Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ki soya bayan kinsa mai.

Tana fita waje ta dire bahon ta fara kiran yara tana cewa "kowa yazo ya kaɓi ta annabi "dama yara kamar jira suke suka rugo da gudu wanan yana cewa "baki bani ba ,da haka har waina ta ƙare , kowane yaro murna yake yau anyi sadaka abin da basu taɓa gani Lami tayi ba ,Ramu ta ɗauku ɗan bahon data kawo musu waina ta wuce gida ,tana shiga Lami ta fara ɗura mata zagi tare da cewa "dan kutumar ubanki waye ya bani jarin ko ubanki ne ya bani da har zaku fitar min da abin siyarwata kimin sadaka ban san dai-dai bane ?.
Baki sake Ramu ke kallon Lami bata ce komai ba sbda tasan tayi laifi kuma idan sukayi laifi zama take a kansu dan haka ta fice da gudu.

Zuwa dare Lami ta huce da asarar wainar da tayi ,suna zaune a ɗaki , Mariya dake  riƙe da kwanon tuwo a hannunta ta kalli Ramu da ta shigo yanzu tace "Ramu babu miya ki daɗo mana "wata uwar harara Ramu ta galla mata kana tace "kinga nayi kama da sa'arki wlh zanci ubanki "baba daya idar da sallah yana ajiye carbi yace "gara kici ubanta tunda bashi da ƙafar tashi yaci naki uban "Lami dai bata kulasu ba ,sbda lokaci zuwa lokaci tunanin asarar waina yana faɗo mata, sanin yau tun da taga Lami na cije baki inba sa'a ba sai ta duki mutane yasa ta zuwa gurin kayanta ta zauna ,jira take Lami tabar gurin ta fice da kayan ,a cewarta gara gidan tsohuwa dan bata takurawa mutane ,cikin sa'a Lami ta miƙe tana harar baba dake kai lomar tuwo a fili tace "ba'a iya aikin komai ba sai mugun cib,anji kunya ka zauna ka naɗe ƙafa mata ta ciyar dakai "kallonta baba yayi yace "ke Lami iskancinki ya fara yawa fa ,da ban barki kiyi sana'ar ba zakiga dai-dai ne ?Lami na kaɗa ƙugu tace "wlh ka kuma magana sai na zauneka ,kai har kanada bakin yin surutu mtsw" yasan ba ƙaramin aikinta bane hakan ya sashi cewa "yi haƙuri "yaci gaba da cin abincinsa , Lami na fita Ramu tace "baba gidan tsohuwa zan koma "waro ido baba yayi kana yace "zaki janyo mata abin zagi ko ?shigowar Lami ne yasa su yin shiru , Lami ta wuce uwar ɗaki tana ci gaba da mita , sai da ramu ta tattara kayanta duka sai da takai bakin ƙofa tace "wlh baba kishiya zakayiwa Lami haka matar gidan su Bashari ma ta....da gudu Lami ta biyota tana cewa "matar gidan ubanki ce marar hankali ,idan ma anyi min kishiyar kune a wahale wlh banda ina da ku bazanyi sana'a ba "ta koma ciki ta gyarawa su Mariya gurin kwanciya .

Cikin duhu haka take tafiya babu batun tsokana dan babu haske a gari ba'a kawo wuta ba , tana cikin tafiya taci karo da wani abu mai gashi , da farko dai ta tsorata ,cikin sa'a wani yaro yana tafiya da fitila a hannunsa tace "kai haska min "haska mata yayi yaron yana kallon inda take kallo , doll ce irin ta wasan yara ta ɗauka tare da cewa "ungo fitilarka ta ranƙwasheshi ,yaro daya ji zafi yace "shegiya ƴar Lami mai waina "harta zuba da gudu zata bisa ya arce  dawowa tayi taci gaba da tafiya har ta iso gidan tsohuwa ,bubuga ƙofa ta fara tana cewa "tsohuwa nice ramu ki buɗemin "tsohuwa datayi bacci akan sallahaya bata ma san ana buga ƙofa ba , duwatsu Ramu ta tsinto ta dinga wurgasu jikin ƙofar tana ƙwalawa tsohuwa kira ama ina bacci yayi daɗi.
Da Ramu ta gaji da kira ta zagaya baya inda windon ɗakin tsohuwa yake ta, buɗe Allah ya taimaketa a buɗe yake kuma babu abin da ya tare sa zata iya shiga ta ciki , tana shiga ta dira tare da ƴar bebinta  ta rufo wundon ,sai a lokacin tsohuwa taji motsin mutum kasancewar duhu daya gauraye ɗakin  ,tsohuwa na daga kan gadonta mai rumfa murya a hankali tace "dan girman Allah waye ya faɗo min ta wundo ? Ramu da ke kiciniyar lalubo ƙafar tsohuwa ,cikin sa'a ta sami ƙafar ta haɗa da ƴar bebin hannunta ta matse , a zabure tsohuwa ta fara kiran ya hayyu ya ƙaiyumu bi rahamatika astagis , dariya ce ta kuɓucewa Ramu ta sauya murya i'zuwa ta maza tace "adu'ar masu naƙuda ce fa "tsohuwa data kiɗime batajin abin da Ramu ke cewa "sai uban kwararo adu'oi take ,tsawa Ramu ta dakawa tsohuwa da muryar maza tace "ke tsohuwa ina naman da ɗanki ya kawo miki jiya ?jiki na rawa tsohuwa tace "a haska fitila wlh Allah yana nan a ƙasan gado a kwano ɗan caina "murmushin mugunta Ramu tayi kana tace "ki rufe idonki ko kuma in harbeki "sbda tsoro daya gama kama tsohuwa babu shiri ta rufe ido har da sakin fitsari, sakkowa Ramu tayi a hankali ta lalubi aljihunta  sbda bata rabo da fitila irin wacce ake samu a jikin leta ,kunsan haskenta kaɗan ne ,ta haska ta janyo kwanon har ta juya zata dira ,ta dawo da baya tare da kuma dakawa tsohuwa tsawa tace "wlh kika buɗe ido sai nasa an markaɗe min ke anyi man shafawa "dama bata buɗe ido ba har Ramu ta dira ita da kwanon sbda ta mance da ƴar bebinta a ɗakin, tana fita ta zauna a tsakar gida dama garin akwai yawaitar zafi a haka wasu na kwana a waje , bayan ta shimfiɗa tabarmar da take zama idan tazo gidan ta kunna ƴar fitilarta tana haska kwanon ,cikin rashin sa'a murfin ya faɗi ƙasa tasss  tsohuwa na daga ɗaki ta kuma firgita a fili tace "in buɗe idona sun tafi ne ? babu mai bata amsa hakan ya sanyata buɗe ido  tana shirin gyarawa ta zauna kan bebi , jin laushi sosai ya sata kurma ihu tana cewa "Bashir kazo ka taimakeni wlh aljanu a gidannan suna neman ganin bayana "matsawa tayi gefe ta kwanta a takure cike da fargaba .
Ramu kam an sami duniya , tsire ne a cikin kwanon da yawa yaji ƙuli ,ta haɗiyi miyu tare da jefawa baki ,tanajin ihun tsohuwa ta ƙi kulata a zuciyarta tace "maganinki kenan ai tunda ke kinzamo masifaaffiya "taci gaba dacin naman , sai da taji tayi nak sanan taja kwanon gefe ragowar naman bai fi guda uku ba ,tana shirin miƙewa zuwa fitsari taji ana buɗe ƙofa ,tsorone ya kama Ramu sbda tasan inhar tsohuwa tasan itace ta shigo wlh ta mutu ,da gudu Ramu ta shige kicin tare da tsugunawa tana jiran tsohuwa ta wuce ita kuma ta kona ɗakin , tsohuwa da taji alamun motsin mutum ya sata komawa ta danna saƙata tare da janyo po ta tsuguna tayi fitsari ,tana gamawa ta janyo buta tayi tsarki ta koma kan gadonta ta kwanta , Ramu najin tsohuwa ta saka saƙata ta dawo tsakar gida kan tabarma ta kwanta a zuciyarta  tace "ga ƙoshi ga kwanan yunwa wayo Allah na , tana tsaka da tunani bacci ɓarawo yayi gaba da ita .

Zaune Saudat take kan yaloluwar katifarta ta ɗauko wayarta ta danna number Abdull sbda jiya bai kira ba , ring ɗaya zuwa biyu ya ɗauka ,a hankali yace "Sarauniyata ya kike ya gida ?"idonta a lumshe tace "baby ka mance dani ko baka ko nema na "murmishi yayi kana yace "bazaki gane bane aiyuka ne sukai min yawa wlh shiyasa nayi busy yanzu "ƙara lanƙwasa murya Saudat tayi tace "yaushe zaka dawo ?yama rasa mai zaice mata dan yasan a zahiri bai je ko ina ba yana nan a garin yace "gobe gurinki zan fara sauka "tsalle ta buga tasan kuɗinta suna hanya gobe insha Allah tace "Allah ya kaimu babyna "Abdull yace "amin" Anty Ummi dake tsaye a kansa bai ma san ta kuma dawowa ba ,jin motsin ƙass da tayi da hannunwanta ne ya sanyashi juyowa jiki a sanyaye ya kalleta yace "anty barka da war haka "barka "antyn tace "masa tana harararsa tace "ina alƙawarin da kukayi kai da Fati tace "min wai zaka tura su Abbanka ?waro ido yayi da mamaki yasan wanan shirinta ne badan yasan anty bazata yi masa ƙarya ba da tun tuni yace "wlh shirya masa akayi , sai ya tsinci kansa da cewa "eh haka ne ayi musu magana "antyn bata jira ƙara jin maganarsa ba ta fice farinciki ya luluɓeta ,sai da anty ta fita ya dawo haiyyacinsa ya share gumin dake wanke masa fuska ya furzar da iska mai zafi a fili yace "oh my god na shiga uku wlh ban san na faɗi wanan maganar ba "yaushe akayi haka ?har yayi kamar zai fito sai kuma ya kuma kan sofa ya zauna yana lasar lips ɗinsa da suka kasance jajaye cikin damuwa.
Anty Ummi na fita ta tarar da Hajiya a dining tana shirin zama tace "yaya ga kyakkyawan albishir wlh da gaske ne Abdull ya amince da auren Fati "alhmdulilh Hajiya tace "tare da ɗaga hannu sama tana mai godiya ga Allah sbda tasan inhar jinin Hajiya kubura ta samarwa ɗanta to tabbas tayi babbar nasara sbda inda suke da ita lokacin suna yara bacci ke rabasu ,duk da mahaifin Hajiyan Abdull sunfi na Hajiya kubura dukiya hakan bai hana iyayen nasu da suke matsayin abokai raba kan ƴaƴan ba.

Fitowa palo Abdull yayi hannunsa riƙe da wayarsa ,yana taka ƙasa kamar yana jin tsoro ,zama yayi a kan kushin tare da sauke ajiyar zuciya kamar wanda yayi kuka , Hajiya ta kallesa tace "auta na yadai ?baya son  ɓacin ran Hajiya yasa shi cewa "lafiya lau hajiya mai aka dafa mana ?hajiya dake sakar masa murmishi tace "Ummi kin kammala tuwon shinkafar kuwa ?"anty Ummi data kasance ƙanwar hajiya tace "eh an gama tun ɗazu har nasa a leda "hajiya tace "auta jeka kitchen ka ɗauko ko kuma ka ɗibi inda zaiyi maka ga farfesun anan "tom Abdull yace "ba tare daya tashi ba ,anty Ummi data kammala cin abinci ta dawo kusa da Abdull ta zauna tace "yarona a wace ƙasa zamu haɗa lefen ne ?Abdul daya kejin kamar ya kori Anty Ummi a gidan sbda yana ganin kamar ita ke zuga hajiya akan ya auri Fati ,bai bata amsa ba sai da yaja lokaci kana yace "a nan Kano "waro ido anty Ummi tayi har zatayi magana taji watarta na ring tana dubawa taga number saurayinta ne da sauri ta miƙe kana tace "zamuyi magana anjima ta shige ciki , Abdull daya gama ƙulewa ya taso yazo gurin hajiya yace "hajiya wlh ki gayawa anty Ummi ta daina takuramin da yawa ,ita Abba bai hanata son wanda take ra'ayi ba amma ni tasamin ido , badan kince kar in ƙara yi mata rashin kunya baki yafe ba da wlh bata isa ta dinga shimfiɗa min dokoki ba nasan dai na girmeta "sai da Hajiya ta bari ya kai ƙarshen maganarsa sanan tace "hakane Abdull kasan Ummi uwace a gareka duk da ƙanƙantar shekarunta bana buƙatar ka rainata ,ni a ganina Fatima bata da makusa da har ake taroka kana zamewa ,amma ai Ummi tace "ɗazu kace kana son ita Fatin ?sbda maganar da hajiya tayi masa na kar ya sake ya raina anty Ummi da kuma kwanciyar hankalin hajiyarsa ya sashi cewa "eh hakane "masha Allah hajiya tace "kasan dai idan Abbanka ya dawo bazai sanya rana mai tsayi ba ko ?,cikin rashin jin daɗin ya faɗi abu ba da niya ba ya sashi runtse ido kana yace "toh "ya miƙe ya fice sbda lokacin anata kiraye kirayen sallah.

Gidan su Fati.
Washe gari da safe Fati da gajiya Kubura da dadynta sun hallara a dining room suna cin abinci , dadyn ya kalli Hajiya Kubura yace "nayi farinciki sosai jiya Fatima ta cemin wai Abdull Jabbar yana sonta "murmishi hajiya Kubura tayi tana kai soyayyar doya bakinta tace "ai nima nayi fatinciki sosai dan wlh yaron akwaishi da hankali ga jin maganar iyayensa nafi kowa farinciki "sunkuyar da kai Fati tayi kunya duk tabi ta luluɓeta ,dady yace "to yanzu jiran iyayen nasa ya rage ance ma yau Alhaji Abban zai dawo "eh Hajiya Kubura tace "sbda naji a bakin Ummi "dady dake miƙewa yace "wai har yanzu Ummi batayi aure bane ?Hajiya Kubura tace "aiko dai kaima ka faɗa ta tsaya ruwan ido "dady baice komai ba yai hanyar bedroom ɗinsa Hajiya Kubura ta bisa ,Fati dake zaune ta bi bayan momynta da kallo a fili tace "oh nima idan nayi aure haka zan dinga kula da Abdull ɗina wayooo.

Gidan tsohuwa.
Washe gari ,da asubha Ramu ta makara har tsohuwa ta buɗe ƙofa bata sani ba , sai da tsohuwa taje alwalah ta dawo har zata wuce sai tayi hanyar kitchen sbda ta buɗe kajinta da suke kwana a keji ,tana shiga taga kwanon ɗan caina a rufe , buɗewa tayi taga naman ciki saura kaɗan ta jinjina kai tace "wato wanan shegiyar ce mai kama da aljana ta shigo min jiya ashe ? to Allah ya toni asirinki ,ta juye mata ruwan butar data ciko duka a jikin Ramu tana cewa "ai dama na sani sai ke irin Lami irin tsiya "Ramu ta miƙe a zabure tace "mai kuma nayi ?murguɗawa Ramu baki tsohuwa tayi ,Ramu ta kawashe da dariya sbda yadda bakin ya juya ko bakayi niyar dariya ba sai ka dara ,tsohuwa tace "wlh ki kiyayeni dama ashe kece kika shigomin jiya ko ?cikin rashin gaskiya Ramu na sosa kai tace "nifa na bubuga ƙofar waje naga kin kulle shine na duro ta katanga wanan kwanon da kike maganarsa banma san dashi ba "waro ido tsohuwa tayi a zuciyarta tace "karfa azo aljanunne da gaske in shiga uku "ganin Ramu ta tafi gurin kwanon ta buɗe ta fara ci kamar mayunwaciya tsohuwa ta hangame baki tare da cewa "Allah sarki ashe ƙazafi nayi miki ,aljanun ne da gaske suka cinye naman ko kuma ɓarayi dama ke naba dana sami lada "sai da ramu ta gama cinyewa sanan ta ɗago da hawayen gulma shaɓe shaɓe a fuskarta tace "ba kince ni na cinye ba "tsohuwa da tausayin Ramu ya kamata tace "kiyi haƙuri ƴar nan gashi ko wanke baki bakiyi ba "Ramu tace "ai nama nagani "tsohuwa tace "to kiyi alwalah sai ki haɗa mana shayi na saka ruwa a flas "to Ramu tace "jiki na rawa bata fatan suyi faɗa a wanan lokacin saboda tana son ta sha madara , buta ta ɗauka ta zubo ruwa ta shiga bayi tayi kashi ta daɗe tanayi sbda gudawa ce ta kamata ,daga ƙarshe ta fito riƙe da ciki tace "tsohuwa bazan iya tashi ba "tsohuwa dake shirin tada sallah tace "mai kuma ya faru ?"Ramu kam har ta kai ƙasa ta durƙushe tsabar jin guwaiwo yinta babu ƙwari da tayi ,leƙowa tsohuwa tayi sbda ta ɗauka sharrin Ramu ne ,tana leƙowa taga ramu a durƙushe kanta a kife tana kuka ,a guje tsohuwa ta taho tana salati ta kamo hannun Ramu dake kuka suka nufi ɗaki ,ta kwanta kan tabarma tana mayar da nunfashi , tsohuwa ta tayar da sallah , bayan ta idar da sallah ,ta juyo taga Ramu har ta fita haiyyacinta a ruɗe tsohuwa ta fice ko takalmi babu iya kacin hijabin dake jikinta, kasancewar tsakaninsu da kemis babu nisa yasa ta isa nan da nan , samu tayi da mutane a ciki sun kai biyar ta kutsa ta shige kowanne na ganin ikon Allah ,tana isa gun da likitan ke zaune ta sa masa kuka tare da shan majina tace "likita dan Allah kazo ka duba jikata wlh tana cikin  wani hali "wani mutumi dake tsaye fuskarsa da rashin walwalah yace "haba baba mu da muke tsaye muna jiransa ba damuwa bace ta kawomu na jikarki kika sani ?"to ni nan da kika ganni wlh ciwon mata ta ne ya tashi kuma sai likitan yaje ya gwadata idan akayi jinkiri za'a iya rasa ranta "cikin rashin kulawa da tasa damuwar tsohuwa tace "likita dan Allah kaje ka duba Ramu karta mutu ita kaɗai iyayenta suka mallaka "wani saurayi ne ya kwashe da dariya kana yace "haba ƴar tsohuwa ba sai kin haɗa da ƙarya ba amma ai Ramatu nada ƙanni da Mariya da wacece ma na mance ba ita kaɗai bace "likita dai najin bidirin da akeyi ganin tsohuwa na shirin kurma masa ihu yasa shi cewa "zomuje ya kamo hannunta suka ɗauki hanya zuwa gidan, suna shiga suka samu Ramu a tsakar  gida ta zuba tagumi rana ɗaya harta rame sosai , kujera tsohuwa ta miƙo masa ya zauna tare da kallon Ramu yace "mai ke damunki ?kuma yaushe kika fara rashin lafiya ?murya ƙasa-ƙasa Ramu tace "gudawa nake ,kuma yau ne ɗazu "ok "likita yace "amma mai kikaci jiya ?...!

Pls vote comments and share dan Allah 😘.

Mom Islm
[29/01, 10:10 PM] Mom Islam Ce: 🤦‍♂️🤦‍♂️🤦‍♂️🤦‍♂️🤦‍♂️🤦‍♂️🤦‍♂️
   
*NI DA   YARINYA*
🪂🪂🪂🪂🪂🪂🪂🪂

Zainab Habib/Mom Islam

P 5-6

Gaban Ramu ne ya bada rass ,tsohuwa dake tsaye hankali a tashe tace "ni anya ma kinci abinci kuwa ?dan nasan Lami muguwa ce "Ramu dake raba idanu ta kalli likita tace "kawo kunnenka in faɗa maka wani abu "ɗan hararata yayi kana yace "ke inada abinyi fa ba wasa nazoyi ba "riƙe ciki Ramu tayi zata dararar ihu tsohuwa tace "haba likita kayi mata a hankali ta jigata ka tsaya kaji mai zatace "likita da yaga hankalin tsohuwa ya mugun tashi ya sashi matso da kunnensa dai-dai saitin ta ,Ramu tace "nama naci wlh shine ya sani gudawa ,dan girman iyayenka karka faɗawa tsohuwa wlh zata yimin dukan mutuwa "likita daya jinjina kai tare da ɗagowa yaga babu tsohuwa a gurin yace "ina tayi ?Ramu da ta ɗago kai itama tace "oho "ganinta sukayi ta fito hannunta riƙe da kofin silba mai murfi ta miƙawa likita tace "gashi ai gani nayi kun dace da Ramu insha Allah ka sami matar aure "likita bai san lokacin daya ɓarar da ruwan bunun dake cikin kofin ba duk da zafinsa bai hanashi bawa tsohuwa amsa ba yace "ba amin ba wlh ,da nasan abin da zan tarar a gidannan kenan wlh da ban zo ba "Ramu ko duk daɗi ya suka haɗa ido da likita tayi masa murmushi ,likita dayaga ana neman ɓatar masa da hankali yace "zan tafi shago anata jirana tsohuwa kizo ki karɓi magani "tsohuwa da ta saki baki ganin yayi mata ɓarin ruwan shayi gashi yazo da abin gwaji bai gwada Ramun ba ,ya sata cakumo gaban rigarsa tace "mutuwa kakeson tayi ?likita dake shirin tafiya babu hali yace "dan Allah ki sakeni inada tarin aiyuka a gabana "sakeshi tsohuwa tayi kana tace "ni da nasan asalinku ,dan dai zumuncin yanzu daya zamo abin wasa ne amma da kakarka da tawa uwa ɗaya uba ɗaya kuma zani gidanku yau in tabbatar maka mu danginku me ,haka mahaifinka ƙani ne a gurina auran zumunci akayi musu da mahaifiyarka "ba tare da ya tsaya jin surutun nata da take ko haɗiyar miyau batayi ya fice da sauri ,yana cewa "Allah ya kuɓutar dani kaji wai in auri wanan yarinyar "yarinyar da kwata-kwata shekararta bai fi sha huɗu ba wlh an cuceni "yana komawa kemis mutane suka fara yi masa masifa akan ya biyewa tsohuwa sun tafi gashi  bai dawo da wuri ba ,ci gaba yayi da harkokin gabansa ba tare da ya basu amsa ba dan yasan yayi laifi .

Likita na fita Ramu tace "tsohuwa nima ina sonshi "murmishi tsohuwa tayi da bakinta da yake ɗan lomawa alamar wasu haƙwaran sun fice tace "ai banga uban da zai hana wanan auren ba ,dan nima ƴar uwarsu ce ,bari idan kika ƙara samun sauƙi zuwa jibi zani gidan kici kwaliya kinji ?"har Ramu na tsalle kamar ba itace mai ciwo ba tace "to "riƙe mata hannu tsohuwa tayi suka wuce ɗaki domin karyawa.

GIDAN SU SAIDAT
Saudat nata murna yau Abdull zai dawo kuma ya faɗa mata zuwan dare zaiyi , tana daga ɗaki misalin ƙarfe sha biyu na rana 12:pm taji yaro yayi sallama ,ƙin amsawa tayi sbda ta ɗauka tela ne ya aikoshi , Umma dake tsakar gida ta amsa tare da cewa "ya maman naka ?lafiya lau yaron yace "wai ga kuɗin adashi , to Umma tace "ta ciro naira goma taba yaron yace "yasi alewa "godiya yayi mata ya fice .
Saudat naji ance kuɗin adashi ta buɗe ragar wundonta tana taya Umma ƙirgar kuɗi , Umma dake shirin tashi ta shiga ɗaki tace "wai ashe mutane sun daɗu kuɗin har yakai dubu goma ?Saudat tai tsalle a fili tace "hhh anjima zan aresu kafin Abdull yazo ya bani.
Umma na zaune a inda take tun ɗazu bata tashi ba ,dan kuɗin ma a cikin kwanon gabanta ta ajiye , Saudat ta fito da ɗaurin ƙirji tace "Umma akwai ruwan zafi ne ?"eh Umma tace "ɗibi na waccar tukunyar "bayan Saudat ta ɗauko bokiti ta ɗiba ta shige wanka ,kasancewar sosonta da sabulu a leda suke ta maƙaleshi da hannunta , ta daɗe tana cuɗa jikinta daga ƙarshe ta kwara ruwan ta fito , samun Umma ta shiga ɗaki tayi itama tayi nata ɗakin , bayan ta shiga ɗakinta ta janyo jakar kayan kwaliyarta tana shafa mai ,tana shirin shafa hoda ne taji Umma ta fito tana ce mata  "Saudat zani gidan mai adashin nan inji inda akayi dan Allah karki bari awakan nan su shigarmin ɗaki ,keda idan kika shige ɗaki kamar bakya gidan "to Saudat tace "tana dariya ƙasa-ƙasa tasan kafin Umma ta dawo ta riga da ta fice a gidan, da sauri-sauri ta shirya ta sanya leshinta baƙi mai adon fulawa ruwan tasa tare da sarƙa da ɗankunne ,kasancewarta wankan tarwaɗa bata cika fari sosai ba ya sanya kayan yi mata kyau , yau kam haɗa sallah zanyi Saudat ta faɗa tana juyi sbda ita kanta tasan tayi kyau (niko nace mai yasa bakiyi alwalar tun kafin ki fara kwaliyar ba ,dan wanan kuskure ne babba).

Tana gamawa ta fito hannunta riƙe da wayarta ,kai tsaye ɗakin Umma ta shiga ta fara dube -duben inda kuɗin suke , har ta fitar da rai da ganinsu tana ɗaga filo taga kuɗaɗen a nannaɗe ta zari dubu biyar tabar dubu biyar ta fice tare da saƙalo ƙofar gidan , ƙasan anguwarsu ta gangara naga ta tsaya a wani ƙofar gida tare da danna wata number , rin ɗaya aka ɗauka Saudat tace "Karima kina gida kuwa ?lalle zakiyimin "wacce aka ambata tace "wlh nayi tafiya ina Kaduna anyi mana rasuwa "cikin rashin jin daɗi Saudat tace "ayya Allah yaji ƙan rai Allah kuma ya dawo dake ɗafiya "amin Karima tace "Saudat ta juya ta nufi shagon mai ɗinkin ta , tana zuwa ta samesa   yana aikin nasa wato ɗinki , yana ganinta ya washe baki tare da cewa "hajjaju kenan kina wuta,sallama Saudat tayi ta shiga cikin shagon tace "afuwan Habu wlh ba haka naso ba kasan gari yaci wuta "Habu na dariya yace "ai nayita aiken yaro wai baki da lafiya "cikin alamun rashin gaskiya Saudat tace "am eh wlh zazzaɓi ne "mai ɗinki yace "Allah ya ƙara lafiya "Saudat tace "amin.

Neman guri tayi kan kujerar dake gefe ta ɗinki ta zauna tare da buɗe ƴar jakarta ƴar mitsi tsiya ba lallai kasan tana tare da ita ba ,ta ciro dubu biyar ɗin hannunta ta miƙa masa ,tela yace "to ai ni dubu huɗu zakibani "Saudat tace "kayimin kirarin da nake mutuwar so shiyasa na baka kyauta "Habu tela yasa dariya yace "tabbas zanyi tayi inci gaba da samun kuɗi a gurin matar governor  Allah yasa mafarkin da nayi jiya ya tabbata "Saudat na dariya tace "amin nagode "tayi masa sai anjima
Hanyar gidansu ta nufa dan tama mance da ta ɗauki kuɗi a ɗakin Umma ta shiga da sallama kamar anyi mata albishir da gidan aljannah tana shiga tace "Ummana yau ina cikin farinciki "Umma dake rataye mayafinta a bakin ƙofa tace "to mai yafaru ne ? Saudat tace "anyi min kirari sosai "dan karta gwaleta Umma tace "kaga matar gwamna "tsalle Saudat ta doka tana murna .

Zuwa yamma wajen ƙarfe bakwai ,Saudat ta sake yin wanka tare da yin sallah tayi kwaliya wacce tafi ta ɗazu ta feshe jikinta da turare masu ƙamshi , ɗakin

Please Login or Register in order to submit comment