Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yasa suka amince akancewa nan da shekara daya ai kaman yaune gurin ubangiji




Alhaji imam ya kudiri niyar komawa Nigeria yaje yayita bincike akan maryam ko Allah zaisa adace




***
Nigeria


Dagash ne zaune kan resting chair dinshi yana aiki a computarshi


Maryam tashigo cikin duguwar hijabinta tace sannu da aiki yaya yace yauwa batare da yakalletaba


Tace yaya Dan Allah inason zanje gidansu rahma Daga nan zamuje gidansu fareeda


Ya watsamata harara yace bazakijeba

Zatayi magana yadaga mata hanu ta tashi jiki bakwari tafito

Tana fitowa shafa'atu na sallama maryam taji dadin ganin shafa'atu sosai tace La anty ashe kina hanya


Shafa'atu tace kinyi mamaki ko Kinga jiya nabar nan yau kuma nadawoko


Maryam tayi murmushi tace a a anty nimurna ma nayi wallahi saboda naji dadin hirar mu najiya


Shafa'atu tayi murmushi ta harareta tace to yau zuwan banaki bane my hubby ne zaizo muhadu a nan


Yafi sakewa anan akan can gida


Bata karasa maganarba ta makale saboda dagash hango can bayan maryam ya folding hannayensa yana jinta


Maryam dabatasan meshafa tagani ba tayi murmushi tace wallahi anty na soyayyarku da yaya Faisal yana burgeni gaskiya kunyi dace da juna



Ganin shafa'atu takasa magana yasa maryam juyawa tankalli inda shafa'atu ke kallo itama ta tsorata sosai


Yace kuna kanananku daku kunsan soyayya ko ke shafa bakiji kunya ba kizauna da wannan yarinyar wai kina mata maganar saurayinko metasani


Kekanki mekikasani bare ita da secondary school dinma yanzu tagama





Maryam ta turo baki tana kunkuni
Shafa'atu dai batace komaiba Sai kayi hakuri yaya take fada


Yace ke baby biyoni yajuya yakoma falonshi


Shafa'atu kanta yadaure tarasa wacece babyn gani tayi maryam tana Dan dire direnta da kafa tana turo bakin tayi hanyar dakin yayan nata




Shafa'atu kusan suman tsaye tayi saboda ganin bakon lamari Dan ko a mafarki bazatayi tunanin yayan nasu yana da sauki hakaba

Wai baby to kodai daman haka sunanta yake

Tayi murmushi tace ikon Allah tana kan tunaninta taji anyi tafi da hanu firgit tafigita
Sai dai ganin me tafin yasata murmushi Faisal tagani

Yace matsoraciya harkin tsorata tayi murmushi ta ai dole ina gidan boss ne fa suka yi dariya gaba dayansu







Dagash kuwa yana zaune yana aikin gabanshi maryam hartagaji dazaman jiranshi

Sai daya gama komai kafin yajuyo yace wayo shafa'atu suna burgeki ko

Maryam ta turo baki tace nifa bance ba

Yace mekikace tace bakomai yace nayi karya kenan ko tace nidai bance kayi karya ba



Yace wato bakyason cigaba da karatu ko kinfison soyayya ko ana hure miki kunne



Maryam tace kodaya ni insha Allah saina cika burina nazama abinda nakeso nazama a rayuwa kafin nayi aure



Ya kalleta da mamaki yace aure wai ke harkinsan Kalmar aure baby

Maryam tace bansaniba amma dai hakan nacewa yaya jabeer yayi hakuri bazan iya auransaba har sai gama karatu


Kuma yanzu yace zaijirani dagash yayi saurin Daga mata yace enough baby

Oya get out of my room stupid girl

Maryam ta kalleshi ta rau rau da ido aikuwa tafashe da kuka abinta




Mamakin kukan nata yakeyi yace lafiya kike min kuka


Cikin murya me sanyi da shagwaba tace bakaibane ka tsoratani


Dagash yace God help me yadafe kai

Yatashi ya haura samanshi itakuwa maryam nan tacigaba da kukanta



Zuwa yayi wanka yafada yafito cikin kananun kayansa


Ya ganta tana gun daya barta yace baby haryanzu oya jeki dauko mayafi kizo kirakani



Maryam tayi mugun mamaki Dan baitaba Neman rakiyarta ba sai yau amma sai boye mamakinta

Tatashi batare da ta kalleshiba tayi dakinta wanka tashiga tafito ta zura doguwar Riga abinta ta haugado Dan bacci tariga tasaba da baccin rana



Dagash kuwa yayi tajira kozata fito amma shiru kakeji wai malam yaci shirwa


Shigowar Faisal da shafa'atu ne yadawo da shi daga tunaninshi

Ya kalli shafa yace ke kiramin yarinyar nan



Shafa'atu tayi kofar maryam tashiga da sallama taga tana ta risgar baccinta takure AC din dakin


Shafa'atu murmushi tayi tace kai wannan yarinyar akwai kyau ita bacci ma kyau yake mata

Fita tayi abinta tace yaya bacci take

Cikin mamaki yace bacci fa kikace tace a bacci


Yace jeki taso ta batayi musuba takoma

Faisal yakalli dagash yace babban yaya yakamn kana bawa matana wahala ne haba Dan Allah kabarta haka ai zaryar tayi yawa


Dagash ya watsa mai harara yace Dan iska ka wani nanikewa yarinya karama kazama kaman soko




Faisal yayi murmushi yashafa gemunsa yace ai nadade dazama sokonta tuntuni



Kaga kuwa kobakomai dole ta kalleta a matsayin abokin mijin ta kaikuma ka kalleta a matsayin matar abokinka


Bawani batun wada kanwa sai anzo gida


Takaici Yakama dagash ya dauki trowing pillow ya wullawa Faisal


Faisal kuwa yasan yagama kular da dagash cikin tsanin dariya yakasa magana yazauna kawai yanacigaba da dariyarsa




Itakuwa shafa'atu suna drama da maryam ne maryam tace alamfur kanta naciwo shafa tayi murmushi tace kitashi muje kifada naga kedin tadabance a gurinshi zaijiki



Maryam tazaro ido tace wa ni caf Dan bakiga tsawar dazu yadaka minbane



Nan dai shafa'atu ta rarasheta suka


Maryam dake rataye dankwalin dohuwar rigar dake jikin ta


Tazauna kasan carpet tace yaya Faisal ina wuni suka gaisa

Maryam ta kalli dagash tace gani yaya baikulataba yacigaba da danna wayarsa



Sai dayaga dama kafin yace menace kiyi tace kayi hakuri namanta


Yace ok tashi kije kishare compound din gidan kaf a Garden area kije duk kigoge kujeru da komai nagurin


Maryam tace to ta tashi tayi hanyar waje yabita da kallo cike da mamaki shifa jira yake tabashi hakuri
amma saiyaga ta nufi aikin dayasata


Hada ido sukayi Faisal yaga alamun dariya yakesonyi


Cikin haushi yace Faisal dauki budurwarka or what ever kubar min gida

Inkuma kaki zakasamu kafarta akarye


Faisal yarike kunne yace afuwan muntafi karka illata min mata Dan tafi matanka kyau


Shafa'atu dama tana waje can gurin maryam yace Honey zo inkaiki gida kinji

Inkika biye maryam da dagash zaki kwana dukansu taurin Kaine dasu

Duk yadda zakice tabada hakuri bazata bayarba yakarasa maganar yana dariya



Shafa'atu tace kuma wallahi hakuri kawai zatabashi zai barta


Maryam tayi murmushi tace wai Dan badama yaya yasa kanwarsa aiki saikuyita tunanin lafinayi

Kodaya ba abinda nayi kawai dai yayi niyyar sani aiki ne
Takarasa maganar tana murmushi


Faisal yace wa shafa'atu kinko honey


Shafa'atu tace naji aidaman nasan halin kayana

Maryam dai murmushi tayi abinta tacigaba da abinda akasata




Dagash ne daga can samanshi yana kallon maryam a wahale take aikin


Cikin takaici dagash ya zago saijitayi kawai an damki kunnenta

Cikin shagwaba tace yaya zafi wallahi mena maka kayi hakuri bazan sakeba


Yana janta yace ok saikinga za a taba lafiyar jikinki zakibada hakuri ko

Tace kayi hakuri bazan sakeba
Har cikin dakinta yakaita yace change your slipas


Ta turo baki tadauki plashoe tasaka yasake kama kunnenta har mota da kanshi yabude motar yasata ya kullo



Ba maryam ba harta security dinsa na gidan sun jinjina al'amarin nan

Saboda duk yadda kuke tunanin dagash yawuce nan akan zafin kai dajinkai
Saigashi yau dakanshi yabude wa mace kofa


Sundade suna mamaki



Shikuwa dagash ba abinda yadameshi da kowa abinda yagadama yakeyi


Maryam kuwa ta rike kunnanta tace wallahi rikonka dazafi


Ya harareta yace oya tied your head tace a a yaya aidan kwalin karamine kabarni na dauko babba


Yace roll it as I said dasauri maryam tayi Rollin Dan karamin dankwalin doguwar rigar a akanta


Itafa wannan kayan manyan mayafai take samusu saboda yadda suke bin jikinta


Ita daya barta ma kawai tayafa akan zaifi mata amma wannan rolling ita duk surar jikin a waje

Ta turo baki yana tafiya haka kawai yake jin nishadi

Sai daya farazuwa dagash shopping complex

Yashiga batare da yace tafito ba yana shiga kuwa ma'aikatan sukayi ta kawo gaisuwa sai dai daga hanu kawai yake musu





Yabada umarnin a kawo ice cream masu kyau yadan na wayarsa sakamon ganin sunan sweet mom dayagani



Yace mummy wai yaushe zaki dawo nayi missing dinki

Mummy tayi murmushi daga bangarenta tace to sarkin korafi gani air Port dinka nayi landing


Cikin murna yace waw dagaske tace kaci danku karya zanma


Cikin dariya yace am sorry mom gani nan zuwa karshiga kowani mota


Mummy tace na nawa kuma sunbada mota akaini gida

Dagash yace ok ganinan zuwa gidan


Yakashe suka kawo mishi ice cream din suka wuce dashi mota


Ya bisu a baya nan suka bude mai yashiga ya tada motar

Yadauko ice cream din dasuka saka a kurar baya ya ajiye kan cinyar maryam


Tabude farinciki yaka mata Dan tana matukar son vanilla ice cream irin Wanda yaya jabeer yake kawo musu school ne kullum sai yakai musu


Cikin murna tace yaya nagode sosai batare da takalleshiba tabude abinta tafara sha



Ganin bagidanshi suka nufa yasa takalleshi tace yaya ina kuma zamu baikulataba


Sai gani tayi sunyi hanyar gidan daddy

Suna isa masu get man yabude musu kofa


Dai dai lokacin mummy mata fito daga motar da aka wota


Dagash yafito da sauri ya rungume mummyn shi saboda sunyi missing din juna


Tace kai Son anya kuwa kayi missing mom dinka kuwa


Yace meyasa kika ce haka mom tace yadda kayi kyau kayi fresh mana


Murmushi kawai dagash yayi


Maryam dake ganin uwa da danta tafito daga motar ta durkusa harkasa tace sannu da dawowa mummy


Mummy cikin mamaki ta kalli dagash shima yakalleta




Tsaki taja tayi hanyar cikin gida dagash yayi bayanta


Maryam cikin mota takoma abinta





Next page





Your comment is needed
Fans



More comment more typing




Voted & share




*Signed by ummu afan*πŸ’»
[15/07, 1:09 PM] SIS UMMY: πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€
🎑🎑🎑🎑🎑🎑
πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€
🎑🎑🎑🎑
πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€
🎑🎑
πŸŽ€

*BISSIMILLAHIR_RAHAMANIR_RAHIM*


*Ummu Afan the Gorgeous writer of the year ,Author of 'YAN BIYAU NE &AKWAI LOKACI*



🌟GORGEOUS WRITERS FORUM🌟


🌟 G.W.F🌟


*Home of gorgeous, intelligent and expert writers we are the best among the rest*



I DEDICATE THIS PAGE TO ummu afan fans group Allah yabar zumunci ina jin dadin comment dinku over wallahi Allah yabar zumunci ❀❀❀❀❀❀❀❀❀






_🎑AL'AMIN DAGASH FANS GROUP_ 4🎑

Ina matukar alfahari da comment dinku gaskiya sosai da sosai

Comment harda read more πŸ€”much love to your love and care




πŸŽ€ *AL'AMIN DAGASH*



*PAGE* 3⃣6⃣to4⃣0⃣






Al'amin yabi mummy har part dinta yace meyafaru ne mom


Mummy ta mishi kallon banza tace son Ashe dagaske ne abinda ake fada min akanka

Yadda suka gama da mahaifinka kaima sukeson gamamin dakai


Dagash yace am sorry mom ban fahimci mekike nufiba


Nan mummy tace me yarinyar takeyi a motarka

Dagash ya dafa kai yace God help me
Haba mom kidaina bin maganganun ummy fa


Yarinyar nan amana dad yabani kuma am very sure ina riketa kamar yadda yace


Kuma kema ina son kirage tsanarsu a ranki saboda rayuwa



Cike da mamaki mom take kallon dagash tace son yau Kaine da min wa'azi
Tadaga hanu tace Allah nagode maka da kanuna min wannan rana

Ta dafa shi tace nabari son amma ina kamin alkawari ba abinda zaishiga tsakaninnka da wannan yar matsiyatar


Dagash yace haba mummy bazaki daina bako tace am sorry son

Da wannan yarinyar amaryar dad dinka


Murmushi yayi ya kamo hanun mummy suka zauna kan bed yace haba mummy keda kanki zakibada shaidar danki kananun yara basa gabana


Kuma namiki alkawarin da zaran dad yadawo zan dawo da ita nan


Ina bata kulawa ne saboda my dad requested

Mummy tayi murmushi hankalinta ya kwanta da jin maganganun son din nata


Tace shikenan my son nayarda dakai
Dagash yace that's my mom


Yace to yanzu dai me wannan tsohuwar tabayar akawo min


Mum tayi murmushi tace sai kakirata katambayeta kunfi kusa

Dagash yace kedai mum kifadi gaskiya idan bata bada komai akawo min yanzu namata saki talatin tawaya

Mummy tayi murmushi tace a a to maida wukar ai sako sosai ma tabayar abaka
Yace Allah yasota

Dagash yace mummy ya my dad imam

Mummy tace yana nan ai yace kuna gaisawa
Yaya nurane baka kiransa sosai


Dagash yace ai shidinne number dinsa baicika shiga


Nan sukayi ta hira da Mum

Sai kusan karfe shida saura yafarga da yar mutane a mota

aikuwa yawa mom sallama

aikuwa abin yaba mom mamaki sosai da baisa mata rigimar abinci ba

Tace to Allah yasa dai bawani abinsuka sakawa danta a abincinsu ba inbaka ba ai abindubawane ace tun tasowarshi baitaba cin abincin kowaba sai nata

Tashi daya ace yafara cin na yarinya karama abin yabani mamaki sosai

Mummy kenan maganar zuciya take tayi itakadai





Dagash yaga maryam bata mota harzai koma ciki yadubota sai ya hangota gurin sweeming pool tasaka kafarta a ruwa tana waya abinta



Cike da mamaki ya laluba wayarsa yaga baya taredashi ya tabbatar wayarsace

Tsayawa yayi yakasa kunne yaji dawa take wayar

Sai yafahimci da maman take wayar

Sai data gama ta ankara da mutum agun Ashe


Yace tashi mutafi gida batayi musu ba tabishi suka dau hanya


Nazeefa dake tsaye daga inda take tace to kodai soyayya suke da yaya sai kuma wata zuciyar tace kai mezaiyi da wannan karamar yarinyar

Tsaki taja takoma ciki abinta





***
Yau jumma'atu babbar rana Wanda yayi sati daya da dawowar mummy


Shafa'atu da maryam zaune a falon tare da matan gidan kowacce tana abinda ke gabanta


Shafa'atu da maryam dai kallon sukeyi abinsu kowacce tayi kyau kamar asaceta
Tsabanin matan gidan da kullum cikin English wear suke su aganin su hakan yana faranta ran dagash tunda shima baya mu'amala da manyan kaya




Maryam kuwa sanye take cikin atampa super Holland Riga da skirt Wanda yayi kaman angwada ta cas ajikinta komai ya zauna mata tayi dauri mai kyau abinta

Shafa'atu kuma tana sanye ne da Arabian dress sunmata kyau sosai

Kowa yayi nisa kan abin dayakeyi


Dagash ne yafito cikin shirinsa na kanun kaya as usual dai

Tunda ya doro ido kan maryam yaga tabalain tafiya dashi kai wannan yarinyar duk kayan data saka saisun mata kyau kamar wata aljana


Ya dade a tsaye basu saniba suhaila ce ta Ankara dashi taga maryam ya kura wa ido kishi yakamata
Gashi badama tayi magana


Shafa'atu tace sannu da fitowa yaya maryam ma tajuya danufin tagaisheshi taganshi yayi cikin shigarshi dayasaba


Ta turo baki ta kalleshi tace haba yayana yaufa Friday ne
Yatsare ta da ido Dan bai fahimci abinda take nufiba


Tace Dan Allah kacanja kayan nan kasa manya shafa'atu cikin tsananin tsoro tadinga tabo maryam akan tayi shiru kar tajawa kan ta



Maryam ta lura da abinda shafa'atu take nufi hakan baisa tayi shiruba saida ta dire a point dinta



Dagash murmushi yasake yace baby wadan nan basa min kyaune maryam tace kodaya ai nasan danka lura suna maka kyaune yasa kakason sasu


Murmushi yayi Dan kadan Wanda yabawa dimple dinshi daman lotsawa

Yace oya tashi kije kizabo min Wanda kikeso nasa

Maryam ta tashi da murna tawuce part dinshi


Ba su suhaila ba hatta shafa'atu saidatayi suman zaune saboda tsananin mamakin wannan al'amari ko a amafarki bata taba tunanin yayanta zaibi ra'ayin daba nashiba

Saboda ba yadda daddy da mummy basuyiba akan yadinga saka manyan kaya yaki sai ranar sallah shima yana dawowa daga masallaci zaicire ya ajiye shikenan




Aymana tafashe da kuka ta tashi tadauki key din motarta tayi hanyar gidansu


Suhaila kuwa takaici bakin ciki ba abinda bai hadu yamata yawaba



Dagash kuwa tunda maryam tawuce dauko mai kayan dazaicanza yake waya baibi takansu ba balle yasan halin da suke ciki


Maryam kuwa tafito dawata haddadiyar shadda harda babbar rigarta da hula da alamu dai ma baitaba sawa ba



Ya kalleta ya kalli kayan yace baby wannan ai kin hadani da wahala
Maryam ta zumburo baki tace gaskiya suzaka saka yaya



Murmushi yayi yakarba yakoma ciki

Maryam kuwa tadawo tazauna a inda ta tashi shafa'atu ta tsareta da ido

Maryam tace kai anty shafa'atu wannan kallon haka saikace kinsamu yaya Faisal


Shafa'atu tayi murmushi tace ai al'amarin naku ne keda yaya abin al'ajabi

Maryam bayasa Mayan kayafa sai ranar sallah amma kiga abin mamaki wallahi yau inbishi inga yadda su mummy dama mutanansa zasu dauki al'amarin


Maryam batace komaiba tayi murmushi tace anty kenan



Dagash ne yafito cikin kayansa da maryam tabashi


Kai masha Dan gaskiya Al'amin dagash dayasan irin kyau da tsari da manyan kayan nan suka mishi dayacigaba sasu


Maryam tace kai yaya na wallahi kafito wallahi Dan da daurin aure zaka ba Wanda zaikalli angon kaizaka koma abin kallo

Tace saura hular yasaka akansa saboda baisaba ba bai iya saka hularbama


Maryam tace yayana barin gyara maka

Shafa'atu tayi saurin daukar wayarta tabude camera

Dai dai lokacin da dagash yadan sunkuyo saboda maryam tsamu saukin samasa shafa'atu tadauka kai baramin kyau yayi ba hoton saikace irin free wedding pictures din nan


Sai kuma lokacin data saka din yayi murmushi yana kallon itakuma irin tana so tayi dariyar nan bata so hada ido

Tarike rike hancinta tana dariya a hankali

Kai gaskiya hotunan bakarya sunyi kyau sosai

Guda biyu kawai tasamu damar dauka tayi sauri maida kanta TV gudun karyaganta


Suhaila ta tashi itama tazari mayafi tayi gidansu
Kai kara



Dagash yatafi masallaci abinshi



Yana fita shafa'atu ta tashi ta dafa kafadun maryam tace maryam Dan Allah kifada min gaskiya


Kuna soyayya da yaya na ko
Maryam jitayi maganar yamata girma ina ita ina wannan basarake mutumin dahar zatayi tunanin soyayya suke




Maryam ta kalli shafa'atu tace anty mekikqa gani yasa kika fadi haka

Nan shafa'atu ta mata bayani
Maryam tace anty shafa'atu wallahi babu soyayya tsakanin Nina da yaya

Yaya yana daukana ne kamar yadda yake daukarku

Kuma batun saboda da kike magana zaiya yuwuwa zama dana yi agidan nan ne



Shafa'atu tayi murmushi ganin yadda maryam duk tabi ta rude
Tace shikenan maryam intayi wari maji

Amma fa ko ahaka kuka tsaya kin yaki wadan nan matan nasa masu siffar mazan shashai


Maryam batace komai ba sai yanzu talura da basa falon

Tace ina su antyn suke shafa'atu tayi murmushi tace duk sunyi waje cikin fushi

Maryam tace nashiga uku
Wallahi bada wata niyar nasa yaya yacanja kaya ba Allah yasa badan haka sukaji haushiba



Shafa'atu tayi murmushi tace kai amma kema akwai yarinta sosai maryam agunki

Inbahaka ba aikema kinajin maganar nan kinsan saboda abinda kika wanda suyakamata suyi amma basu da tunanin hakan aini kina mugun burgeni shiyasa kikaga na nace miki ina koyan wasu kyawawan halayenkine maryam



Maryam dai bataji dadin abinba



***

Daddy yakira wayar dagash alokacin yana motane zuwa gida daga airport


Dagash cikin murna yace dad yanaga number Nigeria
Dad yayi murmushi yace ai ina mota ma zuwa gida nacewa mummynka kartafada maka surprise dinne


Kaga yanzu masallaci zanwuce tunda lokacin juma'a yayi saikazo


Dagash yaji dadin dawowar daddy sai dai yana adduar Allah yasa kar dadddy yace maryam takoma gida


Tunda mamanta tadawo haka kawai yaji yadamu


Ana idar da sallah dadddy ya wuce gidansa yasamu an yi komai Dan tarbarshi


Mummy tasha kwalliya da lapaya saikace wata balarabiya tayi kyau sosai


Hajiya zabbau ma ba laifi tayi kyau da ita saidai batakama kafar uwargida sarautar mata ba mummy



an zazzauna sai dai abinda bai wa daddy dadiba shine ba Wanda yatambayi matarshi lalle ba karamin tsana sukawa maryam ba



Daddy yadauki waya yakira dagash yace kataho min da 'yata naganta


Yakashe wayar su afnan da nazeefa duk suma suna zaune kan dining din ana shirin cin abincin gaba daya


Shafa'atu tashigo dawowarta kenan daga gidan Dagash tace la sannu da zuwa daddy ya amsa yauwa shafa'atu tace dady ina anty kobatare kukazoba

Daddy yaji dadin tambayar shafa'atu yace tana can nima nazo nadubakune na koma yar albarka


Shafa'atu tace Allah sarki antyna barinzo nakirata mugaisa


Sallmar dagash yasa kowa yamaida hankalinsa kanshi


Tabbas dai dagash ne a fuska amma banda jikin

Daddy da mummy suka kalli juna cikin tsananin mamakin son yau shine da manyan kaya



Dagash murmushi yayi yaja kujerar gefen daddy da mummy
Yazauna shafa'atu dai ta kunshe dariya daman za arina wai ansaci zanin mahaukaciya



Shigowar maryam ne cikin falon yasa itama suka maida kallonsu kanta


Haka kawai daddy yaga dacewar Dagash da maryam shiyasa yayi wani murmushin manya


Dagash yace duk kunsamin ido kufadi abinda yake cikinku mana kafin dad yayi magana


Maryam tadurkusa harkasa tanagaida daddy tare da tambayar mamanta

Daddy yayi yayi maryam tazauna kan dining taci abinci taredasu taki


Shafa'atu ta sauko kasa suka zauna kan carpet



Dad yace wai mekefaruwane son you are totally change
Tell me the secret my Son


Mummy tace ai yanzu al'amarin son abin tsorone

Hajiya zabbau tasaka tsalam tace to ai dole yacanza tunda anbashi abinda akabawa mahaifinsa


Dad zaiyi magana Dagash yarufe mishi baki

Dagash yace daddy aini aganina ba abin mamakibane tunda watanku biyu saudiya kaida mummyna kuna min addua

Kunga Dan kundawo kunga canji ai baikamata kuyi mamakiba


Daddy yace hakane son nafi kowa murnar kasancewarka a haka my son


Dagash yayi murmushi sukayi ido biyu da maryam yasakar mata murmushi ta sunkuyar dakanta kasa




***
Aymana da mummynta zaune gaban kasurgumin boka

Suna fada mishi matsalar su yakece da dariya yace mekukeso a muku akanshi



Mummyn Aymana tace somuke yazama sai abinda tace dashi zaiyi ta mallakeshi kawai tako ta ina ko iyayensa karyaji maganarsu sai namu boka yakece dariya yace angama



Zanbaki magani kije kiyi wanka dashi kitabbatar ya kusance ki bayan kinyi wanka da wannan maganin duk yadda zakiyi kiyi ya kusanceki bayan kinyi wankan idan bahakaba akwai matsala



Nan sukabada kudi sukayi godiya suka dawo gida



Dagash kuwa dayamma yasamu wani kiran gaggawa daga America suna da meeting



Ya kalli daddy yamishi bayani daddy yace sai katashi kaje kashirya bara nasa amaka booking kona night flight ne ko Dagash yace ok to dad dama suna lambun gidan ne shida dad dinsa








Next page



Your comment is needed fans




Ina alfahari daku over wallahi





Vote & share




*Signed by ummu afan* πŸ’»
[15/07, 1:09 PM] SIS UMMY: πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€
🎑🎑🎑🎑🎑🎑
πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€
🎑🎑🎑🎑
πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€
🎑🎑
πŸŽ€

*BISSIMILLAHIR_RAHAMANIR_RAHIM*


*Ummu Afan the Gorgeous writer of the year ,Author of 'YAN BIYAU NE &AKWAI LOKACI*



🌟GORGEOUS WRITERS FORUM🌟


🌟 G.W.F🌟


*Home of gorgeous, intelligent and expert writers we are the best among the rest*



I DEDICATE THIS PAGE TO YOU SIS SIS DUMMY'S GASKIYA INA ALFAHARI DAKE OVER SIS ALLAH YABAR ZUMUNCI INAJIN DADIN YADDA KIKE YI A GROUP DINKI KEEP IT UP ❀






_🎑AL'AMIN DAGASH FANS GROUP_ 🎑

Ina matukar alfahari da comment dinku gaskiya sosai da sosai

Comment harda read more πŸ€”much love to your love and care




πŸŽ€ *AL'AMIN DAGASH*



*PAGE* 4⃣1⃣to4⃣5⃣







DAGASH na isa gida yakira maryam yace tahada mai kaya kala biyar


Tace yaya tafiya zakayi yace a tace yau yadaga mata kai kawai yazauna yana dannawa


Maryam ta zazzaba mishi kayan tsab tagama komai



Yace yauwa good girl tayi murmushi tace to Allah ya kiyaye hanya yace amin nagode baby


Sai can kuma kaman me aljanu ya danki kunnanta yace karkifita koina



Cikin shagwaba tace wash yaya dazafi yace ai daman zafin nakeson ya miki saboda kar kisaba maganata



Yasaketa bayan yagama mata warning
Har gurin mota tarakashi

Sai alokacin yatuna da mutanen gidan yadauki wayarsa rana tafarko kenan daya taba kiransu


Nan da nan ya shaida musu zaiyi tafiya na sati

Zasuji alert ta accounts dinsu





Aymana da suhaila suka dawo gida

Itadai suhaila basu je Ga bokaba

Sai munafurci da aka koya mata yadda zatayi ta kori maryam agidan




Kwanan dagash uku datafiya
Maryam nadakinta bayan tagama komai ta kwanta abinta




Dagash yayi diran bazata karfe Tara nadare yadawo
Suhaila daman tana gida tace yau can zata kwana

Aymana ce kawai tayi murnar dawowarsa ganin zata samu daman aiwatar da aikinta


Nan tawage bakin tana mishi sannu da dazuwa bai ki amsawaba ganin Dan sakin fuska sai taji dadi cikin yanga tabishi zuwa part dinsa tana yanga



Yana shiga bedroom din shi yafada wanka
Aymana tayi saurin dauko swan water a fridge tabude ta wurga desire tablets wato maganin kara karfin sha'awa sosai


Wanda idan har mutum yasha maganin tofa idan baisamu maceba

Akwai matsala dan sai yayi karamin hauka sosai maganin yanada karfi




Dan tasan halin wulakancinsa sai yajuya mata baya yayi baccinsa shiyasa tayi maganinsa da wannan maganin



Dagash nafitowa aymana tace sannu

Please Login or Register in order to submit comment