Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

& bena*


*Queenmeemi.WordPress.com*


Bayan komai ya lafa hankalin haidar ya kwanta shida zee zamansu mai cikeda k'auna da amana duk da hausawa nacewa harshe da hak'ori ma na samun sab'ani hak'uri shine jigon komi a rayuwa,zee na tsaye tana sawa haidar mab'allin rigar sa ta fesa mai turare k'ok'arin tafiya office yake Amma saboda shagwab'ar data ke zubamai ya kasa tafiya Bayan sun gama komi ya fito zai tafi suna sak'ale da juna dining table sukaje don karyawa haka sukai ta ciyar da junansu cike da shauk'i da k'aunar juna har bakin mota ta rakashi rik'e da briefcase din sa, ta juya zata tafi ya janyota ta fad'a jikinsa kallon tsakiyar idon ta yayi yace "am proud of you wallahi" nan ya bata peck a kumatu murmushi tayi mai "iluv u my haidar" Jan motar yayi ya d'aga Mata hannu da gudu ta shiga gida tana mai godewa Allah daya bata miji d'aya tamkar da dubu.



hajar kuwa rayuwa ta juya Mata Baya domin ta kuma komawa gidan boka mai kan-kan kan yayi Mata asiri don ta koma gidan haidar,suna zaune boka ya tashi don dauko masu magani sai gashi wuta ta tashi a dakin da gudu ya fito ganga -ganga wuta keci nan Mata kowa ya kama gabansa boka sai sumbatu yake yana ihi kamar ya haukace kafa mai naci ban baki ba su kubra da hajar da sauran Mata ke gudu yana binsu,su hajar yake bi yana hajar ta tsaya har bakin titi suka je garin tsallakawa d'ayan side d'in mota ta kad'e hajar da kubra nan hajar ta karye a k'afa haka ita kuma kubra ta karye k'afa da hannu mai kan-kan. kuwa wata mota tayi ciki dashi ko shurawa baiyi ba yace ga garinku nan dama k'arshen mushirki ke nan .haka aka kawo hajar da kwatance gidan su ranga-ranta nan umma tai shiga dawainiya da ita wajen wata daya har ta samu ta warke ,haka umma take gidan kubra tai Mata kaca-kaca kan karta Kara zuwa gun hajar ,kubra kam ta kanta take domin ita bata da gatan hajar har yanzu tana kwance zaman jinya.



Bayan warkewar hajar umma kam Sabon babi ta bud'e domin ta sakawa hajar ta kunkumi domin duk aikin gidan su wanki shara girki ita keyi duk ta rame ta fita hayyacinta, bata da tsugun ga k'uraje da suka fito Mata duk jiki ba gaira ba dalili Amma tana Shan magani sun fara warkewa zaman gidan ya isheta domin in tayi laifi duka takeci gun babanta domin yace tunda ta kaso aurenta to dole ta fuskanci matsi gashi ko cimar gidan ta isheta nan ta tuno gidan ta komai waja-waja dana sani ne fall aranta, yau ma data ci uban wankin k'annen ta ta gaji lub'us tazo gaban umma tace "umma ki taimakan na koma d'akina wallahi na saduda shed'an ne ya zuga ni nayiwa su Mami rashin mutunci Amma na saduda" harara umma ta wurga Mata "sai yanzu kika gane? ai kinyi rashi sai dai ki hak'uri haidar yayi miki nisa domin kinyi wasa da damarki dama ai na gaya miki ke ai kina ma da gata" kuka ta saka umma ta kai Mata hauri da gudu ta tashi ta tafi tana kuka.



yau haidar ya kawo wa zee sabuwar mota Benz k'aramar ta mai k'ofa d'aya sai shek'i take ihun murna zee take ta rungume haidar Allah Yaso ta iya driving godia take ta zubawa da yamma suka tafi gidan Mami nan ta nuna Mata haka Mami tayi farinciki ta kalli haidar "Amma ka birgeni kyautatawa mai kyatata ma" nan ta janyo zee ta rungume "yata Nima insha Allah Bana zaki hajji keda husy tukwicina kenan" kukan hawaye ke zuba a idonta rungume ta tayi tana godia haka suka tafi gida aranar soyayyar suka gurza abar su son ransu dama Burin zuciya ta samu muradinta.


Washegari zee taje gida tayi kyau tai b'ul-b'ul tasa wata super mai kyau ta d'ana dogon takalmi sai drivin take hankalinta kwance mum da dad sunji Dad'i ganin motar da zee ke ja sunyi wa haidar godia mum kam ganin yanda zee ta ta samu farinciki ya sata farinciki suna d'aki a zaune mum tace "zee kinga ribar hak'uri ko aishi Baya fad'uwa k'asa banza Allah ya dai Baku zama lafiya" sai k'arfe biyar na yamma ta tafi gida.

*Bayan kwana 2*

dayake yau weekend haidar da zee sunje gida gun Mami anata hira da jin Dad'i hajar ce ta shiga da sallama duk ta rame tayi baki ga tabon k'uraje duk ajikinta nan tasa kuka "Mami ki yafemin haidar kaima ka yafe haka kema zee wallahi sharrin she'd'an ne da rud'in k'awaye nasan nayi butulci ku yafe mun"ganin yanda ta koma ya basu tausayi yasa suka ce sun yafe ,gyara zama tayi "ya haidar ka taimakeni ka maidani d'akina" ,nan ya kalleta Kiyi hak'uri idan kin samu miji kiyi aure nai miki alk'awanni kayan d'aki 'yan waja ko ba komi ke k'anwata ce, kin ganni nan zeenatu ta ishen"
Da k'yar ta tafi cike da dana sani dama ita rayuwa yanda ka d'auketa haka zata zo maka


bikin kb da Anee ya taso su zee da haidar sai shirye- shirye ake haka satin bikin ya kama aka gudanar zee ta zamo babbar k'awa shima haidar babban abokin ango, anyi biki lafiya aka kai Amarya gidan ta sai kuma bikin munay da za ai nan gaba saura 2 month.
Bayan wata d'aya suka fara shirin tafiya hajji itada husy sunje lafiya sundawo lafiya basu dad'e da dawowa ba akayi engaged din husy sai jiran biki kawai.

wata biyu atsakani zee ta fara laulayi na samun cikinta sunje asibiti an gwada tana da Shi wata d'aya dai-dai nan Sabon tattali ya tashi gun haidar aikin kirki r Baya barin zee tayi haka school shike kaita ya d'auko ta yace tabar driving har sai cikinta yayi k'wari.

An yi bikin munay da angonta musbahu nan ma zee da Anee sunyi rawar gani duk da zee na fama da laulayi anyi an gama lafiya ankai Amarya d'akinta sai fatan zama lafiya zee munay da Anee sun zamo yan uku sun rik'e kansu bisa amana da kaunar juna haka yanzu bussness suke su ukun ga mazajen su ma kansu a had'e don munay ma ta shigar da musbahu gun kb da haidar.




*Story writte &editted*
*by Queen meemi*
[4:48pm, 23/11/2016] Queen💋Meemi: *ZEENATU by Queen meemi page 96-97*
â™ . â™ . â™ 
â™ . â™ . â™ 


*NWA*



*Dedicated to Lubie &bena*

*Queenmeemi.WordPress.com*

*END OF THE STORY*



Haidar dake driving defense ga zee ta d'au ado da kwalliya zasuje gidan kb ga babyboy a hannun ta kyakykyawa dashi d'an wata uku ga aysha yar hajar yar shekara 2 abayan mota taci ado domin ba adad'e da maidota ba tun Bayan bikin husy da angonta Ibrahim inda aka kaita kano, to Bayan bikin ne aka dawo da aysher parking sukai a harabar k'ofar gidan kb nan haidar ya fito ya bud'ewa zee gaban mota ta fito, munay ce ta fito tana hararar zee da dariya tace "saraakan soyayya tund'azu munata jiranku" zee tace ke "barni kinsan in ban gyare husby na ba Bana samun nutsuwa" munay tace "ashe kina gane karatun" dariya suka sa munay ta karb'i Arif tana mai wasa nan suka shiga gidan Anee ta tare su da cikinta da ya fito dama lunch suka had'a agidan Anee haka suke duk wata sai aje gidan d'aya ai lunch ko dinner kb ya kalli haidar yace shegen sama kana sha'aninka na zeenatu bada kanka adade" haidar yace "to ya za ai tinda madam ta shagwab'ani"



hajar kuwa da k'yar ta samu wani a Bayan layin su mai saida kayan miya matan sa biyu domin duk unguwar gunsa ake sayan kayan miya da farko ta raina Shi kancewa ba ajinta bane sai da dad yayi Mata fata-fata san nan ta yarda aka d'aura auren aka kaita gidan nasa itace ta uku agidan ba yanda za tai dole ta zauna domin girkin 'ya'yan gidan wajen su goma ita keyi,ga jarabar kishiyoyi sun isheta dana sani ba irin wanda batai ba Ni meemi nace wanda baiji bari ba ai yaji hoho.

*Bayan shekara* d'aya zee na driving amotarta Baya ga mai aikinta dasu aysha da Arif parking tayi a gaban wani supermarket nan ta shiga kana kallonta kasan Hutu ya zauna a jikin ta ta gama gama soyayya akayi counting ta fito taga wata Mata na kuka a gaban mota har ta wuce ta tsaya,tai Mata sallama matar ta amsa zee tace "duk da baki gayan matsalarki ba, nasan ciwon 'ya mace na 'ya mace ne kiyi hak'uri domin Shi hak'uri babban jigo ne arayuwa" ,matar ta d'ago ta kalli zee gata agirme matar ta girme Mata nan tace " bakomi wallahi matsalar uwarmijina ce da k'annen mijina ya damun yanzu ma sune sukai min waya suka gayan ba Dad'i" zee tayi murmushi hak'urin dai shine san nan kiyi ta addu'a ki zauna dasu tsakani da Allah ki kyautata musu wallahi da sannu sai kin musu zarra duk rashin sonki da basayi wataran zasu soki" matar tace "bakomi nagode insha Allah na dau shawarar ki" nan tai Mata sallama ta shiga motar ta taja.


haka rayuwar zee da haidar ta kasance cikin so da k'auna awajen haidar kuwa zee ta zamo tauraruwa,domin mace ta gari itace jin dad'in rayuwa.bissalam *ZEETAHAIDAR*


tammat bihamdillah Anan na kawo k'arshen littfain zeenatu abinda nayi ba adaidaiba Allah ka yafemun Amin.

wasallallahu Ala nabiyur rahmati wa ahlihi wasahbihi ajma'in.

Ina mika godia ga d'aukacin yan NAGARTA WRITERS ASSOCIASION Allah yabarmu tare Amin.

gaisuwa ga my frnds:

Autar hajia
Lubie maitafsir
benazir
futha
my miemiebee
umma adnan
Anee
Anush
mamu
ummul fadeela
feenat ja afar
hawwa damary
chuchungaye
ummu samha
sadyjegal
feedoh
jabo
Ashnur pyar
Zahra bb
maman shakur

da sauran wadanda ban fad'oba duk kuna raina

'yan group dina na meemi novel ina mik'o gaisuwa ga duk wanda ke ciki,da kuma 'yan kasaitatun Mata kuna birgeni Allah ya bar k'auna.

haka kuma 'yan excellent writers ban manta kuba.

da sauran groups wanda innace zan fad'o su sai gun ya cika Allah ya bar kauna luv you Lodi Lodi

godia gareku kun nuna k'auna ga zeenatu kamar su
maryam oumeey
aysha nuhu
maryam kabeer
Maryam Ahmed
aysha
husna
danima rayyn
halima sadiya
fiddy

da dai sauran wadan da ban anbato ba duk kuna raina godia Allah yabar zutunci.
da duk wani mai kaunar littafina Nima ina k'aunar sa

Ban mantakuba mutan group na kaleesat haidar Godia Agareku da kulawa luv much.



*takaitaccen tsokaci akan littafin ZEENATU*

*jigonsa hak'uri kunga yanda rayuwar zeenatu ta fara da rashin hak'uri da yanda daga Baya aure yasa ta koyi hak'uri da sanin rayuwa*
*san nan kuma jajircewa gun iyaye kan taribya kunga yanda mum ta jajirce,har zee ta koyi hkr a rayuwa san nan dogaro dakai*

*san nan kunga yanda Mami ta takurawa zee Amma duk da hakan tayi hkr ta jajirce Amma saida k'addara ta afka suka rabu dama rayuwa bata tab'a zuwar wa mutum daidai,kowane k'alubale yana tattare da k'addara*
*aganinta hajar ce ta dace da haidar sai gashi tasa Mami tayi danasani sosai kunga Anan ya nuna matsalane iyaye suna sa yayan su adamuwa su takura musu kan abinda basa so akarshe kuma sune da damuwa*.

*kunga yanda haidar yayi wa Mami biyayya ya shiga damuwa adalilin hakan Amma daga Baya sai gashi hakurin sa da biyayyar sa yasa yaci riba kunga yanda duk budurin da aka sha gashi dai zee ta zamo tauraruwa a gidan mijinta yayinda Mami tazo tana kaunar ta ainun dama hausawa nacewa naka sai naka dad'in zama sai bare wan nan shine*

*Zuwa gidan boka kuwa babbar illah ne gun Mata sab'awa Allah ne ,kunga yanda adalilin hakan hajar tayi dana sani*
*ta had'u da k'awa mai son kanta, ta kuma kaita ta baro Allah ya kiyashemu tabewa*
*Da fatan fad'akarwar dake cikin littafin zata amfane mu nagode*
*sai kun sake jina wataran a sabon book dina mai suna...........luv u oll*




*Story writte &editted*
*by Queen meemi*

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment