Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

KASUWAR RAYUKA
Littafi Na Daya (1)
PART {A}
A WANI Zamani can baya mai tsawo da ya
shude,lokacin da ake kan tsakiyar cinikin
bayi,sa'adda sarakuna ke mulkin KAMA
KARYA,MULKIN ZALUNCI,a zamanin da mutum
bashi
da wani yanci na kansa face ya kasance sarki ko
mashahurin attajiri ko kuma gawurataccen Boka
ko Jarumi.Indai mutum bai taka wannan matsayi
ba'ana
sarrafashi tamkar dabba ba dan adam ba.A
wannan
lokaci kaf duniya babu kasar da tafi BIRNIN KISRA
Daukaka a harkar CINIKIN BAYI,domin basu da wata
sana'a wacce tafita.Sarkin dake mulkin Birnin Kisra
{DR ROKED}
Awannan lokaci ya kasance gawurtaccen sadauki
kuma gagarumin mayaki mai TARWATSA MAZA a
FILI FAM,ana kiransa da suna SARKI UZAIMA IBINI
SARZAF.Sarki Uzaima shine da kansa yake kwasar
dakarunsa na yaki kamar mutum dubu uku su tafi
FARAUTAR BAYI,kuma indai zai fita farautar bayi
baya kai hari a yankin kasarsa ko kasashen dake
makoftaka da kasarsa,yakan tafi wata nahiyar ne
gaba daya kuma mafi akasarin tafiye tafiyen nasa
yana yinsu ne akan TEKU.Duk sa'adda sarki
Uzaima
ya fita farautar bayi baya dawowa gida da kasa da
bayi dubu goma,kuma shi baya kamo yara ko
tsofaffi
sai matasan SAMARI da 'YAN MATA masu jini a
jika.Duk garin da yaje yakan sauka a bayan garin
ne
ya aikawa da sarkinsu wasika.A cikin wasikar sai
ya
bukaci a bashi bayi dubu goma cikin salama,idan
kuwa aka ki sai ya fakawa garin da yaki ya kama
duk wanda ya gadama a matsayin bawa koda
kuwa
sarkin garin ne da kansa.Kasuwar cinikin bayi ta
birnin Kisra tana cine bayan duk karshen mako
biyu.A duk wannan rana attajirai da sarakai suna
zuwa birnin na kisra daga kowanne bangare na
duniya domin siyen bayi saboda babu irin kalar
bawan da mutum bazai samu ba.A wannan rana
sarki Uzaima yana samun kazaman kudade masu
dimbin yawan dashi kansa yana mamaki.Saida
sarki
Uzaima ya shekara ashirin akan KARAGAR MULKI
yana wannan sana'a ta tara arziki wanda har takai
cewa yama rasa abinda zaiyi da kudin.Sau bakwai
yana sawa ana rushe fadarsa ana gina sabuwa,ya
zamana cewa duk duniya babu wata fada data kai
tasa kyawu da kawa.Sarki Uzaima ya tara
gonaki,gidaje,dabbobi da rumfunoni a kasuwa ba
adadi wanda shi kansa baisan iyakar adadinsu
ba.Wani iko na Allah sarki Uzaima ya kasance
mutum mai matukar koshin lafiya domin tunda ya
hau karagar mulki bai taba yin cutar datasa ya
kwanta ba koda tsawon yini daya saidai dan
gajeren zazzabi ko ciwon kai.Sarki Uzaima yana da
matar
aure guda daya jal.Wata kyakkyawar mace mai
suna
Suhaira wacce tun yana da shekara ashirin da
daya
akayi musu auren saurayi da budurwa tun zamanin
mahaifinsa.A yanzu Suhaira ta shekara goma sha
hudu da auren sarki Uzaima amma ko bari bata
taba
yi ba.Sarki Uzaima yana da kwarkwarori guda
ashirin da daya,kuyangi da bayi mata kuwa gasu
nan birjik amma dayarsu bata taba samun ciki
dashi
ba.Duk wannan irin ni'ima da Allah ya baiwa Sarki
Uzaima ta mulki,jarumta,d
ukiya,daula,mata da
ingantacciyar lafiya sai ta zama ta banza,domin
duk
sa'adda ya tuna cewa bashi da magaji sai ya shiga
daki ya kulle kansa yayi ta kuka har sai ya gaji da
kukan barci ya sace shi bai sani ba.Allah shine
mai
iko!Gashi dai duk wata daukaka ta duniya an
baiwa
sarki Uzaima amma sai aka hanashi haihuwa dimin
a nuna masa cewa shima fa ba kowa bane face
bawan Allah.Bokaye da likitoci barkatai sun
tabbatarwa da sarki Uzaima cewa lafiyarsa kalai
kuma zai iya haihuwa amma babu wanda yasan
yaushe ne zai samu haihuwar,kuma babu wanda
yasan macen da zata sami wannan sa'a ta haihu
dashi.A tsawon shekaru ashirin da sarki Uzaima ya
kwashe yana kai hare hare izuwa kasashen ketare
bai taba zuwa garin daya kasa samo nasara
ba,kuma bai taba yin gumurzu da wani jarumi ya
sami nasarar koda lakutar jikinsa ba bare ace
gashi anyi masa wani babban rauni saboda tsabar
KARFINSA,JARUMTAKARSA DA SA'ARSA.A ranar da
sarki Uzaima ya cika shekara arba'in cif a duniya
ne
ya zamana cewa ya sami shekaru ashirin akan
karagar mulki,bisa wannan dalili yasa aka shirya
gagarumar walima ta musamman,kuma ya gayyaci
gaba dayan sarakunan dake nahiyarsa domin suzo
su tayashi murnar cika shekarunsa na haihuwa
arba'in da kuma cikar shekara ashirin akan
KARAGAR MULKI.Baya ga wannan Walima kuma
saiya shirya gagarumar gasa ta yki akan cewa duk
jarumin daya sami nasarar yi masa rauni ko ya
kaishi kasa to ya fadi duk abinda yake so walau
dukiya ko wata kadara tasa zai bashi.Lokacin da
wannan labari ya bazu a nahiyar,sai
sadaukai,jarumai da mayaka sukayi ta tururuwa
izuwa cikin birnin kisra domin shiga wannan gasa
duk da cewa da yawansu sun firgita da al'amarin
sarki Uzaima,sun san cewa babu wanda ya taba
samun galaba akansa amma saboda kwadayin
ladan
da sukaji za'a baiwa mutane sukayi kundunbalar
shiga wannan gasa. ¤ ¤ ¤
DR KABEER LAWAL UMAR ROKED
A YAMMA da Birnin Kisra akwai wata karamar kasa
da ake kira da NURUL AMSAR.Sarki dake mulkin
wannan kasa ya kasance adali,kuma tsoho ne
tukuf!
Har ma takai cewa ya kwanta CUTAR AJALI saboda
tsufan nasa.Shi dai wannan sarki ana kiransa da
suna SA'AD IBINI HUSEIN.Saboda birnin Nurul
Ansar
tana makoftaka da birnin Kisra sai ta sami kariya
daga sharrin mahara da yan FARAUTAR BAYI.Don
haka akwai cikakken kwanciyar hankali da zaman
lafiya a birnin.Kuma Allah ya albarkaci birnin da
arzikin noma,kuma sannan sarki Sa'ad yana
matukar
biyayya ga sarki Uzaima,hakan yasa duk shekara
yake aika masa da kyautar amfanin gona mai
yawan gaske da kuyangi.Bisa wannan dalili ne ko
kadan
sarki Uzaima bai taba sa ido akan kasar Nurul
Ansar
ba,kai har ma zuba dakarunsa yayi akan bodar
birnin domin su basu tsaro daga yan kawo harin
sumame.Sarki Sa'ad yana da matan aure
shida,amma kuma 'yarsa guda daya ce
jal!A duniya wata kyakkyawar budurwa ta gaban
kwatance mai suna ARYALA.A Duniya babu abinda
sarki Sa'adda ke SO da KAUNA sama da gimbiya
Aryala,amma tunda aka haifi Aryala aka boyeta
saboda tsananin Kyawunta.Kai!Hatta Barori da
hadiman gidan sarautar babu wanda ya taba ganin
fuskar Gimbiya Aryala bare ya tsegunta irin
kyawunta saboda kullum ana rufe fuskarta ne da
wata bakar Hula wacce idanunta,bakinta da
hancinta
kadai ake iya gani,kuma mahaifinta ne ya bada
wannan umarni saboda wani sirri da bokansa ya
gaya masa.Lokacin da Aryala ta fara tasowa sai
Sarki Sa'adda yaga ashe Allah yayi mata baiwa ta
sadaukantaka,domin tun tana shekara shida a
duniya take iya dagashi sama ta fyada da kasa a
lokacin da yake koya mata kokawa.
Doctor kabeer kemagana
Koda gain
wannan al'amari na ban mamaki sai sarki Sa'ad ya
sake killace Gimbiya Aryala aka dauketa ita da
mahaifiyarta aka kaisu can wani gidan sarki dake
can bayan gari.In banda dakarun dake gadin gidan
babu kowa a cikinsa face Aryala da
mahaifiyarta.Anan ne kuma sarki Sa'adda ya rinka
zuwa da kansa yana koyawa gimbiya Aryala yaki.A
sannan ne fa ya sake ganin abin al'ajabi daya
shallake tunaninsa.Ba komai ya gani ba face yadda
a kwana uku kacal Aryala ta lakanci sarrafa takobi
fiye dashi.A cikin sati uku kuwa sai gashi tana
baiwa
kanta horon yakin da ba'a taba koya mata ba,sai
gashi har tashi sama take kamar tsuntsuwa tana
kaiwa iska SARA DA SUKA.haka dai Gimbiya Aryala
da mahaifiyarta ZALIMA suka cigaba da rayuwa a
cikin wannan gida na bayan gari su biyu kacal
tsawon shekara goma sha biyu.A tsawon wannan
lokaci Aryala bata da wani aiki wanda yafi baiwa
kanta horon yaki da kuma fita daji farauta a
sirrance ba tare da dakarun gidan sin sami
ba.Daidai da
rana
daya Gimbiya Aryala bata taba cire hular fuskarta
ba
ta kalli kanta a madubi bare taga kamanninta.Bata
cire wannan hula face idan zatayi wanka ko zatayi
barci,saboda dokace sarki ya kafa mata.Gimbiya
Aryala ta kasance tana tsananin son sarki Sa'ad
don
haka tana matukar biyayya a gareshi saboda haka
bata yarda ta sabawa umarninsa.Duk sa'adda
Gimbiya Aryala ta tuna cewa itafa yar sarki ce kuma
mai jiran gado,amma gashi an kawota wani gida
dake cikin kungurmin daji an ajiyeta tare da
mahaifiyarta tsawon shekaru goma sha biyu ba
tare
datasan dalili ba,kuma sannan an kafa mata dokar
rufe fuskarta a koyaushe har yakai cewa ita kanta
batasan kamannin kanta ba.An nisantata da
jama'a,bata ma san yadda ake tafiyar da al'amarin
rayuwa ba face abinda mahaifiyarta ta koya
mata,sai
tayi kuka na takaici da bakin ciki a duk sa'dda ta
zauna tana tunani akan wannan lamari na
rayuwarta.Abu daya ne yake sa zuciyarta tayi sanyi
a duk sa'adda ta kasance a cikin wannan hali,kuma
ba komai bane face duk sa'adda ta tafi farauta daji
tayi gumurzu da wata dabbar mai hadari ta kasheta
sai ta tsinci kanta a cikin dimbin farin ciki,tayi
murna
bisa ganin jarumtakar da Allah ya bata.A duk
lokacin
da Gimbiya Aryala ta tambayi mahaifiyarta dalilin
da
yasa aka killacesu a cikin wannan gida dake daji
aka
hanasu rayuwa a cikin gari da gidan sarauta sai
kawai taga hawaye ya zubowa mahaifiyarta
Zalima,sannan tace da ita kiyi hakuri yake 'yata
lokaci yana nan zuwa da zamu koma cikin gari
kuma a sannan ne zaki gaji mahaifinki ki haukan
KARAGAR MULKINSA!!!Duk sa'adda Gimbiya Aryala
taki wannan batu daga bakin mahaifiyarta Zalima
sai
ta kamu da tsananin mamaki,ta dubeta tace,saboda
me bazamu koma yanzu ba?Yake Ummina ki tuna fa
cewa yanzu mahaifina ya tsufa tukuf,kuma gashi
yana yawan yin rashin lafiya,har ta kai cewa yanzu
sau biyu rak yake iya kawo mana ziyara gidan
nan,shin bakya tsoron AJALI zai iya riskarsa muna
nan bamu sani ba?Yake mahaifiyata keda kanki
kinsan irin tsananin son da nake yiwa Abbana,don
haka ko zai mutu inason ya mutu akan kafaduna
ina
rungume dashi.Koda Gimbiya Aryala tazo nan a
zancenta sai hawaye ya zubo mata daga
idanunta.Itama mahaifiyarta Zalima ta kamu da
tsananin tausayinta ta kama zubar da hawayen
suka
rungume juna suna masu ci gaba da kukan.
Toh ai shikenan
Nima tsananin jin tausayin su yasa na tsaya ina
jimami.
....
Dafatan yayi kuma zakuyi liking da
commenting kamar yadda kuka saba.. Sannan zan
cigaba kaman yadda na saba Insha
Allah.
............
... By AL MUSTAPHA Isah Inkiya #MUSTINDOOKASUWAR RAYUKA
Littafi na Daya (1)
Part B.
Suka rungume juna suna masu ci gaba da
kukan.Tun daga wannan rana sai da sarki sa'ad ya
shafe sati biyu cur!bai kawowa su Gimbiya Aryala
ziyara ba.Al'amarin daya dugunzuma hankalinsu
kenan,kawai sai Gimbiya Aryala ya mike tsaye ta
kama shiri zata fita.Cikin firgici mahaifiyarta Zalima
ta sha gabanta tace,ina zakije?Koda jin wannnan
tambaya sai hawaye ya zubowa Gimbiya Aryala
tace,ya za'ayi naci gaba da zama tsawon sati biyu
ba tare danaga Abbana ba?Bamu san halin da
yake
ciki ba a yanzu yana raye ko baya raye bamu sani
ba.Dole ne yanzu naje cikin gari na shiga har fada
domin nasan abinda ake ciki.
KABEER LAWAL UMAR ROKED
Gimbiya Aryala na gama fadin hakan sai ta juya ta
nufi bakin kofa da
nufin taje inda bargar dawakai take ta kama daya
ta
hau.Koda ganin haka sai Zalima ta ruga tasha
gabanta ta rungumeta kuma ta fashe da kuka tana
mai rokonta akan ta kara hakuri lallai sarki bazai
barsu haka ba.Nan fa gardama ta karke a
tsakaninsu,Gimbiya Aryala nacewa sai ta tafi,ita
kuma Zalima tana riketa tare da rokonta akan ta
hakura da zuwa.Suna cikin wannan hali ne
kwatsam!Sai akaji haniniyar doki a kofar gidan
alamar cewa manzo yazo daga fada.A Guje Zalima
da Gimbiya Aryala suka ruga izuwa kofar
gidan,suna
zuwa kuwa sai sukaga ashe wani hadimin sarki ne
na jikinsa yazo.Take hadimin ya sauko daga kan
dokinsa,koda yazo gaban gimbiya Aryala sai ya
zube bisa guiwoyinsa yayi mata gaisuwa irin wacce
ake yiwa sarki.Duk da cewa fuskar gimbiya Aryala
a
rufe take saida Hadimin yaga alamun tsananin
tsoro
akan fuskarta domin ja tayi da baya a firgice tana
mai dafe kirjinta ta dubi hadimin tace,meya faru ga
Abbana?Hadimin yayi murmushi sannan yace sarki
nanan a raye,amma yana kwance cikin jinya,kuma
shine ua aikoni gareku yanzu.
Sarki yace a shaida
muku cewa yaune ranar dazaiyi murabus ya baki
KARAGAR MULKINSA don haka sai ku shirya mu
tafi.Koda jin wannan batu sai Gimbiya Aryala da
mahaifiyarta Zalima suka kamu da tsananin
farinciki
gami da mamaki.Nan da nan cikin kankanin lokaci
Zalima da Gimbiya Aryala suka yi shiri suka debi
yan kayan dasuke bukata suka hau dawakai
biyu,hadimin yayi musu jagora suka durfafi hanyar
dazata kaisu cikin gari.Tunda suka fara wannan
tafiya sai Gimbiya Aryala ta tsinci kanta a cikin
tsananin farin ciki don haka sai ta rinka kalle kallen
daji tana ta murmushi cikin annashuwa.Koda suka
iso kofar gari kuma taga yadda gaba dayan garin ya
sauya da sabbabin gine gine sai hawaye ya zubo
mata saboda rabon data taka kasar garin yau
shekara goma sha biyu kenan.Kawai sai Gimbiya
Aryala ta sauko daga kan dokinta ta debi kasa da
hannayenta biyu ta shinshinata sannan tayi ihu cikin
murna.
DOCTOR KABEER LAWAL UMAR ROKED
Al'amarin daya firgita hadimin sarki
kenan,yayi sauri ya tsaida dokinsa ya sauko ya
kama Gimbiya Aryala ya tasheta tsaye da sauri ya
dubeta yace,haba ya shugabata,ayau fa zaki zama
sarauniyarmu yaya zaki rinka yin abu na kaskanci
irin haka?Koda jin wannan batu sai Zalima ta dubi
Hadimin ta bushe da dariya tace,yakai SHUBARU
ka
kyale 'yata tayi farin cikinta ta more domin tana
begen birninta ne.Nan dai Shubaru ya kamawa
Gimbiya Aryala Dokinta ta sake hawa suka cigaba
da
tafiya suka kunna kai izuwa cikin garin.Har suka
isa
gidan sarautar babu wanda ya gane ko su waye.Kai
tsaye aka wuce dasu Gimbiya Aryala izuwa fadar
sarki.Al'amarin daya basu mamaki kenan har
Gimbiya Aryala ta dubi hadimi Shubaru cikin
mamaki
da rashin fahimta tace saboda me zaka nufi fada
damu maimakon ka kaimu turakar sarki muga
halin
da yake ciki?Hadimi Shubaru yace,ai sarki yana
fada
yana jiranku.Gama fadin hakan keda wuya kuwa
sai suka iso bakin kofar fadar aka bude musu suka
shiga.Suna shiga suke iske fadar a cike makil da
fadawa da kuma mutanen gari babu masakar
tsinke.Take suka hango sarki Sa'd zaune akan
karagar mulki yana rike da sandarsa ta mulki.Kallo
daya Gimbiya Aryala da Zalima suka yiwa sarki
Sa'ad suka gane cewa yana jin jiki,kawai karfin hali
yayi harma ya iya fitowa fadar ya zauna.Koda
jama'a
sukaga matar sarki Zalima da 'yarta Gimbiya
Aryala
sun durfafi inda sarki sa'ad ke zauna sai suka cika
da tsananin mamaki saboda jama'a da yawa sun
zata cewa Zalima ta mutu tun shekaru goma sha
biyu bayan ta tafi garinsu gaida iyayenta.Wannan
itace jita jitar da akayi ta yadawa har ma ana cewa
jaririyarta data haifa ma ta mutu.A wannan lokaci
Gimbiya Aryala tana sanye da wata doguwar riga ce
ta talakawa wacce mahaifiyarta ce ta dinkata da
hannunta,kuma takalmin dake kafarta mana fate
ne
kalar na talakawa.Duk da cewa fuskar Gimbiya
Aryala a rufe take,amma kyawun siffar jikinta sai
daya dimauta gaba daya mutanen dake fadar
musamman mazaje.Koda sarki sa'ad ya hango
matarsa Zalima tare da 'yarsa Gimbiya Aryala sun
shigo cikin fadar,sai fuskarsa ta fadada da
murmushi,kawai sai akaga sarki sa'ad ya yunkura
cikin matukar karfin hali ya mike tsaye sannan ya
taka matattakalar dake gabansa ya sauko kasa
daga
kan tudun da Kargar Mulkinsa take yazo ya tare su
Zalima duk su biyun sai suka fada kan kirjinsa
suka
rungumeshi suna kuka.Take shima sarki sa'ad
zuciyarsa ta karaya har hawaye ya zubo
masa.Al'amarin daya kara baiwa kowa mamaki
kenan.Bayan sarki sa'ad ya dan jima kankame
dasu
Gimbiya Aryala,daga can saiya janye jikinsa daga
cikin nasun sannan ya fuskanci jama'a yace,yaku
jama'ar birnin nurul ansar da yawanku kun san
kowace ce wannan a hannuna na hagu.To ga
wadanda basu santa ba ina mai sanar dasu cewa
wannan itace matata guda daya jal a duniya wato
Zalima wacce ake ta yada rade radin cewa ta mutu
a can garin su kimanin shekaru goma sha biyu da
suka gabata baya.Wannan budurwa kuwa da kuke
gani a hannu na na dama ba wata bace face 'yata
guda daya jal tilo a duniya,wato gimbiya Aryala.

...

....
By AL MUSTAPHA Isah Inkiya #MUSTINDOO KASUWÀR RAYUKA!!!
Littafi na Dàya (1).
Part C
Wannan budurwa kuwa da kuka gani a hannuna
na dama ba
wata bace face 'yata guda daya jal tilo a
duniya,wato
Gimbiya Aryala.Koda sarki sa'ad yazo nan a
zancensa sai gaba dayan mutanen dake fadar suka
mike tsaye cikin tsananin mamaki suka kurawa
Gimbiya Aryala Idanu.Nan take sarki yasa hannu ya
cire hular dake kan fuskar gimbiya Aryala,jama'a
sukayi arba da tsananin kyawun fuskarta tata,ai
hatta
yan'uwanta mata dimaucewa sukayi saboda
tsananin kyawunta.Nan take sarki sa'ad ya kama
hannun
gimbiya Aryala yajata izuwa kan karagarsa ta mulki
yaje ya zaunar da ita sannan ya cire KAMBUN
SARAUTARsa na danyen zinare da lu'u lu'u dake
kansa ya dora mata akanta,sannan ya mike mata
sandarsa ta mulki ta karba.Kawai sai ya zube kasa
a
gabanta yayi gaisuwa mai nuna MUBAYA'A.Koda
ganin haka sai gaba dayan jama'ar dake cikin fadar
suka zube kasa gaban Gimbiya Aryala suna masu
jadda mubaya'arsu kamar yadda sukaga sarki
sa'ad yayi suna cewa cikin hadin baki munyi
MUBAYA'A
a
gareki ya sarauniyarmu!!!
KABEER LAWAL UMAR ROKED
Nan fa suka yi ta fadan
hakan har muryoyinsu suka cika birnin gaba
daya,jama'ar dake cikin gari ma da basu zo fadar
ba a wannan lokaci saida suka jiyo,kuma labari ya
riskesu da gaggawa cewa ai 'yar sarki sa'ad na
nan
a raye bata mutu ba,kuma gata nan ma a fada har
yayi murabus ya dorata akan karagar Mulkin Birnin
tare dayi mata mubaya'a.Nanfa Jama'a suka rude
da
shewa kuma akayi ta tururuwa zuwa fadar domin
su
wadanda basu ganta ba su ganta su ma kuma suyi
mubaya'a a gareta.A takaice dai a wannan rana
akayi bikin nadin gimbiya Aryala akan karagar mulki
akayi ta shagali.Makada da mawaka sukayi ta
bidirinsu,abinci da abinsha kuwa akayi ta
wadakarsu.Saida aka raba dare ana wannan
shagali
sannan jama'a suka watse suka tafi izuwa gidajensu
cikin farin ciki kowa na tofa albarkacin bakinsa.A
wannan lokaci ne sarki sa'ad ya tura aka kirawo
gimbiya Aryala da mahaifiyarta Zalima daga cikin
gidan sarautar suka kadaita a cikin turakarsa.Saida
gaba dayan hadiman sarki suka fice daga cikin
turakar aka kullo kofofi da tagogin turakar gaba
daya,ya zamana cewa saura su uku kacal!A cikin
turakar,sannan sarki sa'ad ya mike zaune da kyar
daga kan gadon da yake kwance yana mai yin
wani
irin tari mai zafi,ya dubi gimbiya Aryala yace,yake
'yata na sani cewa na jefa rayuwarki data
mahaifiyarki a cikin kunci da matsi bisa tsarewar
danayi muku a can gidana na bayan gari har
tsawon
shekaru goma sha biyu ba tare da kunsan dalilin
yin hakan ba?To ku sani cewa yanzu ne zan gaya
muku
dalilin da yasa nayi muku hakan.Da farko dai
inason
yanzu kije gaban wancan madubi ki dubi fuskarki
da siffar jikinki domin yaune ranar farko dazaki kalli
kanki a cikin madubi kiga baiwar da kike da
ita.Cikin
sanyin jiki da alamun tsananin tsoro gimbiya
Aryala
ta mike tsaye ta nufi inda madubin turakar
yake.Koda ta tsaya a gaban madubin ta kalli
fuskarta
da jikinta taga irin tsananin kyan da Allah ya
bata,sai hawaye ya zubo mata ta juya da dubi sarki
sa'ad tace yakai mahaifina,shin dama yanzu irin
wannan ce baiwar danake da ita amma ka boyewa
jama'armu ni har tsawin shekaru goma sha biyu?
Koda jin wannan tambaya sai hawaye ya zubowa
sarki sa'ad yace,yake 'yata ki sani cewa tun daga
ranar dana daukeku keda mahaifiyarki nakai ku
wannan gida nawa na bayan gari na killace
ku,kullum saina yi kuka saboda tsantsar bakin cikin
rabuwa da ku,kuma da bakim cikin rashim ganin
wannan kyakyawar fuskar Taki.Tun kafin na
haifeki
wani bokana ya taba bani labari cewa za'a haifa
mini kyakkyawar 'yar da babu kamar a kaf wannan
nahiya
gaba daya,amma idan har ban boye ta ba har
tsawon shekaru goma sha biyu ba to za'a rabani
da
ita ta karfin tsiya kuma bazata ta taba gadon
karagar
mulkina ba.To bisa wannan dalili ne yasa na
boyeku
a wannan gida har tsawon wadannan
shekaru,yanzu
ina fadan zaku gafarceni keda mahaifiyarki bisa
wannan babban laifi dana aikata muku,ni akaran
kaina banayi bane don na cuceku sai domin na
kyautata rayuwarku gaba daya dagani
harku,musamman ma ke Gimbiya.Koda sarki
sa'adda yazo nan a zancensa sai hawaye ya sake
zubowa gimbiya Aryala da mahaifiyarta Zalima suka
rungume sarki kuma suka kara fashewa da kukan
murna gaba dayansu.
ADMIN ROKED
Gimbiya Aryala tace,yakai
Abbana nima ka gafarceni bisa damuwar dana shiga
a dalilin wannan gata dakayi mana bisa rashin sani
ba,inda nasan cewa gata kayi mini domin ka tserar
da rayuwata don na gajeka daban damu ba daidai
da rana daya,maimakon hakan zai zamo kowanne
lokaci ina cikin farin ciki mara misaltuwa.Koda jin
wannan batu sai sarki sa'ad yayi guntun murmushi
a lokacin da tari ya sarkeshi kamar zai
mutu,idanunsa sun zazzaro sun fara juyewa har
gudan jini ya subuto daga cikin bakinsa.Al'amarin
daya firgita gimbiya Aryala da mahaifiyarta Zalima
kenan,suka dimauce da matsanancin tashin hankali
ga firgici.Zalima ta yunkura domin ta ruga ta
kirawo
likita,amma sai sarki sa'ad yayi sauri cikin dauriya
ya riko hannunta ya dakatar da ita tare da dubanta
a lokacin da idanuwansa suka kada sukayi jajur
tamakar garwashin wuta,ya bude bakinsa dakyar
cikin dauriya yace,yake matata kiyi sani cewa bakin
alkalami ya riga ya bushe,babu tantama ko jayayya
mutuwa zanyi,don haka babu wani magani da zai
iya warkar mini da wannan ciwo nawa,kawai saidai
jiran
lokaci.Inason ku saurara da kyau kuji abinda zan
gaya muke keda gimbiya Aryala.Yayi shiru yana
mayar da numfashi sannan ya dawo da dubansa
ga gimbiya Aryala yace,yake 'yata ki sani cewa
bincike
ya tabbatar da cewa baza kiyi aure ba har izuwa
lokacin da zaki gushe,amma kuma zaki haifi 'da
namiji wanda zai sami daukakar da babu mai
kamarta a wannan
zamani.Ki kasance mai hakuri bisa duk irin kaddarar
da zata sameki,kuma ki rungumi danki hannu
bibbiyu kada ki tsaneshi ko ki tsani ubansa da yayi
sanadin zuwansa duniya.Koda sarki Sa'ad yazo
nan
a zancensa sai hawayen takaici ya zubowa Gimbiya
Aryala ta dubeshi tace,ya kai Abbana yanzu kenan
ni
zan haifi dan da bata hanyar aure aka sameshi ba?
Ai
wannan babban abin kunya ne kuma abin gori ga
wannan masarauta tamu wanda bazai taba
gushewa
ba har abanda?Sa'adda sarki sa'ad yaji wannan
batu
sai ya girgiza kai yace,a matsayinki na jarumar
dazatayi abin al'ajabin da babu wani jarumi daya
taba yi a wannan nahiya,to ina tabbatar miki babu
wani abu na kunya ko gari dazai kasance a
gareki.Koda gama fadin hakan sai sarki sa'ad ya
zura hannu a karkashin matashin kan gadonsa ya
dauko wata wasika ya mikawa gimbiya Aryala.Nan
take gimbiya Aryala ta karbi wasikar ta warwareta ta
karanceta tsaf,cikin tsananin mamaki ta dago kanta
bayan takai karshen wasikar ta dubi sarki tace
haba
yakai Abbana yaya zakace nayi shiri na tafi izuwa
birnin kisra na wakilceka a gaiyatar da sarki uzaima
yayi maka alhalin kana cikin wannan hali na rashin
lafiya.Sarki sa'ad ya numfasa yace zuwanki
wannan
gaiyata shine zai daukaka darajarki a duniya don
haka bani da wani buri da yafi kije ki halarci wannan
taro.Kamar yadda kika gani a cikin wannan
wasikar
akwai GASAR JARUMTAKA wacce sarki uzaima ya
shirya akan cewa duk jarumin daya kaishi kas ko
yayi masa rauni zai bashi duk abinda yakeso,inaso
ki shiga wannan gasa kema a fafata dake.Koda jin
haka sai idanun Gimbiya Aryala dana mahaifiyarta
Zalima suka zazzaro suka dubi sarki sa'ad cikin
firgici da mamaki.Gimbiya Aryala ta budi baki tace
yakai Abbana saboda me zakace na shiga wannan
gasa tayin gumurzu da sarki uzaima alhalin tun ina
yarinya karama nake jin labarin irin gagarumar
jarumtakarsa?Ance fa tunda yake bai taba zuwa
kasa
ba a filin fama,ta yaya nidana kasance ban taba yin
yaki da mutane ba zakace naje na tareshi har mu
fafata.Sarki sa'ad ya daga hannunsa da kyar ya
dora
akan kafadar gimbiya Aryala yace yake 'yata kiyi
sani
cewa matsoraci baya zama gwani har abada.Don
haka kada ki yarda har abada zuciyarki ta karaya
bisa duk abinda kika sa a gabanki.Daga Yau na
umarceki da ki zama MACE MAI KAMAR
MAZA,domin hakan ne kadai zaisa wannan
MASARAUTA tamu ta wannan gari namu yacigaba
da
wanzuwa a doron kasa.Inason ki fara shirin wannan
tafiya dun daga daren yau domin gobe da sassafe
zaki tafi izuwa birnin Kisra.Zaki tafi tare da dakaru
dubu uku kacal,wadanda zasuyi miki rakiya,kuma
akan keken dokin masarauta zaki tafi dauke da
tutar birninmu a matsayinki na sabuwar
sarauniyarmu.Kada ki boye fuskarki ko kyanki
kuma
ki saki ranki cewa kin fita yakin kare mutuncin
masarautarmu ne da rayuwar jama'ar kasarmu
....
.....
By AL MUSTAPHA Isah Inkiya #MUSTINDOO #PRABHAS kuhuta lfy KASUWAR RAYUKA!!!
Littafi na Daya (1)
Part D
Kin fita yakin kare mutuncin masarautarmu ne da
rayuwar jama'ar kasarmu.Koda jin wannan batu sai
gimbiya Aryala taji dukkan wani tsoro yakau daga
cikin zuciyarta kuma taji cewar zata iya sallama
rayuwarta don kare lafiyar karagarta ta mulki da
kuma jama'arta,don haka saita rungume sarki
sa'ad
tana mai zubar da hawaye tace,yakai Abbana nayi
maka alkawari cewa lallai daga yau na kau da
dukkan tsoro daga cikin raina bisa duk abinda
nasa
a gabana kuma zanyi wannan tafiya cikin burin
samun nasara.Abinda zan rokeka guda daya ne
jal,inason ka rayu har naje na dawo daga wannan
tafiya

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2Chapter 3Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment