Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Alh. Yusuf Abbakar As_siddique, the As_siddique's CEO, the young billonaire, the African's third billionaire, the Nigerians number one billonaire"
So are u satisfied my lil sis?"
Zee ta jijjiga kai kmar kadagaruwa jin wannan uban kirari da ake mishi,
Kuma kinsan meyasa yace zezo? Zee ta sake jujjuya kanta a sanyaye
"Saboda Abban nihal ya fadamishi babu inda ze samu well served delicious food, se a gidanshi" ta karasa fada tana nuna Zee a matsayin ita kenan me wannan girki,
The moment he heard about d nice dish he quickly agreed without any hesitation, do u know why?"
Zee ta sake karkada kai a hankali
"Well bcoss he loves food my dear, he's addicted to nice dishes and he hardly get the time to eat due to his tight schedules"
Miqomin wayata na nuna miki pics dinshi, Zee ta janyo wayar Anty hawwern, itakuma ta tapi searching sunanshi a insta, saidai taga acct. Din nashi private ne, dan haka ta sauya akala ta koma Wikipedia, nan da nan sai ga hoton, Alh. Yusuf ya bayyana, Zee ta amshi wayar tana kallon hoton, he's d same guy data hadu dashi a jirgi sanda zata taho, her jaw drop.... a cikin ranta take fadin "idan dai har shidin billonaire ne kamar yadda anty hawwer ta fadi, meyasa ya biyo flight bebi private jet ba?, and ya akayi yake da time haka da har ze iya sparing yazo dinner kuma why is he all alone sanda ta ganshi babu wani guards, ko P.A atleast".....


Da idanuwa Anty hawwer kebin abincika da kallo kamar ta cinyesu duka, they re all served in an inviting way, plated so nicely and lovely, but u won't judge until the mastication starts,
Karfe 7 ta buga daidai sanda suka ida parking motocinsu suka shigo cikin gidan, sunata hira jepi jepi abinsu, bazaka kalli As_siddique kace shine As_siddique dinba a yadda yake free abinshi saidai in ka kalli suturar jikinshi zaka san naira tayi ihu, already everything is served on d dining area, koda suka shigo falourn babu kowa, ya sule takalmanshi tun daga bakin kofa, kyawawan kafafunshi suka bayyana, ya karasa dining area batareda ya jira uncle muzakkir ya mishi iso ba,
"I just can't wait seeing d dining full already" ya karashe mgnr yana murmusawa, shima Uncle muzakkir yai dariya, babu wani damuwa ya zauna sosai ya sakko da abincikan kasa dan ba al'adarshi bace cin abinci a sama, yayi serving kanshi dan already, his mouth is watering,
Bai tsaya jiran ayi mishi bismillah ba ya soma ci, uncle muzakkir kuma dakinsu ya wuce ya tarar da Anty hawwer taa fito daga wanka tana shiryawa ma almost done, dankwali kurun ya rage, haka ya saka ta daura tasa gyale suka fito,
Koda ta shigo falour mamaki ya kamata ganinshi tsakiyar falour yana baje koli abinci, ta kunshe dariyarta dan da alama ko ganinsu beyi ba, gyaran murya uncle muzakkir yayi, sannan suma suka zauna, uncle muzakkir yai joining dinshi,
"Abban nihal ina Zee?" Ta fada tana dube dube, bayan sun gaisa da As_siddique.... uncle muzakkir dake kokarin fara kai abincin baki, yace gaskiya ban ganta ba tun shigowata,
Miqewa tai ta karasa kitchen dan ta barta tana cewa sai tayi fruit salad, ya mutun zeci abinci babu fruit da zasu taimakwa abincin yai digesting, aikuwa tana ta aiki Anty ta taddata, ta kammala hada fruits din sai coffee datake saukewa,
Ta rike haba, lallai sannu ke bama kya gajiya da girki naga alama
Zee tai murmushi
To kizo muje ku gaisa, Zee ta zaro ido, a hakan? Haba Anty ai kawai ki karasa musu dashi nikam wanka zanje nayi kmr yadda kikai wanka, idan na gama basu gama ba ma gaisa,
Okay cewar anty hawwern,
"To yanxu mene amfanin wani coffee"
"Ai anty dinner babu coffee lami ce" wananan kuma ke kika sani, ta dauki bowl din fruits din ta soma kai musu itakuma Zee ta shige dakinta zuwa bandaki, da kamar bazata kai musu coffeen ba amma se ta haqura dai ta kai gudun kada Zee taji haushi,
Lokacin har ya kamaamala cin abincin be bar komi a plate dinba, haka dabi'arshi take indai abinci ya mishi dadi, bai kula fruit ba bisa mamaki taga yakai hannu ya dau coffee yana fadin "kinsan shi idan ya huce bazeyi dadi ba"
Dadin girkin da As_siddique yaji ne yasaka ciro kudi irin naamu na gida nijeria ya ajiye sanda yazo tafiya yace abama wacce tai girki tukuici,, dan Anty hawwer ta sanar dashi ba itace tai ba,
"Looking forward to see her" shine abinda ya fada sannan ya musu sallama ya tafi, Zee na zaune gaban dressing mirror tana shafa mai, taji alamun sun fito, ta dan yaye curtings din saidai bayansu ta hanga kurun....

Abban nihal yaita bama Zee labarin irin santin da Yusuf As_siddique ya dinga mishi bayan fitarsu itakuma se dariya take, wai harda cewa ban taba cin abinci mai dadin wannan ba kamar ba'a duniya ba, its out of d world" Duk suka saka dariya,
Anty hawwer ce tace "ai gaskiyarshi girkin Zeen is out of d world" uncle muzakkir ya dora da "exactly"
"Yace ma fa badan satar hanya yayo ba da se ya kawo personal cook dinshi ta koyi one or two things"
"Au nan ba'a san ma yazo ba kenan" cewar Anty hawwer
"Ai yallabai baze barshi ba shiyasa kika ganshi single babu ko guard balle cook ko P.A"....
Zee a ranta ta samu amsar tmbyarta ta dazu
Zee ta dauki kudin ta raba biyu ta basu rabi rabi dan sunyi mata komi itakam yanxu tasan battada kamarsu a rayuwa tunda ta rasa su Ammi, gudun kada taji babu dadi yasa suka amsa,

Satikan Zee biyar da kwanaki uku a gidan Anty hawwer zeena ta kirata, tasan tunda taga kiran zeena zancen daya ne dan shi aketa nanatawa cikin en kwanakin nan a cewar zeenan duk sanda sukai waya,
A sanyaye tace "zeena an kafene?"
Zeena tace "eh Zee dazu da safe aaka kafe, nima yanxu haka aka turomin na samu 3.55 CGPA kuma 3.41, Zee ta sauke numfashi ta zaqu taji nata sakamakon,
Nikuma fa? Ta tambayi zeenan?
Kema haka Zee saidai ke kam akwai carryover, gwale idanu tai jin tanada C.O, "practical ce ko?"
Zeena tace eh a sanyaye, hawaye suka ziraro daga idanunta, shikkenan karantunta ya soma tabarbarewa tunda tai rashin su Ammi
Bata baki sosai Zeena takeyi daga haka harta haqura tana mai kara karfafa mata gwiwa da cewar zata iya din....

Da Anty hawwer ta dawo ta tarar da ita babu wani kuzari ta tambyeta, Zee taji ruwa na taruwa a idonta, C.O akwai cin rai, ta rungume Anty hawwer tana kuka, lallashi Anty hawwer ta shigayi dukda batasan dalilin kukan ba saida ta dena dan kanta ta soma ma Anty hawwern bayani
"Result dinmu ne ya fito Anty, kuma inada C.O guda daya" wasu hawayen suka sake ballewa, Anty hawwer ta rike haba, wai dama duk saboda C.O kwalli daya ake wannan kukan,
"Kuma wlhy Anty sau uku ne banyi attending practical dinba, lokacin da nai rashin su Ammi ne danayi sati da kwanaki banje ba, ashe malamin yayi ta fixing classes kuma yace du wanda baya zuwa to bazeyi passing course dinshi ba, ta sake sarce hawayen takaici

Saida Anty hawwer ta jira ta gama sannan ta soma bata baki cikin kulawa tana mai bata haquri da fadin samun C.O bawai yana nupin karshen karatunta bane a'a yana nupin ta kara kaimi ne cikin karatunta.....

Kaimi kam Zee ta kara
Saura sati biyu su fara registration, an kafe musu yawancin courses din da zasuyi dan haka Zee taita browsing littafai tana ajiyewa, saida ta tara harda vedios na karatu sannan ta soma, da biochemistry ta fara karatun nata, to koda aka fara registration Zee ta turawa zeena kudin tayi mata online a can,

Anyi resumming school da sati daya sannan Zee ta soma shirin komawa sanin da tai koda an koma da farko ma ba wasu abubuwa za'ai dayawa ma daga cikin lectures din du ba'a faraba, kuma tana jin dadin karatun datake a can din.... Wayar da zakiyya tayi mata kuwa tapi dari dukdan ta dawo fa an fara lectures, dayake itama ta samu admission a BUK din amma ita computer ne ma to ita a new campus tke....
💍 *AL_HUBB* 💍

The love 💘

By Aysha b. Naseer
Episode 17 & 18: Stranger


Ranar litinin da safe ta sauka a nigeria, bayan goma ta arziki da Anty hawwern ta hadata dashi dan seda ta hadawa kowa tsarabarshi a gidan sanann itama Zee nata daban ma.... Hakama Abban nihal ya karbi acct numberta gun Anty hawwer ya tura mata kudade,,, bawai dan Abbah jabir ya gaza ba sai dan basaso taji kamar itadin marainiya ce ta nemi wani abu ta rasa kuma ta kasa samun wanda zata tmbya
Hutawa tai a ranar litinin din ta kuma rabawa kowa tashi tsarabar, kashegari talata kuma zata koma school, saida ta tabbatr ta kimtsa komi nata, ta duba timetable din da aka turo dazu a watsapp group dan rabonta da watsapp tun barinta Nigeria,, karfe 8 ne lectures din goben, kuma Classrep. Ya tabbatr malamin zezo kuma yayi gargadi da zuwa a makare dan malamin bayaso,
Ganin lecturen biochemistry ne yasa bata wani damu ba tunda already ta karantashi sosai abinda ya rage kawai taje taji sabon lectures din malamin shikuma ta kara da nata ilimin dan wannan semestern bazata saka wasa ba

Abinda Zee take gudu shine ya faru dan kuwa ta makara hakan yasa taketa zabga sauri gashi sai kiranta hudiyya (course mate dinta, saboda yanxu lecturen su ya rabu da zeena) take tana jaddada mata malamin fa ya shiga cikin aji... Karfe 8:40 (2hrs lecture ne 8 to 10am) aka sauke ta ta karasa bakin kofar lecture theatre din mai dauke da mazaunan dalibai kusan dari biyu... Zee ta chanja akalarta zuwa siririyar kofar dake ta bayan theatre din dan ganinta inta shiga ta baya zepi mata sirri dukkuwa da sanin datai malamin nasu me lecture yau bai son makara kuma idanun dalibai du kanta zasu dawo kuma sits din gaba duka tasan an cikesu, da wannan tinani nata tabi ta kofar baya, lecture hall ne me kama da class ba irin sauran theatre dakeda bene ba, sanda Zee ta shiga malamin yanata bayaninshi kamar be lura da shigowarta ba hakan yasaka ta zama daga baya baya sit na biyun karshe inda ta hangi space ta fada gudun kada malamin hankalinshi ya kawo kanta, maida hankali tai ga lecture din da malamin keyi saidai addababben kamshin turarenshi ya debi hankalinta, ta dan lumshe ido tana mamaki wai namiji da Arabian perfume, dan ko bata juya ba tasan namiji ne, tanason Arabian perfumes musamman in tai mixing da humra, A nashi bangaren shima, yajiyo sanyayyen kamshin turarukan datai mixing dukkuwa daba masu tashi ne sosai ba, yanason kamshin nan dayakeji na tashi a jikinta, a hankali ta dan waiga hannun ta na hagu inda saurayin ke zaune, sanye yake cikin yard mai laushi da saukin nauyi, fari kar kafafunshi rufe cikin bakin takalmi, hannunshi dake kan teburin ta kalla ya'daura bakin agogo yatsuntsi kuma biyu sanye da azurfa sai sheqi suke, daga ido tai dan son ganin fuskarshi kadan ta saci kallonshi amma sai taga batasan fuskarshi ba cikin en department dinsu ta basar ta cigaba da jin lecture din dukda a baya take amma tanaji, shima a nashi bangaren ya dan saci kallonta,, ba fara bace kuma ba baqa bace kuma tapi chocolate haske, somehow sandy complexion, "she's cool" ya fada a ranshi..... Babu zato balle tsammani malamin ya nuno Zee yana mai cillo mata tmbya
"Explain all dat i hav explain" hakan dayayi ya tabbatr yaga sanda ta shigo, dan haka yakeyiwa duk wani makararren daya shigo ajinshi a karshe, idan baka iya ba kuma ya disga ka
Zee ta miqe ta soma jawabi wanda yasa duka ajin juyowa gareta amma sam malamin yace shi bejin me take fadi tafito waje, with her full confidence ta fita fuskarta babu yabo babu fallasa kuma babu ko digon tsoro a fuskarta dan taga alamar malamin dan rainin hankli,
Bayan ta daidaita tsaiwarta ne ta fuskanci class din ta soma da fadin "good morning class" dukka aka zuba mata na mujiya da mamakin harda wata gaisuwa ma, sai ta fara bayanin CHO (carbohydrate) din kamar yadda yace tayi
Tun daga bayanin mene shi carbohydrates ta fara wanda bata nan ma sanda yayi sannan ta cigaba da bayani kan CHO (carbohydrate) din amfaninsu na main source of energy for all living organism sannan ta dora da structural component na CHO da inda ake samunshi kamr a structure na DNA da kuma plant cells (cellullose)
Ta cigaba da fadin CHO contains mainly carbon, hydrogen and oxygen atom (C-carbon, H-hydrogen, O-oxygen atom) sannan ta fadi molar ratio din da ake samun atoms din wato 1:2:1 ma'ana carbon 1 hydrogen 2 Oxygen 1,
Ta cigaba da bayanin types na CHO, sune mono-saccride, Di-saccharide, oligo-saccharide and poly-saccharide
Zee ta dora da fasa musu me ake nupi da shi saccharide, which comes from a greek word for SUGAR
Ta cigaba da fadin "let look at each types of dis carbohydrate, their structure and their formation,
Ajin ya sakeyin tsit saboda jin lecturen nata so intresting, yadda take baje bayani dalla dalla yadda kwakwalwar kowannensu zata dauka
Zee ta karasa ta dauki marker, dake jikin white board din nasu, ta soma rubutu, shi kanshi malamin kallonta kurun yake
Monosaccride ta rubuta as a heading
Sannan ta juyo ta kallesu tana musu bayanin shi monosaccride a matsayin simple sugar, kuma smallest unit dat make up any CHO
Sannan ta juya ga allon ta soma zana structures guda uku a kasan kowanne structure ta rubuta sunansu, Glucose, Galactose and fructose ta juya tana cigaba da musu bayanin kowanne CHO (carbohydrate)
Sanda takai gurin fructose sannan maalamin ya tsaida ita dan yaga battada niyyar tsayawa,
Aikuwa nan da nan ajin da dauki tapi ana shewa ana ihu, wani kasaitaccen murmushi ya bayyana a fuskar Zee wanda ya bayyaanar da asalin kyawunta,
Saida malamin ya tsawatar sannan ajin akai shiru, yace "wats ur name" Zee tace "Zainab muhammad sir"
Dalibai suka dauka zainab zainab zainab, yanxun ma saida malamin ya sake tsawatarwa, sanann ya kalli Zee yace "u earn 5marks u really impress me i must say"
Cikin jin dadi Zee tace thank you sir, sanann yace ta koma sit dinta
Kusa dashi ta koma, a nashi bangaren shima kamar yadda Zee ta birge kowa shima din hakanne, tazauna tana mai saita numfashinta dan ita kanta tasan ba karamin kokari tai ba, A haka har aka tashi a lecturen,
Abinda Zee tai ya saka da yawan daliban suke magana da ita duk inda suka ganta sukan gaisa both mata da mazansu, har wasu ke ce mata 'kwaruwa....
Sai yamma Zee ta shigo gidan itada zakiyya da suka biya newsite suka dakkota tun daga parking lot din suke ganin ana fito da kayan furnitures, zee ta kalli zakiyya, "yau kuma mene ke faruwa a gidan, kamar kayan Anty siyama nake gani", zakiyya tace "Au ashe ke fa bakya nan bakisan me ya faru ba" kedai yanxu mu shiga mu huta tukun zan baki labari... Gidan a dan hautsine suka sameshi, zee ta kai jakarta daki ta hau sama dakin Anty siyama, saidai tun kan ta karasa ta jiyo hayaniyar hirar su Anty siyaman da autarsu *Minnatullahi*
Zee ta karasa falourn inda ta tarar du an kwashe kayan ciki hatta carpet da electronics, kujeru ne kawai ba'a dauke ba, Zee ta gaidasu duka su biyun suka Amsa, dan minnatun ma ta girmeta da kusan shekaru 4,
Sai bayan sallar magriba, zakiyya ta shigo dakinsu Zee, Zainab na kokarin fita daga dakin sukai kacibus, dan kusan duk yaran gidan suna babban falour,
Zee tace "ai yanxu gurinki nake shirin zuwa na dauka ma ko kina falour ne",
Zama zakiyya tai, kedai zauna kiji labari, itama zee ta zauna,
"ai bayan tapiyarki ko ince daf da zaki dawo nan, ranar Anty siyama bata dade da dawowa ba, mukaji sunata rigima da umman halipa, wai Abbah yace kar ta sake ta raaba mishi gida, mamanmu ma data dawo tace itama yace ta sake jaddada mata tunda ta dena daukar wayarshi, se a gurin ya_kubra nakejin abinda ke faruwa wai ashe abban Anty siyama ne, ya gina mata wani gida mai kyau, itace tace mai ta gaji da zama gidan yawa" Zee tace "to yanxu babu izinin Abbahjabir zata koma gidan?" Zakiyya tai dariya
"Inafa ya rigada ya yarda dan baze iya ja da sirikinshi ba, kinsan fa dama a yadda mukaji ba wani son Abbah take ba, Abbanta ne ya bashi daya nema, su kuma a gidansu dama shine ke zabawa kowacce 'ya mijin da zata aura, kuma mutun ne dake spoiling yaranshi in suka mai biyayya, dan abinda yapi gida ma ze siya mata tunda ta auri zabinshi" Zee tace "Allah mai iko, kowa da nashi tsarin rayuwar"... "Eh fa kuma har kayan daki du ze chanja mata, kuma ance wlhy gidan me kyau ne irin tsarin en gayu dan harda wallpaper ya saka mata bayaga aircorn gashi ya kubrah tace solar ma ake hadawa yanxu da tuni ta tare" zee ta rike haba, "kice yanada kudi" Zakiyya tace "sosai ma, dukda yanxu duk ya rabawa yaranshi maza kasuwancinshi, kuma yanada manyan mutaane a kasar nan, saidai shi baya zuwa neman aure ma 'yarshi, saidai gidan maza suzo shikuma idan ya yaba da hankalin mutun se ya aura mai"......
Weekend ya kama ranar tarewar Anty siyama a sabon gidan nata, dan hatta kayan sakawarta ta gama hadawa kuma kowa yasan tareda zee zata tapi tunda a gurinta take, hakan yasa itama ta kintsa komi, rakiya sosai akayi musu kowa yaje gidan sai sambarka...
Duk gidan babu wanda zee ke jimamin rabuwa da kamar Zakiyyan, tapi shaquwa da ita fiyeda kowa a gidan, gashi dama basu wani shaqu da Anty siyaman ba, iyakaci ta sakata aiki ne itakuma tayi shikkenan danma aikin gidan beda yawa tunda an dauke wanke wanke da wanki da kuma sauran ayyukan da mai aikin takeyi,
Zakiyya, khairi kubra da Zee kurun aka bari sunata sake kallan gidan sunce sai magariba zasu dawo, sauran yara kau du an maidasu da iyayensu, iyakacin dangin Anty siyama ne kurun a gidan suma din daga Minnatu autarsu se ya Hibba wacce ke tsakanin Minnatu da Anty siyama amma ita mamanta daban dasu,
Zakiyya da Zee suna kitchen Anty ta sakasu hada musu abinci da drinks,
Zakiyya tace "yanxu zee babu ruwanki da hayaniyar gidanmu kinji dadinki, saidai abinda ban gane ba tayaya Duk girman gidan nan Anty siyama bata dauki mai aiki ba....
Bata ida zancenta ba, khairi ta fado kitchen din tana dariya-dariya kadan, Zee da Zakiyya du suka zuba mata ido, ta matso tsakiyarsu da sauri, ta soma magana a hankali
"Kunsan me na jiyo yanxu naje zan shiga dakin Anty siyama na mata sallama?"
Duk suka girgiza kai "wai ciki ne da ita na wata hudu da satika,. Se qanwarta tace meze hana ta dauko er aiki tunda gidan da girma kunsan me tace?" Suka sake girgiza kai suna kallanta "wai ai baga zee ba budurwa mene amfaninta, kuma ita batta son kazantar en aiki wai gwamma dai ke din" khairi ta ida tana kallan zee din, har cikin ran zee bataji dadin furucin da khairi tace Anty tayi a kanta dinba, me hakan ke nupi?....

Anty siyama bata bar su Kubra sun tapi ba saida suka gyara gidan tsaf, sannan suka tapi, ya Hibba ma ta tapi sai minnatu aka bari wacce ba yau din zata tapi ba, gidan Anty siyama dan kyau kam yayi kyau,
Gidane mai babban falour bayan driven, a cikin falour akwai dakuna hudu amma daya babu kaya a rufe yake, sai fantameman kitchen daga baya haka amma ta cikin falourn akwai kofa, sai kuma bandaki a falour da kuma cikin dakuna biyu, daki daya mai bandaki Anty siyama ta dauka ta barwa zee dayan....


Su Zee suka wayi garin ranar lahadi cikin koshin lpia a sabon gidan Anty, dama tun sanda tai sallar Asubahi bata koma ba tana kan daddumar, da misalin karfe 8 na safe Anty ta kwankwasa dakin da zee take, ta tashi taje ta bude mata dukda bata saka key ba, Anty ta shigo dakin , zee kuma ta gaidata da fadin "An tashi lpia, ta gyada kai kurun sannan tace
"Kinga yau i need something early for breakfast, pls" Zee da tasan Antyn na halin laulayi ne tace me za'a dafa Anty?"
"For now ko sandwich ma will be okay, ki duba akwai duk abin bukata a kitchen and pls ki hadomin da coffee" zee ta gyada kai kurun,
Mintuna marasa yawa zee ta dauka ta kammala hada sandwich din mai sauki na bread da minced meat da cheese, sai kuma cup of coffee din, zee bata hada da kanta ba dan ba al'adarta bace shan coffee da safe,
Dakin Anty ta nupa ta kwankwasa, aka bata izinin shiga da yes, ta tura kofar,, kafafunta suka luma cikin foot mat mai laushi dake shimfide a bakin kofar dakin,
Minnatu na kwance kan gadon daga can cikin dakin itakuma Anty na zaune kan cushions din da aka jera cikin dakin, zee ta karasa ta aje mata a kan glass center table din mulmulalle mai kyau sannan tace "gashi Anty", sannu shine amsar Anty sannan ta dora
"Kinga naga falourn yayi kura dan share ki goge" zee tace to ta fita ta hau aiki, ba laipi yana da fadi falourn dukda set daya na kujeru ne cikinsa amma akwai wahalar shara ga bangaren dining, abu kamar wasa haka Anty tai ta saka zee aiki ita ko sedai tace to, itace ta musu komi a gidan
Yanxu haka ma girkin abincin rana ta sauke, babu komi cikinta sai tea data dan kurba da biscuit, tayi serving kanta nata abincin ta bar musu nasu a warmers dan Anty bacci ma take minnatu kuma na wanka, karfe 5 na la'asar minnatu ta kammala duka shirinta ta dubi Anty dake zaune kan cushion din dakin ta miqe kafa,
"Gaskiya girkin dazu yayi dadi, ke kam anty kin samu cook a bagas"
Anty tai murmushi "tsuntsu ne daga sama gashasshe Allah ya aikon"
duka suka saka dariya...
Minnatu ta kammala nata shirin itama ta tapi, Sanda zee sukai waya da Anty hawwer ta sanar mata duk abinda ke faruwa cikin gidan
Haquri shine abinda Anty hawwer ta bata da fadin "kiyi mata biyayya Zee karki sake ki nuna mata wani abu dan in kinyi mata ba faduwa kikai ba, ki bari ku rabu lpia dan ko kinyi mata rashin kunya ma babu abinda ze kareku daga ke har ita"
Wanke_wanke, Shara, goge goge a takaice duka ayyukan gidan zee keyinsu, wanki ne kurun Anty keyin abinta a washing machine
Ranar litinin ma saida zee taiwa Anty aikin gidan sannan tayi nata shirin na makaranta, saukinta ma tapiyar ita kadaice kuma yanxu a sharada suke dukda akwai er tazara amma ba kamar daa da suke darmanawa ba,
Dayake lecturenta na yau ma safe ne amma practical C.O dinta ne
Ta dora labcoat kan kayanta ta shiga lab din, bayan sun kammala practical dinne ta fito ta nemi wayar zeena,
Kina ina? Ta tmbya zeena tace ina class amma lecturer'n ma bezo ba da alaama bazezo ba,
okay zee ta fadi
Sannnan ta nemi layin hudiyya, hudiyya ta dauka tana fadin "zee ina kika shiga ne" ta fada muryarta kasa kasa alamun bataso ajita
Zee tace kardai akwai lecture hudiyya tace "eh mana munada embryo mana tun 9 ya shiga yanxu saura 1hr ya gama" ganinan to....

Tai tsaye a bakin kofar ajin tana jimamin shiga, kofa daya ce da class din kuma ta gaba babu yadda zata shigaa ba'a ganta ba kuma dole ta gaban malamin zatabi,
Wannan gaurayayyen arabian scent ya daki nostrils dinta lokacin iska ta kado zee ta juya gefen hannun damanta inda ta hangeshi yana cigaba da tahowa iska na karkada gyalenta da kayanta suna yawo, he's dressed in a pure white male Nigerian kaftan well ironed, walking majestically, his right hand buried in his pocket...
Ganin da tayi yana nufo inda take yasata saurin dauke idanunta daga kallon datake mishi, ya karaso yana mai shafa beard dinshi da gyaran murya, zee ta daga kanta tana sake maida kwayar idanunta kanshi a karo na biyu,
Cikin cracky voice

Please Login or Register in order to submit comment