Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mutum ba tashikibani guri nan da wata zan daura miki aure da mutum daya acikin mane manki


Aikuwa cikin tashin hankali natashi nayi dakinmu inazuwa nafada jikin innarmu

Tace ya akayi maryama nace innan mu nashiga ukuna wallahi Abba zai aura min Wanda banaso



Inna tace kiyi shiru maryama insha allahu aliyu zaki aura

Yau idan yazo kice ina nemansa nace to innan mu Dan ina yadda damaganar innanar mu Dan tana sadaukar da farincikinta saboda yaranta




Aliyu yazo kiran innan mu
Bayan sungaisa tace mishi aliyu idan dagaske kake yakamata katuro magabatanka gashi mahaifinta har yafara shirin bada ita gawani


Aliyu cikin tashin hankali yace inna Dan Allah kar amin haka wallahi idan na rasa maryam zan iya rasa raina


Inna tace bazaka rasata ba aliyu kawai katuro magaba tanka asan abinyi







Haka kuwa duk abin abbana burinshi na aurar dani baicikaba saboda magabantan aliyu sunzo
An tsaida magana nan da wata biyu za ayi bikin mu da aliyu


Hakan yasa aliyu tafiya Neman kudi kafin lokacin yazo



Munyi bikin kawata deeje yarage saura nikadai shiyasa ma nadaina zuwa ko ina





Wata ranar alhamis ranar da bazan taba mantawa dashiba a rayuwata takarasa maganar tanakuka



Dad ya miko mata robar ruwan swan water batayi musuba tasan tana bukatar ruwan kam


Bayan tasha ruwan tacigaba da basu labarinta





Ina cikin tafiya kan hanyar zuwa islamiyyata naga wata bakar mota sun tsaya agabana naga sunbude kofar motar sunfito


Duk fiskarsu a rufe yake


Suka nuna min bindiga sukace wuce muje ganin bindiga nayita basu hakuri sukaki karshe kawai ma sai suka fesa min wani Abu


Bude ido kawai nayi naganni a wani hadaddan gida mai kyau sosai da haduwa



Kuka nakarka dashi hankalina yatashi can sai naga anbude kofar anshigo

Wani alhaji nagani fari mai mutunci dashi a fuska




Yafi zubin larabawa haka dashi


Yayi dariya yace barka da tashi yake kyakykyawar yarinya


Nace Dan Allah alhaji kaiyi hakuri kafitar dani daga gidan nan

Wasu ne suka satone daga kauyenmu



Wani dariya naga alhaji yayi yace ke yarinya dena hadani da Allah kicuceni Dan kozaki kukan jini ba kyaleki zanyiba



Tabas ninasa akawo minke gidan nan saboda tun ranar danaganki nakwadaitu da surar da Allah yamiki da kyan hallitarki duk da acikin hijabi naganki
Hakan bai hanani ganin wasu sirrika atare dake ba




Na nunawa yarana ke sukaganki shine yau nace akawo minke na huta dake saboda bani da niyyar aure a yanzu Dan da inada niyyar aure zan aureki kodan kyau da Allah ya miki




Cikin tashin hankali nace Dan Allah alhaji kar keta min haddi
Wallahi niba yar iskabace alhaji aurena ya kusa alhaji


Kabarni naje da mutuncina gidan mijina karka bata abinda nayi shekeru ina tattalinsa alhaji karufa min asiri Dan Allah



Alhaji yace wayafada miki nima ba auranki zanyiba

Ai bazan yadda na hada shimfida dakeba sai an daura min aure dake saboda kikwantar da hankalinki auren sunna zakiyi


Sannan kuma kiraya sunna da ni mijinki


Aikuwa nasake shiga tashin hankali sosai yace yanzu dare yayi amma zuwa gobe karfe tara za a daura min aure dake a masallacin anguwar nan



Zanbaki sadakin ki gobe yasa aka kawo min abinci da ruwan sha nisaboda tashin hankali ko yunwar ma da kishin ruwan bana ji
Yadda naga rana haka naga dare saboda tashin hankali ba abinda nakeyi sai salloli da addua




Dasafe karfe Takwas alhaji yashigo yace 'yanmata sunanki saboda liman ne yake zai miki wakilci


Ban dago ba bare naga fuskarshi saboda babu mutumninda natsana a duniya sama da wannan alhajin



Alhaji yayi magana yaji shiru yace toshikenan daman bana son kusantarki batare da aure. Bane tunda kinfi son hakan shikenan bari kiga aiki da gamawa yafara cire kayansa




Cikin tsananin kuka da tashin hankali nace sunana maryam


Yayi murmushin mugunta ya ce Ashe kina da wayo yarinya


Bayan daura auren Alhaji da maryam yadawo cikin gidan yabata sadakinta dubu ashirin


Bata karba ajiye mata yayi yace hakkin kine fa idan baki karba kinyi wa kanki



Har video din daurin auran yakawo mata dan ta tabbatar da andaura


Sati na daya agidan Alhaji a matsayin matarsa


Abinci inacinsa ne kawai Dan yunwa karya kasheni

Amma bawai Dan tana jin dadin komaiba


Ina zaune a falon gidan Dan Alhaji kullewa yake idan zaifita

Sai naga yadawo da wuri yabani takarda yace nasake ki saki daya


Tunda nazo gidan banyi dariyaba sai daya bani takardar sakina

Yace zan koma kasan mu saboda amin waya mama na bata da lafiya


Ina so kisa a ranki baki taba sanina ba a rayuwarki

Saboda bazaki sake ganinaba maryam


Nayi murmushi nace Alhaji nima bana fatan na sake haduwa da mutum kamarka a rayuwata

Nisakin da kamin ma yafi komai dadi a rayuwata

Sai dai kacuceni Allah ya isa bazan taba yafe maka ba Allah ya isa


Murmishi yayi yace wannan damuwarkice kinji nabaki hakuri ne to bana bukatar hakurinki



All what I know dai banyi zaman zina dakeba auranki nayi



Dakin na koma namaida kayana da yasato nidashi harda hijabin da da jakar makarnta nawa tunda nazo nafito yace yauwa ai sai an maidake tace bana bukatar sumaidani


Kafada min kawai nan inane

Alhaji yayi murmushi yace ai abinda bazaki sani ba kenan Dan haka ma ko compound din gidan nan bazakiganiba yadda kikazo hakazi koma


Banyi aune aune ba naji sunfesa min wani Abu aikuwa

Sai bude ido nayi naganni a dakin innata sunata min fiffita ancika akaina


Yaya aliya tace inna ta bude ido sunyi murnan farkawata


Ruwan zafi inna tasa aka hada min nayi wanka suka hada min kunun gyada mai dadi


Ina zaune a kan gadon innata yayuna duk sun zagayeni

Abba yashigo yace sannu maryama nace yauwa Abba sannu


Yace wai ina sukaiki ne wannan tambayar da Abba yamin yadaga min hankali Dana tuno da abinda yafaru dani

Nasan idan nafadi gaskiya Abba bazai amince min ba

Sai kawai nazabi da nayi karya akaro na farko a rayuwata


Nace Abba masu garkuwa da mutane sun tambayeni ko babana mai kudine nace musu a a nafada musu sana arka shine suka min duka suka saka naketa musu wanke wanke kullum muna dayawa Wanda aka kama amma yawancinsu iyayensu masu kudine shine sukace bazasu smdawo damu gidaba sai randa iyayen yaran nan suka kawo musu kudin da suka bukata


Ba a gama turo musu kudinba sai jiya shine duk suka fesa mana wani Abu Dan kar muga inda za a fito da mu


Abba yayi ajiyar zuciya jin cewa ba a musu komaiba


Nan da nan kowa yashiga fadin albarkacin bakinshi na ta tatsallake rijiya da baya



Abba yace Allah yarufa asiri yafita

Innan mu tace kai munshiga tashin hankalin rashinki maryama dagani har mahaifinki ba maici ba maisha

Har gurin hukama ankai maganar amma dayake bamu da gata ba awani damu a yi bincikenba


Yaya aliya tace sannu kinji maryam allah yadada karewa to ai tunda yanzu dai dama can kinsauke kinyi hadda ki hakura da zuwa islamiyyar nan


Har sai kinyi aure kuma sai ki fara zuwa na matan aure


Innan mu tace wannan haka yake tunda ai an kusa ma

Maryama na ki hakura kinji da zuwa makarantar nan har sai kinyi aure kuma sai kicigaba da zuwa makarantar ko


Na daga kai nace to innan mu insha Allah


Yaya sumayya tace ikon Allah duniya ya lalace ace sace mutum ba abin komai bane a gurinsu




Na dawo normal kamar yadda nake da sai dai ansamu canji saboda innan mu ta lura dayawan damuwar Dana ke ciki


Bayan sati uku da dawowata lokacin al'adata yayi banga komai ba hankalin yatashi sosai


Ga kuma yawan tashin zuciya danakeyi


Ina zaune innar tayi miyar taushe yana ta kamshi nikuwa cikin yana ta juyawa aikuwa sai amai amai sosai nayi inna hankalinta yayi matukartashi


Kishiyoyinta suka taso sukayi wa maryam ca suna salati wai kardai zarginsu ya tabbata akan maryam



Inna ta taimaka wa maryam sukashiga daki


akuwa uwargidan tace wallahi bazaa haifama na cikin shege a gida Anje anyi abin kunya za azo ana rurrufewa to bari malam din yadawo dole aje asibiti a tabbatar da abunda muke zargi



Innan mu gabanta yafadi ras jin sun ambaci ciki


Ya ma za a yi hakan takasance da maryam yarinyar arziki kamila baruwanta da duniya





Abba ne yashigo har sun guntsa mishi aikuwa yabanko kofar dakin innan mu yace ke maryam meke damunki tace ba komai Abba


Yace maza dauko mayafinki muje asibiti innan mu hankalinta ya tashi tace malam yadaga amai sai ace za aje asibiti kobaka yarda da yarkabace



Abba yayi murmushi yace halima kenan 'Dan yau ai ba abin yarda bane balle yarinya baliga irin maryam shekarar ta shatakwas ba aure kuma muga tafara amaye amaye acikin gida ai dole hankali ya tashi


Harda innna akaje asibitin aka min duk wasu gawaje gwaje dayawa kamata amin muka zauna jiran sakamoko



Yaya aliya da taje gidan bata samu kowaba ance duk suna asibiti

Itama tayo asibitin




Antyn maryam data kawo nan sai kuka ta fashe da shi mai tsuma jiki harda sheshsheka


Maryam kanta kuka takeyi na tausayin mahaifiyarta daddy da megari ma duk jikinsu yayi sanyi dajin labarin maryam mai ban tausayi


Daddy yace Ashe daman haka masu kudin mu suke basu da imani kokadan



Megari yace hakane abinkam ai sai addua


Megari yace maryam muna sauraronki cigaba da bayaninki



Next page





Your comment is needed fans


Love u love your comment


More comment more typing












*Signed by ummu afan* πŸ’»
[26/06, 11:54 AM] SIS UMMY: πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€
🎑🎑🎑🎑🎑🎑
πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€
🎑🎑🎑🎑
πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€
🎑🎑
πŸŽ€

*BISSIMILLAHIR_RAHAMANIR_RAHIM*


*Ummu Afan the Gorgeous writer of the year ,Author of 'YAN BIYAU NE &AKWAI LOKACI*



🌟GORGEOUSE WRITERS FORUM🌟


🌟 G.W.F🌟


*Home of gorgeous, intelligent and expert writers we are the best among the rest*



I DEDICATE THIS PAGE TO YOU MAMAN IMAM allah yabar kauna ina matukar alfahari dake over sis keep it up wajen nice comment din ki ❀






_🎑AL'AMIN DAGASH FANS GROUP_ 🎑





πŸŽ€ *AL'AMIN DAGASH*



*PAGE* 9⃣




Anty maryam tacigaba da ba su dad labarinta



Tace nurse tafito dauke da sakakamakon gwajin da aka min


Gaba na yafadi dan nasan yau kam asirina ta tonu ga mutanen gidan dam asibitin sai kace wacce nakashe mutum






aikuwa tana karasowa Abba yace yauwa malama yadai tace baba a sakamakon da gwajin yabamu yarka tana dauke da ciki harna tsawan wata daya



aikuwa guri yadau salati da maganganu

Yaya aliya juyawar dazatayi taga innan mu tana shirin faduwa tayi saurin zuwa ta tare ta fadi ajikinta sumammiya

Akayi cikin asibintin da ita


Abba kuwa durkushewa yayi a inda yake zaune yana salati duniyar yashiga juya mishi


Yace halima kincuceni Dakika bari na aurar da yarinyar nan kamar yadda nake aurar da yan'uwanta


Uwargidan Abba tace daman bawani saceta da akayi yawon iskancinta ta tafi za a rainawa mutane hankali wai ansaceta



Abun yasake tu zura baba na ya taso yafara kaimun duka yana tsine mun yana cewa yacireni daga cikin 'ya'yansa


Ina kuka incewa wallahi Abba bacikin shege bane ina gani yake ma na raina mishi hankali

Da kyar mutanen anguwar suka karbeni a hanun abban mu yace daga nan kuma karna koma mai gida ya koreni


Ya sallamawa duniya ni kwatata kwatata yaki yabani daman nayi magana


Haka yatasani agaba yana dukana yana korani har bakin titin garin yace natafi inda aka min ciki shiya yafeni


Nazauna agurin nacikuka nakoshi bansan inda zan nufa ba danni ba bazan iya komawa kauyen muba saboda babu Wanda zai yadda dani



Ina cikin kukana naji andafani na juyo da sauri naga ko waye sainaga deeja ce kawata tana kuka ganinta sai na rungume ta muna kuka sosai


Mijinta ne yakawota a mashin dinsa sunji abinda yafaru tace lalle tasan ina hanya sai dai yakawota kozata ganni




Nace deeja kinga yadda allah yayi daniko deeja tace karkice komai maryam wallahi na yarda dake nasan akwai wani Abu amma bazaki taba aikata abinda wannan abinda kunyar da ganganba




Nayi murmushi nace nagodewa allah dayasa nasamu mutum daya data yarda dani



Nan nabata labarin komai abinda yafaru sosai deeja tayi kuka tace kizo mukoma gida mumu su bayanin komai



Nayi murmushi nasan daman zakice haka amman sai dai kufara zuwa kumusu bayani inan idan sun amince to na yarda saikudawo mukoma gida


Cike da doki deeja takoma inda mijinta yake dan daman yana jinsu tace yakaita gida suje suwa su abban maryam bayanin komai dan allah



Suna tafiya nayi murmushi na duba lalitar innan mu Dana dauko dan daman nike sayar da komai akazo siya shiyasa tabani lalitar na daura saboda bada canji


alokacin da abban yace nafito muje asibiti dama lalitar tana jikina baciireba


Ina ganin haka nayi hamdala natashi da kyar na tari muta akace ina cikin gari

Wato meduguri kenan




Muna isa tasha akace kowa yakawo kudin mota
Bayar danawa


Daga can gefe naga kawai mota na Lodi naje nashiga mota yacika aka dau hanya


Tunda muka fara tafiya ba abinda nake tunani sai bansan ma me motar take ciki ba



Sai ji kawai nayi anacewa kowa yafito na fito natambayi kudin mota

Akafada min nabayar nakara gaba sai kuma tunanin yazomin na wai a wani garima nake


Juyawa gurin motar nayi nakarewa wa memotar kallo

Can na nufa daga gefe naga wata mata da alama akwai abin da take jira ta Tara kayanta a gefe


Namata sallama ta amsa nace baiwar allah Dan Allah nan wani garine


Tambayar Dana mata yabata mamaki dan na fahinci hakan a fuskarta

Tace yanzu kebaiwar allah Ashe bakimasan wani gari kikazoba

Na daga mata kai alamun bansaniba tace to abuja kike tarayyar Nigeria


Mamaki yacikani wai abuja

Matar tace idan bazan damuba zata min tambaya akan rayuwata dan kuma inda zanje


Nan dai na takaita mata kadan tace idan ta fahimceni dai bani da inda zanje kenan nace kwarai kuwa tace idan bazan damuba zata tafidani gidan nace nayarda





Nafara zama da anty hassana me abinci ina tai maka mata a wajen sana'arta tana bani gurin kwana da abinci sai sabulun wanki haka amma ba albashi hakan ma nagode




Ina nan ina rainon cikina har yakai watan haiuwarsa

Tsakar dare natashida nakuda anty hasssana ta kira ungurzoma dan bazata iya da tsadar asibin abuja ba

Akullum addua ta shine allah karyabani yarinya mace saboda renon 'ya mace akwai hatsari musamamn ma a wannan rayuwar danake ciki na rashin gata
Idan kuma yabani macen yabani mummuna yadda bazata ja hankalin mutane har su cutar da itaba



Na haihu lafiya na haifi 'yata kyakkyawa allah bai karbi addua taba don yarinyar harta finima sosai



Anty hassana tana tayaba kyan yarinyar gata fara Sol da ita



Nayi kuka danaga yarinyar da allah yabani saboda ina tsoron abinda yafaru dani yafaru da ita



Ranar da nacika kwana bakwai da haihuwa nawa 'yata huduba da suna na Maryam



Sosai nake kokarin kula da ita dan anty hassana kullum tana kasuwa

Nikuma sainayi arba'in zanfara zuwa nima kasuwar




Muna haka ina ta renon maryam yarinya me wayo da farinjini itama tun tana karamarta



anty hassana gaskiya ta taimaka min a rayuwata duk da bawai tana biyana albashibane

amma zanci zansha zata sai wa maryam gwanjo masu saukin kudi idan tasamu dama amma fa nima ina bautuwa a wajenta



Muna haka shekarar Maryam hudu aduniya anty hassana tafara ciwo bayan kwana biyu kuwa allah yama ta rasuwa


Nayi kukan rashin anty hassana sosai bayan makokin anty maryam narasa abin yi Gashi maryam tayi wayo kullum setamin maganan makaranta insata amakaranta



Ina zaune nida maryam ina bata abinci abaki aiki naje nayi nasamu akaban abincin

Sallama naji shugowa kawai sukayi Ashe wai dillalan gidan ne sunbani nan gobe na kwashe komai nawa zasu zuba wasu agidan ba tausayi a fuskokinsu


Shiyasa ma bansamu damar basu hakuriba


Haka washagari mukabar gidan na tattara mana kayanmu naja hanun maryam muka fita tafiya kawai nakeyi amma bansan inda zanje ba






Bamuzame koinaba sai kofarwani asibiti kawai nasa kai nashiga cikin asibitin



Har dare yayi bansamu abinda zanba maryam taciba Gashi bani da kosisi


Muna zaune kusada wata mata da alama jinya yakawota saita fito shan iska ta shimfida taburma sunata hira da masu zuwa gaisuwa



Wani katon kula ne agabansu kuma wai anemo musu almajiri yakarbi abinci

Banyi sanya ba nace musu inaso da mamaki matar ta kalleni tace to bawair allah dauka kijuye to


Jikina har bari yakeyi nadubo bakar Leda a jakarmu najuye shinkafa ne haddadiya da miya


Harda nama ma aciki


Nan naje fanfo na wanko flask nakawo mata na mata godiya kafin nadawo gurin maryam natasheta a baccin wahalar datakeyi nabata abinci sosai maryam taji dadi nagani a fuskarta



Tabani tausayi sosai kukanayi sosai saida ta koshi da kanta nadebo mata ruwa fanfo nabata tasha sai bacci kuma na shimfida mata zani ta kwanta kafin naci abinci nima


Anan muka kwana abinmu kasancewar akwai masu kawana a wajen ba Wanda yadamu damu


Inatashi naga wata guntuwar tsintsinya nashare asibintin nan tas kaman jaka


Haka dai har mukayi sati a asibitin nan kuma kullum allah baya hanamu abinci idan mutane suna Neman almajirai zankarba kuma kullum ina share asibitin nan tas

Muna zaune da maryam ina mata tatsuniya sai naga wata ma'aikaciyar asibita tazo tace baiwar allah waikizo inji likita nace nashiga uku badai sungaji damu bane zasu koremu



Nan dai nakama hanun maryam mukabi bayan nurse dinan


Muna zuwa muka zube akasa likitan ma ba musulmi bane

Dakyar hausar tashi yake fita
Yace sannu ko nace yauwa likita allah yasa ba laifi mukayiba


Yace a a no karkidamu kece mesharemana hospital kullum ko nadaga kaina yace good

Ya kalli maryam Yace beautiful girl zonan maryam taki zuwa dan bata yadda dakowa sai antynta kamar yadda take cemin


Murmushi yayi yace idan kina so zakicigaba da aikin zamu daukeki murinka biyarki zamu baki dakin dazaki zauna da yarki acikin hospital din nan


Dan farinciki ma rasa mezanyi nayi saboda dadi


Sosai ma mishi godiya yace karkidamu malama zamu ringa biyarki dubo goma kafin muga kokarinki akan aki sai mukara miki albashi zuwa dubu goma shabiyar sosai nayi godiya yace bakomai


Yacewa nurse ta Nina mata dakin dazata zauna acikin reception tace OK sir


Har munyi gaba yace am malama najiyo yace amma kiringa kula da lafiyar babynki karkibarta tacikomai a hanun mutane kinji ko sosai naji dadin shawarar dayabani


Takaimu ta nuna mana dan karamin dakin da toilet aciki da alamu ma office ne suka maidashi daki nan tace to baiwar allah ga dakin nan dazaku zauna ga toilet nan akwai ruwa aciki saiki tsabtace dakin




Sosai naji dadi itama namata godiya nashiga gyaran o koina yayi fes dashi



Likita yakirani yabani Rabin albashina wato dubu biyar wai kozan bukata naji dadi dan muna bukatar abinci






A da lilin aiki a asibitin nan nasa maryam a makaranta tana zuwa school din ta sosai mukejin dadin rayuwarmu a asibitin nan




Munaki kusan shekara goma zaune a asibitin nan munsaba da likitan nan sosai dan yana temaka mana a arayuwa kaman wani musulmi





Shekarar goma sha hudu sukayi sauka a islamiyyarsu tana Jss two sakamakon rashin shiga makaranta da wuri


Kwatsam muna zaune nida maryam tana min kitso sai mukaji hayaniyya a waje naje mukatashi gaba dayanmu mukafita wazamu gani doctor Patrick ne mukaga 'yansanda sunsashi a mota suntafi dashi


Nayi tambaya meyayi akace min wai ana zargin asibitin nan da saida sassan jiki mutane
Kuma ana zargin dasa hanunsa aciki



Nafasheda da kuka nace ya Allah kasa yazauna a matsayin zargi allah karka tabbatar da wannan Abu haba mutumin kirki irin doctor Patrick




Mukazauna cikin jimami abinda za azo a fada mana


Bayan sati daya naji wai za a rufe asibitin har ankai doctor fursuna




Haka muna ji muna gani mukarbar cikin asibin doctor Patrick dake garki village


Maryam tace anty yanzu ina zamuje nace mata sai inda allah yayi zaman abuja kam bazai mana ba saboda tsadar rayuwa



Haka muka hau motar mararrabar abuja dan inayawan jin sunan a bakin mutane


Munje kuwa alhamdullahi munkarbu dan gidan nan ina magari muka fara sauka na nemi da megari yabamu waje zamufara Sana'a shine yabamu wannan runfar Wanda muke zaune acikinta


Yanzu dai shekarar mu daya da wata biyu agarin nan


To wannan shine takaicaccan tarihin rayuwata


Takaarasa tana share hawayenta maryam matso cikin kuka ta rungume anty tace antyna allah ya isa miki allah saiyasaka miki

Danasan abinda zanji kenan na labarin mahaifina da banbiyokiba kuma ina rokonki gafara akan kiyafe na matsamiki danakeyi kibani labarin babana


Anty dai takasa magana sai kuka kawai



Megari da dad sunma kasa magana saboda tausayin maryam da yarta



Megari yace to Alhaji yanzu zabi ya rage naka akan maryam


Dad yayi murmushi yace ai wato wannan labarinta data fada min yasake samin tsananin sonta a raina


Saboda maryam zan aureki zan rike maryam tamkar 'yata zan hadata 'ya'yana narikesu tsakanina da allah


Sannan kuma bayan bikin zan dauki maryam muje garinsu dan ama iyayenta bayanin komai



Anty maryam ta tashe da kukan murna tace mungode Alhaji Allah yabiyaka duniya da lahira



Daddy yace ai bake zaki gode minba maryam nizan gode miki da kikayarda zaki aureni



Megari yace kai amma naji dadin wannan Abu Alhaji allah yasa masu kudin irinku su yawaita aduniya


Daddy yace amin amin


Abinda nake Neman alfarma niba yarobane dan haka banson maganar auren ya wuce nan sati biyu



Megari yace masha Allah hakan ma yayi amma bari muji ra'ayun malama maryam din


Anty maryam tace ba amince amma ina rokon wani alfarma da abari sai bayan maryam tayi jarabawarta na makaranta



Daddy yayi murmushi yace wannan kadai uzirinki anty tadaga kai alamun a




Daddy yayi murmushi yace ai yanzu baki da iko da maryam nikeda iko da ita a matsayina na mahaifinta saboda haka karma tasake zuwa wannan ma karanta zan canjamata



Wani a kano anty da maryam suka kalli juna maryam tace nagode daddy Allah yakara girma


Daddy yace amin yar daddy



Nan dai daddy da megari sukagama shirya komai

Daddy yace kai zakazama waliyyinta idan allah yaimu nan da sati daya zanturo kanina da abokina sukuga juna


amma yanzu inaso amatsayinka na waliyyin maryam inaso zanbiya sadakinta a yanzu


Megari yace masha Allah hakan yayi kyau sosai kuma ya nuna min kai babban mutumne alhaji baka magana biyu



Daddy yaje mota ya dauko brief case dinshi yadawo yaciro bandry din yan 1000 ya ajiyesu agaban megari yace wannan kuma kudinkuma na menene


Dady yace sadakin maryam ne dubu Dari biyarne


Yace zanturo za amaka gyaran gidan nan gone gobe insha ga cheque na 5 million kasa aljihunka


Yajiyo yace gurin maryam zanturo driver yakaiki kihada lefenki da kanji maryam 'yatama inason kimata sayayya yadda takeso



Ya tura mata kudin dake cikin brief case din



Anty kusan suman zaune sukayi itada maryam

Ganin yadda suke kallon kudin cike da rashin yadda da kuma tsoro



Megari yayi malama maryam kokinajin sunan hamshakin mekudin nan dayashara a kafafen yada labarai na duniya wato AL'HAJI SU'AD BABANGIDA



anty Maryam tace kwarai kuwa jin sunan abakin jama'a




Megari yace to yau baki Gashi
Ya nuna Alhaji da hanunsa


Anty maryam cike da mamaki tace yanzu alhaji daman Kaine wannan shaharraren mutumin amma meyasa kaboye min kanka



Daddy yace saboda ba matsayina nazo infada miki ba soyayyarki nazo nema



Nan dai komai ya kammala tsakanin anty da daddy amma fa da temakon megari dan anty dataji waye dady tace allanfur yafi karfin ta



Hartaba daddy dariya ma sosai





Daddy dakanshi yakaisu gida yace oh my God maryam daman airin wannan gidan kukeciki anty murmushi kawai tayi zatafita yace tsaya bansallamekiba



Maryam karama tafito da brief case din da alhaji ya basu cikin dogon hijabi


Tace daddy yar dady Allah yayi miki Albarko tace amin dady


Ya miki mata wata Leda yace ga tsarabarki


Maryam takarba tayi cikin gida



Daddy yace wa anty maryam to amaryata nizankoma kano yau sainasake dawowa kafin ranar daurin auren



Anty maryam kunya yakamata takasa tace to shikenan agaida yayuna



Daddy yayi murmushi

Please Login or Register in order to submit comment