Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

domin idanunka suga arzikin dazan zo dashi
gami da nasarar dana samo.Koda jin wannan batu
sai farin ciki ya lullube sarki sa'ad ya rungume
sarauniya Aryala yana maiyi mata godiya gami
dasa
mata albarka.Kashe gari kuwa tun kafin alfijir ya
keto aka gama shirin dakarun daza suyiwa
sarauniya
Aryala rakiya izuwa birnin kisra kuma aka shirya
guzuri gami da bayi da kuyangi da zasu yi mata
hidama.Kamar yadda sarki sa'ad ya fada haka aka
shirya wato a cikin keken dokin masarautar
sarauniya Aryala ta tafi birnin kisra don amsa
gaiyatar sarki Uzaima.Nan fa suka kama tafiya
suna
masu ratsa dazuzzuka,birane da kauyuka da
garuruwa har tsawon kwana goma sha daya ba
tare dasun hadu da wani mugun abu ba.A ranar
kwana
na goma sha dayan ne da yammaci kafin rana ta
fadi suka yada zango a wani daji a bakin wata
fadama.Tun kafin a yada zango ne shugaban
dakarun wani Barde da ake kira Husam ya dubi
sarauniya Aryala yace,ya shugabata wannan daji da
muka yada zango a cikinsa daji ne mai hadari ana
yawan yin fashi a cikinsa kuma yan fashin dake
cikinsa suna da yawan gaske zasu iya ninka
adadinmu sau goma.Koda jin wannan batu sai
sarauniya Aryala tayi murmushi yace,yakai Husam
ka kwantar da hankalinka kuma na umarceka kai
da
dakarunka duk kuje ku kwanta kuyi barcinku ni
zanyi
gadin kowa.
ADMIN KE MAGANA
Koda jin haka sai Husam ya zube kasa
bisa guiwarsa guda daya kansa na sunkuye yace,ki
gafarcemu ya shugabata ai bamu isa muje mu
kwanta ba ke kiyi gadinmu muna matsayin
bayinki.Cikin fishi sarauniya Aryala ta dakawa
Husam
tsawa tace idan ma bazaku iya barci ba to kawai
ku zuba ido kuga yadda zanyi da duk masu
tsautsayin
da suka kawo mana hari.Wannan umarni ne na
baku
bawai rokonku nayi ba.Koda jin haka sai hankalin
barde Husam ya dugunzuma ainun saboda shidai
bai taba ganin sarauniya Aryala tyi yaki ba bare
yasan irin jarumtakarta kuma yasan cewa idan
lafiyarta ta tabu ko rayuwarta ta salwanta shida
duk
dakarunsa basu isa su koma gida ba,in kuwa suka
koma sai sarki sa'ad yasa an kashesu idan baiga
'yarsa ba saidai idan sun iske baya raye.Cikin
alamun tsananin damuwa da sanyi jiki barde
Husam
ya mike tsaye ya koma gefe daya.Sarauniya Aryala
ta fito daga cikin keken dokin nata sannan ta dubi
gabas da yamma kudu da arewa na dajin ta gama
nazarinsa,sai ta dubi Barde Husam tace ka raba
yaranka biyu kaso daya suje su saro itatiwa masu
tsawo su katange sansani namu suyi mana kofa ta
shiga da fita.Daya kason kuma suka kama aiki
kafin
cikar sa'a biyu da rabi sun kammala.Sarauniya
Aryala ta sake duban barde Husam tace,yanzu kuma
ina son kasa a kafa mutum mutumi na dakaru a
cikin kowacce kusurwa na sansanin nan masu
yawa
kuma a kunna fitilun itace da yawa su haskake ko
ina.Inason gaba dayanku ku fice daga cikin
sansanin
ku barni ni kadai a cikinsa.Koda jin haka sai
idanun
barde Husam suka zazzaro ya dubi gimbiya Aryala
cikin kaduwa da firgici yace,haba ya shugabata ai
wannan ganganci ne kuma sai da rai ne.Sarauniya
Aryala ta sake dakawa Barde Husam tsawa
tace,idan
ka sake nuna mini karayarka ko ka sabawa
umarnina
zan sallameka ka koma gida.
ADMIN DR KABEER LAWAL UMAR ROKED
Cikin rawar murya
Husam ya zube kasa yana mai cewa tuba nake ya
shugabata.Nan da nan cikin hanzari aka aikata duk
abinda sarauniya Aryala ta bayar da umarni ya
zamana cewa gaba dayan dakarun da hadiman
sarauniya Aryala suka fice daga cikin sansanin aka
barta ita kadai a cikin tantinta,su kuma su Husam
sai suka je nesa kadan da sansanin suka kwanta a
cikin wata duhuwa mai kwazazzabai wacce baza'a
taba tunanin cewa mutum zai shiga wajen ba,suka
zuba ido suna kallon can inda sansanin yake cikin
tsananin tsoro da fargaba aka rasa mutum daya
wanda zai iya runtsawa har yayi barci.Har dare ya
fara rabawa shiru ba'a ji motsin komai ba,kuma
ba'a
ga komai ba.Ba tare da fargabar komai ba kuwa
sarauniya Aryala ta shiga cikin tantinta ta kwanta ta
kama barci abindata harda minshari tamkar tana
cikin gidan sarautarta.Kwat
sam! Ba zato ba
tsammani sai su Barde Husam suka jiyo wani irin
takun sawaye mai karfi mai ban tsoro wanda
mutum
bazai iya tantacewa kona mutane ne kona
dabbabo kuma akwai alamun cewa sawayen suna
guda
ne.Cikin kankanin lokaci saiga wadansu dakarun
sumame su dayawa ba adadi wasunsu akan
dawakai
suke wasu kuma akan giwaye suka dukkaninsu
suna dauke mugayen makaman yaki.Tunda Barde
Husam
ke fita yaki gami da yawace ywacen da yayi a
duniya
bai taba ganin yan fashi masu kwarjini da kayan
aiki kamar wadannan ba.Cikin tsananin tsoro Barde
Husam da sauran dakarunsa suka sake kwanciya a
cikin duhuwar da suka kwanta suna masu dade
buya.Ta gabansu wannan runduna ta yan fashi
suka
wuce sukaje suka yiwa sansanin KAWANYA.Ko
shugaban yan fashin yaga ashe dakarun mutum
mutumi ne zagaye da sansanin sai ransa ya baci
ya
budi baki da nufin ya baiwa dakarun nasa umarnin
su bazama neman inda su Husam suka buya
kawai sai yaga sarauniya Aryala ta fito daga cikin
tantinta,kawai sai ta gyara tsayuwarta tana mai rike
da kugunta cikin gadara ta
dubi shugaban yan fashin nan ta daka masa tsawa
tace,kai kuma waye har dazaka zo ka katse mini
barcina a cikin wannan dare da karar sawayen
ababan hawanku?Ka debo gayyar wadansu
banzayen
dakaru naka matsoratan banza da basa iya kawo
hari ido na ganin ido sai dare ya raba....Kafin
sarauniya Aryala ta gama ruge bakinta tuni
shugaban yan fashin ya fusata ainun ya tari
numfashinta yana mai daka mata tsawa yace,ke
kuma wace daga cikin masu fada aji a wannan
zamani har da zaki dubemu kiyi mana rashin
kunya.Waishin ma ke kike takama dashi har da
zaki
fito ke kadai ki fuskanci wannan runduna
tamu.Sarauniya Aryala ta dubeshi cikin gadara
tace,nice sarauniya Aryala ibini sa'ad dan hussein
mai mulkin birnin Nurul Ansar kafin yayi mubaya'a
ya nadani a matsayin sabuwar sarauniyar birnin
nurul ansar.Ina gaggauta shawartakarka da kayi
gaggawar janye wadanann kananun dakarun naka
ku
bace mini da gani in ba haka ba kuwa daga yau
kun
daina yin wannan mumunar sana'a taku ta fashi da
zalunci.Koda sarauniya Aryala tazo nan a zancenta
sai shugaban yan fashin ya bushe da wata
mahaukaciyar dariya yace,waishin ke yanzu a
tunaninki da haukani kina ganin cewa dabarar da
kikayi ta boye dakarunki a wani wurin zatasa ki
kubuta daga sharrinmu?To idan baki sani ba ki
sani cewa gaba daya dajin nan ma a kewaye yake
da
yarana babu ta inda zaku iya guduwa ku
tsira,kuma
koda tsohon mahaifinki da dukkan sauran
dakarun
birninku zasu kawo muku dauki bazasu iya tsira
daga dandanon mutuwar da zamu shayar daku
ba...Sarauniya Aryala ta katse shi ta hanyar daka
masa tsawa tace,kai wulakantacce mahaifina da
dakarun birninmu sunfi karfinku,nidin nan da
kuke
gani na isheku ba sai dakaruna sun taimaka mini
ba,idan kuma kuna shakka to GA FILI GA MAI DOKI
ku gwada ku gani sai ku tantance tsakanin AYA DA
TSAKUWA.Koda Sarauniya Aryala tazo nan a
zancenta sai ta zaro tagwayen masu daga gadon
bayanta ta gyara tsayuwarta tana jiran taga ta inda
za'a fara kawo mata hari.Koda ganin gaka sai
shugaban yan fashin ya bushe da dariyar mugunta
a
karo na biyu sannan ya kada linzamin dokinsa ya
juya da baya yana mai kutsawa ta cikin tsakiyar
dakarunsa tamkar tafiya zasuyi,amma saiyaja
linzamin dokin nasa ya tsaya cak yace ina
maharbana?Na umarceku dakuyi ta sakar mata
ruwan kibiyoyi har sai jikinta ya cika da kibiyoyin
da
babu masakar tsinke.Koda jin wannan umarni sai
maharban kibbau suka zaro kibiyoyinsu daga cikin
kwanson kibiyoyin dake rataye a gadon bayansu
suka dana akan zaren kwarin suka fara sakarwa
sarauniya Ayala hari cikin sauri da zafin
nama.Nanfa
dubunnan kibiyoyi sukayi kan sarauniya Aryala a
guje zasu cake a jikinta.
Ganin ruwan kibiyoyin da aka harbo mata yasa na
tsaya cak.
na rasa abinyi naje na taimaka mata ne ko na tsaya
naci gaba da daukar rahoto

.....

By AL MUSTAPHA Isah KASUWAR RAYUKA!!!
Littafi na Daya (1)
Part E.
Nan fa dubunnan kibiyoyi sukayi kan sarauniyar
Aryala a guje zasu cake a jikinta.Cikin tsananin zafin
nama sarauniya Aryala ta daka tsalle sama ta rinka
kade kibiyoyin da masun hannunta kuma ta nufo
inda shugaban yan fashin yake a sama.Nanfa su
Barde Husam dake labe a cikin duhuwa suka
hango duk abinda ke faruwa suka cika da tsantar
mamakin
sarauniya Aryala bisa ganin irin wannan
gagarumar
jarumtaka da bajinta da takeyi domin duk ruwan
kibiyoyin da ake harba mata ko guda daya bata
shiga jikinta ba.Kawai sai gani akayi sarauniya
Aryala ta daki kirjin shugaban yan fashin da kafarta
guda.Duk da cewa shugaban yan fashin ya
kasance
narkeken katon gaske sai gashi ya hantsilo kasa
daga kan dokinsa.
ADMIN #MUSTINDOO KE MAGANA
Ita kuwa sarauniya Aryala maimakon ta duro kasa
sai ta taka gadon bayan
dokin shugaban yan fashin tayi sama,a saman
kuma
ta rinka kawai dakarunsa sara da suka ta rinka
shawagi a kansu tamkar tsuntsuwa mai fuka fukai
sai gashi tana ragargazarsu suna zubowa kasa daga
kan dawakansu tamkar ana sassabe a gona.Cikin
tsananin fishi shugaban yan fashin ma ya mike
tsaye zumbur ya daka tsalle sama ya tareta suka
ruguntsume da masifaffen yaki,sai gashi sarauniya
Aryala tana yin yakin bangare biyu,ma'ana tana yakar
dakarun kuma tana yakar
shugabansu,kuma
ko sau daya bata bari kafarta ta taba turba ba
saidai
kaga tana taka kan dakarunda gadon bayan
dawakansu saboda tsananin zafin namanta da
jarumtakarta.Babu abinda yafi daurewa su Barde
Husam da sauran dakarunsa kai sama da yadda
sarauniya Aryala ke sarrafa jikinta a sama tana
wurkilashi tamkar ta kasance mazari abin burgawa
da hannu ko filfiluwa abar wasan yara.Duk da
cewa shima shugaban yan fashin ya kasance
gawurtaccen
jarumi mai tsananin karfin damtse,jarumtaka,naci
da
iya yaki,sai gashi ya kasa koda lakutar jikin
sarauniya Aryala,itama kuma ta kasa cutar
dashi,domin duk harin data kawo masa walau da
makami ko da hannayenta koda kafarta yana iya
karewa,saidai inda gizon ke sakar shine cigaba
take
da yiwa dakarunsa sarki ya hana dawa tsaiwa
domin girbar kawunansu take kawai,saidai kaga jini
na
feshi
da fallatsi ta cikin dungulmin wuya,gangar jiki na
subutowa kasa daga kan doki.A cikin abinda bai
wuce rabin sa'a ba sai gashi sarauniya Aryala ta
kashe sama da dakaru dubu bakwai.Kaico!Wuya
mai
sa dole!Kuma Sa Gudu Maganin Ki Gudu!!
Koda
dakarun yan fashin nan sukaga irin mummunar
barnar da sarauniya Aryala keyi musu ta zama
tamkar GUGUWAR ANNOBA mai saukar da mutuwa
a
tsakiyarsu,ko kuma shaidaniya mai karar da
dangi,sai suka firgita suka fara zubar da
makamansu
suna ranta ana kare!Koda ganin haka sai shugaban
yan fashin ya fusata ainun,ya daka musu karkarfar
tsawa yana mai umartarsu da lallai su daina
guduwa
su tsaya,amma ina kamar ma kara tunzurasu
yakeyi domin maimakon su tsaya sai kara karfin
gudun
suke yi don tsira da rayukansu.Al'amarin daya
kara
fusata shugaban yan fashin kenan ainun,kawai sai
ya
daina yaki da sarauniya Aryala ya tayata ragargazar
yaran nasa dake neman gudu.Koda sarauniya
Aryala
taga shugaban yan fashin ya kama sara da sukan
yaransa sai ta sauko kasa ta dira bisa dokinta ta
zuba masa idanu sai gashi dakarun nasa sun kara
kaimin guduwa daga filin yakin kafin kace me duk
sun arce babu dayansu a wajen face gawarwakin
yan
uwansu saishi shugaban nasu shi kadai a tsaye
yana haki da huci tamkar mesa yana mai fuskanta
sarauniya Aryala suna kallon juna.Abinda daya
batawa shugaban yan fashin rai shine yau kusan
shekaru ashirin da daya kenan yana jagorantar
wannan runduna ta yanfashi a wannan daji bai
taba
ganin rashin sa'a ba irin ta wannan rana,domin
komai yawan dakaru ko ayari na fatake sai sun
tarwatsa su sun kwashe dukiyoyinsu amma sai
gashi yarinya karama wacce batafi shekara goma
sha ba ta ragargajesu ita kadai ta
tarwatsasu.Al'amarin dayai matukar bashi mamaki
kenan har ya fara tunanin cewa anya kuwa
wannan jarumar budurwar mutum ce ba Aljana
bace?Abu
na
farko dai gata da kuruciya amma sai masifaffiyar
jarumtaka da bajinta da kuma tsantsar iya
yaki.Kawai sai wata zuciyar tace dashi ai kuwa ko
aljanar ce yau sai yaga abinda ya turewa buzu
nadi,tunda shima ya yarda da kansa a fannin
jarumtaka,bajinta da iya yaki da kuma karfin sihirin
tsafi,duk da cewa a lokacin daya fara gumurzu da
sarauniya Aryala akwai wani abu dayai matukar
bashi mamaki.Ba wani abu bane ya bashi mamakin
ba face sihirin tsafi baya tasiri akan sarauniya Aryala
kumababu alamar cewa tana amfani da tsafi a
cikin
jarumtakarta.Bayan anyi kallon kallo na tsawon
yan
dakiku masu yawa tsakanin wannan shugaban yan
fashi da sarauniya Aryala sai lokaci guda duk su
biyun suka sake rugawa izuwa kan juna kamar
hadin
baki suna haduwa suka sake kacamewa da
masifaffen azababben yaki mai tsananin ban tsoro
tamkar zasu cinye junansu.Ita kanta sarauniya
Aryala sai taji tana matukar mamakin jarumtakar
data keyi a wannan rana a matsayin gumurzunta
na
farko da bil'adam,saboda ita dai bata saba yin
gumurzu da mutane ba sai dabbobi,dodanni da
aljanu a cikin daji tana tarwatsasu tamkar an baje
kayan koli a kasuwa.Saida Sarauniya Aryala da
shugaban yan fashin suka shafe dakika dari hudu
da
sittin da uku suna kaiwa junansu sara da suka
gami da naushi da bugun juna cikin bakin zafin
nama
da
gagarumar jarumtaka sannan sarauniya Aryala ta
sami nasarar yi masa barin makauniya a fuska da
kafarta ta dama a lokacin da tayi wata irin
katantanwa a samansa cikin shammace.Saboda
karfin dukan fuskar tasa datayi saida yai sama da
baya shima yayi katantanwa sau bakwai a saman
sannan ya fado kasa tim!.A lokacin da hakorinsa
guda na sama yayi fitar burgu daga cikin bakinsa
tare da wani gudan jini
.......
.......
........
Abun mamaki mace take suburbudar namji haka to ai shikenan mukafta
Naku har Kullun AL MUSTAPHA Isah Inkiya #MUSTINDOO #PRABHAS saida safe KASUWAR RAYUKA!!!
Littafi na Daya (1)
Part F.
A lokacin da hakorinsa guda na sama yayi fitar
burgu daga cikin bakinsa tare da wani gudan
jini.Saboda tsananin jigatar da yayi a lokacin dayaji
kansa yai masa nauyi tamkar an dora masa dakon
katon dutse sai ya kasa mikewa tsaye ya kife a
kasa
da rub da ciki.Kawai sai sarauniya Aryala ta
dunkule hannayenta cikin hammatarta ta zuba masa
idanu
tana maiyin murmushin farinciki bisa ganin nasarar
data samu.Cikin tsananin takaici da bakin ciki
shugaban yan fashin ya yunkura ya mike tsaye ya
kwarara uban ihu kamar zai sake rugawa gareta su
cigaba da yakin,kawai sai ya durkusa kasa bisa
guiwoyinsa a lokacin da hawaye ya zubo masa ya
dubeta yace,yake wannan jaruma mai ban al'ajabi
na
rantse da darajar iyayena kece jaruma ta farko data
taba kaini kasa a filin fama.Kisani cewa hatta sarki
Uzaima na birnin kisra sau uku muna fafata kazamin
gumurzu ni dashi a wannan daji har sama da
tsawon sa'a uku amma bai taba kaini kas ba,nima
kuma ban taba kaishi kas ba saidai a karshe mu
hakura da yakar juna kowa ya kama
gabansa,amma yau gashi ke kin kaini kas,har ma
kin fitar da jini
daga jikina kin janyo min asarar hakorina guda.Na
rantse da darajar iyayena da kakannina tunda har
kika karya lagona daga yau na zama bawanki,ina
mai rokonki daki karbeni a matsayin shugaban
dakarunki mai tsaron lafiyarki,domin daga yau na
daina sata da fashi ke nan har abada.A daidai
wannan lokaci ne Barde Husam da sauran dakarun
sarauniya Aryala suka ruga daga inda suke boye a
cikin duhuwa sukazo bayan sarauniya Aryala suka
tsaitsaya.Barde Husam ya yiwa sarauniya Aryala
rada a kunne yace,ya shugabata kada ki yarda da
wannan tsohon azzalumin dan fashi wanda ya
shafe
kusan shekaru ashirin yana hana mutane sakat a
wannan daji,in banda sarki Uzaima babu wani
mahaluki daya taba ratsawa ta cikin wannan daji
lafiya ba tare daya rasa dukiyarsa da lafiyarsa
ba.Sa'adda sarauniya Aryala taji wannan batu na
shugaban dakarunta wato Barde Husam sai tayi
murmushi sannan ta dubeshi tace,kuskure ne a ki
karbar tuban mai laifi,domin yin hakan zaisa a
tunzura shi ya cigaba da aikata laifin daya saba
yi.Tana gama fadin hakan sai ta dubi shugaban yan
fashin tace,menene sunanka?Shugaban yan fashin
yace sunana DAMZUR BIN AUKAS.Sarauniya Aryala
tayi masa dan guntun murmushi sannan tace,na
karbi bukatarka amma bisa sharadi guda.
KABEER LAWAL UMAR ROKED
Sharadin kuwa shine idan kaci amanata ko kuma ka
cutar
da
mutum daya daga cikin jama'ata ba tare da izinina
ba zan kasheka.Ka sani cewa ni mutum ce mai iya
zuba idanu akan mutum kamar yadda uwa ke kula
da jaririnta.Koda gama fadin hakan sai sarauniya
Aryala ta dubi barde Husam tace a baiwa jarumi
Damzur bin Aukas tufafi irin na dakarunmu ya
sanya
daga yau ya zama mai tsaron lafiyata.Cikin
tsananin
firgici barde Husam ya kwalalo idanu kuma ya
wangame baki ya kasa cewa komai.Jikinsa na
tsuma
yaje ya dauko tufafi irin wanda ke sanye a
jikinsa,wato dakarunsu ya kawowa jarumi
Damzur,shi kuwa jarumi Damzur sai ya karbi
tufafin yana mai tsananin murna.Nan take yasa
hannu ya
yage rigar jikinsa yayi jifa da ita ya sanya wannan
tufafi da aka bashi yaje ya tsaya a bayan sarauniya
Aryala yana muzurai da kalle kalle don tsaron
lafiyarta,kai kace dama can shine mai tsaron
lafiyarta ta.Sarauniya Aryala ta dubeshi cikin
murmushi
tace,tabbas aikin dana baka ya dace dakai.A
cigaba
da tafiya.Tana gama fadin hakan sai ta nufi keken
dokinta ta shiga ta zauna.A guje Jarumi Damzur ya
ruga ya kamo dokinsa ya hau yazo daf da keken
dokin sarauniya Aryala ya tsaya a bangaren
damanta.Shi kuwa barde Husam sai ya koma
bangaren hagunta aka fara tafiya.Ana cikin tafiyar
ne
sarauniya Aryala ta leko da kanta ta cikin tagar
keken dokin bangaren hagu ta dubi barde Husam
tace,daga yau Damzur ne shugabanku gaba daya
kuma shine zai rinka baku horo na yaki,don haka
albashinsa ya ninka na kowa sau uku.Koda jarumi
Damzur yaji wannan albishir a cikin kunnensa sai
ya
kurma ihun farinciki yayi godiya ga sarauniya Aryala
kuma ya shiga yi mata kirari yana mai cewa:"Ga
sarauniyar Duniya mai haska kowa!Kece mace mai
kamar maza!Kece tauraruwar wannan zamani!Kece
shugabar kyawawan wannan zamani!Kece jarumar
jarumai!Ko dubu ta taru albarka!Kece shugabar
attajiran duniya mai kyautar ban mamaki!Kece mai
ladabtar da barawo yayi tuban dole...!!!Koda
Jarumi
Damzur yazo nan a kirarinsa sai dariya ta kwacewa
kowa a cikin tawagar aka kama kyakyatawa.
MAI ZAI FARU IDAN SU SARAUNUYA ARYALA SUKA
KARASA BIRNIN KISRA DOMIN WAKILTAR
MAHAIFINTA SARKI SA'AD WAJEN GAYYATAR DA
SARKI UZAIMA YAYI MASA NA MURNAR CIKAR
SHEKARUNSA ASHIRIN AKAN MULKI?
WA ZAI LASHE GASAR JARUMTAKA DA SARKI
YASA WADDA ZA'A GABATAR RANAR BIKIN
MURNAR?
SHIN SARAUNIYA ARYALA ZATA DAWO TA TARAR
DA MAHAIFINTA SARKI SA'AD A RAYE?
YAUSHE SARAUNIYA ARYALA ZATA SAMU CIKI BA
TARE DA AURE BA HAR TA HAIFI DAN DAZAI
SAMU DAUKAKA A DUNIYA.?
Mu hadu A KASUWAR RAYUKA kashi na biyu(2)
don
jin cigaban wannan kayataccen kasaitaccen labari.
......
.....
Naku Har Kullun AL MUSTAPHA Isah Inkiya #MUSTINDOO #PRABHAS kuhuta lfy
KASUWAR RAYUKA!!!
Littafi na Biyu (2)
Part A.
LOKACIN da tawagar Sarauniya Aryala suka cigaba
da tafiya suna ratsa dajijjika,kowannensu ka kalleshi
zakaga alamun kwanciyar hankali da annashuwa
gami da nutsuwa a tare dashi.Haka suka cigaba da
tafiya cikin nutsuwa har aka shafe yan kwanaki
aka
iso birnin Kisra,ba'a sake haduwa da wani tsautsayi
ko wani mugun abu ba.Duk da cewa birnin Nurul
Ansar gari ne dan babba,kuma kwatacce,amma da
shigowar sarauniya Aryala sai ta gane cewa ruwa
ba
sa'an kwando bane,saboda birnin kisra ya ninka
birninsu na nurul ansar sau uku a girma,ginuwa a
kawatuwa.Batun arziki kuwa da tarin al'umma sai
taga kamar a dauko kwayar hatsi guda daya jal!A
karata a kusa da buhun maiwa,
DR ROKED KEMAGANA
wato dai a takaice
bambancin dake tsakaninsu a baiyane yake.Da
shigowarsu cikin birnin Kisra suka gane cewa lallai
akwai babban taro da akeyi a birnin,domin garin
ya
cika ya batse da al'umma ba masakar tsinke,duk
inda mutum ya hanga baya ganin komai sai
dandazon kawunan bil'adam rututu.Kai!Hatta
hanyar wucewa ma da karfin tsiya dakaru ke buda
jama'a
sannan ake samu a wuce.Nanfa sarauniya Aryala ta
rinka ganin tawaga tawaga ta sarakai suna ta biyo
bayan tasu,wasu kuwa ma tuni suna gabansu.Da
yake ita tana cikin keken doki ne,kuma dakarunta
na dauke da tutar birnin nurul ansar sai aka zata
cewa
sarki sa'ad ne yazo da kansa duk da cewa ansan
cewa yana kwance cikin halin rashin lafiya.Haka
dai
aka cigaba da tafiya aka ratsa ta tsakiyar kasuwar
birnin kisra.Koda sarauniya Aryala taga yadda
girman kasuwar yake cike da rumfuna ga yan
kasuwa sun baje kayyakinsu tuli ba adadi,kuma ga
fatake ana ta cinikayya sai taji batada wani buri a
duniya wanda yafi ta habaka kasuwancin birninta
yakai koda rabin na wannan birnin ne."Ta yaya
zan iya cimma burina?Amsar data kasa baiwa kanta
kenan.Nan dai gaba dayan tawagogin sarakunan
suka iso kofar gidan sarautar birnin kisra.Koda
sarauniya Aryala ta leko da fuskarta kadan ta dubi
kofar gidan sarautar wacce ita kanta anyi tane da
zallan karfen lu'u lu'u gata katuwa mai tsawo da
fadi
saita gyada kai cikin alamun takaici tace,ashe dai
ni
da a kauye nake ban sani ba?Ai kuwa idanunta na
kaiwa kan ginin masarautar sai ta dimauce kuma ta
cika da tsananin mamaki,saboda ganin irin aljannar
duniyar da aka shirya.Tace a ranta,lallai ashe ma
mu
miskinai ne ba sarakai ba akan sarki Uzaima!Duk
sarkin daya iso kofar gidan sarautar birnin kisra
sai fadawan sarki uzaima su tareshi suyi masa
barka
da
zuwa kuma sai ya fito daga cikin keken dokinsa ya
gaisa da manyan fadawan sarki uzaima sannan a
bashi takarda da alkalami ya rubuta sunansa,kuma
ya buga hatiminsa,sannan ne za'ayi masa jagora
izuwa masaukinsa dake cikin gidan sarautar.Haka
aka cigaba da saukar sarakuna har akazo kan
sarauniya Aryala amma ita da akazo kanta sai taki
fitowa daga cikin keken dokin,dama tun kafin su
iso
ta baiwa jarumi Damzur umarnin ya wakilceta a
komai.Shidai jarumi Damzur mutum ne mai
matukar
kwarjini da cika idanu,don haka mutane ma basa
iya
hada ido dashi sau biyu.Da isowar keken dokin
sarauniya Aryala gaban kofar da fadawan sarki
uzaima ke tsaitsaye sai jarumi Damzur yai sauri ya
sauko daga kan dokinsa yazo gaban fadawan ya
tsaya ya mika musu dannu don su gaisa.Cikin
kaduwa da mamaki gaba dayan fadawan suka dan
ja
da baya kadan a tsorace,sannan daya daga cikinsu
yayi karfin hali ya dubi jarumi Damzur yace,me
yasa
sarkin naka bai fito ba daga cikin keken dokinsa
baya wakiltoka alhalin ba haka dukkan sauran
sarakunan da suka fi sarkin naka daukaka da
girman masarauta sukayi ba?Cikin daurewar fuskar
da
alamun fishi jarumi Damzur yace,waye a nahiyar
nan
baisan cewa sarki sa'ad na birnin nurul ansar yana
cikin halon rashin lafiya ba?Ku bani takarda nasa
hannu na buga hatiminsa,umarnin daya bani
kenan,don haka bazai iya fitowa ba da kansa.Koda
jin wannan batu sai bafaden da ke rike da takardar
ya matso da sauri gaban jarumi Damzur jikinsa na
tsuma ya bashi ya rubuta sunan sarki sa'ad kuma
ya buga hatiminsa.Ba tare da bata wani lokaci ba
aka basu dan jagora wanda zai kaisu izuwa
masaukinsu aka bude musu kofa suka shige cikin
gidan sarautar.Nanfa gaba dayan jama'ar dake
cikin
kofar gidan sarautar sukabi Jarumi Damzur da
kallo
saboda gaba dayan dakarun sarakunan da suka
shigo birnin babu wani badakare mai
girmansa,kwarjininsa da kirarsa ta jarumtaka.Da
yawa daga cikin irin mutanen da suka taba ratsawa
ta cikin dajin da yake fashi suka tsira da rayuwarsu
sai suka kura masa idanu suna son su tuno a inda
suka sanshi,amma sai suka kasa tunowa saboda
tsananin kwarjininsa da tsoron hada idanu
dashi.Bayan an gama saukar dukkanin sarakunan
da
suka shigo birnin kisra da kuma dukkanin jarumai
da sadaukan da sukazo domin su shiga GASAR
JARUMTAKA daza suyi da sarki Uzaima,an gama
rubuta sunan kowa da hatiminsa da sunan
kasarsa,sai aka kaiwa sarki Uzaima takardar ya fara
dubawa.Takardun a ware suke,ta jarumai da
sadaukai daban,ta attajirai ma daban,haka ta
sarakuna,don haka ana kai masa wadannan
takardu takardar sarakan ya fara dubawa,koda yayi
kicibus
da sunan sarki sa'ad na birnin nurul ansar sai ya
cika da tsananin mamaki saboda yana da labarin
halin da yake ciki na tsananin rashin lafiya wanda
yakai matsayin saidai a kwantar dashi a tayar
dashi baya iya yiwa kansa komai saidai ayi
masa.Cikin
mamaki sarki Uzaima ya dubi fadawansa yace,shin
da gaske sarki sa'ad da kansa ya halarci wannan
gaiyata wata?
DOCTOR KABEER NE
Wazirin sarki uzaima yayi gyaran
murya yace,ya shugabana mu dai munga keken
dokinsa amma wani babban badakarensa ne ya
wakilceshi ya rubuta sunansa da suna
Birninsa sannan ya buga hatiminsa,amma mu
bamu
ganshi da idanunmu ba tunda ance yana cikin
keken
doki a kwance bazai iya fitowa na yazo ya rubuta
da
kansa ba saboda halin rashin lafiyar da yake
ciki.Sarki Uzaima yayi ajiyar numfashi cikin
matukar
mamaki sannan yace,ai mutumin da yake cikin
halin rashin lafiyar da saidai a kwantar a tayar bai
kamata
ace ya halarci wannan taro ba.Koda gama fadin
hakan sai sarki Uzaima ya ajiye takardar sunayen
sarakunan ya karbi ta jarumai ya fara
dubawa.Kwatsam!Yna cikin dubawa sai yayi kicibus
da sunan JARUMA ARYALA daga birnin nurul
ansar.Cikin tsananin mamaki sarki uzaima ya sake
karantasunan domin a zatonsa ko idanunsa basu
gane masa daidai ba.Abinda ya bashi mamaki
kuma ya daure masa kai shine a cikin sunayen
gaba
dayan jaruman gasar kusan mutum dari uku da
doriya sunan mace ko daya babu sai wannan
jaruma
mai suna Aryala ita kadai.Sannan kuma bai taba
jin labarin cewa akwai wata jaruma mai wannan
suna
ba
a cikin birnin nurul ansar.To wai shin ma yaushe
ne
wannan bakuwar jaruma ta wanzu har da zata
shiga wannan gasa?Amsar da sarki Uzaima ya kasa
baiwa
kansa kenan.Nan fa ya fada kogon tunani.Nan take
dabara ta fado masa kawai saiya dubi wazirinsa
yace,na sauya tsarin walimar dana shirya ta gobe,a
daren yau nakeson a gabatar da wannan walima ta
murnar cikar shekarun haihuwata arba'in da kuma
cikar shekaruna ashirin akan KARAGAR
MULKI.Maimakon gayyatar sarakuna kadai izuwa
dakin walima inason a shiga har da gaba dayan
JARUMAN GASA,kuma inason a shiga dasu din ne
bisa tsarin daya bayan daya domin na gamsu da
idanuna kafin a fara walimar.Koda jin wannan batu
sai waziri da sauran fadawan suka cika da mamaki
babu mai ikon tankawa koyin tambaya da jayayya
akan wannan umarni,kawai sai waziri ya sake
risina
yace,an gama ya shugabana.Nan take aka tashi
manzanni suka tafi izuwa masaukin bakin suna
isar
da wannan sabon sakon gaiyatar walima na sarki
uzaima a daren yau.
ΔRΔOΔKΔEΔDΔ
SARAUNIYA ARYALA tana zaune a can cikin turakar
masaukin da aka bata tare da kuyanginta ta
kishingida akan wata doguwar kujera ta alfarma
anayi mata gyaran gashi saiga wata kuyangarta ta
shigo da sauri.Da zuwanta gaban sarauniya Aryala
sai ta zube kasa tace,ya shugabata jarumi Damzur
ne ya iso kofar dakin nan yace a gaya miki cewa
wani sabon al'amari ya taso daga sarki uzaima a
yanzu yanzun nan.A wannan lokaci sarauniya
Aryala
tana sanye da wata riga ce mai shara shara wacce
ta bayyana komai na surar jikinta don haka sai tasa
aka miko mata mayafi ta daurashi kamar zani
sannan ta dubi wannan kuyanga tace,jeki kice da
Damzur ya shigo.Cikin mamaki gaba dayan
kuyangin suka dubi Sarauniya Aryala suna masu
zazzaro idanuwansu.Wacce ta kawo rahoton zuwan
Damzur dama itace shugabarsu ana kiranta da
suna
HIMAILA.Kuyanga Himaila ta dubi sarauniya Aryala
cikin alamun tsoro da fargaba tace,haba ya
shugaba saboda me zaki aminta da jarumi Damzur
haka har
ki amince masa shigowa cikin turarki?Koda jin
wannan tambaya sai sarauniya Aryala tayi
murmushi
tace,idan kana son ka sami damar sarrafa jarumi
yadda kakeso kuma ka sami yardarsa dole ne ka
fara bashi amincinka da yardarka.Ina bukatar
amincin jarumi Damzur domin na cika wadansu
burika na rayuwata duk da cewa ya zama bawa
na.Bamu san abinda ke karkashin zuciyarsa
ba,babu
mamaki nan gaba ya bultuce mini ko yaci
amanata,amma idan na jashi a jikina hakan zai iya
karya zuciyarsa ua fasa aiwatar da mugun nufinsa
a
kaina idan ma shi yayi niyya a zuciyar tasa.Maza
kije ki shigo dashi yanzun nan kamar yadda na
umarceki.Kuyanga Himaila ta sake risina tace an
gama.Ta juya ta fice daga cikin turakar,zuwa can
sai
gata ta dawo tare da jarumi Damzur yana biye da
ita
a baya.Koda Jarumi Damzur yayi arba da
sarauniya Aryala yaga wani bangare na saman
kirjinta,kuma
yaga kyakkyawan gashin kanta mai tsananin
haske,baki da kyalkali wanda aka tajeshi ya zuba
izuwa kasan kwankwasonta sai ya dimauce jikinsa
ya kama tsuma.Cikin sauri ya sunkui da kansa
kasa a lokacin da zuciyarsa ta raya masa cewa"Aini
ko
sarauniya Aryala bazata

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment