Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sama miki wallahi tab" hajar tayi Dariya tare da zama kusa da kubra "Allah k'awas Amma naji dad'in had'uwa dake" nan dai sukai ta hirar su ,haidar ne yayi sallama ya shigo falon harara hajar ta wurga mai sai kubra ce amsa sallamar tab'ota kubra tayi "lalle dole mijinki yaja aji handsome" haka dai kubra ta k'araci sumbatun ta, data tashi Tafiya hajar tai Mata alk'awarin zata je.. . . ********** kuka take ta sharb'a d'ankwali a hannu fiskar nan duk tai face-face duk ta b'ata kwalliyar da tai numfashi taja "me yasa zakai mini haka? ka rasa abinda zakai min sai kishiya bayan kasan ni kad'ai ce taka, me na rage ka dashi? don tsabar cin amana" kallonta yayi ya sunkwi dakai ya kurb'i tea "Haba maryam kanki farau ne? ni nace ba don kin mini komi zan K'ara aure ba kawai don sunnce", "to ni ban isheka ba, haka kawai ina zaman zamana kazo kace zakai mun kishiya to wallahi sai dai koni ko ita don wallahi Bazan zauna da kishiya ba" "maryam Ina lallab'aki kina kutsewa karfa ki manta ni mijin mace hud'u ne, badon wai bana sonki bane", d'aukan waleed tayi suka Shiga d'aki tana kuka dafe kunci ma'aruf yayi nayi niya kuma sai nayi na samu yarinya sakin wawa zan yi sake tab haka ya tashi ya fice .... . *Story writing & editing* *Queenmeemi* .
.




. *ZEENATUby Queen meemi page69-70* . .. .  . .  . . . *®NWA* . *Queenmeemi.WordPress.com* . . *Bayan kwana 2* . haidar na office wayar sa tayi k'ara d'agawa yayi "Aa kb yade"? daga can kb yace "pls idan ka taso daga office ka biyo ta gidan mu akwai labari", haidar yace "ok ba damuwa zan biyo" bayan kamar 1 hour haidar ya parking motar sa k'ofar gidan su kb 5:30 dai-dai d'akin ya Shiga kb yace "mijin hajara ya kwana 2" tsaki haidar yayi "kana son b'atamin rai, pls tell me kawai" kb ya matse gemu "zee aure zatai" da sauri haidar ya tashi ya kalle Shi "da gaske!? Pls in wasa kake ka daina",kb yayi tsaki "to sai akace don kai kad'ai aka halicce ta,tsaya ma kaji ma'aruf zata aura fa", "wane ma'aruf kake nufi ne"? kb yace "ma'aruf dai yayan muzzam abokin mu haidar ya daki bench d'in dake kusa dashi "oh my god! kai- kai da sake Bazan bari wani ya auri beauty ba" ,kb yace "tun yaushe kuma Ina gaya maka ansa rana kasan Aneesa budurwata to k'awar zeey ce ita Ke gayan" dafe kai yayi "kb meye shawara",kb yace "kawai ka hak'ura ka rik'e hajar d'inka", haushi ne ya kama haidar kawai ya shuri wayoyinsa ya fad'a mota ko sallama baiwa kb ba. . . aguje haidar ya aje motar sa ,part d'in mami kawai yayi suna zaune suna hira ita da husy,zama yayi kan kujera ya kalli mami yace "mami dama kince zaki gidan su zeey" mami tace "munje ai Amma aure ma zatayi damm! Yaji k'irjinsa ya bada "mami don Allah duk yanda za ki karki bari zee ta auri wani batare da ta dawo mini", idanuwan sa ne sukai jajawur mami tace "sai hak'uri" ganin yanda ya birkice lokaci d'aya yasa mami tace "Amma zan dad'a gwada sa 'ata Allah yasa adace" husy tace Amin, jiki a sanyaye ya tashi ya fice side d'insa muk'ulli ya gani a jikin k'ofa alamar hajar bata nan, dafe kai yayi ya zauna gun yana Maida numfashi,ganin zai b'atawa kansa lokaci yasa ya tashi ya koma part din mami ya bud'e tsohon d'akinsa ya baje kan gado tunano ranar daya fara ganin zee yayi da irin rayuwar da sukai har suka rabu,bai San sanda bacci ya kwasheshi ba. . . ******* _your love is always growing up in my heart zeenatu pls ki dawo Guna karki auri wani plss_ msg d'in daya shigo a wayar zeey kenan suna lecture karantawa tayi ta Maida wayar jaka Sam ganin msg d'in yasa ta daina ma gane karatun, tashi tayi kawai ta fita ,bakin bishiya taje ta zauna ta fad'a duniyar tunani ,wayar ta d'akko ta k'ara karanta msg d'in ,nan ta Maida mai reply kamar haka: _haidar rayuwa bata zuwar wa mutum yanda yake so ka d'au komai a matsayin k'addara kayi hak'uri haidar Ina sonka har abada ,Amma komawa gidanka bazai yiwu ba sabod Na kusa auren wanin ka Bissalam_gaba d'aya tama kashe wayar ta maida jaka ta cigaba da zama wajen. . Haidar kuwa ganin msg ya shigo da hanzari ya duba yana d'aki ko Aiki baije ba saranda yayi ganin abinda tace kawai ya aje wayar a gefe, ya tashi ya fita falo hajar na zaune tanacin gyad'a tana ganin sa tace "Yawwa ya haidar dama kud'i nakeso" ko kallonta bai ba, ya koma d'aki binsa tayi ta jawo shi ta baya ya Juyo tace "dubu ashirin nake buk'ata" mamakin rashin nutsuwar hajar yake yace "Ke ban dasu ko angaya miki hak'osu ake" "wallahi sai ka bani" bincike rigar sa da ya cire wadda ta gani a sakale tayi dubu goma ta gano ajiki ta d'auke tace "na d'auka" ta fice kasa magana yayi shi kawai tunanin zee ya Cika mai k'wak'walwa,ganin zaman bazai fishshe Shi ba yasa ya yi wanka ya d'au key ya fice.... .

Please Login or Register in order to submit comment