Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

biyani albashi ba indai zan
kasance a kusa da ita ina ganin wannan
kyakkyawar
surar tata zan iya cigaba dayi mata bauta har
izuwa karshen rayuwata"Koda sarauniya Aryala taga
jarumi
damzur ya sunkuyar da kansa kas ya kasa cigaba
da
kallonta sai ta taso daga kan kujerar da take zaune
ta tako har inda yake tsaye ta kama hannunsa.Take
yaji gaba dayan tsigar jikinsa ta tashi,amma sai
yayi
ta maza ya kame.Sarauniya Aryala taja jarumi
Damzur izuwa kan wannan kujera da take zaune ta
zaunar dashi kuma tasa aka zuba ruwan inibi a cikin
kofunan zinare guda biyu masu daraja aka kawo
musu.Kawai sai ta dauki kofi daya ta mikawa
jarumi
Damzur itama ta dauki daya kofin ta kurbi ruwan
inibin sau daya sannan ta umarceshi da shima
yasha.Ba tare da fargabar komai ba kuwa jarumi
Damzur ya kurbi ruwan inibin har sau
biyu.Sarauniya Aryala ta dubeshi cikin murmushi
tace,yakai Babban jarumi abin dogaro na kuma
abin
alfahari na kayi sani cewa daya yau na baka izini na
bani shawara bisa duk abinda kake ganin zai
amfaneni ko zai taimaki masarautata.Kan
a da
izinin
kawo mini ziyara a kowanne lokaci walau
safiya,dare ko rana.Maza ka sanar dani sabon
al'amarin daya
taso yanzu.Koda jarumi Damzur yaji wannan
jawabi
na sarauniya Aryala sai ya kara kamuwa da
tsananin
farinciki bisa amincin data bashi ba tare da fargaba
ko shayin zai iya cutar da ita ba.Jarumi Damzur
yayi gyaran murya ba tare daya dago kansa ba ya
sake duban sarauniya Aryala ba sannan yace ya
shugabata sarki uzaima ne ya canja
tsarin walimar daya shirya tare da sarakai.Yanzu
yace zaiyi walimar ne tare da sarakai da kuma
jaruman gasa a daren yau.Yanzun nan wani
manzonsa yazo ya isar da wannan sako a
garemu.Koda jin wannan batu sai sarauniya Aryala
ta kyalkyale da dariya tace,to saime kuma?ai babu
wani abin damuwa ni hakan ma yafi mini
dadi.Zanyi shiga ta mace jaruma,kuma zan halarci
wannan
walimar da matsayi biyu,ma'ana nice wakiliyar
sarki
sa'ad a matsayin 'yarsa,kuma nice jarumar gasa
daga birnin nurul ansar,kuma kaine mai take mini
baya a duk inda nasa kafata.Koda sarauniya Aryala
tazo nan a jawabinta sai idanun jarumi Damzur
suka
zazzaro ya dubeta cikin alamun matukar tsoro
yace,ya shugabat sarki uzaima ya sanni fa
sosai,yana ganina zai shaidani.Sarauniya Aryala
tayi murmushi tace,ai hakan nakeso ta kasance,idan
yaga cewa jarumin daya kasa kaishi kas ne mai
tsaron lafiya bazai yi mini kallon raini ba kuma
bazai
hanani shiga gasar jarumtaka dashi ba.Amma idan
ya ganni ni kadai kyawuna ne zai ribaceshi kuma ya
kamu da tsananin sona yadda bazai iya barina na
shiga gasar jarumtakar ba.Koda jin wannan batu
sai
jarumi Damzur ya sake dago kai ya dubi sarauniya
Aryala a karo na biyu cikin murmushi yace,ya
shugabata na rantse da gemun ubana ban taba
ganin mace mai basira da hangen nesa kamarki
ba.Kina zartar da al'amuranki kamar wacce take
samun wahayi daga ubangijinta.Sar
auniya Aryala
tayi murmushi tace,shin bakayi mamakin
jarumtakata da kyawuna ba sai mamakin basirata.?
Wannan shine abinda yasa na aminta dakai saboda
kwakwalwarka tana da tunani mai kyau,kuma tana
yanke hukunci mai kyau a lokacin daya dace.Na
sallameka ka tafi izuwa dakinka domin ka huce
gajiyar tafiya sai idan lokacin tafiya wajen walima
yayi kazo mu tafi.Inason kafin kazo kayi gagarumar
shiga ta yaki mai kwarjinin gaske saboda ana son
idan mutum yana da kyau to ya kara da
wanka.Koda
jin haka sai jarumi Damzur yayi murmushi gami da
godiya yace,an gama ya shugabata.Kawai sai ya
mike tsaye ya fice daga cikin turakar
.ΔKΔAΔEEΔRΔΔ ΔΔΔ
Wani Babban daki mai fadi da tsawon gaske a cikin
gidan sarautar wanda zai iya cin mutum dubu
goma
wanda aka kawatashi da kujeru da tebura na
alfarma.
Zan dakata anan:
. By AL MUSTAPHA Isah Inkiya #MUSTINDOO KASUWAR RAYUKA!!!
Littafi na Biyu (2)
Part B
Wani babban daki mai fadi da tsawon gaske,a cikin
gidan sarautar wanda zai iya cin mutum dubu
goma
wanda aka kawatashi da kujeru da tebura na
alfarma,sannan an zuba fitulu masu hasken gaske
birjik!Ba adadi kai kace rana ce alhalin dare
yayi.Akan kowanne dogon tebur na dakin an zuba
kayan ciye ciye da shaye shaye iri iri har da wanda
ma mutum bai taba gani ba.Nama kuwa tsakanin
kaji,zabi,agwagi,talo talo,rago,saniy
a,rakumi da
sauran tsuntsaye kala kala babu wanda babu a
wajen.Wani naman gasasshe ne wani soyayya da
kuma dafaffe wato farfesu.'Ya'yan itatuwa kuwa
dangin su inibi,lemo,ayaba,tuffa,baure,f
asa dabur
babu irin nau'in da babu.Cikin kankanin lokaci
wannan daki ya cika da sarakuna da jaruman gasa
suka kama ciye ciye da shaye shaye.Acan gefe
daya
kuwa wadansu kyawawan 'yan mata ne su goma
sha biyu a cikin shiga iri daya suna sanye da wata
riga mai siffar tsuntsun dawisu suna ta faman tika
rawa don debewa baki kewa,makada sunayi musu
kida mai taushi a cikin bushin wata sarewa mai
zakin gaske da taushi.Komai rashin son kidan
mutum idan yaji wannan bai san sa'adda zai kama
rausayawa ba.Sarki Uzaima ne ya fara halartar
wannan dakin walima,kuma tunda ya shige yaje ya
zauna a gaban wani katon tebur dake can sama
bisa
wani gini mai tudu dauke da mattakala inda duk
wanda ya shigo cikin dakin shi zai fara
hangowa.Duk
sarkin daya shigo sai a kaishi can inda sarki
Uzaima
ke zaune su gaisa,dama akwai kujeru da zai zauna
an tanada a kewayen inda sarki Uzaima
yake.Tunda
aka fara shigowa cikin dakin sarki Uzaima ya kasa
ya tsare,ma'ana yasa idanunsa akan bakin kofar
shigowa kawai jira yake yaga mace jaruma ta
shigo
yaga kalarta da siffarta,kuma sannan yasa ido
yaga
yadda sarki sa'ad na birnin nurul ansar zai shigo
tunda bashi lafiya wata kila saidai a daukoshi akan
karaga.Saida gaba dayan sarakai da jaruman gasa
suka gama shigowa amma sarki sa'ad baiga
shigowar sarki sa'ad da bakuwar jarumar da zata
fafata gasar jarumtaka wacce tazo daga birnin
sarki
sa'ad din,wato birnin nurul ansar.Al'amarin dayai
matukar bashi mamaki kenan ya fara tunanin ko
ciwon sarki sa'ad ne ya tsananta shi yasa basu
shigo ba.Har sarki Uzaima ya kirawo wani hadimi
nasa zai turashi izuwa can masaukin sarki sa'ad
domin ya gano halin da ake ciki,kawai sai jama'a
sukaji an buga tambari na musamman irin wanda
ba'a taba jin mai dadin sautinsa ba.Kwatsam!Sai
ga
Sarauniya Aryala ta shigo cikin dakin taron.A
wannan lokaci sarauniya Aryala ta caba ado na
gasken gaske.Tana sanye da wata koriyar riga
doguwa wacce akayi ta da siffar fure.Rigar ta
dame
jikinta dukkan surorin jikinta sun bayyana a
fili.Gashin kanta an tattareshi an daure a baya da
wani abun ado mai siffar kwaron malam buda
mana
littafi,shima kalar kore ne.Kai!Hatta sarka,dan
kunne
da awarwaron dake hannunta na zinare koraye
ne,haka ma takalmin dake kafarta duk koraye
ne.Hakika shigar tayi mata tsananin kyau,kuma
sai
kyawunta da kyawun surar jikinta suka kara
haskaka
kyan nata.Jarumi Damzur na biye da ita a baya
cikin gagarumar shigar kayan yaki,kuma shima
garkuwarsa,kufen takobinsa da duk launin abinda
ke
jikinsa kore ne abin gwanin ban sha'awa.Da
shigowar sarauniya Aryala da jarumi Damzur cikin
wannan dakin walima sai gaba dayan jama'ar dake
cikin dakin taron suka mike tsaye cikin kaduwa da
tsananin mamaki,ciki kuwa har dashi kansa sarki
Uzaima din.Sai gashi kowa ya kame kamar gunki
ko
gifta idanu babu mai yi sai kace gumaka ne,kuma
dukkaninsu sarauniya Aryala suka kurawa idanu.Ba
komai ne ya janyo hakan ba face ganin tsananin
kyawunta da kuma ganin badakaren dake tsaron
lafiyarta.Abinda ya kara daurewa sarakunan da
jaruman gasar kai shine ganin yadda sarauniya
Aryala tasa damara a kugunta gami da wadansu
takubba da TAGWAYEN MASU guda biyu a kuibin
cinyoyinta alamar cewa itama tana cikin JARUMAN
GASA.Kallon farko da sarki Uzaima yayiwa
sarauniya
Aryala yaji nan take ya kamu da tsananin sonta da
sha'awarta,kuma ya aiyana a zuciyarsa cewa ko
sama da kasa zasu hade sai ya mallaki wannan
kyakkyawar budurwar a matsayin matarsa ta
aure.A
wannan lokaci bokan sarki uzaima wanda ake kira
ZARDASH IBINI ULAIMA na zaune a daf dashi akan
wata kujera.Koda boka zardash yayi arba da
sarauniya Aryala sai zuciyarsa ta buga da karfi a
lokacin dayaga wani irin haske a goshinta.Nan
take
yai sauri ya dauko madubinsa na tsafi ya shafeshi
take madubi ya disashe ya zama bakikkirin.Cikin
tsananin firgici da matukar mamaki boka zardash
ya
yiwa sarki uzaima rada a kunne yace,ya
shugabana
wannan ce kadai macen da zata tara da ita ka
sami
haihuwa a duk duniya.Koda jin wannan batu sai
sarki uzaima ya dimauce,bai san sa'adda ya
yunkura cikin farin ciki da nufin yaje ya taryo
sarauniya Aryala,amma sai bok zardash yai sauri
ya
riko hannunsa ya zaunar dashi akan karagarsa ya
dubeshi yace,haba ya shugabana,kada ka janyi
mana
abin kunya mana.A matsayinka na shugaban
sarakunan wannan nahiya bai kamata ka rude ba
don kaga wannan kyakyawar sura.Koda jin wannan
batu sai sarki uzaima ya dubi boka zardash cikin
yake yace,ai kuwa bai kamata kaga laifina ba
tunda
wannan ce macen dana dade ina jira a tsawon
shekaruna akan KARAGAR MULKI.Kuma babu wani
'da namiji dazai ga wannan kyakyawar sura ba
tare
daya kamu da tsananin sonta ba da sha'awarta a
lokaci guda.Kafin boka zardash ya budi baki ya
sake
cewa wani abu tuni sarauniya Aryala har ta iso
gabansu.Kawai sai jarumi Damzur da ita suka
risina
a gareshi sukayi gaisuwa sannan jarumi Damzur
ya
budi baki yace,yakai sarkin sarakuna ina mai
farincikin gabatar ma
ka da sabuwar sarauniyar birnin nurul ansar,wato
Gimbiya Aryala Ibini Sarki sa'ad mai mulkin birnin
nurul ansar a baya kafin yayi MUBAYA'A ya dorata
a
matsayin sabuwar sarauniyar dazata mulki birnin
iya
tsawon rayuwarta.Sannan kuma abu na biyu itace
jarumar jarumai ta birnin nurul ansar wacce tazo
birninka domin ta shiga GASAR GUMURZU dakai
don
jarraba sa'arta akanka.Koda jin wannan batu sai
gaba dayan jama'ar dake cikin dakin walimar suka
sake kamuwa da tsananin mamaki musamman ma
sarakunan,domin babu wanda ya taba sanin cewa
sarki sa'ad mai mulkin birnin nurul ansar yana da
zukekiyar 'ya haka ba.Shi kuwa sarki Uzaima
mamaki biyu ne ya turnukeshi.Mamakin farko
shine,na ganin sarauniya Aryala ne bisa ganin
tsananin kyawunta da kuma matsayin data samu
na
zama sabuwar sarauniyar birnin nurul ansar a cikin
kankanin lokaci ba tare da labarin hakan yazo
gareshi ba.Mamaki na biyu kuma shine ganin
jarumi
Damzur a tare da ita a matsayin mai kare
lafiyarta.Take sarki Uzaima ya tambayi kansa a
cikin
zuciyarsa yace,"ta yaya akayi sarauniya Aryala ta
mayar da wannan tsohon dan fashi,kuma
gawurtaccen jarumi mai tsaron lafiyarta alhalin ni
kaina na kasa kaishi kasa kuma na kasa kamashi
na
daure?Nanfa sarki uzaima ya kasa baiwa kansa
amsar wannan tambaya.To waishin ita sarauniya
Aryala wacce irin hatsabibiyace mai tataka da har
zata mallaki jarumi Damzur kuma har da zata
shiga
gasar gumurzun dani ba tare da shakkar komai ba
a
matsayinta na karamar yarinya kuma 'ya mace?
Sarki
Uzaima na cikin yin wannan tunani ne sarauniya
Aryala ta matso daf dashi fuskarta a murtuke ta
dubeshi tace ko bani da matsayin dazaka sa a
bani
wurin zama ne shi yasa ka barni a tsaye?Koda jin
wannan tambaya sai sarki uzaima yayi murmushi
tare da girgiza kai yace,kinda da babban matsayin
daya wuce duk wani bako dake cikin wannan
daki,don haka zo muje na baki wajen zama.Nan
take
ya shiga gaba yayi mata jagora da kansa har
izuwa
inda aka tanadarwa mahaifinta sarki sa'ad mai
mulkin birnin nurul ansar.Dama an ware wata
kasaitacciyar kujera dabam a gefe daya ita
kadai.Koda jarumi Damzur yaga sarki uzaima na
neman hada kafada da sarauniya Aryala sai yai
sauri
ya shiga tsakaninsu,har suka isa gaban
kujerar,sarauniya Aryala ta zauna akai.Gaba dayan
sarakai da jaruman dake cikin wannan dakin
walima
har izuwa wannan lokaci babu wanda yake cikin
hayyacinsa sosai saboda tuni sarauniya Aryala ta
birkita tunaninsu da nutsuwarsu kuma sun dimauce
bisa ganin tsananin kyawunta.Saida sarauniya
Aryala
ta zauna akan kujerarta sannan sarki Uzaima ya
juya
ya koma izuwa inda kujerarsa take,amma yana
waigenta har yana tuntube kamar zai fadi.
...........

.... Al Mustapha isa nake Inkiya #MUSTINDOO KASUWAR RAYUKA!!!
Littafi na Biyu (2)
Part C
Amma yana waigenta har yana
tuntube kamar zai
fadi.Ita kanta sarauniya Aryala
bata san sa'adda
dariya ta kwace mata ba,amma sai
tayi sauri ta
guntse bakinta da hannayenta
biyu ta sunkui da
kanta kasa.Kowa dake cikin
wannnan dakin baiyi
mamakin rudewar da sarki uzaima
yayi ba bisa
ganin tsananin kyawun sarauniya
Aryala da kuma
kyawun surarta,saboda da
yawansu ma sun fara
zubar da hawayen takaici saboda
sunsan cewa
wutsiyar rakumi ta yiwa yaro
nisa.Kuma babu mai
iya mallakar wannan sarauniya
face mai tsananin
sa'a da rabo bisa ganin yanayin
shirinta da kuma jin
izzarta tunda gashi shi kansa sarki
uzaima magana
take yi masa da kakkaifan harshe
ba tare da shakkar
komai ba,kuma ko kadan babu
annuri akan
fuskarta.Har sarki Uzaima ya dawo
kan kujerarsa ya
zauna bai daina waigen sarauniya
Aryala ba,kuma
ko kunya baiji ba ya rinka yawan
kallonta kai da ka
gani kasan cewa ya dimauce
harma yana neman ya
fita daga hayyacinsa.Haka dai aka
cigaba da walima
babu wanda keda sukuni a cikin
dakin.Duk sa'adda
sarauniya Aryala ta dago kai sai
taga kowa ita yake
kallo in badon ma akwai
wadannan yan mata da
suke ta faman tika rawa ba da
bazata iya zama ba
tunda ita kadaice 'ya mace.Shi
kuwa sarki uzaima
sai ya kasa zama dam akan
kujerarsa yayi ta mutsu
mutsu da waige waige kuma ya
kasa cigaba da shan
komai in banda waige waige babu
abinda
yakeyi.Take yaji cewa babu abinda
yake so face ya
mike tsaye yaje ya zauna a gaban
sarauniya Aryala
domin su tattauna maganganu
masu
muhimmanci.Maganar farko da
yakeson ya gabatar a
gareta itace batun ta bashi
soyayyarta suyi
aure.Magana ta biyu kuma itace
yana son ta janye
batun shiga wannan gasa ta
jarumtaka dashi.Ba wani
abu bane yasa sarki uzaima ya
kasa mikewa yaje
wajenta domin suyi wannan
magana ba face sai duk
sa'adda ya waigo suka hada ido
sai yaga ta murtuke
fuska tana harararsa ko kadan
babu annuri a tare da
ita.Al'amarin dayai matukar bashi
mamaki
kenan,kuma ya fusatashi yace a
cikin ransa"Yaya ma
ina sarki mai cikakken iko haka
wanda ake tsoro a
wannan nahiya gaba daya amma
yau 'ya mace guda
daya zata yimin kwarjini da har
zan kasa aiwatar da
abinda zuciyata ta raya min a
kanta?Koda yake
tunda boka zardash yace itace
kadai macen dazan
sami haihuwa da ita lallai zan
lallabata har na samu
nasarar siye zuciyarta,amma fa
hakurina yana da
iyaka,idan ta kaini makura zata
aureni bisa dole ko
don na sami magaji.Haka dai sarki
Uzaima yayita
zancen zuci har aka gama wannan
Walima bai iya
komawa inda sarauniya Aryala ke
zaune ba bare ya
gabatar mata da bukatunsa
biyu,haka kuma bai
dandana komai ba a bakinsa na
abincin
walimar.Itama sarauniya Aryala ko
ruwa mukurwa
daya bata sha ba a dakin walimar
saboda tsorone
ya kamata ta fara tunanin kada
asa mata wani abu a
cikin abinda zata ci ko wanda
zatasha ya cutar da
ita ko ya zamo sanadin da zata fita
daga cikin
hayyacinta har a sami damar yi
mata wani
abun.Sarauniya Aryala bata sami
nutsuwa da
kwanciyar hankali ba har saida ta
taga an kammala
walimar ta tafi izuwa masaukinta
take ta kwanta
akan gado.Kwanciyarta keda wuya
sai taji zuciyarta
ta buga da karfi,ba komai ne ya
janyo hakan ba face
tunowa da maganar mahaifinta
sarki sa'ad lokacin
da yake cewa da ita zata sami
haihuwa amma bata
hanyar aure ba.Kawai sai
sarauniya Aryala taji
hawaye ya zubo mata,take tace a
cikin ranta"Ai
kuwa dole ne na dauki matakin
nisantar kowanne
'da namiji don ba zata taba yarda
wani ya sanni 'ya
mace ba muddin ina
numfashi,kuma ina cikin
hayyacina da lafiyata.Duk yadda
zanyi na canja
wannan kaddara dake kaina
sainayi bazan bari wani
'da namiji ya sanni ba face ya
zama mijina na
aure"Koda gama aiyana hakan sai
sarauniya Aryala
ta mike tsaye zumbur ta fito daga
cikin kuryar dakin
da take kwance ta iske kuyanginta
zaune a falo suna
hira.Kawai sai ta dubesu tace,aje a
gayawa jarumi
Damzru da Barde Husam su kara
matakan tsaro a
kewayen wannan masauki nata ko
tsuntsu kada a
bari ya kusanceshi.Nan take daya
daga cikin
kuyangin taje ta sanar dasu jarumi
Damzur wannan
sako.Koda jin hakan sai jarumi
Damzur da Husam
suka dubi junansu cikin alamun
tsananin mamaki
domin basu ga wani tsaro da zasu
kara ba tunda
gaba dayan dakin kewaye yake da
dakaru gabas da
yamma kudu da arewa,duk abinda
yazo ko ta sama
ne zai gita sai an ganshi an
harboshi da
kibiya.Lokacin da sarauniya Aryala
ta koma cikin
kuryar dakin nata saita dauko
tagwayen masunta ta
kwanta akan gado rike dasu bayan
ta tabbatar da
cewar ta kulle kofar dakin da
dukkan tagoginsa.Tana
rike da masunta tacigaba da sake
saken zuciya har
barci ua saceta bata sani ba.
ΔΔΔ ΔΔΔ ΔΔΔ
AL'AMARIN Sarki Uzaima kuwa
lokacin da aka
kammala walima ya isa turakarsa
ya kwanta domin
yayi barci sai idanunsa suka
bushe,ya zamana cewa
da zarar ya rufe idanun nasa babu
abinda yake gani
sai kyakkyawar fuskar sarauniya
Aryala.Koda ya
shafe sama da sa'a uku a cikin
wannan hali sai
ransa ya baci,kawai sai ya mike
tsaye zumbur ya
sauya tufafin jikinsa ya kure adaka
sannan ya dauko
turare mafi kamshi ya shafe
jikinsa ya fice daga cikin
turakarsa.Yana fitowa sai dakarun
dake tsaron
lafiyarsa suka take masa baya ya
tunkari hanyar zata
kaishi masaukin sarauniya
Aryala.Gaba daya hadimin
gidan sarautar saida suka cika da
dumbin mamaki
saboda tsawon shekaru ashirin da
hawansa karagar
mulki ba'a taba ganin yaci ado ba
haka kuma bai
taba fitowa daga cikin turakarsa
ba a tsakiyar dare
irin haka sai yau.Kai tsaye sarki
uzaima yaciga da
tunkarar masaukin sarauniya
Aryala har ya iso kofar
gidan da take.Da iso
warsa dakarunsa na take masa
baya suka iske
jarumi Damzur da Barde Husam
tsaye a kofar gidan
sun rike kugu,sauran dakarunsu
kuwa sun kewaye
gidan gaba daya wasun su ma
akan katangar gidan
suke a zaune.Koda ganin sarki
uzaima a wannan
lokaci sai mamaki ya kama su
jarumi Damzur.Cikin
hanzari barde Husam ya tari su
sarki Uzaima ya
risina a gareshi ya kwashi
gaisuwa yace,ya
shugabana lafiya kazo garemu a
cikin wannan dare
haka?Koda jin wannan tambaya
sai sarki uzaima
yayi murmushi sannan yace aje a
gayawa
sarauniyarku cewa lallai inason na
gana da ita a
yanzu domin ina da wata
muhimmiyar magana da
nakeson mu tattauna da ita.Dajin
haka sai barde
Husam ya sake risina yace,zamuyi
kamar yadda ka
bukata ya shugabana.Nan take
barde Husam ya juya
ya shige cikin gidan.Jim kadai sai
ga Husam ya
dawo da saurinsa.Da zuwansa ya
dubi sarki Uzaima
yace,ya shugabana ai
sarauniyarmu tayi barci,kuma
ta baiwa kuyanginta sakon cewa
ko waye yazo
wajenta kada a tasheta daga
barci,mu kanmu ta
bamu umarnin cewa kada a bar
wani abu ma ya
kusanci wannan gida koda tsuntsu
ne yazo giftawa
ta sama to a gaggauta
harboshi.Ya shugabana ina
ganin cewa zaifi kya ka hakura ka
tafi saida safe ka
sami damar ganawa da ita.Koda
jin wannan batu sai
ran sarki Uzaima ya baci cikin
alamun fishi ya
dakawa barde Husam tsawa yace
wacece sarauniyar
taku har da zata kafa mini doka a
cikin gidan
sarautata wacce ban isa na
karyata ba?Ina mai
umartarka daka koma da gaggawa
ka tashi
sarauniyarku daga barci domin
sarki sarakuna ne
keson ya gana da ita yanzu,in ba
haka ba kuwa
yanzun nan takobina zata sama
mini hanya izuwa
cikin wannan gida da karfin
tsiya.Koda jin wannan
batu sai jarumi Damzur ya zare
takobinsa yasha
gaban sarki uzaima yace,idan har
hakan zata faru to
saidai bana raye.Cikin tsananin
fishi sarki Uzaima ya
zare takobin wani badakare dake
gefensa ya yunkura
da nufin ya afkawa Jarumi
Damzur,kawai sai yaji an
daka masa tsawa.Cikin mamaki da
tsananin fishi
sarki Uzaima ya juya domin yaga
wanda yayi masa
wannan tsawa,kawai sai yaga
ashe.....ne.
....
....
By AL MUSTAPHA Isah Inkiya #MUSTINDOO KASUWAR RAYUKA!!!
Littafi na Biyu (2)
Part D
Cikin mamaki da tsananin fishi sarki uzaima ya
juya domin yaga wanda yayi masa wannan
tsawa,kawai
sai yaga ashe boka Zardash ne.Boka zardash ya
karaso wajen sarki uzaima ya kama hannunsa ya
jashi gefe daya sukayi kus kus.Bisa mamaki sai
akaga sarki uzaima ya juya ya koma baya izuwa
cikin gidan sarautar tasa.Ai kuwa sai dakarunsa
suka bishi da sauri yana tafe yana huci da ciza
lebe
tamkar zakin daya ratso daji a fusace yana neman
abinda zai ci a lokacin da yake cikin tsananin
yunwa.Kashe gari da sassafe jama'a suka fara
taruwa a filin gidan sarautar inda za'ayi gasar
jarumtaka.Nan da nan filin gasar ya cika ya batse
da
mutane ya zamana cewa duk inda mutum ya
hanga
baya ganin komai face kawunan bil'adama fululul
kai kace kwari ne ba mutane ba.Jaruman gasar
kuwa
su
dariya biyu da casa'in da tara ne suka iya hallara a
cikin filin gasar.Har tsawon
ADMIN ROKED KEMAGANA
wannan lokaci sarki
uzaima da sarauniya Aryala basu iso filin gasar
ba,su kadai ake jira su fito filin gasar a fara gabatar
da GASAR JARUMTAKA!
# ΔΔΔRΔΔΔOΔΔΔKΔΔΔEΔΔΔDΔΔΔ
LOKACIN da Sarauniya Aryala ta gama shiri ta
sanya
sulke a jikinta kuma ta daura damararta ta zuba
TAGWAYEN MASUNTA a jikinta sai ta fito daga
cikin
dakinta.Tana isowa ta iske su Jarumi Damzur a
tsaitsaye cikin kaguwar jiranta.Sarauniya Aryala ta
dubi Jarumi Damzur da Barde Humas cikin
murmushi tace,na sani cewa mun makara,amma
kada ku damu wannan itace IZZAH irin ta jarumin
daya yarda da kansa.Yanzu ne zamu iya zuwa
FILIN
GASAR JARUMTAKA!Tana gama fadin hakan sai ta
wuce gaba faga cikin falon.Cikin sauri su Jarumi
Damzur suka bita a baya suka nufi hanyar da zata
kaisu filin gasar.Sarauniya Aryala suka iso filin
gasar,jama'a na hangota aka rude da shewa
tamkar
dama can an saba ganin jarumtakarta.Na
nfa
makada
da mawaka suka shiga yimata kirari suna kodata.A
wannnan rana matan da sukazo kallon wannan gasa
sun ninka maza yawa sau hudu,saboda tuni labarin
sarauniya Aryala ya baza ko ina a cikin birni da
kauyukan kasar harma da kasashen dake
makoftaka
da birnin kisra.Da yawan matan da sukazo sun zone
kawai domin suga iyakar kyawun sarauniya Aryala
da ake ta zuzutawa musamman ma maza da suke
yabonta da kurantata koda a gaban matansu
ne.Wasu kuma daga cikin matan da sukazo sunzo
ne kawai saboda dasu kara mata kwarin guiwa a
matsayinta na 'yar uwarsu mace,kuma 'ya mace ta
farko a nahiyar da zatayi gasar gumurzu da sarki
Uzaima.Lokacin da su sarauniya Aryala suka shigo
filin gasar,ta hanga inda kujerar sarki uzaima
take,taga baya nan sai ranta ya sosu,domin ba
haka taso ba.So tayi ace ya rigata zuwa filin
gasar,ya
zamana cewa ya zauna ya jira isowarta.Haka dai
sarauniya Aryala taje inda jaruman gasar suke ta
tsaya,amma sai aka dakatar da dukkanin
dakarunta
daga waje,Jarumi Damzur kadai aka bari yayi mata
rakiya.Saida sarauniya Aryala da jaruman gasa
suka
shafe kusan rabin sa'a a tsaye suna jira sannan
akaji
an buga tambarin sarki.Kafin ma aga sarki filin ya
rude da shewa gami da tafi da kuma bugun
ganguna,kirari da jinjina ninkin wanda aka yiwa
sarauniya Aryala sau uku.Tabbas masu iya magana
sunyi gaskiya da sukacewa,KOWA A GIDANSA
SARKI
NE!A wannan lokaci sarauniya Aryala ta fahimci
cewa mutanen birnin kisra suna matukar son
sarkinsu,domin mazansu da matansu jinjina suka
kama yiwa sarki uzaima suna ihun farincikin
ganinsa.Kai tsaye sarki Uzaima ya shigo filin gasar
fuskarsa cike da annuri yana tafiya cikin izza ta
kaisata har ya iso cikin tsakiyar filin gasar.Kawai
sai
ya tsaya a gaban jaruman gasar ya fuskancesu a
lokacin da yake kokarin kirgasu.Koda ya hada
idanu
da sarauniya Aryala sai yayi mata murmushi,ita
kuwa saita murtuke fuskarta tamkar taga babban
makiyinta a duniya.Al'amarin dayai matukar bashi
mamaki kenan kuma ya sosa masa rai.Lokacin da
sarki Uzaima ya gama kirga jaruma gasar yaga su
dari uku ne cif har dashi kansa,kuma ya kare musu
kallo ya tabbatar da cewa zakwakurai ne wadanda
dole ne ayi fama dasu sai ya dubi alkalin gasar
yace,inaso a raba jaruma gasar nan gida uku
domin
abin kunya ne a gareni nayi yaki dasu daya bayan
daya.Inason nayi yaki da mutane dari dari sau uku
ADMIN KABEER ROKED KEMAGANA
alokaci guda,amma banda jaruma mace,ita a
wareta sai a karshe zan fafata da ita.Koda jin
wannan batu
sai filin gasar ya sake rudewa da shewa aka cigaba
da yiwa sarki uzaima kirari da jinjina.Itama
sarauniya Aryala farin cikin ne ya kamata da taji
cewar ita dashi ne kadai zasu fafata,amma fa data
dubi sarki uzaima da kyau taga ashe yafi jarumi
Damzur cika da haiba da kuma kira ta
sadaukantaka,take ta aiyana a ranta cewa,inda ace
sarki uzaima da jarumi Damzur sun taba shafe
sa'o'i
masu yawa sun fafatawa da dole ne sarki Uzaima
yayi nasarar akan jarumi Damzur saboda da ganinsa
zai zama mai tsananin juriya da dauriya.Ba tare da
bata wani lokaci ba aka raba dakarun gasa izuwa
kaso uku,wato dari dari guda biyu,sai kuma
mutum
casa'in da tara,cikon darin ce sarauniya Aryala aka
wareta a gefe daya.Ba tare da bata wani lokaci ba
aka buga tambarin fara gasa take jaruman gasa
kashi na farko su dari suka zare takubbansu suka
fuskanci sarki uzaima.Kafin suyi wani yunkuri tuni
sarki uzaima ya zare zabgegiyar takobinsa ya
kwarara karkarfan ihu mai matukar firgitarwa,sann
an
ya ruga da gudu izuwa kansu.Da karfin tsiya ya
kutsa ta tsakiyarsu yana kai musu mugun SARA
DA
SUKA suma suna kai masa
.. By AL MUSTAPHA Isah Inkiya #MUSTINDOO #PRABHAS KASUWAR RAYUKA
Littafi na 2 Part E
.********
posting
By AL MUSTAPHA Isah
.MUKAFTA@@@@@
££££££
Da karfin tsiya ya kutsa ta tsakiyarsu yana mai kai
musu mugun SARA DA SUKA suma suna kai
masa.Amma kafin yakai karshen su saida ya sami
nasarar yankar kowannensu,suka rinka zubewa
kasa
suna ihu a lokacin da jininsu ke tsartuwa daga
jikinsu,amma suko lakutar jikinsa ba sami wanda
yayi ba.Koda ganin wannan gagarumar jarumtaka da
sarki Uzaima yayi sai filin gasar ya sake rudewa da
shewa a karo na uku,
ADMIN Al Mustapha KEMAGANA
shewar ta cika birnin gaba
daya da amsa kuwwa har izuwa cikin daji.Faruwar
hakan ce tasa ragowar kasa biyu na jaruman su
dari da casa'in da tara suka firgice ainun,kawai sai
suka
zubar da makamansu suka fice daga cikin filin
gasar,alamar cewar sun jante daga gasar bazasu
iya
ba.Ai kuwa sai filin gasar ya sake rudewa da
shewa fiye da karon farko dana biyu.Filin gasar ya
rage
saura sarauniya Aryala da sarki Uzaima kacal a
tsaye.Kawai sai filin yayi tsit!Tamkar mutuwa ta
gifta
a lokacin da sarki Uzaima da sarauniya Aryala
suka fara kallon kallo.Sai a yanzu ne sarki Uzaima
ya
lura
da yanayin siffar baragen jikin sarauniya Aryala,ya
gane cewa lallai akwai jinin sadaukantaka a tare da
ita,kuma yana kallon cikin kwayar idon nata ya
gane cewa zuciyarta a kekashe take babu alamar
tsoro.Nan take ya tambayi kansa a cikin zuciyarsa
yace,"Yaya ni da MANYAN MAZAJE kuma
GWARZAYEN SADAUKAI ke shakkar yin GABA DA
GABA dani,amma yau gashi wai 'ya mace 'yar
shekara goma sha ce ta tsaya a gabana zata yakeni
ba tare da wata alama ta fargaba ko tsoro
ba.Tabbas
na gamsu cewa wannan ce macen dazan iya
haihuwa da ita.Bari na fara jarraba iyakar
jarumtakarta na gani.Gama aiyana hakan keda wuya
sai sarki uzaima ya daga takobinsa sama ya yafito
sarauniya Aryala da hannu yana maiyi mata nuni
yana mai yi mata kira irin na raini.Maimakon
sarauniya Aryala ta ruga izuwa gareshi kawai sai
akaga ta dako tsalle a sama daga inda take tsaye
tamkar daga cikin baka aka harbota.A saman ta
zare
takobinta ta kawo masa wawan sara da nufin ta
tsarge kansa gida biyu.Cikin tsananin zafin nama
sarki uzaima ya daga takobinsa sama ya kare
saran,amma saboda nauyin saran nata saida ya dan
durkusa kasa bisa guiwarsa guda sannan ya mike
tsaye zumbur suka kacame da masifaffen
azababben
yaki mai tsananin muni da tayar da hankali.Ya
zamana cewa suna kaiwa junansu SARA DA SUKA
cikin mugun bakin zafin nama,juriya,jarumtaka da
bajinta ta ban al'ajabi irin wanda idanuwa basu
taba
gani ko kunnuwa suji labari.Nanfa jama'ar dake
wajen suka rude da ihu da shewa gamo da
tafi,kowa yana mai tsananin mamaki bisa ganin irin
jarumtakar da sarauniya Aryala keyi.A wannan
lokaci
ne sarki Uzaima ya gane cewa lallai sarauniya
Aryala
ba kanwar-lasa bace,kuma jarumtakarta ta
musamman ce wacce ta wuce yadda yake zato ko
tsammani.Nan take zuciyarsa ta fara aiyana masa
cewa lallai babu yadda za'ayi ace akwai wata 'ya
mace BASADAUKIYA mai tsantsar jarumtaka da
bajinta gami da bakin zafin nama irin sarauniya
Aryala,saidai idan wani sihirin tsafi gareta mai karfin
gaske,domin al'amarin nata ya zama tamkar
almara
a gareshi.
TSAKANIN SARKI UZAIMA DA SARAUNIYA ARYALA
WAYE ZAI SAMI NASARA A WANNAN AZABABBEN
YAKI NA GASAR JARUMTAKA DA SUKE
FAFATAWA?
YAUSHE SARAUNIYA ARYALA ZATA HAIFI YARON
DAZA'A SAMESHI BATA HANYAR AURE BA KUMA
WAYE MAHAIFINSA?
IDAN YARON YAZO DUNIYA WACCE IRIN DAUKAKA
ZAI SAMU KAMAR YADDA KAKANSA,WATO SARKI
SA'AD MAHAIFIN SARAUNIYA ARYALA NA BIRNIN
NURUL ANSAR YA FADA?
SHIN SARKI UZAIMA ZAI SAMU NASARAR CIKA
BURINSA NA AUREN SARAUNIYA ARYALA HAR YA
SAMU MAGAJI DA ITA KAMAR YADDA BOKANSA
ZARDASH YA SANAR DASHI?
YAUSHE SARAUNIYA ARYALA ZATA CIKA BURIKAN
DAKE CIKIN ZUCIYARTA?
Mu hadu a littafin KASUWAR RAYUKA (3) don jin
cigaban wannan kayataccen kasaitaccen labari.
Alhamdulillah!!! Godiya ga Allah madaukakin Sarki
Daya bamu ikon kammala wannan littafi.
Dama kamar yadda na fada muku 1&2 ne kadai ya
fito 3 bai fito ba,gashi dai mun kammala 1&2,sai
muyi jiran fitowar 3&4 da sauransu.
AL MUSTAPHA Isah nee Inkiya #MUSTINDOO

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment