Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

takira katon gardin nan a waya tace yazo zata bude mishi hanyar baya yashigo



Haka kuwa akayi tsaf yashigo ba Wanda yaganshi yashi harcan bedroom anty na taimakon Hajiya zabbau



Itakuwa anty tana bathroom dinta tana aikin kuka tagama wankan har ta zura doguwar Riga amma tana ta aikin kukan rashin iyaye



Daddy suna zaune a compound din gidan sa shida su alhaji dan asabe suna tattauwa


Sai yaga motar da yabayar aje a dauko su matan maigari sabada anty tadan ji dadi


Cikin farinci ya musu iso har part dinta

Yanuna musu kujera suka zauna yace yace bara nakira muku ita tana ciki ne


Kafin daddy yakarasa dakin anty sa shegen gardin nan yafara magana kamar haka


Kai amma Gaskiya maryam kinsan kan duniya wato dan kinga bakowa a ashashinki shine kika zamu inzo gidako


Shifa wannan tsohon mijin naki yana dauka kedin wata ta Allah ce ko


Dan Allah kiyi sauri kufito daga wankan nan nima na watsa nace kibari muyi tare kince na tsaya kifara saboda kifita da farko


anty dake durkushe bandaki taji kaman magana a bedroom dinta sai tayi saurin budewa dai dai lokacin da daddy yabanko kofar yashigo


Jiri ne kefaman diban daddy saboda abinda yaji kuma yagani


Maryam dinsa takawo mai kwarto daki
Matar dayake so fiye dakomai ya yarda da ita



Ai kuwa wannan katon yafara shikenan kinja mana maryam yau asirinmu ya tuno anty ta daga hanu tasa akai tace nashiga uku


Waye kai dan Allah kafadi gaskiya cewan bansan ka ba


Wallahi alhaji bansanshi ba tana kuka daddy kuma da idonsa suka canja kala zuwa ja yace kincuceni maryam kinci amanata maryam

Duk hallacin Dana miki ace da wannan Abu zaki saka min


Ya bar dakin dasauri anty tabi bayanshi tana kuka tana wallahi alhaji bansanshi ba sharri aka kulla min


Daddy bai saurareta gashi duk inda suka wuce sai abinsu kafin wani lokacin gida yadauka ai kwarto adakin amaryar alhaji

Maryam suna daki bata San meke faruwaba ganin su nazeefa sukayi sunbanko kofar dakin


Nazeefa tace to kina ga uwarki can an kama ta dabkwarto yau dai asiri ya tuno



Cikin zafin nama maryam ta tsinke na nazeefa da kyawawan marika har uku

Tace har kin isa kidan ganta uwata wanann kazamin aikin ban dau mataki ba


Tana gama fadin yahaka tayi waje falo ta nufa ganin taron mutane a falon yasa gaban maryam faduwa ta karso taga antynta a tsugune tana kuka


Muryar daddy taji yanacewa nasakeki saki uku maryam


Iya Kalmar dataji kenan ta yanke jiki tafadi kasa sumammiya anty tayi kan maryam tana maryam kitashi dan Allah karki mutu kibarni kedai kika rage min yanzu



Anty asiya ta zo aguje itama ta tallafo maryam din sai suka ga jini na zuba yana bin kafar maryam



Anty shukura tayi salati ta dauki waya takira doctor nabila ba afi minti biyarba ta karaso tana ganin maryam tace ai bari tayi tasamu miscarriage ai kuwa anty kukan ma yakasa zuwa saboda tashin hankali

Kasa kawai take kallo takasa motsi

Falon yadauki magana Hajiya zabbau tace Allah mungode maka da maka da tuni asirin munafukan agidan nan



Mummyn Dagash tace nice da godiyar Allah ashe an yi rufarufa za a aura wa Dana yarinyar datagama yawon taxubar dinta to ta Allah bataku



Kowa da abinda yake fada Mara dadi akan su anty


Daddy king da alhaji dan asabe jikinsu duk yayi sanyi ballantana uban gayya daddy



Shigiwar Dagash da alhaji imam da abokin shi alhaji sudais ne yasa kallo yakoma Kansu



Dagash yace mekefuruwa haka agidan

Mummy cikin jin dadi tace Allah yasoka my Son da ka rainin dan shege agidanka


Kan dagash yadaure kafin yayi magana Alhaji imam yace mekike fada Aisha tace ai yaya bazaka gane ba mushiga kawai kuhuta kwaji komai



Kaman daga sama yaji muryar da bazai taba mantawa dashiba a rayuwarsa anty tadago kai tana kuka tace Allah meyasa baka kashe ni ba kafin zuwan wannan rana


Caraf idonsu cikin najuna cikin tsanin firgici anty tazuba razanannar kara tana nuna Alhaji imam da hanunta tayi bayan tafafi anty asiya tayi saurin tareta



Alhaji imam kuwa salati yake ta na natawa yazube shima dagash ne yayi saurin taroshi



Mummy tace wai me kefaruwane bangane ba na shiga uku na






Next page



Your comment is needed






*Signed by ummu afan*πŸ’»
[15/07, 1:12 PM] SIS UMMY: πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€
🎑🎑🎑🎑🎑🎑
πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€
🎑🎑🎑🎑
πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€
🎑🎑
πŸŽ€

*BISSIMILLAHIR_RAHAMANIR_RAHIM*


*Ummu Afan the Gorgeous writer of the year ,Author of 'YAN BIYAU NE &AKWAI LOKACI*



🌟GORGEOUS WRITERS FORUM🌟


🌟 G.W.F🌟


*Home of gorgeous, intelligent and expert writers*


Dedicate this page to duk wani wanda page 41 to 45 yatabashi to nabashi kyautar wannan page keep it up keep smiling keep pushing don't ever think to ignore my novel saboda zai muku anfani zai nishadantar daku 😘😘😘😘😘😘😘😘😘😘😘



Gaskiya masoya Al'amin ba abinda zance akan wannan touching hearts page din sai godiya saboda yanuna tabbas ana tare so I choose page 41 to 45 to be my best page much love to this page 😘😘😘😘😘😘😘😘😘😘😘😘😘😘😘




πŸŽ€ *AL'AMIN DAGASH*



*PAGE* 4⃣6⃣to5⃣0⃣




Al'amin zaune a gidanshi dakusan two weeks kenan yana cikin ta kuma ba abinda yakeyi sai ibada kuma alhamdullila yana jin saukin zuciyarsa



Ya dauko wayarsa ya kunna
Kaman jira akeyi yaga kira yashigo yana dubawa yaga Vicky ce wani sabon tsanarta yaji tsaki yayi ya rejecting call


Sai kuma Ga kiran zayyad yana dagawa zayyad to mutumin tunda naga number din Nigeria nasan kasauka kenan

Dagash yace ai tunjiya nayi landing ina gidana na GRA


Zayyad yace ok ganin zuwa nima ina kusa da GRA din dagash yace ok saika karaso



Mummy zaune falonta suna waya da yayanta Alhaji imam yace next months zai shigo Nigeria tace to Allah yakawoka lafiya amma dan Allah ka kawantar da hanklinka yaya


Wallahi damuwarka yana affecting dinmu sosai ni anyama yaya ba aljanabace kuwa



Alhaji imam yayi murmushi yace Aisha kenan bazaki fahimta bane


Maryam yarinya ce sosai dan I was think ko Dana Al'amin ma yagirmeta


Kuma mutumce kaman ke mummy taja numfashi tace to Allah yasa adace yace amin Aisha kiringa sani a adduarki tace insha Allah yaya Kaine mutum nafarko a adduata
Sukayi sallama ta ajiye wayar cike da tausayin dan uwan nata






Zayyad yayi sallama a falon dagash
Yaganshi kwance kan doguwar kujera



Zayyad yace subhanalla Dagash kaga yadda karame kuwa


Murmushi yayi yace ai dole na rame zayyad ace mutum ba 'abincin kirki sai snacks ai dole



Zayyad yace dan iska ashema laifinkane wai kai yaushe zakadena wannan akidar kyamar taka


Abincin mutum biyu kawai kakeci a rayuwarka


To aidakasani sai kayi tafiyar da ita maryam din

Jin zayyad ya ambaci sunan maryam yasa gabanshi yafadi



Zayyad bailura da hakan ba yacigaba da maganarsa

Yace amma dai yakamata ka koma gida yau ko tunda kace tunjiya kana gidan nan


Dagash yace yanzu kuwa bara nayi wanka nafito mutafi







Dagash yayi parking a parking space na compound dinsa yafito cikin kasaita kamar yadda yasaba


Maikatan gidan suna ta gaisuwa yana daga musu hanu

Yana shiga falon tunda yaga baiga su suhaila a falonba toyasan basa nan


To ina maryam ya tambayi kanshi yatura kofar dakinta



Yaganta kan abin sallah tana ta tunani da alamu ta Dade a haka


Karasowa yayi yasa hanu yacire tagumin datayi frgit maryam ta zabura ganin dagash ne gabanta ya mugun faduwa


Gani take zaigane abinda yafaru da ita


Yace lafiyanki kuwa tayi murmushi tace lafiya kalau yaya kawai dai banji shigowarka bane shiyasa naji tsoro

amma yaya karame kasake haske lafiya kuwa

Murmushi dagash yayi yace nayi kanwata da abincinta Kinga kuwa ai dole na rame beside ma kema kinrame baby meyasameki kinyi rashin lafiyane
Maryam tace a nayi kuma anty shafa ta kuladani dagash yazaro ido yace shine baki fada minba baby

Wani hospital kukaje maryam tace bamuje asibiti magunguna ta karbo min yace no banyardaba zansake dubaki da kaina bayan nahuta banason musu

Me kika dafa ne kitemiki dan al'amajiri


Maryam murmushin dan almajirin dayace takeyi ta tuna rabonta da shiga kitchen ma ta manta shafa'atu tace me dafa musu abinda yasauwaka

Ta tafi school ne duna da lectures


Ta kalleshi tayi murmushi tace to kaje kahuta zan dafa maka Abu maisauki yanzu insha Allah


Yaja hancinta yauwa good girl yamata murmushi yafita daga dakin maryam ta bishi da kallo


Tashi tayi tashiga kitchen din tafara shirin girka mashi abinda zaici

Shafa'atu tayi sallama ganin Maryam bata daki saitayi nocking din toilet

Bata ciki sai tafito falo ganin kofar yayanta a bude yasa tashiga harsama ta haura tasameshi har yayi wanka yashirya cikin wata lallausar farin yadi half jamfa ya balain mishi kyau shafa'atu tayi sallama tagaida yayan nata yace a a shafa'atu kindawo tace a yaya


Yace ya lectures kina karatunko baki bari soyayya ya rinjayi karatunkibako ta sunkuyar kanta tace ina yi yaya


Shigowar maryam cikin doguwar hijabinta da tiren abinci yasa shafa'atu mamaki

Tace au dama ciwon duk na rashin ganin yayane


Kafin maryam tayi magana dagash yayi yace ai ba itakadai bane tayi missing din nima bakiganni ba kwana biyu babu nice food dinta


Shafa'atu tayi murmushi tace gaskiya kam karame sosai

amma itama maryam yaya harda rashin cin abincin

Ya kure maryam da ido sosai yace hakane baby bakyason cin abinci ko


Maryam cikin salon muryarta tace inacifa yace banyardaba

Zonan muci abinci tace yaya nakoshi yace banason musu


Ba yadda zatayi haka tadauki spoon tana ta jujjuya abinci batayi tsammani ba taga yakawo abinci bakinta


Shafa'atu ganin kaman ma sun manta da ita agun tace barinje na watsa ruwa

Tace maryam Allah yasa da wannan abinci ba yaya kadai kikawa ba maryam dai murmushi tayi abinta


Tace yaya zanci dakaina yace banyardaba haka yasauko kasa shima yana bata shima yana ci

Tundaga wannan ranar kulawa ta musaman take samu daga yayan nata


Abin yana mugun daga hankalin mummy sosai tarasa yadda zatayi






***
Bayan wata biyu maryam hankalinta ya Dan kwanta sakamakon kulawa datake samu wajen yayan nata



Duk yadda su Aymana da suhaila suka kaiga ganin sun takura wa maryam basu samu damaba





Maryam tana zaune a dakinta tana zaune kan resting chair fruit salad tayi takesha


Dagash yafado dakin murmushi suka sakarwa juna murmushi karasowa yadauki fruit salad din yafarasha


Yace kinsan meye ta girgiza kai alamun a a yace to daddy yakirani anty ta aihu 'Dana miji yau dasafe



Maryam cikin tsananin farinciki tace Alhamdullilah lalle ma anty shine bata fada minba cikin murna tafara kokarin kiran anty a waya



Hajiya zabbau bakarakaramin hauka taso tayiba jincewar anty ta haifi yaro namiji


Sosai tashiga bakincikin abin har yakaita ga takasa zama ta samu mummyn Aymana dazancen nan da nan kuwa tabata shawarar da zuwa gurin boka



Mummyn al'amin kuwa ba abinda yadameta ita damuwar daman akan uwarce karta jamusu tsiya saboda ance idan talaka ya rabi mekudi zai iya talaucewa


Takira daddy dakanta tamishi barka yaji dadi sosai Dan baiyi tsamanin hakan ba


Sai dai yayi yayi sugaisa da anty taki acewarta itafa ba abinda zai hadata da amaryar daddy


Kwanansu anty shida acan bayan ta haihu suka dawo Nigeria saboda so yake ayi suna sosai

Ranar suna daddy yawa yaro huduba da AL'AMIN wato dai yawa dagash takwara kenan saboda tsananin soyayyar dake tsakanin daddy da dagash yasa yawa dagash takwara


Sosai dagash yaji dadi dama gashi tunda yadaura idonshi kan yaro yaji yashiga ranshi
Yaron sosai suke kama da daddynsa komai nasu daya
Dagash yayi rawar gani sossai yasaki kudi wa takwararsa

Har ya mallakawa lil al'amin jirgi guda daya Wanda yake mallakin dagash yabashi kyauta sosai daddy yaji dadi sosai


Harda gida abin dai ya daddy dadi sosai yayin da mummy ma bata damu da kyautar da danta yayi ba saboda itama taji dadin yadda daddy ya karrama danta nata kwallidaya

Hajiya zabbau dai mutuwane kawai batayiba


Anty asiya kuwa yau take hanyar zuwa shiyasa aketa murnar zuwanta

Sosai dangin su daddy suka zo suka taya shi murna anci ansha sosai


Maryam kuwa taki rabuwa da jaririn

Antynta tayi kyau sosai tasake dawowa yarinya shakaf kowa yaganta bazaice tana da kaman maryam ba gaskiya daddy ya iya kiwo sosai


Maryam ta kalli anty tace anty na kinga yadda kika dawo kuwa ai bawanda zaiyarda cewar wannan uwatace sai dai ace yayata ce

Anty tayi murmushi tace kinci gidanku
Kebakiga inda kika komaba ko Maryam kinyi kyau sosai lalle a gaida wannan yayan naki

Lokacin da muka barki wajenshi hankalina baikawanta ba kwatata amma Dana ganki a yanzu na tabbatar da ya rike minke yadda yakamata Allah yasaka da alkairi



Shigowar anty asiya ne yasa Maryam shiru daga maganar datakeson yi

Anty asiya da murmushi ta karasa wajen anty tana murmushi tace koda bansani ba kece small mama dinmu ko anty tayi murmushi tace asiya ko


anty asiya tayi murmushi tace la ashe nima zakiganeni

Anty tace haba asiya ai tunda naji kince small mama nagane wacece duk da banganki a fuska ba ainasan muryar ki


Anty asiya tayi murmushi tace toyanzu dai ina kanwarmu Maryam ita nakeson gani


Anty tayi murmushi tace to ga Maryam a bayanki tana nane da jarari kamar bazata ajiyeba


Anty asiya suka hada ido da Maryam tayi saurin cewa anty sannu da zuwa


Anty asiya takasa magana ta kalli anty tace small mama yanzu kina da budurwa kaman Maryam what's a surprise


Anty batace komaiba Maryam tayi murmushi tace kema kema dai kya fada anty asiya saboda haka daga anty kinkoma yayata Dan nasan kona fada bazasu yadda ba



Anty asiya tace gaskiya kam ba mai yadda
Tace amma gaskiya Small mama Maryam ta dabance ai tafiki kyau ma sosai duk da kema din batayan baya bace wajen kyau


Anty tace ina zaki hadani da Maryam asiya baruwana duk sukayi dariya gaba dayansu


Anty asiya takarbi lil al'amin
Tace kai masha Allah gaskiya baby maikyau duk tunranda aka haifeshi naganshi ta watspp



Anty asiya tace anty saura kihaifo mana mace maikama da sis Maryam kyakykyawa

Anty tayi murmushi tace rufa asiri asiya wani haiuwa kuma wannan ma Allah yaraya

Anty asiya tayi murmushi tace ai insha Allah yanzu kifara
Nan dai sukayi ta hirarsu






Bayan sati uku Maryam na zaune a falon antynta tana kallo

Sai taga wayarta nakara tayi kaman bazata dauka ba
Sai kawai ta daga abinta aikuwa al'amin yazo gidan yace futo kisameni a falo


Yakashe wayar shi Maryam ta tadauki hijibinta tasaka tayi hanyar falon


Shikadai tasamu agurin nan tazauna yace wato kinbar gidana shine harni kinbari ko baby

Maryam tayi murmushi dayake sata takara kyau sosai

Tace bahabane yaya yace oya jeki kawo min lil al'amin kizo muyi hira

Ta tashi tana murmushi tana dawowa da lil al'amin dagash yakarbeshi yaji dadin ganin yaron Dan indai yazo gidan to yakan sa adauko mishi yaron

Duk da bawani iya rike jararai ya iya ba sosai


Maryam tayi ta mishi dariya


Mummy ce ta fito ganin dagash da Maryam bakinciki yakamata


Takaraso gurinsu tace son wai yaushe zakafara jin maganata agidan nan


Meyasa kullum kake Abu kaman karamin yaro ne

Bana hanaka mu'amala da wannan matsiyaciyar yarinyar bane jinin matsiyata mayu matsafa dabbobi Wanda ba abinda suka sani sai zuwa gidan boka da malamai


Duk abinda ake was Maryam agidan baitaba damunta ba sai wannan zagin mummyn nayau din Ashe kuwa duk a kunnen antynta


Dagash yace haba mummy why meyasa zakiyi haka for God sake wannan kalmomin naki sunyi yawa akansu



Kafin dagash yacigaba anty ta matso kusa dasu tasamu fuskar maryam cikin zafin rai ta zabbaga mata mari tace kukan mezakiyi maryam tunda muke a rayuwar mu babu inda aka taba cimanata mutunci irin wannan

Kinsan meyasa namareki sosanake kiji zafin aranki sannan kuma kisan maganar dazan fada miki kidauke da muhimmanci

Su hajiya zabbau ana jin hayaniya dukansu suka taru a falon
Dinjin wainar da aketoya wa sosai taji dadin cin mutuncin su maryam da mummy tayi anty asiya kuwa cikin bakin ciki takoma daki takira daddy a waya
Su naxeefa kuwa da afnan abin nema yasamu

Anty tacigaba da magana Maryam banyarda ko hanya yasake hadaku da Al'amin ba wallahi idan kikasake nasake ganinku tare sai tsine miki maryam


Cikin tsananin kuka maryam tadago ido haba wannan wani irin masifane antynta bata taba zaginta ba bare ta sa hanu ta taba lafiyar ta


Sai gashi yau har tana ikirarin tsine mata da gudu takarasa dakin su tabar falon


Anty ta kalli mummy tace hajiya mungode da cin mutuncin dakike mana nida yata acikin gidan nan amma inason kisani bazan baki amsaba saboda sanin darajar manya Dan koba komai ba maryam nima kin haifi Wanda yafini bare maryam
Dan haka Allah ya huci zuciyarka ta kalli dagash Tamika mishi hanu yabata danta yabata takuwa juya tayi cikin part dinta



Dagash ya kalli mummy yace mummy yaushe kika dawo haka nasan bakyason talakawa amma bata tunanin zaki iya cin mutuncin mutum har haka ba


Tace au yanzu duk abin dayafaru agabanka son baimaka ciwo ba abinda akamin


Mena maka haka ina soyayyar da kake nunamin son akan wadan nan matsiyatan mutanen
Yace haba mummy enough please


Daddy ne yashigo shida daddy king wato memartaba kenan dama suna tare asiya takira daddy tace mishi gida balafiya wai me ke faruwane
Haka mummy tace wai daga na yanke alakar dake tsakanin shi da wadan nan matsiyatar mutanen



Daddy ya mata wani mugun kallo yace suwaye matsiyatar tace akwai wasune ne bayan matarka da yarta


Ran daddy yayi dubu yabaci
Yace haka kikace tace to na nawakuma alhaji


Shikenan to ina mai tabbatar miki al'amin bashida mata sai matsiyaciyar dabakyaso kinga sai a Haifa maki matsiyatar jikoki kenan kinga daga nan sainaga nazagin matsiyata




Cikin da tashin hankali mummy tace wallahi alhaji baka isaba Dan kwalli daya kace zaka bashi wadan nan marasa asalin Wanda tunda suka zo gidan nan ba Wanda yabata zuwa Yace yau gashi Dan uwansune yazo

Karkamanta sunkai kusan shekaru hudu agidan nan saboda wallahi idan sama da kasa zata hade bazan yarda ba



Cikin dacin rai daddy yakalleta
Kafinta yayi magana maryam ta zo da gudu tarike kafan daddy tace daddy Dan Allah karkayi haka wallahi bazan auri yaya ba

Koba Dan komai ba kodan bamu da gata shi maigatane
Hakan baifaruba ma mummy batason mu bare kace haka daddy Dan Allah karkiyi min haka



Daddy yadagota Yace maryam tunda nake daku nataba banbantaki tsakaninki da yarana

Maryam ta girgiza kai yace ok to indai hakane ninake da iko da Ku acikin gidan dama duk wani Abu me numfashi saboda babu Wanda ya isa yasake saku kuka agidan nan kuma hukunci na Riga nayanke shi


Cikin meban tausayi tace daddy Kaduba Dan Allah koda ba Dan komai ba shima yayan baice yanasona ba taya za a mishi dole daddy abin zai min yawa kayi hakuri takarasa maganar Tana kuna kuka


Kaman daga sama dagash yace wayafada miki bana sonki maryam inason ki kuma nashirya auranki kaman yadda daddy yabukata


Abin yadaki zuciyar mummy dama su hajiya zabbau sun rikice shikenan gida zai koma na wadan nan matsiyatar


Hajiya zabbau tace gaskiya alhaji wannan ba adalcibane yaza a yi daga zuwan mata gida duk sun asirceka kaida danka

Kuma badama muyi magana wannan ma ai zalincine komai an mallaka musu ko uwarsa bai wa kyautar jirgi ba sai wannan yaron Dan matsiyaciya


Daddy yace ke kuma wayasa bakinki aciki shasha kawai wato nine matsiyacin tunda danane kince matsiyaci ko


Maganar anty ta fito daga part dinta daman duk abinda kefaruwa Tana jinsu

Tace kayi hakuri alhaji bazan taba bari maryam ta auri duk wani abunda yashafi hajiya ba saboda tadade tana cimana mutunci agidan nan

Kuma bazata hakuraba zatacigaba da ciwa maryam mutunci saboda tunfarko ta nuna bata kaunar mu Dan Allah kayi hakuri bazan iya ba



Daddy ya kalli anty yace maryam wato kinason nuna min in ban isa da maryam ba kenan da har zanzartar da hukunci kice be mikiba


Cikin kuka anty tace kayi hakuri alhaji Dan Allah banufina kenan ba duk duniya maryam bata da uba da yawuce ka
Kasamo mata koda megadin gidan nan akan kabata al'amin



Hajiya zabbau tayi shewa tace to mungaji da garafa sa bamuga kahoba

Wai idan yarinyar tana da uba kimaida ita gurin ubanta mana kodayake anshigo daula ai baza aso afitaba towa yasani ma ko yar gaba dafatiha ne




Batayi tsamaniba taji saukar mari a fuskarta daddy ne yazabga mata zai karamata daddy king yayi saurin rike hanunshi


Cikin zafin rai yace zauna yaya

Ya kalli hajiya zabbau yace ashe haka kike hajiya wallahi kunbani mamaki bantaba tunanin haka daga gareku ba


Kuma ina mai tabbatar muku nan da sati biyu zan daura auren al'amin da maryam

Bawanda ya isa ya hana sai Allah


Mummy al'amin cikin zafin rai ta wuce dakinta anty kuwa takasa tashi jin wannan tonan sililin da aka musu agaban jama'a akaci mutuncin su


Da kyar daddy da daddy king suka bata hakuri suka mata nasiha daddy dakanshi yaraka anty daki yadawo suka fita da daddy king



Dagash yakalli maryam da inbanda kuka ba abinda takeyi



Yace baby bazakiyi shiruba

Cikin kuka tace yaya meyasa kace kansona bayan nasan bahakabane kawai kafadane Dan kana cikin haushin abinda mummy tayimana



Dagash yace maryam waya fada miki bana sonki

Tunda nake bantaba jin son wata maceba sai akanki bansan soba sai akanki


Maryam bansan yadda zan lissafa miki yadda kike acikin rainaba




Inason ki ina kaunarki zan aureki zan baki gatan dabaki taba tunain samuba a rayuwa in fact maryam kece rayuwata I can't do without you




Maryam tadaga kai takalleshi shima yadaga mata gira







Next page




Your comment is needed fan





Much love to your nice comments







*Signed by ummu afan* πŸ’»
[15/07, 1:13 PM] SIS UMMY: πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€
🎑🎑🎑🎑🎑🎑
πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€
🎑🎑🎑🎑
πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€
🎑🎑
πŸŽ€

*BISSIMILLAHIR_RAHAMANIR_RAHIM*


*Ummu Afan the Gorgeous writer of the year ,Author of 'YAN BIYAU NE &AKWAI LOKACI*



🌟GORGEOUS WRITERS FORUM🌟


🌟 G.W.F🌟


*Home of gorgeous, intelligent and expert writers we are the best among the rest*



*Dedicated to gorgeous writers forum*







_🎑AL'AMIN DAGASH FANS GROUP_ 🎑

Ina matukar alfahari da comment dinku gaskiya sosai da sosai

Comment harda read more πŸ€”much love to your love and care




πŸŽ€ *AL'AMIN DAGASH*



*PAGE* 5⃣6⃣to 6⃣0⃣






Cikin tsananin tashin hankali dagash yazaunar da Alhaji imam dake kokarin faduwa



Dagash yace asiya kudauko to mutafi hospital acan zan fidubata dakyau


Cikin sauri yaga maryam wacce ke kwance cinyar shafa'atu jini nazuba mata


ai baisan sanda yaisa waje yaduketa cak yayi motaba


Anty asiya da doctor nabila su kama anty zuwa mota


Shafa'atu kuma ta je tadauki lil al'amin ta goyashi suka nufi hospital



Alhaji imam yatashi yayi hanyar waje duk da jirin dake dibansa

Dasauri alhaji sudais yakamashi yace haba imam kanutsu hankalinka yadawo jikinka kafin katashi



Alhaji imam yakalli alhaji sudais yace maryam ce fa itace fa akafita daita bata numfashi sannan kace nazauna annan nutsuwa tazomin ai bazaiyuwuba ma nitsuwata yana tare da maryam


Cikin rashin fahimta mummy ta karaso tace wai yaya mekefaruwa ne kasanar dani Dan Allah kasani a duhu

Kafin yabata amsa daddy king yace duk wannan maganar agida bazai mana ba kutashi mubisu hospital din kawai


Dakyar alhaji Dan asabe suka rike daddy yashiga mota


Mummy da hajiya zabbau da dai sauransu masu son jin gulma haka aka nufi dagash memorial hospital




Yanazuwa zuwa yakira zayyad a waya shiya duba anty a inda aka shigar da ita imagency shikuma dagash yasamu yaduba maryam



Mutane damkam a acikin tafkeken reception din hospital din dagash


Dagash ne yafito cikin sauri yayi hanyar waje megadi yakira yabashi watafarar takarda yace Dan Allah malam Abdul kaje ka karbo wadan nan magungunan please




Yanzu yanzu Dan Allah kayi sauri
Wanda dagash yakira da malam Abdul yayi saurin karba


Matashine shima Wanda bazai wuce dagash din a haifeba

Kawai dai saboda talauci da rashin wayewa yasa yake aikin gadi a hospital din dagash


Yaji mamakin ubangidan nasa sosai yau shizaiyi aika harda Dan Allah da rokonsa


Gaskiya wannan Mara lafiyar tana matukar

Please Login or Register in order to submit comment