Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zuciyarta ta ji zafin maganarsa, hakan ya saka ba ta yi attempting sake fada masa wata maganar ba.

“Da kin shiga na sauke ki gida”

“Ba zan shiga ba my friend will come and pick me up, and this is the last time da zan shiga motarki”

Namra ta amsawa Nimra a fusace, Nimra ta daga mafadunsa tana rufewa Ameer kofar.

“What ever... ”

Wannan karo na biyu da Nimra ta kara burge shi, domin yana son ya ga an nunuwa mutane shi din wani na mai muhimmanci, a wulakanta wani saboda shi abu ne da ke matukar faranta masa rai. Da karfi ya fisgi motar bayan Nimra ya rufe front door din.

“Da gaske ku twins ne”

“As you can see, ita ce Namra ni kuma Nimra, kuma kama sosai sai dai mun banbanta a hallaya”

Be sake ce mata komai ba, tukin kawai yake ba tare da ya san inda zai je ba. Shiru abun da ya shiga tsakaninsu har ya samu wani gurin can kusa da Galadimawa ya faka motarsa, the place is so quiet nesa da mutane ne sai ka yi ta bawa idanuwanka abinci, ba tare da ya kashe motar ba ya bude ya fito ya jingina jikin motar ya rumgume hannayensa yana kallon wasu gidajen dake gefensu. Ganin hakan ya saka Nimra ma ta bude motar ta fito ta zagayo gafensa ta tsaya juyowa yayi ya kalleta sai ta ji wani irin faduwar gaba da bata taba jin irinsa ba, ba faduwar gaba irin mai tsoro ko fargaba ba, ba faduwar gaba ka kyaun da ta gani a fuskarsa ba, ba kuma ba damuwar dake bayyane a idonsa ba, faduwar gaba ne da ita ma kanta bata san dalilin hakan ba, kuma hakan be taba samuwarta ba sai a yau, wata kila kwarjini yayi mata, wata kila wani abun ne zai faru duk kuwa da kasancewar jikinta be raya mata haka ba, domin ba faduwar gaba ne irin wanda ake neman tsari da shi ba, wani irin faduwar gaba ne mai kama da na dadin da bata san na minene ba. Can cikin wani yanayi mai kama da tunani ta jiyo sautin muryarsa.

“Karki tambaye mi yasa na yi fada da Daddy, don't ask me anything i feel like ba zan iya miki karya ba, kuma i don't want to talk about it now, i just want to go somewhere nesa da nan”

A take ta ji babu dadi, domin tana kokarin juye damuwarsa ta zama nata ne.

“Why”

“Just wani gurin nake son zuwa inda ban san kowa ba, kowa kuma be san ni ba”

“Zaka iya zuwa gidanmu, Ummi bata da matsala yanzu muka sauketa da tare zaka gan mu ma har ka gaisa da ita, Abiey din mu ma haka we're like family to you”

“No Abujar bake son bari gaba daya”

“Ka rika hakuri, karka yi saurin yanke hukunci a cikin fushi idan ma baka son gidanmu zan sama maka wani wajen da zaka zauna”

“Ina da hakuri sosai, da ace ba ni ne Daddy yayi ma haka ba, da yanzu wani labarin ake dabam ba wannan ba, amman ni na san ina da hakuri sosai shiyasa nake son na yi nisa da nan”

Shiru ta yi tana tunanin kalaman da zata hada ta gamsar da shi ya janye kudinrinsa na fasa tafiya.

“Miye wannan”

Ya tambaya tana kallon Box din dake hannunsa. Ya kalli Box din ya fara shafawa da dayan hannunsa.

“Sarewace a ciki wanda nake busa”

Kusan a tare suka kalli wayar hannunta da ta yi kara.

“Ummi ce”

Ta fada sannan ta matsa nesa da shi ta yi picking call din, binta yayi da ido kamin ya dauke ya mai da gurin wata honda da ta faka nesa da su kadan, wata yarinya ce ta fito cikin motar sakale da jakarta ta goyo irin ta teddy da yan mata suke yayi wacce ake saka littafai a ciki. Kallonta ya sake yi da kyau fuskar yarinyar da ta tare shi a office tana rokon ya bata dama ta yi koyi aiki a ma'aikatarsu na dan lokaci ya gani shimfide a fuskarta, idonsa baya masa karya dan haka ya tabbatar da ita din ce. Ita ma kallonsa ta yi cike da fahimtar shi ne mutumen da ya fada mata ba su bukatar irinta a gurin, ta dauke idonta daga barin kallonsa a lokacin da Nimra ta dawo daga wayar da take ta kalli yarinyar ganin idon Ameer yana kanta ita kuma kallonsa take.

“Kasan ta ne?”

Sai a lokacin ya sauke idonsa sai dai be ce amsa mata da eh ko aa ba.

“Kun yi kama kamar yar'uwarka”

‘God forbid’

Ya fada a ransa a fili kuma yawu ya tofar ya yamutsa fuska alamar maganar bata masa dadi ba. Hakan ya saka Nimra jin babu dadi domin ko be fada mata ba ta san ransa ya bace ita kuma a dan lokacin idan akwai abun da ya tsana to bacin ransa ne.

“Ya kamata ka sauke ni gida, Ummi ta kira tana nemana”

Be ce mata komai ba, ya bude motar ya shiga sai ta zagaya ita ma ta shiga, har suka koma cikin birnin Abuja be kalli inda take ba balle ya furta wani abu, sai dai ita ta kan kalleshi lokaci zuwa lokaci.

“Ina zan sauke ki?”

“Kofar gidan mu”

Ta fada cike da fatar idan suka isa ya yarda ya shiga gidan domin bata son tafiyar da zai yi, kamar yadda bata isa ta hana shi aiwatar da kudinsa ba.

“Duba nake yi da zan san gidanku ba tare da kin fada min ba”

“Wuse zone 2”

Yanayin yadda ta yi magana ya saka ya juyo ya kalleta sai ya ga shi take kallo, cike da takama ya kawar da idonsa ya cigaba da tukin, tana fada masa inda zai bi har suka isa gaban wani farin Gate, da shi kan shi ya san masu gidan sun amsa sunan su na masu arziki. Pen ta dauka a motar ta zari tissue ta rubuta masa number ta, ta aje a gurin da jakarta take aje.

“Ka kira ni please, karka bar ni da tunanin halin da kake ciki”

“Na fasa wayar”

Na fada ba tare da ya kalleta ba, kallonsa take da mamaki tana tunanin wane kalar zuciya ne a jikinsa da baya iya controlling dinta, sannan ta maida idonta a gurin jakarta ta bude ta dauko ATM dinta ta aje a saman tissue din da ta yi rubutu akai.

“Maybe zaka bukaci yin wani abu, akwai enough kudi a ciki, kuma zan sake saka wasu a account din just for you”

Ya mika masa dayan wayar dake aje a cikin motar.

“Akwai Sim a ciki, zaka iya kira da ita take care of yourself”

Kallon wayar kawai yayi isa da takama ta hana shi mika kallo ya karba, ko ba komai dai wayar ta masa karama domin baya rika kananan wayoyi, iPhone 14 ce while wayar dake dayan hannunta is iPhone 14pro max duka wayoyin yana jin ba ajinsa ba ne, ko ba komai shi baya son abun da kowa zai rika yayi, ya fi son nasa ya zama dabam ace kalilan ke da abun hakan kan banbanta da sauran mutane.

“1742 is my ATM Password, wayar kuma ba password”

Ganin ba zai karba ba ya saka ta aje wayar a muhalinta dake cikin motar, ta sake bude jakarta ta dauko dollars ta aje a gurin.

“Ko da bukatar cash ta kama ka”

Ta bude motar zata fita.

“Miyasa kike min duk wannan?”

“Because I care for you, i don't want why i don't how, kawai ina jin na damu da kai, don't hurt yourself please”

Wannan karon ta yi sa'a ya daga mata kai, sannan ta sake dubansa ta fice daga motar ta rufe masa kofar, tsaye ta yi har sai da ta daina hango shi sannan ta shigo cikin gidan da masu gadi suka dade da bude mata gate.




WAIRA POV.

Har cikin dakinta Eid ya kawota, a nan wani babin nishadi ya sake bude sabon shafi, sai dai wannan karon hira yake mata irin na wanda ya saba mata lokaci zuwa lokaci, na wasu mutanen da suka banbanta da su ta bangaren abinci, al'ada da kuma addini da ma rayuwar kacokam.

“Ai akwai zafi sosai”

Ta fada a lokacin da yake mata bayanin yadda matansu suke rufe jiki, domin ita duka tufafinta guntaye ne, rigar da zata iya kiranta da doguwar riga bata rufe mata kafafuwa ba, da kadan ta wuce quiwarta, wani lokacin kuma zata saka riga da skirt na fata ko na saki irin na mutane da da ake yi da kaďa rigar iya cibiya skirt din iya guiwa ko ya wuce kadan, ba al'adarta bace saka talkami komai zafin rana da ake, komau hadarin guri haka take shiga da kafafuwanta babu ruwanta da saka talkami balle kuma wanke kafar.
Ta mika hannu beran dake lalen kwanon da take cin abinci ya hau hannunta ta saka shi a tsakankanin kafafuwanta tana shafa shi.

“Akwai wanda na san idan ya shigo dakin nan sai ya mutu ko ya suma saboda tsananin tsabtarsa”

Ta juya ta kalli dakinta da yake ya mutse, ita kam sam bata ga wani abun kyama ko Allah wadai a dakin ba, ita dai yadda take rayuwarta a haka tana jin dadin rayuwarta sosai.

“At takfr hur verrr gulta jaget”

_Yayi tsabtarka?_

“Ya fi ni sau dubu”

Ya fada yana kallonta, sai ta ya mutsa fuska domin Eid ma ganinsa take mai tsananin tsabta da idan zai ci abu sai ya wanke ga wanka a kullum idan kuma aka ce akwai wanda ya fi shi ai abun be burge ba.

“Bana son irin wadanan mutanen sam, amman fatar jikinsa ba irin wannan bace ko? Saboda tsabta”

Yayi murmushi mai sauti, ya kama hannunta ya dora saman goshinsa ya yana kallon kyakkyawar fuskarta dake dauke da datti, so yake kawai ta ga yadda suka yi rayuwa da mutumen na dan lokaci kadan domin ya san tana da wannan tsafin da idan ta dafa kan mutum tana iya ganin da jin abun da ya faru a rayuwarsa ta baya. Runtse ido ta yi sai ta fara arba da karar wani abu mai da bata taba jin irinsa ba, karar ta girmin kunnuwanta, hayaniyar da take ji ta yi yawa, dishe dishe ta fara ganin wani abu bata taba gani ba yana gudu wasu kalar na binsa a baya karar karfe da karfe suna gaduwa kamar za su tashi kwakwalwarta, da sauri ta dauke hannunta ta bude ido domin karar da take ji ta girmi kunnuwanta.

“Kara sosai”

“Abun da nake baki labari kenan Mota, ita suke hawa a madadin dabobin mu”

“Outar.... ota...”

Ta maimaita tana mamakin wace irin rayuwa ce wannan. A gurinta ya wuni har dare sannan ya kunna mata wutar tsafi ta haska mata dakin na adadin awawanin da zai yi kamin ya kwanta a daidai lokacin da wutar zata mutu.
[06/06, 9:40 am] 𝐊𝐡𝐚𝐝𝐞𝐞𝐣𝐚 𝐂𝐚𝐧𝐝𝐲 ✍️: *⚜️ ...WANI GARI... ⚜️*


_Na Khadeeja Candy_


9️⃣

Kai ta daga sama ta kalli Namra dake tsaye tana kallon duk abun da yake wakana a kasan murmushi kawai ta yi ta maida kanta kasa ta cigaba tafiyar ta har ta shigo cikin gidan, sai da ta duba ko'ina bata ga Ummi ba sannan ta hau sama ta duba dakin Ummi nan ma bata ciki, sai ta zagaya ta inda yar'uwarta take tsaye tana kallon harabar gidan, tun kamin ta karasa kusa da ita ta ce.

“Ummi bata dawo ba?”

“Suna can gurin case din”

“Kirana fa ta yi wai na dawo gida, ta ji abun da na yi miki”

“Na fada mata komai ai, akan wani banzan saurayi zaki wulakanta ni”

Duk maganar da suke Namra bata juyo ta kalleta ba, ita kuma bata fasa murmushi da mamakin halin yar'uwarta ba.

“Kyakkyawa ne ko ba haka ba? Yana da masifar kyau Namra baki gani ba”

“Kyaun ne matsalarki?”

“Yana da kwarjini, yana da natsuwa yana jin kanshi, samarin dake jin kan su ba su cika kula mata ba, domin gani suke kowace mace ba tsararsu ba ce”

Magana take tana murmushi domin ji take kamar yana a gabanta tsaye tana kallonsa. Namra ta juyo ta kalleta.

“Ke wai tsaya ba dai shi kika bawa motarki ba?”

“Mota kawai kika gani? Ke baki ga alamar zan iya ba shi rayuwata ba ma?”

“Love is stupid....”

Ta fada tana jan tsaki, tsabar haushi ma ya saka ta bar mata gurin, Nimra ta yi murmushi domin ita kadai ta san abun da take ji a game da Ameer.
Bata sauko ba sai da ta hango Shigowar iyayenta tare da Yayanta Maleek da kuma Mahmood, kamin ya zagayo ta sauko har sun shigo cikin falon.

“Ummi an kama shi?”

Shi ne abun da ta fara tambaya, Hajiya Zahra ta yaye mayafinta ta zauna saman kujerar da ba a isa a saka a gidan wani karamin mai arziki ba tana fadin.

“Abban ku be bari na shiga ciki ba, a mota suka bar ni ban san ya aka yi ba, sai fada yake min wai miyasa na bi su”

Nimra na kallon Abiey ya dankaro mata harara.

“Daga yau kar mu sake fita akan wani issues irin wannan ki dauki mahaifiyarki ku bi bayanmu”

Nimra ta marairaice fuska try to act innocent.

“Ba laifina ba ne fa, ita ta ce sai mun kaita saboda hankalinta ba zai kwanta idan tana gidan nan ba”

“Na fada miki dai, this should be the last, kuma an rufe case din nan daga yau kar na sake jin maganar mun yi solving da mahaifinsa”

Ummi ta kalleshi da sauri tare da mikewa tsaye Nimra da yar'uwarta ma haka, Mahmood da Maleek da suka san abun da ya faru ne kawai ba su yi mamaki ba, ba ma kamar Maleek da hakan yayi masa dadi.

“Saboda me? Shiyasa ka hana na shiga? Yaron ya fi karfin a hukunta shi ne? Taya mutum zai nemi kashe min yaro kuma kace kun sulhunta Ba sulhu nake so ba, hukunta shi nake son ayi idan ya saba yi ana kyaleshi to yanzu ya kai karshe”

Abiey be ce mata komai ba, ya wuce dakinta sai duk suka bishi da kallon mamaki, har sai da ya shige kofar da zata sada shi da bangarensa. Sannan Ummi ta juyo tana kallon Maleek.

“Waye yaron nan ne? Ya fi karfin kowa a garin nan ne? Waye Ubansa?”

Nimra ta dafata tana kokarin kwantar mata da hankali.

“Ummi, Abiey fa ya fiki son yaya tun da kika ga ya bar maganar nan abun ya fi karfinsa ne please calm down”

“Yaron ba a san inda yake ba Ummi, DSS din da aka tura su kama shi sun ce ba su same shi a gidan ba, kuma step mother dinsa ta zo tana kuka ta yi ta ba mu hakuri, ta ce yanzu haka mahaifinsa ya koreshi ya karbe komai nasa saboda abun da ya aikata, kuma mahaifinsa yana can ya fadi ba lafiya”

Mahmood ne ya bata amsa, daman can bata sa ran samun wannan dogon bayanin daga bakin Maleek ba.

“Karya ne sun shirya hakan ne saboda su kare dansu”

Namra ta fada, a daidai lokacin da wani tunanin na dabam ya zowa yar'uwarta Nimra.

“Waye Ubansa?”

Ummi ta tambaya tana jin kamar ba zata iya kyale maganar nan hakan nan ta tafi ba. Maleek ya fara tafiya ya nufi kofar fita daga falon domin ya tsawalla dan tsayin da yayi a falon da kanennensa da kuma mahaifiyarsa.

“Sunan Yaron Ameer dan gidan Alhaji Bashir something Mr Bashir shi ma dan Kano ne”

Da wani irin karfi Ummi ta zabura sakamakon bugawar da zuciyarta ta yi cikin rashin shiri, sai ta ja numfashi da karfi. Nimra ta nufi Mahmood tana fadin.

“Ka san shi Mahmood? Kana da hotonsa?”

“Na san shi, lemme see”

Ya ciro wayarsa ya shiga Instagram yayi searching Account dinsa, a nan yayi ta haduwa da fake account da sunan nasa, sai dai be damu da hakan ba domin abun da ya kai shi Application din neman hotonsa, hotunansa ya kama ya mikawa Nimra, ita ma faduwa gabanta yayi jikinta ya fara rawa kamar marar gaskiya.



WAIRA POV.

By the time din da Eid yake tsammanin ta yi bacci sai ya kashe wutar, ita kuma ganin wutar ta mutu ya saka ta tashi zaune ta fito daga cikin dakin, a bakin kofa ta zauna tana kallon sama, taurarin da suka yi ma samaniya ido suka fara burgeta kallonsu take sosai kamin ta fara kirgasu. Tun tana zaune har abun ya kai ga ta mike tsaye ta fito waje gaba daya yana juyawa idonta na sama kamar wanda aka cewa idan kika kalli kasa zaki mutu, bata ankara ba ta ji ta bugi mutum da sauri ta dawo da dubanta gabanta sai ta yi arba da wani saurayi da be wuce sa'ar Eid ba, dariya ta yi ta sauke kai kasa tana cewa yayi hakuri, shi ma dariyar yayi ya rike walkin dake kugunsa yana kallonta.

“Ba sai kin ba ni hakuri ba, laifina ne”

“Laifina ne dai ban kalli gabana ba sai sama”

“Ba ki yi bachi ba har yanzu me kike yi?”

“Bana komai bachin ne be zo ba, kai miyasa baka yi bachi ba”

Ta tambaya yana saka yatsanta a baki tana watsa da yawun dake cikin bakinta.

“Daman na kan dade ban yi bachi ba”

“Waira....”

Kamar daga sama suka ji muryar Eid daga ita har shi juyowa suka yi suna kallon inda sautin muryar ke fitowa, Saurayin ya kalleta.

“Matsalar kenan Eid baya barin kowa ya rabe ki, ba ya barin kowa yayi magana da ke, shi yake tafiyar da ke”

Ita dai ban da kallonsa babu abun da take domin bata fahimci komai a cikin maganarsa ba, karaso Eid yayi gurin fuska babu annuri.

“Mu je ki kwanta”

“Bana jin bachi”

Ta amsa kai tsaye sannan ta juya zata cigaba da tafiya, wani irin fisgota yayi ta dawo baya da karfi ya daka mata tsawa

“Muje ki kwanta”

A ka'idarta ba a mata fada, haka zalika ba a mata tsawa, sai kawai ta fisge hannunta ta yi tafiyarta wani gefen dabam, kallon Saurayin kawai Eid yayi ya bi bayan Waira, gurin wasu manyan duwatsu ta nufa ta zauna tana kallon wajen garin iska mai dadi na kadata.

“Kar wani ya sake miki magana ki amsa?”

Ta juyo da karfi kamar ta dake shi.

“Zan amsa ko yanxu wani yayi min magana sai na amsa, ba ruwanka da ni”

Kallonta kawai yayi be ce komai ba, ya juya ya fara tafiya, ba shi da halin hukunta wacan saurayin da ya haddasa masa ruruwar wuta a zuciyarsa, domin idan yayi masa wani abun dole za a gani idan aka yi tsafi, ya san kuma babu makawa dole ne sarki ya hukunta shi, Waira ce kadai ke da ikon ta illata wani ko ta kashe shi a kyaleta, sai dai ayi mata fada ko dan hukuncin da be taka kara ya karya ba. Jin kamar ba zai iya barinta a gurin ba ya saka ya dawo ya sake cewa ta tashi ta je ta kwanta.

“Ba zan kwanta ba, na fada maka babu ruwana da kai”

Matsawa yayi kusa da ita sosai ya dafa kafadarta, tana kokarin kai hannunta ta janye na shi hannu ta ji tafiyar wani abu mai kamar Maciji ya shiga cikinta yayi bayanta da sauri kamar mai neman gurin boya haka ta rika jin abun na mata yawo har sai da ya zagaye jikinta ko'ina sannan ta ji yayi kasan cikinta. Da wani irin karfi da bata san tana da shi ba ta tura Eid ta fara dukansa babu kakkautawa.

“Me ka saka min a jiki me ka yi min? Eid me ka yi min me ye wannan abun nake ji?”

Hannayenta ya rike ya juyar da ita ya matseta a jikinta sosai ta bayanta har sai da ta natsu sannan ya sake ta.

“Kin san ba zan cutar da ke ba ko?”

Bata taba jin tsanarsa a ranta irin yau ba, gaba daya ya gama canja mata tsarin daren yau da take jinsa da nishadi, ya jagula mata lissafi ya bata mata rai. Wani irin huci take kamar zaki tana masa wata hararar da shi kanshi ya san sai ta dauki lokaci kamin ya su shirya. A gurin ta bar shi tsaye ta dawo dakinta ta kwanta tana ta jin haushinsa a ranta, shi kuma ya kasa tafiya ya kyaleta sai ya dawo bakin kofar dakin ya zauna ba tare da ta san yana gurin ba, sai da ya tabbatar da ta yi bachi sannan ya leka dakin, da idonsa ya haska fuskarta, bakinta a cige yake ta rumgume hannayena irin na masu fadan nan. Wani abu mai kama da Ƙulba ya fito daga kafafuwanta Eid yayi tsaye yana kallonsa har ya fice daga dakin, sannan ya koma ya zauna kamar mai gadinta, be bar gurin ba sai da sanyin safiyar asuba ya fara sauka. Waira kuma bata farka ba sai da rana ta hasko dakin nata da wata bolar zuba shara ta masu kudi ya fita.
Ba musulma ba ce balle alwala da sallah ya zama abu na farko da zata fara yi, ba mai tsabta bace balle wankr baki ko wanka ya zame mata dole, haka ta fara lalaben abun da zata ci, babu komai a cikin akushin dake dakin, ganin bata samu komai ba ta nufi gurin da zakarunta suke ta leka ramen bera ta dora hannunta a bakin ramen, da gudu bera uku suka hau hannunta, sai ta saka daya a cikin gashinta dayan kuma a cikin aljihun walkinta na dama, daya daya rage ta saka shi a na hagu sannan ta fita kafarta babu talkami daman can bata da su gaba daya ko ma akwai bata damuwa ta saka, wata mahaukaciyar rayuwa take da babu mai burin yin irinta.

Waje ta fito gaba daya ta murza idonta so that ko da akwai kwantsa ta fita ba tare da ta wanke ba, gurin da ta saba zuwa ta ci yayan itatuwa ta nufa kamin ta karasa ta hango mutane sun doso inda take da sauri irin na wadanda aka bawa umarni, ganin haka ya saka taja ta tsaya domin mutanen na gidan Sarki ne dakarunsa ne ba gama garin mutane ba, ko ba a fada mata ba ta san laifi ta yi domin ba kasai Sarkin zai sa a kirata ko zo masa da ita ta sunan su gaisa ba sai idan ta yi laifi.

“Fada ta yi kira, Sarki yace a zo da ke”

Bata ce musu uffan ba, ta kai ta taba hannunsa in 5 seconds ta ga abun da ya faru a fada kamar a gabanta aka yi komai.

“Ban kashe shi ba”

“Mu yan aike ne kawai”

Dayan ya amsa mata, sai ta yi baya baya alamar ba zata je ba, domin zuciyarta bata raya mata komai sai cewar ita ma kasheta za'ayi kamar yadda ta ga gawar saurayin da yayi mata magana jiya a fada matacce. Kai ta girgiza musu alamar ba zata je ba, su kam daman can musu da jayayya ba na su ba ne sai abun da Sarki ya fada, sai suka juya domin sanar da Sarkin yunkurin Waira na cewa ba zata je ba kamar yadda ta yi musu alama. Waira na ganin sun bace sai ta juya ta fara gudu zuwa bayan gari can gurin manyan duwatsun da Eid ya taba kaita, tana gudu tana kuka har ta isa, sai da ta isa ta boya bayan wani dutse tana tuno abun da ya faru jiya, sai ta sake fashewa da kuka, a rayuwarta babu abun da ta tsana kamar mutuwa, domin ta san duk wanda ya tafi be dawo ba, kuma ta san halin Sarki da tsananin hukunci kuma ba ya yafewa kowa musamman idan zalinci ne aka yi. Mikewa ta yi tsaye ta fara tafiya tana sauka ta gafen garin tun tana yi a hankali har ta fara sauri tana hadawa da gudun, duk da ita da kyamar ruwanta sai gata ta saka kafarta ta gafen da ruwan be da yawa ta tsallaka ta fara ratsa dajin dake gurin tana gudu, har da faduwa take ta tashi ta jefa kafarta can ta cire ta saka a nan bata damu da ciwon da ta ji a kafa ba ita dai burinta ta bar garin gaba daya....



EID POV.

Eid dake tsaye cikin fadar yana jiran Dakarun Sarki su dawo tare da Waira da Sarkin ya ce a zo da ita ko ta halin yaya bayan sun shaida masa abun da ta fada. Ya daga kafarsa da ya ji tana masa mugun

1 Comments On WANI GARI
avatar
naima-3

1 year ago

Reply

Thank you

Please Login or Register in order to submit comment