Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kuskure”

“Ko dai abokin da kuka samu matsala da shi ne?”

Abiey ya tambayar yana kallon wayar Maleek dake ringing.

“Karka daga wayar nan, bari mu gama magana”

Maleek ya aje wayar gefe ya shafa kansa.

“Ba na jin zai yi haka”

“Wani lokacin wanda baka tunani shi zai aikata maka abu, wata kila kai baka dauki abun da zafi ba amman shi ya dauka kuma gashi har ka ce wani yayi kissing dinka wannan abun ba a saba da shi ba, kuma baka san manufarsa ta yin haka ba”

Cewar Namra cike da damuwa.

“Siyasa ai ba zamu kyale ko waye ba, musamman yadda ya tashi hankalinmu a gidan nan jiya, a inda ya kaika ya aje wani abu zai iya samunka a can din ma, kuma duk wanda zai maka wannan abun zai iya silar rasa rayuwarka, dole mu gane ko waye wannan tun daga kan drink din da ka sha”

Abiey ya fada with serious face, Maleek ya kalleshi cikin yanayin dake nuna baya son iyayens su shiga cikin lamarin domin yana jin kamar Ameer ba zai iya masa haka ba, duk kuwa da kasancewar wani bangare na zuciyarsa na raya masa shi din ne.

“Abiey wannan a tsakaninmu ne?”

Hajiya Zahra ta daka matsa tsawa.

“Wani irin a tsakaninku? A tsakaninku wani zai maka haka? Wannan shi yake nuna friends dinka ba mutanen kirki ba ne, su waye ma friends din duk ba mu sani ba, basa zuwa gidan nan sai dai ka je can kana haduwa da su wani guri”

Abiey ya saka hannunsa ya ciro wayarsa dake aljihun jallabiyarsa yayi dialing.

“Duk masu aikin gurin sai an dauresu sai sun fadi wanda ya saka su”

“Abiey kar aja abun nan da nisa kar aje inda ba a so”

Cewar Maleek domin ya fi son a bar maganar a hannunsa.

“Ba za a bari ba, Maleek kuma sai an hukunta yaron nan ko dan gidan uban waye, domin zai iya kashe ka ma”

Ummi ta fada cikin bacin rai, Nimra ta ce.

“And the most annoying part ma Yaya baya iya zama ya fadawa kowa damuwarsa sai dai ya bar abu na cinsa Allah kadai ya san abun da ya faru a tsakaninsu amman be fada ba, gashi abu har ya fara wuce gona da iri”

Kallonta kawai Maleek yayi ya mike tsaye ya nufi hanyar stairs.

“Ja ka a duba lafiyarka, whats if yayi poisoning dinka?”

Ya juyo ya kalli mahaifiyarsa dake maganar.

“Zan je, wanka zan yi na yi sallah tun jiya ban yi magariba ba”

Sannan ya juya ya hau sama yana jin yadda Abiey yake yi ma abokinsa bayanin yadda ďansa ya dawo.

“Ba zan sake bari ya rabi friends dinsa ba, ba mu san su waye yake abota da su ba, ji yadda suka saka shi ko sallah be yi ba, dole ne a hukunta ko waye....”

Wannan karon ma Hajiya Zahra ce take maganar cikin fushi tana jin kamar ace wanda ya aikatawa ďanta haka yana a gabanta.


[06/06, 9:40 am] 𝐊𝐡𝐚𝐝𝐞𝐞𝐣𝐚 𝐂𝐚𝐧𝐝𝐲 ✍️: *⚜️ ...WANI GARI... ⚜️*


_Na Khadeeja Candy_


6️⃣


WAIRA POV.

Tun daga lokacin da sarki yayi mata gargadi sai ta rika ware kanta dabam, daman can bata da abokan wasa sai dai tana dan shiga cikin mutane a yanzu kuma ko fita gida bata yi sai dole, Eid din ma da take sakewa da shi sai ta daina, sai dai hakan be saka ya kyale ta hakan be canja komai daga alakarsu idan bata fita ba shi zai zo ya same ta har cikin gidan, wani lokacin zai mata hira ranar da aljanun kwarai suke kanta sai ta amsa masa su yi ta hira yana bata labaran duniyar da ta sha banban da tata, wani lokacin kuma har ya gama abun da zai yi ya tafi ba zata ce masa komai ba. Sai dai tana jidadin idan yana labarta yadda wasu abubuwan suke a wasu garuruwan kuma yana fahimtar hakan a fuskarta domin ya fi kowa sanin halinta, abun da zai faranta mata ko ya bakanta mata rai.

Karar jirgin saman da ya ji ya saka shi riko hannunta ya fito da ita daga cikin dakin da take ya nuna mata jirgin saman, ba a yau ta fara ganinsa ko jin kararsa ba, sai dai yau ne rana ya farko da ya taba labarta mata cewar mutane ne a ciki, kuma tsuntsun yana daukar mutane da yawa har da kayansu, kana ya misalta mata yadda girmansa yake a kasa, ta bude baki sosai tana fiddo idonta waje.

“Kuma mutum ne yake tukawa?”

Ta tambaya tana saka hannunta ta tare ranar dake haska fuskarta.

“Mutum ke tukawa, yana da sauri fiye da tsuntsu”

Ta dawo da dubanta gurin fuskarsa tana murmushi.

“A ina yake sauka?”

Shi ma ya sauko da kansa kasa yana kallonta domin yayi mata tsawo sosai.

“A can garuruwansu, sun tanadar masa muhalli mai girma sosai wandanda za su hau sai an tantance su suke hawa, kuma sai sun biya kudi”

Ta sake juyawa tana kallon inda jirgin ya bi amman ko alamarsa babu.

“Me suke bautawa su? Miyasa komai na su ya banbanta da mu?”

“Saboda sun yarda sun karbi sauyin da duniya ta zo da shi, wanda mu muka kasa haka, na nesa da mu suna da addininai kala kala na kusa kuma na san ana kiransu Musulmai”

Ya amsa mata yana kallonta irin kallon nan dake tafiya da ruhin mai yinsa.

“Ina ma ace an baki damar fita wajen gari, da na bawa idanuwanki abinci, na zaga dake duniya ki ga wata rayuwar data banbanta da taki sai dai an iyakance miki iya cikin garin nan, fitarki a garin nan zai saka ki manta hanya dawowa, hakan kuma na nufi rasa rayuwarki gaba daya”

Ta sauke kanta kasa ta fara tafiya.

“Miyasa rayuwarsu take burgeka?”

“Rayuwarsu tana da kyau, wani abu na su yana burgewa ke ma da zaki leka ki gwada zama a cikinsu da kin jidadin rayuwar”

Bata sake ce masa komai ba har suka isa gurin da dade bata zauna ba saboda gargadin da Sarki yayi mata, zaunawa ta yi a gurin shi kuma ya tsaya yana kallon itatuwan da suka kawata gurin ga ruwan dake gudana gwanin sha'awa.

“Wasu kan kawata cikin gidajensu da irin wannan ruwan”

Ta yamutsa fuska.

“Saboda su yi wanka?”

Ya amsa da kai yana murmushi, a take ta ji ta tsani mutanen domin mutane masu yawan wanka ko son tsabta basa burgeta.

“Bana son zama a cikinsu”

Zaunawa yayi a gurin yana kallon ruwan da take kallo.

“Akwai wanda na taba haduwa da shi, a rana zai yi wanka kamar sau biyar ko sau goma saboda tsabta”

“Kuma baya jin wahala?”

“Baya ji kuma baya gajiya”

Ya juyo ya kalleta sai ya kama hannunta ya rike.

“Waira baki taba jin marmarin wani abu da kika rasa ba?”

Da manyan idanuwanta ta kalleshi tana kokarin fahimta tambayarsa, sai ya saka yatsansa ya daki hancinta.

“Taya mutum zai yi marmarin wani abu da da be san da wanzuwarsa ba?”

Ya kallonta yake wannan karon kallon tausayi yake mata, ta tashi babu iyaye kuma tana rayuwa ita kadai kuma tace bata jin marmarin wani da ta rasa ba.

“Baki marmarin zama da iyaye?”

Ta kyalkyale da dariya irin dariyar nan ta yaran da ba su gama sanin ciwon kansu ba.

“Mi zai saka na yi marmarinsu? Bayan ban rayu da su ba? Abun da ka taba kasancewa da shi shi kake marmari ai”

“Zaman da kike ke kadai be taba sakawa kin ji marmarin iyaye da yan'uwa a kusa da ke ba?”

“Ina da yan'uwa ai”

“Su waye?”

Ta saka hannunta cikin gashin kanta ta ciro karamin beranta ta dora a hannu ta nuna masa.

“Gashi tare da zakaru, ina jindadin rayuwata ni”

Ya kawar da kansa.

“Wannan ba jindadin rayuwa ba ne, Waira kin tashi babu iyaye kin ware kanki dabam kina rayuwa tare da abubuwan da ake kebewa, a haka kuma jiran ake ki shekara ashirin a baki sarautar da idan kika haihu zaki mutu ki bar abun da kika haifa, to ina jindadin rayuwa a nan?”

Hannu ta saka ta raba gashin kanta biyu ta saka beran a tsakiya sannan ta mike tsaye ta doshin gurin iccen abaya, Eid na kallonta har ta haye sama tana tsinko ayabar tana jefowa kasa sai da ta gama sannan ta kwanta a saman itacen tana cin wata. Eid na ganin haka ya tashi ya karasa gurin ya daga kansa sama yana kallonta.

“Zo mu tafi gida”

Ta girgiza masa kai alamar aa, yana jin haka ya san ba yanzu zata tafi gidan ba, sai ya juya yayi tafiyarsa, tashi ta yi zaune sai da ta daina hangoshi sannan ta share hawayen da suka cika mata ido. A yau kam Eid ya saka ta marmarin da tunanin abun da bata taba ba, su waye iyayenta wace kalar kulawa za su bata duk bata sani ba, ta ware kanta daga yan'uwanta saboda ta fi jindadin rayuwarta a inda take rayuwa a yanzu. Saukowa ta yi daga kan itacen ta nufi gabar da ruwa ke gudana ta rika bi tana kallon ruwan har ta isa inda mahadarsu take, sai ta taka wani tsauni ta tsaya akai tana hango wani gari da ba ta taba sanin akwai a gurin ba, domin yawonta be tana kawo ta a nan ba, hangaga ta hangame baki tana dariya domin yanayin iskar gurin ma a dabam take.

‘Wannan ba jindadin rayuwa ba ne, Waira kin tashi babu iyaye kin ware kanki dabam kina rayuwa tare da abubuwan da ake kebewa, a haka kuma jiran ake ki shekara ashirin a baki sarautar da idan kika haihu zaki mutu ki bar abun da kika haifa, to ina jindadin rayuwa a nan?’

Maganar Eid ta dawo mata, a ciki babu abun da ya fi tsorata kamar cewar zata haihu ta mutu, kamar yadda mahaifiyarta ta mutu bayan haihuwarta, a duniya babu abun da take tsoro kamar mutuwa, ta zauna a gurin ta sako kafafuwanta kasa tana kallon yadda dacin ya wadatu da ni'imar Allah da albarkarsa.


AMEER POV.

Ya dago yana yi ma sakatarensa wani mugun kallo irin na kaskantaccin mutane.

“Ga file din”

Ya aje masa file din akan Table cike da Ladabi.

“Waya baka inzinin shigo min office?”

With confused sakataren yake kallonsa.

“Na yi knocked kamin na shigo”

“Amman ban maka izinin shigowa ba ai, ko kuma rainin wayo ne ya saka ka fara yim yadda kake so a office dina?”

“No ba haka ba ne, wani lokacin ko an yi knocked ba zaka ce komai ba har sai idan na shigo, a yau ma na yi zaton haka din ne, amman ka yi hakuri zan kiyaye next time”

Wata harara ya watsa masa sannan ya dauke idonsa ya maida gurin wayarsa, a take fuskarsa ta cika da murmushi ganin kiran mahaifinsa.

“Daddy”

“Ameer kana ina?”

Ya mike tsaye yana wani irin kamshi kamar wanda kwalbar turare ta fashe a jikinsa dark blue suit din dake jikinaa ya karbe shi sosai ya kara fito da kyaunsa.

“Daddy a irin wannan lokacin ai kasan ina gurin aiki, ka san ni bana wasa da aiki sai dai ace na yi ba daidai ba”

“Ka zo gida yanzu nan ina son ganinka”

Ya duba tsadadden agogon hannunsa.

“Yanzu?”

“Yes”

Ya sauke wayar yana nazartar muryar da be saba jin fitowarsa a bakin mahaifinsa ba sai idan yana cikin wata damuwar, ko wani abun da ya gagare warwarewa. Fito yayi sai kuma ya daga kadunsa alamar ba damuwa ya nufi gurin da jacket dinsa take ya dauka tare da keys dinsa ya fice daga office din. Yana kokarin sauka second floor ya ji ance.

“Kai Malam...”

Da gangan ya ki juyowa duk kuwa da muryar mai kiran ta yi nuna da shi take kira kai tsaye, sai dai yanayin yadda ta yi kiran da yadda yake jin kansa ba zai bar shi ya juyo ba ma balle har ya  amsa mata.

“Malam da kai ba nake magana mai blue suit”

Ya juyo ya kalleta jacket dinsa na rike a hannunsa, sai dai girman kai ba zai bar shi ya fara yi mata magana ba. Ganin ita ce mai bukata a gurinsa ya saka ta dawo daidai inda yake tsaye ta tsaya cike da ďa'a ta ce.

“Sannu, dan Allah office din Manager nake nema?”

Kallonta kawai yake izzar kudi ta hana shi tambayar dalilinta na son ganin manager, kamar ta san waye shi sai ta gyara zaman jakarta ta yan makaranta ta ce.

“Ina karantar Information Technology ne a nan jami'ar Abuja, to shi ne aka bawa kowa zabar inda yake son yin IT ni kuma na zabi nan saboda ya fi min kusa da gida, na yi magana da wasu suka ce na je na yi magana da manager ni kuma ban san office din ba.”

From head to toe ya kalleta, ba laifi shigarta bata nuna cewar ita din yar gidan manyan masu kudi ba ce, shiga ce irin ta matsakaitan masu arzikin Abuja, kuma ta masu arzikin wasu garurun da ba a karyar naira kamar Babban birnin taraiyya, sai dai wani abun da zai iya yaba a tare da ita shi ne kamshin turaren da take. Ba tare da ya ce da ita komai ba ya juya ya cigaba da tafiya.

“Karya fa na yi na ce yayana ya aiko ni gurin Manager shiyasa aka bar ni na shigo, dan Allah ka taimaka ka fada min”

Ya tsaya sai kuma ya sake juyowa ya kalleta.

“Ba ma bukatar irinku”

Ta kalli tufafinta zuwa kasanta.

“To na gode”

Ta sauko ta wuce ta fice daga gurin cikin yanayi na rashin jindadin, bata san waye shi ba, sai dai da alama yana da babban mukami shiyasa har yake korarta, samun kansa yayi tsaye yana kallonta har ta sauka daga gurin gaba daya sannan ya fito, a gurin da ya saba aje motarsa ya nufa ya bude motar ya shiga ya dora rigarsa a kan kujerar sannan yayi reverse ya fice daga kamfanin da irin tukin da ya fi kwarewa akai.
   A harabar entrance din falon ya faka motarsa sannan ya fito ya doshi kofar, a ka'idarsa baya taba door Bell din wai be san iya mutanen da suka tsaba ba zai iya tabawa ya kwashi cuta, wannan ya saka yafi jindadin yayi knocked ko ba komai knocked kan banbanta shi da sauran mutane a san da cewar shi ne zai shigo so that ayi saurin bude masa. Sai da ya tsaya ya cire talkaminsa ya saka na shiga falon sannan ya shiga, as usual ko'ina na falon kamshin turaren wuta yake bayan air freshener da aka saka da kuma turaren goge tile. Karamar kofar da suka saba budewa su shiga ta sada su da bangaren Mahaifinsa ya bude ya shiga dan karamin corridor dake cike da kayan kawa, karamin falon ya shiga sai ya samu Daddy a tsaye Momy na daura masa a gogo a hannu.

“Lafiya Daddy?”

Da hannu Daddy yayi masa alama da ya zauna, sannan shi ma ya zauna Momy ma ta zauna cikin yanayin damuwa.

“Ameer ka yi fada da wani?”

Ameer ya kalli mahaifinsa kamin ya kalli Momy dake maganar.

“Kamar ya?”

“Police aka turo su tafi da kai”

Dariya yayi ya dan yamutsa fuska.

“Ni kuma? Ni police za su tafi da ni?”

Sai a wannan karon Daddy yayi magana.

“Calm down na yi magana da CP bana son ka je gurin nan but it seems like dole sai ka je da alama yaron da ka taba shi ma dan masu gari ne”

“Me suke zargina da shi?”

“Wai cin mutumci da barazana akan rasa rayuwar wani, da wa ka yi fada Ameer? Na sha gargadinka akan abun da kake tun kana yi abu yana wucewa yanzu ya kai har a turo police a gidana da sunan ana son a tafi da ďana? Na so na kashe case din ba tare da kaje ba amman CP ya nuna min abun ba zai yiyu ba Ameer ina tsoron ka dauko rigimar da zata fi karfina na kasa cireka daga wata matsalar”

“Waye yayi karata ne Daddy? Shi nake son sani”

“Akwai yaron da ka saka yayi wani aiki a gurin da kuke shakatawa?”

Ameer na jin haka sai yayi murmushi abun da ya bawa mahaifinsa mamaki.

“Yeah akwai wanda na saka ya bawa wani abokin mu abu”

“Kamar ya? Ka yi min bayanin komai so that na san yadda zan bullowa lamarin”

Daddy ya bukata.

“Ya taba ni ne Daddy, kuma zan koya masa hankali nan gaba kadan”

“Me ka yi masa a yanzu?”

Ameer ya kalli mahaifinsa.

“Ba su fada maka ba?”

“Wata kila laifin yana da girma shiyasa CP be fada min ba yace min sai na zo”

Babu kunya babu tsoron Allah Ameer ya fadawa mahaifinsa abun da ya aikata da kuma wanda yake da kudirin aikatawa a gaba. Daddy ya mike tsaye yana kallon đansa cike da tsoro.

“Ameer yaushe ka lalace har haka? Ka kullawa abokinka Sherri saboda kawai ya watsa maka yawu a fuska? Bayan kai ka fara takalarsa?”

Ameer ya daga kai yana kallon mahaifinsa.

“Daddy sai ka rika daga hankalinka akan abun da be kai ya kawo ba”

“Ameer kana da hankali kuwa?Miye be kai ya kawo ba? Kokarin bata sunan abokinka ko kuma kallon tsabar idona ka fada min saboda ka tambayi friends dinka yarinyar ka ta zo ya hada ka da abokinka? Ko kuma abun da ka aikatawa abokinka?”

Momy ma kallon Daddyn take  tashin hankalin da ta gani a fuskarsa ya daga mata hankali sosai, ta dade ta sanin cewar Ameer yana gwada aron hannu sai dai ba damar ta fadawa mahaifinsa gudun kar ta hada su ko kuma yayi zaton tana yi ma ďansa sheri ne. Daddy ya nuna kansa.

“Kwarin idonka ya kai ka kalleni ka fada min cewar kana da budurwa sheke aya? Dukanin arzikin da na baka na nufin ka lalace ba, amman kullum sai ka saka ni ciwon zuciya, a kullum ina nuna maka abun da kake be dace ba amman ka kasa fahimtar hakan, tun kana dauko kanana har ka fara dauko mana magana”

Ameer ya mike tsaye yana kokarin danne bacin ransa.

“Daddy wannan abun da na aikata har ya kai ka fada min magana marar dadi kamar wannan? Simple abu? Ashe wani ba zai iya taba ni na gudu bayanka na buya ba”

“Zaka iya only idan kana sa gaskiya, bana son zalinci bana son cin mutunci da rainin wayo, ka wuce mu tafi gurin CP yanzu nan, kuma karka kuskura amsa cewar ka aikata laifin nan”

Daddy ya fada yana nuna shi da yatsa, domin ya san karamin halinsa ya amsa laifin a gaban kowa a kokarinsa na nunawa duniya cewar shi baya tsoron kowa ko kuma babu mai iya hukunta shi. Ameer ya kalli Daddy kamar yace wani abu sai kuma ya juya ya fice daga falon rai a bace. Motar da ya shigo ya sake shiga yayi mata key Daddy na jin karar tashin motar ya san ďansa ba zai bi umarninsa na zuwa inda ya bukata, wani kulikulin bakinciki ne ya taso masa har sai da ya fadi kan kujera zaune.

“Ba mu yi ma iyayenmu haka ba, kullum muna gudun bacin ransu, tarin dukiya da yawan gata be saka mun lalace ba”

Momy ta matso kusa da shi tana kokarin kwantar masa da hankali.

“Zamani ne ya zo, wasu abubuwan da baka tana ji ko gani ko zato ba za su faru, wani abun jarabawa ce dole sai ka yi hakuri zaka iya ci, dan Allah karka saka komai a ranka, shi ma na san anjima kadan zai sauka ya gane kuskurensa”

Daddy ya lumshe ido ba tare da yace komai ba.

“Yanzu ka samu kashe wannan wutar, da alama shi ma yaron da ya tsokano dan manya ne shiyasa har CP ya aiko maka da police har cikin gida, idan ba haka ba ba zaka san ma an kashe case din ba”

Ya amsa mata kai yana jin yadda zuciyarsa take masa mugun ciwon, irin ciwon da ta saba yi masa tun kamin ya samu Ameer.




A gurin da ya koyawa kansa zama ya nufa, ya isa gurin a lokacin da wata zuciyar ta jika da jiransa, gaban motar Nimra ya faka motarsa sannan ya fito motar ya nufo inda Nimra take jingine da motarta fuskarta ba yabo ba fallasa ba kamar yadda ya saba yi ganinta da far'a ba.
Tsaye yayi ya kasa ce mata komai, he need someone to talk to amman ba ya jin zai iya fara yi mata magana sai dai ita ta yi masa.

“Tun safe nake a nan”

Ta fada tana kallon harabar cikin wani yanayi da ya fi kama da na damuwa. A gogon hannunsa ya kalla 12pm da mintuna ya gani, ya saka hannayen nasa aljihu yana wani shan kamshi.

“Why?”

Ta kalleshi a karon farko.

“Daman na saba zama a nan, saboda guri ne da babu hayani sosai, kuma babu mutane da motoci idan kuka kake son yi zaka yi kuka babu mai ce maka domin me? Idan kuma nishadi zaka yi duk zaka iya yi a nan, na saba na kan zo wani lokacin da kawatau zauna a nan mu ci wani abu ko mu yi hira, kamar yadda ka tararda muna ci abincin a farkon zuwanka gurin nan”

Ya daga kai yana karewa gurin kallo.

“Mi ke damunki?”

“Ban sani ba, tsoron rasa mahaifiyata ne ko kuma damuwar da ďan'uwana ya shiga ne? Na matukar son family na, musamman mahaifiyarmu ko kadan bana son na ganta a cikin damuwa, damuwarta tana haifar min da tashin hankali, wani lokacin sai na rika jin kamar zan iya rasata idan na rasata ya zan rayu? Ummi tana yawam shiga damuwar da bata fadawa kowa, tashin hankalin da na gani a cikin idonta a jiya saboda yaya da kuma halin da yayana ya shiga ya saka na tashi ina jin wani yanayi na dabam”

A karon farko ya jingina jikin motarta ba tare da tunanin kar tufafinsa su kwashi datti ba kamar yadda ya saba jin tana cikin damuwa ya saka ta sa damuwar nisantar ruhinsa.

“Akwai ta inda zan iya taimakawa?”

Murmushi ta yi.

“No... Karka damu komai ya wuce a yanzu, fada min ya kare da abokinka?”

“Kamar baki cikin yanayin da ya kamata mu yi wannan hirar, but na yi nasara kuma ina daf da sake yin wata nasarar, but yau din ma an sake mata min saboda shi”

“Waya bata maka rai?”

“Daddy na”

“Karka damu da sannu zamu ga bayansa da yardar Allah, duk makiyin da ya saka mu gaba sai mun ga bayansa”

Ya daga mata gira

“Yeah...”

Tare da yin murmushi mai sauti kamar ba shi ba, ita ma ta yi murmushin tare da busar da numfashi.
[06/06, 9:40 am] 𝐊𝐡𝐚𝐝𝐞𝐞𝐣𝐚 𝐂𝐚𝐧𝐝𝐲 ✍️: *⚜️ ...WANI GARI... ⚜️*


_Na Khadeeja Candy_


BARKA DA SALLAH
Allah ya maimaita mana ya karbi ibadun mu, Ameen.


7️⃣


MALEEK POV.

Maleek ya hade carpet din da yayi sallah da shi ya mike tsaye ya juyo ya kalli Mahaifiyarsa dake cikin shirinta na fita.

“Ummi da zaki taimaka ki fita a maganar nan, tsakanina da friends dina ne?”

“Friends...?”

Ummi ta tambaya tana matsowa kusa da shi da wani irin mugun kallo.

“Maleek har kana da karfin halin sake kiran mugayen mutanen nan friends dinka? Maleek kasan abun da abota take nufi? Abota na nufin mutanen da za su tsaya da kai a lokacin da kowa ya guje ka, ku fadi tashi ku tashi tare, ba mutumen da zai cutar da kai ko a hada kai da shi a cutar da kai ba, kamin na haife ka na yi wata ƙawa wanda na gudu da cikina na farko na tafi garinsu na boya, kuma ta bani mafaka a lokacin da nake tsananin bukatar mafakar, na ji ciwo na kwanta asibiti ta kwanta tare da ni da yi jinya ta har na samu sauki, idan na fada mata sirri na ce bana son kowa ya ji ba zata fada ba, wannan ake kira abota, ba mai cutar da kai ba...”

Cikin fada take masa maganar, sai ya jefar da carpet din saman gadonsa ya kalleta.

“Ummi kin taba haihuwa kamin ni?”

A take sai ta ji kamar ta kwancewa kanta zane a kasuwa, tsoron kalar amsar da zata bawa danta Maleek ya maye gurbin bacin ranta.

“Cikinka nake nufi.....”

Ta furta murya na rawa tare da dauke idonta daga barin kallonsa ta juya ta fice daga dakin. Iskar bakinsa ya juya fuskarsa gurin wayarsa dake ringing.

“Dawood”

Ya fada sannan ya karasa ya dauki wayar ya danna picking.

“Hello”

“Maleek ya ne kana lafiya”

Ya fada kansa

“Lfy Kalau for now”

“Muna tare da Abdull zamu zo gidanku yanzu nan”

“No karku zo yanzu, Ummi fada take zan kira ka

1 Comments On WANI GARI
avatar
naima-3

1 year ago

Reply

Thank you

Please Login or Register in order to submit comment