Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kalli screen d'in ya kara tabbatarwa eh zafard'in ne sannan ya mayar kunnen shi.

"Wacece da wannan sunan ko cikin relatives d'in ka na kauyen ne aka samo maka wata". Sadiq ya tambaya.

"God for bid, bakin ka ya sari d'anyan kashi mugu kawai meya had'a ni da 'yar kauye, wannan village girl da kuka had'a ni da ita mana Abba ne ya saka mata wannan funny name d'in koda yake it suits her" ya karasa yana kara saka dariya dan d more zai fad'i sunan d more yake saka shi dariya.

"Ikon Allah, amma ban san Kai cikakken d'an rainin wayo bane sai yau, yarinyan da ta sace maka zuciya at first sight shine zaka ce mu muka nemo maka ita?"

"Damn it wai har sai yaushe zaka fahimta ni *BA SONTA NAKE BA* kuma kafi kowa sanin why I will marry her amma ba zaka daina fad'a min rubbish ba, anyway phone no ta nake nema in fad'a mata sakon Abba" yana kawo nan a zancen shi katse kiran yayi jifa da wayan kan gadon shima yabi shi ya kwanta ringine yana huci shi ala dole an b'ata mishi rai.

Ko minti 5 baiyi da kwanciyar ba yaji karan shigowan sako wayan shi, sai da yaja tsaki sannan ya bude sakon ba dan komai ba sai dan yaga daga Sadiq ne.

Number kad'ai ya gani babu rubutu hakan ya tabbatar mishi da number na daya nema ne ya turo mishi, sai da ya fara saving sannan ya kira ni lokacin muna zaune da Inna tana had'a min tea dan tace inzo mu karya nace bana jin yunwa, shine ta shiga had'a min wai ko shi kad'ai in sha.

Inaji har tagama ringing ban d'auka ba ganin sabon no ce, kara kira yayi Inna ta dakata da had'a shayin tace min " Wai ke ba wayar ki ake kira bane?"

"Inna sabon number ce babu suna" na amsa mata a sanyaye.

"Ko ba suna ai zaki daga kiji ko waye ko?" Inna ta sake fad'a min.

Koda na juya da niyan daukawa naji ya katse dan haka banyi magana ba nayi shiru Inna ma bata kara cewa komai ba ta cigaba da had'a min.

Miko min tayi bayan ta gama harda 🍞 tace in gusura ko kad'an amma na ce mata sai anjima, sama-sama itama ta karya bata ci wani abu dayawa ba ta ture gefe duk gani na cikin rashin walwala yana hana ta sukuni itama.

Gwaggo Aisha sai bayan fitan mu da kusan minti goma ta tashi ta zauna tana goge fuskan ta da hijabin da Hajara ta lullub'a mata ba hawayen amma duk ta jike da zufa.

Harara ta zabgawa Hajara da take ta jera mata sannu tayi kana tace" ke dai Allah yayi magulmaciya da kinibibi in banda gulma waye yace ki gaiyato min wacan manufukar matan can da 'yarta fitinanniyan nan?"

Baki a hangame hajara take kallon ta tace " haba Umma in baki gode musu ba ba zaki tsine musu ba, ihu fa kike tayi kina birgima kan an k'ona abinda kika binne dan su cutu ita da yarta amma matan nan ta zauna tana tofa miki addu'oi ita da yarta har kika samu lafiya, mutane nawa ne a gidan nan babu Wanda yazo kan ki sai su hatta Baba ma tafiyan shi yayi ya bar ki....."

"Ki min shiru wawuya kawai mai fifita uwar wasu kan uwar ta koda yake ba laifin ki bane duk asirce ku tayi Kuma wallahi ba zan saduda ba sai na warware duka mugun kulli da tayi a cikin gidan harda Baban naku..."

Shiru tayi tana wur-wurga ido kaman me neman wani abu, a zabure ta mike tana " kan bala'i in na yarda shigiya nake" tana gama magana ta fice fuuu zuwa tsakar gida.

Cikin daga murya ta fara magana" ina kake ka fito shanyayye kawai wallahi na gaji da rashin adalci da kake nuna min a cikin gidan dole ne ayi abu d'aya ehe"

"Ke Wai wace irin dakikiya ce mara hankali meya faru da zaki zo tsakar gida kinawa mutane ihu" cewar Abba kenan daya tsaya daga nesa yana kallon ta.

"Eh dole ka kira ni da sunaye da kaga dama Amma kada ka manta ko rigar sakawa na kirki baka da ita lokacin da na aure ka sai yau dan ka samu abu zaka wukanta ni, ace Wai gini zakayi a gidan baka fara ta kaina ba nida nake uwargidan ka sai wancan jamammiyar matar taka".

"Kinga dakikancin ki da nake fad'a ko, in kika ga abu tambaya ya kama kiyi ba Wai kiyi tayiwa mutane ihu ba, toh kudin daga hannun mijin da zai auri yar albarka ya fito kinga kuwa dole afara gyara mata b'angaren ta tunda auren ma ba zai fi wata d'aya ba".

Ras-rass naji zuciyata ya tsinke duk da na san da zancen amma jinta a bakin Baban mu yafi daga min hankali, a zabure Inna ta mike tana girgiza kai tana magana " ba zai yiwu ba wa zai aurawa 'yata ba tare dasani na ba,ba zan yarda da wannan cin fuskan ba zan iya jure ko wani irin cin mutunci amma banda kan 'yata ba"
[1/26, 7:12 AM] Golden Pen Writer's Assoc: 🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹
🦚🌹
🦚
*BA SONTA NAkE BA*
🦚
🦚🌹
🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹

_A story about love and sacrifice._

_Written by_ *UMMEE YUSUF*
_(Maman Yusuf)_

_*From The Fantastic Writer of*_

```FARHAT```
```KAMACE```
```UKUBAR KISHIYATA```
```UMMU~SALMA```
```UWANI```

*_And now_*

*_BA SONTA NAKE BA_*

✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍

*wΜΆΜΆΡ” Ξ±rΜΆΜΆΡ” Π²Ρ”Ξ±rΜΆΜΆΡ”rΜΆΜΆ'sΜΆΜΆ ΟƒfΜΆΜΆ sΜΆΜΆΟƒ gΜΆΜΆΟƒlΜΆΜΆdΜΆΜΆΡ”nΜΆΜΆ pΜΆΜΆΡ”nΜΆΜΆ*
*wΜΆΜΆΡ” wΜΆΜΆrΜΆΜΆΓ­tΜΆΜΆΡ” Ξ±sΜΆΜΆsΜΆΜΆΓ­dΜΆΜΆΓ­ΟƒuΜΆΜΆsΜΆΜΆlΜΆΜΆΡ‡ pΜΆΜΆΡ”rΜΆΜΆcΜΆΜΆΡ”Γ­vΜΆΜΆΡ” nΜΆΜΆΟƒ pΜΆΜΆΞ±Γ­nΜΆΜΆ,*
*sΜΆΜΆΟƒ mΜΆΜΆΞ±gΜΆΜΆΓ­cΜΆΜΆΞ±lΜΆΜΆ ΟƒuΜΆΜΆrΜΆΜΆ cΜΆΜΆrΜΆΜΆΡ”Ξ±tΜΆΜΆΓ­vΜΆΜΆΡ” gΜΆΜΆΟƒlΜΆΜΆdΜΆΜΆΡ”nΜΆΜΆ pΜΆΜΆΡ”nΜΆΜΆ* ✍ *,Π²Ρ”hΜΆΜΆΟƒlΜΆΜΆdΜΆΜΆ ΟƒuΜΆΜΆrΜΆΜΆ wΜΆΜΆΟƒrΜΆΜΆdΜΆΜΆsΜΆΜΆ.Ξ± pΜΆΜΆrΜΆΜΆΟƒdΜΆΜΆuΜΆΜΆcΜΆΜΆtΜΆΜΆ ΟƒfΜΆΜΆ ΟƒuΜΆΜΆrΜΆΜΆ pΜΆΜΆΡ”nΜΆ*ΜΆ *,sΜΆΜΆΞ±vΜΆΜΆΟƒuΜΆΜΆrΜΆΜΆ ΟƒuΜΆΜΆrΜΆΜΆ wΜΆΜΆΟƒrΜΆΜΆdΜΆΜΆsΜΆΜΆ, fΜΆΜΆΟƒrΜΆΜΆ Γ­tΜΆΜΆ wΜΆΜΆΓ­lΜΆΜΆlΜΆΜΆ* *cΜΆΜΆΞ±uΜΆΜΆsΜΆΜΆΡ” Ρ‡ΟƒuΜΆΜΆ nΜΆΜΆΟƒ pΜΆΜΆΞ±Γ­nΜΆΜΆ.*

*Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.*

Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa.

*INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?*

*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*

Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buΖ™ata namu daga farko.

https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/

Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana Ζ™ara mana Ζ™arfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa.

*Bismillahir Rahmanir Raheem*

*23&24*

"Na sha had'iye wulaΖ™anci da cin fuska daga wajan sa da matan shi, amma wallahi kada wani yace zai tab'a min ke anan ne zasu ga fushi na". Tana magana ne a wannan lokacin tare da saka hijabinta ta kama hanyan waje.

Da gudu nima na miΖ™e ina kwala mata kira akan kada ta fita wajan nasu amma ina har ta fice daga d'akin, bakin gado na koma na zauna dabas ina jin zuciya ta na suya tsanar bawan Allah nan na ninkuwa a cikin ta ba dan komai ba sai dan yanda naga tashin hankali da bacin rai shimfud'e akan fuskan ta wanda zan iya cewa tunda aka haife ni ban tab'a ganin koda kwatancin shi a tare da ita ba.

Gata kuma ta fita sa-in-sa da Baban mu da Gwaggo Aisha shima wannan ban tab'a ganin Inna ta kula kowa ba a gidan,koda kuwa me zasu ce mata ko suyi mata bata tankawa kowa sai dai ta shige d'aki tayi zaman ta,nice dai a baya nake dan kula su kasancewa ta bana iya wuce tayi in dai na fad'a ne sannan kuma na tsani wulakanci da raini wanda duk Gwaggo Aisha tayi degree akan su.

Sosai take min fad'a kaman ta doke ni akan kula su da nayi amma yau itace dakanta ta fita yau; " Innalillahi wa inna ilahi raji'un" na zauna maimaitawa ina kuka, wannan wani irin mutum ne shi tunda ya shigo rayuwa ta komai kara cakub'ewa suke " I hate that ugly creature" nace ina Kara fashewa da sabon kuka.

Naci kuka na na more sai dai ga mamaki na banji motsin Inna ta a tsakar gidan ba balle inji muryan ta, Baban mu ma na daina jin muryar sa sai Gwaggo Aisha da take ta ihun ta ita kad'ai.

Shirun da naji yayi yawa ne yasa na mike a hankali na l'eka waje bayan na yaye labule kad'an, tsakar gidan babu kowa da alamu Gwaggo Aisha tayi ta gaji ta koma ciki sai masu aiki da suke ta aikin su sai kanne na da suke wasa a gefe,toh ina Inna ta ta tafi???

Ras-ras naji zuciyata ta harba da karfi kar dai yaji Inna tayi, abinda tunda akayi mata aure bata tab'a yi ba.

Cikin mutuwar jiki na koma d'aki na zauna ina tsiyayan hawaye masu zafin gaske, ban jima da zama ba naji waya ta ta fara ringing ko juyowa banyi ba balle in sa ran zanyi answering, haka ya gama ihun sa ya daina.

Kwanciya ta nayi akan gado ina rokon Allah yasa ba yajin tayi ba cos I can't imagine myself in dis house without my inna, wayance ta fara ringing Kuma cikin gajiyawa na d'auka ina kallon no data kasance special in ban manta ba kaman d'azu dashi aka jera min 2 missed calls.

Saura kad'an ya katse na daga kai kunne na nayi shiru ba tare da nayi magana ba, shiru naji shi wanda ya Kiran ma yayi bashida niyyan magana,mun kusan minti 2 a haka ina shirin cire wayan a kunne na kaman yana kallo na yace;

"Who do you think you are? Da har zaki dinga ignoring calls na, be very careful with whom you are dealing with or akwai lokacin da yana zuwa da zakiyi regretting duk abubuwa da kike".

Yawu mai d'aci na had'iye da ya makale min a makokoro ina sauraran bakaken kalaman sa da suka fi wuta zafi, sarai na gane muryan nashi wanda kullum in yana magana zaki jita cike da isa da kasaita.

Bai san cewe nima a wuya nake ba tunda har ya zama shine silan fara fitan Inna a gidan auren ta da sunan yaji, tsab zan juya mishi duk rashin mutunci da nake dauke dashhi dama nima ba tayar baya bace.

Muryan shi ce ta maido ni hankali na naji yana cewa; " 'yar Mallam kada kice wai saboda na damu da kene nake ta jera miki kira haka, nooo ko daya I just want you to tell Mallam Abbana zasu zo anjima". Kit naji ya katse kiran ba tare da ya jira yaji me zance ba.

" 'yar Mallam!! " Na maimaita sunan a fili "kunbu in na yarda shegiya nake nice 'yar Mallam din, wallahi sai na koyawa dan raini nan hankali ni har akwai wanda zai takale ni in kyale shi never".

Tsakani da Allah na zage ina masifata ni kad'ai kaman yana gaba na, danna mishi kira nayi ina jiran ya daga nima in rama amma har ya katse bai daga ba, ban hakura ba sai da na jera mishi missed calls 5 bai daga ba, cillar da wayan nayi na fashe da kuka sosai dan jin zuciya ta nake kaman ta fashe da ban samu na rama ba dama can ina da wannan halin tun ina karama na taso da abuna, cikin 'yan gidan mu babba ko karami ya tab'a ni sai na rama hankali na yake kwanciya, har duka Inna ta sha yi min akan in daina amma na kasa saboda a jini na yake. Wannan dalilin yana daya daga cikin dalilan da Gwaggo Aisha take min zazzafan tsana.

Inna kuwa tana fita a d'aki bata ko kalli inda Baba da Gwaggo Aisha suke ba ta fice zuwa gidan su, suma dai basu lura da ita ba duk hankalin su yana kan fad'an da suke.

A tsakar gida ta samu Maa da kanwar ta wacce suke kira da Ya ma'aji suna hiran su na 'yan uwan taka gwanin sha'awa, da sallama ta shiga sai dai bata tsaya taji amsawar sun ba ta shige d'akin Maa.

Da ido duk suka bita har ta shige cikin d'aki ba tare da ta tsaya wajan su ba kaman yanda ta saba ba ko kuma ince yanda ya kamata ba, Ya ma'aji ta dubi yayar ta tace" Yaya da alamau yarinyan nan tana cikin damuwa,dubi yanda ta shigo gidan nan hankali tashe, ni wallahi wannan kaddararren auren nata da kina jin shawara ta da tuni ta rabu da shi haba yarinya tana 'yar karamar ta amma kullum cikin tashi hankali take dubi yanda duk ta motsare,ga fitinan miji gana kishiyoyi da wanne zata ji" ta karasa da matukar fushi a fuskarta domin ita halin ta daban dasu Maa fad'a ne da ita sosai ga rashin hakuri.

Murmushi mai sanyi Maa tayi mata tana girgiza kai tace "kai ma'aji akwai ki da daukan abu da zafi baki san halin yaran yanzu ba abu bai kai ya kawo ba zasu d'auke shi da zafi........".

"A'a Yaya kada ki raina hankalin ta na tabbata ko ke da kika fimu sanyin hali aka ki gidan nan nata zasu kure ki,bari inje inji meya faru" tace tana mikewa tare da nufan d'akin da Inna take ciki.

A kan carpet da yake shimfid'e a tsakar dakin ta samu Inna ta had'a kai da giwa tana kuka kasa kasa.

Dafa ta Ya ma'aji tayi yasa ta d'ago da kai suka had'a ido tayi mata murmushi ita kuma kukan ta kara fashewa da shi cikin muryan kuka ta fara magana"Ya ma'aji ku ceci Zareefa dan Allah ku cece ta ni na yarda suyi min duk abinda suke so amma dan Allah su kyale ta tayi rayuwa mai yanci da farin ciki, yarinya ce k'arama bata san rayuwa ba dan Allah kada su jefa rayuwar ta cikin.........."

"Ya isa haka ya isa, ki natsu ba abinda zai faru da Zareefa muna tare da ke kuma Allah yana tare da mu dan haka ki kwantar da hankalin ki, ki min bayanin me yake faruwa?. Ya ma'aji ta katse Inna da take magana cikin fitan hankali.

"Wai aure zaiyi mata kuma ni baiyi shawara dani ba ban san waye zai bawa ba,kawai yau da safe ya shigo da masu gini wai zai canza ginin gidan zuwa na zamani kuma yana so ayi da wuri kuma a bangare na aka fara saboda auren wai ba zai wuce wata d'aya ba. ni abinda yake bani tsoro na san halin shi in game da kud'i ne komai zai iya yi......."

"Ba 'yar sa bace ko saida ta zaiyi ina ruwanki " suka ji muryan Maa a bakin k'ofa wacce da alamu ta dad'e tsaye a wajan,duk kallon ta suka tsaya yi har ta shigo ta samu waje ta zauna tana fuskantar Inna.

"Kin bani mamaki Bintu da har zaki tada hanklin ki kiyi abinda baki tab'a yi ba wato kawo karan miji, yanzu da kika kwashi kafa kika zo min gida menene a zuciyar ki ko so kike ni in kira shi ince bashi da daman zabawa 'yarsa mijin aurex ko kin manta addinin musulunci ne ya koyar da hakan...."

"Maa na sani wallahi na sani amma kema kin san halin shi zai iya yin komai akan kud'i, sannan ya kamata ya shawarce ni ya fad'a min abinda yake faruwa ba wai inji maganan ta sama ba" Inna ke fad'an haka cikin wani irin murya mai nuna tsananin halin da take ciki.

"Menene halin sa Bint? koma wani irin hali ne dashi ba zai tab'a cutar da Yar cikin sa kuma maganan shawara da kike so yayi dake, wani shawarwan zaiyi bayan ke kan ki a karkashin sa kike.

Tashi ki koma d'akin ki ki cigaba da ibadan ki cikin kwanciyar hankali kaman yanda kika saba sannan kija yarinyan nan a jikin ki,ki kwantar mata da hankali kiyi mata tuni da duk wanda yayiwa iyayen sa biyayya to tabbas zai ga alkhairi a cikin rayuwar sa, kada ki kuma yin abinda zai tashi hankalin ta, duk halin da zata shiga in fana ganin ki a kusa da ita zata ji sanyi,

Sannan ke kuma ki bita da addu'oin zaman lafiya da farinciki Mai daurewa ya tabbata a gidan ta, insha Allah sai ts samu fiye da yanda muke hasashe".

Inna share hawayen ta take wasu na zubowa bata son musu da mahaifiyar ta amma ta san halin Baban mu sai shi, mikewa tayi da niyyan komawa Ya Maaji da bata da hakuri ga zafin zuciya ta bud'i baki da nufin zatace wani abu Maa tayi saurin dakatar da ita ta hanyan daga mata hannnu, kawar da kai gefe tayi tana cize lebe na haushin an hana ta magana.

"Ya Maaji na tafi ki gaida su Bayuram,Maa na gode Allah ya saka da alkhairi ya baki nisan kwana insha Allah zanyi kaman yanda kika ce" Inna ke fad'an haka tana gyara hijhabi dake jikinta.

Ya Maaji da duk takaici ya hana ta saka baki cikin maganan nasu da taga Inna ta juya zata tafi tayi yunkurin magana nan ma Maa bata bata dama ba ta kara daga mata hannu alaman tayi shiru.

Shirun tayi tana kallon Inna har ta fice sannan ta dawo da hankalin ta kan 'yar uwar ta tace " haba yaya yanzu sanyin halin naki ya kai kija baki kiyi shiru a cuci 'yar jikar ki guda d'aya tilo, ni dai wallahi tafiya ta zanyi ba zan zauna bakinciki ya kashe ni ba"

Hijabinta ta shura tayi hanyan waje, Maa tana ta kwala mata kira bata yarda ta juyo ba balle ta amsa, Dan murmushi Maa tayi tana girgiza kai tare da mata addu'a Allah ya rage mata wannan zafin zuciyan.

Lokacin da ta dawo bacci ya d'an sace ni ban san ma ta dawo ba sai cikin bacci naji kaman kuka harda shashheka, a hankali na bud'e ido na dan tabbatarwa, bayan ta na gani tana ta kuka tsakanin da Allah wanda tun tasowa ta banga ko kwatanci sa tayi ba.

Tausayi da kaunar tane naji yana bin ko ina a cikin jinin jikina saboda na san duk a kaina ta tada hanklin ta kan auren da taji Baba yace zai min, banida zab'i dole in kwantar da hankali in nuna mata babu komai ta wajena ko zata samu natsuwa, wannan dalilin yasa naki fad'a mata tun farko kenan amma ba yanda zanyi dole ne ta sani.

D'an motsi nayi yanda zata ji, aiko nan da nan ta shiga share hawayen sannan ta d'an juyo sai taga ido na a rufe, bakin gado tazo ta zauna tana shafa min gashin kaina, jin ta daina kuka yasa na bud'e ido na kaman yanzu ne na tashi daga baccin.

Murmushi ta sakar min tace " bacci kika koma kenan?" Gyad'a kai na nayi nima ina maida mata martanin murmushin.

Ina ta jira inji ko zata min maganan auren amma naji tayi shiru sai jana take da hira tana bani labaran ban dariya, nima dan in kwantar mata da hankali yasa na saki raina nayi ta dariya amma can kasan raina cike ya tab da damuwa.

Bayan sallah magarib sai ga Abban Zafar da tawagar sa a kofar gidan mu Kuma sun taki sa'a Baba yana nan bai tafi ko ina ba, Baba duk ya rikice ya susuce ganin manyan masu kud'in garin maiduguri a kofar gidan sa kuma da sunan sun zo had'a zuri'a dashi.

Makotan mu biyu ya kira sannan ya kira Baban Dije wanda zance shi ya jagoranci komai ya hana Baban mu gudun kada ya kwafsa ko ya saki layi, hakan da yayi ya taimaka kuwa dan shi Abban Zafar tunda yaji ance Mallam ya zata Baban Mallamin ne da gaske.

Wata 2 ciff aka saka na biki mu aka rabu cikin mutunci bayan sun sauke carton carton na minti da chewing gum da goro na rabawa yan uwa, Abba yaja Baba gefe ya bashi check na wasu kud'ad'e kan yayi hidimar biki da gida sannan ya d'aura da basa bukatan a kaini koda cokali guda d'aya su zasu tanada min komai su kawai surka suke bukata.

Murna da Baba yake ji kaman ya daka tsalle amma ganin yanda Baban Dije ya kama kai yake musu magana shima hakan ya kwaikwaya har yayi mishi sallama ya shiga mota driver yaja suka tafi.

Muna zaune sai gani mukayi anata shigowa da kwalaye kaman za'a bud'e shago, kowa kallon kayan yake tare da neman karin bayani sai dai babu mai bamu, sai da aka gama shigowa da kayan tass sannan Baba ya shigo yana jan banban rigan shi a kasa cikin d'aga murya ya fara magana yanda kowa na gidan zai ji.

"Allahu yayi Allahu yayi!!! Ina kuke mutanen gidan nan kowa ya fito yaga abin arziki daya same mu, kayan saka rana ne na 'yar albarka, wata 2 kacal iyayen ango suka ce a saka dan suna bukatan ayi auren da wuri.


Ba wayan nan kayan kawai ba har takardan karb'an kud'i na banki sirikin nata ya bani sannan yace basa bukatan mu kai ta koda cokali su zasuyi mata komai...."

"Aaaaaaayyyyyyiiirrrrrrrr!!! Inna Asabe ce ta rangad'a wannan gud'a cikin farinciki tace" Masha Allah 'ya tayi goshi duk abubuwa daka lissafo duk na saka rana ne ina ga Allah ya nuna mana ranan auren ba magana....."

"Aikin banza aikin wofi kowa yaga dama zaiyi ai tunda abin shige-shige ne" Gwaggo Aisha ta katse ta, Inna Asabe dai bata kula ta sai shewa suke da Allah ya sanya albarka suke da Mama Dije.

Tashin hankali sosai na shiga da ganin kayan da muka maganan Baba duk da na san da zancen, kokarin dannewa nake saboda kada in karawa Inna tashin hankali amma na kasa daurewa,kuka na fashe dashi sosai har jikina yana rawa na shiga d'aki da gudu na fad'a kan gado ina mai cigaba da kuka mai tsuma zuciyan mai sauraro.

.
Jiki a sanyaye Inna ta biyo baya na ta zauna a gefena ta kura min ido itama idon ta na cikowa da hawaye amma ta hana su zubowa, tana rayawa a ranta inama zata iya dakatar da wannan auren da tuni ta dakatar da wanne zan ji cikin lokaci d'aya na had'u da jarrabawan rayuwa ga rad'ad'in rabuwa da Yaya na bai bar ni ba ace kuma ga auren da bamu san daga ina ya fito ba.

Sai dai bata da zab'i dole ne ta karfafa min guiwa inyiwa mahaifina biyayya kaman yanda itama tayiwa nata mahaifin, gyara zama tayi tana gyaran murya sannan ta fara magana cikin rarrashi" wani lokacin kuka bashi ne waraka ba ga matsaloli na rayuwar mu ba,sai dai mu kanji sauki da rad'ad'in da zuciyoyin mu suka tsinci kan su a ciki dan haka ba zan hana ki kuka ba kiyi Zareefa kema ko zaki ji sauki.

A al'adance da kuma addinin musulunci ya bawa mahaifi daman zab'awa 'yar shi miji daya ga ya dace da ita bi ma'ana ya yarda da addinin shi da kuma tarbiyan shi dan haka kada kiyiwa mahaifin ki mummunan fahimta domin ba zai tab'a Kai ki inda zaki wulakan ta ba kuma albarkacin biyayya da kikayi mana Allah zai saka miki da mafi alkhairi ko kuma da abinda baki tab'a zato ba balle tsammani.

Abu d'aya da nake son ki tuna wannan auren ko dan Abdulbasit ya kamata ki rike shi da hannu bibbiyu saboda na san duk inda yake zai ji cewa za'a miki aure,kn ga kuwa kin nuna mishi zaki iha rayuwa ko babu shi sannan zai fahimci cewa kina da masoya ba shi kad'ai ne gare ki ba".

Tun ina kuka kasa-kasa har na daina nayi shiru ina sauraron kalaman Inna, ya zanyi dole ne

2 Comments On BA SONTA NAKE BA
avatar
maryam-4

2 years ago

Reply

How to download it

avatar
daiy

2 years ago

Reply

replying to @maryam-4 you must sign in in order to download

Please Login or Register in order to submit comment