Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

be san duk wannan wahalar ba, idan zai yi tafiya kamin time din tafiyar yayi an shirya masa komai, sannan jirgi yake hawa ba mota ba, sai idan zai isa Airport ko kuma daga Airport zuwa gida ne kawai yake hawan mota sai kuma yawon cikin gari, motar ma sai wanda ta amsa sunan motar da ba kowa ya isa ya hau ba, ya kwanta a gado mai kyau gida mai kyau tufafi baya saka mai karamin kudi, kudin Naija ma idan ba ganin dama ba ba zai rike ba sai Dollars kuma babu mai ce masa dan me? Wani lokacin ma a private jet ma za a kai shi inda yake so na mahaifinsa , tun da yake a rayuwarsa be taba hawa motar haya zuwa wani gurin ba sai a yau. Sai a yanzu yake jin be kamata ya bijirewa umarnin mahaifinsa ba, mi zai saka yayi haka? Why? Gashi makiyinsa ya samu yadda yake so bayan raba shi da abokansa, ya busar da iskar bakinsa ya dago kadan yana kallon hanya sosai yake son yin bachi amman ya kasa saboda babu ac a motar kuma iskar dake shigowa ta gilashin motar yayi masa yawa, abu ne da be saba da saba da shi ba. Haka dai ya daure har suka isa kano. GRA suka shiga direban be sauke shi ko'ina ba sai cikin gidan Hajiya Jamila. Yana fitowa motar ya ciro kudin aljihunsa gaba daya ya mikawa direban.

“Ka kara da wannan”

A firgice direban ya fito daga cikin motar gaba daya ya zagayo inda Ameer yake tsaye ya fadi kasa ya rike kafafuwansa yana masa godiya har da hawayensa, shi kansa Ameer ba zai fadi ko nawa ne kudin ba, balle kuma wanda aka bawa kyautar domin babu wanda ya kirga a cikinsu, sai dai ganin yan 1k da yawa ya san kudi ne mai yawa.

“Ba wani kudi ba ne fa”

Ameer ya fada domin ba ga wani abun godiya da mutumen zai masa ba, akan abun da be taka kara ba balle har ya karya.

“A gurinka ba komai ba ne ranka ya dade, amman ni a gurina kudi ne mai yawa, da tsoro na kawo ka Kano ashe ban sani ba rabo ke kirana, motar nan ba tawa ba ce amman ka ga abun da Allah yayi min”

Ameer ya dan ji wani irin for the first time domin yau ne karo na farko da yayi sadaka, not just sadaka wannan ne karo na farko da yayi ma wani abun kirki kuma har aka masa godiya, this is the first time da ya kyautataw wani. Tabe baki kawai yayi ya nufi cikin gidan da harabarsa ma ta ishe talaka da wani bakauye kallo domin kana ganin gidan ka san Ameer ya isa har ya wuce, a tunanin direban gidansu Ameer ne, shi kuma ya zabi zuwa Kano ne saboda ba zai iya jure tafiya a Abuja a motar haya da babu ac ba, kudin dake aljihunsa ma ya bashi kyautar su ne saboda baya jin zai sake taba kudi mai datti again, daman ya matsu su fita aljihunsa sai yake jin kamar tsukarsa suke.

This is the second reason da yake son zuwa gurin Hajiya Jamila kullum kofar falonta a bude take not like gidansu da sai danna ko ka yi knocking za a bude maka, talkaminsa ne abun da ya fara cirewa sannan ya shiga falon. Hajiya Jamila dake zaune kam carpet rike da carbi ta dago ta idonta dake sanye da gilashi ta kalleshi, a take annashuwa da farinciki suka wanke zuciyarta har suka kasa boyuwa sai da suka bayyana a fuskarta.

“Ameer... Dana....”


Ta fada tare da aje carbin ta mike tsaye ta cire gilashin ta bude masa hannayensa tana masa alama ya karaso gareta, sai ya tsaya yana kallonta.

“Akwai datti a jikina sosai i can't hug you like that, idan na fada miki wahalar da na sha sai kin yi wahala”

Ita da kanta ta karasa inda yake tsaye ta rumgumeshi.

“Ban taba jin kyamarka ba ďana, ba zan taba kyamarka ko kuwa datti duniyar nan zai tabbata a jikinka ne”

Maganar take hawaye na sauko mata, shi kansa ya san Hajiya Jamila tana matukar kaunarsa, kamar yadda yake kaunarta sosai a ransa domin mahaifinsa ya fada masa ita ce second macen da nononta ya kai cikin cikinsa bayan mahaifiyarsa.

“I miss you so much Ammyna and i Love You”

“I love you more Son”

Shi ma rumgume ta yayi sannan suka nufi kujera suka zauna tana rike hannunsa, wani irin kaunarsa take kamar ta bude zuciyarta ta saka shi ta rufe ta hana kowa iko da shi sai ita kadai.

“Ina ka je Ameer?”

“Daddy ya kira ni?”

“Ya kira ni, kuma hankalina ya tashi sosai, Ameer ashe ni ba mahaifiyarka ba ce idan Mr Bashir ya koreka ba zaka iya guduwa ka zo gurina ba? Ka daga min hankali sosai ina ta fargabar abun da ya same ka, duk inda na san zaka iya zuwa na bincika amman ban san samu ka ba, Wayoyinka duk a kashe”

“Ance Daddy be da lafiya da gaske ne?”

Ta daga masa kai.

“Kuma Saboda kai ne Ameer, ni yanzu na yanke shawara tun da har matsala kuke samu zaka zauna a gurina shi kuma sai ya zauna a can tare da matarsa da yayansa, daman ni bana ni da kowa sai kai, kai kadai nake da Ameer Allah be bani kowa ba sai kai kadai”

Jikinta har rawa yake tana taba fuskarsa, akwai wani irin rauni da tarin damuwa a gurin macen da girma ya kamata kuma bata ganin sanyin idaniyarta ba, bata da wani ďa na cikinta sai dan ya sha nononta kamin girma.

“Ina da duk wani abu na jindadin rayuwa da zan baka Ameer, kuma zan jidadi idan ya zabi zama a nan, ko ba komai mahaifinka zai samu space kuma za su daina fada da juna”

“Ammyna kin san ina sonki, amman ba zan iya zama a Kano ba, rayuwata gaba daya a Abuja nake yinta musamman a yanzu da ya kamata na dauki fansa, mun saba na kan zo na dubaki ke ma kuma kina zuwa dubani idan kika yi marmarina”

“Haka ne”

Ta fada ba dan ranta na so ba, sai dan ya zame mata dole ta so abun da yaron da take kallo a matsayin ďanta yake so, tana da ƴaƴan yan'uwa da take riko maza da mata amman bata son kowa kamar yadda take son Ameer saboda ya sha nononta shi ne kadai ďan da ta shayar a matsayin nata ta rumgume shi a hannunta ta yi masa duk wata hidima da uwa take yi ma ďanta.
Ya mike tsaye tare da cire rigar jikinsa

“Ina yan matan gidan nan?”

“Basa nan kasan an koma makaranta duk suna makaranta, bari na shirya maka abun da zaka ci kamin ka yi wanka”

“I hope my room is clean”

“Kullum dakinka a gyare yake Ameer, kullum ina sakawa a gyara shi a saka turare saboda ina saka ran zuwanka a ko da yaushe kamar yadda kake yi ba tare da ka fada min ba”

Yayi murmushi sannan ya nufi hanyar fita falon domin dakinsa ba a cikin part dinsa yake ba, gidan kuma ba bakonsa ba ne.




MALEEK POV.


“No ba sai kin zuba min ba, zan karya tare da yarana”

Abiey ya dakatar da Ummi a kokarinta na zuba masa ruwan zafin da suke ta kamshi. Dagowa ta yi ta kalleshi doguwar riga ce a jikinsa har yanzu babu annuri a fuskarsa, dawowar da yayi ma bayan kauracewa gidan ta yi tambayarsa dalilin haka sai ya fada mata ba komai aikine ya biyo da haka, yanzu kuma yana kokarin kauracewa abincinta.

“Fushi ne har yanzu ranka ya dade?”

“Ke fa kika fada min cewar mu ba yara ba ne a yanzu, to mi zai saka mu yi ta abu kamar yara?”

Yaja kujerar daya saba zama ya zauna, daman ya saba ya kan yi breakfast tare da yaransa irin weekend haka ita kuma ta yi da yan matansa, saboda Maleek da baya kaunar zama kusa da mace ko jin muryarta ko da kuwa mahaifiyarsa ce balle kuma kanenesa sai dole, idan har ana son aga sakewarsa sai idan an bar shi ya kebe da maza yan'uwanshi ko kuma mahaifinsa da kanensa, wannan ya saka Abiey ya ware musu gurin karyawa ko yin lunch saboda Maleek. Ta bude baki zata yi magana Mahmood ya shigo falon sai ta yi saurin hade kalamin ta dauke hannayenta daga teburin ta nufi kofar fita, hakan yayi daidai da shigowar Maleek matsawa yayi gefe domin ya bata hanya ta fita, secondly kuma baya son jikinsa ya taba nata. Tsayawa ta yi kallonsa shi kuma ya sauke kai kasa.

“Ina kwana?”

Bata amsa masa ba sai ta tambaye shi abun da ya fi tsaya mata a rai.

“An gano inda Abokin ka yake Maleek?”

“I don't think so”

In a very law voice ta yi masa maganar, amman hakan be hana Abiey jiyo abun da take tambayar ďansa ba, domin hankalinsa gaba daya yana kansu.

“Ina matukar kaunar yayana, hakan ya saka nake kaunar farincikinsu, ko kadan bana son abun da zai daga hankalinsu ko ya saka su a damuwa”

Ko be ambaci sunanta ba ta san da ita yake, jiyowa ta yi ta kalleshi sai kuma ya juya ta fice ba tare da tace komai ba, fuskar mamaki Mahmood yayi ya kalli mahaifinsa sai dai be ce komai ba, Maleek kuma yayi zaton saboda Ummi ta tsaya a kofa ne ya saka Abiey fadin haka sanin baya son kusanci da mace sai dole.
Kuskus Ummi ta samu Nimra da yar'uwarta na yi, suna ganinta sai suka daina Namra ta shiga hadawa kanta Tea Nimra kuma ta saka taba komai, sanin cewar tsakanin Uwa da ya ana sirri haka aboki da aboki balle kuma dan'uwa da yar'uwa ya saka bata damu ta san abun da suke tattaunawa akai ba, sai dai ta damu matuka da damuwar da take gani a fuskar yarta Nimra, domin abu ne data kasa boyewa gaba daya mu'amalarta da annashuwarta basa tare da ita yanzu, a baya kuma ba hala take ba, da m Namra ce ba za a gane idan tana cikin damuwa ba domin ita bata sakewa da mutane kuma bata da yawan far'a da raha ba kamar Nimra ba. Ummi da kanta ta zuba mata tea ta aje mata komai sannan taja nata kujerar ta zauna, no matter how take jin damuwa idan ta ga yaranta a cikin wata damuwar sai nata damuwar ya gushe. A hankali Nimra ta kai ta fara cin abinci gaba daya jin sa take kamar dusa ba domin ba abincin ne a ranta ba, Ameer take tunani ko a wane hali yake a yanzu, ta san yana raye saboda alert din da ta gani na kudin da aka cire a ATM din data bashi sai dai har zuwa yanzu wayar bata shiga idan ta kira. Idan ya dawo ya za'ayi ya yarda da ita? Shi ne babbar damuwarta a yanzu, and miyasa take damuwa da haka shi ya zama third damuwa a gareta.
Misalin karfe biyu da rabi na rana Nimra na zaune falo not knowing what to do, Namra kuma bata gidan ta fita gurin aikinta Mahmood na zaune a dinning tare da Ummi, yayinda mai aikinsu take aikin aje manyan warmers a dinning din, Abiey ya shigo hannunsa rike da waya Maleek na bayansa. Ummi na ganinsa sai hankalinta dana Mahmood ya koma kansa domin be a yanayin da ke nuna lafiya ta kawo shi, Nimra ma tashi ta yi zaune.

“Lafiya Abiey?”

Ummi ta tambaya tana baro dinning din ta nufo inda yake tsaye. Be amsa mata ba ya kalli Nimra ya ce.

“Nimra ina motarki?”

Kamar saukar aradu haka Nimra ta ji tambaya, wani irin dakan goma goma ta ji zuciyarta na yi, yawu ta hade da karfi numfashinta ya fara rawa.

“Ta... Tana gareji...?”

“Don't lie to me girl ina motarki take?”

Wani karin faduwar gaban ne ya sake samunta. Ummi ma kallonta take domin babu wanda yayi noticing motarta bata gidan sai yanzu.

“Daman motarki bata gida?”

Ummi ta tambaya sai ta kalleta ta daga mata kai.

“Eh tana gareji”

“Daman mun kun saba kai mota gareji da kanku a gidan nan ne? Karki min karya Nimra motarki tana police station din Katsina and they are on their way to arrest you for what you did”

Wani irin gumi ne ya karyo mata bata san lokacin da ta saki wayar hannunta ta fadi kasa ba.....





©Khadeeja Candy
©®Copyright
2023
[06/06, 9:40 am] 𝐊𝐡𝐚𝐝𝐞𝐞𝐣𝐚 𝐂𝐚𝐧𝐝𝐲 ✍️: *⚜️ ...WANI GARI... ⚜️*


_Na Khadeeja Candy_


1️⃣1️⃣

Ganin yana kokarin saka babbar rigarsa ta kalleshi tana karasa bude abincin.

“Abun da ka fi so ne na girka”

“Eh na ji kamshi ai, akwai abun da ya taso min na na gaggawa, zan ci abinci a waje”

Ya fada ba tare da ya kalli inda abincin yake ba, da fuskar mamaki ta sake kallonsa.

“Ba ala'adarka ba ce cin abinci a waje, na san na bata maka rai amman ka yi hakuri”

Ya juyo ya kalleta irin duba na manya yana tambayar abun da ta yi masa kamar da gaske be san abun da ya faru ba. 

“Akwai abun da kika min ne? Zan tafi sai na dawo”

Ya nufi kofa yana daidaita tsayuwar hularsa. Ganin haka ya saka ta mike tsaye.

“Ranka ya dade a gafarce ni, idan ba fushi kake da ni ba, me zai saka ba zaka ci abinci ba? Baka yi min irin haka sai idan shaidan yayi galaba akan mu”

Be amsa mata ba be kuma juyo ya kalleta ba har ya fice, komawa ta yi ta zauna ta rufe abincin tana jin wani iri a zuciyarta, ko kadan bata son ganin bacin ran mijinta kamar yadda shi ma baya son ganin bacin ranta, wannan na daga cikin abun da ya karawa rayuwar aurensu karko da dadewa. A bangarensa ta zauna tana ta jiran dawowarsa zuwansa har aka yi magariba aka sauko daga Sallah Isha'i Abiey be dawo gidan, tun abun na normal a zuciyarta har ya fara daga mata hankali, gurin karfe 1 na dare ta kira wayarsa ta shiga tana ringing amman be daga ba, a nan hankalinta ya tashi sosai ba na tsoron halin da yake ciki ba, sai na fushin da yayi da ita, domin be taba fushi ya kaurace mata ba, iyakar fushinsa da ita ya shareta ko ya kauracewa abincinta ko shimfida amman ban da kauracewa gida kuma ta kira shi ya ki dagawa, ba abu ne mai kyau ga namiji mai iyali ya kwana a waje ba, balle kuma shi da yake da manyan yayan da idan suka aikata hakan zai yi musu fada. Sai a lokacin ta fito daga bangare, daman ban tunanin rayuwarta ta baya babu abun da take gaba wunin yau ta ji shi wani iri. Bangarenta ta shigo sai ta samu wutar falonta a kunne Nimra na zaune saman kujera ta rumgume hannayenta, da sauri Ummi ta nufi gurinta domin duba lafiyarta, kusan wannan shi ne karo na farko da ta samu yarta Nimra a farke kuma a falon ba a dakinta ba, ko da tana kaiwa wannan lokacin ita dai bata taba gani ba, Namra ce mai dade wani lokacin bata yi bachi ba, tana kallon ko wani abun na dabam, sai kuma Maleek dake kwakwayar aljannu domin shi daren ne yafi jindadinsa fiye da rana.

“Nimra...”

Ta juyo ta kalli Ummi da idonta dake nuna alamar ba su shirya bata hadin kan yin bachi a yanzu ba. Ummi ta zauna kusa da ita tana fahimtar damuwar dake bayyana a fuskarta.

“Miya hana ki bachi a wannan lokacin Nimra?”

“Ummi ban sani ba, kawai kaina yana dan ciwo kuma bana jindadin rai na”

Lamari irin na uwa mai kula, sai ta danne nata damuwar ta fuskanci yarta.

“Akwai abun da yake damunki Nimra? Karki boye min”

“Ban sani ba, ina jin kamar akwai damuwar na tsoron rasa abun da ban riga na samu ba”

“Are you in love?”

“No, ban ce ina son sa ba, shi ma ba so na yake ba, amman shakuwar da muka fara ne bana son na rasa”

Ta fada idonta na cika taf da kwalla.

“Wani abun kika masa?”

“Shi yana kallon abun a matsayin laifi, amman ni a gurina ba laifi ba ne domin ban aikata dan na bata masa rai ko na cutar da shi ba, shi ya juya min baya yanzu ina ta kiran wayarsa be daga ba”

Be like a best friend to your kids, shi ne abun da Ummi ta yi har ta san damuwar Nimra, sannan ta fara kokarin kwantar mata da hankali.

“Ban san waye wannan Saurayin ba Nimra, amman na san yana da muhimmanci a gareki, domin duk wani abun da zai hana yata bachi a wannan lokacin to abu ne mai muhimmanci, kaurace miki da yayi da kuma fushi hakan na nuna cewar shi din mutum dan'adam wanda ke ma zaki iya yin abin da yayi, saboda haka ki daga masa kafa har sai ya sauko daga fushin, wani lokacin nisantar juna yana da amfani domin mutum zai gane muhimmancinka, kuma zai yi kokarin kiyaye laifin da ya saka aka yi haka agaba, kamar yadda zai bawa wanda aka cutar ko yayi fushi damar hucewa kuma yayi tunani, ki kwantar da hankalinki komai zai daidaita”

Ta kwantar da kanta a kafadarta, maganar take wani sashe na zuciyarta na tuna mata da abun da mijinta ya aikata a yau, ko ba komai dole ta kiyaye maganar Ameer a gabansa kamar yadda take ta kokarin yi shekaru masu yawa baya, shi kuma zai samu kebewa ya huce haushin abun da ta aikata, ta san yayi haka ne saboda kar matsalar ta su ta yi yawa, kuma yayi mata hakan ne saboda ya ladaftar da ita da abun da ta yi masa. A hankali Ummi ta aje numfashi tana jin abun nan da ya saba tsaya mata a zuciya ya tsaya kyam ya tokare mata zuciya.

“Tashi muje ki kwanta”

Ba musu ta mike tsaye Ummi ma ta yi tsaye tana rike da hannunta kamar wata karamar yarinya suka nufi upstairs, sai da Ummi ta tura kofar dakinta ta bude sannan Nimra ta shiga ta kwanta Ummi ta kashe mata wutar tana tunatar da ita cewar ta yi addu'ar kwanciya, sannan ta ja mata kofar dakin ta rufe. Ummi na fita Nimra ta mike tsaye ta rumtse ido tana jin wata sabuwar damuwa na kwankwaso mata kofa, a nan ma bachi yace ba da shi ba, fir idonta suka ki kusantar inda bachi yake har asuba gashi shaidan yayi galaba a kanta ta kasa raya daren da ko da Nafila biyu ne ko karatun Qur'ane. Gaba daya tunaninta ya tafi akan abun da zata aikata Ameer ya yarda da ita, wace hanya zata bi ta gamsar da shi cewar ba da hadin bakinta aka yi ma abun sa yake zarginta da shi ba, ta damu sosai ita kanta neman dalilin damuwar take ta rasa.
Misalin tara ta fito dakinta Namra da mai aikinsu Ramatu suna zaune falo suna kallon maimaicin wani shiri da Zee word suke, kallo daya yar'uwarta ta yi mata ka gama fahimtar akwai damuwa a tare da ita, domin idonta ya nuna bata samu bachi ba kamar yadda idon Mahaifiyarsu ma ya nuna dazun da ta shiga ta gaisheta. Sai dai bata ce mata komai ba domin ta lura Nimra bata son kallonta abun da ke nuna mata son magana akan hakan kenan. Har zuwa lokacin da ta zauna a falon trying number wayarta da ta bawa Ameer take amman bata zuwa.


Bachi ya dauke shi sosai be san lokacin sallah azuba yayi ba har sai da rana ta fito ta haska fuskarsa, sannan ya tashi zaune sai da ya karewa kereren dajin kallon sannan ya ja tsaki ya mike tsaye one of the best thing dake bata masa rai akwai missing Sallah, ya tsani lokacin Sallah ya fita be yi Sallah ba, mika yayi sannan ya fara leka sannan ya juya da zimmar ya juyawa ba dan ransa ya so ba ya koma gurin motar Nimra ya dauki ruwan da ya siya yayi alwala, sai kuma ya juyo ya duka ya dauke carpet din da ya kwanta a kai, sannan ya nufi wani gurin kai kama da hanya, to his surprise sai ya hango manyan duwatsu da korama a gafensu, hakan ya faranta masa rai daman dan dole ne kawai zai tafi dauko ruwan da suke cikin motar natar da yake yi mata kallon makiyiyarsa a yanzu.

Gurin wani karamin dutse ya aje carpet din sannan ya nufi gurin ruwan, a hankali ya rika sauka har ya isa bakin gabar da ruwa sai da ya mika hannu zai saka a cikin ruwa sai kuma ya tuna, ya kwanta a gurin da be san mi ua taba shi a gurin ba, secondly ya taba carpet be wanke hannunsa ba, to taya zai yi amfani da hannu ya taba ruwan da zai kai bakinsa ya kuskure. Wani dogon tsaki yaja ya juya a dolensa ya koma gurin motar ya bude ya dauko sabulu da ruwan ciki ya wanke hannunsa sannan ya dauki box din sarewarsa da wasu abubuwan da zai iya ci ya sake dawowa gurin koramar, can gefen duwatsun ya nufa yayi fitsari, ya dawo carpet din ya fara shimfidawa ya aje komai a gafe sannan ya sake wanke hannunsa ya shigar da hannayen ya fara alwala sai da ya gama da yanayin fitowar rana yayi amfani ya gane gabas a dajin, cikin natsuwa ya gabatar da Sallah asuba dinsa sannan ya gyara zama yana karanta ayatul kur'asiyu bayan ya gama ya daga hannunsa sama yayi mahaifiyar addu'a, bayan yi ma uwarsa da Daddy ya fada masa cewar ta rasu addu'a, baya kara wata addu'a ko wace iri ce ba halinsa ba ne weather ta neman tsari ce ko ta neman wani abun duniya, sai dai be taba fashin yi ma mahaifiyarsa addu'a ba, domin yana jin marmarinta duk da kasancewar be taba ganinta ko da a hoto kamar yadda be san kowa nata ba, domin Daddy be hada shi da kowa a matsayin dan'uwa ko yar'uwar mahaifiyarsa shi kuma be damu da hakan ba, sai dai a yau yana jin marmarin mahaifiyarsa fiye da ko yaushe, ya tabbatar da ace yau mahaifiyarsa tana raye da ba zata bari mahaifinsa yayi masa wannan korar ta wulakanci ba.
Jikinsa ne ya bashi cewar ana kallonsa sai ya juya da sauri ya kalli tsakankanin manyan duwatsun da suke gefensa, sai dai be ga kowa ba, ido ya kurawa gurin sosai yana kallo ko wani abu zai fito ko kuma a sake lekowa amman be ga komai ba. Gyara zamansa yayi ya bude box din sarewarsa ya daukota ya rike yana shafawa. Tunawa yayi da lokacin da yake busar da Nimra ta ji har wata yar karamar alaka ta shiga tsakaninsu, duk wasu kalamai da ta furta masa a lokacin sai da suka dawo masa, a take ya kara jin ransa ya kara hauhau wa ya jagula, busar da iskar bakinsa yayi ya kai tsarewar bakinsa ya rumtse ido, busar sarewa na daga abun da ke kawar masa da bacin rai ko damuwa idan ya samu kansa a daya daga ciki. Busawar ya fara yi cikin kwarewa da gwaninta kamar yadda ya saba, a take gurin ya dauka.


Kai ta daga sama tana kallo kamar a saman ne ake busar, cikin karfi hali ta dago ta mike tsaye zuciyarta na bugawa da mugun karfi ta taka kafar tana dingishi ta sake lekoshi a karo na uku. A take zuciyarta ta raya mata cewar Eid ne, sai dai kammanin da tsayin ba iri daya da Eid ba, kamar yadda tufafin jikinsa ma suka banbanta da na garinsu, sai dai ta yi imanin Eid ne kadai ya iya irin wannan busar sarewar, komai kwarewar mutum ba zai iya yinta ba, kuma babu wanda ya san tana a gurin balle ya zo sai Eid da zai iya ganinta ko Sarki a cikin tukunyar tsafinsu. Ta sani idan Eid ne ba zai cutar da ita ba, sai idan wani ne zai yi yanayi da shi din amman ta iya zai iya busar kamar shi? Idan kuma Eid ne me

1 Comments On WANI GARI
avatar
naima-3

1 year ago

Reply

Thank you

Please Login or Register in order to submit comment