Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba sai zare ido da nake zuciya ta na cigaba da bugawa, Inna zata kara min magana muka ji muryan yaron daya rako mutumin nan ya ce,"wai ana neman zareefa".


Wani kallo Inna tabi ni dashi sannan ta dubi yaron ta ce," yana ina?" Yana nan k'ofan gidan nan" yana gama bata amsa ya juya ya tafi abinsa.


"Waye shi kuma me kika masa ya biyo ki har gida?"



"Sh...shine wan...wanda ya biya min kud'in jarrabawa" na bata amsa.


"Shine ya biyo ki har gida,ko dai da wani abu daban?" Shiru nayi na kasa bata amsa sai zare ido da nake saboda ban manta abinda tayi min akan shi ba.



Hijabinta da yake gefenta ta saka ta fita dan taji me yake tafe dashi,a tsakar gida ta tarar da 'yan gidan mu kwan su da kwarkwatan su suna tsatsaye suna k'us-k'us.



Suna ganin ta suka fara yi da karfi wasun su na cewa k'ila sata nayi mishi,wasu kuwa cewa suke asirin mu ne ya tonu k'ila yana cikin mazan da nake bi,tunda dama cewa suke karatun karuwanci nake.



Inna ta bata kula kowa ba ta fito 'yar rub'abb'en zauren gidan mu da niyyan yi mishi iyaka dani domin ta gane fad'an da tayi min kwanaki shi ya firgita ni haka.



Katuwar mota da ta gani ana sauke kayan abinci a ciki kaman za'a bud'e 'yar karamar shago yasa ta tsaya cak tana kallon d'an matashin saurayin da ba zai haura shekaru 21 zuwa 22 ba yana danna wata laftatiyiyar waya a hannun shi.



Inna sai yayi mata kwarjini ta kasa karasa fitan balle tayi mishi magana,shine dai daya gaji da danne-danne shi ya d'ago da kai karaf suka had'a ido da Inna ta,asalin kamanin ta na d'auko shiyasa yana ganinta ya gane ta.


Wayar nashi ya mayar aljihun rigan shaddar shi lafiyayya blue ya karaso gaban ta cikin sauri ya duka har k'asa ya fara gaishe ta,fuska a had'e ta amsa kana ta ce," lafiya kake neman zareefa,ko kuma akwai wani abinda kake nema daga gare ta,dan ta bani labarin duk abinda ta faru tsakanin ku kuma shine yau ka biyo ta har gida"?



Girgiza mata kai ya fara wasu waye na taruwa a idon shi ya ce," ba haka bane Aunty kada ki min mummunan fahimta saboda ni ba nufi na kenan ba,domin duk had'uwa da muke da ita Allah ne yake had'a mu,lokacin da na gan ta a hanyan makaranta na fito zan tafi wajan aiki ne na gan ta tana kuka sai na biyu kuma na tsaya siyan ruwa a gefen hanya ne na ganta ita da wani yaro suna zaune a gefen titi suna kuka,and still yau shima gefen kwata na ganta zaune tana kukan garin ta ya fad'a kwata mutane duk sun zagaye ta ana taje gida ta fad'a amma taki tashi saboda wai Baban ta ba zai bar ta duk taji ciwo amma ko jin zafin bata yi.


Ni suna na Abdulbasit kuma ni maraya ne da tunda na taso ban san kowa nawa ba,banida kowa akan titi nake rayuwata cikin yunwa,kunci da kuma kad'aici sai daga baya na samu wani bawan Allah ya tallafawa rayuwata har kika ganni haka sannan shiyasa na tsani inga karamin yaro yana kuka domin yana tuna min da lokacin kuruciya ta kuma duk yanda zanyi sai na san yanda zanyi in share mishi hawaye sannan hankali na zai kwanta.



Ba ita kad'ai nakewa haka suna dayawa Aunty bana son kowa ya sha wahalan da nasha a baya amma in har hakan ya b'ata miki dan Allah ina neman alfarman ki yafe min".



Inna da jikinta duk ya gama yin sanyi sai ta kasa furta komai saima jin ba dad'i da tayi kan yi mishi mummunan zato.



"Ga wannan kayan abincin a saka su ciki Aunty sannan a bawa Baba hakuri kada ya dake ta tsautsayi ne " taji ya yanke mata tunani.



Tulin kayan abincin ta kalla ido a waje ta girgiza mishi kai,"ta ce a'a ka tafi da kayan ka mun gode Baban ta kuwa zanyi mishi bayani zai fahimta kuma...."


Katse ta yayi cikin sauri ya ce,"haba Aunty ba'a maida hannun kyauta baya,sannan ni ina farincikin na samu ahali da zan iya nunawa a ko ina amma kika ce haka? Sannan hakan na nunawa baki karb'e ni a matsayin d'an uwa ba,ina neman alfarman ki rike ni a wannan a matsayin inji ya ake ji in mutum yana da ahali".


Wannan furucin da yayi saida yasa Inna hawaye,gyad'a mishi kai ta iya yi domin ta tabbata tana bud'e bakin ta kuka ne zai kufce mata saboda tsananin tausayi daya bata, shima cike da farinciki ya mike yana share hawayen idon shi ya ce,"nagode Aunty Allah ya saka da alkhairi zan tafi sai bayan kwana 2 zan rink'a zuwa mu gaisa".



Bai jira cewar Inna ba ya fad'a motan shi sai da yayi ribas sannan ya kira wani yaro ya bashi kud'i masu yawa ya ce ya kaiwa Inna ta,yaja motan shi ya fita a layin namu.



Inna tana tsaye ta rasa ta ina zata fara tab'a kayan sai ga yaron da aka bawa kud'in yazo gaban ta ya mik'a mata kud'in ya ce," wai gashi inji wancan mai motan ya ce in baki"


Wani yawu ta had'iye da kyar hannun ta na rawa ta karb'i kud'in a ranta tana ayyana anya wannan bawan Allah abinda ya fad'a gaskiya ne kuwa? Nan wani sashi na zuciyar ta ya ce mata tunda take bata tab'a cutar da wani ko tabi wani da mugun kulli ba insha Allah in ma da wata manufar yazo Allah ba zai bashi sa'a ba.



Da wannan kwarin guiwan ta samu ta kira wasu matasa da suke zaune gefe tace su taimaka mata su shigar mata da kayan abincin ciki,ba musu suka fara jidan kayan domin suna ganin girman ta sosai.



Su Gwaggo Aisha baki da hanci suka bud'e suna kallon kayan da ake wucewa dashi d'akin mu,bakin ya mutu murus sun rasa abin fad'a,nima ina nan a bayan k'ofa duk na had'a zufa naga a nata shigowa da kayan suna jerawa a gefe har suka gama suka fita ban fito daga mab'uya na ba dan haka basu san da mutum a d'akin ba.



Suna gama shigo da kayan Inna ta basu 500 cikin kud'in hannun ta tace su raba,cikin farinciki suka karb'a tare da yi mata godiya suka koma wajan zaman su,hannayyen ta cikin hijabi ta shigo dan haka babu wanda yaga abinda ke hannun ta.



"Hmmmm kun ga ikon Allah ko 'yan gidan nan gaskiya ta fito fili ga ribar boko nan mun gani yarinya 'yar k'arama an koya mata bin maza har gida ake biyo ta,Allah yayi mana tsari ya kare mana 'ya'ya".cewar Gwaggo Aisha kenan cike da hasada.


Suma sauran kaman jira suke suka fara nasu kowa na fad'an albarkacin bakin shi, Inna ko kallon inda suke ba tayi ba ta shigo d'aki ta cire hijabin jikin ta tare da zama dab'as kan simintin d'akin mu dako leda babu tana kallon kayan zuciyar ta na bugawa,kud'in hannun ta ta shiga kirgawa taga dubu goma ne cif ta ajiye a gefe.



Hango ni tayi a bayan k'ofa ina lek'en ta tace," ba zaki fito bane ko sai nazo na same ki" cikin sauri na fito ina goge gumin jikina,kallon tausayi tabi ni dashi ta san Allah bai bata haihuwa dayawa ba amma alhamdullilahi tana alfahari dani domin jumm'ar da zatayi kyau tun daga laraba ake gane ta.



Na zata zatayi min fad'a ko ta ce wani abu akai amma naji tayi shiru bata ce komai ba sai tagumi data zuba tana yawan ajiyan zuciya,da taga zaman ba zaiyi mata ba ta mik'e ta saka hijabi tare da yi min gargad'in kada in fita koda k'ofar d'aki ne kuma kar in kula kowa duk abinda zasu ce min.



Bata jira amsa ta ba ta fita daga gidan zuwa gidan su wato gidan kakanni na da muke makotaka dasu,da sallama ta shiga.


Kakata Ya Jalo da suke kira da Maa tana soya gyad'a na sayarwa ta amsa tana mata sannu da zuwa,bata gama suyar ba ta sauke gyad'an ta taso sanin cewa in taga kafar Inna ta a gida da dalili ne ya kawo ta duk da kasancewar muna makota basu bata daman zuwa gida any how ba.



"Bintu komai da kike gani na duniya mai wucewa ne sannan kowa yayi hakuri zai ga riba a gaba dan haka bana son kina sawa kan ki damuwa ko kad'an ki cigaba da hakuri wata rana sai labari" cewar kaka ta kenan ganin damuwa karara a fuskan Inna ta,dama haka take mata kullum koda tazo da damuwar ta bata bari ta fad'a sai dai tayi mata nasiha tare da kwantar mata da hankali ta koma gida.



"Nagode Maa Allah ya kara girma amma ba matsalan gida ne ya kawo ni ba akan Zareefa ne...." nan ta kwashe labarin Abdulbasit tun farko har zuwa yau da yazo ya tafi.


Shiru kaka tayi tana tunani kaman na second 20 can ta d'ago ta ce," a yanda na fahimci maganan nan yaron nan bashi da aibu da gasken sa taimakon yake yi in da bashi da gaskiya a yanda kika ce yana da kud'i nan ba zai tsaya yi miki wannan dogon bayanin ba balle ya gaya miki asalin sa,in kuma da yana da niyyan cutar da ita da tuni ya cutar da ita dan haka ki kwantar da hankalin ki Allah ne ya dubi zuciyar ki ya kawo wanda zai taimake ku ke da 'yar ki cikin ruwan sanyi".



Cike da gamsuwa maganan mahaifiyarta ta ciro kud'in ta bawa Maa dubu uku a ciki amma taki karb'a ta ce," ki bar shi ki had'a dana wajan naki ki saka Zareefa makarantan gaba kaman yanda kika ce".


"Maa akwai saura ai zasu isa ki karb'i wannan d'in ki saka albarka" cewar Inna kenan.


Dubu 1 kawai ta zara a ciki ta mayar mata da sauran tare da cewa," Allah ya sanya albarka".


Sun d'an tab'a hira kad'an sannan tayi mata sallama zuciyar ta fari kal ta dawo gida.


D'ari biyar ta cire ta bani a cikin kud'in tace inje in sayo naman miya harda kayan miya,cike da murna na fita a guje yau za'a dafa shinkafa a gidan mu kuma harda nama abinda ada sai sallah yake faruwa.



Ina dawowa Inna ta fito ta hura wuta ta fara girki nan da nan ko k'amshin miyan ta ya cika gidan, Inna Asabe ce ta fara mita," oh in da ranka zaka sha kallo yanzu fisabillilahi wannan abinci da aka samu ta haramtaccen hanya shi za'a girkawa 'ya'yan mu su shi?" Ta karasa maganan tana kallon gwaggo Aisha ko zata ce wani abu.



"Hmmm ni yara na ba zasu ci ba dama kowa ya san ni ba irin ku bace ina da abinda zasu ci nan wata ko 3 ne koda ace bana sana'a dan haka ku kuka sani" Gwaggo Aisha ta fad'i haka tana yiwa karamar 'yar ta da muke sa'anni da juna kitso wato Jameela.


"Ke kuwa daga magana sai ki wani dawo kaina kina wani cika baki,meye naki bamu sani ba wallahi mun san inda Hajara take zuwa tallah da abinda yake tafiya wallahi duk mun sani, a toh kada a cika mana baki kuma ba'a karya kusa da gida" Inna Asabe take mayarwa Gwaggo Aisha magana cikin fushi dan taji haushin maganan da ta yab'a mata.



Nan fa fad'a ya kaure ba abinda kake ji sai ifacce-ifaccen su suna zagin juna tare da tonon asiri kala-kala, sai Maman Dije ce da ta gaji da hayaniyar tasu tazo ta shiga tsakanin su sukayi shiru.



Inna ta dai tana gefe tana aikin ta ko inda suke bata kalla balle tayi gigin raba su domin ta sha gwadawa a baya sai fad'an ya dawo kan ta data fahimce su sai ta kama kanta ta koma gefe ta zama 'yar kallo.



Ana kiran sallah magariba Inna ta gama girkin ta duk da taji sun ce ba zasu ci ba amma haka ta nemo kwanukan kowa ta zuzzuba musu ta bani na kaiwa ko wacce d'akin ta suka bini da zagi da tsinuwa kuma wai inzo in d'auke tsiyar mu amma nayi musu kunnen uwar shegu domin Inna taja kunne na kan ina ajiye musu in juya in basa ci su bawa almajirai amma ni kar in d'auko.



Sai bayan sallah isha'i Baban mu ya shigo dama ko girkin Inna tane baya shigowa d'akin mu bare yaci abincin mu dan haka Inna tana jin muryan shi tace in d'auki abincin shi in kai mishi.


"Na'am" na cewa Inna ba tare da na shirya ba jin tace wai in kaiwa Baba abinci,sai naji abin wani banbara kwai.


"Ki kaiwa babanku abincin shi nace" ta kara maimaita min,amsawa nayi na d'auki tiren abincin da Inna ta d'aura kwanon tuwo daban miya ma daba sai kofin silver mai murfi da ta zuba ruwan randa mai sanyi.


A tsorace na nufi d'akin nashi ina jan k'afa dan na san karamin aikin shine ya koro ni da abincin,ba yanda na iya haka na karasa bakin k'ofan d'akin cikin rawan murya nayi sallama,da yake tsanan da yake min bana wasa bane nan da nan ya gane murya ta cikin tsawa ya ce," uwar me kike nema a nan?"


"Inna tace ta ce in kawo abinci" na bashi amsa cike da fargaba.


"Ita Bintu dan yau ta haukace shine zata aiko ki kawo min jagwalgwalo,kafin in kirga uku ki bar nan ko kuma in na tashi wallahi...." Ai ban bari ya karasa ba na jiyo cikin sauri Allah ya taimake ni babu kowa a tsakar gidan dan haka babu wanda ya ganni na shige d'akin mu.



Inna murmushi tayi ganin na dawo da abincin ta ce," koro ki yayi ko?" Gyad'a mata kai kawai nayi bata kara cewa komai ba ta sauke min tiren akaina ta zuba mana namu muka fara ci abin mu.


Saida naji ciki na barazan fashewa sannan na hakura da tura shinkafa da jan miyan da nake na kwashe kwanukan na fitar sai ga sauran yaran ma suna fitowa da nasu kwanukan suna ta tsid'e hannu su da iyayen su suka ce ba zasu ci ba.


Ina dariya na koma d'aki nake bawa Inna ta labari ta kwab'e ni kan bata son surutu in nemi waje in kwanta,ba musu kuwa na kwanta kan shimfid'a ta cikin abinda bai kai minti biyar ba bacci yayi gaba dani.



Da washe gari da sassafe Innata da ta tashi hura wuta tayi ta d'aura abin karyawa duka gidan abinda tun tasowa ta ban tab'a ganin anayi ba, spaghetti ta dafa mana harda kifin gongoni da take d'ibawa su kakata kayan a nan data bud'e wani kwali taga duka shine a ciki.


Kamshin girkin yauma ya cika ko Ina har ta gama, tana gamawa ta samu tire ta zuzzubawa yaran gidan ta ce duk su zauna su karya iyayen su kuma a kwano ta zuba na kai musu suna ta cika da batsewa bakinciki kaman su mutu.



Baban mu yazo fita kaman yanda ya saba yaga yara suna ta kai loman taliya baji ba gani wasun su kuma suna kokawa akan kifin da yake ciki.


"Kai uban wa ya baku abinci da sassafen nan kuke mana hayaniya a gida" Baba ya tambaya yana kara matsowa kusa dan tabbatar da abinda idon shi ya gani gaskiya ne ko akasinta .


"Innar Zareefa ce ta bamu" cewar Ibrahim d'an gidan Inna Asabe.


"Jiya ma shinkafa da miya ta zuba mana harda nama" shima musa d'an gidan Gwaggo Aisha ya kara akai.


Cike da mamaki Baban mu ya ce," ita Bintun ce tayi girki harda nama?" Yana magana ne yana kallon k'ofar d'akin mu.


Fasa fitan yayi ya koma d'akin shi yana tunanin ta ina zai fara rarrashin Inna ta zuba mishi wannan kayan dad'in shima.
[8/31, 6:05 PM] Ummee Yusuf: 🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹
🦚🌹
🦚
*BA SONTA NAkE BA*
🦚
🦚🌹
🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹

_A story about love and sacrifice._



_Written by_ *UMMEE YUSUF*
_(Maman Yusuf)_


_*From The Fantastic Writer of*_

```FARHAT```
```KAMACE```
```UKUBAR KISHIYATA```
```UMMU~SALMA```
```UWANI```

*_And now_*


*_BA SONTA NAKE BA_*



*✍✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾

*wΜΆΜΆΡ” Ξ±rΜΆΜΆΡ” Π²Ρ”Ξ±rΜΆΜΆΡ”rΜΆΜΆ'sΜΆΜΆ ΟƒfΜΆΜΆ sΜΆΜΆΟƒ gΜΆΜΆΟƒlΜΆΜΆdΜΆΜΆΡ”nΜΆΜΆ pΜΆΜΆΡ”nΜΆΜΆ*πŸ–Š
*wΜΆΜΆΡ” wΜΆΜΆrΜΆΜΆΓ­tΜΆΜΆΡ” Ξ±sΜΆΜΆsΜΆΜΆΓ­dΜΆΜΆΓ­ΟƒuΜΆΜΆsΜΆΜΆlΜΆΜΆΡ‡ pΜΆΜΆΡ”rΜΆΜΆcΜΆΜΆΡ”Γ­vΜΆΜΆΡ” nΜΆΜΆΟƒ pΜΆΜΆΞ±Γ­nΜΆΜΆ,*
*sΜΆΜΆΟƒ mΜΆΜΆΞ±gΜΆΜΆΓ­cΜΆΜΆΞ±lΜΆΜΆ ΟƒuΜΆΜΆrΜΆΜΆ cΜΆΜΆrΜΆΜΆΡ”Ξ±tΜΆΜΆΓ­vΜΆΜΆΡ” gΜΆΜΆΟƒlΜΆΜΆdΜΆΜΆΡ”nΜΆΜΆ pΜΆΜΆΡ”nΜΆΜΆ* ✍ *,Π²Ρ”hΜΆΜΆΟƒlΜΆΜΆdΜΆΜΆ ΟƒuΜΆΜΆrΜΆΜΆ wΜΆΜΆΟƒrΜΆΜΆdΜΆΜΆsΜΆΜΆ.Ξ± pΜΆΜΆrΜΆΜΆΟƒdΜΆΜΆuΜΆΜΆcΜΆΜΆtΜΆΜΆ ΟƒfΜΆΜΆ ΟƒuΜΆΜΆrΜΆΜΆ pΜΆΜΆΡ”nΜΆ*ΜΆ πŸ–Š *,sΜΆΜΆΞ±vΜΆΜΆΟƒuΜΆΜΆrΜΆΜΆ ΟƒuΜΆΜΆrΜΆΜΆ wΜΆΜΆΟƒrΜΆΜΆdΜΆΜΆsΜΆΜΆ, fΜΆΜΆΟƒrΜΆΜΆ Γ­tΜΆΜΆ wΜΆΜΆΓ­lΜΆΜΆlΜΆΜΆ* *cΜΆΜΆΞ±uΜΆΜΆsΜΆΜΆΡ” Ρ‡ΟƒuΜΆΜΆ nΜΆΜΆΟƒ pΜΆΜΆΞ±Γ­nΜΆΜΆ.*

Yin Kabbara tare Da Kowace Tsakuwa Yayin Jifan Jamra.
Annabi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya kasance yana yin kabbara tare da kowace tgsakuwa idan ya jefi jamrori uku. Sannan sai ya yi gaba kadan ya yi addu'a yana mai fuskantar alkibla, ya daga hannayensa biyu yayin addu'ar. Yana yin haka ne bayan jifan Jamra ta farko da ta biyu. Amma bayan jamratul Akaba (jamra ta karshe), sai ya yi jifan kawai, ya yi kabbara tare da kowace tsakuwa, sannan ya tafi; ba ya tsayawa ya yi addu'a a wajenta.


*~INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?~*

*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*


_Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samun wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook_. πŸ‘‡


https://www.facebook.com/101594048306878?referrer=whatsapp


_Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana Ζ™ara mana Ζ™arfin gwiwa a wajen rubutu._


*5*

Baba ya kasa zama yayi a d'aki sai safa da marwa yake,sai yayi kaman zai kira wani kuma sai ya fasa can dai yaja wani dogon tsaki shi kad'ai yana," in banda b'atawa kaina lokaci nake ba ita Bintun yaushe har tayi wani abin kanta zan tsinka kaina gaban yarinya k'arama" yana magana ne shi kad'ai tare da neman hanyan fita.

Ta gefen ido yake kallon yaran da suke ta buduri da taliyarsu bakin nan duk mai yasa kai ya fice.



Yana fita teburin mai shayi ya tafi kaman yanda ya saba ya bayar da naira d'ari yace a bashi shayi empty na naira ashirin da bredi na hamsin,ana bashi canji akwai mai kosai a gefen mai shayin itama ya sayi na talatin a wajan ta ya samu waje a rumfar mai shayin ya fara karyawa.


A da in yana cin wannan had'in ji yake kaman mai cin kaza amma yau sai yaji babu taste sam sai tuno taliyan nan daya sha mai da kifin gongoni yake,kaman dole haka ya rinka cuccusawa har ya gama ya tashi ba dan dad'i ba.



A gida kuwa muna gama karyawa da Inna ta tace mu shirya ta kaini makaranta kada wani abu yazo ya fad'awa kud'in,



Muna gama shiryawa muka kama hanyan ainihin makarantan mu na da wato *YERWA PRACTICE* akwai jss a ciki daga 1 zuwa 3, cikin ikon Allah komai yazo mana da sauki ba kaman yanda Inna ta zata ba domin kud'in registration da kud'in PTA duka dubu biyu suka karb'a,daga nan uniform,takalmi,jaka,takardu duk kyauta aka bani kuma principal yace gobe in fara zuwa domin har an fara karatu.


Cike da farinciki muka kama hanyan gida, a hanya sai da mukayi 'yan cefanen mu da kud'in hannun mu sai dubu uku ya rage muka dawo da kaya niki-niki a hannu.



Gwaggo Aisha tana yiwa Hajara fad'a a tsakar gida kasancewar Inna Asabe ma ta fita,tana ganin mu tayi shiru sai rarraba ido take alaman basu da gaskiya,mu dai bamu bi ta kan su ba muka wuce d'aki suka bi ledojin hannun mu da kallo.



Muryan Gwaggo Aisha ya cika gidan tana yiwa Hajara masifan me take bata fito ta tafi tallah ba gashi har azahar tayi,na fito da buta a hannu na dan zagawa makewayi muka had'a ido da Gwaggo Aisha ta gallah min wata muguwar harara,niko dan in cusa mata bakinciki sai nayi mata dariya dama in ina son kullar da ita haka nake yi.



Ai kuwa ta hau yanda ya kamata ta hau zagina harda Inna ta da bata san wainar da ake toyawa ba,ni kuwa ko a jikina na shige bayan gidan na kama ruwa na fito tsakar gidan na fara alwala ita kuma bata fasa zagin nawa ba,dana lura bata da niyyan dainawa nayi mata gwalo amma sai na fake da cewa Jameela da take kusa da ita tayi min nima na rama.



Ban gama wanke d'ayan kafa na ba naga ta rarumo murfin tukunya da yake kusa da ita ta jefi ni dashi, Allah ya taimake ni kamin ya karaso na gauce nayi d'akin mu da gudu ina dariya.



Had'iye dariyan nawa nayi ganin fuskar Inna ta babu alaman wasa ta ce," wai ke wace irin yarinya ce Zareefa,ban hana ki kula su ba ko akwai sa'ar ki a ciki,bayan haka duk matan Baban kine saboda babu abokin wasan ki a cikin su tsakanin ki dasu shine girmamawa".



Jiki a sanyaye na ce ," kiyi hakuri Inna ba zan sake ba dama ni bada ita nake ba nida Jameela ne"


"Naji ki kiyaye bana son neman magana" ban kara cewa komai ba na fara sallah na a zuciya ta kuwa banga zan kyale ta ba in ta min wannan shegen kallon tunda ba wani laifi nayi mata ba.



Da yamma Inna ta fito tayi tuwan ta na shinkafa da miyan yakuwa da yaji biscuit bone da wadacaccen gyad'an miya, jin yauma kamshi ya cika gidan yara suka fara tsallen murna suna," yauma Innar Zareefa zatayi mana kayan dad'i" iyayen su na hantaran su amma basu fasa ba.



Yauma d'aki nabi su da abincin ba wanda ya kalle ni balle inji sun ce basa cin abincin da aka same ta ta haramtaccen hanya.



Da wuri yau Baban mu ya dawo gida tare da tsammanin an girka kayan dad'i irin na d'azu,yana saka kafa a gidan kamshin abincin ya mishi maraba wanda sai da ya had'iye yawu yana bin tsakar gidan da kallo,yaji tsit kaman babu kowa a gidan saboda kowacce tana d'aki da yaran ta suna kwasan gara.



Da gangan ya d'aga murya wai dan Inna taji ta aiko mishi nashi ya hau fad'an an watsar da kaya a hanya amma aka rasa wanda zai kula shi.


Yana nan tsaye yanayi Ibrahim d'an gidan Inna Asabe ya fito da kwanukan da suka ci abinci yana kokuwa da kashi tare da tand'e yatsu.



"Kai zo nan,zo ka kwashe kayan nan" ya yafito Ibrahim da hannu yazo yasa hannu ya kwashi kwanuka guda biyu da suke gefe har ya juya zai tafi ya rike shi murya kasa-kssa ya ce," kai yauma Bintun ce tayi girkin" gyad'a mishi kai Kai yayi dan santin kashin ya hana shi magana.




Maida hankalin shi yayi kan d'akin mu da muka sauke d'an yalolon labulen mu, juyawa yayi ya shiga d'akin shi ya zauna jiran ko yauma za'a kawo mishi.



Ya kai kusan rabin awa zaune yana kallon k'ofa amma ko motsin mutum bai jiba balle yaga mutum,tsaki yaja a karo na ba adadi ya mike ya fito tsakar gida tare da kama hanyan waje,bukutin roba na Maman Dije da yake ajiye a gefe akai ya sauke haushin sa sannan ya fita,ji kake kararass ya fashe sakamakon harbi daya kaiwa bucket din da k'afa.



Fita yayi yana ta zage-zage shi kad'ai dole ne yasan yanda zaiyi ya shawo kan Inna ta kamin girkin ta ya zagayo.



Da washe gari ba girkin Inna ta bane d'an haka indomine ta girka min na karya dashi ta bani talatin kud'in tara na fita makaranta cikin tsantsan farinciki domin haka naga sauran yara ake musu nima yau anyi min.



Sosai a ranan na mayar da hankali na nayi karatu tsabani da,karfe d'aya dai-dai aka tashe mu na kama hanyan gida.


Tun daga zaure na fara jin muryan Gwaggo Aisha tana zagina tare da aibata ni ga dukkan alamu kuma Baban mu take fad'awa,a jikin bango na makure naki karasowa sanin halin Baban mu ya kware a rankwashi.


"Munafuka daina kallo na

2 Comments On BA SONTA NAKE BA
avatar
maryam-4

2 years ago

Reply

How to download it

avatar
daiy

2 years ago

Reply

replying to @maryam-4 you must sign in in order to download

Please Login or Register in order to submit comment