Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya halarta CEO kawai ake jira, duka mikewa tsaye akayi ganin Alhaji, wucewa Zayn yayi direct asalin babban kujeran na Baban shi yawuce directly yawani fada akai yazauna kowa na tsaye yana kallonshi amman ko ajikinshi saima zare glass din idanunshi dayayi yakalli Uncle dake tsaye shima akujeran farko na right hand dinshi, tabe baki yayi abinshi daidai Alhaji yakaraso wajen baimabi takan mutanen ba sai tsayawa kan Zayn dayayi cikeda tsantsan so yace “kagaji ko inbude maka bottle water dinan kasha” girgizamai kai yayi ahankali hakan yasa Alhaji yazauna kan kujeran dakenan close to Zayn din na left side sanan yace “settle down” hakan yasa kowa na dakin ya zauna yana murmushi daidai lokacin wata secretary ta shigo takawoma Alhaji wasu files sanan ta wuce tafita, kafin Alhaji yace “barkanmu da safiya duka, nasan kuna mamakin wanan urgent meeting dinan dana kira ko” yadanyi murmushi sanan yakalli Zayn, hannunshi yakai yadaura akan Zayn cikeda asalin so yana murmushi yace “this is my only son Zayn Ganuwa, yayi graduating from one of the best schools in this world wato Oxford university, yanada 2 degrees daya under business management daya kuma under mechanical engineering, yanada masters a business administration not to talk of wasu good Human Resources courses, programs dayayi, he’s 26 by the way” Alhaji yasake maganan yana murmushi still yana kallon Zayn din dayama ciro waya yana daddannawa abinshi, ahankali Alhaji yazare hannunshi daga kanshi sanan yajuya ya fuskanci mutanen yace “the reason for this meeting shine” yaydan shiru sanan yace “inaso na sauka daga matakin CEO na wanan kampanin nawa, inaso nabarma dana Zayn all my companies” shiru dakin yayi kaman kankara koshi Zayn din tsayar da danna wayan nashi yayi yana kallon mahaifin nashi, Alhaji yace “lawyer na yariga yagama aiki on all the paper works komi nawa yanzu sunan Zayn ne akai, Zayn ne mamalakin sa” tura file din yayi gaban Zayn sanan yabashi pen ahankali yace “sign here son” shiru Zayn yayi kaman bazai karbi pen dinba saikuma ya karba ahankali sanan yay signing, tafi mutanen wajen suka hauyi, hadiye wani abu uncle yayi awuyanshi sanan shima yashiga tafi yadafa kafadan Zayn yace “congratulations Zayn” maganganu sukayi na wanda kampanin zai kara bunkasa sai wajajen 1 sanan aka gama, Alhaji da Uncle da Zayn suka fito masallaci sukaje salla sukayi sanan Zayn yace “Dad mutafi gida” tashi Alhaji yayi yace “bari na maida Zayn gida zan dawo anjima” gyadamai kai Uncle yayi sanan suka fito daga masallacin sukai mota.



Suna shiga motan kwanciya yayi yadaura kanshi kan cinyan Alhaji, Alhaji yace “kagaji ko” gyadamai kai yayi batare dayace komiba idanunshi a lumshe, Alhaji yace “karage gudu direba Zayn zaiyi bacci” “Toh Alhaji” direban ya amsa yana rage gudu sosai, shima Alhajin dan gyangyadi ne ya kwasheshi, kaman daga sama yaji direban su yataka wani mummunan burki da saida Zayn yawani fado kasa yabugu da kujera shikuma Alhaji kanshi yabugu da kujera baima damuwa ta Zayn dayay kasa yakeji yace “Subhanallahi Zayn tashi tashi are u okay, kai Labaran (direba) Maiya faru kataka burki haka?” Duka yay maganan nan ne in few seconds trying yadago Zayn dake yunkurin tashi zaune kawai sai hayaki cikin motan within a blink of an eye, wani kalan mahaukacin tari daga Zayn har Alhaji suka fara suna rike wuyansu cikin 12secs dukansu sukai passing out.


Bude bayan motan akayi wasu gardawan maza ne dake sanye da bakaken kaya sun rufe fuskokinsu da mask, Zayn suka wani fizgo a sume suka fito dashi daga motan akan titin da ranan Allah suka sashi akan machine dasuke taredashi guda 4 dasuka zagaye motan sanan sukai wani harbi a sama dayasa mutane da motocin dake titin kowa ya rude sanan suka saki tear-gas kusan guda 10 wajen yahau hayaki sanan sukai cikin dajin gefen titi da machinan suna arna wani uban gudu, gudu suke cikin dajin nan nakusan 1hr sanan sukakai wani babban fili da akai clearing grass na wajen ga helicopter 🚁 pake awajen sauka duk sukayi sanan suka hadu suka dauki Zayn dayake a sume zuwa cikin helicopter biyu daga cikinsu suka koma wajen machinan suka dauki wani jarkan man fetur suka bude suka zuzzuba a machinan suka kunna lighter machinan suka kama da wuta sanan sukai wajen helicopter suka shishiga daya daga cikinsu yace “let’s go” pilot din ya kunna jirgin kafin sutashi sama.


Tofa jama’a!!!
Yanzu nafara book kucigaba da bina sannu sannu zankai inda kukeso nakai.


Chat me up on WhatsApp idan kinason this book wa.me/+2347012181461

💫 FARRAH💫


✍🏻M SHAKUR


EPISODE 8️⃣
“Alhaji, Alhaji” sama sama yaji ana kiran sunanshi kaman amafarki, ahankali yake bude idanunshi dayaji sunmai wani irin nauyi da tunda yake zai iya cewa basu tabamai nauyi hakaba ga kanshi dake wani irin sarawa, alamun mutane yake gani akanshi yana kokarin ganesu kafin idanunshi sugama washewa tastas wani baturin likitan shine akanshi hakan yasa yadan ware idanu da kyau yana kallon inda yake ganin asibiti ne Dr yace “can you hear me Alhaji? Talk to me” yunkurowa Alhaji yayi zaitashi yace “ya akayi nake asibiti? Ina Zayn? Where is my Son”? Yay maganan recalling abinda yafaru dasu a mota kaman direbanshi yay hatsari ne the last thing daya tuna was hayakin daya cika motan. “Ina Zayn dina” Ganin Alhaji yay magana da kyau yama rude sai tambayan Zayn yake yasa Dr yace “are you having pains anyway Alhaji”? girgiza kai Alhaji yayi yace “just headache but bashine damuwa ta ba yanzu ni, ina Zayn, hope babu abinda ya sameshi? Yafadi daga jikina yabugi kujeran mota hope nothing happen to him kasan jikinshi bai son wahala hope wajen daya buge bai kumbura ba, shi yana wani daki ne? Ina yake Dr”? Ahankali Dr yadanja baya sanan ahankali yakalli kofan shigowa dakin yace “police are here lemme send them in they will answer all your questions” baima jira maganan Alhaji ba yafice da sauri, wasu manyan polisawa ne agaban dakin, sai Uncle, Mami da sauran matan Alhaji agaban dakin, matan Alhaji kuka wiwi Mami dai idanunta sunyi jaaaa kana ganinta kasan tafi kowa damuwa amman ta natsu sosai labbanta na motsi alamun kodai zikiri take kokuma addu’a take, polisawan Dr yasa su shiga ciki, suka shiga duk suna tsaye anan gaban dakin sukaji ihun Alhaji, daidai police daya nafitowa yace “come Dr” dasauri Dr yabisu Mami dasu Uncle sukai dakin suma.


“Dr wanan wani kalan wasa ne, wayay kid……na….pi….ng Zay….” Yama kasa karasa magana ya sume numfashinshi na daukewa wani irin salati kowa yahauyi, Uncle yakalli police din yace “Yaya can’t handle this news, do whatever it takes a samo Zayn dan Allah, Zayn shi kadai Allah yabama yaya na, Zayn is his entire life, please bring Zayn back” gyadamai kai Babban dan sandan yayi yace “inhar yanda muke suspecting hakane kidnapping nashi akayi to kuzamto kusada wayoyinku za’a iya kiran daya daga cikinku suyi maganan iya adaddin kudin dasuke so abiyasu kafin su sakeshi, meanwhile bari mukoma bakin aikin mu, idan Alhaji ya farfado yana cikin state dazai iya magana damu Dan shine yasan enemies nashi da wayanda zasuso su cutar dashi ko danshi asanar damu Dan mudawo muyi magana dashi, dole mu tsananta bincike bana fatan case dinan yay nisa” gyadamusu kai Uncle yayi yabasu hannu suka gaisa sanan sukai musu sallama suka tafi
Wanan kenan………
********



Wani irin bude idanunshi yayi tarr sabida wani ruwa wanda yake nan uwa kankara mai kuma bala’in wari dayaji an watsamai, afirgice yatashi zaune yana kokarin tattaba jikinshi amman yakasa sabida hannayenshi da aka kulle warin dayakeyi nawani irin shiga hancinshi yace “f*ck” kafin chan kaman wanda yatuna wani abu yabi hannayenshi guda biyu da kallo dayaga an kulle da igiya dakuma kafafunshi da suma yaga an kulle a igiya an dauresu tamau dan har zugi hannun da kafafun sukemai sanan ahankali yashiga dago kanshi in a very slow manner yana tuna the last inda yake yana tareda Baban shi a mota aka taka burki harya fado yabuge bin inda yake yayi da kallo gabanshi daji bayanshi daji gefenshi daji dayan gefenshi ma daji, Babban daji ne sosai mai girma, sai gawasu mutane daya tabbata maza ne suna sanye da bakaken kaya su hudu da mask a fuska dukansu suna tsaye tare sun bashi baya babban cikinsu da karaman waya Nokia mai tocula yana waya da bayajin abinda yake cewa, jakunkunan yagani irin manyan bag pack dinan guda hudu saikuma babban bargo guda daya, da toculoli sai bindiga dasuke cikin wani babban jaka manya dayasa yaji gabanshi yafadi, ko sunji ajikinsu ana kallonsu daya daga cikinsu ne yafara juyowa hada idanu sukai da Zayn din da idanunshi sukai jajir yana kallonsu taba sauran yayi alamun suma sujuyo sanan yafara tahowa gabanshi yace “Dady’s boy ya tashi daga baccin, Hello Zayyanu” wani mugun kallo Zayn yamai cikin zuciya da fushi yace “who the heck are you guys? What do you want from me? Where am I? Kunsan ni waye”? Har mutumin zaiyi magana wanda ke waya yace “give me chair Lamido” dasauri dayan yajuya yana saramai yace “to Oga” sanan yadauko kujeran karba yayi ya ijiye daidai gaban Zayn yay wani irin zama agaban Zayn yana kallonshi kaman yanda Zayn ke kallonshi da jajayen idanunshi, cikin dakewa yace “kaine Ogan su”? Gyadamai kai Ogan yayi, cikin fushi Zayn yace “then who the f*ck are you”? Fas! Wani mummunan mari yama Zayn da saida Zayn yay ihu. “Shit!” Yakai hannunshi yana shafa wajen tunda aka haifeshi ba’a taba marinshi ba sai yau, cikin wani irin zuciya still yana shafa kuncin nashi da kullallen hannuwanshi yace “how dare you slap? I will make you pay for this, sainasa arayuwan nan baraka karajin kwadayin Marin wani ba” HAHAHA! Ogan yay dariya kaman wani Boss yana kallon Zayn din sanan yakalli yaran nashi yamike tsaye yace “kumai ladabi bakin nan nashi ya mutu kafin nazo nai magana dashi” sanan yawuce chan yana ciro wayanshi yana dialing number dan cigaba da wayanshi.


Wani irin faduwa gaban Zayn yake ganin gardawan maza su uku sunyo kanshi yanaso yatashi yagudu amman babu dama, duwaiwai yashiga ja yana komawa baya suna binshi yace “don’t touch me, don’t f**king touch me, I am telling y……” bai karasa maganan ba daya daga cikinsu yamai kafa abaki sai jini kafin ya ankara saukan dukan maza kawai yakeji ta ko’ina babu ko digon tausayi sumai ta kafa sumai da hannu, tun yana iya ihu har bakinshi yau liss ya mutu yana kwance awajen kaman wanda yamutu bakinshi ya kumbura sosai yana fitarda jini hakama fuskanshi duk ya kumbura sabida da kafansu dake Dante da jungle booth sukamai duka.

“Oga angama” Lamido yafadi suna komawa baya, Oga ya katse wayan dayake yi sanan yataho ahankali yazauna akan kujeran yana kallon Zayn din dake kwance akasa yace “Lamido adagomin shi ya zauna” dasauri sukai kanshi dagashi sukai suka zaunar dashi saida yay kara sabida azaba sanan suka koma bayan Oga suka tsaya.
Kallon fuskan Zayn din Ogan yayi yace “welldone boys” sanan yakalli Zayn yace “you look Cute Dadys boy” HAHAHA yakara dariya sanan yace “dagamu sai kai adajin nan babu mai kwatan ka, kariga kabaro Abuja kabaro yankin garinku ma kwata kwata inda zan fada maka inda kake dasaikasha mamaki so kada ma kayi tunanin zaka kubuta daga hannunmu” yay dan shiru sanan yace “mutane uku suka bamu Wanan kwangilan na kidnapping naka, biyu daga cikinsu naso mu halakaka har lahira kamutu kawai babu labarinka, mutum daya kuma nasonka da ranka amman sai an gama karbe komi na mahaifinka sanan za’a maidaka, so the whole case akanka is interesting, kidnapping aikina ne tun inada saurayi amman bantaba kamo babban nama iri ka ba, kasan irin kudin dana samu nakuma ke samu akanka kuwa? Yanzu muka fara wasan” Hahaha yasake dariya sanan ahankali yace “kubashi abinci” hanyar jakansu Lamido yayi sanan yadauko wani bushashen buredi na irin na naira hamsin da pure water guda daya yataho gaban Zayn sanan ya Yar akasa kaman yabama kare, ture abincin Zayn yayi azuciye yace “I am not eating” dariya dukansu sukahau yi harda tafi, tsinkewa zuciyanshi yayi da kyar ya iya bude baki yace “konawa mutanen dasuka saku ku kamoni zasu baku zan baku x10 inhar kun sakeni” duk kallonshi suka tsaya yi kaman wayanda suka gamsu da maganan shi sanan sukahau dariya, kafin Ogan yace “ku karyamin hannunshi daya” wani kalan zaro idanu Zayn yayi tsabagen shock yama kasa magana, ganin sun taho kanshi gadan gadan yasa yafara ihu. “Somebody help me, help me, mutanen nan sun saceni, mutanen nan sun saceni” hannunshi suka fuzga suka warware kullin sanan suka kama left hand din Zayn yanajin yana gani wanda ke kama da doki ya ballamai hannu bass tsabagen azaba sumewa ma yayi, Ogan yace “finally gwara yayi bacci yadameni”.
Wanan kenan……




Tana zaune acikin dakin nan nata ita kadai dayake da duhu ko fitila babu tana zaune ta idar da sallan isha’i taji muryan Rakiya ta kwalamata kira cikeda bala’i. “Farrah” tashi tsaye tayi da sauri jikinta harya fara rawa hannunta dasauri takai ta taba goran pepper spray da Shafa tamata dake makale gefen zaninta tana numfashi da sauri da sauri. “Wai bakiji ina kiranki ba Shegiya Yar Jaka nazo dakin nan naki na tumakai kashekine kawai bazan yiba” Rakiya tafadi ranta abace, ahankali tasa hannu tabude kofan taramo tafito daidai lokacin itama Inna dake sallan isha’i lokacin da Rakiya tashigo gidan tafito tana kwace hijabin tana daurawa kan igiyan tsakar gidan tace “meya faru Rakiya”? Cikin fushi Rakiya takalli Farrah daya fito tana rabewa abango daga nesa dasu, Rakiya tace “yau kin hadu da Modibbo kobaki hadu dashi ba”? Da bala’in sauri Farrah ta girgiza mata kai tana hadawa da yatsu alamun a’a basu haduba, cikin fushi Rakiya tadubi Inna tace “Inna kinga dai yarinyar nan da Baba yasaka mana agida bata gabana bana shiga harkanta, wlh Inna takiyayan mini Moddibo na, ko ganinshi tayi tama chanza hanya dan banso ko hanya yahadasu, Inna yau ina kawomiki karanta na karshe wlh wlh na rantse da zatin Allah ko magana aka kara zuwa akacemin anga ta tsaya tanayi dashi koko kima hada hanya dashi komenama yarinyan nan ita taja, komenamata ita taja, Modibbo nawa ne nikadai ne matarshi a kap karkaran nan, idan kunne yaji……” Inna tace “gangan jiki ya tsira” Rakiya tajuya tawuce dakinsu itakuma Inna takalli Farrah da kanta ke kasa tanaji kaman ta kasheta tace “in ciyar dake sanan in ciyar da Baffan ki da kudina sanan kice zaki kwacema y’ata Modibbo Farrah wlh wlh zan iya halakaki har lahira ki kiyayeni” tana maganan tajuya fuuuu tai ciki ganin Malam yaleko daga dakin ahankali itakuma tajuya takoma dakinta tasamu gefe daya ta kwanta sai bacci Allah yasota takoshi.

Da asuban fari ta bude ido tana fitowa ta zaga bayangida sanan tadauro alwala, tadawo dakin ita harta saba rayuwa acikin duhu salla tayi na asuba sanan tazauna tana addu’a, mahaifiyarta kafin tarasu takoya musu karatu sosai dan haka ta iya ta iya salla daidai gwargwado sanan bata wasa da addu’a.
Gari nafara haske tafito ita kadai da sanyin safiyan nan nan tadauki tsintsiya ta share gidan tass, sanan tai wanke wanke, saida tagama sanan tabama tumakan gidansu da shanaye abinci daidai lokacin Inna tafito daga daki fitowa tayi daga wajen tumakan ta tsugunna har katsa alamun gaisuwa ko amsata Inna batayiba tawuce bandaki itakuma tadauki tulu dan fita debo ruwa rafi tanada kuzari da zafin nama nan da nan tashiga cike ko’ina, tana cikin tafiya zata koma rafin zuwan karshe kenan zatayi ko’ina yacika agaban rafin taga Modibbo tsaye rikeda wani paranti mai kyau da buredi kekai da kofi babba dayacika da shayi sai cinyan kaza agefe soyayye dakuma soyayyan kwai, kallo daya tamai tawani irin juya, dasauri yabiyota yace “Farrah Farrah tsaya” tana shirin kwasa dagudu yasha gabanta yana kallonta yana murmushi yabi kayan jikinta da kallo sunyi daka daka dan tabe baki yayi yakalli fuskanta dahar wani sheki yake dudda ko wanka ma batayi ba ga uban gashi a goshinta da giranta baki sudik har wani kyalli suke yace “bakiji ina kiranki bane zaki gudu, Kari nakawo miki nasan ba’a baki abinci awanan gidan bani tulun nan kigani” yakai hannunshi zai sauke tulun daga kanta dasauri takoma baya tace “iiiiii” cikin yanayi na kurmanci alamun yabar shi, jiyayi ranshi yabaci daurewa yayi yamika mata tray din yace “to gashi kici” dauke kai tayi takalli gefe dasauri dan bamataso taga abincin ranta yabiya, sosai yaji ranshi yabaci cikin fushi yace “wlh idan baki amsaba zansa akulleki amiki bulala dariya wawiya kawai sabida kinga ina sonk……” “Farrah” wani irin bari jikinta yayi jin muryan Rakiya daga ita har shi Modibbo juyawa sukayi suka kalli Rakiya, kana ganinta zakaga tsantsan bacin rai da kishi a idanunta dan takai minti daya tsaye a wurin amman ta daure dasauri takaraso wajen Farrah tai baya dasauri danta dauka dukanta zatayi Rakiya tasa hannu ta amshi tray dake hannun Modibbo tace “Allah sarki Hamma haka kake sona kabama Farrah takawomin gida, gidan su Atine fa zani nace bari nabiyo tanan, nagode Hamma Modibbo” tai maganan tana amsa tana juyawa dantama Farrah mugun kallo amman harta bace daga gudun, juyawa Modibbo yayi fuuu yawuce batare dayace ma Rakiya uppan ba, saida yabace mata sanan tai kwafa tawuce gida.


Awani irin zuciye Rakiya tashiga gidansu tana ihu. “Farrah, Farrah” Inna datagani na rege shinkafa atsakar gida tace “Inna ina Farrah”? Baki Inna ta tabe tace “kinfasan tunda tagama gyara gida ta debo ruwa sai kwasan awakai da shanaye ta wuce daji kiwo ko Rakiya baki sani bane? Me Wanan ahannunki” ko kallon Inna batayiba tajuya tawuce tashige dakinsu.




💫 FARRAH 💫


✍🏻M SHAKUR



Littafin nan is 500 pay into 3107021073 aisha Muhammad first bank Saiki turomin evidence of payment ta WhatsApp number na 07012181461 sainai adding naki a group din danake posting.



EPISODE 9️⃣
Tunda aka haifeshi yataso yafara wayau baitaba shiga wani yanayi na azaba dazaisa harya furta sunan mahaifinshi ba sai yau, yanada gatan dakome yakeso basaiya fadi ba za’amai, kafin yay tari anmai providing, baitaba shiga wani yanayi dazai kira mahaifinshi ba dan mahaifinshi has always being there for him kafinma ya nemeshi, yau shine dayaji azaban karya kashin hannu da idanunkashi biyu kuma yana cikin hayyacinshi bawai anmai anesthesia bane kowani abu ba baisan lokacin da bakinshi yafurta. “Paaa….paaa!” Da bala’in karfi hawaye na tsantsan azaba na zubomai, dariya gardawan sukahau yi babu ko alamun imani a tattare dasu sukace “sannu yaron Papa, ko Papaya kakira yau ba Papa ba bazaijika ba” sukai maganan suna haska fuskanshi da tocula dan duhu yasomayi amman tuni yasume sai hawaye dasuke kan fuskanshi nan fresh ganin haka yasa suka koma wajen Boss dinsu dake waya, juyowa yayi ya katse wayan dayake Lamido yace “Oga wai yaya ake ciki ne”? Dan ajiyan zuciya yasauke yace “sunce nabasu awa ashirin da hudu, yisu yisu su ukun sun kasa tantance abinda sukeso na akashe yaron ne koko abarshi da ranshi ne, kuma uban yaron da shine kadai zai iya bada order kudi idan muka kira ya gigice yana asibiti anyi kidnapping rayuwarshi wanan katon banzan dakuke gani, nidai nabasu 24hrs din, inhar basuyi making decision ba suka bani order kiran uban yaron ba dan Billyan dari nakeso yabamu toni kashe yaron zanyi asalin aikina najirana chan, bazan wuce gobe agarin nan ba saina kammala aikin nan, kuma bayan na kashe shi ko sunaso ko basaso saisun biyani kudin aikina da resources dina da akai amfani dashi inba hakaba suma sun sanni shi kidnapper baida amana dan tonamusu asiri zanyi ku yageta kawai” Lamido yace “bakada case Oga kome kace ayi hakan zamuyi bamaja dakai” yay maganan da muryan nan nashi irin na yan wiwi dinnan, murmushi Ogan yayi yanajin dadin aikin Lamido, dan sosa kai dayaga Lamido nayi yasa yace “ya akayi dawata maganan ne” dan yake Lamidon yayi yace “ahhh Oga dama nazo nadan zaga dajin nanne naga kaman akwai rugan fulani kusa sonake naje nasamo mana taba sanan idan akwai bani (yammata) nadan girgije nasa chaji kagane ai Oga eh yane” dariya Ogan yayi yana zare safan fuskanshi yace “dakai da Lamba kuje, Sagir yazauna gadin wanchan yaron kada kubata lokaci” angama Oga yay maganan yana cire tashi safar fuskan shima Lamba da Sagir duk suka cire sanan suka wuce shikuma Sagir yatafi gadin Zayn dake baccin wahala anan kasa kan ciyaye.


Wuraren 6 nasafiya wani kalan sanyi dakuma zugi na innanaha da hannunshi keyi yafarkan dashi daga wahalallen baccin dayakeyi bude idanunshi tass yayi yanabin dajin dasuke da kallo gasu Lamido duk suna kwance akan bargon dasuka shimfida akasa suna shakan bacci abinsu shikuma kwance a kan ciyayi, wani kalan fuzar da iska yayi abakinshi yana kokarin yunkurawa yatashi zaune amman yakasa sabida hannunshi dayake akarye kaman ya kurma ihu yakeji hannun ya kumbura, ahankali yabi buredi da pure water da aka bashi jiya daya zubar yakeyi akasa da kallo, yunwa yakeji bana wasa ba rabonshi da abinci tun na safen jiya da Mami tabashi baida wani cin abinci dama sabida su taba da sauransun dayake sha suna cikamai ciki amman inhar bai shaba sanan baici abinci ba yunwan dayake zuwa yaji yana zama extreme, dudda kalan yunwan dayakeji baikai kalan kishin ruwan dayakeji ba, lips dinshi sun bushe, bakinshi ya kape sabida tsan tsan kishi dayakeji ga azaban ciwo, tunda yake shi baima taba ganin pure water ba sai jiyan dasuka bashi, ganin abin yayi kaman fitsari amman yanda yakejin kishin nan yanzu he’s willing yasha maybe yamasha zaiji sassauci a zugin da hannunshi kemai, yunkurawa yayi da hannunshi dakeda lafiya amman ina abin yagagara sabida hannun a daure suke tare koyaya yay motsi damai lafiyan saiyaji amara lafiyan, wani kalan kara na azaba yasaki yahakura da tashin yana kallon sama yana tunani cikin tsananin tsoro da azaba da fargaba dakomi ma yace “am I going to die”? Yay maganan ahankali muryanshi a tsinke shi baitaba sanin akwai kalan wahala da azaba haka aduniyan nan ba saiyau, hawaye ne suka zubo daga gefen idanunshi na tsananin wahala ahankali yace “Dad, Mami I am scared” yay dan shiru sanan kaman karamin yaro yace “I am afraid of this place, I am afraid of this people, Papaaa” har cikin ranshi yakejin tsoron komi na wurin, shi baitaba fada ba, he just lived a wired life, baidama friends at all, rayuwanshi kawai yayi shaye shaye, yaci abinda yakeso, yasha abinda yakeso and have sex, ko matayen dayake sex dasu bawai yana magana dasu bane no, kawai yayi abinda yakeso yabasu kudi su wuce, ko kina sonshi kin sama kanki wahala ne dan baimasan yaya ake soyayya ba, baisan anything kan life ba, his entire life revolve around, shaye shaye, cin mata, kallon ball, ga zuwa club, babu any aboki namiji ko Aboki ya mace in his life, he is Zayn, and he is alone kaman yanda Baban shi ya haifeshi alone haka ma life bashing yake alone. Baisan inane wajen nan ba, baitaba zuwa wani gari a Nigeria ba banda Abuja wanda nan iyayenshi suke sai lagos, lagos ma airport kadai baitaba fita daga airport ba, baisan inane nan ba, baisan wani daji ne nan ba, baisan tayaya aka kawoshi nan ba, tayaya su Papa zasu rescuing nashi, ahankali yace “am I gonna die today”? Yakara tambayan sararin samaniya dayake kallo wanda rana ke shirin fitowa, hawaye ne suka zubomai ahankali cikin wata kalan raunanniyan murya irin muryan wanda yay loosing hope completely dinan yay giving up yace “Ya Allah save me please” (niko M shakur nace yau kasan da Allah Zayn).
Tafiyan abu dayaji akan hannunshi yasa dasauri yajanye idanunshi daga sararin samaniya yakalli hannu, wani bakin babban gizogizo yagani irin na dajin nan wani kalan zabura yayi yatashi yakwala ihu. “Ahhhhhhhhhh Spider, Spiderrrrrrrrrrr somebody help meeee” yanda yake ihu with all his power saika tausayamai kaman zai zare, farkawa kidnappers din sukayi jin kalan ihun da Zayn keyi duk atsorace suka zazzauna, ganin yanda yake ihu yana juye juye yakasa kabar da gizogizon shima gizogizon ya rude dan ihun Zayn ya rudashi yana neman hanyan guduwa, wani kalan tsaki Oga yaja. “Mtssswwwww what kind of a spoilt boy is this” sanan yakalli Lamido yace “please tashi kaciremai abinchan daga jiki koyabar kunnuwanmu suhuta

1 Comments On FARRAH
avatar
bertoul

10 months ago

Reply

Thanks

Please Login or Register in order to submit comment