Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

be rage ta da komai ba infact he likes her tun a farkon ganinta dashi sae dae ita zuciya tana son mai kyautata mata, she already wiped all the love,

Gobe ake saka ran yallabai ze dawo kasar dan haka sae goben zeje gidan, ya san kuma dole yallabai bayanshi zebi, yayi murmushi, a bangaren mint tunda taji labarin dawowar yallabai a gobe ta hada ya nata ya nata ta komo gidan yusuf ta sani sarae beson lepin danshi Allah yasa randa ce da ita ba ciki ba, babu abinda ya mai zapi indae kan yusuf ne

Yana wanka ta shigo gidan dan fita ma zeyi, ta je ta ajiye kayanta sanna ta dawo bangarenshi lokacin ya gama shiri, ya tsaya yana kallonta ta taho gurinshi tana murmushi ya tabe baki ya dau turarenshi ya soma fesawa, tayi hugging dinshi ta amshi turaren ta ajiye ta soma shafar sumar kanshi, im back ta fada yace u're welcome, sae ta bashi takardar dake hannunta, ya karba yana dubawa at once kuma ya mance da komai yana mai bayyanar da faffadan murmushi, "are u serious?" Four month pregnant? Tayi nodding with a smile,
Ya yi hugging nata da kyau yana godiya ga Allah, masha Allah, ya xaunar da ita yana matsa kafarta... Da yallabai ya dawo kasar da kanshi yaje yayi mai Albishir zo kuga bakinciki karara a fuskar mafi yawan mutan gidan, shikuwa yallabai ya mata kyautar kujerar makkah guda biyar sannan a take ya zuba mata 5mil a acct. Ranar mint taga gata,

Dadi ya isheta ta rikice jin uban kudaden da aka zuba mata a acct., tun daga nan mint ta dinga rashin mutunci a gidan, kuma duk abinta kan zee yake karewa ko zee tapi mai kaulayin shan wahalar cikin wasu abubuwan kuma duk mint tana sane duka dan ta kuntatawa zee dinne se kace ba itace ta nemi tazo gidan ba, se zee ta dafa abinci kala shida mint tana cewa beyi mata ba, amma baiwar Allah bata nuna mata ta damu, dukkuwa da takanji babu dadi
Inma sharar dakine sae ta hana kowa shigowa ta dage se zee ce zatai mata, har tausa take mata amma batayi a gaban yusuf se baya gidan, a haka cikin mint yayi ta girma zama da kyar tashi da kyar, addu'a kuwa sosae yusuf ya dage da ita yakuma tilastawa mint yinta dan sanin yawan makiyan dake harin wannan cikin, kujerun makkan da yallabai ya bata kuwa tuni ta rabarma yan uwanta tana fadi wai ita matar billionaire, sanda lokacin haihuwar yayi ta saka aka gayyato wani mashahurin likita daga india yayi mata c.s ya fidda babynta katuwa mace, zokuga farinciki gun yusuf sae hamdala yake wa ubangiji akwae shi da son yara sosae...

Wannan yarinya tasha gata ko iya towel din da aka sakata a ciki ma ihun kudi yake, tasan tazo gidan dukiya, akayi suna aka sakamata sunan mami, (Asma'ul Husner) suna ce mata Husner

Gurin momy mint ta koma tayi wankan jego, abu daya da suka lura dashi shine yadda babyn batada ishasshiyar lpia musamman zainab da itace ta kasance mai raino dan ko yaushe Husner na gurinta indae mint ta karbeta to abinci zata bata...


Na kusa tsayawa da typing dan bana jin ruwan comment, se ku karanta kuyi mukus 😡 nima kuwa zakujini tsit, my wattpad people is it dat had to vote and comment?
💍 *AL_HUBB* 💍

The love 💘

By Aysha b. Naseer
Episode 09 : Selfish

Gabadaya a gidan momy t zauna har tayi arba'in kuma tace lallai zee ce meyi mata raino, hakan yasa yusuf kusan koyaushe yana gidan, dan babu yadda za'ai zee tai nisa dashi kodan cikinshi,,,, Bayan Arba'in dinne ta shirya zuwa kano gidan iyaye da enuwanta, yusuf yace ze hadata da ma'aikatan momy amma zee bazata bita ba, ta kama hanya kuwa ta tapi abinta, a ranar ne ta saka atampa, akayi mata hoto (its on wattpad)

Saeda ta shafe satika biyu sannan ta dawo, amma da ganinta kasan akwae matsala, ta koma shiru shiru gabadaya, tun data dawo ta hana kowa taba husner, ita kadae ke hidima da ita, daga karshe ma tace ma yusuf zata ajiye aikinta sae husner tayi wayau, shi kuma bawan Allah zokuga murna gurinshi, hakan ya tado da tsohuwar soyayyarta a ranshi da ta danyi saura, zama suke najin dadi sosae duk son duniya ya kwallafa shi kan husner dukda ba zama yake a gidan bama, idan ya dawo kuma mafi yawan lokuta tana bacci ne abinta

Rannan yusuf baya a gidan daga mint sae zee,,, zee tazo wucewa ta hanyar falourn mint taji kamar kuka, ta danyi knocking sannan ta shiga tana daki tana kuka tana fadin
"Dan Allah doctor Raghav ka kara rufamin asiri yadda besan zancen nan ba tun a farko karka fasa kwae, im trying my best na ganin na boye, i can't afford loosing Assiddique, im his one and only wife the mother of his kids"......
Zee ta shiga thinking, me hakan ke nupi mint tayi wani abu?
Har dare tunanin abu daya ne a ran zee "tasan babu yadda za'ayi mint ta ajiye aikinta kawae dan ta kula da husner dole akwae wani boyayyan al'amari amma me yayi zapi da har zesa yusuf ya rabu da ita,,,,
Tun daga ranar kuma zee ta soma lura da abubuwan mint, se lokacin ta lura duk kusan kwana biyu sae ta fita ita da husner amma basu dadewa suke dawowa shiyasa ma batasan tana fitar ba tunda kowa da nashi part din,
Wata ranar lahadi da dare, mint da husner sunyi bacci yusuf yana zaune yana yaba chanji da mint tayi a ranshi, zee kuma tana serving dinner dinshi aka kira wayarshi, yayi picking tunda yayi sallamar farko be sake tofawa ba, ya kuma nutssu ya maida hankaali kan bayanin da ake mishi, bayan ya ajiye wayar ne ya miqe yana zirga_zirga a falourn

Zainab ta tsaya tana kallonshi, "meke faruwa haka" tasan ba karamin abu ne ze tadashi daga gaban abinci ba, sun jima a haka yana kaiwa yana kawowa daga baya kuma yace ta tashi taje, ta fita tana wondering what's wrong,

Kashegari da wuri ya fita, yau zee tai shirin bin mint a baya dan ta sa a ranta sae taga inda take zuwa, tana da kudi a hannunta dan haka bata wani damu ba, bayan mint ta fita itama ta shiga napep ta bita a baya, asibitin da take aiki taje, zee ta tsaya a compound din tana kallon mint dake shiga cikin asibitin, ta saka kafa zata fita a napep.din kenan motocinshi suka shigo guda uku, dan ko a maafarki babu abinda ze hanata sheda motocin yusf, ranshi kamr a bace bema jira driver yayi kyakkyawan parking ba ya fito ranshi na suya, ya shiga a fusace, ganin a yadda ya shiga yasa zee fitowa ta sallami mai nepep ta kama hanyar shiga ciki da hanzari,

Mint na office din dr. Suraj ya shigo yana huci, ta miqe ba tareda aanyi wani furuci ba ruwan hawaye suka soma ambaliya a fuskarta, daedae nan zee ta karaso har tana haki amma ta tsaya daga dan nesa yadda zatana ganin komi,
A hankali ya juya jin kamar motsi suka hada ido da zee ta lumshe mishi ido da sigar rarrashi dukkuwa da batasan me mint din tayi ba, ita mint dake ciki da dr. Basu lura da zee ba, duk fushin daya taho dashi dayake tunanin ze iya shaqe mint a lokaci daya ya kaita barzahu yaji yana cooling, yayi folding hannayenshi biyu a kirji yana kallonta, ya furzar da iska waje ya girgiza kai kawae ya fita, zee ta bishi da sauri,
Mint kuma ta tsaya inda take cikin rashin kwarin gwiwar binshi,

Gida suka koma zee tana ta biye dashi har ya karasa falournshi na kasa ya zauna kan kujerar ya cire hular kanshi ta dafe kan nashi, zee ta tsugunna a gefenshi itama tai tagumi, sun dade a hakan
"she's selfish" furucinshi ya sata kallonshi, mint is a selfish woman" kawae sae hawaye suka zubo mishi, wayarshi ce tai kara yaga yallabai ne ke kiranshi ya tabbatr labari yaje kunnenshi ne, ya daga da fadin barka da warhaka, yallabai yace "Anwar divorce her, bazata zauna cikin zuri'a ta ba, THIS IS NOT A MISTAKE" ya katse wayar, yusuf ya ajiye wayar yana jimami, mint cee ta shigo a rikirkice ta karasa gaban yusuf tayi kneeling fuskarta da hawaye, pls don't divorce me, pls yusuf duk abinda nayi saboda ina sonka ne" ya girgiza kai, "no kina son kanki dae" ta hadiyi daci a makogwaronta, idan yusuf ya sake ta itakam ta kade,
"Menene wannan innocent child din tayi miki, now its all over mint" ya fada yana wucewa ciki, bata bishi ba sae ta dubi zainab dake zaune tana kallonsu kanta a kulle da tmbyoyi fal ranta, "zainab pls ki bashi haquri ki tayani bashi haquri" zainab tayi nodding tana tashi itama ta wuce

Kwnaki biyu suka shude gidan nan a birkice yake kowa hankalinshi be jikinshi, gashi yallabai ya takura sae yusuf ya saki mint, zee kuma duk tabi ta damu, gashi batasan mene ya faru ba batakuma san wa zata tunkara ya mata bayani ba, damuwarta kuma yadda be tmbyar ta girka mishi abinci ta sani kuma ba ci yake ba saedae yasha tea kawai, ta miqe yau kam se taji mene ya faru, falournshi na sama da qasa duk be nan kuma tasan be fita ba tunda ga securities ga motoci a gida, wannan bolcony din ta karasa hoping ta saameshi a can, aikuwa ta sameshi din yana zaune ya tsurawa flowers din gurin ido, ta ja kujera ta zauna kusa dashi, barka da warhaka ya dan juyo ya kalleta sannan ya dauke kai, ya ciji lower lip dinshi, tace "bana ganin husner a gidan nan" kawae sae hawaye suka gangaro daga idanunshi, ya miqe tsaye kamar ta kunna shi ya soma bayani
"Banyi sa'ar mace ba zainab, do u know what she did?" Zee ta girgiza kai jiki a sanyaye " she killed my innocent poor child husner is gone kukan ya kwace mishi, kawae sae ta fara hawaye itama, musamamn data tuna irin son dayakewa husner, ko ita mint din darajar husner takeci duk wasu shegantakarta yana daga mata kafa
Idanunshi jajawur ya girgiza kai, nagaji da haquri zainab, wadanda suka kulla auren sunce na warware" zee tace "say it say it all
Ya soma mata bayani kamar haka "ina zaune abina, yallabai yaa kirani yace ya samamin matar da zan aura he'll sent her pics, tunda ake kawomin proposal na aure yallabai be taba hadani da kowa ba, and he specifically told me "Anwar she's beautiful u'll love her"
Wannan shine kuskuren da nayi na biyewa yallabai da kyawunta ya rudeshi, ba tareda dogon bincike ba dukkuwa da yallabai yasan gidansu gidan mutunci ne amma karin bincike kan halayyarta ma nada muhimmanci tunda itace zan zauna da ita, i accepted the proposal, because i love that man, yes i love my dad i can never turn his proposal down, yana turamin picture dinta from the first glimpse nayi realizing she's a beauty, she's beautiful naji a raina irin matar daya dace na aura kenan, komi na biki ya cigaba da gudana nida ita bamu taba ko magana ba dan bana kasar a lokacin, kafin a tsaida rana yallabai ya nemi ayi genotype saboda yasan ni AS ne bayan tayi nata sukayi presenting result kuma aka tabbatr she's AA pattern.... babu dadewa aka tsaida rana aka soma shirin biki, ranar da suka shirya event din kamu a kano shine ranar dana fara ganinta, se naga ai hoto ma karya yayi min, she's beyond all my expectation and that made me felt so excited,,,, i feel relaxed knowing that i got a wife, and now do you know what happen?, she lied her genotype is not AA pattern its AS she tempered with the result as she's a medical doctor" ya sunkui da kanshi, a hankali zee ta soma bitar maganganunshi
" kenan hakan na nupin husner is a sickle cell baby?" Ya gyada kai, and the worst part of it shine ta sani since from day 1, amma taki fada sae da jikin ya fara tsanani ta nemi hutu ta zauna a gida, tana kaita asibiti ana dubata, kuma ta sani sarae ba abinda yankamata ayi kenan ba, she need proper treatment, that poor baby has been seriously sick, and at last she's in comma, even the doctors gave up"
Zee taji wani hawaye me daci ya zubo mata how could a mother do this, for her selfish reasons? Oh Allah its so bad, har haka takeso sunanta ya ra'bu dana Assidique, all she cares is fame, money in short worldly attachments

Ranar zee da kyar tayi bacci da ta fara sae taga fuskar husner sanda tana jinjira sosae, the baby is cute
💍 *AL_HUBB* 💍

The love 💘

By Aysha b. Naseer
Episode 10: RIP



Kashegari husner tace ga garinku nan, rae yayi halinsa, aka fito da ita daga cikin na'urorin, aka kaita gidan yallabai, tunda yusuf yaji labarin gawar husner na gidan yallabai yaqi koda motsawa, labarin rasuwar husner ya shiga ko ina cikin dangi amma babu wanda yasan cewar SS ce,

Yayi karfin halin shiryawa, mint kuwa tana daki ko falour bazata iya fitowa ba, zainab kuma tana ta kaiwa da komowa a falournta, tunda taji labarin gawar husner na gidan yallabai taketa leqa motocin yusuf ko ze fita amma shiru kakeji, kmr a mafarko taji an tadasu tasan ya kusa fitowa kenan, tai saurin daukan gyalenta dama a shirye take ta sauka da sauri, ta karasa gun motocin taja ta tsaya itada sauran securities suna jiran fitowarshi, kamar walkiya se gashi ya fito, fuskarshi ba a hade ba kuma ba a sake can ba, saeda zee taga motar daya shiga itama tayi wuf ta shige, bece mata komai ba suka soma tapiya, a hankali tace "ya haqurinmu" ya gyada kai kawae,
Tana kallon titi tace " Allah yasa mai ceto ce" sae lokacin ya amsa da Amin"
A haka suka karasa jefi jefi zainab na yiwa husner addu'a wanan yasa zuciyar yusuf tayi calming dama abinda take buqata kenan... Suna isa ta koma bangaren momy ko ina jama'a ne, akayi mata sallah sanannn aka miqata gidanta na gaskiya...Sae yamma likis ya kira zee yace ta fito su koma gida

Wanna karan ma motar dayake ciki ya shiga, suna tapiya zee tace "forgive her" kamar ta yanki naman jikinshi yayi mata wani kallo, "pls badan ita ba saboda Allah, dukkanmu mutane ne, we all make mistakes, im sure she learned from her mistake, kuma abinda yake a rubuce baze chanja ba, Allah yayi husner ba me zama bace, muma kuma duka can zamu tapi duniyar ba gurin zama bace, Allah yana tare da masu haquri, nasan ka fini ilimi kuma ka fini sanin ya kamata bazakayi abinda Allah yake qi ba, abinda al'arshin ubangiji ke girgirza sakamakon shi (saki), please give her another chance" be ce mata komai ba har sukaje gida amma yana juya maganganunta a ranshi, bayan sun shiga ne yace ta sama mishi fruits, tace to, ya shiga ya samu kujera ya zauna yana huce gajiya,
Idanunshi a lumshe suke hakan yasa besan da shigowarta ba se kama kafarshi datai yaji, ya bude idanunshi, "please Anwar im sorry, ka dubi girman Allah kayi haquri, wlh nayi kuskure" ya zuba mata ido, she's crying ya ayyana a ranshi, hawayenta suka cigaba da zuba tana rokonshi da Allah karya saketa, zee ta karaso rikeda fruits din ta ajiye gefenshi sannan ta d'aga mint ta zaunar da ita kan kujerar gefenshi.ta fita ta basu guri tana fatan zeyi considering magananta karya saki mint

Wayarshi ya saka ya kira yallabai ya saka a speaker, bayan sunyi gaishe gaishe yusuf yace "yallabai ta bani haquri kuma na haqura yanxu hukunci na hannunka, kaine ka hada, kuma kanada ikon sakani warwarewa" yallabai yace "tunda ka haqura shikkenan amma fa ka sanar mata ni ban haqura ba se na huce tukunna" sukai sallama
mint ta sauka qasa tasaka guiwarta a kasa tana rike hannayenshi cikin kuka tace "nagode mijina nagode,
Yayi shiru be amsata ba ta dago ta dubeshi, sai taga jikinshi ya saki, a hankali yake binta da kallo, sae kuma idanun suka rufe ya fadi dayan side din kujerar, a rikice ta miqe tsaye, ta soma girgiza shi "yusuf, yusuf yuuusuuf"
Kafin kace me zance ya karade ko ina yusuf Assidique ya suma ba'asan mene ke damunshi ba, suna tsaye duka harda zee manyan likitoci nata kaiwa suna komowa, amma sun kasa gane mene ya dameshi
Tunda aka kwantar dashi a asibiti haankalin yallabai ya tashi, kwanaki uku amma babu cigaba dan haka yallabai yace su fita dashi gun dr. Raghav, yallabai ya sanar a sanarwa zee da ita da wani yayanshi zasuje mai suna Abdul, a ranar suka wucee indian an sha fafutuka da kyar suka samu ya farfado, ranar yallabai saeda yayi sadaka sosai, dan ya ajiye komi yana kula da danshi tsoka daya a miya, zainab kuwa a nata bangaren ba karamar tashin hankali ta shiga ba addu'a take babu dare babu rana babu wanda ake bari ya shiga inda yake se yallabai iyakacin ta dashi saedae kallo daga nesa ta glass,
Ranar daya farfado tana tsaye a jikin glass din tana hangenshi ya bude ido yana yatsine fuska dukkan alamu sun nuna bejin dadin jikinshi, ya juya kanshi kenan ya hangeta tana kuka tana goge hawaye, tana dagowa taganshi yana kallonta da idanunshi, tayi gaba da hanzari sae ta buge kai, sae sannan ta tuna ashe glass ne ta koma da baya har suna karo da nurses,

Kwanakinshi biyu komai ya samu sauki sosai, saedae abu daya da doctors suka kasa ganewa shine yadda be magana kuma be responding, amma jikinshi ko ina lpia qalau,
Kwanaki biyar suka diba suna duba kunnenshi amma komai normal har zuwa brain dinshi atlast suka fadama yallabai abinda ake ciki
"Komai nashi is normal, amma bayaji kuma be maidawa ma'ana baya magana, munyi duk iyakacin kokarinmu ganin yayi responding amma shiru kuma mun duba komai a kunnenshi normal ne tun daga external ear har zuwa brain" yallabai ya shiga tashin hankali mai tsanani taya za'ace Assiddique heirs be magana kuma beji, its impossible, ya daukeshi ya chanja mishi asibiti, amma same problem, se ya chanja kasar gabadaya suka koma America sunyi sati anan amma babu wani cigaba,
Saida yallabai ya kusa zagaye kasashen duniya duk gurin neman maganin yusuf amma abu yaci tura, kamar zeyi hauka,
Yusuf da kanshi ya nemi pen and paper ya rubutawa yallabai kamar haka "lets go back home"
A ranar yallabau ya zubda hawaye, "duk dukiyarshi amma ya gaza nemawa dan dayake mafi soyuwa a gareshi magani
Yusuf ya taso yazo inda yake yasa hanky ya goge mishi hawayenshi dan ya gane duk irin zapin da yallabai yake ciki, a haka ya rarrasheshi suka komo gida, duk inda zasuyi kuwa in babu zainab sai yusuf yaja ya tsaya, suka dawo gida amma aka boyewa media batun rashin jinshi da maganarshi,
Da farko yallabai cewa yyi yusuf baze koma gida ba saedae ya bishi amma yusuf ya rubuta mishi cewar ai ga zainab nan zata kula dashi kuma mint ma tana nan sannan idan ya koma gida abin ze zama kamar tonan asiri ne,
Da wannan dalili yallabai ya barshi ya koma gida, amma abin mamaki suna zuwa gidan a ranar mint ta hada kayanta ta karasa gabanshi ta dan doki kirjinshi, "ka zama dutse nikuwa bazan zauna da musaki ba, aji na ya wuce nan"
Zee ta tsaya kamar statue tanajin rashin halacci irin na mint, dukda beji me tace ba amma ya bita da ido har ta fice,
Zainab da kanta ta dakko takarda biro ta rubuta divorce her, har wani huci take bazeyi arguing da zee ba ya rubuta saki daya ma mint, zee ta bita dashi tana Allah wadae da halayyarta, ya zauna a kujerar, kamar dazu daxu ne fa mint tazo ta durqusa tana kuka kar ya saketa, and now, ya gane saboda beda lpia ne yasata tapiya, zee ta shigo ta sameshi yana tunani idanunshi sun kada sunyi jawur, ta dakko paper ta rubuta 'what's wrong' ya karanta sanann ya amshi pen din ya rubuta, "please don't leave me" ruwan hawayenta suka zubo ta rufe fuskarta da tafin hannunta, tana girgiza kanta kamar bazata dena ba, ya dora hannunshi kan nata, ta san zapi da dacin rabuwa dda masoyi, laushin hannunshi dataji kan nata yasata dagowa
Ta sharce hawayen idanunta ta rubuta mishi "in life's trial, in hardship and ease, in sorrow and happiness, i ll accompany you, ubangiji Allah ya baka ikon cin wannan jarabawar", ya dunkule hannunta cikin nashi ya dora kanshi kan hannayen hawaye mai zapi ya zubo mishi

Ayi haquri da wannan
💍 *AL_HUBB* 💍

The love 💘

By Aysha b. Naseer
Episode 11: Faruq

Barrister ne ya amshi wasu ayyukan nashi saura kuma suka koma hannun yallabai, tunda shidae ba yadda za'ae ayi meeting dashi, wannan abu na kara dugunzuma mishi hankali, zee ta lura gabadaya walwalarshi ta ragu sosae duk soyayyarshi da abinci kuwa yana faraci zeji ya fita a kanshi, wani sa'in ma se yaji tmkar ya bar duniyar ya huta, gashi brothers dinshi na kara rura wuta, wajen yawan damunshi da kira dukda be dauka amma abin na bata mai rai, idan be dauka ba kuma se su mishi da tex da ya jikin Allah ya sawwaqe, zainab ta sanar da Anty hawwer duk yadda suke ciki a nan ne ta bata shawarwari gameda abinda zatayi
"Ki kyale duk wata harka ta asibiti, ki tuno karatukan ammi, zan turo miki da zamzam sae mu tsara yadda addu'o'in zasu na tapiya ina fata dae ze yarda" zee tai jinkirin amsawa kamin tace "eh a tunani na dae bazeyi musu ba"
Bayan kwanaki uku kuwa aka turo da zam zam din, da kanta taje ta sanar dashi abinda take kokarin farawa, beyi wani jaa ba ya bata go ahead,

Farko da laqad ja akum ta soma ta tofa mishi gwargwadon yadda zata iya sannan ta karanta suratu ra'ad kafa 7 da niyyar koma mene ke damunshi Allah ya saukaka mishi ya bayyana, ya karbi ruwan data tsiyayo a cup ta miqa mishi yasha da bismillah acikin ranshi, kwanaki bakwae suka jera sunayin wannan, kuma a kwanaki bakwan ta lura walwalarshi ta soma dawowa amma yakan zauna shi daya ya rike newspaper kamar yana karatu amma ba karatun yake ba,

Yauma yana zaune rike da news paper din ta karaso bema san da zuwanta ba ta amshe newspaper din sannan ta bude Al'qur'ani mai girma suratur rahman ta miqa mishi, ya karba ya soma karantawa, ta fita ta kyaleshi yana karatun a zuci, be dena ba seda ya kai nasi, ya kuma ji dadi, sae ya soma istigfari, shikam yaushe rabonshi da bude Al'qur'ani ya ruqe ya karanta shi haka saedae ya saka a audio ya saaurara ko yana mota yace da driver ya saka musu, amma wannan nutsuwar da ladan rikewar da kallar ma ya rasasu, gashi yanxu da beda wani abu dayakeyi ya dauko ya karanta, tabbas d'an adam ba abakin komi yake ba, yanxu gashi ya koma kamar mara amfani, yayi hamdala daya tuno wasu ni'imomin ubangijin...

Yallabai kuwa dayaji maganar tafiyar mint hankalinshi ya tashi dan bazeso taje ta tonawa d'anshi asiri ba, gashi bemaji labarin tapiyar tata ba sai da tai sati da tapiya, ya dau waya ya kira Abbanta, bayan sun gaisa yallabai yake sanar dashi abinda mint tayi, dan da alama ma be sani ba, Abban ta yace "karka damu yallabai in shaa Allah zata dawo, yanxu bana kasar ne shiyasa ma bansan hakan ta faru ba amma idan na dawo zamu ga yadda za'ai"

Next abinda zee tai shine ayatus_shifa da ayatul_rukiya, to dayake sunada yawa yasa ta dan dau lokaci mai tsayi ma tana tofasu, suma kamar wadancan ta bashi yakesha da kadan kadan, rannan sunyi sallar magrib itada shi suna zaune a gurin da aka kebe domin yin sallah cikin falournshi, bayan sun kammala addu'a ne ya juyo ya kalleta ta mishi alama da ya dan dakata da hannunta, ya juyo yana dubanta ya tankwashe kafafunshi, ta dakko Al'qur'anin ta soma rera mishi kira'a, hakan yasata tunawa da Amminta, yayi shiru yana saurarenta

Please Login or Register in order to submit comment