Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yanada girma kaman haka,ban taba saniba saboda shirginsa,gaskiya kinsha aiki sosai na gyarashi"
Ƴar dariya nayi tareda matsawa na cire masa canvas ɗin ƙafarsa.
"Tohh yanzu abinci zaka faraci kokuma wanka zakayi?"
"Uhm bari naci abincin,dan yunwa nake ji sosai,sannan inason shan magani,saboda tafiyar danayi wajen yana min ciwo sosai"
Yaƙarisa maganar harda lumshe ido yana maida numfashi. Ganin yanda yake bansan lokacin dana kai hannuna ba na bude maballin rigar,wajen da ciwon yake nake kallo,hatta fatar cikinsa ma tayi ja,saidai bayyi jini ba alama yafara kamewa kenan.
"Uhm take it easy mana madam,sauri kike har haka ne?"
Yanayin magana na kulada yanda na ɗora hannayena akan cikinsa,saurin janyewa nayi tareda matsawa baya. Me yake damuna ne haka,yaushe na fara ɗaukar taba jikinsa ba komai bane ba.
Dariya yakeyimin tareda ƙarisa cire rigar gabaɗaya ya ajiye a gefe.
"Uhm nagode da kulawarki,hakan yana yimin daɗi idan naga kin damuwa da halinda nake ciki,sannan karki damu bazan ɗauki komai ba dan kin taba jikina,ya hallata a garekine ba shiyasa kika taba ba uhm?"
Ohh kunya ce takamani naji kaman na nutse a ƙasa,maza fa daman sun iya zarar zance.
"Yawwa yanzu naji kayi turanci dama ka iya ne?"
Nayimasa tambayar dan ya manta da waccar maganar,kaman hakan kuwa yayi tasiri,dannaga ya tafi tunani.
"Turanci kikaji nayi,uhm zai iya yiyuwa,dan wani lokacin mutane kan faɗa cewar inayi,ko karanta rubutu danake kawai gani nayi ina rubutawa,amma ban tuno makarantar danayi ba kuma"
"Taya ya hakan zai kasance toh?"
"Uhm ta haka mana,zubamin abincin naci inason shan maganinnan"
Zancenne yaƙare a haka na zuba masa abincin kaman yanda ya buƙata.
Har yashiga wanka ya fito ina zaune a ɗakin,dan cewa yayi kada na tafi na jirashi,daga shi sai gajeran wando ya shigo yana goge kansa da,wani ƙaramin ƙyalle.
Ɗauke kaina nayi,amma sai naji ya zauna a kusadani har muna gogar juna...ohh wannan sabon hali na goje na kasa gane kansa sam.
Mai yasaka na miƙo masa yafara shafawa,shuru mukayi dagani harshi babu wanda yace komai.
Tashi nayi zan tafi ya riƙo hannuna,
"Ina kuma zakije,ni kaɗai zaki tafi ki bari a ɗakin?"
"Uhn zan ɗora girkin dare,Sannan ba kace bacci zakayi ba?"
"Oh na tuna,to ki dunga zuwa kina leƙowa akai akai harna tashi"
"Hhhh to shikenan yanzu na tafi?"
Ɗaga kai yayi kaman baya so,wai dama wannan bawan Allah haka yake ne,kokuma yanzu ya koyi waɗannan abubuwan..
Bayan na fito inna tayi mamakin daɗewata a wajen gojen,amma batace komai ba,nima kuma banyi maganar ba.
Ina cikin jajjaga kayan miya naga ya fito daga ɗakinnasa ya fita,ƙananan kayane a jikinsa yana tafiya normal ba wannan bubbuɗawar. Ko ciwonne yasakashi oho..
Tsayawa nayi daga abinda nake na zubawa bayansa ido yana tafiyar,saida yaje saitin zaure ya juyo muka haɗa ido.
Kunya ce ta rufeni ganin yakamani ina kallonsa,da hannu yayi min alama nazo,fuskarsa ɗaukeda murmushi.
Zatona wani abu zaicemin,sai kawai ji nayi ya sumbaci goshina,tareda ɗallamin yatsarsa kuma a wajen duk lokaci guda.
Shafa wajen nayi tareda turo baki.
"Meyasa dana juyo kika ɗauke idonki kaman wacce nakamaki kina laifi?"
"Dama zaka iya fita ne?"
"Silly girl na kula wani lokacin idan bakyason bani amsa saiki yimin tambaya koh"
Hannu yakawo zai sakeyimin ɗall amma wannan karon na koma gefe ina dariyah,shima murmushi yayi tareda cewa.
"Zanje wajen su dunga ne karsuga shuru bayan sunsan nadawo"
"Banda bawa mutanen gari tsoro"
Nafaɗa ina komawa cikin gidan da sauri,yanda nasan bazai dawo ya kamani ba.

__***__


"Wayyo Allah nah"
Wani yaro yasaka kuka ana cikin karatu a aji. Malaminne ya tsaya da karatu tareda juyowa yana kallon yaran ajin,wanda yayi kukan ya kalla tareda tambayarsa mai yafaru.
"Kai tashi,miye kake yiwa mutane kuka a aji?"
"Malam Deejah ce ta sokamin wani abu a wuyana"
Tun kafin malamin yayi magana tayi caraff tace.
"Malam bacci yakeyi a aji kana karatu"
Jijjiga kai yayi tareda riƙe kai,ya akeso yayine da wannan tantiriyar yarinya,duk ajin yarane masu shekaru biyar zuwa bakwai,amma ita shekararta kusan sha uku,dukka tafi yaran aji girma. Shi ba abin yace akaita aji sa'anninta ba babu abinda ta iya,in yayi kokarin cewar a koreta kuma abokinsa Musbahu ne ya roƙeshi akan ya barta a ajin.
"Zo nan kizo ki tsaya a gaban aji"
Yafaɗa a zuciye,tahowa tayi tana kallon ƙasa kaman wata ta Allah.
"Karanta min Kul'azubi rabbin nass naji,tunda shi bacci yakeyi ke ai idonki biyu ina"
Wuri wuri tafara da ido alamar bata ma san mai yakecewa ba,sai wuss wsusss takeyi kawai ta bakinta.
Bulalar hannunsa ya ɗaga ya zambaɗa mata a gadon baya,sake zura mata yayi,aikuwa take ta kwarara ihu.
Ƴan ajinne suka sheqe da dariyah ganin yanda take tsalle tana dadare.
"Malam aradu ya isheka,dan kaga abokaina basa biyoni cikin wannan makarantar taku ne ina ko,wlh zaka fito daga ciki ai saina ƙona ka kurmus mungu kawai,ku kuma ni kukeyiwa dariya koh,idan na dawo gobe sai nayi muku shegen duka"
Tana gama faɗan hakan ta fita da gudu daga ajin.
Hanyar gidnasu tanufah tana ihu,duk inda ta shige sai an kalleta,amma ko a jikinta..
Tana yankowa kwanar gidan turuss tayi da suka haɗa ido da Musbahu a zaune a ƙofar gidan.
Raragefe tafara zata shige gidan taji muryarsa.
"Zo nan wato da girmanki kika zagaye anguwa kina kuka kaman mahaukaciya koh?"
Dawowa tayi gabansa ta zauna a ƙasa,har sannan bata daina kukan ba,wanda yasan na iskanci ne bakomai ba.
"Menene me aka miki,iyanzu ba'a tashi daga makaranta ba,meyasa kika taho"
"Haka kawai wannan abokinnaka mai gemun bunsuru sai yayi ta dukana ban masa komai ba,ai aradu dan yaga abokaina basa bina cikin makarantar ne shiyasa yakemin abinda ya dama,da duk saina ƙone makarantar naga tsiya"
Shuru Musbahu yayi yana nazarin maganar tata,tunda yake da ita bata taba maganar wasu abokanta ba sai yanzu.
"su waye abokanan naki?"
"Uhm uhm kona fadamaka baka sansu ba,sannan sunce kada na faɗawa kowa waye su.....nidai bazan koma makarantar nan ba"
"Zaki koma mana khadija,makaranta ai yanzu kika fara,saidai in kinaso nayi fushi dake na daina saya miki shayin safe toh,idan nasiyo abuna da daddare ma na daina baki"
Zaro ido tayi,da alama batason aikata abinda yace ɗin.
"Zan dunga zuwa toh,amma wlh ni na tsani wajennan banasonsa,nafison wannan ta safen,saidai ita daɗewa ake ba'a dawo gida ba. Kuma ma in gaskiya ne naga ƴan gidan basa zuwa makaranta,kowa in yace bazaije ba barishi ake saini za'a takurawa"
Kan gari ya gari take maganar tana kuka kaman ance sai ta faɗa dole.
"Yau bakiyi wanka ba ko"
"Uhm taya ka gane baka gidan,nasan ma faɗamaka akayi banyi ba,gidannan akwai ƴan baƙin ciki buhu"
Dariya Musbahu yayi jin tambayar tata lokaci guda.ba wai sanin yayi ba,kawai dai yasan idan ya tambaya zaigane tayi ko batayi ba
"Tun bakiyi wanka ba yau babu abin daɗi,kuma kika gudo daga makaranta,tashi ki shiga gida."
"Nashiga uku ka bari yanzu zan shiga gida nayi wankan,makaranta kuma bazan sake gudowa ba,amma kacewa abokinnan naka ya daina dukana toh"
Tana gama faɗan hakan tashige gidan da gudu. Dariya Musbahu ya dungayi ganin wauta irinta Deejah. Haka kawai yake tausayinta,yarinyar tana buƙatar tallafi na gyaran rayuwarta,wanda in ba'a taimaka mataba zata tashi kaman gara.
Allah ya gani yayi niyyar inganta rayuwarta daidai ƙarfinsa,gashi kuma wani satin yake shirin tafiya interview na shiga soja,dama ya daɗe yana son tafiyar,sai yanzu yasamu nasara.
Ga kuma wani abu daya gano a wajen Deejah,aljanun da take tareda su ba ajikinta suke ba,zaman ta a jeji ita kaɗai da rashin kula yasa suka zama makusanta fiyeda mutane ƴan uwanta,shiyasa mutane ke ganinta kaman itmaa ba mutum bace.
Dan haka Maganin dayake tunani bazayyi wuyar yi ba,muddin tana shiga cikin mutane tana alaƙa dasu akai akai,sannan tafara yin karatu musamman na addini akwai alamar zasu iya barinta.
Wanda yasan babu mai iya yimasa wannan aikin sai Sumaimah,indai tana tareda itah zata iya taimakonta,amma ta yaya.
Tana gidan mijinta yaushe zai ɗora mata wani nauyi da bai shafeta ba,duk da yaji ana labarin rayuwar gidan ba kaman daba,shikansa mijinnata yanzu yanada nutsuwa sosai,wanda shima yaga hakan da idonsa a tattare da itah lokacin dataje asibiti.
Ganin abun kaman bazai yiyu ba kawai barin zance yayi a ransa.





Littafi na ɗaya ne dana biyu kaman yanda na sabayi,na ɗaya bati siddan,na biyu kuma Naira 300 ne dan haka zaka iya biya tun yanzu kafin a shiga kashi na biyu.

3131951977
Auwal Sadiya
First bank

Ko katin mtn ta nan
09035784150

VTU ta nan
2347068390570

Shaida kuma ta nan
09035784150

Ƴan niger ku tuntubi wanann number.
+227 97 21 16 15
----------------------------------------------------

Sadi-sakhan ceh
09035784150
Share please




*SANADIN CACA*


Mallakar SADI-SAKHNA


PROFICIENT WRITER ASSOCIATION



*USERNAMES*
FACEBOOK PAGE:Sadisakhna
WATTPAD:@SAKHNA03
AREWABOOKS:@sadeesakhna
PHONE NO:09035784150
________________________________
*Book 1*
Chp[29]


[Sumaimah a mahangar gani]


Tun lokacin da Goje ya fita har dare yafara kafin ya dawo,ina kwance akan gadona na ɗakin inna najiyo muryarsa yana ƙirana.
Shuru na ɗanyi saida inna tace
"Sumaimah ba ƙiranki yake bane?"
"Uhmm eh"
Kaina a sunkuye naje bakin kofar ɗakin,saidai ban ganshi ba da alama ya yi ƙofarsa.
Dan haka hijabina na saka akan doguwar rigar jikina na nufi ƙofar tasa.
Ɗakin a bude yake amma baya ciki,da alama yana bandaki,dan haka zama nayi akan katifa ina jiransa.
Ganin yaɗan daɗe yasa nayi tunanin inaga wanka yakeyi,hakanne kuwa dan shigowa yayi dagashi sai gajeran wando.
Bai min magana ba ya fara shafa mai,nima bance masa komai ba ina nan zaune. Sai bayan yagama kafin yazo inda nake ya zauna,kallona yake kaman mai nazari yakasa cewa komai.
Duk da cewar babu wani wadataccen haske iya na wayarsa ne daya kunna amma ina ganin fuskarsa.
"Meyasa baki bude wannan abunba da kikaga ina wanka?"
Saida yayi magana na kulada ledar da take tsakar ɗakin,sakkowa nayi na buɗe,tsirene a cikin yaki albasa.
"Lahh ban gani bane shiyasa"
"Uhm toki ɗibama inna kema kuma in zaki ji sai......."
"Wai anya kuwa inna zataji yanzu,dan yanzu muka gama cin abinci,nima kuma gaskiya ba lallai ba,amma barina tafi dashi koh?"
Nafada inason barin ɗakin,danna kula babu wani abu dayake buƙata,kawai ƙirana yayi,sannan yasamu sauƙi sosai bare yace da wani abun zan taimaka masa.
"Ahah tunda kun ƙoshi shikenan ajiyeshi kawai sai kuci da safe"
Na ajiyeshi,ba tafiya zanyi ba sai na tafi dashi kawai ai.
"Uhm naga nima tafiya zanyi to...."
Dariya yayi min tareda cewa.
"Ki tafi inaaa,aikin dawo ɗakin mijinki kekam,daga yau ban yadda ki dunga kwana a ɗakin inna ba,nan ne ɗakinki"
Dumm gabana ya buga,ban taba tunanin hakan nan kusa ba.
Hannuna ya zawo ya zaunar dani a gefensa,wanda hakan yasakani ajiye ledar da take hannunnawa. Kallona yake cikeda sigar damuwa da neman taimako wanda bansan na menene ba.
Hannayennawa yahaɗa dukka biyun a cikinnasa,tareda tattaro dukkan wani sauran nutsuwarsa,nima ganin hakan yasa na kafeshi da ido.
"Sumaimah nine na koreki da ɗakinnan a zuwanki na farko,a yau kuma na buɗe baki ina rokon daki zauna a cikinsa,ko kaɗan bawai tilastaki zanyi ki zauna dani ba,illah iyaka ina son hakan. Kiyi haƙuri da abubuwan dasuka faru a baya waɗanda nayi miki,bazan ce ki manta dasu ba,amma please kada ki ƙullaceni akansu. Dan Allah ki zauna dani ƙarƙashin inuwa ɗaya,idan kin amince dani kaman yadda kika faɗa,ki bani damar shiga a rayuwarki a yau ɗin,idan kinga kuma abin yayi miki sauri ki faɗamin zan barki kiyi nazari akai"
Bayan yagama maganar shuru yayi domin yaji mai zance,ganin nayi shuru yasa ya murza hannaye na.
Ajiyar zuciya na saki tareda cewa.
"Ba....bansan mai zance ba takamaimai akan wannan maganar,abinda ya faru da baya ya riga ya wuce wanda dama hakan ake fata a manta dashi. Batun nadawo kwana ɗakinnan kuma idan hakan ka buƙata to dole shi zanyi,saboda gidanka ne kuma ikonka ne,inda kaga dama ka sakani matuƙar bawai cutarwace ta shigaba dole anan zan zauna.
Sannan kana alaƙar aure kuma haƙƙinka ne daman,kaine da baka biɗa ba tunda. Zan iya hanaka idan da a bayane baka ciyardani ba baka tufatar dani ba. Amma a yanzu idan nace baka ɗaya daga cikinsu nayi ƙarya,dan kayimin wanda ban tsammata bama. Dan haka ka buƙaci samun nutsuwa dani na hanaka saboda wai kayimin ba daidai ba a baya bai tasoba"
"Hmmm naji daɗin bayananki,sannan ina jin daɗi a duk lokacin dakika faɗomin matsayin da nake dashi a wajenki,amma a yanzu ra'ayinki na buƙata ba wai matsayina ba,na yanke shawarar son fara rayuwa dake,sannan banason batun musgunawa ko cutarwa yashigo ciki. Shin kina ji a ranki nayi cancantar da zaki iya miƙamin amanar kanki?"
Wannan tambaya ta taba zuciyata sosai,ni wacece da bazan amince ba. Zare hannuna nayi daga cikin nasa tareda saqalasu ta bayan wuyansa,kuka na fara na farinciki,ganin lokaci guda kaman almara Allah ya karkato da hankalinsa gareni,ya kasance namiji mai nutsuwa da ban taba tunani zai zama,idan wani yace a lokacin baya zan kasance a tsakanin kafaɗun goje to zan iya rantsewa ƙarya yake. Amma yanzu sai nake ganinsa kamar yafi sauran mazan garin ma sauƙin kai.
Hannunsa naji yasaka yana bubbuga bayana,mun dan ja lokaci a haka kafin nazare hannayennawa,a yanzu kuma ina kan cinyarsa a zaune.
Naso kafin na bashi kaina kona shirya yin mu'amala ta aure dashi sai yaƙara nutsuwa da kuma sanin addini sosai,amma tunda ya buƙata ɗin zan amince masa,wataƙila hakan yaƙara tasiri wajen gyaruwar tasa.
Ina cikin tunanin naji bakinsa akan nawa,bansan lokacin daya iso kusa har haka ba.
Kwantarni yayi akan katifar a hankali,tareda ƙoƙarin maidani cikin sahun jerin matan aure masu albarka. Lokacin danaji mai afkuwa tana shirin afkuwa saurin buɗe bakina nayi tareda karanto Addu'ar da ma'aiki muhammad (SAW)ya umarcemu dayi,dan nasan gogan koda ya iyata ma bata ita yake ba a lokacin,abune dama da bai dameshi ba yanzu ake ƙoƙarin ganar dashi.
Nasha wahala ba kaɗan ba a wajensa,duk da cewar yayi iya ƙoƙarinsa wajen ganin bai min ta ƙarfi ba,amma halitta ta da tasa ba ɗaya bace.
Bayan komai ya lafah shuru naji yayi lokacin daya gangara ɗaya barin katifar,zato na idonsa biyu,saida naji minsharinsa kafin na jijjiga kai,wato a wannan yanayin najasar shi bacci yayi abinsa.
Tashi nayi da ƙyar ina cije baki na ɗaura zanina,jikina banda tsami babu abinda yakeyi,abinka da ban saba wannan dambarwar ba.
Randarsa na leƙa naga akwai ruwa a ciki,godiya nayi ga Allah kafin na ɗiba na nashiga banɗakinsa domin tsaftace jikina.
Lokacin dana fito har baccinsa yafara nisa,ruwan dayake hannuna na yarfa masa,nayi sa'a kuwa ya juyo yana kallona.
"Ka tashi ka tsaftace jikinka,bai kamata ka kwanta da najasa ba,ina ka iya wankan tsarki ko"
Tashi yayi ya zauna yana kallona,ba fuskata yake kallo ba,dan haka sai na bi inda yakalla,kan kirjina idonsa yake,kasancewar iya zaninne kawai jikina..
Hannuna na saka a wayance na tare saboda kunyar data kamani..
"Uhm badai wannan wankan bane da ake wanke bangare bangare na jiki,na iya shi mana,na kanyi innayi mafarkin wata......wanann kam maza dayawa ai sunayinsa..
Meyasa kike kare jikinki,bayan yanzu naga......."
"Am na bar maka ruwa a banɗaki,wataƙila zai isheka"
Da sauri nayi maganar ina nuna masa ƙofah,dariya yayi tareda dan jan hancina,dan ya kula so nake yabar zancen..
Kafin ya dawo kayana mayar tareda yaye zanin kan gadon naɗauko wani na saka,duk da yanda jikina yake min magiyar zai kwanta.
Ina kwanciya naji alamar shigowarsa ɗakin,yi nayi kaman bacci nake saboda in yayi magana ma bansan mai zance ba..
Ina jinsa ya hawo kan katifar tareda jawoni jikinsa,daga ƙarshema ya ɗora kaina akan kafaɗarsa.
"Saida safe matata,nagode sosai da kyautarki"
Yafaɗa a hankali tareda sumbatar goshina.
Zanyi ƙarya idan nace hakan bayyimin daɗi ba.

Dasafe dana buɗe ido ni kaɗai nagani a ɗakin,tashi nayi zaune ina ƙarewa ɗakin kallo. Hannu nasaka a inda goje ya kwanta,wajen ya dan lotsa saboda nauyinsa. Murmushi nayi ina shafa wajen,yayinda ƙwaƙwalwata tafara tariyomin abinda ya faru jiyah..
Zabura nayi zan tashi amma naji ƙafafuna kaman lilo saboda rashin ƙarfi,haka na manta dasu cikin dauriya na fito daga ɗakin,kaman zanyi kuka na nufi ƙofar inna.
Wayyo ni ƴasu mai zancewa inna,daga cewa jeki ana ƙiranki kawai sai kwana,nasan kuma tana kallona zata san mai yafaru,wayyo Allah ka taimakeni.
Daga bakin ƙofar na rakabe ina kallonta,a zaune take tana saqa tukarta,gefenta kuma rediyo tana jin labarai,kana kallon yanayin zaka san rana tayi sosai,meyasa goje bai tasheni ba to.
Kaina ya sunkuye nashiga ƙofar,ko kaɗan naƙi bada ƙofah mu haɗa ido da inna..
Zama nayi a gabanta tareda gaisheta cikin wata munafukar murya,wadda nasan saita nutsu tajini.
Amsawa tayi cikin fara'ah tareda tashi ta nufi ɗakin da muke ajiyar kayan abinci.
Kwanuka da ɗauko dakuma ledar tsiren jiyah,kenan gojene ya kawo mata ita da safe?
"Ga nan abinci kici"
"Uhm inna ke kikayi abin karyawar?"
"Ehh mana nice nayi,tun da sassafe goje dayazo gaisheni yace nayi abincin karyawa bakyajin daɗi,yaran gaji ma korarsu yayi daga gidan sassafe,wai sai sun tafi makaranta kada su dameki,nasan lokacin ko mai gadi ma bai buɗe makarantar ba. Gaji haka tayi ta faɗa daya fita har tayi shuru"
Wayyo goje bazai gasheni ba,saikace wata ƴar sarki,wato da kansa ma yazo yafaɗawa inna abinda yafaru,ninan nake wata haukata....kai maza kunyarsu da sauƙi.
Daukar kwanon abincin nayi daga gaban inna nashige ɗaki da gudu.
Ina shiga nasamu ta shiryamin kayana a cikin jakata tsaff.
"Inna yanaga kin shiryamin kaya koh....."
"Gojene yace na shiryamiki kayanki ki koma ƙofarsa,daga yau bazaki sake kwana a wajen ba,kinga kuwa mai abu zai karbe kayarsa ai dole na tattaramiki kayanki,duk da banason zaman ni kaɗai ɗin,saina ƙira su kursiyyah kwana"
Ohh jinayi kaman ƙasa ta buɗe na shige,wai dama haka yakene ko yanzu yazama haka.

.....bayan wata biyu.....
Abubuwa da dama sun faru,ciki harda sabuwar rayuwar data ɗinkeni da goje,mukayinta cikin farinciki da mutunta juna.Na koma ɗakinsa da zama,wanda yanzu yazama ɗakinmu,zama na dashi na gane ɗabi'unsa na sauƙin kai da kuma soyayyar dayake nunamin babu kama hannun yaro.
Makaranta ma shine yake kaini kullum ya dawo dani. Yanzu nasan lalurar dayake ɗauke da itah harda aljanu,na gano hakanne tun bayan bamu daɗe dafara zama tare ba sai naga yafara sauyamin,wani lokacin ko kwana bayayi a gida.
Hakan ya dameni sosai da sosai,gashi duk yanda zanyi dashi bazai bani amsa ba.
Hakan yasa na samu Tunga na tambayeshi,baicemin komai ba kawai sai rakani bukkar da goje ya haɗa a jeji dayayi..
Ranar har kuka nayi daga halinda yake ciki a bukkar,harma da labarin halin dayake ciki duk ya faɗamin komai. Da ashe shine abinda zai faɗamin duk ranar dana tambayeshi.. Nida Tunga daƙyar muka lallameshi yafito daga wajen,anan nabawa Tunga shawarar ya ƙona bukkar,da dafarko yaji tsoro amma nace masa ya aikata bakomai..
Nikuma tundaga wannan lokacin nafara nema masa magunguna na islamic batareda saninsa ba,ko turarene na maganin saina sakashi da sunan turaren ɗakine,tun yanacemin bayaso yana sakashi ciwon kai har ya fara sabawa.
Ruwan shankuwa dama anan nake saka masa tofin da ake na ganyen magarya na aljanu. Sannan na dage da kunna karatun ƙur'ani ko yawan karantawa a koda yaushe.
Yanzu ya daina yin wannan fushin da kuma shaye shayen,amma wani lokacin ko tafiya yake sai ya tsaya kaman ya daskare,sai daga baya kuma sai ya cigaba da tafiyah,ko zance yake sai ya tsaya kaman mai son tuno abin. Tsoro ne yafara shigata da wannan sabon halayen,wanda hakan yasa nasake dagewa na yimasa maganin a boye,yanzu har da daddare idan yana kwance saina ina tofa masa Addu'o'i,amma maimakon naga sanji saima gaba gaba dayakeyi.
Duk kuma wannan abun da akeyi babu wanda yasani dagani sai Tunga,saboda baya shiga cikin mutane sosai. Soyayyarmu da mu'amalarmu bata sanja ba ko kaɗan,dan ko yana waje yaji ciwon kai da sauri yake dawowa wajena,nikuma sai nake amfanj da wannan wajen bashi maganin batareda yasani ba.
Yauma a zaune yake akan kujerar daya saka a ɗakinnamu,ruwan Addu'ar dana karbo a wajen wani mai magani nabashi,cemasa nayi na ciwon kansa ne,dan haka bayyi musi ba ya karba. Bayan ya shanye miƙomin kofin yayi na ajiye.
"Sumaimah inason yin tafiyah zuwa gwagwalada yau,amma ba kwana zanyi ba"
Innalillahi badai waɗancan mutanen bane da mukasamu wata biyu bayyi zancensu ba. Aikuwa sune dai.
"Sun gano ina raye har sun nemi naje meeting ɗin dazasuyi yau ɗin,bai kamata na boye tamkar matsoraci ba,inason na tunakresu na kuma faɗamusu cewar na fita daga ƙunyarsu"
Ajiyar zuciya nasaki na jin daɗi ganin ya yarda zai fita daga shirginsu,dan dama sunyi magana da wani dan auguwar kan zai fara safarar shinkafa dashi,nayi farinciki sosai danaji yadaina dabanci zai fara sana'a irinta sauran kamilallun mutane.
"Eh to hakan yayi,amma dai bazaka je da wannan jakar ba ko?"
"Uhmm kekam yadameki da jakar nan,waya sani ma ko kinfi damuwa da itah kanni"
Yafaɗa yana sauya fuska,zama nayi akan cinyarsa tareda kama kumatunsa ina murmushi.
"Ni na isa,kawai dai ina tunanin danshi zasu nemeka ne,sannan indai har za'a dawo dakai garinku ace ka kulada ita,to tanada matuƙar muhimmanci"
"Uhm hakana kam bazan je da itah,idan kuma naga sunsan tana wajena to zan san yanda zanyi"
"Inaso na faɗamaka ma yau nakeson zuwa gida,rabona da zuwa tun lokacin danaje baba yana asibiti"
"To shikenan kije,dama nima bana nan,za'a bar inna ita kaɗai yaukenan"
"Eh kam,amma da kaɗau Tunga ku tafi mana tare,kaga kowani abune ma biyu yafi ɗaya ko a wajen ƙirge"
Da bai yarda da zancennawa ba,amma a hankali nashawo hankalinsa ya yarda zasu tafi su biyun a mashin ɗinsa. Kasancewar bamuda nisa da can ɗin.
Sai bayan ya shirya yafita daga gidan kafin nima na shirya... Tunda ya fita nakejin faɗuwar gaba wacce bansan ta mecece ba.
"Allah dai yasa alkhairi ne"
Nafaɗa a raina.




Littafi na ɗaya ne dana biyu kaman yanda na sabayi,na ɗaya bati siddan,na biyu kuma Naira 300 ne dan haka zaka iya biya tun yanzu kafin a shiga kashi na biyu.

3131951977
Auwal Sadiya
First bank

Ko katin mtn ta nan
09035784150

VTU ta nan
2347068390570

Shaida kuma ta nan
09035784150

Ƴan niger ku tuntubi wanann number.
+227 97 21 16 15
----------------------------------------------------

Sadi-sakhan ceh
09035784150
Share please




*SANADIN CACA*


Mallakar SADI-SAKHNA


PROFICIENT WRITER ASSOCIATION



*USERNAMES*
FACEBOOK PAGE:Sadisakhna
WATTPAD:@SAKHNA03
AREWABOOKS:@sadeesakhna
PHONE NO:09035784150
________________________________
*Book 1*
Chp[30]




Goje baya nan,dan haka da ƙafata na taka zuwa gidan,kasancewar ba wani nisa ne dashi sosai ba.
Lace ne a jikina mai kyau a jikina wanda goje yayimin,sai hijabi dana saka da takalmi,naƙara fari da ƙiba ainihin siffah ta ta jin daɗi ta bayyana,ko makaho ya shafani yasan na sanja fiyeda da..
Sallama nayi daga shigata gidan,kasancewar ƙofarmu na dan ciki saida na gaisheda matan dake wajen tukunna.
Suma kallona suke da mamakin sanjawar tawa.
Wucesu nayi zuwa ƙofar tamu,ammi tana zaune da tiren gyaran shinkafa a gabanta,faɗi in faɗa suke da rammah wacce take daga cikin ɗakinta.
"Haka kawai dankin rainani kinga bana magana,lokacin da aka kawo Sumaimah nina ɗauketa,wannan kuma har an baki kice wajena zata dawo? To naji da nawa tarin gayyar mana,ba kayanta dazan ɗauka,kuna nan dake da itah mutu ka raba,indai kin auren ubanta. Yo ubanta mana tunda ya riga ya lakato ai dole ya tanɗe"
Sallama nayi ganin abinnasu ba ƙarewa zayyi a lokacin ba.
Ammi ce tafarayin shuru tareda ɗagowa ta kalleni,murmushin ƙarfin hali nayi mata kana na zauna a wata ƙaramar kujera a gefenta.
"Lahh Sumaimah kece a gidan"
"Ammi na sameku lafiya ya gida?"
"Uhm gida kam gashinan mana,kekam ai kinji daɗinki,muna jin labarin goje ai a gari yazama tamkar ba shiba"
Uhm kawai nace,daga zuwa sai zancen daɗi kawai,koda yake haka gidannamu suke,basuda aiki sai zancen ayi auren yarinya ta huta,a ga mai take sakawa kokuma mai take ci,sannan ya kuɗin mijinta.
Wata maganar da rammah tayine ta katseni daga tunanin.
"Ahh lallai kam,tayi bulbul da ita ga zahiri nan ma harda shigar ciki,da alama shine yasaka ta kyan bawai zallan jin dadin bane yanda ake tunani"
Wani takaici ne ya cikani amma haka na shanye,wai basuda abin faɗa sai wannan ne,ita kam inna rammah ko gaisawa bamuyi ba da itah,tafara zancen da bai shafeta ba.
"Ammi ina baba kuwa,ko ya fita?"
"Wai ya fita,tun safe ya tafi akan magana gonarsa rabin,ya siyar da ɗayan ai kuɗin ya bata,shine har kika samemu a asibiti wancan karon,to zancen ya tafi yau ma..
Shiga ɗaki ki cire hijabin mana,sannu da zuwa ya innar gojen?"
"Tana nan ƙalau"
Hira muka dan fara tabawa,wanda yawanci na abubuwan da suka faru bana nanne,muna tsaka da haka najiyo kukan yarinya tundaga bakin shigowa gidan,saikuma muryar Musbahu yana magana kaman mai faɗa.
Butt suka shigo a ƙofar yana riƙe da hannayenta,sai dadare take tana jijjiga kai.
"Kayi min rai yaya Musbahu wlh bazan sake fasawa kowanne yaro goshi ba daga yau,Allah da gaske nake"
Ihu take kan gari ya gari kowa na jiyota a gidan,abinda yabani mamaki babu wanda ya kulada sha'anin,har inna ma batace komai ba sai cigaba da tayi da aikinta. Hakanne yasa na gane cewar Deejah ce yar baba uwaisu daya samo a caca,wacce nake jin labarin ta..
Bulalar hannunsa ya zuba mata a gadon baya,ta kuwa sake ƙara saurin kukannata,ganin bazan iya jurewa ba yasa na tafi da sauri na karbeta,lallai itama wannan da sakarci take,ta kusana girman jiki amma take abin yara haka.
Haƙuri na fara bashi tareda janyeta daga hannunsa,har sannna bai kulada ni ba sai dukanta yake.
"Kayi haƙuri yaya Musbahu duka baya magani ko kaɗan,kada ka jimata ciwo a garin gyara"
Sakin hannunta yayi ta zube a wajen tana burburwa. Shikuma sai numfashi yake sakewa kaman wanda yayi faɗa da bijimi.
"Hmmm ƙyaleni Sumaimah na koya mata hankali,bakisan abinda tayi bane shiyasa,ɗan shugaban makarantar fah ta rotsewa kai,kuma a hakan bai isheta ba za'ayi mata hukunci ta zazzagi malaman da sunyi jikanu da itah,shine yanzu suka ƙirani kan naje na tafi da itah sun koreta a makarantar. Wannan fah itace makaranta ta uku dana sauya mata,banida buri illah naga tayi hankali,amma ita da alama

Please Login or Register in order to submit comment