Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

murmushi yay yace "ai duk na kuresu bama wanda zai somin Mata"
Tagumi kaka tay tace " kori kuma?"
Eh mana duk samarin ta ni nake koran su, lbrn komai ya bata tare da cewa " nidai ki taimakamin don Allah"
Numfashi kaka taja tace " toh shekinan na yanda da mgnr ka amma zan kara tunani akai"
Murmushi yyi yace " ngd Matar shiyasa nake kara sonki wlh" itama murmushi tay , lkcn yayi dai² da shigowar Yasmeen d'akin fuskar ta dauke da murmushi" kallonta kaka tay tace " dariyar me kuma kike" tabe baki tay tace " ba komai kakus ta fada tare da hararan Mahmud dake kallonta yana murmushi" yini sukayi a asibitin har dare Daddy ya dubashi ganin ba wani matsala ne yasa ya bashi sallama suka dawo gidan tare, sosai wanan daren Mahmud yay baccin farin ciki domin yau dai ya samu ya furta abunda ke ransa sai yake jin kanta watsai"
Washe gari da Asuba ya fito masjeed inda suka hadu dasu Abba, bayan sun gama sallah ne ya gaishesu inda suka masa ya jikin?" yace " alhamdulillah" murmushi Daddy yay yace " kar kayi wasa da shan magungunan ka"
Cikin jin kunya yace " insha Allah daddy na gode sosai"
Da haka suka dawo gida, Mahmud ya wuce part dinsa su kuma suka wuce na kaka, sallama suka shiga bedroom dinta, samunta sukayi tana lazumi hakan ya sasu zama suna jiranta" domin ko wani rana idan sun dawo masjeed part dinta suke wucewa su gaisheta" sanda ta gama lazumi kafin suka gaisheta, ta amsa cikin tsakin fuska k'amar yanda ta saba, kafin ta gyara murya tace " inason zanyi mgn daku akan lamarin Mahmud dinan ne"
zama suka gyara sukace " muna jinki" nunfashi taja tace "
A ganina me zai hana a hada yaran nan Aure k'awai"
Abba ne yace " wani yara kenan ko akoi wacce Mahmud din keso?" Tace " Auren Mahmud da Yasmeen tunda dai ita Yasmeen ba wani wanda ta tsayar har yanzu, shima Mahmud din haka, wata kila son junan su suke shiyasa ba wanda ya finda kowa acikin su" ko ya kuke gani?"
shiru dukansu sukayi suna nazarin mgnr da kaka ta fada, To me kuke gani kunyi shiru cewar kaka dake binsu da kallo" nisawa Abba yay yace " in hakan ya faru zamufi kowa farin cikin hakan, amma a yanda suke basa jituwa sosai din nan anya kuwa zasu iya son junan su kuwa?" Murmushi kaka tay tace " hakane amma ai Mahmud din da kansa ya fadamin yana son Yasmeen abunda ya hanashi finda wacce yake so kenan"
Murmushi Daddy yay yace " ai shikenan indai shi Mahmud din yana sonta" Abba yace " toh ita Yasmeen din tana sone?" Daddy yace " ko bataso dole sai an daura tunda shi Mahmud din yana so"
Abba yace " nidai a ganina a tambaye Yasmeen dinma aji ra ayinta, kaga tana masayin Yayar shi da wuya ta aminci" ya Fad'i hakan ne don ayi komai cikin farin ciki" amma kuma har cikin ransa zaiji dad'in haka domin har idan Mahmud ya mallaki Yasmeen a masayin mata zaiyi farin ciki sosai"
Murmushi Daddy yay yace " ai mace duk girmanta na miji shine gaba da ita" bama wanda zai kalleta yace ta girmi Mahmud" mudai kawai mu musu fatan alkairi da zaman lafiya, a fara shirye ² biki kawai ba wani bata lkcn nan da Wata daya"
dukan su dariya suka sanda tare da musu fatan alkairi , kafin suka taba hira kad'an suka mata sallama kowa ya wuce part dinsa"
Dukan su suna shiga part dinsu suka sanar wa Matan su abunda suka yanke tare da cewa " zasu fada musu idan sun gama breakfast don kowa ya fara shirinsa",.sosai abun ya girgiza su domin abunda basu taba tunani ba kenan,amma ba yanda suka iya haka suka musu fatan alkairi"
Haka kuwa akayi bayan an kammala breakfast kowa ya fito harda Mahmud daya shigo ya gaida kuwa, ya zauna sukayi breakfast, bayan sun kammala, Yasmeen ta kwashe komai ta mayar dashi kitchen ta dawo ta zauna" kallonsu Daddy yyi yace " Mahmud da Yasmeen ku bani hankalin ku anan, zanyi mgn daku" Abba dai baice komai sai kallonsu da yake yana karantar yana yinsu"
Gaban Yasmeen ne ya yanke ya Fad'i take taji zuciyar ta ya mata wani iri da sauri ta dago da kanta ta kalle Daddy, sai kuma ta sunkuyar da kanta"
Shima Mahmud gaban sane ya Fad'i, addu'a kawai yake cikin ransa yana suraron suji me Daddy zai fada"
Gyara murya Daddy yay ya fara da nasiha, kafin yace " amatsayin mu na iyayenku munyan ke wani shawara a kanku ba tare da mun tambaye kuba ku munji ta b'akin ku, mun yanke shawaran hakan ne sbd munsan bazaku bijire wa umarnin muba, shawaran da muka yanke akan ku shine na hadaku Auren da zamuyi, nan da wata d'aya insha Allah ina fatan dai zakuki mana biyayya ba"

" wani irin dum² kirjin Yasmeen ya buga, da sauri ta dago da idanunta da suka sauya launi ta kallesa tare da sunkuyar da kanta, tama k'asa tantance mafarki take ko da gaske"
Shi kuwa Mahmud farin ciki k'amar ya kasheshi, sai murmushi yake Aransa yana mai godewa kaka domin yasan itace tay wanan abun ai yau dole ya bata k'yauta ta musan man"
Sun dauki 5 minutes kafin a hankali sukace" insha Allah bazamu baku kunya ba, murmushi daddy yayi yace " Allah ya muku Albarka ya sanya alkairi idan akoi abunda kuke so sai ku sanar dani" yana fadar haka suka fita daga parlor"

Suna fita daga parlor Yasmeen ta dago da idanunsa da suka koma ja ta kalle Mahmud, had'a idanu sukayi ta b'alla mishi wani uban harara, shima hararan ya watsa tare da mikewa cikin burin kunya yace " kan bala'i taya ma hakan zai faru?" Aure dake wai tab abunda bazai yuba kenan, BANA SONKI BAKI SONA taya hakan zai faru kai akai akoi sake zancen, Kodai ² ke kikace kina S.....!


share fisabilliah Habibaty 🥰
[1/30, 21:25] ~Ms Fatima: 💅 *K'ANINA NE* 💅


*Story and written*


*By Fatima Mrs Ahfat*


*ELEGANT ONLINE WRITER'S 📚*

*Bismillahir rahmanin Rahim*

Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*

*I selling MTN data with this cheap price*

*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance.
*Validity 1 month*

*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR
Call 08066268951*



*Page 9*


__________ Saka makon ganin sa da tayi yana ko karin fad'awa daga saman bed din baya cikin haiyacinsa"
Da sauri da k'arasa ta tarosa ya fada jikinta, "innalillahi wa inna ilaihi rajiu'n!!" Ta furta lkcn da taji ya lafe ajikinta nunfashisa ya dauke"
Saurin mayar dashi saman bed din tay, ta fara kiran sunan sa amma shiru, hakan ya sata fitowa daga dakin da sauri jikinta na wani irin rawa, Aranta tana cewa"Allah yasa dai ba mutuwa yyi ba, tun bamu yafewa junaba" jin zuciyarta na bugawa da sauri ² yasata kawarda tunanin a cikin ranta"
Parlor ta fada tana haki tace " Yana kwance baya nunfashi"
Mikewa dukan su sukayi Abba yace " Mahmud din kowa?" Eh Abba Mahmud baya nunfashi" ai kafin ta k'arasa mgnr dukan su suka fita da sauri, Anty Amarya ce ta haura bedroom din Daddy ta dauki key din Motar ta fita itama"
Suna shiga dakin suka gansa kwance ba alamar Numfashi a jikinsa, da sauri suka daukesa suka sanya shi a Mota suka fice d'aga gidan da mugun gudu" kakus na ganin haka ta fashe da kukas tace " itama zataje domin baza iya zama agida mijinta na asibiti ba" su Ummi ne suka fara bata hakuri da rarrashinta har suka dawo parlor, suka sami Yasmeen na zaune ta buga uban ta gume, tana masa addu'a cikin ranta domin yau dai taji tausayinsa sosai, fatan ta dai kar ya mutu basu yafewa junaba"
Kallonsu tay a sanyaye tace " meke faruwa kakus naga sai zabga kuka kike harda majina?" Da kuwa Anty Amarya ta mata tace " tashi ku tafi da kaka asibitin kafin muzo"
Tom ta fad'a tare da wucewa bedroom dinta ta dauki hijab dinta da key ta fito, tace " mutafi ko kakus"
Kakus na kuka tace " anya maryam ma wanan yarinyar ta kware a tuki kuwa karta jefeni a bakin hanya"
Dariya taso bawa Anty Amarya tace " ta kware sosai"
Toh shikenan ai gara na tambaya kar garin dubu mijin nawa abu ya baci"
Dariya Yasmeen tay tace " kakus mezai baci kenan?"
Harara Ummi ta watsa mata tace " ban son tsakarci, idan kunje duk abunda ke ciki ki sanar mana" okay" ta fada suna ficewa daga parlor, parking space ta wuce ta dauki farin Mota ke kyau tazo dashi kaka ta shiga taja Motar suka bar gidan"
********Bangaren su Abba kuwa direct asibitin su suka nufa dashi, suna isa direct emergency room suka shiga dashi daman kafin su k'araso Daddy yace a shirya komai"
Sosai Daddy da dr Habib suka d'ukufa a kansa har suka samu Numfashi sa ya dawo dai² sunyi mamakin ganin abunda ke damunsa, haka dai suka bashi duk wani kulawa harda karin drip suka masa kafin suka fito dashi, suka mayar dashi wani special room dake asibitin"
Wucewa office dinsa Daddy yay da sallama inda ya same Abba zaune ya buga uban tagumi yana tunanin halin da dan nasa yake ciki"
Dafashi Daddy yay hakan ne ya dawo dashi daga tunanin daya fad'a" murmushi Daddy ya masa yana yana zama kan kujeran" Abba yace " meke damunsa?"
Ba wani Babban masala bane, amma kuma babba"
Kamar ya"
Eh abinci ken da nayi na gane Mahmud irin mutanen nanne masu matsanancin sha'awa, kuma yasan da wanan amma yake buyewa yana shan magunguna"
Numfashi Abba ya sauke yace " toh yanzu kuma sai ya buye mana mugani, murmushi Daddy yay yace "yanzu dai dazaran ya samun lafiya ya fada mana wacce yake so kawai ayi Auren"
Murmushi Abba yay yace " Allah yasa akoi wacce yake so din" da Amen suka amsa tare da mikewa suka fice daga office din"
Suna fita kenan suka hadu dasu kaka suna faman k'araso wa"
Kallonsu kaka tay tace " meke damun dan jikalle nadin?"
Murmushi Daddy yay yace " ba wata matsala sosai bane"
Ajiyar zuciya Yasmeen ta sauke tana hamdala a ranta tace " kome ke damunsa ohoo"
Dakin da aka kwantar dashi suka wuce, kwance yake yana baccin sa cikin kwanceyar hankali"
Zama sukayi kaka tace " ku fad'amin a bunda ke damunsa ko hankalina zai kwanta"
Bayanin komai daddy ya mata, sauke ajiyar zuciya tay tace " oh ni Aisha ace yana sane da wanan masalar shine ya kasa findo mata, ai dole yana tashi ya fad'amin wacce yake so"
Murmushi kawai su Daddy suka" Yasmeen kuwa tabe baki tay tana kare masa kallo"
Mikewa su Daddy sukayi suka fice daga dakin, suna fita Yasmeen ta dauki wayarta ta kirasu Ummi da hankalin su duk a tashe ta fada musu komai, ajiyar zuciya suka sauke tare da mishi addu'a sukace sai sunzu, kashe wayar tay ta bude data abunda taci gaba da chat dinta hankali kwance"
Bai farka ba har karfe 12 ya bude idanunsa a hankali ya sauke su kan Yasmeen dake chat tana murmushi"
Kakus ne ta kallesa tace " harka tashine mijin, waro idanunsa yay yana kallon inda yake, a ransa yace " shikenan abunda nake gudu shi ya faru"
Yasmeen ne ta dago ta kallesa tace " uhmm harka tashi, ta fada tare da mikewa tazo inda yake kwance ta cire masa ruwan dake hannunsa wanda ya kare"
Murmushi yay yace " thanks but waya kawoni nan?" Harara ta wasa mishi tace " ban saniba"
Murmushi kawai yay domin ya tuna itace ta shiga dakin dagan kuma bai san abunda ya faruba"
Kakus tace " sannu ya jikin naka?" Kallonta yay da murmushi a fuskar sa yace " da sauki sosai matar"
Yasmeen kuwa ba tare data kallesa ba tace " ya jikin ko akoi inda yake ma ciwone?"
Da sauke Anty na, ai na samu lafiya tunda ke kika dubani"
Tabe baki tay taci gaba da lasa wayarta"
Su Ummi ne suka shigo d'akin da sallama, amsa musu sallamar sukayi, zama sukayi suka masa sannu da jiki, ya amsa musu cikin jin kunya domin yasan yanzu sun san abunda ke damunsa" basu dade sosai ba suka musu sallama suka fita, Yasmeen tace "bari ta rakasu ta dawo"
Suna fita kakus ta kallesa tace " Mahmud inason ka fadamin wacce yarinya ce kake so sakani da Allah domin mahaifanka sunce Aure zasu maka, don haka inason ka fadamin ni kuma sai na sanar dasu?"
Kallonta yay a ransa yace " tabbas yanzu lkcn daya dace ya fadi abunda ke raina"
Murmushi yyi yace " Y.....


Happy Friday 🕌📿

Share fisabilliah Habibaty 🥰
[2/1, 14:39] ~Ms Fatima: 💅 *K'ANINA NE* 💅

*Story and written*

*By Fatima Mrs Ahfat*

*ELEGANT ONLINE WRITER'S 📚*

*Bismillahir rahmanin Rahim*

Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*

*I selling MTN data with this cheap price*

*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===150
1GB@=====270
2GB@=====550
3GB@====800
5GB@====1,350

Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance.
*Validity 1 month*

*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR
Call 08066268951*


*Page 11*

________ Kodai² ke kikace kina SONA" cikin b'acin rai ta mike tace " baka da hankaline zance ina sonka kana masayin K'ANINA"
Tabe baki yyi yace " waye sani abu a duhu"
B'akin ciki kamar ta shakeshi haka takeji"
sun dad'e suna tsaye k'owa da abunda ke ransa, can dai ta sauke ajiyar zuciya a hankali tace " please Mahmud zauna muyi mgn ta fahimta, don musan yanda zamu bollowa alamarin"
Shima Numfashi ya sauke yace " gara kam"
Zama sukayi suka fuskanci juna, Yasmeen tace " me kake ganin zamuyi yanzu?"
Baki ya tabe yace " nidai kaina ya d'aure ki kawo shawara"
Nisawa tay tace " okay yanzu dai abunda zamuyi shine kaje ka samu Daddy ka fad'a masa cewa mufa bamuson junan mu, kuma kai ma kana da wacce ta wuff da zuciyar ka, sai ka masa bayanin yanda zai gane, k'aga ai shikenan zai hakura kai ka Aure wacce kakeso nima na Aure wanda nakeso"
Tunda ta fara mgn ya zuba mata idanu yana kallonta a ransa yace " umm Lallah yarinya dani zaki mutu ko kinaso ko bakiso"
A fili kuma yace " Umm hakane amma gaskiya batun mgn da Daddy bata taso ba" sai dai ki samo wata mafitar, domin gaskiya ni bazan iya bijirewa mgnr da iyayena suka yanke akai naba"
" gara na bawa zuciyata hakuri da kuma masoyiya ta, Allah sarki masoyiya zataji ba dad'i kam k'amar yanda nima nakejin ba dad'i ji nake kamar nata zun duma ihu"

Tsororo Yasmeen tayi tana kallonsa, wani hawayen ne me zafin gaske ya zubu mata a kuncin ta, zuciyar ta na mata zafi sosai, k'asa mgn tay sai ido da take binsa dashi"
Mahmud kuwa ganin tana hawaye ne ya sashi shima fara shekshekan kukan karya ya fara yace " wlh bake ya dace kiyi kuka ba sai ni wlh, zuciyata zafi takemin domin rabuwar da zanyi da bugun zuciyata"
Allah sarki masoyiya ta bugun zuciyata, kiyi hakuriii! Na miki laifi wlh dole na naje nayi ta lallashinta har ta hakuraaa!!"
K'asa cewa komai tay domin taga alamu Mahmud dinan iskaci ke damunsa, mikewa k'awai tay da gudu ta haura bedroom dinta"
Yana ganin ta shiga bedroom din ya fashe da dariya yace " yes² kakus dolu na miki Babban k'yauta wlh, mikewa yyi ya fara takawa da rawa sanda ya gaji"

"da dan gudunshi yana murmushi ya wuce part dinsa ya dauki key din Motar sa direct parking space ya wuce ya shiga Motar sa ya kunna music tare da janta ya fita d'aga gidan cikin anna shuwa"

"Yasmeen kuwa tana shiga ta fad'a kan bed dinta ta fashe da wani irin kuka me tsuma zuciyar wanda ya saurara, Sosai take kuka k'amar ranta zai fita"
Wayarta ne ya fara ringing dubawa tay taga Khadija ne ke kiranta, Khadija Babban kawar Yasmeen ce tun suna yara, Khadija nada hankali sosai , ga ilimin Boko dana islamiya, ga rikon Amana, hakan yasa suke mugun shiri da Yasmeen duk wani shawaran su sukan yishi ne tare"
Dagawa tay tare da fashewa da kuka"
Subhanallah! Yasmeen me ya sameki kike irin kukan?"
Batace komai ba saima sautin kukan ta d'ata kara"
Please Yasmeen ki daina irin kukan nan ki fad'amin meke damunki wlh duk hankali yyi bala'in tashi, don Allah kiyi hakuri kisawa zuciyar ki nisuwa please dear"
Dan tsakai ta kukan nata tay ta b'ata labarin komai, ta kare da cewa " wlh sai ma rainin hankalin da yake son ya min"
Ohho Yasmeen ki kwantar da hankalinki ki tsami nasuwa kibi komai a hankali, nidai a shawaran dazan baki kiyi hakuri ki danne zuciyarki kiwa iyayenki biyayya k'amar yanda shima ya hakura"
Haba Khadija abunda zakice kenan ki dubafa ki gani K'ANINA NE tay zan Aure shi har muyi tarenyar Aure dashi haba kema kinsan abun baiyi ba wlh"
No Yasmeen me zai hanasa yuwa please kiyi hakuri insha Allah next week zan dawo, ina dawowa zamusan abunyi kinji yanzu dai ki daina kukan nan haka, ai idan kinayi ma sai ya kara raina ki" ta Fad'i hakanne don ta samu nitsuwa a ranta"
Sosai tay ta lallamin ta harta hakura ta daina kukan, janta tay da hira harta tsake jikinta, kafin sukayi sallama"

Bangaren Mahmud kuwa Babban super market ya shiga yama kakus shopping na musan man, aka zuba mishi a booth ya dawo gida, yana dawowa direct part din kakus ya wuce da shopping din, da sallama ya shigo, kaka dake zaune saman kujera ne ta amsa m fuskar ta dauke da murmushi, ajiye k'ayan yyi a gabanta yana murmushi"
kallonsa tay tace " Mahmud wanan uban k'ayan fa?" Murmushi yyi yace " duka nakine Matar"
Zaro ido tay tace " to fa wanan duka nawa?" Ai kin can canci fiye da hakan ma Matar"
washe baki kaka tay tace " kai ² na gode sosai Allah ya kara budi"
Da Amen ya amsa yace " gaskiya ina mai Kara mika godiya ta a gareki kaka, yau ina cikin farin ciki mara misaltuwa Matar"
Murmushi kaka tay tace " Mahmud Yasmeen Amana ce na baka a hannunka, karka yanda ka bani kunya"
Insha Allah kakus bazan taba baki kunya ba, duk yanda zanyi ² don na shawo kanta ta soni k'amar yanda nake sonta"
Da fatan kema zaki taimakamin ko Matata rabin raina"
Dariya kakus tay tace " insha Allah yanzu dai dauki k'ayan nan ka shigar min dashi cikin bedroom dina kar wani munafin yazo ya gani balle a fara bincike akai"
Yana murmushi ya dauki kayan ya shigar mata dashi ciki ya dawo sukaci gaba da hiransu"

Sun dad'e suna hira, Yasmeen ne ta shigo parlor da sallama, kallon juna sukayi da kaka ta mishi tsiginal, yyi murmushi iya lips dinsa"
Kallon Yasmeen kakus tay tace " Yasmeen yana ganki haka jikinki duk a sanyaye k'amar wanda kwai ya fashe mata a ciki, ko dai baki da Lafiya ne kawal lina?"
Had'a ido sukayi da Mahmud ta zabga mishi harara ta k'araso ta zauna kusa da kaka a hankali tace " wlh kakus ki fad'uwa wanan jikan naki me kama da inya murai y......!

Share fisabilliah Habibaty 🥰
[2/2, 16:53] ~Ms Fatima: 💅 *K'ANINA NE* 💅

*Story and written*

*By Fatima Mrs Ahfat*

*ELEGANT ONLINE WRITER'S 📚*

*Bismillahir rahmanin Rahim*

Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*

*I selling MTN data with this cheap price*

*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===150
1GB@=====270
2GB@=====550
3GB@====800
5GB@====1,350

Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance.
*Validity 1 month*

*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR
Call 08066268951*



*Page 12*

______________Ya fita d'aga idona na rufe, yanzu ace kakus kina nan su Daddy zasu had'ani Aure da wanan  inyamurin, bayan yana da wacce yakeso, nace masa yaje ya fad'uwa Daddy akoi wacce yakeso , shine ya zauna yana fad'amin maganar banza"
Kema ai  shedace kakus bason junan mu mukeba, alhalima ni bazan taba son K'ANINA ba, please kima Daddy bayanin yanda zai gane" ta kare maganar tana kwantar ta k'anta saman cinyar kaka"
Shafu k'anta kaka tay tace " haba jikalleta kiyi hakuri kibi zabin iyayenki mana insha Allah wata ran zakiyi alfari da haka kinji ko" batace komai sai hawayen da take kokarin dannewa karsu zubo take"
Mahmud tabe baki yyi tare da mikiwa tsaye yace " Matar nidai na wuce ki huta lafiya keda shugub'e beyar jikarki" yana fadar haka ya fice d'aga parlor"
Sosai kakus ta bawa Yasmeen hakuri da kwantar mata da hankali da nasiha har bacci ya dauke a wajen, Numfashi kaka taja tace " Allah dai ya hada kanku"

Haka dai rayuwa taci gaba da tafiya duk inda Yasmeen taso a fasa Auren nan ta gagara, gashi Khadija ma bata dawo ba, inda tasha kuka harta gaji tun su Anty Amarya na lallashin ta har suka kyaleta sai idon da suke binta dashi, duk wani gyaran jikin da akewa Amare sai da Anty Amarya ta mata da dole" ana gobe daurin Aure ne aka kawo lefinta, domin Mahmud da k'ansa yaje Dubai ya had'a mata lefen son ransa, k'owa yyi mamaki ganin yawar k'ayan da kudin da aka barna tar akai"
Zaune take ta zabga uban ta gume, bud'e kofar da akayi ne ya sata dago da idanunta ta sauke su k'an Khadija dake kallonta, harara ta wasa mata ta kauda k'anta gefe"
Murmushi Khadija tay ta k'araso bakin bed din tace " am so sorry my dear" ta fad'a tana zama gefin bed din" kallon Yasmeen tay dake ta cin mgni tace " kinga lefen da Mahmud ya miki kuwa kai sai dai muce masha Allah, ni dai a ganina Mahmud na sonki sosai, dago da idanunta tay tana meson karin bayani, murmushi Khadija tay tace"Yes Mahmud sonki yake wlh domin idan ba sonki yake ba bazai yi barnar kudinsa akan kiba ehee, yarinya gara ma ki kwantar da hankalinki kusha soyyanku ehee,
Tabe baki tay tace" d'ani? Toh Allah ya kiyayeni' shiya ya fad'a miki SONA yake da wani zaki zo ki dameni da mgnr sa"
Murmushi tay tace" okay abar mgnr kawai yanzu me muke ciki kinga gobe ne daurin Auren" idanunta ta rintse sai hawaye sharrr! Subhanallah! Meyen kuma?" Idanunta ta bude tace " wlh na tsani naji an furta min ace gobe ne Aure na da K'ANINA"
Goshinta Khadija ta dafe tace " wai baki yanda da kaddara bane Yasmeen? Yaka mata ace ki rungumi kaddaran ki aduk yanda yazo miki kiyi hakuri wata rana fa sai labari"
Ummm! Khadija kenan na yanda da kaddara man, but da kinji yanda zuciya ta kemin ne bazan iya daure waba"
Hmmm hakura k'awai zakiyi ki tashi mu sauka parlor domin sauran kawayen suna zaune a parlor" kwaciya tay tace " nidai ba inda zanje" dariya sosai Khadija tay domin taga alama shugub'a ba na damun Yasmeen, da k'yar ta lallaba ta suka fito parlor"

Bangaren Ango Mahmud kuwa sosai yake cikin farin ciki da abokanan sa, sai washe baki k'awai yake, duk da yace " shifa ba Taron da zaiyi mai da Amaryasa bare su kalle masa mata ko rakiyan ma shi ya yafe musu, dariya suka masa sukace rakiyan nan dai sai sunyi, yace " tab sai kun ganni ne ai zaku rakani" dariya sosai suka masa wai shi gashi mai kishi, sosai sukayi bidirin su su kad'ai" da daddare su Abba suka had'asu a part din kaka suka musu wa'azi mai shiga jiki, kafin suka musu fatan zaman lafiya da zuria dai yiban, Yasmeen dai ba abunda take sai shenshekan kuka"

Washe gari Saturday aka d'aura Auren Mahmud da Amaryar sa Yasmeen, Auren d'aya tare dunban jama'a Yan uwa da abokan arziki sai congratulations suke masa da fatan zama lafiya, hmmm washe baki gun Mahmud Ba'a mgn, shi kad'ai sai smile yake"
Bangaren Yasmeen kuwa tunda taji an d'aura Auren duk jikinta ya mutu sai kuka take, Ummi ne ta shigo dakin ta mata Nasihar daya kara sa jikinta mutuwa sosai sai hawayen da take, har lokacin da Khadija ta shigo ta sameta"

*Cigaban labari*

Murmushi yyi ya dauki drink din zuba a cup ya farasha hankali kwance yana lasar wayar sa har aka fara kiran la'asar kafin ya wuce bedroom dinsa ya watsa ruwa ya d'auro

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment