara maimaita maganar sai a
lokacin yusuf ya dago yai murmushi yace ai alhji
bansamu wadda nakeso ba, jin yusuf ya fadi hakane yasa
alhjin yin hamdala g Allah a zuciyarsa dan dama yanada
kudiri azuciyarshi nasan ya hadashi da yarsa saidai yana
gudun ya tareshi d maganar ko yana d wadda yakeso
amma yanxu komai zaixo d sauki,cikin hikima alhji ya'u
yace kamarka yusuf kace bakada wadda kakeso? Yusuf y
sosa kai tare d sunkuyar d kai yace babu , jin amsar d
yusuf y bada yasa alhjn cewa to indai wannan ne ga yar
wajena nan rukayya kaje ka ganta idan kana sonta na
baka,amma idan kaji bata kwantama a raiba dan Allah
karka boyemin sai ahakura Allah ne baiba tinda shi aure
yine na Allah, godiya yusuf yaimasa sukai sallama. A
daren wannan ranar yusuf ya je gurin rukayya, alhmdllh
sun daidaita kansu ba bata lokaci suka amincewa juna
dan rukayya yarinyace mai kamala d nutsuwa g kunya
gata da kyau daidai gwargwadon yadda Allah yayita
dadin dadawa kuma wankan tarwadace , a lokacin ta
gama makarantar sakandire b dadewa. mlm sule
yasamu labarin abin arzikin d ubangidan dannasa
yayi,yayi farinciki da adduar Allah y tabbatar d alkhairi
yasa ayi dasu, haka shima alhji ya'u yai murna da hakan
gami da adduar sanya albarka,alhji yau dakansa yasa
lokacin biki wata biyu tare da cewa zaiyi komai da
yakamata su yusuf suyi hatta gidan da zasu zauna
zaibasu dan yadau yusuf tamkar dan da yahaifa tinda y
rikemasa amana kuma yazamo sanadin yalwatar
dukiyarsa,mlm sule har gida yaje yaimsa godiya,kwanci
tashi ba wuya lokacin biki yazo akasha shagalin biki aka
kai amarya gidanta,zaman lafiya sosae tsakanin yusuf da
rikayya har Allah ya kawo rabo,murna agun yusuf baxata
misaltuba, kullin adduar Allah y sauketa lafiya yakeyi,
lokacin d cikin rukayya yashiga wata n tara Allah ya karbi
ran mahaifiyarsa Halimatu, tsiran sati uku d mutuwar
mahaifiyarsa rukayya ta haihu tasamu 'ya mace,da kanta
tabawa yusuf shawara asawa yarinyar sunan
mahaifiyarsa wato halimatu, hakika yusuf yai farin ciki d
hakan, ranar suna yarinya ta amsa sunan halimstus
sa'aadiyya ba dangin yusuf b har dangin rukayya sunyi
murna da hakan sosae. Haka rayuwa tacigaba tsakanin
yusuf d rukayya cikin kulawa da kwanciyar
hankali,lokacin da rulayya ta haifi yarta ta biyu ne alhaji
ya'u ya mallakawa yusuf shagon daya bude masa inda
akai takarda d shaidu da sahannun alhj ya'u Data mai
unguwa cewa ya mallakawa sirikinsa yusuf shagonsa
kyauta halak malak, ranar yusuf kasa magana yai
acewarsa baida bakin godiya,har gida yusuf da iyalinsa
sukaje suka sake wa alhjn godiya,haka yanuwan yusuf
ma baa barsu abayaba suka dinga zuwa godiya harsaida
alhjin yace ya isahaka,ana cikin wannan farin cikin aka
sanya lokacin auren kannen yusuf wato maryam d
hadixa,mlm sule yaci burin bikin yayan nasa saidai Allah
baya barin wani dan wani yaji dadi,ana saura wata biyu
bikin mlm sule y amsa kiran ubangijinsa,ba yusuf,
maryam d hadixaba hatta alhj ya'u mutuwar nan
tadakesu dan har lokacin bikinsu maryam basu daina
jimamin mutuwar ba, alhji yau ya taka radar gani a
auren su maryam yaxame musu jigo a rayiwarsu wato
uba suma sun rikeshi matsayin uuba. Allah y sa albarka
akasuwancin yusuf inda ya bunkasa ya zama babban
dankasuwa, a shekara daya yabiya wa kanshi da rukayya
kudi sukaje suka sauke farali, shekara data zagayo
yabiyawa maryam da hadiza suma sukaje, bayan
dawowarsu ne hadiza tasamu ciki a wajen haihuwa Allah
yaimata rasuwa, haka yusuf ya dakko yaron data haifa ya
kawowa rukayya ta raineshi, saboda lokacin ta yaye
fatima,haka rukayya ta raineshi tamkar dan d tahaifa
cikin kulawa irin ta uwa. A yanzu haka alhji yusuf yana
da yaya bakwai,mata biyar maza biyu,halimatu itace
babba sannan fatima sannan mariya sai abdullah sai
sulaiman sai sumayya da surayya,sai kuma dan yar
uwarsa d yake ruko kamal,tsarin alhji yusuf ne daga
sakandire yayansa mata basa jami'a dan haka
halimatu,fatima d mariya duk ya aurar dasu inada
halimatu keda yara uku, fatima d mariya kuma
biyu,yanzu haka abdullh yana aji 6 a sakandire sulaiman
kuma aji 4, sumayya da surayya kuma aji 2, kancewar
alhj yusuf mai kudi baya tsawwalawa kansa da sai
yayansa sunyi makarantar kudi,abdullah d sulaiman
suna boarding schl wato Govt Boys Secdry Schl Gwarzo,
Sumayya kuma suna Day Science kano,shi kuma kamal
yana jamiar Ahmadu Bello dake zariya,alhji yusuf ya
kasance mutum mai takatsantsan d gudun duniya dan
haka a gidansa ko yar aiki babu komai matarsa hajiya
rukayya dakanta takeyi tare da taimakon yayanta, driver
d maigadi ne kawai a agidansa sai almajirin da suke aike,
shima dan drivern aikinsa kawai ya ringa kai su sumayya
makaranta da yadawo dasu zai ajiye motar sai wata
safiyar,hakika alhji yusuf ya tarbiyyantar d yayansa akan
tarbiyyar islama ya nuna musu tausayi, hakuri da
kaskantar da kai tare da nuna su ba yayan kowa bane,
wani lokacin zasu tambayeshi kudi yace baidashi kuma
yana dashi saidai yaki basune dan ya nuna musu in yau
akwai gobe fa babu,kuma alhmdullh yaran sun taso akan
irin tarbiyyar da yadorasu akai. A halin yanzu alhji yusuf
yana da shaguna da dama a kasuwar kwari inda shima
yaja yara ajiki ya bude musu kamar yadda mahaifin
rukayya wato alhj ya'u yaimasa. *BADAI KAFI SONTA
BA* *Written by Ayisha Iliasu.* *Story by Hawwa
Saleh.* *Dedicated to Abeeda n Baseera.* Page 41 to 50
*CIGABAN LABARI* Ranar da sarah ta cika kwana goma
a gidan alhji yusuf da safe bayan sun gama breakfast
suna zaune a palo da iyalinsa alhajin ya gyara zama gami
dacewa sarah firgigit t dago kai takalleshi tace naam
abba (kmr ydd taji su sumayya nafada masa) cigaba d
magana yai yace yanzu kinga yau kwananki goma a
gidannan batare da munsan daga ina kike ba dan haka
nakeson yau kifadamin meye dalilin dayasa kika baro
gidanku da wannan daren? Shiru ne ya ratsa gurin
nawani lokaci batare da sarah tace komaiba, su sumy n
sury anbaza falafalan kunne anson jin kwaf, shurun d
alhj yaji yai yawane yasanyashi dakawa sarah tsawa da
kakkausar murya kasancewarsa mutum da bayasan
wasa yace badake nake ba, kwallace ta zararo tabiyo
kunnucintalokacin da tadago, ganin hawayen yasa alhji
yakara cewa duk kukan da zakiyi saikin fadamin ,dan
bazai yiyu muyita zama dakeba alhalin bamusan
kewaceba, jin alhj yafadi Abdullahi Aliyu Alkas
Facebook.com/Abokinhira WhatsApp Me 09038188199
Facebook.com/Abokinhira Page No. 4 hakane yasa sarah
ta goge hawayenta gami da cewa abbah labarina mai
tsahone zamudau lokaci ban gama sanar dakuba,alhaji
yace komai yawansa ina sauraronki dago kanta tasakeyi
sannan tafara magana cikin dakushewar murya kamar
haka:- Nidai sunana sarah muhamma, mahaifina
yakasance yana da matan aure guda biyu,ummana
Hajara d kishiyarta bilkisu, ummana tana da yaya biyu ni
d kanina khalid, itakuma kishiyarta tana da ya guda daya
rufaida, babana mutumne d Allah y doramai son
ummana saboda hakurinta da biyayyar da takemasa
koda yaushe yana nuna mata soyayya a fili hakan
nabatawa kishiyarta rai tin tanai aboye har take nuna
kishin haka agabansu ,duk randa abbana yaiwa ummana
wani abu najin dadi ko yayabeta agaban idanunta yana
juya baya a gaban ummana zata gyada kai tace wayaga
buyouts, takara d crew zata gani ne wllh,wannan kalma
tanaiwa ummana ciwo amma bata taba fadawa abbana
abinda d take cewa saidai tai hakuri taita addua, akwana
atashi tin abin nadamun ummana har tasaba da wannan
kalmar ta hassada, ganin ummana bata taba tarar
abbana dan fadama sa, hakanneyasa yasa kishiyar tata ta
bullo da sharri kala kala, idan abbanmu ya tafi aiki yana
dawowa zata fadamasa ummana tafita batare da izininsa
saba ko tace ta gayyato mutane ta dafa abinci ta juye
musu tahansu ita da yarta, ko idan tai baki ummana tai
girki bata basu, sharri d tuggu dai kala kala tin abbanmu
yana yiwa ummata fada agabanta, har yagane sharri
kawai take mata ya daina yimata fada, idan tafada masa
saidai yace tayi hakuri zaiwa ummana fada, ganin
yadaina yiwa ummana fada ne yasa ta bullo d wani
makircin duk ranar girkin ummana saita daidaici tagama
miya ko abinci saita faki idobta taje takara gishiri
aciki,duk mu kasa cin abincin hakama idan abbanmu
yazo zai ci yakasa ci yai taiwa ummana fada, tanaji yana
fadan saita sallallabo ta zo ta cewa abbanmu yunwa
sukeji sunkasa cin abinci, haka komai dare abbanmu
zaicewa ummana ta tashi ta dora wani abincin, batare d
musu ba ko kosawa zata sake wani girkin, akwai randa
abbanmu yakawo nama a soya kuma ranar ummanace
da girki saita soya naman nan takai kitchen, tana ganin
ummana tashiga wanka dan lokacin abbanmu yakusa
dawowa gida saitai sauri tadau galan din kalanzir ta
tsiyaya acikin naman ta jujjuya tamayar tarufe,
abbanmu yana dawowa aka xubo masa naman yanacin
yanka daya yace da ummana ya akai kalanxir kalanzir y
taba naman ,abinne ya daurewa ummana kai tace
kalanzir yace eh, tace wllh ita batasan yadda akaiba, nan
abbanmu yafara yiwa ummana fada yana zaginta yana
cewa wace muguntace wannan tasan d yadda yai yasiyo
naman zata zubamasa kalanxir aciki, budar bakin
ummana tace yai hakuri kawai ya wanketa da mari,
(sarah tanakaiwa nan sai naga sumy d sury harma d
hajiy sun zaro ido suka hada baki mari tabdijan, nima
kaina ayusha saida tausayinta y shigeni,abinda y baiwa
su sury d Sumy mmki shi ne tin tasowarsu basu taba
ganin abbansu y mari mamansu b, amma take cewa
nata uban y mari mahaifiyarta. Jin karar saukar marin da
kukan ummana ne yasa na zabura da gudu nayo waje dg
cikn dakinmu dan ganin meke faruwa da ummana take
kuka,ina fitowa mukai idohudu d kishiyar ummana ta
watsomin hararagami dacewa indai nice zata yabawa
aya zakinta tinda,aranta tace *Badai kafi sonta taba*
kadanma kenan sai tagwammace kida da karatu, jin
abinda da take fadene yasa jikina yai sanyi nakasa
karasawa inda ummana take kukan banyi auneba sai
jinai nima kukan ya subucemin. *BADAI KAFI SONTA
BA* *Written by Ayisha Iliasu.* *Story by Hawwa
Saleh.* *Dedicated to Abeeda n Baseera.* Page 51 to 60
Sarah ta share hawayen dake gagarowa a fuskarta taci
gaba da cewa ganin da ummana tayi na taho nakasa
karasawa na tsaya ina kukane yasa ta karasowa inda
nake tsaye ta kama hannuna muka shiga daki, bayan
munshiga ne take tambayata meyasa nake kuka nace
mata naji kara kamar ta duka ne sannan najiyo muryarki
kamar kina kuka shine nai hanzarin fitowa naga meya
sameki shine naji ammi (wato kishiyar babata dan haka
muke kiranta) tana fadin wasu maganganu da ummana
bata bari na fada matasuba, hakuri tashiga bani tana
cewa ba abinda yasameta, taki fadamin ne dan kar kima
da mutuncin abbanmu ya ragu agurina, amma tabbas ni
naji komai yafaru, haka naita bawa ummana hakuri akan
duk abinda ake mata a gidan nake cemata malamin
islamiyyarmu yana fada mana Allah yace acikin alkurani
mai tsarki *( _Hakika masu hakuri su ake cikawa ladansu
batare da hisabiba_)* kuma ya kara fada mana annabi
SAW acikin hadisinsa ya cewa *(Hakuri haskene)*jin
haka ne yasanya ummata tai murmushi tace Allah yai
miki albrk ya kara mana hakuri nace amin. Tin daga
wannan ranar abbanmu yace duk sanda ya kara kawo
wani abu gidansa kar ummana t kara tabawa koda ranar
girkinta ne saidai ammi tinda ummana mugunta take
masa a kan kayansa,dadi kuwa kamar yakashe ammi dan
farin ciki, haka muka hakura intai girki tadan zuba mana
baikai ya kawoba haka zamu karba muci da dadi ko
badadi mun koshi ko bamu koshi bamu isa mufadawa
abbanmu ba saidai muyi hakuri, ganin haka ummana ta
hakura tazuba ido ba yadda ta iya saidai kullin tana
kaiwa Allah kukanta yai mata magain abun, nima kullin
addua nake Allah ya bayyanar d mai gaskiya. Haka
rayuwar ummana taci gaba cikin kunci da takaici batada
ikon tai kwakkwaran motsi acikin gidan, in kaganta a
tsakar gida saidai alwala ko wata bukatar amma
koyaushe tana daki tana kaiwa Allah kukanta, ita kuwa
ammi gari nata kasuwa tata,gari na wayewa abbanmu y
fita aiki zatai ta shewa da habaice habaice taci karenta b
babbaka duk dan ummata takulata suyi tashin hankali
itakuwa ummata tai banza da ita ta nuna batasan
tanaiba. Tsananin adduar d ummana takeyine Allah ya
fara karkato da abbanmu kan ummana,godiya ga Allah
muka shigayi sanda abbanmu yace da ummana zata
cigaba da girkinta tare d yimata gargadi data kula kar irin
abinda ya faru a baya ya sake faruwa,wai acewarsa
yagaji dacin abincin ammi baya dadi kamar na ummana
baisan tsananin adduar da mukeyi bane yasashi fadar
hakan,hajiya ce ta katsere sarah ta hanyar cewa ai dama
addua bata faduwa kasa banxa,tabbas sarah tace takara
d cewa Allah ai yafada a cikin Alkur'ani *"Duk wanda ya
dogara dashi (Allah) zai isar masa".* mamakine ya kama
alhj jin yarinya karama da hankali ga uwa uba ilimi ta iya
zaro ayaoyi da hadisai kamar wadda ake kitsawa, take
yaji kaunarta takuma shiga zuciyarsa. Ranar da ummana
taci gaba da girki takaici da bakin ciki ba wanda ammi
bata nunaba har tana cewa bari munafikin mijin naki y
dawo yasameni, ai baifadan zaki cigaba da girkiba shine
ya zage kuka kulla muna fircinku a daki wallahi indai nice
bilki zamusa kafar wando daya dake tinda *Badai yafi
sonki ba*,maganganun ammi sunyiwa ummana zafi
saidai tadanne zuciyarta taki kulata saida taji abun ya
isheta ta dago tace aimu da Allah muka dogara kuma ba
haka kawai yafi sonaba hali nagari shikesa aso mutum,
idan mutum yana so asoshi shima saiyai koyi da irin
halin ibaiga ansoshi ba, wannan maganar da ummana t
fad ita takara ruta wutar kiyayya da gaba tsakaninsu
fuuuuu tashige dakinta tana cewa zaki ganine,ummana
tace Allah yasa muga alkhairi, tindaga ranar ta dau gaba
da ummana harma damu ta daina yimana magana hatta
yarta rufaida tasa tadaina kulamu,duk ranar girkin
ummana intai abinci bataci bata barin rufaida taci koda
yunwa zata kasheta. Idan abbanmu yadawo taita kuka
taba fada masa karya d gaskiya shikuwa bayabin takan
magamarta tinda y fahimci duk karyane kawai batason
zaman lafiya ne saidai yace tayi hakuri, ganin zaman
lafiya yadawo kamar ada tsakaminshi da ummana ne
yasa ammi kullatar saita raba tsalaninsu kotawani hali
nan tafara zuwa gurin yan bori d yan tsibbu d bokaye
ahada ummana d aljanun da zasu sa abbanmu ya
tsaneta yaji baya son………….sai kuka ya subucewa
sarahbata iya karasawa ba. *BA DAI KAFI SON TA BA daga www.hausaebooks.com.ng*
*Written by Ayisha Iliasu.* *Story by Hawwa Saleh.*
*Dedicated to Abeeda n Baseera.* Page 61 to 70
Abdullahi Aliyu Alkas Facebook.com/Abokinhira
WhatsApp Me 09038188199 Facebook.com/Abokinhira
Page No. 5 Duk lokacin d ammi zata gurin boka sai
tabari abbanmu ya tafi aiki saita fita batare d ta
tambayeshi ba,tinda ummana ta fahimci tafara zuwa
gurin bokaye tasake dukufa addua da salloli ba dare ba
rana tana kaiwa Allah kukanta y kareta dg sharrin da take
son kulla mata,akwai ranar da tadawo dg gidan bokan
tazo kofar dakin ummana ta barbada wani magani wai
indai ummana ta tsallaka shikenan abbanmu xai saketa,
ita ummana batasan tazuba ba data tashi zata fito dg
dakin tai bismillah tafito,murna ammi tashiga yi ganin
ummana tsallaka maganin tana jiran abbanmu y dawo
taga yasaki ummana amma daya dawo sai taga baice
yasaketa ba saidai ma cewa yai d ummana ta shirya
zasuje unguwa, nan takaici y isheta, abbanmu suna fita
unguwar tasa kafarta itama tafita, ashe gurin bokan
takoma take fadamasa aiki baiyiyuwa, nan boka yace
mata ai sharadin maganinsu ba'a ambaton Allah idanko
aka sake aka ambaceshi aiki ya lalace,jin boka yafadi
haka yasa abin duniya yaiwa ammi yawa ya zatai da
ummana tinda bata wasa da addini, sake dabara tai
takoma gurin yan tsubbu kullin d kala kalar abubuwan d
zata zo dasu taita binnewa a gidanmu muna kallonta
tanayi tana maganganu d habaici, ummana bata taba
tanka mataba balle tafadawa abbanmu, saidai dagewa da
addua da mukeyi. Haka kullin d abbanmu yana fita itama
zata fita bazata dawoba sai tadaidaici yakusa dawowa
sannan ta dawo dan tasan ummana baxata taba
fadamasa b, ganin duk abin d takeyi baya kama ummana
saidai zaman lafiya d kwanciyar hankali da yake karuwa
tsakanin ta d abbanmu,nanfa ta tashi a tsaye d
gagarumin asiri yau da gobe tafi karfin wasa dare daya
abbanmu y juyawa ummana baya ko ta gaisheshi baya
amasa dg karshe ya daina shiga dakinta ya daina cin
abincinta balle yadau butar ta,kukane yaci karfin sarah
cikin shashsheqa taci gaba d cewa tindaga wannan
lokacin ummana ta fara mugayen mafarki tana bacci
saitai ta ihu tana tsorata tana cewa zasu kasheta gasunan
sun taho ku tainaka min zasu kasheni haka zatai t ihu
tana zabura amma abbanmu baxaizo gurinta ba saidai y
daga labule y leko yace taimusu shiru mahaukaciya
kawai ta hanasu bacci, haka zan rungumeta ina karanta
mata ayatul kursiyyu har tasamu bacci, farin ciki agun
ammi bazaya misaltuwa, haka ummana tashafe wata
uku a wannan halin kullin cikin dare bama bacci
makaranta ma daina zuwa nai saboda indan natafi
bansan abin d ammi zataiwa ummanaba,ganin abbanmu
yaki nemawa ummana magani ne yasa naje nafadawa
kawu sani wato kanin ummanmu halin da muke ciki.
Zuwan kawu sani gidanmu yaga irin halin da ummana
take ciki duk ta rame ta susuce kamar mahaukaciya tayi
baki ba yadda yasanta ba dan duk danginsu ba wanda y
kaita kyau da kwarjini gata fara mai manyan idanuwa d
dogon hanci idan tai murmushi sai wushiryarta ta
bayyana kyanta ya karu,kasa magana yayi kawai kuka
yakeyi yana cewa yanxu haka ummana
takoma,tambayata yashigayi meya sameta? Meya janyo
mata fadawa wannan halin? nan na zayyana masa
abinda yake faruwa da yadda ummana take tsorata cikin
dare d kalmar d ammi take fadawa umman kullin ta
*BA DAI KAFI SON TA BA daga www.hausaebooks.com.ng* wallahi zata gani ne,abinne ya
daurewa kawu sani kai shi kanshi kalmar tayimasa zafi a
rai dan yadda fuskarsa ta nuna alama, atake ya dauke ni
d ummana a motarsa bamu tsaya ko inaba sai gidan mai
magani tare d cewa zai dawo y sami abban namu,sautin
kukan su sumayya ne yasa sarah yin shuru. Nima danake
sauraransu kukan nake shabe shabe d hawaye. ina fadin
Allah y rabamu da sharrin kishiya.amin *BADAI KAFI
SONTA BA* *Written by Ayisha Iliasu.* *Story by Hawwa
Saleh.* *Dedicated to Abeeda n Baseera.* Page 71 to 80
Sanda kawu sani y dawo y samu abbanmu yake
tambayarsa ya akai y bar ummana a wannan halin?abin
d yafito dg bakin abbanmu sai yace baisan batada lafiya
ba sabida kin Allah, kawu sani ya jinjina maganar d
abbanmu ya fadamasa y zaai suna gida daya yace baisan
batada lafiyab,kawu sani shiru kaeai yai masa batare d ya
tanka masa b a matsayinsa n mijin yayarsa. Haka muka
zauna a gidan magani tahom wata daya batare d
inaganin sauki a tattare d ummana b saidai kullin abu
karuwa yake har takai saidai a kulle ta a daki inba hakaba
neman guduwa takeyiashe dg wannan somi somine,
wasa farin girki wata rana muka wayi gari ummana t fara
hauka tibiran duk wnd yaje kusa d ita sai duka amma
abin takaici duk wannan halin d muke ciki abbanmu sau
daya yazo ya ganmu sai randa muka cika kwana 35
sannan y dawo, ganin haukan d ummana takeyi ne y
sanya jikinsa yai sanyi nan ya ashiga nema mata magani
ka'in d na'in sbd tsananin son d yake mata.
Alhamdulillah daga sanda abbanmu y fara neman
maganin ne tafara samun sauki ganin haka yasa kawu
sani y daukemu dg gidan mai maganin y maidamu
gidanshi, har gidan abbanmu yake zuwa y kawo mana
maganin batare da ammi tasan yana yiba,wasa wasa
cikin ikon Allah sauki y dada samuwa satinmu biyu
muna amfani d magungunan ummana ta warke, lokacin
d abbanmu yazo yaga t warke yace mukoma gidanshi
nanfa kawu sani yace ai baiga abinda xaisa ta koma
gidan ba, saida abbanmu yaita bashi hakuri kan cewar
insh Allah hakan bazata sake faruwa ba nanma dakyar
kawu sani y yadda amma yace saitayi wata daya kafin t
koma badan abbanmu yasoba ya hakura sai randa ta
cika wata gudan sannan ta koma. Ganin ummana t dawo
gidan cikin koshin lafiya ya dada tinzira ammi wjn yin
asiri,shikuma abbanmu baifasa kawowa ummana
maganin neman tsari b,haka kuma muma bamu fasa
dagewa d addua ba, haka alamari yaci gaba d tafiya
agidan ba dadi saidai zaman hakuri d mukeyi,duk sanda
muke hira d ummana tana cewa yanzu sarah haka zamu
kasance a gidannan b dadi sai nace tayi hakuri har ranar
d Allah zai tona mata asiri,sai tace min wannan wace irin
masiface, hakuri nake kara bata tare d kawo mata misali
da Allah yana fada cikin littafinsa mai girma cewa
*"Dasannu zamu jarrabeku da wani abu na dg tsoro d
yunwa d tawaya ta dukiya d rayuka d 'yayan itacuwa,
amma kuyi bishara d masu hakuri"* ko kuma *"Zakuce
kunyi imani ne sannan kuce baxamu jarrabeku ba"*
haka zanta bata hakuri d cewa jarrabawace dg Allah ita
wannance jarrabawar d akai mata idan tai hkri zataga
sakayya a gaba kamar yadda Allah yace *Yaku wadanda
kukai imani kuyi hakuri kuyi juriya kuyi dako (ma'ana ku
jira sakanakon d Allah zaiyi)"* dan hk kowane bawa d
akwai gwargwadon ydd ake jarabtarsa a duniya, wani iya
wahalar da yasha adunia zata zamemasa sauki d
rangwame ranar lahira, wani a saka masa tin aduniya
wani kuma a barshi sai ranar hisabi, dan annabin rahma
yace *"Idan Allah y nufi bawansa d alkairi saiya gaggauta
yimasa azaba a duniya idan kuma yaso saiya kyaleshi d
zunibinsa har xuwa ranar alkiyana."* hakadai zanta bata
hakuri d kalamai mai nutsar d zuciya nace mubarwa
Allah zai saka mata,kuma kowane abu yana da iyakarsa
kmr yadda annabi yace a hadisi *"……………Hakika
kowane abu akwai lokacin da aka iyakance masa dan hk
kuyi hakuri ku nemi lada.………"* take zanga fuskarta ta
bayyanar d nishadi d annashuwa. Haka zamuci gaba d
hira cikin jin dadi d nisha lokacin d nake cewa d ita insha
Allah wannan jarrabawar alkairice a gareta tace kamarya
wahala zata zama alkairi ga bawa nace saboda annabi
saw yace *"Duk wanda Allah yake nufinsa d alkairi saiya
dora masa wata larura."* ko kuma ta zama makankarin
laifin d yake aikatawa kamar yadda annabi saw yace *"
Duk abin d yasamu mumini na wahala kona cuta kona
damuwa kona bakin ciki kona cutarwa kona bacin rai
harta kayar d ya takata har sai Allah y gafarta masa
zunubansa da ita."* sanda n karantaw ummana wannan
hadisin sai tacemin amma wata jarrabawar d akewa
bawa tana tsanani a gareshi sai nake cewa d ita babu
wata jarrabawa d xata zamo mai tsanani g bawa kuma
Allah baya jarabtar mutumin d bayaso kinga kuwa b
kowa Allah yake gwada imaninsa b sai bawa n kwarai
tinda manzon Allah saw yace *"Hakika mafi girman
sakamako yana tare d girman bala'i,lallai Allah
madaukakin sarki idan yana son mutanensa saiya
jarabcesu, duk wnda ya yarda d wnn jarrabawar Allah y
yarda dashi hk duk wnda yai fishi akan jarabawar Allah
zai fishi dashi."* kawai sai naga ummana tana kuka
saboda jin wannan hadisi tan rungumeni tana cewa
jarrabawar d Allah yaimin kenan y hadani zama d
azzalumar mata, ya Allah ka bamu ikon hakuri akan
dukka musibar d zata samemu ka kuma bamu ikon cin
jarrabawar d kai mana, gaba dayanmu da muke
sauraron sarah muka hada baki mukace amin. *BADAI
KAFI SONTA BA* *Written by Ayusha Iliasu.* *Story by
Hawwa Saleh.* *Dedicated to Abeeda n Baseera.*
Abdullahi Aliyu Alkas Facebook.com/Abokinhira
WhatsApp Me 09038188199 Facebook.com/Abokinhira
Page No. 6 *Ayushailiasu.blogspot.com* Page 81 to 85
Haka muka zauna a kurkuku tsahon wata biyar batare d
ko saudaya wani yazo ya ganmu ba kamar yadda ake
zuwawa sauran yan kurkukun,ummana saida tai wata
cuta kamar baxa tai raiba, shugaban gidan kurkukun
yasa aka fadawa abbanmu amma yaki zuwa haka
takaraci ciwonta har Allah y bata lafiya. Tsananin adduar
da mukeyi ne ya sa wata ranar juma'a d misalin karfe
3:00 na rana abbanmu yazo yai umarni da a sakemu,
bayan munfito dg kurkukun azatanmu tare d abbanmu
zamu tafi gida sai mukaji yana cewa karmu sake mu
dosarmasa gidinshi duk inda zamuje mutafi amma
banda gidanshi, ummana kasa magana tai saini nai
karfin halin cewa yanzu abba idan ummana tana d inda
zataje ta tafi gidansu aini 'yarka ce ina zanje, abinda
yafito dg bakinshi sai cewa yai nashiga duniya mana,
bansan lokacin dana fadi a gurinba ashe suma nayi, yana
gani nasuma ya juya yai tafiyarsa ya barmu a gurin,
bayan na farfado ne ummana tace mutafi gidansu,haka
muka kama hanya a kafa muna ta tafiya har mukaje.
Dakyar dangin ummanna suka yadda muka zauna
agidan,sakakon ammi duk tayi asiri ta rabamu dasu,
wani daki dake hanyar kofar gida suka bamu ko kofa
babu sukace anan zamu zauna bamu d zabi illah zama a
cikinsa dan idan ba hakaba bamuda inda zamu,,bayan
fitowarmu dg kurkuku da kwana goma ne ummana ta
kwanta ciwo ashe ciwon ajaline bazata tashiba, amma
duk gidan babu wanda zai leko ya dubata ni kadai naita
dawainiya d ita,idan tana ninfashi kirjinta yaita bugawa
kamar zuciyarta zata fito,lokacin da sa'i yai take cemin
sarah kiyi hakuri da duk halin d xaki tsinci kanki a ciki ki
rike gaskiya d amana a duk inda kike karki yadda ki cutar
da wani dan ni tawa takare baxan tashiba,dan haka nake
miki fatan alkairi Allah yai albarka a rayuwarki, tana
kaiwa nan naji tayi salati shikenan ashewai ta mutu, kuka
na rusa ina ambaton Allah, jin kukan d nake yine
yasanya mutan gidan zuwa inda nake suna tambayata
lafiya, gawar ummana n nuna musu suka karasa inda
take bayan sun tabbatar tamutune suke cewa ai gara
haka sun huta d jaraba dunguremin kai sukeyi suna
cewa nima dole nabar gidan dan baxan zauna ba basu
barni d radadin mutuwa b suka dinga fadamin
maganganun da sukaga dama. Bayan anyi sadakar uku
ne yayan ummana yace nabar masa gidansa ba yadda n
iya haka fito batare danasan inda zaniba tafiya kawai
nake saida naga dare yayi nasamu wani kango nashiga
saida nai kwana biyu acikinsa ba ci basha. A bangaren
ammi kuwa batasan abbanmu yasa anfito damu dg
kurkuku b saida taji labarin mutuwar ummanmu sannan
tasan anfiti damu, haka da taji labarin yayan ummana ya
koreni farin ciki kamar y kasheta, gida ya dawo dg ita sai
yarta koshi abbanmu bashida katabus a cikin gidan sai
dai ita. Tsananin yunwar da t dameni ne yasanya nafito
dg cikin kangon ko Allah zaisa nasami abinda zansa a
bakina,wani gida dake dan nesa d kangon nashiga danyin
bara,nayi sa'a mai wanke wanken gidam t hado kayan
wnke wnken zatayi rokarta nashigayi ta taimakamin d
ragowar abincin d akaci aka rage a wani kwano,da tai
kmr bazata baniba saidai t mikomin, sabida da ka ganni
kaga siffar mahaukaciya dan nagama fita a hayyacina
sbd yunwa d kishir ruwa,d hanzari n karba na koma gefe
n rakube nafaraci,daidai lokacin d nakai wata loma
bakina ne yai daidai d fitowar mai gidan daga ckn gidan
ganin ydd nake cin abincin hannu baka hannu kwarya ne
yasashi tsayawa yana kallona,niko kallanshi ban karayiba
nacigaba

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment